SARAN BOYE COMPLETE

Nu'aymah da har yanzu keta faman jan tsakin takaicin mutanen ta nufi clinic ɗin gidan kanta tsaye, tasan dai bazai wuce can suka nufa da yaron ba. Kasancewar tafiyar tata sai a hankali, ba wani sauri ta iyaba kuma akwai tazara tsakanin gate ɗinma da clinic ɗin saiga Yusrah harta isketa. A tare suka ƙarasa batare data kula Yusrah daketa son taga ta sakko ba. Tsaitsaye suka iske su Nanah a reception da guards ɗin mutumin, sai bah-bah hindatu ɗaya daga cikin masu kula da yaran, da kuma Abban Adawiya da ashe tun ɗazun yana a cikin gidan marayun su Nu'aymah basu saniba.
Waige-waigen inda zataga gayen ta farayi, sai dai babu ko mai kama da shi a wajen. Wani takaicine ya sake dirar mata a zuciya, cikin ranta ta ayyana ‘Wato shi yamafi ƙarfin shigowa kenan? To ai idan yasan wata baisan wataba’. Ta nufi hanyar fita tana surutunta a zuciya.
Yusrah da tunaninta ya bata Nu'aymah zata iya zuwa ta sakemusu ɓarna a motoci tai saurin riƙo hannunta tana faɗin, “Ina kuma zakije?”.
“Yusrah sakeni, bakiga wannan mai shegen taurin kan bai biyosu ba”. “Oh ALLAH, to minene idan bai shigo ɗinba, baga guards ɗinsaba, nasan ai zasu wakilcesa. Ki tunafa ba shine ya buge yaron ba ma, cikin guards ɗin nasane tunda shi yana a motar tsakkiyane, sannan ba shinefa ke tuƙinba”.
“Wannan matsalarsace kuma, ai wanda ya bige ɗin dai yaronsane ko? To ya zama dole shina ya kasance a wajen wlhy dan ya ja masa matsala”.
Kafin Yusrah ta samu damar mata magana sai gashi ya fito daga ɗaya a cikin ɗakunan clinic ɗin, Dr Safwan biye da shi a baya, taku yake cike da nutsuwa irinta zaratan samari masuji da lokacin ƙuruciya da kwanciyar hankali. Handglop ɗin dake a hannunsa taga yana zarewa ya jefa cikin shara. Har yanzun dai idanun nasa a toshe suke da Google ɗin, kuma fuskar a tamke, tana ƙoƙarin janye idanunta daga kallon nasa caraf suka sauka bisa kan ƙatuwar sarƙar Cross ɗinsa da aɗazun masifa baisa ta ganta ba.
Cikin suɓutar baki tace, “Ashe Arne ne shiyyasa baida imani”.
Karaf wannan magana a kunnensa. Sai dai yanza yazo ya gittata ya barta da ƙamshin turarensa mai sanyin daɗi batarr da ko kallon inda takeba ne, zaka fahimci da wahala ace yamaji mitace, maybe ma bayajin hausar sam.
Wajen Abbah dake zaune ya ƙarasa, suna ɗan nesa dasu kaɗan shiyyasa bazasu iya jin mi suke faɗa ba. Ta taɓe baki da nufar Dr Safwan tana tambayarsa yaya jikin yaron?.
“Jikinsa Alhmdllh, ai bama wani ciwo yaji sosai ba, yadai bugune a kansa da hannunsa na haggu, insha ALLAH kuma fatan komai zaiyi normal da wuri”.
Duk da taji daɗin hakan sai bataji ranta ya huce daga haushin mutuminda ita kanta shaidace tasan ba shine ya aikata laifin ba. ‘Amma kuma ai ogan wanda ya aikata ɗinne’ ta raya a cikin ranta cike da gamsuwa da jawabin zuciyarta.
Ɗakin da yaron yake kwance suka nufa suka dubashi duk da ansa masa ruwa barci ya ɗaukesa. Lokacin da suka fito basu iske mutanenba har motocinsu. Hakan ya bama Nu'aymah tabbacin sun wuce kenan.
Suma nufar hostel ɗin yaran sukai suna sake tattauna abinda ya faru, tare da yin gulmar mutumin dako sunansa basu saniba. Nu'aymah dai uffan bata cewa, dan ita takaicima suke ƙara mata a kanshi kawai.
ZAFAFA BIYAR 2021
Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka karanta idan baka biyaba, karka kuma yaɗa dan ALLAH idan ka gani????????????.
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????
09033181070
Tunda suka baro cikin Orphanage ɗin ya kwantar da kansa jikin kujera yay shiru idanunsa dake da cikar baƙin gashi da gira a sama suna a lumshe. Sai faman juya glasess ɗinsa dake a hannunsa na dama yake tamkar zai karyasa. Gaba ɗaya abinda ya farune ke dawo masa cikin zuciya daki-daki. Ya yarda yaran Arewan nan basajin magana tamkar yanda yakeji ana shan faɗa. Jibafa yanda ƴar yarinya ƙarama sa'ar ƙanwarsa Victoria ta tsaya agaban bindiga tana musu raini tamkar wasu sa'anninta. A karan farko yaja ƙaramin tsaki da furzar da iskar daya cika baki da ita yana maijin takaicin komai a ransa. A hankali ya buɗe idanunsa ya kai dubansa ga glass ɗin gaban motar tasa da Papansa yasa maƙudan kuɗi wajen siya masa. Yau shine hawansa na farko da motarma gaba ɗaya, dan sati biyu da suka wuce papa ya bashi ita a birthday ɗinsa matsayin gift. Amma sai gashi cikin sakanni an mata walmakalifatu, kamar Mom tasan hakan zai faru tace bata yarda yazo kano a mota ba daga Abuja, shi kuma gashi yanada uzirin da bazai yuwu ya fasa tafiyarba, dan dama zaibi jirgine kamar yanda ya saba sai akace jirgi bazai tashiba dan yanayi babu ƙyau yau. Shinefa ya zaɓi tahowa a mota duk da Mom bataso hakanba. Sake rumtse idanunsa yay da shegen ƙarfi da cije lip ɗinsa na ƙasa sosai tamkar zai hudashi da haƙori.
Duk abinda ya keyi drivernsa na kula ta cikin mirror, hakanne ya saka zuciyarsa sake zafafa da abinda yarinyar tai musu shima, ya kai hannu ya shafa inda Nu'aymah tai masa rotse da dutse aka saka masa bandage, wlhy yau badan oga ya hanasu ba da yarinyarnan saidai uwarta ta haifa wata. Shiyyasa shifa a rayuwarsa yay mugun tsanar ƴan Arewa ɗin nan musamman hausawa, ƙauyawa dasu ko karatu basayi sai rashin mutunci. (Humm malam driver naka tunanin kenan, amma ƴan Arewa sun wuce da sanin duk wani gurɓataccen tunaninka ai????????). Shi yanzu babban tashin hankalinsa ma mi zasuce da Madam ɗinsu akan wannan al'amarin daya faru?, dan kowa yasan yanda family ɗin gaba ɗaya ke masifar so da ƙaunar ogan nasu tamkar wani tsoka ɗaya a miya.
Haka dai suka cigaba da tafiya kowa da abinda yake saƙawa a cikin rai. Gashi mahaukacin gudu sukeyi kai kace Lagos suka nufa ba Abuja ba.
Tunda 6pm tayi kiran Mom ya fara shigowa a wayarsa, sai dai ko sau ɗaya bai amsa mataba ya share, sai ma kwanciya daya gyara cikin lallausar kujerar motar ya cigaba da latse-latsen laptop ɗinsa har yanzu da takaicin Nu'aymah a ransa.
ABUJA
*_09:30pm_* Dai-dai suka shiga garin Abuja saboda holdup daya riƙesu a madalla zuwa Kubwa expres, da ƙyar suka fita a jigace, dan kafin su iso Asokoro ji yay tamjar ya fasa ihu dan gajiya, shi dama can mutum ne da baida jimirin tafiya mai nisa a mota, duk da tafiye-tafiye sun kasance cikin ginshiƙin aikinsa kuwa.
Anguwace da bata da maraba da a cikin turai saboda rashin hayaniya da haɗuwarta. Ko ina ƙwanyar yake da wutar nepa tamkar rana, duk da dare baiyi nisaba babu abinda kakeji sai haushin karnuka. Motocin uku suka tsaya dai-dai saitin wani ƙaton baƙin gate da zaka iya hango cikin gidan daga waje kasancewarsa tamkar net. Horn sukai, da gudu sai ga wani dake cikin Blue Uniform ya iso da sauri ya buɗe musu.
Tunkan su gama dai-daita parking idanunsu suka sauka akan Madam Chioma dake ta faman kai kawo ta barandar saman bene. Sai dai ganin shigowar motocin tuni tabar wajen da alama zata fitone.
Tuni Securitys ɗin gidan kusan su goma sha biyar suma sukayoma motar caaa. Buɗe masa akai da sauri, sai dai kafin ya fito Madam Chioma harta iso. Da kanta tasa hannu ta fiddosa a motar, tai saurin rungumesa tana magana cikin yarensu. “Yarona miya sameka? Ina kuka tsaya? Miyasa kaki ɗaga kiranmu?”. tashiga jero masa tambayoyin batare data bashi damar amsa ko guda ɗaya ba daga ciki.
“Relax Maa! i'm okay”. “Ka tabbatar?”. Ta faɗa tana ɗagosa daga jikinta hannayenta duka biyu akan kwantaccen sajensa tana shafawa, sai kuma tabi jikinsa da kallo daga sama har ƙasa. Ganinsa dai lafiya lau saita sake rungumesa tana faɗin, “Thanks God”.
“Ɗan uwa sannu da zuwa”. Wata murya ta faɗa daga bayansu cikin harshen nasara. Sakinsa Madam Chioma tai suka juya suna kallon mai maganar. Matashin saurayine da bazai wuce 22years ba, sai kuma wasu dake bayansa su kusan bakwai. Kallonsu yay ɗaya bayan ɗaya kafin ya buɗe masu hannayensa sukazo duk suka rungumesa suma suna masa sannu da zuwan. Sai da duk suka gama sannan ya amsa musu da “Thanks you”. a jimlace.
Har sun nufi babbar ƙofar shiga ainahin cikin gidan ɗaya daga cikin yaran cikin harshen turanci tace, “Jesus!! Miya faru da motarka Brother?!”.
A tare duk suka juya suna kallon motar, amma banda shi dama yay gaba abinsa tamkar baiji mi Joy ɗin ta faɗa ba.
Cike da firgici Madam Chioma ta shiga ƙwala kiran sunan guards ɗinsa ɗaya bayan ɗaya. Aiko jikinsu har rawa yake suka nufota ransu cike da tsoron amsar da zasu bata akan abinda sukasan dole su amsa tambayoyinsa dama.
Aiko a jajjere ta shiga jero musu tambayoyin ko bari su bada amsa batayi. Sai da ɗaya a cikin yaran da zatama iya kai sa'ansa tace, “Mom ki shiru haka mana su bamu amsar miya faru?”. Zata sake magana budurwar tai saurin sake faɗin, “Please Mom”. Shiru tayi badan taso hakanba. Ta maida hankali ga guards ɗin da saima yanzune ta kula da masu fasashshen goshi biyu a cikinsu. Babban ne ya shiga mata bayanin duk abinda ya faru tsakanunsu dasu Nu'aymah daga farko har ƙarshe. A take takaici da baƙin ciki suka sake rufeta ta shiga zagin Hausawa da kiransu da sunaye marasa daɗin ji. Sai da tayi iya iyawarta kafin ta bar wajen tabi bayansa. Suma sauran yaran bayan nata sukabi suna zagi.
Shikam yana shiga ƙaton babban falon gidan dake ɗauke da set ɗin kujeru biyu mabanbanta kala baiko tsaya ba yay saurin hayewa sama inda sashensa yake. Baya buƙatar kowa ya biyosa, dan haka yay saurin maida ƙofar corridor ɗin sashen nasa ya rufe, sannan ya ƙarasa nasa madaidaicin falon daya gama haɗuwa, yanata wani tattausan ƙamshi mai daɗin shaƙa da kwantar da zuciya. murza ma ƙifar falon key yayi sau biyu sannan ya shige. dispencer dake acan gefen dining mai ɗauke da madaidaicin d/table ya nufa, ya ɗauki glass cup dake cikin wani showglass mai ƙyau da ɗaukar hankali ya matsi ruwa. Tas ya shanye wanda ya ɗiban, ya ajiye kofin saman d/table ɗin ya baro wajen zuwa wata ƙofa dake a cikin falon. Nan ɗinma dai corridor ne, sai dai ƙofa biyu ce kawai a cikinsa, ƙofar ƙarshe ya nufa yana zame baƙar jacket ɗin jinsa tunkan ya buɗe. Ya riƙeta a hannu ɗaya sannan ya ƙarasa ya murda handle ɗin ƙofar ya tura ya shiga.
Fes ɗakin yake shima, yanata tashin ƙamshin fresheners data haɗe da turaren da yake amfani da shi. Jefa jacket ɗin yay saman gadon ya ƙarasa gaban mirror yana ƙoƙarin cire sarƙar cross ɗin wuyansa. Ya ratayeta jikin wani ɗan hangar ƙarami mai ƙyau dake cike da sarƙoƙin kala-kala a ajiye saman mirrorn. Zama yay a stool ɗin gaban madubin yanata faman yamutse fuska dan yunwa yakeji, sai da ya cire takalman ƙafarsa da safar, farar ƙafarsa dake fes ta bayyana kafin ya miƙe kansa tsaye ya nufi wata ƙofar da ko ba'a faɗaba kasan toilet ne.
Yana shiga aka fara knocking ƙofar falonsa, amma sai ya share ya cigaba da abinda yake a ciki. Anyi kusan sau uku sannan aka bari. Ya ɗauki tsahon lokaci a bayin kafin ya fito sanye da bathrobe Milk color. Hannunsa riƙe da ƙaramin towel yana tsane sumar kansa da kallo ɗaya zakai mata ka fahimci tana masifar lasar kuɗaɗe kodan ƙyawun da take dashi ga mai kallo a ido balle kuma wanda ya taɓa.
“Yoohan! Buɗe min ƙofa”. Ya tsinkayo muryar Mom tana faɗa cikin yarensu da ɗan buga ƙofar yanda tasan bazai takurasa ba. Gefe ya karyar da wuyansa yana yamutsa fuska da yarfar da hannayensa duka alamar shifa an takura masa. Fuskarsa cike da takaici yaje ya buɗe mata tare da juyowa a binsa batare da ya tsaya saurarenta ba.
Ƴar dariya tayi abinta, dan ko kaɗan hakan bai dametaba, tasan ya gajine matuƙa, shikuma idan ya gaji to lallai sannan baƙin ransa ke ƙara hauhawa, kowa kuma yimawa yakeyi har ita da Papa. Ƙarasawa tai inda yake tsaye a gaban mirror yana cigaba da tsane kansa. Kama hannunsa tai ta zaunar, ta amshi towel ɗin ta cigaba da goge masa kan tana kallonsa ta cikin mirror fuskarta washe da murmushi.
Shiko ya ciskule tasa kamar zai fasa ihu. Sai da ta tsane masa kan tas kafin tajawo hand dryer ta jona a jikin soket ta fara busar masa da shi. Ajiye dryer ɗin tayi da jan hancinsa tana faɗin, “Nasan wannan fushin bana komai bane sai yunwa da gajiya my boy. Taso kaje kaci abinci ka kwanta ka huta”. Tai maganar da turanci
Yana shirin miƙewa danya shirya akai knocking ƙofar, jiyay tamkar ya fasa ihu dan takaici, shiyyasa sam bayason zaman gidan nan wani lokacin, dan ana hanama rayuwarsa shaƙatawa da hutawa. A hakanma gwara nan, abinda yafi tsana shine zuwa ƙauyensu, dan anfi cika masa ciki da takaici acan fiyema da nan Abuja. Mom ce tai magana, shiko tuni ya miƙe ya koma wajen kayansa. Ɗaya daga cikin ƙannensa ce mai suna Victoria. Tarkacen kayansa ne daya bari a mota cikin guards nasa ya kawo tun ɗazun, shine yayta masa knocking lokacin daya shiga bayi, da yaji ba'a buɗeba ya koma dasu ya bama yaran akan idan ya fito saisu kawo masa.
Zubesu tai akan table ɗin gaban gadon, ta juya garesa zatai magana ya ɗaga mata hannu da sauri tare da nuna mata ƙofar fita. Baki ta kumbura ta juya ta kalli Mom nasu dake murmushi sannan ta fice tana buga ƙafafu da ƙananun kukan taɓara.
Miƙewa Madam Chioma tayi itama tana faɗin, “Ina jiranka kai maza ka fito”. Kansa kawai ya ɗaga mata ya cigaba da abinda yakeyi...........✍
Read more har bakwai yau?.????????????????????.
SAHFAT PREORDER!
Wani kaya sai amale ka ɗauka????.
SAHFAT PREORDER maida tsohuwa yarinya.
Kaji masu kawo kayan adon gida dana jiki ƴan gaske.
Ina mata masu ƴan bana bakwai? ko uwargidar da ake shirin kawoma ƴar bana bakwai?. Kai hardama matan gayu ƴan ƙwalisa masu son sabunta gida da kayan ado ƴan waje masu sauƙin farashi da nagarta!.
To ku garzayo dama ta samu, dan SAHFAT PREORDER sune na ɗaya a wannan fanin. Idan kayan kitchen kikeso masu ƙyau da nagarta a farashi mai sauƙi kuma zaki samu a Sahfat preorder. Idan kayan sakawa kikeso na manyan mata ƴan gayu suma akwaisu babu ƙayarya. Jaka ko takalma na nunawa tsara suma ba’a barsu a baya ba harma da mayafai. Hakama kayan ɗaki basu da tsara.
Ni shaidace domin dukkan kayana ta hannunsu nake samu nima. Ku garzayo kuma a dama daku dan nasan zakuyi alfahari da hakan insha ALLAHU.
Kiyi magana ta wannan Number 08142957548 insha ALLAH zaki samu ƙarin bayani ƴar uwa.
Siyen nagari????, maida kuɗi gida???? sai SAHFAT PREORDER????????????????????
ZAFAFA BIYAR 2021
Hafsat miss xoxo????
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).????????
Mamu gee????
MIN ƘALB!!????????
Hafsat rano????
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!????????
Safiyya huguma???? SIRAƊIN RAYUWA????????
Bilyn Abdull????
SARAN ƁOYE????????
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka????????????????
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????
09033181070
????????????????????????????????????????
TEAM—-ZAFAFA BIYAR????????????????
ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????.
[5/28, 3:14 PM] Queen Meenali????: Typing????
No. 10
ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE
*_KAJI shahararrun kuma mandiyoyin ƴan ƙwalisar kawo kayan kitchen masu tafiya dai-dai da zamani. Idan nace nadaban ina nufin suɗin nadabanne wajen kaya ƴan gaske dake ƙawata kitchen ɗin amarya harma dana uwargida ƴar ƙwalisa. Ka siya ka tabbatar ka saya ɗin ko a gaban tsaranka sai *ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE*. sunan kayansu sa kishiya cin bashi????, dan tana ƙyalla ido taga kitchen ɗinki tsarin amerikawa tuni zata fara ƙwafa da tunanin zuwa gidan delu dillaliliya mai saida kwanika. Sai dai kuma kama da wane akace bata wane, dan haka ku maza ku garzaya ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE* domin samun naku kuma. Suna kawo kaya daga ƙasashen ƙetare akan farashi mai sauƙi da rahusa. Suna order ɗin products kamarsu, dukan kayan kitchen na zamani, bedsheets, shoes dade sauransu, products ɗinsu pre-order ne dake zuwa akan lokaci batare da mai kaya ya ƙosa da jira ba ko samun matsala. Zaku iya samunsu a Number waya kamar haka ko Location nasu. Phone number: 08102393622. Location Gombe. Amma Zasu iya turawa kowani gari dake a lungu da saƙo na ƙasarnan. Sayen nagari maida kuɗi gida. Ku garzaya kar ayi babu ku. Da ƙyar nasha yafi da ƙyar aka kamani inji masu iya magana????????????????????._*
_________________________
………….Yau Nu’aymah ta tashi jikin nata daɗan dama, sai dai rashin ƙarfin jiki. Tunda Ahmad ya tafi raka Hajjo asibiti ganin Doctor saboda ƙafarta saita dawo sashensu ta kwanta. Barci tai sosai dan har sai gab da azhar ta tashi tai wanka. Shiri tai da ɗan sauri-saurinta ta fice zuwa ɗakin Umm, dan wani irin maitan awara takeji. Babu kowa a ɗakin, sai gyara da yasha yanata uban ƙamshi. Tai murmushi da faɗawa saman gadon ta kwanta tana mai sake shaƙar turaren wutar da ƙyau cikin hancinta. Tana masifar son ƙamshi a rayuwarta. Shiyyasa turare kwana kaɗan yake mata ya ƙare. Ga baba malam da Yah Ab sun mugun ɗaure mata ƙugu wajen siya mata. Sam basa gajiyawa. Kafin wani ya ƙare an saya mata wani. Ga khumra da Umm itama take bata ita da Adawiya. Tun Adawiya bata damu da ƙamshiba harta fara biyema Nu’aymah saboda yanda take bulala musu shi a cikin ɗaki kamar shagon saida shi………
“K! Kuma yaushe kika shigo nan?”. Umm ta faɗa tana kallon Nu’aymah dake kwance a kan gadonta idanu a lumshe.
A hankali ta buɗesu akan Umm dake kallon yanda tai rama cikin kwanaki kaɗan. Tai ɗan ɓata fuska kamar zatai kuka. “Umm dan ALLAH awara zanci”. Kai Umm taɗan girgiza da nufar gaban mirror ɗinta ta ɗauki ƙaramar wayarta da tazo ɗauka. “Indai banda fitina ni ina naga awara yanzu Nu’aymah? Ke dai inhar kikai zazzaɓi sangarta iri-iri kin iyata mara dalili, ko Muhammad baya iya shegenki a gidan nan”.
“Umm Please!”. Ta sake faɗa cike da shagwaɓa kamar zatai kuka. Zama Umm tai a bakin gadon kusa da kanta. Taɗan shafa goshinta a hankali, “Nu’aymah banson rigimar nan, yanzu dai kinsan baza’a samu awaraba ko? Sai ki bari sai anjima, bara dai na bama Saude takai kuɗin gidan ƴan awaran”.
Kai Nu’aymah ta ɗagama Umm tana murmushi, sai kuma ta tashi zaune ta rungumeta tana ƴar dariya. Zame hular kanta Umm tai ƙoƙarin yi. Da sauri Nu’aymah takai hannu zata riƙe dan tasan mi Umm ɗin zata duba. “Umm kainafa ke ciw…..”
“Ƙaniyarki keda ciwon kan, wai Nu’aymah bazaki daina wannan shegen ƙazantan nakiba na rashin son ƙitso? Kalla kiga fa kanki gashinki duk ya lalace saboda rashin kula. Tashi maza ki wuce wajen Adda ta kama miki kai kafin na ɓata miki rai”.
Ƙwalla cike da idonta ta kalli Umm, “Umm dan ALLAH ba yau ba”. “Kin rainani ko?”. Umm ta faɗa tana ɓata fuska.
Muhammad dake ƙoƙarin shigowa ya ƙyalƙyale da dariya yana faɗon, “Umm ALLAH fa ta rainaki, inba rainiba ya zakice taje kitso ta zauna shagwaɓa……”
Filo Nu’aymah ta ɗauka ta wurgama Muhammad ɗin. Ya goce yana dariya. “Wlhy idan na kamaka a gidannan saina tsiyayar maka da man kai tas. Umm ki faɗama yaron nan nifa ba sa’arsa bace”. Yanda tai maganar idanunta cike da ƙwala ya saka Umm yin ƙaramar dariya itama, tai saurin saka hannu ta rufe bakinta tana haɗiyeta ganin hawayen harsun sakko a guje.
“Uhghumm!” Umm tai gyaran murya tana haɗe fuska da wurgama Muhammad harara. Hannayensa ya haɗe waje guda fuskarsa da murmushi yace, “Am Sorry aunty N”. Ya ƙare maganar da mata gwalo kaɗan. Harara ta zuba masa ta koma ta kwanta da juya masu baya shi da Umm ɗin.
Hannu Umm ta bashi suka tafa, kafin ya haye gadon yana faɗin, “Banace kiyi haƙuri ba Noorunnisa”. Juyowa tai fuskarta ɗauke da murmushi ta dungure masa kai tare da ja masa hanci tana faɗin, “Yaro 1-0”.
Dariya sukayi a tare. Umm ta miƙe tana murmushi ta bar musu ɗakin.
★★★★
Sashen Addah Umm ta nufa, dan tanason su tattauna game da al'amarin nan na Nu'aymah tun jiya, sai dai rashin lokaci yasa bata shigaba. Tasan itama Addahn bata shigo bane saboda taga baba malam ya wuni a gida jiya, yauma ya daɗe bai fitaba.
Kubrah kawai ta iske a falon tana yankan ƙumba. Ta gaidata cike da girmamawa kamar yanda suka saba. Dan bayan mahaifiyarsu Umm itace mace ta biyu a gidan da suke ɗauka tamkar mahaifiya. Fuskar Umm ɗauke da murmushin itama ta amsa mata, “Ɗiyata saike kaɗai a gidan kenan?”. “Eh Wlhy Umm, daga ni sai Addah kawai. Hajarah da su Jafar sun fita aika”. “To ALLAH ya maidosu lafiya. Ina Addan?”. “Umm tana ɗaki ki shiga mana”.
Kafinma Umm ta amsa mata Addah ta fito daga ɗaki. “Haba nifa ince kamar muryar Umm, ashe kuwa kece?”. “Ƙyaface haka mana, tun jiya rabon danaga idonki a gidannan Addah. saboda kinga ƴarki ta samu lafiya”.
“Wacefa lafiya Umm, anason a ganmin bayanta”. Addah ta faɗa cikin ɓacin rai. Murmushi Umm tayi da kama hannunta, dan tasan Addah dama bata barin saita kwana sam. “Kinga nidai muje sarkin hawa”.
“Bazaki ganeba Umm. Daga jiya zuwa yau naje sashenki yafi sau a ƙirga amma sai na iske Baba malam na nan. Wlhy na kwana tamkar na ciji kaina dan baƙin ciki. Gaskiya Umm wannan al'amarin bai kamata mu zuba masa idanuba a wannan karon, yanzu dan ALLAH minene na ɗaukar Number wayar likita idanba zalunci ba? Lafiyarta ne ba'ason anema kenan ko minene?”.
“Humm Addah wlhy nama kaina wannan tambayar yafi sau dubu tsakanin jiya zuwa yau. A a daren jiya har musabbabin ciwon Nu'aymah sai da ya dawomin a rai. Bansan minene laifin yarinyar nanba akeson rayuwarta ta salwanta. Ni harma na rasa wane kalar tunani zanyi Addah, wanene? Miyasa? Mi mukai masa?......”
“Umm nidai tsakanina da ALLAH na fara zargin jama'ar gidan nan fa, idan har mai aikata wannan abubuwan ba'a gidan nan yakeba to daga ina yake zuwa? Nifa dagama jiya na fara tantama akan barin Nu'aymah gidan nan akan maganar aurenta. Shiyyasa ni dama tun farko ban yardaba. ni dama tun jiyan wani shawarace tazomin akan yanda zamu saka ido akan motsin kowa, na tabbatar insha ALLAH a hankali zamu samo bakin zaren”.
Kai Umm ta ɗaga mata cikin alamar nuna gamsuwa. Addah ta matso kusa da kunnen Umm ta gwargwaɗa mata hanyar daya kamata subi. Ɗari bisa ɗari Umm ta amince, suka ɗaura da addu'ar dacewa. Daga nan suka cigaba da tattauna al'amarin suna ƙarama juna haske. Umm bata bar sashenba sai da lokacin salla yayi. Ta koma sashenta tana jin daɗi a ranta, koba komai zuciyarta ta rage nauyin da tai mata. Shiyyasa akoda yaushe take sake godema ALLAH daya haɗasu aure gida ɗaya ita da aminiyarta. Su kashe su rufe matsalolinsu babu maiji sai ALLAH.
ZAFAFA BIYAR 2021
Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka karanta idan baka biyaba, karka kuma yaɗa dan ALLAH idan ka gani????????????.
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????
09033181070
DUBAI
Tun randa Abdallah yay waya da wadda yake zaton Momynsa ce ransa ya sake dagulewa gaba ɗaya. Wani lokacin ji yake tamkar ya naɗama Adawiya mugun duka ya cillata jirgi ta koma Najeriya. Sai dai tsoron fushin iyayensa ke sakasa dannewa.
A maimakon kwanaki bakwai ɗinma da yay niyyar suyi a kwana na huɗu yasa suka wuce Saudia. Adawiya sai jin daɗi takeyi dukda bata ganin koda murmushinsa. Ita kasancewa da shi a ƙarƙashin inuwa ɗaya kawai ya wadatar da ita a cewarta.
Ba wannan bane karonta na farko zuwa ƙasar saudia, sai dai yanda tazo a wannan karan yanada banbanci da sauran zuwanta na baya. Shiyyasa take wani jin kanta a sama. Wanda kuma takeyi dominsan ma baisan tanayiba. Tunda suka iso gidan da zasu zauna ya nuna mata ɗakinta bata sake ganin koda ƙeyarsa ba. Tsalle ta dingayi bayan fitarsa, dan ɗakin yayi matuƙar ƙyau da tsari. Sai dai kalar komar zaɓin Nu'aymah ne, harda ma manyan frames ɗinta guda uku da aka manna a bango, sai na Abdallah guda biyu shima. Dukansu sunyi masifar ƙyau. Ta taɓe baki da jan wawan tsaki, stool ɗin mirror taja duk ta juya na Nu'aymah dan har cikin ranta ta tsani ganinta, tunda itace sanadin hana tabbatar farin cikinta, saboda Nu'aymah yah Abdallah yaƙi sake mata, saboda Nu'aymah ta gagara daraja a garesa matsayinta na matarsa. Saboda Nu'aymah saboda Nu'aymah..... Komanta yaƙi dai-daita kamar yanda tai fata, tabar na Abdallah kawai tana faman kuka kashirɓan da zagin Nu'aymah da batasanma tanayiba.
Rayuwarsu ta saudia tana kadaran kadahan ne, baya shiga harkarta bakuma ya takura ma rayuwarta. Sai dai har yanzu ya hanata wayarta, idanma zata gaisa da Addah da Abbanta ko wani a ƴan gidan nasu saita wayarsa. Kuma yay tsaye a kanta har saita gama ya amshe abarsa. Hakanna bata haushi, amma sonsa da tsoronsa ya hanata ta nuna masa koda a fuska.
A haka suka kwashe watanni biyu a gidan. Shirye-shiyen makarantarta ya gama kammaluwa ta fara zuwa. Da farko bata shiga harkar kowa ta maida hankalinta a karatu kamar gaske. Tana wata na biyu da fara karatunta tai ƙawa mai suna Abida, sai da ana kiranta Maman Aaida, itama matar aurece harda yaranta biyu, asalin Mamana Aaida itama ƴar Nageriya ce, amma yanzu iyayenta na nan Saudia. Ta girma Adawiya da kusan shekara uku zuwa biyar, dan itakam zatai 22years. Maman Aaida irin matan nanne masu shegen iyayi dason gayu, ga Ƙwanƙwanin tsiya kamar jikar ƙaruna, kullum cikin bama Adawiya labarin mijinta take a zatonta Adawiya budurwa ce. Adawiya dataga iyayin Maman Aaida yayi yawa saita fito ta nuna mata itama ai tanada auren. Sosai Maman Aaida tayi mamakin hakan, danta tabbatar saita shirya zuwa gidan Adawiya a wani weekend. Babu wani ja'inja Adawiya ta bata address ɗinta. A kuwa ranar Alhamis saiga Maman Aaida har gida ita da maigidanta da yaransu biyu, da yake Abdallah na gida sai har mijinma ya shiga. Abdallah dai bai wani sake musu ba, bai kuma wulaƙantasuba aka gaisa da ƴar hira suka wuce, bayan tafiyar tasu kuma bai cema Adawiya komaiba akan zuwan nasu ba duk da yasan ya dace ace yayi hakan.
Sanadin haɗuwa da Maman Aaida fa idanun Adawiya ya ƙara buɗewa. Dan tunda Maman Aaida ta bigi cikinta taji yanda akai aurenta da Abdallah sai ta shiga ɗorata bisa wasu hanyoyi da zata ringa jan hankalin Abdallah, ciki harda abubuwan irinsu turaren jan hankali da sauransu. Tun Adawiya najin tsoron yin hakan harta fara hawa kan network da sha'awar fara gwadawa ko zata dace Abdallah ya manta da Nu'aymah.
A ranar farko da ta fara buɗe jikinta da turare Abdallah bai kwana gidanba, yamayi tafiya bata saniba. Da yake sai ya gadama take ganinsa sai bata fahimci baya nanba, washe gari ta wuce makaranta. Data dawoma bata gansaba bata kawo komai a ranta ba har dare, lokacin kwanciya ta sake shanana turare ta nufi ɗakinsa. Sai dai kuma wayam. saida ta leƙa har toilet sannan ta lurama ba'ai amfani da toilet ɗinba ma kwata-kwata. A take kuma sai tsoro ya kamata duk ta tsure, leƙe-leƙe ta shigayi cikin gidan kamar wata zararriya. Data ga dai lallai babushi a gidan saita fara kuka, ta koma ɗakinsa ta ƙulle ƙofa ta ƙudundune a bargo. Ta kusa awa guda a haka sannan ta fara jin motsin za'a buɗe ƙofa. Sake rikicewa tayi da kuka catake wanine ya shigi. Cike da mamaki Abdallah daya shigo yake sauraren kukan nata dan baiyi zaton ganinta a ɗakin nasa ba. Ƙarasawa yay gaban gadon ya yaye bargon. Tako dage zata kwarara masa ihu dan ruɗewa ya hanata nutsuwa taga wanene. Saurin hayewa gadon yayi ya rufe mata baki ruf da hannunsa yana kallon yanda jikinta ke rawa.
A take yanayin nata ya juye masa tamkar na Nu'aymah, dan duk lokacin da abu ya tsoratata haka zakaga jikinta na rawa duk ta fita hayyacinta, daga haka kuma saita suma. Yanda zuciyarsa ke ƙawata masa Nu'aymah sai tunaninsa ya gushe zuwa gareta harya rungume Adawiya batare daya fargaba. “K malama ki nutsu nine?”.
Sosai Adawiya ta sake maƙanƙale masa dan a rikice take sosai, amma taji daɗi da taji shine.
Tun Abdallah na shaƙar ƙamshin turaren data saka matsayin ƙamshi kawai harya fara canja masa yanayi. Hancinsa ya ɗaura bisa wuyanta yana shinshina da lumshe idanu, kafin a ɗauki tsahon lokaci jikinsa ya fara tsuma, sai ya sauya salon riƙon da yay mata. Anan nefa Adawiya ta dawo hankalinta da ƙyau. Da farko nishaɗin abinda yake matan ta farayi. Sai dafa taji al-amarin bawai wasan yara bane sannan ta fara kuka da roƙo da magiya. Da al-amari yay zurfi saiga hajiya malama mandiya ƴar ƙwalisar soyayya Adawiya na tsinema Maman da jamata ALLAH ya isa????????????.
Oho, Abdallah baisan tanayiba, morewarsa yakeyi dai-dai gwargwado, yama manta dawa yake tare. Iya wahala ya bama Adawiya batare da tausayawaba, kafin ya koma gefe ya barta ko numfashin kirki bata iya yi.
Tun daga wannan ranar Abdallah ya maida Adawiya abar hutawarsa. Daya samu biyan buƙatarsa kuma ya watsar da ita tamkar bai taɓa sanin daga inda ta fitoba. Sam ta gagara gane kansa balle inda ya dosa. Komai nasa yana yinsane da kulawa da lura. Abincinta dama kam bai taɓa ci ba, zai dai ajiye mata duk abinda ta buƙata ya kuma bata kuɗi. Amma babu wani farin ciki da kulawa kamar yanda Maman Aaida ke faɗa mata. Duk iya dabarun Maman Aaida cikin gwadasu take ga Abdallah amma saiya yi kamarma baisan tanayiba. ba shiga ɗakinta yakeba, ko abu zai bata sai dai yay knocking ta fito ta amsa. Idan yana buƙatar moranta ma zai mata knocking ne idan tana ɗaki yace ta samesa nasa ɗakin.
A haka rayuwar auren nasu ke tafiya tare da karatun Adawiya da ta fara saka shiririta saboda damuwarta kawai itace Abdallah ya sota a yanzu.
NAJERIYA
Rayuwa ta shuɗa, kwanaki nata gangarawa, inda ake neman watanni na takwas kenan da lalacewar auren Nu'aymah da Abdallah. Tana cikin tsananin damuwa da begensa, kullum dare sai tayi kuka, tana sonsa matuƙa, dan ta rayune da son nasa. Yawan damuwar da take a cikine ya haifar mata da yawan yin ciwo, saboda ciwonta bayason damuwa sam. A duk sanda ta takura kanta da tunani da damuwa yakan yawaita motsa mata akai akai, tana kuma matuƙar shan wahala.
Gaba ɗaya a awatannin nan lafiya taƙi wadatarta, haka taketa fama yau fari gobe tsumma. Gashi baba malam kullum cikin mata jan ido yake akan ta kawo Ameer yay musu aure. Tayi kuka tayi rantsuwar akan Ameer ba saurayinta bane amma sam yaƙi ya saurareta. Umm kanta wannan al'amari na tada mata hankali. Amma babu yanda ta iya ta zuba musu ido kawai taga iya gudun ruwan mijin nata.
Burin Nu'aymah cigaba da karatu a yanzun, amma Baba malam yay banza da maganar karatun nata, bayan kuma kowa a gidan yasan burinta a rayuwa shine ta zama likita ko Nurse tun tana yarinya. Addu'arta kullum itace Baba malam ya haƙura a sake nema mata makaranta kafin ALLAH ya dawo da hankalin Abdallahnta gareta, dan ita duk ɗaukarta Abdallah fushi yake da ita akan ta gudu ran aurensu, shiyyasa yaƙi nemanta koda a wayama. Ta dage da azumin litinin da alhamis da sallar dare tanata gayama UBANGIJI kukanta.
Ana cikin wannan yanayin su Baba malam suka gama shirya gagarumar walima na saukar Al-Qur'anin yaransu na gidan marayu, tare da aurar da waɗanda suka samu mazan aure. Wasunsu anan cikin gidan suka dai-daita kansu. Wasu kuma a waje suka samu mazajen aure da mata.
Shirye-shirye ake babu kaman hannun yaro, dan shinema ya ɗauki Baba malam Busy sosai ya samawa Nu'aymah lafiya daga takurar zancen fiddo mijin aure. Duk da dama dai yana matane kawai dan hukuntata ta cikin ruwan sanyi akan abinda ya faru. amma ta ƙarƙashin ƙasa neman hanyar ganin likitan nan kawai yakeyi da nema mata makaranta batare da ko Umm ta san da hakan ba.
Ana saura sati ɗaya su Yusrah suka iso, washe gari kuma su Amal. Hakan ba ƙaramin daɗi yayma Nu'aymah ba, koba komai ta rage kaɗaicin da ta tsinci kanta a cikin a waɗannan watanin ai. Abinda ya ƙara faɗaɗa farin cikin natama shine Amal da Yusrah bazasu komaba, dan zasu zaunan zana jarabawar ssce anan. Cikin kwana biyu kacal da dawowar tasu ta fara komawa cikin walwalarta.
Tuni suka fara addabar gidan da ƙiriniyarsu da bata ƙarewa, sauƙinma babu Adawiya, amma hakan baisa sun fasa abinda suka saba yiba. tun ana saura kwana uku suka saka Hajjo ta roƙa musu baba malam komawa cikin gidan marayu har sai an kammala komai. Dan yawancin ƴammatan da za'aima auren duk ƙawayensu ne, duk da dai a shekaru gaskiya zasu girmesu da kusan shekara bibbiyu ko ɗai-ɗai.
Bai hanasu ba, dan gidan marayun nan nada matuƙar muhimmanci a garesa dama family ɗin gaba ɗaya. Yanda suke ƙoƙarin dagewa akan tarbiya da karatun yaransu haka suke dagema yaran gidan marayun nan suma. Shiyasa suma yaran suna tsananin ƙaunar wannan family, su suke ɗauka danginsu da komai a rayuwa.
★★★★★
“Wai wannan akwatin da kika lodama kaya duk na miye Nu'aymah?”. Umm data shigo ɗakin Nu'aymah ta faɗa tanabin Nu'aymahr daketa shirin kaya da kallo.
Ɗagowa tai ta kalli Umm cike da ɗoki, “Umm yo na bikine mana, sati guda zamuyi a can”. “To lallai, ashema kune iyayen bikin kenan?”. Dariya Nu'aymah tayi dajin zancen Umm, Umm kam daga haka bata sake cewa komaiba ta ajiye mata magungunan ta tana faɗin, “Gasu nan, saura kije kita wasa da shansu Nu'aymah, dan ALLAH ki kula da kanki, duk abinda kikasan zai zame miki matsala ki kujesa, ku kuma riƙe mutuncin kanku, na kira Baba Habi a sashenta zaku zauna kafin Hajjo ta iso gobe idan ALLAH ya kaimu, saura naji wani abu mara ƙyau na shegen tsiwanki, ALLAH saina ɓata miki rai”.
“Umm insha ALLAH bazakiji komaiba ma”. “ALLAH yasa”. Umm ta faɗa tana juyawa ta fice daga ɗakin..
Bayan sallar azhar su Nu'aymah sukai sallama da kowa suka wuce, Yah Abubakar ne ya kaisu. Da yake shima irinsu ne ɗan taraliya saida ya kaisu sukai shopping sannan ya wuce dasu gidan marayun.
Ƙaton gaske ne, sannan an ƙawatashi ta ko ina babu makusa. Akwai makaranta da asibiti da duk ma abinda masu rayuwa da iyayensu suke samu. Makarantarsu ta fara tun daga noziri har zuwa sakandire. Ana koyar da boko da arabic, idan kaji yanda yaran ke larabci da turanci sai kasha mamaki da al'ajabi. Rayuwarsu suke cike da farin ciki da jin daɗi wadda ko wasu masu iyayenma basa samu. Gasu da tarbiyya abin birgewa.
Ɓata lokacine zama bayyana muku yanda gidan marayun nan ya ginu da tsari mai ƙyau, kusa a ranku kawai ya haɗu. Dan sosai su baba malam ke samu taimakon manyan mutane dama masu mulki game da riƙe gidan. Ga kuma suma kansu masu nemane basu zauna jiran na sadakaba. Kaso mafi yawa na ɗunbin dukiyarsu yana tafiyane wajen tattalin rayuwar marayun nan da kulawa da su. Shiyyasa Alhmdllh da wahala ace sun nema abu sun rasa. Sai dai ace yau da gobe sai ALLAH, komai arziƙinka dama wani abun sai ya gagareka.
A yanda su Nu'aymah suka sami tarba zai tabbatar maka da sanannune a gidan, kuma ba wannanne farkon zuwansu su kwanaba. Dan rigima aka shigayi musamman ga sa'anninsu, kowa na faɗin sashinsu su Nu'ayma zasu sauka. Bayan ansha taƙaddama dai kowa ya haƙura zasu zauna a sashen da amare suke, wato sashen baba habi da Umm ta faɗama Nu'aymah tun a gida.
A yau kowa ya kalli Nu'aymah yasan tana cikin farin ciki sosai, haƙoranta sun kasa rufuwa. Tsiyarsu sukaita tsulawa uwa ba kwaɓa uba babu tsanani, dan suna son suga sunzo gidan nan, shiyyasa wani lokacin baba malam da kansa yake cewa suzo suyi weekend ɗinsu anan, dama anan duk yaran gidansu ke karatunsu tun daga noziri har zuwa sakandire, shiyyasa sukeda shaƙuwa sosai da yaran gidan marayun fiye da zaton mai tunani.
Washe gari Nanah tace suma gasunan zuwa ita dasu Suhailat, hakan yasa bayan sallar la'asar ana tsaka da musu ƙunshi dan ranar itace suka saka ranar ƙunshin, Nanah ta kira wayar Yusrah ta sanar musu gasu a bakin titi suzo su shiga dasu dan baza'a barsu su shigaba kai tsaye.
Nu'aymah da Yusrah da biyu cikin ƴammatan gidan suka fita shigowa da su Nanah dansu ƙunshinsu harya bushe sun wanke, Nu'aymah ce kawai bata wanke nata ba amma ya bushe. da ƴar tafiya tsakanin gate da gidajen yaran, amma haka suka taka a ƙasa suna hira har suka iso. suna a gab da fitane suka haɗu da yaran gidan maza da bazasu gaza shekaru sha biyu ba kusan su bakwai wai wajen ball suka tilla ƙwallon waje ta katanga shine zasu zagaya ɗakkowa. Security ɗaya ne tare dasu zai rakasu. A tare suka fita dasu Nu'aymah da zasuje tarbar su Nanah.
Gidan marayun yana akan babban titine, shiyyasa sam ba'a barin yaran fitowa ko ina su kaɗai koda hakan ta kama sai da security.
Dariya Nu'aymah tai ganin su Nanah acan ɗayan tsallaken basu tsallakoba, tasan Nanah matsoraciyace akan tsallaka titi dama, shiyyasa yanzuma abun ya bata dariya data tuna. Su Yusrah ma dariya suka sanya famhimtar dariyar Nu'aymah da sukayi. Bayan sun kalla ɓangare biyu na titin babu mota suka sa kai zasu tsallaka. Da sauri security ɗin daya rako yaran nan yasa hannu ya fisgo Nu'aymah dake ƙarshen tafiya saboda tahowar wasu motoci guda uku a jere cikin masifaffen gudu.
Ta juya zataima security ɗin masifar taɓatan da yayi dukda tasan hakan na halinsu bane sukaji razananniyar ƙarar ɗaya daga cikin yaran wanda motar farko ta kwashesa yana ƙoƙarin ɗakko gyalen Nu'aymah daya zame ya faɗi lokacin da security ɗin nan ke ƙoƙarin maidota baya.
“Ƙuuuuuwww!!!” motocin suka bada sautin taka birki a tare, yayinda mai napep dake bayansu ya bugi motar ƙarshe shima.
A tare su Nu'aymah suka fasa ƙara da rumtse idanu kunnuwansu a toshe da hannayensu, sai da sukaji tsitt sannan suka bubbuɗe ido dan son ganin yaya akayi.
“Innalillahi.... Suka shiga ambata kusan a tare saboda hango yaron a kwance ƙasa cikin jini. Sunma manta a titi suke, suka tafi da gudu kansa suka rufu masa. Sunkai mintuna uku akan yaron nan suna kuka da jujjuyashi amma ko mutum ɗaya bai fito daga motocin nan uku ba balle kai tunanin sunsan ma abinda suka aikata. Cikin tsananin fushi da zafin zuciyar gado Nu'aymah ta rarumi wani dutse dake a gefen titin ta nufi motar tsakkiya dake a saitinta, wadda kuma tafi kowacce haɗuwa da ƙyau ta buga dutsen jikin glass ɗin.
Ko gezau glass ɗin baiyiba, dan haka ta koma na gaba wanda tasan insha ALLAH zata dace ta sake bugawa da iya ƙarfinta. Aiko a take ya shiga tsatstsagewa. Ta sake ɗagawa zata buga aka riƙe mata hannu. Fisge hannun nata tai ƙoƙarin yi ta kasa, dan haka ta juyo bakinta cike da tsiwa.
Ido huɗu tayi da manyan garada masu suffar ƴan dambe cikin baƙaƙen suit da glasess zagaye da ita su shidda, daka gansu kaga cikakkun marasa imani dan babu alamar sunsan ma minene dariya a rayuwarsu, babu tantama kuma zasu iya halaka mutum batare da sunji koda ɗar ba.
A mamakinsu sai gani sukai ta ɗaga dutsen ta bugama wanda ya riƙe mata hannu a goshi. Saurin sakinta yay ya dafe goshinsa daya fashe a take ya fara zubda jini.
Kusan a tare suka fiddo bindigu suka nunata da shi. Duk da Nu'aymah tasan zasu iya harbin nata ta mutu kuma, amma sam cikin idanunta babu tsoronsu, saima masifa dake cinta. Haka take ita sam batasan tsoroba. Idan kaga tsoro ga Nu'aymah to duhu ne ko tsawa, ko allura.
Ɗasss! Ɗasssss!! Ɗassssss!!!
Sukaji sautin buga yatsu a bayansu. Gani tai duk sunja baya daga kusa da ita amma basu sauke bindugunba, sundai risinar da kawunansu ƙasa na alamar girmamawa ga koma wanene mai buga yatsun.
Kamar bazata juyaba sai zuciyarta ta bata shawarar juyawa taga wane shahararran ƙwallan mara imanine da mutuncine shiɗin………..✍
Nidai nama rufe idona bazan gansa ɗinba????????????.
Yau dai ga dogon page nan ku more harda na jiya na haɗa muku. Saura kuma naji wata tace bai isheta ba????????????????????????????????????
ZAFAFA BIYAR 2021
Hafsat miss xoxo????
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).????????
Mamu gee????
MIN ƘALB!!????????
Hafsat rano????
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!????????
Safiyya huguma???? SIRAƊIN RAYUWA????????
Bilyn Abdull????
SARAN ƁOYE????????
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka????????????????
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????
09033181070
????????????????????????????????????????
TEAM—-ZAFAFA BIYAR????????????????
ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????.
Typing????
No. 12
ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE
*_KAJI shahararrun kuma mandiyoyin ƴan ƙwalisar kawo kayan kitchen masu tafiya dai-dai da zamani. Idan nace nadaban ina nufin suɗin nadabanne wajen kaya ƴan gaske dake ƙawata kitchen ɗin amarya harma dana uwargida ƴar ƙwalisa. Ka siya ka tabbatar ka saya ɗin ko a gaban tsaranka sai ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE. sunan kayansu sa kishiya cin bashi????, dan tana ƙyalla ido taga kitchen ɗinki tsarin amerikawa tuni zata fara ƙwafa da tunanin zuwa gidan delu dillaliliya mai saida kwanika. Sai dai kuma kama da wane akace bata wane, dan haka ku maza ku garzaya ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE. domin samun naku kuma. Suna kawo kaya daga ƙasashen ƙetare akan farashi mai sauƙi da rahusa. Suna order ɗin products kamarsu, dukan kayan kitchen na zamani, bedsheets, shoes dade sauransu, products ɗinsu pre-order ne dake zuwa akan lokaci batare da mai kaya ya ƙosa da jira ba ko samun matsala. Zaku iya samunsu a Number waya kamar haka ko Location nasu. Phone number: 08102393622. Location Gombe. Amma Zasu iya turawa kowani gari dake a lungu da saƙo na ƙasarnan. Sayen nagari maida kuɗi gida. Ku garzaya kar ayi babu ku. Da ƙyar nasha yafi da ƙyar aka kamani inji masu iya magana????????????????????._*
…………….Sai da ya kammala ƙalular shirinsa cikin kayan barci wando 3quarter da riga Armless sannan ya zura slippers masu taushi ya fita. Kusan su shidda ya iske a falon kowa da hidimar da yakeyi. Wasu kallo wasu danna waya wasu surutu.
Da sauri Miracle ta ɗauki remote ta rage ƙarar television ɗin dan tasan ya tsani hakan. Shikam baimabi takan kowaba ya nufi d/table. Kafin ya ƙarasa Miracle ta rigashi isa, yana ɗaura hannunsa saman kujera zai jata baya ta ɗora nata akan nashi. A take fuskarsa ta sake tsukewa, ya ɗago fararen idanunsa ya zuba mata wani banzan kallo. Maimakon ta janye hannun saita kashe masa ido ɗaya tana murzawa a hankali. Kallon hannun yayi cike da tsantsar fushi. Duk da tsoronsa dana yanayinsa a yanzu ke ratsata bata fasaba, saima karta zaƙo-zaƙon faratan ta ta farayi tana matsawa da hannunta gaba akan nashin cike da salon iskanci.
Ita da kujerar ya haɗa ya wancakalar gefe, kafin takai ƙasa ya bita da halbi, sai gata ƙasa wanwar. Ƙarar data firgita kowa a gidan ta ƙwalla tana faman ihu kamar wadda aka yanka. Dukansu kanta sukayo, yayinda Yoohan ya sake ɗaga hannu zai ƙwaɗa mata mari Gebrail ƙaninsa yay saurin riƙesa, fisgewa yay yayi ƙwallo da kujerar kusa da shi ta dining ɗin ya juya fuuu kamar wani kumurci ya nufi sama. Da sauri Mom data fito daga wani ƙofa yanzu saboda jiyo ihun Mira ta shiga ƙwala masa kira da turanci. “Yoohan! Yoohan!! Yi hakuri zo kaci abinci”.
Baiko waiwayeba balle tai tunanin samun amsa. Da gudu ta bisa tana haɗa steps ɗin da bibbiyu. Kafin ta ƙarasa har ya tura ƙofar ya maida ya rufe. Bugawa Mom ta shigayi tana kiransa cike da lallashi “Yoohan! yi haƙuri kaji, kar kayi fushi zo kaci abinci Please”. Duk da yaransu take maganar, amma yaƙi buɗe mata. Shi tunima yabar jikin ƙofar harya shige bedroom ɗinsa.
Zuciyarsa cike da matsanancin ƙunci ya faɗa saman gadonsa ya kwanta a rufda ciki. Ji yake gaba ɗaya duniyar ta masa masifar ɗaci, yaja filo ya danne kansa da shi da ƙarfi.