NOVELSSARAN BOYE

SARAN BOYE COMPLETE

Hajara kuwa ta bud’e k’ofar d’akin sai dai Naseer ya kulle k’ofar ta ciki itama da Sauri ta dawo Baya

Abinda basu fiye Yi ba b’acewa Dan sai Abu yaci tura sosai suke amfani da Wanan karfin.

Akan Dole Hindatu ta b’ace daga hannun Naseer

Duk da Naseer ya tsorata sai Haka ya cigaba da karatunsa da k’arfi tsoro na Kara shigarsa
[6/13, 10:50 AM] Queen Meenali????: NAGA TA KAINA

 *NA SADNAF*????????

®️ PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
{We Don’t just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}????????

Free Novel

Page 20

           Duk da yasan Hindatu da mahaifiyarsa suna cikin kungiya Bai San haka Abun yake ba yanzu macen da take tsafi wacce take Mayya mahaifiyarsa ta aura Masa Maganar Allah ne basa so suji kenan ma Mahaifiyarsa ba musulma bace toh a wane sahu zai sakata kenan kafura ko me innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Amma Abun mamaki mahaifinsa ya bashi labarin Mahaifin Hajaran Dalibansa ne Kuma musulmi toh Ina Hajara ta Samo wanan halin nata ko a cikin danginta akwai kafuran arna da basa sallah ne shiyasa ta Kauce hanya Haka bacewar da Hindatu tayi a hannunsa ya Kara gasgata Masa zargin su suka d'auke Nadeeya Yana ta imagining yanda hakan zai yiwu Wai mutum.ya b'ace sai da yaga zahiri.

Sosai.ya Kara k’arfin muryarsa Yana Shan alwashin ma Kiran mutane zaiyi suzo su Masa Saukar Qurani a gida.

Yana Jin Hajara na kwalla Masa Kira daga nesa da d’akin ya shareta

Shugubarsu kuwa ranta ba karamin b’aci yayi ba dan karatun ba iya Hindatu ya tab’a ba har da ita hakane yasa cikin bacin rai ta bayyana gabansu Hajara da lami Hajara kuwa suka zub’e a kasa suna k’ok’arin Magana ta daga musu hannu ta Shiga d’akinsu ta d’auke tukunyar Tsafin su da mudubinsu da duk shine karfinsu.

Tace wa Hajara sai ta hukunta su zata dawo musu dashi Kuma Hindatu bazata sake dawo wa Naseer ba

Kafin ma suyi magana har ta b’ace.

Hajara zaman dirshan tayi a kasa ta hau kuka Dan ko kad’an Bata San abinda zai rabata da Karfin tsafinta gashi Naseer yaja Mata daga ita har yayan nata an kwace musu k’arfin.

Naseer kuwa tsoro yasa ko bacci baiyi ba sai da aka Kira sallah asuba ya fito da alwala baiga kowa a palon ba sai Tijjani dake ta sharar bacci.

Shau da Masa carbin hannunsa yayi ya mik’e a firgice

Naseer kuwa yace Masa ya tashi su tafi.massallaci ya Fadi hakane sabida yaga ko shima baya sallar ga mamakinsa sai yaga ya mik’e yayi band’akin palon ya d’aura alwala ya fito.

Tare.suka.tafi Massallaci Naseer kuwa Bai dawo gidan ba sai da gari ya waye sosai wajen Shidda da rabi ya shigo gidan.

A Palo ya tarar da Hajara da idonta ya kumbure sabida kuka ta zauna tana ta jijiga kafa.

Wani irin kallo take Masa kamar zai wuceta kuma ya fasa ya tsugunna ya hau gaisheta.

“Burinka ya cika ka batamin komai Naseer na Haifeka Amma bakada burin da ya wuce ka bak’antamin toh burinka ya cika Hindatu ta bar rayuwarka Amma fa kasani wlh Tallahi sai na Kara Nemo wata na aura maka ita Idan Dan Naeema.kake ta haukar Nan toh wlh gwara ka Shiga hankalinka”

“Umma Maganar Allah ne bakwaso ko me karatun Qurani ne bakwaso nayi a gidana umma kinsan kuwa Allah ya hallicemu ne Dan mu San shi.mu Kuma bauta Masa Umma jiya karatun Qurani nake Hindatu ta b’ace a hannuna Umma kinsan kuwa hanyar da kike Kai b’ataciya ce ba mai billewa bace Umma Dan Allah Dan annabi ki tuba ki komawa Allah Umma wanan tsaface tsafacen ba Inda zai bille dake Umma tun sanin Dana Miki ban taba ganin kinyi Sallah ba Umma balle azo Kan sauran ibadan Umma lokaci Bai kure Miki ba ki tubarwa Allah ki dawo kan hanya Umma na saka ki a islamiyya ko Ni na koya Miki sabida kisan Allah “

“Naseer Ni ka saka a gaba kana zagi yanzu so kake kace bansan Allah ba kafura ce Ni ko me a takaice dai kana so kace Ni jahila ce ko Naseer Dan Hindatu ta b’ace a hannunka sai aka ce maka nima Ina bacewar Naseer Banga laifinka ba Naseer Kai da ka daga hannu ma zaka Mareni yanzu ai kanka ba daidai bane tunda wancan mayyar yar ta Shiga duniya ka haukace tunani ma ba daidai kake ba maganar da nake ma daban Wanda kake min daban idan ma.duk.kana wanan surutan ne Dan Kar Kayi aure wlh sai kayi

Kaji ma na Gaya maka.sanan wadanan munafikan daka saka a shago ban yarda dasu ba ka koresu Tijjani ya rike maka shagon.

“Umma Tijjani bazai iya rikemin shaguna uku ba ba yanda Zan Kori mutanen da suke samu a karkashina Zan dai bawa Tijjani jari ya rik’e kansa namiji ne shima ai ya kawo girman da zai Yi aure.

Safiya da Lami Kuma ya dace ace sun fito da mazajen aure Haka Dan wanan ba rayuwa Mai kyau suka zabawa kansu ba”

“Naseer a takaice dai kora da Hali kakeso kayi Mana toh bari kaji na fada maka babu Inda zamuje Kuma jari ba iya Tijjani zaka bawa ba har dasu lamin ka Gama duk abinda ka Dama Aurene sai kayi Dan ban Haifowa Naeema Kai ba yarinya duk tabi ta saka ka fice daga hayyacinka”

Naseer tashi yayi ya Shiga d’aki ita kuwa ta cigaba da bambamin fad’a kamar zata Ari baki.

Ahaka ya shirya ya zo ya fice daga gidan

Bai tsaya a koina ba sai a sharada lokacin Naeema tana daki tana bacci Inna zuwaira Kuma tana Dan Kara gyagyara gidan su Zahira kuwa Suna makaranta

Sai a gidan ya Rama baccin dake kansa yaci abinci ya huta sukayi ta Hira kamar basu da wani matsala yaso kwana sai da Naeema ta dage Masa Akan Kar ya kwana Dan Hajara na iya ganewa

Yana dawowa kuwa gidan ya d’auko Quraninsa a Palo ya hau karatun Qurani Dan sosai yake so su Umma su ma su bashi space ya sarara Amma ga mamakinsa ba Wanda ya tashi a cikinsu ya gudu kamar yanda suka Saba.

Sosai kansa ya daure da mamaki Hajara kuwa sai jefa Masa harara take sai daya Kai Aya ya mik’e zai Shiga d’aki tace “wato k’arfi da yaji kake so mu bar gidanan babu Inda zamuje Naseeru muna Nan tare da.kai zanyi maganin taurin kanka

A Haka rayuwa ta kasancewa Naseer da Naeema.

Acan yake yin komai kwana ne kawai baya yi a gidan shima da an kwana biyu zai cewa Hajara tafiya ta taso Masa ahaka zaije yayi sati ko sati biyu a gidan Naeema sosai suke taka tsantsan Dan Kar Hajara ta gano suna tare.

Duk da lokacin sosai ta matsa Masa da zancen aure har mamaki take yanda Naseer din yake rayuwarsa batare da ya damu ba gashi ba komai na tsafi da zasu iya gano komai a game dashi Koda akwai yanzu idan Suka so ganin Naeema ta mudubi basa iya ganinta har mamaki suke Nan kuwa basu San layyar data saka a kanta bane.ya hanasu ganinta shugabarsu ma sai cewa.tayi kila ma Naeema mutuwa tayi shiyasa basa ganinta

Naeema sosai Jin dadi da kwanciyar hankali ya zauna Mata har ta ringa tunanin duk wanan lokacin Mai yasa dabaran hakan Bai fad’o musu ba.

Naseer shima sosai ya samu kwanciyar hankali sai zai je gidansa da mahaifiyarsa take ciki yake d’auko wata fuskar ya aza idan yaso ma tsokano Hajara idan tana Masa zancen aure shi kuwa sai yace Mata Shi bazai yi aure ba sai Naeeema ta dawo anan fa Hajara xata hayayyako kamar zata masa.baki tayi ta cewa Naeema ai ta mutu ko ba mutuwa tayi ba Bata isa ta dawo gidansa ba.

Ahaka har sai da suka kwashi watani shidda cas watarana ya dawo daga gidan Naeema.

A Palo ya tarar da Hajara ta balain had’e Rai Safiyya Kuma tana zaune a gefenta.

Gaishe ta yayi ya mik’e zai wuce d’akinsa Hajara ta dawo dashi ya zauna.

Ta fara magana cikin b’acin rai “Naseer kana so kaga b’acin Rai na ko kana so sai na balain Bata maka kafin mu shirya dakai ko ka Nemo matar aure ko na nemo maka da kaina na gaji da ganin ka Haka ko na nemo maka matar auren

Sai ka wulakanta ta kamar yanda ka wulakanta Hindatu na baka Nan da sati biyu ka nemo matar aure idan ba Haka ba wlh da kaina Zan Nemo maka Kuma baka Isa ka wulakanta ta ba”

“Tom Umma Zan nema Ina ta ganinsu babu wacce tamin ne Amma insha Allahu zanyi kokari na nema din”

Daga Haka ya mik’e ya shige dakinsa

Fada Hajara ta ringa yi bayan ya Shiga d’akin Saffiya kuwa ta tab’a ta tana “Umma Anya Yaya baya tare da Naeema kuwa “?

Wani irin hantsulowa Hajara tayi daga Kan kujeran ta dafe kirjin ta tana “Mai kikace Suna tare fa kikace Mai kika gani kikace Haka”?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button