SARAN BOYE COMPLETE

“Umma kema kinsan yanda ya Naseer yake San Naeema yake Kuma San yaransa banajin da basa tare zai samu kwanciyar hankali Haka ke bakiga yanda.yaya ya danyi kib’a Yana sheki ba wlh kila Raina Mana hankali yake”?
“Zan Miki baki wlh Safiyya karki soma min wanan fatan idan suna tare a Ina ya ajiyeta Naga dai gida yake zuwa ya kwana sai idan tafiya ta Kama shi yake kin kwana a gida kin manta bama.ganinta a mudubi shugaba.kuma data duba da kanta tace kila hatsari sukayi suka mutu”
“Hmmm toh shikenan tunda Kikace Haka Amma nidai gani nake da Yaya baya tare da Naeema bzaki kansa fes Haka ba”
Mik’ewa Hajara tayi da Sauri tana “idan kuwa hakane Safiya na gano rainamin hankali sukayi wlh sai nayi wa Naseer baki wlh sai na kashe Naeema da hannuna Kinga Banga ma ta zama ba ya zama Dole mu koma Calabar muje mu bawa Shugaba hakuri ko Dan na ringa sanin abubuwa da ke wakana wlh tunda ta kwace komai namu banajin dadi Banga ta zama ba ya zama Dole mu d’auki hanya gobe”
Sosai hankalin Hajara ya tashi da maganar da Safiyya ta Mata washegari kuwa da sassafe Bata ma jira Naseer ya dawo daga Massallaci ba Suka dau hanya su uku Dan Tijjani tunda Naseer ya bashi jari ya Kama wani shago a gwammaja ya zuba kayan provision yake siyarwa Bai ma fiye dawowa gida ba.
Naseer sosai yaji dadin tafiya da Hajara tayi dasu Safiyya cikin kwanciyar hankali ya koma sharada da zama dama sabida gidan ya masu kad’an ya Kara siyan fili a jikin gidan aka hade da yake da kudi a hannunsa tuni gidan yayi kyau da tsari.
Arziki Kam har yaci uban na da Dan Naseer yanzu Yana da gidaje sun Kai shidda filaye kuwa zasuyi hudu Kuma duk manya shagunansa kuwa shidda.banda wasu kasuwanci da yake danyi kudi na shigo Masa.
A cikin wanan shekarar yake burin idan Allah ya amince zasu je aikin Umara shi da Naeema.
A kuma cikin wanan yanayin Naeema ta Kara samun ciki Wanda Naseer ya balain kwallafa Rai akansa yake Kuma sawa a addua Allah ya azurtashi da samun da namiji.
Naeema kuwa tunda Naseer ya dawo gidan yace Masa Hajara sunyi tafiya hankalinta ya kasa kwanciya Haka kawai takejin kamar babu alheri a tafiyar tasu hakane yasa ta dage da Addu’a duk da Bata tab’a Zama ba adduar ba Naseer ma har ya zama Masa jiki adduar.
Hajara kuwa dak’yar shugabarsu ta hakura ta maida musu karfinsu Inda ta gargadesu da nisantar duk Inda ake Karatun Qurani anan Hajara tasa a duba Mata Naeema ta mudubinsu ko tana rayye anan suka duba Amma duk Inda suka kai ga tsafinsu basu iya ganin Naeema ba Naseer kawai suka gani a zaune a kasuwa Yana ta zabga lissafi.
Satinsu uku a Calabar suka dawo.
Naseer bai.ma San sun dawo ba sai daya zagayo wajensu Lukman Dan ya karbi takardar lissafi da sukeyi yasan sun dawo.
Sosai yaji Bai ji dadin dawowarsu ba.
Ahaka ya b’oye abinda ke Ransa ya musu Sannu da zuwa.
Sai a lokacin Hajara ta ga kibar da Naseer yayi na kwanciyar hankali.
Yana tashi ta kalli Safiyya tana “Akwai wani Abu a kasa wlh ban yarda da Naseer ba gobe idan ya fita inaso kiyi ta bimin bayansa har kiga Mai yake ciki”
Naseer kuwa ba a San Ransa ya kwana a gidan ba
Washegari da sassafe Naseer ya fice daga gidan ya nufi gidansa dake sharada.
A Haka Safiyya tayi ta binsa a baya batare da yasani ba har ya Shiga gidan.
Sabida tsabar balai Haka Safiyya ta labe a kangon jamaa sai da Naseer yaci ya koshi yayi wanka ya shirya tafiya kasuwa.
Haka kawai Naeema ta ringa Jin fad’uwar gaba jikinta ba dadi addua kawai take a ranta har Naseer ya tafi.
Safiyya kuwa cikin mamaki ta ga Naseer ya fito daga gidan daga wajen gate Naeema ta rakoshi da Hijabinta tayi wani irin fari Kamar ba ita ba
Bata tsaya ma ganin tafiyar Naseer ba ta fita titi da balain gudu ta hau taxi Suka nufi goron dutse sai vibrating take Kamar itace Hajaran.
Ko parking din kirki Mai taxi Bai Gama yi ba ta fito daga motar ko kudin Bata bashi ba ta hau sama da balain sauri Tana kwallawa Hajara Kira
Zumbur ta mik’e tsaye
Tace “Wlh Naga Naeema Yaya Yana tare da naeema”
Yaraf Hajara ta zub’e a kasa kamar an doka Mata guduma ta Kara mik’ewa cikjn tashin hankali tana Kika ce me”?
Safiyya hannun Hajara kawai ta jawo Suka sauka da gudu Suka fada taxi din tana ce Masa ya maidata Inda ya d’auko ta zata hada Masa kudinsa.
Hajara wani irin jijjiga kawai take Tana vibration har suka Isa sharada.
Jikinta sai rawa yake yanda zata.shake Naeema.
Suna sauka Safiyya ta hau buga gidan da hannu biyu.
Ina zaune naji Ana buga gate da balain k’arfi mik’ewa nayi cikin fad’uwar gaba na dafe kirjina haka kawai Umma ta fado min a Raina.
Inna zuwaira ce ta bud’e gidan tana bud’e gidan Safiyya ta bangajeta suka shige suka hau kwallawa Naeema Kira ahaka har Suka shiga palon dana daskare a tsaye tunda naji muryar Safiyya.
Kallon kallo muka fara da Umma tana tsaye daga bakin kofa Ni kuwa in Banda sallati babu abinda nakeyi…….ƙama Hajjo yana faɗin, “Da wannan zaku gansa dole, dan ƙa’idarsa sai yaga bayanan ciwon mutum na baya inhar ya taɓa ganin likita akan hakan”.
Nanma godiya suka sake masa. Hajjo ta sake miƙama baba malam. Amsa yay ya saka Numbers ɗin da aka bashi a cikin file ɗin ya ajiye.
Kasancewar lokacin sallar isha’i yayi duk sai suka fice har Doctor. Bayan an idar da salla Doctor ya sake dawowa tare dasu Ahmad ya shiga ya ƙara duba Nu’aymah. Sai da ya sake tabbatar da komai ya zauna sannan ya fito yay musu sallama akan insha ALLAH da sassafe zai dawo yaga jikin nata. Idan kuma sunga da wata matsala komai dare su kirashi.
Sun masa fatan alkairi da godiya ya tafi.
★_★_
Baba malam bai shigo gidan ba sai kusan goma saura, dan ya tsaya sunyi karatu ne. Sashen Hajjo ya fara shiga ya duba Nu'aymahn. Har sannan barci take, dan haka ya ɗauka file ɗin nata ya fice da shi zuwa sashensu.
Duk abinda Umm take masa bata fasaba. Yanda kuma bai mata magana akan Nu'aymahr ba itama batace da shi ƙala ba har suka kwanta.
ZAFAFA BIYAR 2021
Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka yaɗa dan ALLAH idan ka gani????????????.
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????
09033181070
WASHE GARI
Alhmdllh Nu'aymah ta tashi jikinta da sauƙi, kuma kamar yanda kowa yay fata bata manta da komai ba kamar yanda Doctor yayta jin tsoro. Hajjo ce ta taimaka mata tayi wanka. Yusrah ta kawo mata abinci tama zauna da kanta ta ringa bata. Ta ɗanci babu laifi, dan Yusrah lallaɓata ta dingayi ita da Hajjo.
Kamar yanda kowa na gidan yazo ya dubata da safen haka Baba Malam da Umm ma sukazo suka dubatan. Sunji nutsuwa sosai a zukatansu ganin jikin nata Alhmdllh. Sai dai kowansu bai nunaba a fuska, sunma haɗe mata gabas da yamma.
Hakan ba ƙaramin sake ɗaga hankalin Nu'aymah yay ba, harta kasa haƙuri ta shiga tambayar Yusrah ko wani abu ya faru bayan barinta gida ne? Dan ita tayi zaton idan ta dawo zataga kowa na murnar dawowar tata. Amma saita samu saɓanin hakan, sai ma kalaman baba malam na jiya keta mata kaikawo a cikin rai.
Ƙasa Yusrah tayi da kanta hawaye na cika mata idanu, haka kawai ta tsinci kanta da jin kunyar Nu'aymah ɗin mai tsanani. “Yusrah dan ALLAH kimin bayani mana? Ina Yah Ab da Adawiya duk bamma gansu ba”. Nu'aymah tai maganar cikin sanyin murya na alamun rashin jin daɗin jiki.
Saurin miƙewa Yusrah tayi ta juya mata baya zata bar ɗakin. Nu'aymah ta riƙe hannunta itama da sauri. Hannu Yusrah tasa ta goge hawayen dake rige-rigen sakko mata a kumatu batare data juya ta kalli Nu'aymah ba.
Dai-dai nan Hajjo ta shigo tare da Doctor da yazo sake zuwa ganin jikin nata.
“Kai lafiyarku?”.
Hajjo ta faɗa ganin Nu’aymah da Yusrah duk suna hawaye.
“Ba komai Hajjo”. Yusrah ta bama Hajjo amsa tana zare hannunta daga cikin na Nu’aymah. Kamar hajjo zata sake magana sai kuma tayi shiru suka bama Doctor damar duba Nu’aymahn. Yaji daɗin ganin jikin nata normal, sai dai yanason mata allura yana tsoron rikicinta da zasu kwasa. Nu’aymah ta mugun tsanar allura a rayuwarta, indai akace za’ai mata allura to lallai an taro match kuwa. Dan sai kowa yaji a gidan harma makwafta.
Kallon hajjo yay murya ƙasa-ƙasa yace, “Hajjo ko za’a kira mana su Ahmad ne kusa. Allura zan mata kinsan kuma sai ansha yaƙi”.
Sosai hajjo ta waro idanu waje. Taɗan kalli Nu’aymah data kwanta idonta na kallon fanka dake juyawa a hankali. Sake kallon Doctor tayi, itama a hankali tace, “bara dai a dubamin cikin iyayen nasu tunda duk basu fita ba”.
Kansa ya ɗaga mata ya tashi ya fita falon dan ya haɗa allurar. Itama Hajjo biyosa tayi.
Kusan mintuna biyar da fitar tasu duk suka dawo harda Baba malam dake cikin shirin fita. Batare da yayi maganaba ya kama Nu'aymah da kansa ya tayar zaune. Kallonsa take cike da so da ƙaunar mahaifin nata. Amma yanda yay kicin-kicin da fuska sai yake ƙara tsoratata. Ganin yanda ya jata jikinsa ya rungumene ya saka ƙirjinta bugawa. Dan tun tana yarinya inhar taga ya mata irin wannan rungumar to lallai allura za'a mata. Saurin ɗagowa tai ta kalli Doctor daya ɓoye hannunsa a baya. Jikinta ne ya fara tsuma, zatai magana Baba malam ya balla mata hararar da ta sakata maida kanta jikinsa ta kwantar.
Rikici sosai akasha kafin Doctor ya mata allurar, ba ita kanta ba har baba malam da hajjo masu riƙetan saida ta tarama gajiya. Doctor kam har ƴar zufar wahala yakeyi a goshi, a ransa yana sake jinjina daru irin na Nu'aymah.
Tunda baba malam ya maidata ya kwantar ajiyar zuciya kawai taketa faman saukewa hawaye na zirarar mata da gudu. Hajjo ta zauna inda baba malam ya tashi ta ɗago kan Nu'aymah ta aza bisa ƙafarta tana shafa mata dogon gashinta.
Sauran magungunanta Doctor ya ajiye yayma hajjo sallama suka fice shi da Baba malam.
Hajjo ta jima tana lallashin Nu'aymah kafin ta samu tayi shiru barci ya saceta. Amma har cikin barcin tsabar rikicinta ajiyar zuciya taketa faman saukewa a jajjere. Haka dai hajjo ta lallaɓa ta kwantar da ita da gyara mata kwanciya ta tashi ta fice.
ZAFAFA BIYAR 2021
Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka yaɗa dan ALLAH idan ka gani????????????.
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????
09033181070
DUBAI
Amarya Adawiya da ango Abdallah sun isa ƙasar dubai lafiya, sai dai gaba ɗaya ya canja tsarin daya shiryama kansa da Nu'aymah. Ya dai kama musu babban hotel kuma a ɗaki ɗaya. A randa suka isan kuma ya sace wayar Adawiya ya ɓoye batare data saniba.
Ita dai duk abinda yake mata bai ɓata mata rai, haɗe fuska da ƙin mata magana tunda suka taho baisa taji haushinsaba balle sonsa ya ragu mata a zuciya. Saima ƙaruwa da ya sakeyi tanajin kamar ta haɗiyesa.
Gadon ya bata ta kwanta shi kuma yasa bargo a ƙasa yay kwanciyarsa. Da asuba ya rigata tashi, yay wankansa yay shiri tsaf. Sai da ya kammala komai sannan ya tadata. Mamaki ya kamata matuƙa ganinsa cikin shirin fita, sai dai kuma babu fuskar tambayarsa.
Murya a shaƙe yace, “Duk abinda kike buƙata ki kira zasu kawo miki”. Daga haka bai sake tofa komaiba yay ficewarsa daga ɗakin yaja mata ƙofar. Ta jima zaune a wajen tamkar wata gunki har gari yay haske sosai kafin ta sakko jiki a sanyaye taje tayo alwala. Duk da hakan da yay mata babu daɗi sai bataji haushinsaba. Haushin Nu'aymah nema ya kamata, dan a ganinta zaman dataine cikin zuciyarsa yasa baya ganin kowa da gashin mutunci sai ita. Aiko ta ɗauki alwashin sai ya manta wata banza Nu'aymah a zuciyar tasa har abada balle kuma wata Yusrah da tasan bata a gabansa.
“Hajiya Adawiya, ke dai kike kiɗanki kike kuma rawarki????????”.