NOVELSSARAN BOYE

SARAN BOYE COMPLETE

    Duk abinda ke faruwa akan idanun Baba malam ne dake tsaye a jikin daga ƙofar falon Hajjo yana kallonsu. Kallo ɗaya zakai masa ka fahimci yana cikin tsananin tashin hankali. Nu'aymah zuciyarsa ce, yana dannewa ne kawai, amma bazai yuwu ya bari son da yake mata ya hanashi hukuntata akan kuskurenta ba, dan yasan icce tun yana ɗanye ake tanƙwarashi, idan ya bushe karyewa yakeyi.

  Sun cigaba da ƙoƙarin ganin ta farfaɗo kafin Doctor ya iso, sai dai fa ko motsi babu wani sashe na jikinta dake nuna alamar zaiyi ma...........✍

Tashin hankali????, kumuje zuwa.


SAHFAT PREORDER!


    Wani kaya sai amale ka ɗauka????.

SAHFAT PREORDER maida tsohuwa yarinya.

Kaji masu kawo kayan adon gida dana jiki ƴan gaske.

Ina mata masu ƴan bana bakwai? ko uwargidar da ake shirin kawoma ƴar bana bakwai?. Kai hardama matan gayu ƴan ƙwalisa masu son sabunta gida da kayan ado ƴan waje masu sauƙin farashi da nagarta!.

To ku garzayo dama ta samu, dan SAHFAT PREORDER sune na ɗaya a wannan fanin. Idan kayan kitchen kikeso masu ƙyau da nagarta a farashi mai sauƙi kuma zaki samu a Sahfat preorder. Idan kayan sakawa kikeso na manyan mata ƴan gayu suma akwaisu babu ƙayarya. Jaka ko takalma na nunawa tsara suma ba’a barsu a baya ba harma da mayafai. Hakama kayan ɗaki basu da tsara.

Ni shaidace domin dukkan kayana ta hannunsu nake samu nima. Ku garzayo kuma a dama daku dan nasan zakuyi alfahari da hakan insha ALLAHU.

Kiyi magana ta wannan Number 08142957548 insha ALLAH zaki samu ƙarin bayani ƴar uwa.

Siyen nagari????, maida kuɗi gida???? sai SAHFAT PREORDER????????????????????


ZAFAFA BIYAR 2021


Hafsat miss xoxo????
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).????????

      Mamu gee????

MIN ƘALB!!????????

    Hafsat rano????

ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!????????

    Safiyya huguma???? SIRAƊIN RAYUWA????????

     Bilyn Abdull????

SARAN ƁOYE????????

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka????????????????

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????

09033181070

????????????????????????????????????????
TEAM—-ZAFAFA BIYAR????????????????

ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????.
[5/28, 3:14 PM] Queen Meenali????: Typing????

No. 9

……………..Sosai Adawiya ta tsorata da mugun kallon da Abdallah ke jifanta da shi. Jan jikinta ta farayi baya a hankali ganin ya fara takowa yana nufota. “Y…y..Yah Ab wlhy babu abinda nayi da wayarka, Please dan ALLAH karka dak……”
Ta kasa ƙarasawa saboda kiran wayar da akayi. Shima cak ya tsaya daga bin nata yana kallon wayar. (Sweet Momy) ya hango ɓaro-ɓaro yana yawo akan fuskar wayar kamar yanda yay saving. Iska mai zafi ya busar daga bakinsa yana lumshe idonu. Tsinkewa wayar tayi aka sake kira. Yanda bai motsaba haka ma Adawiya ta kasa motsawa. Kallon wayar take kawai daga nesa tamkar yanda yake kallonta shima. Sai ka ɗauka gamo sukai da bomb.
Sai da Momy ta jera ma Abdallah kira har biyar bai ɗaga ko guda ɗaya ba a ciki. Daga ƙarshema saiya nufi wayar a fusace ya takata da ƙafarsa. A take screen ɗin ya shiga bada sautin fashewa.
Baya Adawiya tai da sauri tana mugun waro idanu da buɗe bakin mamaki. Al’amarin bai ƙara firgitataba sai da taga ya ɗauka wayar ya zare sim card ɗin ya karyashi biyu. ya kuma nufi toilet ya jefashi yay flushing a take.
Da sauri Adawiya ta koma inda take da ta tsaya zuciyarta na mata wani masifar bugu, ga wani irin tsoron Abdallah daya sake shigarta mai ƙarfi. Sam batai tunanin yanada zuciya irin hakaba. Duk da tasan ƴan gidansu kowa yanada wannan shegen zuciyar amma tazata tashi mai sauƙice ganin yanda bata cika ganin fushinsa ba. Ta gabanta yazo ya fice ko kallon inda take bai sake yi ba. Ya bugo mata ƙofar da ƙarfi har saida ta zabura jikinta na karkarwa……..

NIGERIA

         Cike da mamaki Momy ke kallon wayar tata tamkar idanunta zasu zubo ƙasa. A ranta take raya ‘To miya samu wayar Abdallah? Ta shiga bai ɗagaba, daga ƙarshema wayar ta jita a kashe’.
   “Momy lafiya?”. Omar daya shigo falon ya faɗa idanunsa akan Momy dake tsaye tana ta faman juya waya.
 Saurin ɗagowa tai ta kallesa, sai kuma cikin sanyin murya tace, “Omar yayanku ne wlhy, ya kirani bana kusa inaga ko cikin su Amal wani ya ɗaga, shine yanzu dana fito naga alamar ya kira an ɗaga saina kirashi. Amma har missed calls biyar na jera masa bai ɗaga minba, yanzu daga ƙarshema wayar a kashe take”.
    Murmushi Omar yayi yana zama da faɗin, “Oh Momy ƙila to baya kusa ne, kinsan hidimar Yah Abdallah ba ƙarewa takeba. Nasan zai kiraki shima”.
   Kai Momy ta girgiza masa, “Omar ba rashin ɗaga kiran bane damuwata, jin wayar a kashe bayan kuma duka kiran danai sun shiga”.
   “Momy Please ki kwantar da hankalinki, nasan insha ALLAH babu wata damuwa. Koma baida cajine kokuma network”.
Kamar zata sake magana sai kuma tai shiru taɗan jinjina kanta. Tashi tai ta maida wayar a caji dan fama cajin ta saka ta shiga kitchen tun ɗazun. Yanzuma tana maida wayar a caji saita koma kitchen ɗin suka cigaba da aiki ita da masu aikinta su biyu tabar Omar daya kwanta cikin kujera yana canja chennal a falon. Sai dai kuma abin yaƙi barin ranta sam.

    Har dare Momy na jiran kiran Abdallah shiru, ta kuma sake nemansa itama amma har lokacin wayar switch up. Tun tana danne damuwarta harta bayyana fili. Abbah da tun ɗazun yake kula da yanayinta ya tambayeta ko lafiya?. Batai nauyin bakiba tai masa bayanin abinda ya faru.
 Shi dariyama ta bashi ganin yanda duk tai wani iri kamar ance Abdallahn ya rasu ne, dan haka yaɗan murmusa yana girgiza kansa, batare da ya ce mata komaiba ya cigaba dacin tuwonsa. 
    “Abban Abdallah dan ALLAH ko zaka kira min shi da wayarka?”. Sake kallonta yayi da ƙyau, sai kuma yay gyaran murya da ɗauke idonsa. “Khadija ki rage ruɗiyarnan taki, yanzu dan ALLAH Abdallah ƙaramin yarone halan? Maybe baida caji ne kokuma ya shiga wata sabgar. Kiyi haƙuri kiga zuwa safiya idan ALLAH ya kaimu idan bai kiraki ba”.
   A sanyaye tace masa “to” kawai badan hakan ya mata daɗiba. Sai ma ta tattare kwanikan daya kammala cin abincin ta fice da su. Saida takai kitchen sannan ta nufi ɗakin su Amal. Zaune ta iskesu suna karatu, Amal na ƙarama su Imran. Duk shiru sukai suna kallonta. Itama kallon nasu takeyi.
  “Amal wanene a cikinku ya ɗaga kiran yayanku ɗazun?”.
  “Kira kuma Momy? Wlhy bansan Yayah ya kira wayabama ni, dan tun ɗazun danace miki zanje na sake duba Nu'aymah ina can wajenta ɓangaren Hajjo ni da Yusrah. Amma wani abune ya faru?”. Kai momy ta girgiza mata tana kallon su Imran suma. Da ɗai-ɗai suka shiga bata amsar suma duk basu baneba.
 Kanta taɗan dafe zuciyarta na neman faɗawa a ruɗani, lallai yaran sunada gaskiya, dan idanma tai dubi da lokacin da Abdallah ya kira ai duk basa gidan ma suna islamiyya. Kasancewar yau lahadi sunayin harta safe zuwa uku a tashesu, to indai suna garin suma yaran suna zuwa anan ma. Kuma tunda safen duk suka fita. Amal ce kawai batajeba saboda ta tashi da ciwon mara, daya ɗaga matane tace zataje ta duba Nu'aymah. Sai da ta fita da kusan awa ɗaya ma Abdallah ya kira.
  Ficewa tai taja musu ƙofar tanason tunano ko wani ya shigo a wannan lokacin, to amma kuma babu wanda ya shigo ɗin, daga ita sai ƴan aikinta. Abba ma baya nan, Omar ma ganin datai masa bayan kiranne ya shigo gidan, dan tare suka fita da baba malam tunda safe.

          Momy da taga tunaninta na kaita wasu nazari daban sai kawai ta ajiyesa gefe, ta barsa akan uzirine yayma Abdallah yawa. Waya kuma ƙila sanda yake kira cikin sauran ƙannensa yaran gidan wani ya shigo ya gani ya ɗaga. 
 Washe gari da safe batabi takan kiran Abdallah ba ta cigaba da hidimominta kamar yanda ta saba. Abin mamaki kuma har dare bai kirantanba, sai itace dai da dauriyanta ya gaza ta nemesa kusan taƙwas na dare. Switch up dai ɗin yauma.
        Ganin yanda ta zuba tagumi yasa Abba jin tausayinta. Wayarsa yasa ya kira Abdallahn, amma sai yaji layin a rufe. maida kiran yay a ɗayar Number Abdallah ta business. Bugu biyu kuwa ya ɗaga. Bayan sun gaisa yace masa ga Momy.
   Jimmm Abdallah yay kamar bazaice komaiba, sai da Abbah yace, “Nace ga Momynku ko bakajiba?”.
     “Amm sorry Abbah network ne, bata to”.
  Miƙama Momy Abbah yayi, ta amsa zuciyarta na mata sanyi, dan tana matuƙar ƙaunar Abdallah sosai a cikin ƴaƴanta, sai dai tana ƙoƙarin dannewa gudun saka ruɗani a tsakanin ƴaƴanta.

ZAFAFA BIYAR 2021


             Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka karanta idan baka biyaba, karka kuma yaɗa dan ALLAH idan ka gani????????????.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????

09033181070


        Da ƙyar Abdallah ya danne zuciyarsa ya gaida Momy da fuskarta ke shimfiɗe da murmushin farin cikin jinsa. Ta amsa masa cike da kulawa tana tambayarsa yaya suke? Ina Adawiya?.
       Muryarsa a ɗan cinkushe yace tayi barci, shima shirin kwanciya yakeyi.
       “To Alhmdllh tunda dai lafiya kuke. amma jiya miya samu wayarkane? Na kira har sau biyar baka ɗaga ba, daga baya kuma saima naji switch up”.
       Ba ƙaramin haushine ya kama Abdallah ba dajin maganar Momy, bayan sharaɗin data gindaya masa mai ƙarfi akan abinda yake tsananin so shine kuma zata kirasa?, yanzu kuma dan taga tana kusa da Abbah take nuna kamar batai komaiba. To mizata faɗa masa bayan wanda ta faɗa masan kuma?............ 
   “Abdallah lafiya kuwa?”. Momy ta katse masa tunani. “Babu komai Momy, wayarce ta faɗi a cikin ruwa bayan mungama waya jiya shiyyasa”.
     “Abdallah ai ni bamuyi way.......”

Zare wayar Abba yay daga kunnen Momy yana faɗin, “Haba Khadijah tunda kinji lafiyar tasu ya isa haka. Bakiga dare yayiba ne? Yanzu kuma Abdallah yanada iyali”.
“Afuwan Abban Abdallah na shafa’ane wlhy. Ni saima naji muryarsa kamar wanda bayajin daɗi”.
Kallonta Abba yay sosai, sai kuma ya matsota jikinsa ya gwargwaɗa mata magana a kunnenta. Idanu ta ɗan zaro waje, sai kuma tai saurin miƙewa tana kare fuska da hannu alamar maganar tasa ta bata kunya.
Murmushi Abba yay yana binta da kallo harta shige toilet. Yaɗan girgiza kansa yana gyara kwanciyarsa.


      Jikin Nu'aymah yayi sauƙi sosai Alhmdllh, sai dai har yanzu bata koma sashensu ba tana sashen hajjo. Tana dai zuwa ta gaishesu da safe, ta kuma taya Umm aiki kamar yanda aka horesu. Babu wanda yay mata maganar Yah Ab a gidan, itama tayi ƙoƙari ta danne tana jira taji daga garesu kamar yanda Yusrah ta bata shawara data dameta da tambayar yanda akayi.

   Kwana biyu da samun lafiyar Nu'aymah su Momy sukai shirin komawa Abuja saboda karatun yara. A wannan karon Nu'aymah jitai batason tafiyar su Yusrah da Amal, dan suna ɗauke mata kewar Adawiya sosai. Tasan kuma idan suka wuce zata koma ita kaɗaine babu wani abokin ƙiriniyarta kamarsu a gidan, daga yayu sai ƙanne sai iyaye.
    Babu yanda ta iya, a washe gari su Amal suka fara wucewa Lagos da safe. Da yamma kuma su Yusrah. Nu'aymah harda hawaye. Hajjo da taji tausayinta har tayi tunanin ko Nu'aymah tabi cikinsu Yusrahn, sai kuma ta tuna ashe akwai shirin zuwa ganin Doctor da sukeyi. Zama tayi taita lallashinta harta saki jikinta, yayinda su Hajarah da sukazo sashen Hajjon suka ɗan rage mata kewar tafiyarsu Amal ɗin.

★★★★★★

       Kwanaki sun shuɗa, jikin Nu'aymah yayi garas, gidan ya koma kamar da sai su kaɗai. itama harma ta tattara ta koma ɗakinsu ita da Adawiya dake a sashensu. Sosai takejin kewar Adawiya, musamman ma idan tazo kwanciya ko zata shiga toilet. Dan ƙa'idane kullum sai sunyi faɗa akan bargo da filos, hakama shiga wanka sai sunyi faɗa. Haka sabo yake turken wawane.
   A yanzun kam sai Muhammad ƙaninta ya zame mata abokin hira. Daya dawo makaranta koda yaushe suna tare, duk da dai ta dage wajen maida hankali a karatunta na islamiyya itama. Dan a ɗan tsakanin nan ba ƙaramin ƙoƙari takeyi akan haddar Qur'aninta ba. Ga sauran littatafai ta dage sosai suma.
  Wannan karatun shine ya ɗauketa busy matuƙa. Tunma rashin sakewar da su Umm suke mata yanzu yana damunta har abin ya fara raguwar mata a rai. Dan tasha tambayar Umm ɗin kota musu wani laifine?. amma sai Umm ta shashantar da zancen taƙi bata amsa, haka shima Baba malam baya cemata komai akan hakan. A yaran gidan ma duk wanda taima tambayar ina Adawiya taje? Sai suce mata makaranta, Yah Ab kuma ya koma Saudia.
  Takanyi shiru taita tunanin miyasa  za'akai Adawiya makaranta ita kaɗai a barta? Bayan kuma tunda suka taso komai tare sukeyi, makaranta da komai da komai tare ake sakasu, kuma tare ake musu komai. Wannan tafiya makaranta da taji na Adawiya saida ya sakata kuka, daga ƙarshe ta haƙura da fatan ALLAH yasa haka shine mafi alkairi. Tana kewar Yah Ab sosai a zahiri da baɗini. Gashi yanzu bata da waya, ta kuma kasa aron ta wani ta kirashi koda ta Umm ce. Dan da idan tanason suyi magana wayarta babu caji data Umm take amfani. Shima daya kira yaji bai sametaba zai kira Hajjo ko Umm a bata. Amma a wannan karon ganin shima ko sau ɗaya bai nemeta ba sai al'amatin ke ɗaure kanta da bata mamaki. Da taga dai zuciyarta na neman ƙuntata sosai sai taje ta tsare Hajjo da tambaya tana kuka.
   Hankalin Hajjo ya tashi sosai. Ta zauna tana lallashinta amma Nu'aymah sai taƙi saurarenta. Tana cikin darzar kukan Baba malam ya shigo sashen hajjon da daddare bayan ya taso daga wajen karatu a massallaci.
     Tsawa yayma Nu'aymah amma ba wadda zata sakata firgitaba. Tai saurin nutsuwa hawaye na sake rige-rigen sakko mata a kumatu.
   “K wai kin koma jaririyane a gidan nan yanzu? Da zaki zauna kitama mutane kukan banza da wofi. Ki fita idanuna Nu'aymah tunkan na saɓa miki. Bake kika zaɓama kanki hakanba da kanki? To daga yau na baki sati biyu kima shi wanda kika gudu dominsa magana ya turo iyayensa”.
     Cikin tashin hankali Nu'aymah ke kallon Baba malam. Bakinta na rawa tace, “Abbah wlhy ban guduba, dan ALLAH ka saurareni na faɗa maka yanda akayi”. “Bana buƙatar jin komai daga gareki Nu'aymah, dan saƙwannin da kika bar mana sun isheni dukkan amsa. To kin samu yanda kikeso. Kinso tozartamu ALLAH kuma ya hana faruwar hakan ya rufa mana asiri. Abdallah ne dai kince baƙyaso, ALLAH kuma ya canja masa da waɗanda suka fiki alkairi, sai kima wanda kikeson magana ya fito a aura masa ke kuje ku ƙarata”.
  “A....Ab....Abbah!” ta kira sunan Baba malam bakinta na rawa da jikinta. Sosai kalamansa suka nema zautata. ‘Yah Ab ɗinta ne yay aure da wata ba itaba?. Kai ina bazai yuwuba ma’. Tai maganar a fili tana kallon Hajjo dan baba malam tuni yay ficewarsa ma.
  Kamota Hajjo tayi ta rungume tana lallashinta. Tausayinta na ratsata. “Hajjo dan girman ALLAH kimin bayani, wlhy na kasa fahimtar kalaman Abbah gaba ɗaya. Da gaske yake Yah Ab yayi aure? Ya auri wata ba ni Nu'aymah ba?. Hajjo faɗamin dan ALLAH, taimakeni ki faɗain dan girman ALLAH hajjo”.
      “Ya isa haka Zainabu. Ki nutsu na miki bayanin komai to kinji”.
 Da sauri Nu'aymah ta shiga ɗaga mata kai tana share hawayenta da hannaye biyu. Hajjo ta ruƙo hanun nata, cikin nutsuwa tai mata bayanin komai daya faru a ranar bayan an wayi gari babu ita a gidan. Saƙwannin data ajiye musu akan ita ta tafi batason Abdallah sai Ameer.

ZAFAFA BIYAR 2021


             Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka karanta idan baka biyaba, karka kuma yaɗa dan ALLAH idan ka gani????????????.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????

09033181070


             “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un. Mike shirin faruwa dani ni Nu'aymah? Hajjo wlhy kinji na rantse miki bani nabar saƙon nanba. Kuma Ameer da ake magana akansa ni babu abinda ya taɓa haɗani da shi sai sako da Yah Abdallah ke bashi yana kawomin. Rabon kuma dana sake ganinsa wlhy anfi wata huɗu Hajjo”.
    “Ah ah! To amma shi kuma Abdullahin yace bai san Ameer ɗinba, bai kuma taɓa aiko wani wajenki ba sai Ahmadu”.
       “Bai taɓa ba Hajjo? Shi Yah Ab ɗin da kansa yace haka kuma?”.
      “Sosaima kuwa, a gaban kowama ya faɗa a randa al'amarin ya faru. Amma kwantar da hankalinki, Zainabu nima dai al'amarin nan ya ɗaure min kai matuƙa, yanda nasan kike da Abdullahi tayaya zaki aikata wannan abun? To amma iyayenki duk sun kasa fahimtar akwai wani ɓoyayyen al'amari daya faru a wannan ranar, musamman ma ɗan malam daya ɗauki zafi sosai akan al'amarin”.
     “Hajjo dan ALLAH ki taimakeni, wlhy inason Yah Abdallah fiye da yanda kowa yake tunani, dan ALLAH ku tausaya mani karna rasashi hajjo. Idan na rasashi mutuwa zanyi......”
    “Bazaki mutuba Zainabu kinji, ki kwantar da hankalinki muyita addu'a ALLAH na nan, yana sane da komai kuma shine maiyin maganin komai”.
   Kai Nu'aymah ta ɗagama Hajjo dake share mata hawaye, ta kwantar da kanta a jikinta saboda kanta dake wani irin bala'in sara mata kamar zai tsage. “Hajjo kaina”. Hankalin hajjo ne ya sake tashi, dan sam ba'ason ciwon kai ga Nu'aymahr, daboda ciwonta. Saurin tada ita tayi daga jikinta ta kwantar da a kujerar tana faɗin, “Ina zuwa, bara na amso miki maganinki kisha”. 
    Hajjo da kanta ta nufi sashen su Nu'aymah dan yaran duk basu shigoba daga ita sai Nu'aymah ne kawai. Baba malam da Umm suna zaune a falo ta shigo, Muhammad na gefe yana homework.
    Da sauri suka shiga tambayarta ko akwai abinda take buƙata?. Fuskarta babu ko ɗigon walwala tace su bata maganin Nu'aymah kanta ke ciwo. Ba ƙaramin faɗuwa gaban Umm yayi ba, amma saita danne ta tashi taje ɗakin Nu'aymahn ta ɗakko ɗan box ɗin da magungunanta ke a ciki ta kawoma Hajjo. Tanason taje taga mike faruwa da ɗiyar tata amma tanajin nauyin hakan. Ga baba malam yay kamar abin bai damesabama, ya cigaba da shan fruit salad ɗinsa hankali a kwance.
 Hajjo dai batabi takansuba ta amsa tai ficewarta. Da kanta ta bama Nu'aymah maganin, sannan ta kamata ta kaita bedroom ɗinta ta kwantar. Cikin amincin ALLAH babu jimawa barci yay gaba da ita.

      Washe gari da zazzaɓi Nu'aymah ta tashi ga ciwon kai. abinda ya tada musu hankali Doctor ɗinta yayi tafiyar da yace, gashi kuma basu nema wancan likitanba. Andai kaita asibiti wani likitan daban ya dubata, yaɗan mata abinda zai iya ya turasu asibitin dawanau. Kamar koda yaushe Baba malam yaƙi yarda a kai Nu'aymah dawanau, dan acewarsa yarinyarsa ba ciwon hauka take ba. Yasan dai ance tanada matsala a ƙwaƙwalwa. Hakan yasa ya ɗakko file ɗin Nu'aymah da shirin neman wancan Doctor ɗin. Amma abin mamaki da al'ajabi babu takardar da Numbers ɗin take. Anyi ɗai-ɗai da file ɗin babu ko alamar takardar. Kamar wasa aka bincike littatafan baba malam dake tare da file ɗin tas babu takardar dai.
 Wannan al'amari ba ƙaramin ɗaure kan kowa yayiba a gidan. Musamman da ya zam agaban kowa Doctor ya bada takardar da file ɗin. Wannan al'amari ya sake ɓata ran baba malam matuƙa, amma jarumar fuskarsa taƙi nuna hakan. Sai Hajjo ce keta masifa kamar zata haɗiye harshenta. Dan wannan ɗauke takardar ya sake tabbatar mata da akwai mai yin ƙulle-ƙulle a gidan da gaske. Sai dai yanda kowa ya nuna damuwarsa akan al'amarin baka isa nuna zarginka kai tsaye akan wane ne ɗin ba.

           “Maganar gaskiya al'amarin gidannan ya fara bani tsoro Abban Nu'aymah. Anfa daɗe ana ruwa ƙasa na shanyewa, dolene a wannan karon nasan wanene ke mana SARAN ƁOYE. Tunda har aka iya toshe hanyar neman lafiyar Nu'aymah lallai za'a iya kashe mana ita ma”. Umm tai maganar hawaye na zuba mata masu zafi.
      Zama baba malam daketa kai kawo a ɗakin yay kusa da Umm, ya kafeta da idanunsa da sukai jajur shima saboda damuwa. “Jannat idan munce zamu ɗauki mataki, akanwa zamu ɗauka? Akan kuma mi?”.
   “Amma Abbah Nu'aymah karka manta musabbabin ciwon Nu'aymah fa faɗo da ita akai daga kan gado tun tana jaririya, kanta ya bugu ta samu ciwo a ƙwaƙwalwa. Badan ALLAH ya taƙaita wahalaba da zata tashine cikin halin rashin hankali kamar yanda Doctor ya sanar mana. Addu'a da hikimar UBANGIJI ce ta cigaba da jagorancin lafiyar Nu'aymah hartakai wannan lokacin cikin hankalinta, sai dai idan ciwon ya motsa tasha wahala. Tun Nu'aymah batasan ma'anar magani ba ake ɗura matashi a ciki, kanaji kwanaki badan ALLAH yasa Doctor ya farga ba hantarta fa harta harbu da ciwo saboda yawan shan magani. Abban Nu'aymah baka tunanin game da al'amarin aurenan akwai wani abu da bamu hasasoba kuwa?”.
       “Kiyi haƙuri Jannat karmu zargi kowa akan al'amuranmu, mu daure mucigaba da ɗaukar komai akan jarabawa ne. Duk abinda yay farko nasan zaiyi ƙarshe. Da ALLAH na dogara game da lafiyar Nu'aymah nasan kuma shi mai jine mai kuma ganine. Indai bamu da haƙƙin kowa ALLAH bazai bama kowa damar shiga haƙƙinmu ba. Ki kwantar da hankalinki, insha ALLAHU zan sake samo Number likitan nata, dan mantawama nai nace masa idan ya tafi ya kiramu”.
       Kanta ta jinjina masa hawaye na cigaba da sauka mata. Ya saka hannu ya share mata yana murmushin da shima iyakarsa laɓɓansa ne kawai. Shi kaɗai yasan mi yakeji a ransa. Yana dai ƙoƙarin dannewane dan yasamu Umm ta kwantar da nata hankalin kodan hawan jininta............✍

SAHFAT PREORDER!


    Wani kaya sai amale ka ɗauka????.

SAHFAT PREORDER maida tsohuwa yarinya.

Kaji masu kawo kayan adon gida dana jiki ƴan gaske.

Ina mata masu ƴan bana bakwai? ko uwargidar da ake shirin kawoma ƴar bana bakwai?. Kai hardama matan gayu ƴan ƙwalisa masu son sabunta gida da kayan ado ƴan waje masu sauƙin farashi da nagarta!.

To ku garzayo dama ta samu, dan SAHFAT PREORDER sune na ɗaya a wannan fanin. Idan kayan kitchen kikeso masu ƙyau da nagarta a farashi mai sauƙi kuma zaki samu a Sahfat preorder. Idan kayan sakawa kikeso na manyan mata ƴan gayu suma akwaisu babu ƙayarya. Jaka ko takalma na nunawa tsara suma ba’a barsu a baya ba harma da mayafai. Hakama kayan ɗaki basu da tsara.

Ni shaidace domin dukkan kayana ta hannunsu nake samu nima. Ku garzayo kuma a dama daku dan nasan zakuyi alfahari da hakan insha ALLAHU.

Kiyi magana ta wannan Number 08142957548 insha ALLAH zaki samu ƙarin bayani ƴar uwa.

Siyen nagari????, maida kuɗi gida???? sai SAHFAT PREORDER????????????????????


ZAFAFA BIYAR 2021


Hafsat miss xoxo????
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).????????

      Mamu gee????

MIN ƘALB!!????????

    Hafsat rano????

ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!????????

    Safiyya huguma???? SIRAƊIN RAYUWA????????

     Bilyn Abdull????

SARAN ƁOYE????????

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka????????????????

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????

09033181070

????????????????????????????????????????
TEAM—-ZAFAFA BIYAR????????????????

ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????.
[5/28, 3:14 PM] Queen Meenali????: Typing????

No. 11


ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE

   *_KAJI shahararrun kuma mandiyoyin ƴan ƙwalisar kawo kayan kitchen masu tafiya dai-dai da zamani. Idan nace nadaban ina nufin suɗin nadabanne wajen kaya ƴan gaske dake ƙawata kitchen ɗin amarya harma dana uwargida ƴar ƙwalisa. Ka siya ka tabbatar ka saya ɗin ko a gaban tsaranka sai ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE. sunan kayansu sa kishiya cin bashi????, dan tana ƙyalla ido taga kitchen ɗinki tsarin amerikawa tuni zata fara ƙwafa da tunanin zuwa gidan delu dillaliliya mai saida kwanika. Sai dai kuma kama da wane akace bata wane, dan haka ku maza ku garzaya ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE. domin samun naku kuma. Suna kawo kaya daga ƙasashen ƙetare akan farashi mai sauƙi da rahusa. Suna order ɗin products kamarsu, dukan kayan kitchen na zamani, bedsheets, shoes dade sauransu, products ɗinsu pre-order ne dake zuwa akan lokaci batare da mai kaya ya ƙosa da jira ba ko samun matsala. Zaku iya samunsu a Number waya kamar haka ko Location nasu. Phone number: 08102393622. Location Gombe. Amma Zasu iya turawa kowani gari dake a lungu da saƙo na ƙasarnan. Sayen nagari maida kuɗi gida. Ku garzaya kar ayi babu ku. Da ƙyar nasha yafi da ƙyar aka kamani inji masu iya magana????????????????????._*

…………….Kamar bazata juyaba sai zuciyarta ta bata shawarar juyawa taga wane shahararran ƙwallan mara imanine da mutuncine shiɗin,
Abun mamaki babu kowa a wajen, sai dai an sauke glass ɗin motar kaɗan alamar tanan koma wanene ya isar da saƙon nashi. Jitai zuciyarta ta sake hawa sama fiye da da. Ta yunƙura da nufin nufar motar gayun nan suka sake mata zobe. Kallonsu tai sama da ƙasa a wulaƙance da faɗin, “Wlhy idan baku matsamin ba ɗaya bayan ɗaya saina muku fashin goshi da dutsen nan”.
Babu wanda ya motsa a cikinsu, da alama ma basa fahimtar yaren datai maganar, dan kallonta kawai suke tamkar wasu zakaru. Dutsenta da har yanzu ke a hannu ta sake ɗagawa zata bugama wani again. Da sauri yay baya da ɗana kunamar bindigarsa yana huci. Nu’aymah ta taɓe baki tamkar bata fahimci abinda yake shirin yiba, ta sake ɗaga dutsenta ta makama na gefen hannun haggunta a goshi cikin rashin tsamanin hakan daga garesa.
Ƙara ya saki da duƙewa ƙasa bindigarsa na faɗuwa dan abun yazo masa a bazata, babu yanda za’ay kai tunanin shiɗin zata bugamawa. Ƙafa ɗaya daga ciki ya saka ya taɗeta tai baya zata faɗi cikin security ɗin gidan marayun da suka iso yanzun wajen yay saurin tareta. Ai tanajin bata kai ƙasaba tai wani irin ɗagowa da sauri ta wulwula dutsin nata sai akan motarnan dai ta ɗazun data fasama glass, kuma a gaba ya sauka, dan haka glass ɗin ya ƙara tsatstsagewa fiye da ɗazun.
A yanzunkam bodyguards ɗinsa sun tabbatar bazasu iya haƙura da tsagerancin yarinyarnanba, sai sun ɗauki mataki duk da ogansu bai basu damar yin hakan ba. Hannu ɗaya daga ciki ya ɗaga zai kwasheta da mari iya ƙarfinsa, sai dai ganin za’a buɗe ƙofar motar ne ya sakashi dakatawa da nufar motar da sauri ya ƙarasa buɗewa yana saurin cewa, “Sorry Sir”..
Banji an amsashi ba, sai dai motsin da naga anyi daga cikin motar ya bani tabbacin wanda ke a ciki zai fitone. Ba Nu’aymah kaɗai ba, harsu Yusrah sun zuba idone suga mai fitowar.
Ƙafarsa dake cikin baƙin takalmi mai shegen ƙyau ta fara bayyana, kafin farin wandonsa. A hankali ya dire sandarsa ƙasa itama tare da ɗayar ƙafarsa ya fito gaba ɗayansa.
Koni mai ɗaukar rahoto saida na furta ‘masha ALLAH’ a zuciyata. Zuƙar iskar yammaci data fara kaɗawa yay a hankali cikin hancinsa ya fesar yana sake tamke farar fuskarsa dake zagaye da baƙin gashin saje siɗik, dan a rayuwarsa ya tsani kallo. Baiko kalli ko sashen dasu Nu’aymah da guards ɗinsa sukeba ya nufi inda su Nanah suka rufu kan yaron tare da securitys ɗin gidan marayun. Hannun Malika dake a saitinsa ya kama ya matsar da ita gefe, hakanne ya sakasu farga da isowarsa duk suka dawo cikin hankalinsu daga kallon ƙurullar da suke masa. Baice dasu uffanba yay wani ɗan dirƙuson gayu gaban yaron tare da kai yatsunsa biyu saitin hancinsa, yakai kusan sakan goma kafin ya janye, sai kuma ya maida kan jijiyar wuyansa dake a saitin kunne. Nanma ya kwashe sakan goma da ɗoriya sannan ya ɗauke. Miƙewa yay tsaye, idanunsa dake cikin baƙin glasess akan ƙaton symbol ɗin da aka rubuta sunan gidan marayun, kafin ya janye ya maida dubansa ga guards ɗinsa da har yanzu suke zagaye da Nu’aymah kamar wata ɓarauniyarsu. Da hannu yay musu nunin su barta, tare da yin wani salo da yatsunsa biyu wanda shi da su ne kawai sukasan ma’anar yaran nasa.
Cike da takaicin rashin ɗaukar mataki a kanta sukaja baya kowanne na zuba mata harara a ƙasan ido da huro hanci. Gaba ɗayansu garesa suka nufo. Ɗaya daga ciki ya matso sosai inda yake, A hankali ya furta maganar da babu wanda ya iya jinta a cikinsu Nu’aymah, dan kuwa jajayen laɓɓansa ne kawai suka motsa kaɗan. Ganin haka ya saka Nu’aymah nufosu da sauri itama. Yana ɗaga ƙafarsa zai bar wajen tana isowa tasha gabansa.
“Kai malam dakata mana! Shin babu zuciyane a ƙirjinka kokuwa kana tunani da zuciyar takane bada ƙwaƙwalwa ba?”.
Kallonta yake daga sama har ƙasa ta cikin glasess ɗinsa, batare da yama nuna alamar ya fahimci yaren da take maganar da shiba ya raɓata zai wuce abinsa. Hanzarin riƙo sandarsa tai ƙoƙarin yi Yusrah ta riƙeta. Cikin magana raɗa-raɗa tace, “Aymah calm down Please, kalla kiga”.
Sai da ta zubama bayansa harara kafin ta kalli abinda Yusrah ke nuna mata. Securitys ɗin gidan marayun ne tare da guards ɗin nasa uku dasu Nanah ta hango harsun kusa shigewa cikin Orphanage ɗin ɗauke da yaron a hannun ɗaya daga cikin guards ɗinsa. Juyawa tai da sauri ta kalli inda yake shima sai ganin motocin uku tai har sunyi reverse suma da alama gidan marayun zasu shiga.
“Zuciyarki tayi sanyi ko? Iya masifa! ALLAH wataran sai kinsa an maidamu kwalta Nu’aymah, jibesu tamkar wasu bajiman zakuna su da ogan nasu. Da ganinsu kasan ba hausawa baneba ma, ke koma tsoro baƙyaji”.
“Mtsoww! Ina ruwana da rashin kasancewarsu Hausawa, inda banyi musu hakanba ai guduwa zasuyi dan tsabar rashin sanin darajar ɗan adam. Ko dabba suka bige ai ta cancanci su fito suga lafiyarta balle mutum, shegu masu suffar baƙaƙen aljanu”.
Dariya Yusrah ta kwashe da ita tana faɗin, “Amma dai banda wannan Handsome ogan nasu ko? Dan wlhy dai kam komai yaji zammm anan kema kin sani”.
“Ke kikaga wannan”. Nu’aymah ta bata amsa tana fisge hannunta dake cikin na Yusrahn ta tsallaka titi ta barta tana dariya. Dan ta kula bori kawai Nu’aymah keyi itama tasan gayen ya haɗu masha ALLAH, sai dai yanayinsa sam bai mata kama dana Musulmai ba, dan askin kansa kawai da ƙaton sarƙan Cross na diamond dake a wuyansa, da ɗan kunne guda ɗaya manne a kunnensa ya isa amsar hakan a garesu.
Hango Nu’aymah har zata shige cikin Orphanage ya sakata saurin tsallaka titin itama ganin babu mota tabi bayanta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button