NOVELSSARAN BOYE

SARAN BOYE COMPLETE

Bansan lokacin Dana taka da Sauri na Isa wajensa tare da durk’usawa a gabansa ba

Yana dagowa ya wawuroni ya kankameni cikin wani irin murya daya karyar min da ba iya zuciyata ba komai na jikina

“Naeema taya Zan soma rayuwa batare da ke ba Taya Zan soma rayuwa da wata matar idan ba ke ba Naeema nafiki Jin ciwon halin da kike ciki sanadin halin Mahaifiyata na kamu da mumunan hawan jini ban taba fada Miki bane Naeema Tayaya Zaki ce na sawake Miki ya kikeso nayi da Raina ke da yarana nake gani nayi farinciki da Ana canja uwa da na Dade da canja Umma badan Mahaifina da Abba sun tabbatarmin da ita ta haifeni ba Naeema da sai nace Umma ba Mahaifiyata bace Dan Uwa da tausayi aka santa uwa bata cutar da dan data Haifa na rasa yanda zanyi da Umma nayi nasihar nayiwa waazin duk tak’i ji bakece Bata kauna ba Naeema Ni data Haifa nine Bata so Dan tasan farinciki da kwanciyar hankalina kune Naeema wlh da Umma zata ce na mallaka Mata duk abinda nake dashi zata barni mu Rayu cikin kwanciya hankali ko daki dayane na Kama Mana na ringa dako muna ci muna Sha da.naji dadi na.rasa yanda Zan mata Dan Allah Naeema rabuwa Dani bashine mafita ba na yarda Zan Kara nema miki wani gidan batare da saninta ba Ni Kuma zance Mata har yanzu banganki ba”

“Naseer bazan koma Garin kano ba sai dai ka gyarmin Wanan gidan ka ringa zuwa kana ganinmu “

“Ya zamuyi da Karatun yaran namu kasuwanci na fa danake yi a garin Kano wlh Zan iya takuna bazan Bari Umma ta.san naganki ba Zan ringa zuwa ko sau ukune sati Dama akwai wani karamin gida Dana siya a sharada inaso na zuba Yan haya tallansa akamin Mai gidan na bukatar kudi shine na siya kawai Zan gyara miki ki koma can wlh Umma bazata Sani ba”

A takaice duk ta Inda na b’ullowa Naseer sai ya zame ya kalamanceni abinka da tsakanin mata da miji sai Allah tuni Naseer ya shawo kaina duk alwashin Dana Sha yabi iska muna zuwa gaban Mai gari yayi wa Naseer fada da naseeha washegari muka fara shirye shiryen komawa Naseer sai lallab’ani yake Yana riritani (Nafeesa Naseer na balain Sona rabuwa daya k’iyi Dani ya jawo Mana masifu da ko makiyina bana fatan yyi kwatan rayuwar da mukayi)

Matar Mai unguwa ita ta yarfamin kitso da Jan lalle na garjajiya yayana ma.aka musu kitso

Naseer kuwa ya cika Mai unguwa da abun arzki da matansa da yayansa tun kafin mu taho aka fara gyara gidanmu Inda Naseer ya bawa Mai unguwa kwangilar Ana Gama gyarawa a nemi Yan haya a saka a ciki kudin Kuma ya ajiyemin.

Hotel ya Kama Mana da muka iso sosai Naseer jikinsa ke rawa kamar Wanda yayi sabon aure duk wani Abu daya gani sai ya siyo Mana Dan sati daya ya kama Mana abinda ke fita dashi kawai gyaran gidan sharada ne da Abubuwan bukata da zamu yi amfani dashi.

Inama Umma ta saka Mana albarka a aurenmu ta daina daga Mana hankali da sai nafi kowace mace dacewa da gidan miji Dan ranar da muka kwana biyar Naseer ya siyomin set din sarka da dankunne har da zobe na daham Dubu talatin a lokacin ba karamin kudi bane sababin Kaya kuwa Haka ya cike Mana shi a akwati biyu atamfofi na ma kuwa Mai karamin kudi a ciki shine dari bakwai Wanda a kudin yanzu Zan iya yin Dubu biyar.

A Dan tsakanin kuwa sosai na dage da Addu’a Naseer kuwa shima Bai zauna ba.

A ranar da muka cika sati daya muka tare a karamin gidan Naseer dake sharada.

Cikin kwana biyu ya samowa su Zahira makaranta har da Minal suka fara zuwa

Har wani Dan sheki yake Yi na kwanciyar hankali.

Ni kuwa Inda ya kasance d’akina sai Dana rataya abinda Mallam Musbahu ya bani Dan dazan tafi sai Dana cire na kaina kuwa bana Wasa dashi sai idan Zan shiga bandaki nake cirewa Ina fitowa kuwa na maida kayana.

Dak’yar na samu na Shawo Kan Naseer akan ya koma gidan Sabida Kar Umma ta zargi wani Abu Yama nuna Mata ya hakura Dani zai zauna da Hindatu anan ya harareni nayi dariya nace yayi maganinta cikin sauki da kafarta zata gudu sai a lokacin yace na kawo shawara Mai kyau shi Kuma zai na karyar tafiya Yana zuwar mana.

A ranar da zai koma goron dutse da yamma Inna zuwaira da zata iya haifata tazo gidan Ashe Naseer Mai Tayani Zama ya Nemo min wacce Kuma zata ringa Tayani aikace aikace idan ya dawo Kuma sai ta tafi idan zai tafi sai ta dawo.

Sosai naji dadin zuwanta Dan Zan samu Mai debb’e min kewa kila ma har Abu Idan ya shigemin duhu Zan iya neman shawarar ta.

Naseer sai daya ajiye Mana komai har da kudin da bansan Mai zai yi.dasu ba Wanda har dagewa.nayi bazan karba ba Dan cemin yayi kullum sai yazo har abinci ma anan Zai ringa ci kwanciyar bacci ne zai ringa Mai dashi gidan.

Wajen karfe Tara ya Isa gidan fuskarsa kalar tausayi kamar gaske irin neman Naeema yake.

Tun Kan ya karasa Hawa sama yake jiyo Shewa.

Da Sallama ya tura k’ofar

Ba Wanda ya amsa sai juyowa da sukayi gabad’aya suna kallonsa Hajara har da mik’ewa tayi dage tana kallon bayansa Wai ko ya dawo da Naeema sai data ga shi ka dai ne ta washe baki tana “ko Kai fa ka hakura kazo ka zauna da Yar albarka tace.tana nuna Masa Hindatu.

Naseer Bai ce komai ba ya hau kallon mutanen palon Hindatu ce da Saffiya da Lami har dasu Tijjani sun zauna a tsakiyar Palon sai barjen Naman kaza suke ga kwalaban lemo a bubude.

Wato ma budurinsu kawai suke da Naeema ta tafi shi Kuma daga tafiyarsa shine su Saffiya suka dawo gidan.

Ba wacce yayiwa magana a cikinsu har Tijjani dake gaishe shi

Ya d’auke kansa tare da nufar d’akinsa Kai tsaye yana Jin muryar Umma tana duk hade Ransa Naeema bazata dawo ba idan ma.zai ware ya ware.

Sai daya Dan gyara d’akin ya watsa ruwa ya kwanta ya hau tunani su Naeema Dan lokacin ba wayar hannu da ya Kira yaji lafiyarsu Naeema

Dan kwanakin da yayi dasu ba karamin nutsuwa da kwanciya hankali ya samu ba babu abinda ya Kai Zama da iyali dadi.

Bai San da shigowar Hindatu ba sai ji yayi ta fado kansa shi kuwa ya mik’e da Sauri ya wancakalar da ita ya fara binta da wani mugun kallo Yana “duk ranar da Kika Kara shigomin daki wlh sai na balla Miki kafa juya ki fita”

Hindatu da Sauri ta fita ko minti biyu baayi ba Suka dawo d’akin da Hajara cikin masifa ta fara magana tana “Wai Mai kake nufi dani.ne. Naseer akan me zaka auri Yarinya Kuma ka ringa wulakanta ta toh wlh ka kaini bango Kar sake ka Kara korarta daga d’akin Nan Dan nan da wata tara inaso a haifomin jika Ni naga masifa duk da shegiyar matarka ta Shiga duniya ka ki nutsuwa ka dawo hankalinka toh wlh ka nutsu Dan nasan Tama Dade da mutuwa an rage mugun iri”

Wani irin kallo Naseer yabi Hajaran dashi ya d’auke kansa Bai ce Mata komai ba sai data gaji Dan kanta ta fita waje tare da Kara rufo musu kofa har da su mukullin.

Hindatu kuwa har da wani murmushnta ta Kara haye.gado tana murmushi.

Naseer shima mik’ewa yayi ya kullo k’ofar da mukulli ya zare ya saka key din a aljihunsa ya Shiga bandaki ya dauro alwala yazo ya hau Kan Sallaya.

Tuni ya ware murya ya fara karatun Qurani Hindatu kuwa ta mik’e hankali a balain tashe ta nufi wajen kofa ta fara jijigawa sabida Karatun sosai yake kona fatar jikinta.

Naseer kuwa Yana ganin Haka ya mik’e ya Ajiye Quraninsa ya nufi wajen Hindatun ya rik’e hannayenta biyu da k’arfi ya cigaba da karatunsa da k’arfi Yana tofa Mata yawun bakinsa.

Hindatu kuwa da iya karfinta take ihu tana Kiran sunan Hajara Dana Mahaifiyata take Hajara ta Gane Mai ke faruwa hankalinsu ya tashi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button