SARAN BOYE COMPLETE

Anan hankalina ya tashi danaji abinda yace kuka na fara yi.masa inaso na Gaya masa gaskiya abinda ke faruwa bakina yamin nauyi Kamar an dinke inaji Ina gani yace na tashi na tafi idan an kwana biyu zai saka a cikin yaransa wani ya rakani na mayarwa Naseer yayansa.
Sosai hankalina ya tashi na hau nazarin abin yi Inda a karshe na yanke kafin ya karamin magana gwara na Gaya masa gaskiya ko da zai iya taimakamin tunda Naga gidanmu na Nan a kulle Dan har maganar gidan yamin akan mallakina ne gwara na gyara na zauna a ciki nida yarana Dan canjin hannuna na ringa juyawa.
Ranar da muka cika kwana biyar a garin washegari.na karbi mukulin gidan nace Zan je na Dan gyara.
Na tafi da yarana gabadaya shigata gidan ya hau fad’omin da irin Rayuwar danayi da.iyayena cikin so da Kauna da kwanciyar hankali.
Haka kawai na samu waje na zauna na hau bawa yayana labarin iyayena da yayana da ya tafi soja har yau banji labarinsa ba da irin San da sukemin.ina basu labari Ina kuka Inda mahaifina yake yawan Zama nake nuna musu Ina murmushi kamar ance na juya na kalli bakin kofa Naga Naseer a tsaye ya zubomin Ido Yana kallona badan nasan Naseer ba danace mahaukaci ne a tsaye a bakin kofa…….
Iabarin na da Dan tsayi shiyasa nake typing kullum na matsu Nazo. Ta tsakiyar labarin Dan haka inaga Zan Dan daddatse sabida mu fara Dan bana shiri da novel Mai tsayi Nan da Nan nake gajiya????????????
[6/13, 10:50 AM] Queen Meenali????: NAGA TA KAINA
*NA SADNAF*????????
®️ PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
{We Don’t just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}????????
Free Novel
Page 19
Cikin fad’uwar gaba na d’auke kaina banji dadin yanda mmn Mannir ta karya alkawarin data daukar min ba ba yanzu naso Naseer ya ganmu ba naso sai mun Dade na samu hutu kafin ya ganmu kasan Raina Kuma tausayinsa ne ya cike min zuciya amma kuwa saman fuskata hade Rai nayi Dan bazan tab’a binsa ba nafi jina cikin kwanciyar hankali tunda na baro Garin Kano
Jiki ba kwari ya daga Minal Ya Dan matsar da Zahira da Nadeeya da suka kankameshi suna ihun murnar ganinsa.
Ina Jinsa suka karaso gefena ya sauke Minal ya saka hannu ya dauki Humaira Dana kwantar da ita a gefena
Ya sauke wani irin ajiyar zuciya.
Har lokacin ban yarda na kalleshi ba duk da Yana ta lallubar kwayar idona Dan mu had’a Ido daga ni har shi ba Wanda yayi magana
Ni kuwa sosai na Kai zuciyata nesa wajen ganin na danne hawayen tausayinsa dake neman fitowa ta k’arfi da yaji ko ince tausayinmu gabad’aya.
Shi kuwa ganin naki kallonsa yace “Taimakamin da ruwa in Sha Naeema”
“Mik’ewa nayi nayi hanyar waje Dan babu komai a gidan.
Cikin gidan Mai unguwa na Shiga na d’ebo Masa ruwa a kwanun Sha na rufe na kawo masa na ajiye a gabansa.
D’auka yayi ya kafa baki sai daya shanye tas ya Ajiye anan na saci kallonsa Naga yanda yayi wurjan wurjan lebb’ensa duk ya bushe.
“Naeema Mai yasa Kika min Haka a ganina bai Kamata ki dau matakin guduwa da yaran ba da kin fadamin da na San Abunda ya Kamata nayi Sabida ki wahalar Dani Kika cemin Kaduna Kika tafi sai danayi kwana hudu a can kafin tunanin zuwa Nan yazomn haba Naeema Mai na Miki Dana cancanci ki zabi rabuwa dani”?
Cikin hade Rai Dan yasan dagaske nake bana San komawa gidansa marairaicewar da.yake bashi zai Saka na bishi da yarana ba
“Idan na Gaya maka Naseer hakuri zaka bani kace mu cigaba da Addu’a kullum kalmar kenan alhalin sababin abubuwa Umma ke kara bijiromin dashi kana kallon irin dukan da take wa Zahira duk sabida tsabar tsanar da tamin ta ringa jifanta da mugayen kalamai Wai baza tayi albarka ba Yar iska zata Zama kuka na fashe dashi Dan kalmomin Nan data jefi Zahira dashi ya balain yimin ciwo na cigaba da Magana Ina iya wanan Bai isheta ba ta d’auke min Nadeeya tsabar bakin cikin an ganta Naseer ta fito tana kururuwa Tana watsawa kanta kasa Naseer da kiyayyar ta zata tsaya iya kaina wlh Zan jure amma yanzu ta fara tab’a min Yara bazan jure ba Naseer ba tare aka halliceni dakai ba zaka iya rabuwa Dani ka cigaba da rayuwarka kana da Daman da zaka auri Mata hud’u ka Shimfid’a irin rayuwar da kake so dasu a ganina idan kana kaunata zaka so samun kwanciyar hankalina na Kuma Rayu cikin farinciki Ina kaunarka har a Raina Amma idan akwai cutarwa gwara mu hakura ka sauwake min ikon Allah yasa kagani a zaune a yanzu har nake maka magana a cikin Minal ba irin azabar da Umma Bata gana min ba ta window na duro danake nakudarta sabida Kar ta kasheni banajin addua Zai iya sauko da Umma ta kaunaceni Allah na tuba Umma sosai nake ganin tsanata a idonta Dan Haka Naseer na hadaka da girman Allah ka sauwakemin albarkacin yaran Nan ka gyara min gidanan da iyayena Suka barmin na Rayu da yayana cikin kwanciyar hankali idan ma bazaka iya bani jari ba Ni zan nemi aikin da Zan ciyar dasu Naseer Dan Allah ka sauwakemin na gaji wlh Nagaji”
Na karashe Ina fashewa da kukan da nakejin yinshi ne kawai zai saka naji zuciyata ta rage nauyi da zafi idan har Zan tuna wani zalunci da umma tamin sai kirjina yyi nauyi Haka Zan ta kuka har sai naji sanyi a Zuciyata
Naseer kuwa Bai iyamin magana ba in Banda idonsa daya kad’a.yayi ja jijjiyoyin kansa sukayi rud’u rud’u ni nasan sabida gaban yayansa yake shiyasa yake ta mayar da hawayen daya cike Masa ido.
Zahira kuwa da Nadeeya duk da karancin shekarunsu Haka suka hau kuka suma.
Naseer kuwa kamar maganuna bulala Suka Masa a jiki a Haka ya zauna jiki duk ba kwari nasan Dan muna gaban yarane da ya janyoni ya rungumeni ya rarrasheni.
Sai Dana ci kukana na koshi na mik’e tare da d’aukar Humaira.
Ban kalleshi ba nacewa su Zahira suzo mu koma gidan Mai unguwa Dan ko tabarma babu a gidan namu bansan wayanda suka kwashe ba
Naseer Bai mana magana ba har muka fice
Muna zuwa na bawa Zahira tabarma da ruwa a buta Akan ta Kai Masa yayi sallar Magriba.
A hanyar Kai masa ruwa da tabarmar
Mai unguwa ya ganta ya hau tambayarta inda zata je ita kuwa tace Masa Abbanta zata kaiwa.
Take Mai unguwa ya hau washe baki cikin farinciki zuwan Naseer
Yana iddar da sallah ya shigo har d’akin da aka bamu muka zauna da yayana ya daga labulen Yana “Ashe babansu yaran Nan yabi yo sahu Kai Masha Allah naji dadin zuwan da yayi Allah ya daidaita ku Dama kullum sai nayi addua akan Allah ya sa ya mayar dake dakinki Dan shine rufin asirnki an Riga an haifi Yara har hudu ai sai Kuma ayita zaman hakuri Allah ya Kara kau da fitina Zan Masa magana shima Bari na saka a kiramin shi
Nauyin Mai unguwa da yanda ya nuna farincikin zuwan Naseer yasa na kasa Koda magana har ya fice daga gidan.
Sosai naji da gasken bazan koma gidan Naseer ba shiyasa na bi dashi ta ruwan Sanyi Dan ya bani takarda ta Amma idan yak’i kuwa ya zama Dole na fito na gayawa Mai unguwa halin da nake ciki da mahaifiyarsa nasan shima idan yaji bazai so na koma ba tunda neman rayuwata Dana yayana mahaifiyarsa take.
Ana iddar da sallah ishai Mai unguwa ya aiko a kirani
Ina zuwa yace na Kira Masa Naseer ba yanda zanyi Haka na juya na nufi gidanmu Dan na Gaya masa rufin asirinsa shine ya sauwake min cikin ruwan Sanyi sabida bana San na ringa fallasa Sirrin mahaifiyarsa.
Ga mamakina Ina Isa Naseer na zaune a Inda muka barshi ga tabarma da ruwan da Zahira ta Kai Mai a gefe ya tsurawa waje daya Ido kirjinsa sai sama da kasa yake