SARAN BOYE COMPLETE

A falo kam Mom data sakko a ranta a ƙuntace ta ƙarasa inda Mira ke faman kuka har yanzu, cikin faɗa tace, “Miracle bance ki fita hanyar Yoohan bane? Kin riga da kinsan halinsa baya son wannan banzan halayar amma ke kam bazaki kama kankiba. Ki cigaba, wataran idan ya karyaki ko ya miki mugun dukan da za'a gaza ganeki zaki kiyayesa ai”. Batare da ta saurari amsa daga Mira ba ta wuce ɗakinta cikin fushi itama, dan a rayuwarta ta mugun tsanar ganin an ɓatama Yoohan rai a gidan. Tana masifar son yaronta fiye da sauran ƴaƴanta.
Kuka Mira ta sake ɓarkewa da shi iya ƙarfinta su Joy na lallashinta, da ƙyar suka iya ɗagata dan tanada jiki sosai bawai siririya bace, sannan a shekaru sai dai suyi sa'anni ma da Gebrail ƙanin Yoohan ɗin.
Da taimakon su Joy Miracle taje ɗakinta, sai da suka kwantar da ita a gado Gebrail ya kalleta shima cike da takaicinta. “Mira idan baki fita hanyar Brother ba na tabbatar shine zai maidaki gurguwa kafin ki koma gidanku, nasha faɗa miki shifa a rayuwarsa yanda ya tsani shan giya haka ya tsani harka da mata. Wanda yay kashi biyu cikin ukun rayuwarsa a turai matan can basu sakashi ya iskance ba ta yaya kike tunanin ke ƙaramar ƙwaruwar Najeriya zata iya sakashi aikatawa? Ƙilama dakin kama kankine zai soki kamar yanda kikai fata, amma a haka ina tabbatar miki tsanarki yake ƙarayi dan baya ɗaukar lamarin ta fuskar soyayya, idan kinji shawarata sai ki kiyaye”. Yana gama faɗa ya juya yay ficewarsa, kafin duk suma sauran su fito a barta daga ita sai Joy da take kusan sa'arta itama. Dan twins ne ita da Gebrail ɗin. Hawayenta ta share tana danna ƙafarta data buge, da yarensu tace, “Joy wai miyasa Brother ɗinku bashi da kirki?, gashi duk iskancin da wulaƙancin da yakema mutane su Mom sai sudinga goya masa baya basa son ɓacin ransa, kamar sunajin tsoronsa ma......” da sauri Joy ta rufema Miracle baki da hannu tana girgiza mata kai, sai da ta tabbatar tayi shiru kafin ta saketa, ƙofa ta nufa da sauri ta leƙa, ganin babu kowa saita maida ta rufe sannan ta dawo wajen Miracle ɗin. Daf da ita ta zauna cikin magana raɗa-raɗa tace, “Ni kaina na daɗe inason yin maganarnan da Wani Mira, kinga dai su Mom duk su suka haifemu, amma idan kika lura sunfi son Brother Yoohan, ko yaya suka gansa a damuwa sai kiga sun rikice, sannan duk abinda yakeso shi ake masa. Kiga dai yanda kike sonsa yana wulaƙantaki a gidan nan amma basu taɓa nuna masa rashin dai-dai akan hakan ba. Kowafa tsoronsa yakeji anan gidan har Mom ɗin”. Mira dake sauraren Joy kamar mai ɗaukar karatu tace, “Yayi kuɗi ne shiyyasa ai”. Kai Joy ta girgiza mata da faɗin, “Sam ba haka bane Mira, ki tuna tuntuni suke masa wannan gatan na fitar hankali, makaranta saida ya zaɓa ya darje mai mugun tsada a ƙasar waje, har sai da ya cika burinsa na zama babban likitan da yakema duniya aiki bama Najeriya kaɗaiba, amma kina gani ni da Gebrail a 9ja muka fara karatunmu, sai yanzune da shi yace zai fita damu sannanfa suka yarda”. “Hakane Joy. to ammafa kinsan Yoohan yanada bala'in ƙwaƙwalwa, dan sister Divine tace min sanda suna primary yafi kowa hazaƙa da ƙoƙari a ajinsu, yanzu za'a karanta masa yanzu zai ɗaukesa a kai. Ni yanda ya tsaya yay karatun ya birgeni, dan masu irin shegen kaifin ƙwaƙwalwar nan tasa basu da yawa a cikin mutane, zakiga kuma mafi yawansu sunfi yarda su zama mugaye fiye da mutanen kirki, balleshi daya tashi ɗan gata ma. Amma kigafa shi a ma tsarinsa baya shan komai har giya da ba komaiba, baya neman mata, abinda kawai ya sani a rayuwarsa shine aikinsa da Family ɗinsa. Gaskiya ina masifar son gayen nan Joy, komai nashi yana birgeni”.
Dariya Joy tayi sosai, ta wani juya idanunta cike da yanga, “Ai bake kaɗaiba Mira, koni da yake Brother ɗina sonsa nakeyi, haka ƴammata da yawa suke haukacewa a kansa, shiko babu wacca ta ishesa koda kallo ma, Mom tace tunda suke da shi bai taɓa ce musu ga budurwarsa ba. Ke nifa da ƙanwa zata iya auren yayanta da Brother Yoohan zan aura fa”. Baki Mira ta taɓe cike da kishi ta ɗauke kanta batare data bama Joy amsaba.
Joy data fahimci kishi Mira keyi saita kwashe da dariya ta miƙe, amma ita tasan har cikin ranta son Brother ɗinta take da gaske. Kuma harga ALLAH tana kishin ganinsa da wata mace har Mira ɗin, dan yau sosai taji daɗin mazgar da yayma Miracle.
????Joy kedai muguwace to.
ZAFAFA BIYAR 2021
Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka karanta idan baka biyaba, karka kuma yaɗa dan ALLAH idan ka gani????????????.
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????
09033181070
A tsarin gidan dolene duk safiyar duniya ka fito babban falo inda suke taruwa su duka har ma'aikatan gidan suyi addu'oinsu. Yoohan ne dama sai ya gadama randa ta raya masa yake fitowa idan har ya kwana a gida, dan yafi ganema yayi tasa a ɗaki shi kaɗai baisan hayaniya, garama idan Papa ya takura masa.
Yauma kamar kullum duk sun hallara, har ƙananan yaran duk an tasosu, Papa da yay tafiya ne kawai babu sai Yoohan da kowa yasan yau bazai fitoba tunda jiya da haushin Miracle ya kwanta. Amma duk da haka sai da Mom taje ta buga masa ƙofa.
Yana jinta sarai, dan tashinsa kenan yana zaune a kan gadonsa ido a rufe yana addu'ar shima. amma yay mata banza, sai da ta gaji dan kanta ta haƙura. Sauka yay a gadon fuskar nan kamar kullum a cinkushe, amma hakan bai hana ƙyawunsa da ALLAH ya azurtasa dashi bayyana ba (damma babu hasken bautar UBANGIJI a cikinsa Yoohan daya zarce hakan ga mai kallo????).
Slippers ya zura ya nufi toilet, ya kusa mintuna goma a ciki sannan ya fito, da alama dai ba wanka yayi ba, dan kayansane a jikinsa bai canja ba. Ficewa yay daga ɗakin gaba ɗaya ya fito falonsa, a mamakina sai naga ya ɗaga labulen bangon gabas, sai ga ƙofa a wajen ƙatuwa ta glass. Danna wani abu yay a bangon ta zuge da kanta ya shiga. Ƙaton ɗakine da aka cika da kayan motsa jiki kala-kala. Gaba ɗayansa kuma da glass aka yisa, ta ciki kana iya hango harabar gidan dama cikin anguwar gaba ɗayanta. Zama yay ya ɗaura takalma a ƙafarsa batare daya canja kaya ba ya fara motsa jiki a style kala-kala. Yana a kusan mintuna hamsin da farawa amintaccen yaronsa da Nu'aymah ta fasama kai jiya ya shigo ta wata ƙofa ba wadda shi ya shigoba. Madaidaicin tiren hannunsa ya ajiye kan wani table dake can gefe gaban kurera doguwa guda ɗaya kacal dake a ɗakin, sannan ya dawo inda Yoohan ke cigaba da ɗaga ƙarfe yace, “Good Morning sir”. Sai da ya furzar da zufan dake sakko masa har kan laɓɓa sannan yace, “Morning” a taƙaice.
Ajiye ƙarfen yay ya miƙe ya sake komawa kan wani machine ɗin, sai da ya fara batare daya kallesa ba yace, “Solo! Aikin dana saka ka fa?”. Kan Solo a ƙasa yace, “Sir komai ya kammala, yanzu haka ma nasan sun kama hanyar tafiya dan tunda daddaren na sanar masa, ya kuma tabbatar min za'a haɗa komai tun a daren, a yau su tafi kaiwa”.
“Good” ya faɗa a taƙaice yana kallon agogon dake manne a bango ƙato. Lumshe idanunsa yay ya buɗe yanata faman fidda numfashi da sauri-sauri. Sajensa kansa ɗigar da zufa yakeyi balle murɗaɗɗen jikinsa dake sharkaf tamkar wanda yayi wanka. Sauka yay daga saman machine ɗin ya amshi ƙaramin towel dake a hannun Solomon ya fara goge fuskarsa zuwa wuya.
Da sauri Solo ya ɗakko tiren daya shigo dashi shima. Iska Yoohan ya furzar kafin ya ɗauka babban kofin glass dake cike da tatattun kayan marmari da babu koda suga a ciki akan tiren dake hannun Solomon. Barin wajen yay da kai kofin bakinsa yana sha, ya ƙarasa kujerar nan ƙwara ɗaya ya zauna da ɗaura ƙafa ɗaya a kan ɗaya ya ɗauka remote ya kunna television dan akwai program ɗin da yake kallo a NTA kullum safiya a irin wannan lokacin a duk inda yake, inhar kaga bai kalli wannan shirinba to sai dai inda yake babu wutar nefa kuwa.
Dawowa Solo yay gefensa ya tsaya suna kallo a tare, yana shan lemonsa suna magana jefi-jefi akan tafiyar da zasuyi yau har aka kammala shirin, dan minti ashirin ne dama. Ajiye kofin yayi ya miƙe bayan ya cire takalman yabar Solomon na gyara ɗakin da maida kowane abu inda yake.
Kusan 9am ya fito daga ɗakinsa cikin gayunsa dake rikita ƴammata, sai baza ƙamshi yake kamar wani gonar turare. Sai dai tamkar kullum fuskar dai babu fara'a. Sajen nan da gashin sunsha uban gyara na ɗaukar hankali kamar dansu kawai aka yosa duniyar.
Tunda ƙarar takunsa ta fara bayyana garesu falon yayi tsitt, kowa ya zubama hanyar benen idanu duk da sunsa wanene ɗin mai tahowar kuwa.
Kallo ɗaya yay musu ya ɗauke kansa yana sake tamke fuska musamman da yaga Miracle zaune. Mom ce cike da farin cikin ganinsa ta miƙe tsaye tana buɗe masa hannayenta alamar yazo. Fuskarsa ya ɗan saki amma ba murmushi ba, ya nufeta ya ɗan rungumeta a gefe saɓanin ita da ba haka take buƙatar yi masaba, ta fison ta jisa sosai a jikinta, sai shi kuma sam baiso. yace, “Good morning Mom”. “Good Morning my boy, ka tashi lafiya?”. Kansa kawai ya gyaɗa mata. Tai murmushin jin daɗi tana kama hannunsa cikin nata.
“Good morning Brother”. Suka haɗa baki wajen faɗa yaran suma, amma banda Mira data haɗe rai wai ita a dole fushi take da shi. Kallonsu yay sosai da fararen idanunsa ɗaya bayan ɗaya kafin ya amsa musu da muryarsa mai amo. Ya ɗaura da tambayar lafiyarsu kamar yanda ya saba cike da kulawa da sonsu. Dukansu fuska a washe suke amsa masa, dan sunsan yana ƙaunarsu. Idan dai baƙin halinne ya motsa ba sani ba sabo yakema kowa a gidan.
A tare suka ƙarasa d/table shi da Madan Chioma, ta zaunar dashi da kanta ta shiga zuba masa abincin da tasa akai masa na musamman. “Thanks” ya faɗa a saman laɓɓa ya ɗauka cokali ya fara ci. dai-dai misali yaci, dan badan ma tafiya da zaiyiba bazai karyaba a irin wannan lokacin. Dan shi mutum ne mai ƙa'ida da tsari. Komai nasa a tsare yake tamkar wani bature???? (mudai munsan ALLAH shike tsara rayuwa ba mutum ba????).
Cikin damuwa Mom daketa kallonsa tace, “Badai ka ƙoshi ba?”. Idanunsa ya ɗan lumshe mata alamar amsawa. Tai saurin kamo hannunsa tana girgiza masa kanta. “Jiyafa bakaci abinciba ka kwanta, shine yanzu kuma......” “Shiiii!!” ya faɗa yana ɗora ɗan yatsansa akan bakinta, “Mom ya isheni haka”. Badan tasoba ta barsa. Yasa tissue ya goge bakinsa sannan ya miƙe, “Mom zan wuce Lagos, zata iya yuwuwa daga can bazan dawo nanba zanje ƙasar Kenya. Cike da damuwa take kallonsa, har yanzu ta kasa sabawa da waɗannan tafiye-tafiyen nasa, dan ko kaɗan batason yay nesa da ita, a koda yaushe tafison taita ganinsa tare da su.
Kansa yaɗan girgiza dan yasan miyasa jikinta yay sanyi. Ya kama hannunta da yasha farce zaƙo-zaƙo, murya a tausashe yace, “Mom kimin addu'a mana, baƙyaso na cigaba da taimakon mutane ina samun lada?”. Da sauri tai murmushi, “Inaso sosai Yoohan, sai dai aikin nan ya maka yawa, gaba ɗaya baka da wani lokacin kanka kai saina wasu. ALLAH yasa kaje lafiya ka dawo lafiya”.
“Amin” ya faɗa da yin kissing hannun nata.
Gaba ɗayansa suka fito domin masa rakkiya har wajen da motar da zai shiga take, cikin girmamawa guards ɗinsa da securitys gidan suka iso ɗaya bayan ɗaya suna gaishesa. Kamar yanda ya saba musu alkairi idan zai yi tafiyar kwanaki haka yauma duk ya bisu da shi ta hanyar Solomon dake da kusan ci dashi fiye da kowa, dan duk inda zaije tare suke tafiya, sannan komai nasa shi yake sakawa. Dan haka yasan sirrinsa sosai da halayensa fiyema dasu iyayensa. A tare suka shiga masa addu'ar fatan alkairi, ƙannensa kowa na masa shagwaɓar zaiyi missing ɗinsa. Babu dai dariya a fuskarsa, amma duk yana binsu da kallon kulawa. Kafin ya bisu ɗai-ɗai yay kissing nasu a kumatu, banda Miracle dako kallon inda take bayayi. Gebrail ya buɗe masa mota ya shiga, shima ya zagaya ta ɗayan gefensa ya shiga dan zai masa rakkiya airport ne.
Ɗaga fararen idanunsa yay ya kalli Mom da duk fuskarsa tai kalan damuwa. Yatsunsa biyu yasa a gefen bakinsa yay mata alamar *_Smile_*. Murmushin kuwa ta saki har haƙoranta na bayyana kafin ta ɗaga masa hannu. Shima yatsunsa biyu ya ɗaga mata daɗan motsa laɓɓansa kaɗan yay maganar da shi kaɗai yaji kayarsa. (Dan nidai banjiba????????).
Ganin motocin sun fice Madam Chioma ta sauke ajiyar zuya, yayinda Miracle ta share hawaye masu zafi da suka gangaro mata batare data shirya hakanba.
Juyawa sukai suka koma ciki, dama yaran sun wuce school su tun ɗazun.
NU’AYMAH
Tunda garin ALLAH ya waye kaikawonsu suketayi na hidimar walima a cikin gidan marayun. Da safe kusan goma Hajjo ta iso tare dasu Hajarah. Su Umm kuma sai zuwa anjima.
A babban harabar farkon shigowa cikin gidan marayun aka kafa manyan rumfuna tare da kujeru masu yawan gaske. Sai babban munbari da malamai zasu gabatar da lectures insha ALLAH.
Nu'aymah harkokin gabanta take kawai, tama manta da wani faɗa da tayi da wasu jiya. Haka take, akwai saurin fushi da tsiwa akwai kuma saurin sauka da mantuwa. Itadai wuyarta ace ta rama kota maida murtani, daga haka kuma ta manta sai wata ta taso.
Wajen misalin sha biyu saura ta kammala shirinta cikin baƙar jallabiya datasha adon manyan jajayen duwatsu masu ɗaukar ido. Itace shigar da gaba ɗaya ƙawayen amare zasuyi a wajen walimar. Tayi ƙyau sosai, ta sake gyara gashinta da saida akasha dagama kafin ta yarda aka tsefe aka wanke mata shi. Tanada gashi gwargwado dan yana sauka mata har kan kafaɗa, amma ta tsani kitso, gashi ta zama budurwa amma batabar kukan kitso ba har yanzu. Tsifar kai ma kuka take masa da wankewa balle kuma kitso.
Jan veil ɗinta madaidaici ta naɗa, kalar saita sake bayyana ainahin hasken fatarta da kwarjininta da ƙuruciya. Ga jambakin data saka kaɗan a laɓɓa ya sake ƙawata madaidaiciyar kwalliyar tata. Sauri take taje kiran da baba malam ya aiko ai musu yanzun nan tana wanka. Tasa turare kaɗan ta fito da ɗan hanzarinta.
Tare suka tafi ita da Amal da Yusrah, dan su ukun ya aiko kira. Suma sunsha ƙyau cikin kalar rigar da Nu'aymah tasa iri ɗaya komai da komai. Akwai tazara tsakanin office ɗin baba malam zuwa sashen gidajen yaran, amma haka suka taka cikin nutsuwarsu suna ƴar hira har suka isa. Sai da aka nemar musu iso sannan suka shiga.
Baba malam ya ɗan kallesu ya ɗauke kansa, a ransa yanajin daɗi da godema UBANGIJI daya azurtasu da kamilan yara da yayi. Basu izinin zama yay kafin su gaidashi. Ya amsa musu kamar yanda ya saba. Sannan ya lissafa musu aikin da zasuyi a wajen walimar. Sai dai ba komai ya saka Yusrah a cikiba kasancewar tanada aure ita.
Suna shirin miƙewa zasu fita security yay knocking ƙofar office ɗin dayin sallama. Amsa masa sukayi, baba malam ya bashi iznin shigowa. Cike da girmamawa yace, “ALLAH gafarta malam saƙone wani bawan ALLAH ya aiko dashi”. Baba malam dake saurarensa yace, “To aike kuma Rufa'i. Nami kenan?”.
“Kayan abincine dai mota guda gasu can a waje”. Baba malam bai sake cewa komaiba ya miƙe. Shi ya fara fitowa sannan su Nu'aymah a bayansa.
Mota ce ta kamfani, dan haka baba malam ya ƙarasa suka gaisa da drivern cikin mutuntawa. “Malam ko zan iya sanin saƙo daga ina haka?”. Baba malam ya faɗa cikin fara'a da mutuntawa. Murmushi drivern yayi, shima cike da girmamawar yace, “Ranka ya daɗe wlhy nima bansan daga wa kayan sukeba, amma dai wani bawan ALLAH ne ya saya a kamfaninmu ya kuma bada wannan address ɗin a kawo tare da wannan”. Ya ƙare maganar da miƙa masa leda madaidaiciyar ruwan ƙasa.
Sai da baba malam yay ɗan jimm kafin ya amsa, dan su gidan marayunsu nada tsari, ba komai suke amsa kai tsayeba babu bincike saboda gudun abinda zaije ya dawo. “Idan bazaka damuba ko zaka bani Number ɗin Manager ɗinku?”. “A babu damuwa ranka ya daɗe, dan dama shima yace na baka idan nazo”. “To Alhmdllh”.
Wucewa sukai tare office ɗin baba malam ɗin, inda suka bar su Nu'aymah nan tsaye suna kallon kayan cike da jin daɗi da jan addu'ar alkairi ga wanda ya aiko ɗin. Suna a wajen tsaye baba malam da drivern nan suka sake figowa, a yanda sukaga fuskar baba malam ɗin yanzun sunsan ya amshi kayan shima. Umarni ya bama security ɗin nan akan a raka drivern har jikin store ɗin Orphanage ɗin a sauke kayan................✍
ZAFAFA BIYAR 2021
Hafsat miss xoxo????
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).????????
Mamu gee????
MIN ƘALB!!????????
Hafsat rano????
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!????????
Safiyya huguma???? SIRAƊIN RAYUWA????????
Bilyn Abdull????
SARAN ƁOYE????????
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka????????????????
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????
09033181070
????????????????????????????????????????
TEAM—-ZAFAFA BIYAR????????????????
ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????.
ANNUR PERFUMES: GIDAN KAMSHI KENAN.! WANI KAYA SAI AMALE! HAKAN TAKE, INA MASU NEMAN INDA ZASU SAMU INGATATTUN KAYAN TURARE NA GIDA DANA JIKI DANA KAYA NA MAIDUGURI? KU MATSO KUJI! NESA TAZO KUSA, ANNUR PERFUMES. KAMFANIN TURAREN MAIDUGURI NE DA RESHEN SA KENAN JIHAR KANO. MUNA DA KOWANE IRIN SAMFURIN KAYAN KAMSHI KAMAR SU; TURAREN WUTA NA KAYA DANA JIKI DANA TSUGUNNO, MUNA DA KHUMRAH, KULACCAM GANGARIYA DA ALMISKI(THAHARA/AYSHA/BAKI DA JA) MUNA DA DECORATIONS NA TSINTSIYA DA SAURAN SU, AKWAI KAYAN MATA INGATATTU MAI SA KISHIYA KWAFA, BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA, MUNADA KAYAN MATSI YAN GASKE, NAMU BA IRIN NASU BANE.
DUKA WADANNAN JERIN TURARUKA MUNA BADA SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYI ‘DAI DAI. ADIRESHEN MU; MUNA KANO, UNGUWAR GAIDA, LAYIN MASALLACIN IMAMU MALIK. LAMBOBIN TARHON MU: 07086341096/07069036534. MUNA AIKA KAYAN MU KO’INA A FADIN NAJERIYA, KAMSHI RAHAMA NE YAN’UWA, MUSANMAN KAMSHIN ANNUR PERFUMES DAKE SANYA NUTSUWA DA KWANCIYAR HANKALI. GA ARHA GA LAGWADAR KAMSHI SAI ANNUR PERFUMES
13
……………..An gudanar da gagarumar walimar aure da saukar alkur’anin marayun ALLAH da waɗanda son zuciya ta saka iyayen nasu ajiyesu saboda gudun abin kunya. Sai kuma UBANGIJI mai rahama yay musu gata ta hanyar waɗanda basusanma sanda kikaje kika aikata ɓarnanrba.
An sha wa’azi mai ratsa jiki ga manyan malamai, tare da addu’oi ga waɗan nan yara. Sai ƙyaututtuka daga manyan mutane ta hanyoyi da dama. Al’amarin dai sai muce Alhmdllh. Sosai su baba malam da ƙannensa da Hajjo harma da iyalansu suke cikin dunbin farinci da zagayowar wannan rana a garesu, dan kuwa ba itace ta farko ba, dan wannan shine karo na bakwai da zasu aurar da yara a cikin wannan gida. Al’amarin kam ya burge mutane matuƙa, inda wasu sukaji inama sune da wannan ƙyaƙyƙyawar zuciyar haka irin tasu baba malam. Yayinda wasu kuma suka ɗauki ɗammarar shigowa cikin tawagar a dama dasu da iya abinda ALLAH ya hore musu suma. Komai ya ƙaytar, dan ya tafi cikin nutsuwa, sarki ya bama waɗanan yara ƙyaututtuka, hakama Gwamna daya turo wakilinsa dan shi bai samu damar zuwaba ya dai bada tashi ƙyautar ga waɗannan angwaye da amare.
Su Nu’aymah ansha kaikawo, dan kuwa sunyi tiɓis kamar sune amarorin. Bayan an tashi daga walimar da ƙyar suka rarrafa masaukinsu suna maida numfashin wahala. Su dai su Umm sunbi mazansu sun koma gida kamar yanda sukazo tare. Su Nu’aymah d Hajjo kuwa suna nan sai sunga ƙwal uwar daka.
Bayan sallar isha'i baba malam ya tattara ƴan uwansa su duka uku a falonsa. A tare sukaci abincin dare, tare da tattauna yanda walima ta tafi cikin aminci da farin ciki babu wata matsala. Sunyi godiya ga UBANGIJI da ya zamemusu garkuwa, sannan baba malam dake tsaye akan komai.
Ɗan murmushi kawai yayi batare da yace dasu komai akan hakanba. Kafin cikin nutsuwa ya nuna musu leda ruwan ƙasa da aka kawo ɗazun kafin walima tare da kayan abinci. Kasancewar bai samu zama dasu ba ɗazun sai bai sanar dasu komaiba ya bari sai sun dawo gida suyi maganar a tsanake sannan su duba abinda ke a ciki.
Abba Musbahu da ya kasance ƙarami shi baba malam ya mikama ledan yana faɗin, “Musbahu buɗe muga minene a ciki, dan shi manager ɗin kamfanin da aka kawo kayan ta hanyarsu yace dukkan bayanan da muke bukata zamu samu anan. Amma mu kwantar da hankalinmu wanda ya bada ɗin baiyi da wata manufa ba, kuma shi yayine badan musan wanene shi ba, idanma muna tsoron wani abune to duk abinda mukaga be kwanta mana a raiba ko wata matsala ta biyo baya to mu nemesa shi, zai kaimu ga mai saƙon idan buƙatar hakan ta taso”.
A tare sukace masha ALLAH, ALLAH ya sakanka masa da alkairi, ya biyasa da sakamakon abinda yafi wanda yayi. Shima ALLAH ya faranta masa fiye da yanda ya farantama mabukata.
“Amin". baba malam ya amsa musu, yayinda Abba Musbahu ya fiddo abinda ke naɗe cikin leda mai ƙyalƙyali. Buɗe ledar yayi sai ga madaidaicin kwali ya bayyana. ya buɗe kwalin shima. Sun sami envelope guda biyu, ta farko check na kuɗi da suka basu mamaki fiye da zato. Dan a irin wannan halin da ake ciki mai bada ƙyautar irin waɗanan kuɗi masu yawa haka ai dole a jinjina masa. Sai zungureriyar wasiƙa, wadda bayanan cikinta ke magana akan su bada sunan yara talatin na gidan marayun da suka ƙare sakandire, ya ɗauki nauyin karatunsu na jami'a harsu ƙare, maza 15, mata 15. sai sunan kuma wasu ashirin din, maza 10 mata 10 sukuma waɗanda suka kare karatun zai nema musu aiki. Daga ƙarshe yace yana roƙonsu alfarmar sakashi cikin jerin mutane da zasu dinga hidima ga wannan gidan marayu gwargwadon ƙarfinsa.
dukansu ajiyar zuciya suka shiga saukewa na mamaki da al'ajabin wannan mai saƙo. Kafin su shiga ja masa dogayen addu'oi, daga ƙarshe suka tattauna sosai akan lamarin. Sun yake shawarar faɗama UBANGIJI akan lamarin. Idan alkairine kuma mai wannan ƙudiri bada niyyar cuta musu ya zoba ALLAH yay riƙo da hannayensu gaba ɗaya. Idan kuma da wata manufa tattare da shi ALLAH yay musu maganinsa tunkan ya samu damar shiga jikinsu balle ya cutar da bayin ALLAH.
Daga haka suka tashi akan zasu mikama UBANGIJI kukansu tsahon kwanaki uku, inda zuciyarsu ta karkata akan al'amarin zasu ɗaukesa a matsayin shine zaɓin da ALLAH yay musu, saisu yanke hukunci akan hakan. zasu cire kuɗaɗen daya rubuta ɗin a maidasu asusun gidan marayun. bayan an gama ƙurar ɗaurin auren gobe idan ALLAH ya kaimu kuma saisu tantance yaran daya buƙata game da cigaban karatunsu da kuma waɗanda za'a nemarwa aiki.
ABUJA
Bayan tafiyar Yoohan da kamar awa biyu sai ga papa da tawagarsa shi kuma ya dawo gida. Dama sunje taron manyan fastocine daya gudana a jihar Lagos, yau kwanansu biyar kenan a can. Ya samu tarba daga iyalansa da ma'aikatan gidansa, inda madam Chioma ke maƙale da shi har sashensa tai masa rakkiya.
Bayan ya ƙimtsa ya fito sukai zaman yin lunch su duka a dining, sosai suka cika falon da surutu kamar ba abinci suke ciba, kowa na bama papa labarin abinda ya faru da baya gida. A cikin surutun nasu ne Abraham ke faɗama papansu an fasama Brother Yoohan motarsa a kano.
Cak Papa ya tsaya daga cin abincin yana kallon Abraham ɗin, kafin ya maida kallonsa ga Madam Chioma da a lokaci guda ɓacin rai ya mamaye fuskarta. “Mi naji Abraham na faɗa Darling?”. Kanta ta jinjina masa tana ɗan karta cokalin hannunta akan filet ɗin abincinta, “Hakane Honey, jiya da yaje Kano abin ya faru, dama jira nake ka dawo asan matakin daya dace a ɗauka, shiyyasa bance masa komaiba dan karya ce bayaso ayi komai dan kasan halinsa dai”.
Ɗan dukan table ɗin papa yayi da ture kofin da aka zuba masa lemo ya faɗi. A tare yaran duk suka zabura dan tsorota. Ya miƙe a fusace yana faɗin, “Miyasa tun a jiyan baki sanar minba, Gebrail ka tattaramin guards ɗin Yoohan gaba ɗayansu yanzun nan”.
Cike da jin daɗi Gebrail ya amsa ma papa yana miƙewa. Dan shima burinsa a ɗauki matakin dama.
Cikin mintuna ƙalilan guards ɗin Yoohan suka taru a falon, kallo guda zakai musu ka fahimci hankalinsu a matuƙar tashe yake. Musamman da suka shigo falon suka iske Papa nata kai kawo rai ɓace, kai kace gadin wani abu ya keyi. Sunkai tsayuwar mintuna goma kansu a ƙasa kafin ya kallesu da jajayen idanunsa.
“Inaga baku da wani amfani game da tsare lafiyar Yoohan, zamu sallameku mu canzaku da waɗanda zasu iya, dan na inhar kune zaku cigaba da kulamin da yaro wataran sai an masa yankan rago kuna kallo baku iya yin komaiba akai”.
Cikin ƙololuwar tashin hankali suke bashi haƙuri da roƙonsa. Suka ɗora da faɗin, ba laifinsu bane suma, boss ɗin nasune ya hanasu kowanne irin yunƙuri akan yarinyar. Kuma suna isowa sukaima Madam bayanin komai da ya faru....
Tsawa papa ya daka musu wadda ta sakasu yin shiru lokaci guda. “Idan ya hanaku ɗaukar mataki miyasa bazaku kirani tun a lokacin ku sanar mini ba?! Tunkan ku fara aiki ban sanar muku duk randa kukayi kuskure wani abu ya faru da yarona abakin aikinku ba?”.
Ka faɗa mana sir. Suka bashi amsa kowanne rai a dagule a tsorace kuma.
Hannu yasa ya bugi kujerar gabansa, “Oh shine kuma baku tuna wannan dokarba?!!”.
Madam Chioma dake bayansa ta kama hannunsa ta riƙe cikin nata tana ɗan murzawa alamar lallashi, dan bata buƙatar a sallami guards ɗin, itama suna mata nata aikin ne daban. “Darling relax, kasan halin Yoohan ɗin namu ai, kai musu afuwa su kiyaye gaba kawai. Sai kuma musan abinda ya dace a ayi, idan aikawa za'ayi a kamo mana yarinyar shikenan, dan bana goyon bayan a barta”.
Iska ya furzar daga bakinsa, ya zare hannunsa daga nata ya zagaya cikin falon sosai ya zauna a kujera. Kwalba dake a saman ƙaramin tray ya ɗauka ya tsiyaya abinda ke a cikinta a kofin glass ɗan ƙarami da shima yake a kan tray ɗin. Gaba ɗaya ya juye a baki yana ya mutsa fuska, kafin ya ajiye kofin ya kallesu ɗaya bayan ɗaya.
“A ina abin ya faru?”.
“A ƙofar gate ɗin wani orphanage ne sir, kuma muna ƙyautata zaton yarinyar itama ƴar gidan ce, dan ciki boss yasa muka shiga akai treatment ɗin yaron”.
“Daga nan zuwa safiyar gobe ku tabbatar wannan yarinyar tana nan cikin abuja, inba hakaba a bakin aikinku”.
A tare suka saki murmushin jin daɗi, dan koba komai suma dama ƙulle suke da yarinyar, da kuma takaicin hanasu ɗaukar mataki da Yoohan yayi jiya. Yanzukan sun sami damar cin ubanta dai-dai gwargwado. Cike da girmamawa da alƙawarin yin abinda papan ya sakasu suka amsa. kafin ya basu izinin barin falon.
Ko cikakken mintuna ashirin basu ƙaraba a gidan suka ɗakko hanyar kano duk da kuwa a lokacin ƙarfe ɗaya na rana ya gota.
Tofa, ana wata ga wata kenan???????? .
NU’AYMAH
A ɓangaren su Nu'aymah suma a washe garin wannan ranar bayan sakkowa sallar juma'a a massallacin aka ɗaura auren yara talatin da shida dake a gidan marayu na ƊAN JIBIYA FAMILY. Inda bayan kammala ɗaurin auren aka rakasu da addu'oin fatan alkairi kuma.
Da yamma su Nu'aymah suka ɗanyi shagalinsu iya mata a sashen matan, suma mazan anguna sukayi nasu a sashensu tare da sauran angunan da ba'a gidan marayun suke ba suma. Bayan sallar la'asar kusan ƙarfe biyar da tai dai-dai da isowar tawagar guards ɗin Yoohan gidan marayun aka kwashi amare gaba ɗayansu aka miƙasu ɗakunan mazansu, bisa rakkiyar iyayensu su baba malam. bayan doguwar nasiha da sukasha daga garesu tamkar yanda mahaifa kema ƴaƴansu idan zasu miƙasu gidan miji.
Duk wani jan ido da barazanar Guards ɗin Yoohan securitys sun hanasu shiga cikin Orphanage ɗin, acewarsu sai dai su faɗi miya kawosu anan gate, idan sunga da damar barinsu su shiga shikenan, idan sunga babu damar hakan kuma sai dai su juya. Ran guards ɗin ya ɓaci matuƙa, sunji kamar su harbesu kowama ya huta. amma sai suka danne sukai musu bayani akan abinda ya kawosu, tare da tabbatar musu suna tare da ƴan sanda.
Duk da securitys ɗin gidan marayun sun gane wa ake nufi da kuma miya faru jiya sai suka nuna bama su ganesuba, dan a ganinsu bai kamata su bada damar da za'aci zarafin ƴa ɗaya tilo ga wanda bai taɓa gajiyawa wajen musu hidimaba. Sun kaɗasu dambu taliya sunce basu gane Nu'aymah ba, su bama susan anyi wani abuba.
Ran guards ɗin yayi ƙololuwar ɓaci, sai dai ɗaukar mataki ya gagaresu, dan suma securitys ɗin gidan marayun bawai kanwar lasa bane. Sun san taɓasu babban bala'ine ga ogan nasu papa balle su ɗin karan kaɗa miya. Dan haka suka bar orphanage ɗin ransu a ɓace, akan zasuje su sake shiri gobe su dawo.
Hotel suka kama, kafin su kira papa su sanar masa da komai daya faru.
★★★★
Su Nu'aymah da basusan wainar da ake toyawaba ana kammala miƙa amare baba malam yasa Yah Ahmad ya tattara masa su aka wuce dasu gida badan sunso hakanba. Dan so sukai sukam sai sunyi sati ɗai-ɗai a gidan kafin su koma gida. Sai dai baba malam ya ɓata musu shirinsu.
Aiko koda suka koma gidan sai suka dinga fushi da kumbure-kumbure. Kayan biki da baba habi ta haɗa musu ma sunƙi kulawa. Babu wanda yabi takansu a gidan, saisu Kubrah ne ma ke musu dariyar tsokana suna sake ƙulal dasu dan duk suna sashen Hajjo ne da suka dawo tare.
Gaba ɗaya ran guards ɗin Yoohan a ɓace yake, tunda suka iso hotel ɗin da suka kama basu zaunaba, sai faman ƙulle-ƙullen yanda zasu sami Nu'aymah da matakin da zasu ɗauka a kanta sukeyi. Kai kace wata babbar ƴar ta'adda suke bibiya.
Sun ƙulla yafi sau hamsin suna warwarewa. Suna tsaka da sake ƙullawa saƙo ya iso garesu daga hannun ɗaya daga ma'aikatan hotel ɗin. Number wayace daga wani, ya basu damar su kirashi idan suna buƙatar sanin inda wadda suke nema take..
Da yake burinsu kenan jiki na ɓari suka kira kuwa. Ba'a ɗagaba har sai da ta kusan tsinkewa. Ƙinyin magana akayi. sai da ɗaya daga cikin guards ɗin ya fara magana.
“Duk da bamusan ko wanene ba, mun maka alƙawarin inhar ka sanar mana inda yarinyar take zamu biyaka da kuɗi masu nauyi, oganmu ma zai maka ƙyauta ta musamman”.
Batare da an basu amsaba aka yanke wayar. Kallon juna suka shigayi tambayoyi fal ransu. Kafin ɗayansu ya iya furta wani abu sai ga saƙo ya shigo. Da sauri suka buɗe ganin Number da suka kira ɗince. Ba komai bane a saƙon face cikakken address ɗin gidansu Nu'aymah, da sunanta harma da hotonta.
Daɗine yay mugun kamasu, dan kuwa sun sake tabbatar da itaɗince, dan haka jiki na rawa suka sake kiran wanda ya tura musu ɗin. Yanzun ma dai baiyi maganaba, sai sune suka buƙaci ya turo musu accaunt details nashi ko nata zasu tura masa ladan aikinsa. Ƙitt aka yanke wayar batare da ance komaiba. Mintuna kaɗan kuwa saiga accaunt Number an turo. A take suma sukaima papa massege bayan sun kirashi sun sanar masa komai.
Har a lokacin cike yake da ɓacin ran abinda ya faru, dan yaje yaga yanda akaima motar bugu na fitar hankali, shiyyasa ransa ya sake ɓaci, ya kuma tabbatarma kansa ko ɗiyar uban wacece yarinyar sai ta yabama aya zaƙinta.
Babu ko tantama ana turo masa accaunt details ɗin ya antayama maishi kuɗi masu tsoka, dan a ganinsa bukatarsa ta biya. Mizaisa yaji ciwon biyan wanda ya taimakesu.
NU’AYMAH
Yau sama-sama Nu'aymah ta wayi gari, dan ta tashi da ciwon ƙafa alamar zuwan period ɗinta. Ita dama takan fara da ciwon ƙafane, randa yazo kuma zataita amai har saita jigata. Kafin daga bisani ta koma normal sai shegen ƙwaɗayi kamar taci mutum ɗanye.
Tunda Umm ta shiga tadasu sallar asuba ta lura batajin daɗi, dan maimakon kwance saita isketa zaune ƙasa a bakin gado kan kafet ta kife kanta a kan gadon. Yusrah da Amal nata barcinsu a kan gadon su. Ita ta fara tadawa kafin su Amal, har zata juya ta fita sai kuma ta dakata ta kalli Nu'aymahn data maida kanta ta kife tsakanin ƙafafunta.......
“Ke kuma lafiya?”. Da ƙyar Nu'aymah ta ɗaga kai ta kalli Umm, sai dai gudun kar ace ta shirya aje asibiti a mata allura sai ta daure tace, “Umm lafiya lau, kawai gajiyace tasa ƙafafuna ciwo”.
Ɗan ƙura mata idanu Umm tayi na wasu mintuna, kafin ta janye tai ficewarta batare data sake cewa komaiba. Yusrah ce ta ƙaraso wajen Nu'aymah ɗin ta durƙusa. “Baby ƙarya kikaima Umm wlhy, daga gani baki da lafiya”.
Yamutsa fuska Nu'aymah tayi kaɗan tana maida ƙwallar data cika mata ido. “Ƙafafuna ke ciwo wlhy Yusrah, nasan kuma period ɗinane zaizo zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu ko anjima”.
Amal dake fitowa daga bayi tace, “To miyasa kikaƙi faɗar gaskiya?”. Yusrah data harbo jirgin Nu'aymah tai saurin cewa, “Allura”. A tare suka kwashe da dariya ita da Amal. Nu'aymah kuma tai tsaki idonta cike da ƙwalla ta miƙe. Da ɗingishi ta shiga bayi batare data kula dariyar dasu Yusrah ke mataba har yanzun.
Bayan sun idar da salla Yusrah da Amal suka fice taya iyayensu aiki, Nu'aymah kam saita koma saman gado ta kwanta. Babu jimawa barci yay gaba da ita.
Umm da duk ta gama fahimtarta bata nemeta ba, dan tasan zata gama zagayenta ne tazo ta nemeta. Bayan sun kammala breakfast ita da ƴan aiki ta shirya na baba malam da sauran ƴan uwansa a falonsa da kanta kamar yanda ta saba inhar duk suna gari, dan tare sukecin abincin safe da dare. Na rana ne dai bai zama dole su dukansu suna a gidaba shiyyasa. Garama idan ta kama juma'a ace dan duk basa zuwa ko ina a wannan ranar sai massallaci.
Sai da taga komai ya mata yanda takeso sannan ta saka turaren wuta ta leƙa bedroom ɗinsa. Yana wanka, sai kawai ta buɗe Wadrobe ɗinsa ta zaɓo masa kayan da zai saka, saboda yau zasuje taron wani wa'azi a jihar katsina. Bayan ta ajiye masa duk abinda tasan zai buƙata ta fita zuwa ɗakin Muhammad danta taimaka masa yayi shirin makaranta shima.
08:15am
Kusan takwas da kwata su baba malam suka hallara a falonsa shi da sauran ƴan uwansa domin karyawa. Sun sake gaisawa cikin girmamawa kamar yanda suka sabama kansu. Kafin su zauna su fara karyawa abin cike da birgewa.
Sunyi nisa da cin abincinsu sukaji sallama. A tare suka amsa idonsu akan ƙofar. Ƙarasawa ciki falon Abbas da yay sallamar yayi. Ya durƙusa har ƙasa ya gaidasu. kafin cikin damuwa yace, “Abba ƴan sandane ke sallama”.
“Ƴan sanda kuma Abbas? Lafiya dai ko?”. Baba malam dake kallon Abbas babu ko ƙyaftawa ya faɗa.
“Abba ban saniba wlhy, amma sun nuna wai an turosu su tafi da Nu'aymah ne”.
Ran Abban Adawiya a ɓace yace, “Wace irin Nu'aymah kuma? Miya haɗata da ƴan sanda banda shashanci irin naka Abbas?”. “Wlhy Abba haka sukace, dan hotonta ma suka nuna”. Miƙewa sukai su duka huɗun, sai dai su uku suka fara fita, kafin baba malam yabi bayansu..............✍
ZAFAFA BIYAR 2021
Hafsat miss xoxo????
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).????????
Mamu gee????
MIN ƘALB!!????????
Hafsat rano????
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!????????
Safiyya huguma???? SIRAƊIN RAYUWA????????
Bilyn Abdull????
SARAN ƁOYE????????
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka????????????????
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????
09033181070
????????????????????????????????????????
TEAM—-ZAFAFA BIYAR????????????????
ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????.b
ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE
*_KAJI shahararrun kuma mandiyoyin ƴan ƙwalisar kawo kayan kitchen masu tafiya dai-dai da zamani. Idan nace nadaban ina nufin suɗin nadabanne wajen kaya ƴan gaske dake ƙawata kitchen ɗin amarya harma dana uwargida ƴar ƙwalisa. Ka siya ka tabbatar ka saya ɗin ko a gaban tsaranka sai ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE. sunan kayansu sa kishiya cin bashi????, dan tana ƙyalla ido taga kitchen ɗinki tsarin amerikawa tuni zata fara ƙwafa da tunanin zuwa gidan delu dillaliliya mai saida kwanika. Sai dai kuma kama da wane akace bata wane, dan haka ku maza ku garzaya ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE. domin samun naku kuma. Suna kawo kaya daga ƙasashen ƙetare akan farashi mai sauƙi da rahusa. Suna order ɗin products kamarsu, dukan kayan kitchen na zamani, bedsheets, shoes dade sauransu, products ɗinsu pre-order ne dake zuwa akan lokaci batare da mai kaya ya ƙosa da jira ba ko samun matsala. Zaku iya samunsu a Number waya kamar haka ko Location nasu. Phone number: 08102393622. Location Gombe. Amma Zasu iya turawa kowani gari dake a lungu da saƙo na ƙasarnan. Sayen nagari maida kuɗi gida. Ku garzaya kar ayi babu ku. Da ƙyar nasha yafi da ƙyar aka kamani inji masu iya magana????????????????????._*
14
……………..A tare suka fito harabar gidan, inda suka iske matan gidan da sauran samarin da basu kai ga ficewa sabgoginsu ba duk sun fito suma.
Suna ƙarasawa ga ƴan sandan Nu’aymah da Amal taje ta kira itama sai gata ta fito tana ɗan ɗingisa ƙafa. Sanye take da siket da riga na atanfa, sai ƙaramin hijjab da Umm ta sabar mata da sakawa a cikin gidan saboda samarin gidan tunda ba muharramanta bane ba.
Tunda su Baba malam suka fito jikin wasu a cikin police ɗin yayi sanyi ganin dai da gaske an turosune gida mai daraja kamar wannan dan suyi abinda basu da tabbacin faruwarsa tunda ba’a gabansu akaiba. To amma yaya zasuyi, d.p.o ne da kansa ya sakasu zuwa su kama Nu’aymah, ga kuma kuɗaɗe da sukaci har kashi biyu daga Papa da kuma guards ɗin Yoohan na toshiyar baki. (Ya rabbi ka tsaremu cin rashawa da bada ita. Amin????????????).
Sun gaisa dasu Abba cikin girmamawa, kafin su sanar musu daga station ɗin da aka turosu da kuma abinda zasuyi. Kusan a tare su Abbah duk suka juya suna kallon Nu'aymah. Baba malam ne kawai kansa a ƙasa yana ɗan murmushi. Batare da yace komaiba ya nufi inda jama'ar gidan ke tsaitsaye suma suna kallonsu hankali a tashe.
Hannun Nu'aymah ya kama batare da yacema kowa uffanba. Itama kuma babu musu ta bisa har wajen ƴan sandan. Ya miƙama macen hannun Nu'aymah yana faɗin, “Itace wannan?”.
Kallon hoton dake a waya babban nasu yayi, kafin ya kalli Nu'aymah. “Eh itace ALLAH ya gafarta malam”. Ya faɗa cike da girmamawa ga baba malam. Murmushi baba malam yay musu yana nuna masu Nu'aymah dake kallonsa kamar wata sokuwa. “Gata nan, zaku iya tafiya da ita”. Da sauri Abban su Abdallah ya yunƙuro zaiyi magana baba malam ya ɗaga masa hannu fuska a ɗaure. Cak ya tsaya hankalinsa a ƙololuwar tashe. Hakama su Abban Adawiya hankalin nasu a tashe yake da hukuncin da baba malam ya shirin yankewa. A ganinsu ai basai anje station ba, zasu iya tsayawa su tattauna anan, musamman ma shi Abban Adawiya da yana cikin Orphanage randa abin ya faru. Kuma an sanar masa komai akai.
Godiya ƴan sanda sukai tare da juyawa da Nu'aymah zasu tafi. Tirjewa tai tana kallon Baba malam daya ɗauke kansa gaba ɗaya daga garesu tamkar baisan mi akeyiba. Hannunta ta fara ƙoƙarin fisgewa idanunta na cika da ƙwalla. “Abba wlhy bansan mina musu ba”. Tai maganar muryarta na rawa.
Juyawa baba malam yayi zai bar wajen batare daya kula maganar Nu'aymah ba. Sai da yay taku biyu uku sannan ya tsaya tare da juyawa ya kalli ƴan sanda da Nu'aymah data fisge zata dawo. Cikin tsananin kaushin murya yace, “Idan bazata biku da arziƙiba ku ɗauketa!!”.
Tsayawa Nu'aymah tayi cak tana kallon baba malam ɗin. Sai kuma ta kalli inda su Umm suke. Sake dawo da idonta tayi kan ƴan sandan da suma ita suke kallo. kunyar baba malam ce kawai ta hanasu fara cin ƙaniyarta tun anan. Tsaf ta haɗiye kukanta. Ta juya cikin ɗingishi ta nufi ƴan sandan. Basuce mata komaiba suka tasa ƙeyarta gaba suka fita waje inda motarsu take.
A gaban ƴan anguwa daketa kai kawo aka sakata a motar ƴan sanda. Gaba ɗaya hawayen da Nu'aymah ta fara ɗazun sun ƙame ƙaf. Ta cusa kanta tsakanin cinyoyinta tai shiru. Sai faman cije baki kawai take saboda zugi da ƙafarta ke mata. Har suka isa police station ɗin bata ɗagoba. Sai da ƴar sandar ma ta taɓata sannan ta san sun iso. Ɗago kanta tai a hankali ta kalli station ɗin, sai kuma ta juya ga ƴar sandar dake mata kallon tausayi. Dan ita yanda taga mutanen na hanƙoro akan yarinyar ta zata ma wata tsohuwar macece, ashe yarinyace ƙarama. Itace ta taimaka mata ta fito, ta kama hannunta ganin kamarma ta kasa tsaiwa. A haka suka shiga cikin station ɗin da taimakon ƴar sandar.
“Amma Yaya ka.......” hannu baba malam yay saurin ɗagama Abban su Adawiya dake son masa bayanin ainahin abinda ya faru. Ya kallesa fuskarsa babu wasa, “Banason jin komai akan hakan Mustapha. Kaje ka shirya mu wuce banason yazam mu ake jira”.
Kai kawai Abban su Adawiya ya kaɗa masa. Kafin ya kalli su Abba Musbahu ya bar wajan jiki a sanyaye. Da sauri su Abban Abdallah suka nufi mota da nufin bin bayan su Nu'aymah, sai kawai a bazata suka tsinkayi muryar Baba malam na faɗin, “Na haramtawa kowa bin bayanta a cikin gidan nan, idan kuma wani ya aikata koda ban saniba zai fuskanci fushina”.
Cak suka tsaya daga yunƙurin shiga motar, kowannensu goshinsa na tara zufa. Babu wanda ya iya sake cewa komai har Baba malam ya shiga sashensu ya fito cikin shirin fita. Ta gabansu ya wuce zuwa sashen Hajjo data sha maganin mura tun ɗazun ta kwanta. Duk wainar da ake toyawa bata saniba dan barci takeyi. Baifi mintuna biyarba sai gashi ya fito. Yanzunma bai kalli sashen da kowa yake ba ya nufi inda motar da zasu tafi take, sauran motocin uku da ɗalibansu zasu shiga da ƴan agaji kuma duk suna a harabar massallaci.
Suna kallo motar ta fice batare da ko mutum ɗaya ya iya cemasa a dawo lafiya ba, shima kuma bai nuna ya damu da hakan ko jiran cewar tasu ba.
Umm ce ta fara sulalewa ta koma ciki, kafin sauran suma su fara zare jiki ɗai-ɗai suna shigewa sashensu. Addah dai bayan Umm tabi tana share hawayen da ke sakko mata batare data farga da fitowarsu a cikin idanunta ba.
ABUJA
Tunda labarin kama Nu'aymah ya isa kunne Papa farin ciki ya mamayesa shi da Madam Chioma, breakfast da suke shirin zamanyi ma su kasawa sukayi, sai kai kawo sukeyi zuciyoyinsu fes kamar an basu rabin duniya.
Dolene yasa a koyama yarinyar hausawan nan hankali, dan shi a rayuwarsa idan da abinda yafi tsana a rayuwarsa to ƴan yankinta ne. Ya tsani yarenta fiye da mutuwarsa, a cewarsa babu abinda suka iya sai haihuwa, ƴaƴan nasu kuma babu tarbiyya sam, daga ƴan bangar siyasa sai masu bara. Sam mutanen da yankinsu basu masaba, inda ace zai iya zama shugaba, sai ya shafe yankin ko tarihinsu baza'a sake aji ba. (hummm Papa, a ringa sara dai ana duban bakin gatari).
Abinda papa ya keta faman rayawa a ransa kenan yana murmushi. Waya ya sake ɗagawa yay magana da d.p.o ɗin akan yanzunan a bama guards ɗin Nu'aymah su taho masa da ita Abuja. Shi kuma d.p.o ya turo da accaunt Number ɗinsa yanzu zaiji alert.
Cike da farin ciki d.p.o ya amsama papa. Babu ko tunanin komai a ransa ya aika da accaunt details nashi, ya kumayi zaman shirya takardar ƙarya akan laifin da bashi Nu'aymah ta aikataba.
(Humm! Ya ALLAH ka shiryemu ka shiryi shuwagabannin mu da jami’anmu. Ka tsame bara gurbin cikinmu, idan masu shiryuwane ka shiryesu. Idan bazasu shiryuba UBANGIJI kafimu sanin miya dace dasu, mun barka dasu????????????).
LAGOS
Fitowarsa kenan daga ɗakin theatre a matuƙar gajiye. yanda yake tafiya kawai zai baka wannan amsar. Tare yake da likitoci uku da suka tayasa aikin, sai Nurses suma guda uku. Dai-dai sun ƙaraso ƙofar wani office nurse ɗin dake a gefen damarsa ta miƙa masa tasar hannunta ya jefa hand gloves ɗin daya cire daga hannunsa ya jefa a ciki, hannu ya ɗaga musu kawai alamar su dakata anan ya tura ƙofar ya shige.
Basu damu ba, dan kowa yasan Dr Yoohan haka yake, mutum ne mai ƙoƙari akan aikinsa da himma, ga tausayi sosai musamman ga marasa ƙarfi. Bashi da yawan magana, sannan baida fara'a. Wanda bai fahimcesa ba zaita ɗauka kamar kullum shi cikin ƙuncin rayuwa yake, kokuma girman kaine bisa ga ɗaukakar da ALLAH ya basa. Idan kuma ka fahimcesa zaka gane cewa haka halayyarsa take, shi kawai aikinne a gabansa ba shiririta da shashanci ba. Akance likitoci mafiya yawansu sunada son mata, sai dai ga Dr Yoohan sam ba haka baneba. Duk yanda matan ke binsa da soyayya shi bama su ishesa kalloba, shi fa a rayuwarsa damuwarsa kawai shine aikinsa, sai ko family ɗinsa da taimakon marasa ƙarfi. Idan ya shiga cikin musulmi bazaka taɓa cewa shi ba musulmin bane, musamman daya ajiye ƙasunba da yanda yake gudanar da al'amuransa sak halayyar musulman ƙwarai. Sai dai fa idan kaci karoda sarƙar Cross a wuyansa da akoda yaushe baya fashin sakawa ne zaka gane daga ina ya fito. ALLAH ya ɗaukakashi a duniya a dalilin ƙwaƙwalwar aikin likitanci daya azurtashi da ita, likitane shi da kota wane fanni zai iya gunar da aikinsa akan mara lafiya, sai dai abinda ba'a rasaba kam, dan UBANGIJI shine mai komai da kowa.
Office ne daya amsa sunansa office. Bakajin komai sai sassanyan ƙamshin turarensa dana ac. Wanda ke zaune a rikunin kujeru uku dake can gefen office ɗin yana aiki ya miƙe yana masa barka da fitowa cike da kukawa.
Kansa ya ɗaga masa fuska a yamutse na alamar gajiya. kafin ya ƙarasa ga kujerar zamansa yaja wani file dake a jiye ya fara singing.
Tasowa Richard yay da sauri garesa yana murmushi, ya ajiye files ɗin hannunsa gaban Dr Yoohan ɗin yana faɗin, “Doctor akwai mutane biyu da zaka ganifa yanzun kafin ka tafi hutun awa uku da rabi, idan lokaci ya cika zaka sake shiga theatre room, na mutane biyu da suka rage suma”. Da sauri Yoohan ya ɗago yana kallon Richard fuska a marairaice kamar zai fasa kuka. Richard yay saurin haɗiye dariyar dake neman kufce masa dan yasan shima da gaske Yoohan ɗin ya kai iyakar gajiya, amma sai ya fiske yace, “Da gaske nake Yoohan, gama files nasu na kammala dubawa”.
“Rich.. Please, wlhy na gaji, sai dai kai ka dubasu” ya faɗa yana sauke numfashi da miƙewa ya nufi wata ƙofa.
Murmushi Richard yayi yana binsa da kallo harya shige. Ya ɗan girgiza kansa da kwasar files ɗin ya fice daga office ɗin zuwa nashi shima.
ALLAH ne ya haɗashi da Yoohan tun a secondary school, a farkon haɗuwarsu sam basa shiri, dan abokan faɗan junane a aji. Ba komai yasa rashin jituwa tsakaninsu ba sai kasancewar su duka sunada matuƙar ƙoƙari, kafin Yoohan yazo school ɗin shike ɗaukar na ɗaya a ajinsu, amma Yoohan na zuwa ya amshe wannan matsayin. Kafin zuwan Yoohan ɗin kuma kowa sonsa da girmamasa yake a ajin, hasalima shine Monitor, ƴammatan ajin ji suke tamkar su haɗiyesa kuma. Amma Yoohan na zuwa nanma komai ya canja, kan ƴan ajin ya rabu biyu, wasu na ɓangaren Yoohan wasu Richard. Dan haka aka zama abokan dabin juna, duk da sam Yoohan baya kula duk haukarsu. Rashin kulawar Yoohan ɗin tasa a koda yaushe shi da tawagarsa suke ɗauka Yoohan matsoracine, dan babu wanda ya taɓa ganin faɗansa. Sai fa wataran da suka kaishi bango yayma Rich dukan mutuwa, da ƙyar aka karɓesa a hannunsa dan Yoohan akwai zuciyar tsiya. Tun daga wannan duka da Yoohan ya masa suka koma abokan juna, tun sauran ɗalibai na ƙalubalantar abotar tasu har suka fahimci ta gaskiyace suma sukabi. Shi da Yoohan duk burinsu ɗaya ne akan karatu, dan haka haɗewarsu waje guda ta ƙara musu himma da ƙwazo. Koda suka kammala secondary kuma cikin amincin ALLAH iyayensu suka amince musu tafiya karatu tare. A gaba ɗaya rayuwarsu tare ta gudana, sai daga bayane Yoohan daya cigaba da wasu kwasakwasai (Courses) ne suka ɗan rabu, danshi ya amshi aikin da aka bashine a ƙasar London bayan zamowarsu cikakkun likitoci, saɓanin Yoohan daya ƙi amincewa.
Daga baya Yoohan ya kuma samun ɗaukaka fiye da tashi, danshi ya ƙara faɗaɗa wasu karance-karancen daya bashi damar iya duba marasa lafiya ta kowane fanni, aikinsa ya zam zai iya yinsa a kowacce ƙasa kuma.
Bayan shekara ɗaya da fara wannan gwagwarmayar Yoohan ya fahimci bazai iya shi kaɗaiba sai da taimakon Richard, dan haka yaje ya dabaibayesa da daɗin baki har saida ya amince suka sake curewa waje guda suke gudanar da aikin a tare. Yanzu haka shekararsu ta biyu kenan da fara aiki, suna ɗaya daga cikin manyan matasan likitoci da duniya ke alfahari dasu bama ƙasarsu ko yankin Africa kawai ba.
A yanzu haka dai shi Richard ana shirin aurensa ma da wata baturiya, shiko Yoohan yaƙi motsawa sam, a cewarsa shi bama zaiyi aure yanzuba sai nan da wasu shekarun daya tsara.
Ɗakine madaidaici dake ɗauke da kayan ɗaki complete, shima sai ƙamshi yakeyi kamar ba'a cikin asibiti ba. Kansa tsaye toilet ya nufa yana faman lullumshe idanu dan barci yake matuƙar ji. Tunda ya iso Lagos a daren jiya bai hutaba, dan ya iske patients da yawa da sukai booking ɗin ganinsa. Tun a jiyan yay dauriyar zaman duba files ɗinsu, waɗanda yasan akwai mafita ya rubuta musu Doctors ɗin da zasuje su gani ya turama Rich. Waɗanda kuma yasan sai shine zai duba ya sanar da Richard ya sanar musu time ɗin da zasu gansa ta hanyar text messeges.
A safiyar yau tun ƙarfe huɗu na asuba ya baro gida, tunda yazo kuma aiki yake bai hutaba. Bayan ya gama duba adadin daya ƙayyade ya shiga theatre akan matsaloli daban-daban kuma, yanzunma ba ya gama baneba, yanada loacin hutawa ne na awa uku da rabi kafin ya koma ɗakin theatre ya ƙarasama mutane biyu dake a ƙasa kamar yanda Rich ya faɗa. Bayan ya kammala dasu zai ƙara hutun awanni uku jirginsa ya ɗaga zuwa ƙasar Kenya inda wasu patients ɗin ke jiransa canma.
Bayan wasu mintuna ya fito daga toilet ɗin sanye da rigar wanka Blue, sai hular wanka data kare gashinsa daga jiƙewa, da alama dai baya buƙatar jiƙawar. A bakin gadon ya zauna yana mai furzar da iskar daya cika bakinsa da ita, yajawo wayarsa dake a drowar gefen gadon a jiye ya cireta a silent. Dan ya sakata a silent ɗinne tun lokacin dazai shiga theatre room. Solomon ya kira, sai akai rashin sa'a ya samu wayarsa a busy.
Kume fuska ya sakeyi alamar baiso hakanba, ya ajiye wayar. ɗayar ya ɗauka itama ya cireta a plane mode daya sakata. Kamar jira ake ya cire ɗin sai ga kira ya shigo, kafin ya amsa kuma akai knocking ƙofar. Rasa wanne zai farayi yayi. Ɗaga wayar? Kokuwa buɗe ƙofar?.
“Yoohan!” ya tsinkayi muryar Richard na kiransa. Duk da yayi tunanin akan maganar patients ɗin da Rich ɗin yay maganar zai dubane hakan bai hanashi tashi ya buɗe masa ƙofaba, sai dai ya sake haɗe fuska alamar da gaske ya gaji baison takura.
Yana buɗe ƙofar yace, “Rich plea.....”
Saurin katsesa Richard yay da faɗin, “Yi haƙuri ba wancan maganar bane, akwai damuwa Yoohan, matar da kaima aiki a kano yanzun nan Doctor Sa'ad ke sanar min an samu matsala”.
“What?!” ya faɗa hankali tashe. Shima Richard da hankalin nasa ke a tashe ya shiga jinjina masa kai. Juyawa cikin ɗakin yay da sauri, yama manta da wata gajiyarsa. Wayarsa ya ɗauka domin neman Dr Sa'ad. Ganin ashe shinema ya kirasa ɗazun lokacin da Richard ke knocking ya sakashi kiransa. Bugu ɗaya kuwa Dr Sa'ad ɗin ya ɗaga.
Ko gaisuwa basuyi zaman yiba Dr Sa'ad ya shiga masa bayanin dukan abinda ya faru, da halin da matar ke a ciki yanzun.
Hannunsa dafe da kansa cikin tsagwaron damuwa yace, “Dr Sa'ad ta yaya hakan ta faru? Ince duk yanda ya kamata a bata kulawa na sanar muku. Miyasa kuke da sakaci akan rayukan mutane!!?” ya ƙare maganar da ɗan kaushin murya.
Dr Sa'ad da maganar Dr Yoohan tai masa zafi ya buɗe baki zaiyi magana cikin ƙoƙarin danne fushinsa, amma sai Yoohan ɗin ya kuma dakatar dashi ta hanyar faɗin, “Bana buƙatar jin komai please, zan turo maka hanyar da zakubi wajen fara bata taimako yanzun, nima ina hanyar tahowa”.
“Okay Sir” Dr Sa'ad ya amsa masa daga can cikin wata irin murya mai cike da ɗaci da takaici. Yaro ƙarami dashi yana juyasu dan kawai ALLAH ya basa baiwar da tafi tasu, tabbas idan ba kawar da Dr Yoohan sukaiba a duniya rayukansu da hanyar cin abinsu na a cikin garari.
(Ni dai nace Humm).
Shi Yoohan baima saurari amsawar Dr Sa'ad ɗinba, dan tuni yayi wurgi da wayar saman gado cike da takaicin likitoci irin Dr Sa'ad, da a kullum basu da kishin ƙasarsu da jama'arsu, burinsu sudai kuɗi kawai da taƙama da aikinsu. Da hanzarinsa ya fito ainhin Office ɗin yana faɗin, “Rich Please ka bincika min idan akwai jirgi mai tafiya kano daga nan zuwa mintuna talatin”.
Da sauri Richard ya fita daga office ɗin zuwa nasa, dan yabar wayarsa a canne. Shi kuma Dr Yoohan yaja Laptop ɗinsa dake saman tebirin daga tsaye ya shiga dannata da sauri sauri cikin ƙwarewa. A haka Solomon ya shigo ya samesa, batare daya tsayaba yay saurin shigewa bedroom ɗin domin fidda masa kayan da zai saka dan Richard ya sanar masa halin da ake ciki, kuma shi Dr Sa'ad ya fara samu a waya kafin Richard ma.
Dr Yoohan na kammala tura abinda zai aikama Dr Sa'ad ya nufi ɗakin shima. bai wani damu da tsayawa duba kayan da Solomon ya ajiye masanba ya ɗauka ya fara ƙoƙarin sakawa, shi kuma Solomon ya fito ya bashi waje.
Shirin yake ransa duk a jagule da takaici, yana kammalawa ya fito jacket ɗin suit ɗinsa a hannu, necktie ɗinma haka. Gashinsa kansa yau sama-sama ya samu gyara. Haka yake shi, a kullum matsalar al'umma itace tashin hankalinsa da damuwarsa. Da kaga damuwa a idanunsa to patient ɗinsa na cikin matsala ne. Baiko kalli inda Solomon ke tsaye da jikkarsa a hannuba ya nufi hanyar fita fuskarnan babu alamar wasa.
Kusan cin karo sukai da Richard dake ƙoƙarin shigowa ya sanar masa an samu jirgi, kuma cikin amincin ALLAH zai tashi nan da mintuna goma sha bakwai ne, da ƙyar akama samu ticket ɗin guda biyu. A yanda Dr Yoohan yasan garin Lagos da yammaci irin haka yasan kafin su isa airport ma lokacin tashin jirgin ma ya wuce, dan haka ya yanke shawarar su tafi a Ambulance kawai zasufi samun hanya da sauri.
Rich kansa yayi na'am da wannan tunanin na Yoohan, dan haka yama yanke shawarar kaisu da kansa ko Yoohan ɗin zai kuma samun nutsuwa.............✍
ZAFAFA BIYAR 2021
Hafsat miss xoxo????
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).????????
Mamu gee????
MIN ƘALB!!????????
Hafsat rano????
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!????????
Safiyya huguma???? SIRAƊIN RAYUWA????????
Bilyn Abdull????
SARAN ƁOYE????????
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka????????????????
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????
09033181070
????????????????????????????????????????
TEAM—-ZAFAFA BIYAR????????????????
ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????.
SAHFAT PREORDER!
Wani kaya sai amale ka ɗauka????.
SAHFAT PREORDER maida tsohuwa yarinya.
Kaji masu kawo kayan adon gida dana jiki ƴan gaske.
Ina mata masu ƴan bana bakwai? ko uwargidar da ake shirin kawoma ƴar bana bakwai?. Kai hardama matan gayu ƴan ƙwalisa masu son sabunta gida da kayan ado ƴan waje masu sauƙin farashi da nagarta!.
To ku garzayo dama ta samu, dan SAHFAT PREORDER sune na ɗaya a wannan fanin. Idan kayan kitchen kikeso masu ƙyau da nagarta a farashi mai sauƙi kuma zaki samu a Sahfat preorder. Idan kayan sakawa kikeso na manyan mata ƴan gayu suma akwaisu babu ƙayarya. Jaka ko takalma na nunawa tsara suma ba’a barsu a baya ba harma da mayafai. Hakama kayan ɗaki basu da tsara.