Uncategorized

MUSAYAR RUHI 3-4

 *⚜️MUSAYAR RUHI⚜️*

               *NA*

      *NPEEDY A AJI* 

 _(MARMIY ZARAH CE)_

“`LITATTAFAN MARUBUCIYAR SUNE“`

*1. NAYI RAYUWA DASHI*

*2. SANADIN ACCIDENT*

*3. SAKAYYAR CUTA*

*4. RUFAFFIYAR ZUCIYA*

*5. MUGUN SARTSE*

*6. FURUCI….*

*7. JUYI BIYU*

*8. HAYATUL MAHAYAT*

        AND NOW

“`MUSAYAR RUHI“`

*_____________________________________*

 *????????AINUWA ????RITER’S✍????*

*????SSOCIATION????????*

 “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

 *Page 3 & 4*

*S* osai zuciyar Hammat tayunquro duban momcy yayi cikin ‘bacin rai yace ” toseme dan ansakar miki yarki to ammafa kisani duk sanadintane wannan abun yafaru na tabbata idan badan wannan auran ba bazaiyi gaggawaba wajan sakkowa daga jirgi ba sannan fad’ar doctor bafad’ar uban giji bace in sha Allah bro na zaiwarke nankusa kisani komameye yasameshi shi yafi qarfin akwatantashi da mace namiji ne tsayayye ” 

Daga haka yanufi room din da Hamut yake afusace dubanta mahaifin Hamidat yayi cikin ‘bacin rai yace 

” Salma kece kike fad’in haka dabakinki tabbas kinzama butulu to amma kisani idan har nine mahaifin Hamidat to batadawani miji wanda yawuce Hamut koda kuwa bazai warkeba har abada idan nasakejin wannan banzan furucin senayi mugun ‘bata miki rai ” shima barin gurin yayi cikin ‘bacin rai Sosai hankalin Sarki jafar yatashi itako hajiya kilishi wasu hawaye masu d’umi taji suna sakkowa daga kuncinta hakama hajiya Fulani Hammat yana shiga yaga Hamut yasaka hannu saman fuskarshi hawaye nagangarowa tagefan fuskar shi sosai Hammat yaji zuciyar shi tasakeyin kunci sosai zama yayi yakamo hannunshi cikin tausayawa yabud’e baki zaiyi magana kafin yace komi Hamut yace 

” bro yanzu shikenan nida matata sede kallo nashiga uku kenan nazama rabin namiji Hamidat zata haqura tazauna dani ahaka ? ” duk cikin kuka yake fad’in haka girgiza kai Hammat yashigayi yace ” haba bro nasan kayarda da qaddara mai kyau dakuma marar kyau nasani zuciyarka batada qarfi musamman akan waccan yarinyar to amma dan Allah kasaka zuciyoyin iyayen mu susamu  karfi inaso kadaure kanuna kamar bakadamuba sosai hakan zaisa Ammi tasamu karfin zuciya kukafa takeyi ayanzu haka shiko maimartaba duk irin dauriyar shi amma tashin hankali seda yabayyana acikin idanun shi karkadamu zaka warke in sha Allah zamuje China muga doctor komu d’akkoshi yadubaka kaji  ” jin haka yasa Hamut saurin share hawayen shi yace 

” in sha Allah zannunamasu Ammi kamar banida damuwa kuma inada tabbacin Hamidat bazata gujeniba koda majnun nazama nasan zata zauna dani cikin soyayya dakulawa ” ajiyar zuciya Hammat yasauke yace ” to Allah yasa haka ” dede lokacin su Ammin sukashigo ganin su yasa Hamut tashi zaune dukda irin ciwon da kasan mararshi keyi amma haka yatashi yazauna sabida su Ammin suga kamar babu matsala saurin zama Ammin tayi tarungumoshi cikin damuwa tana zubda hawaye sosai zuciyar Hamut tasake karyewa amma yayi saurin sakin murmushi yace 

” haba Ammina nifa banajin ciwon komi kumani maganar doctor bata d’agamin hankaliba sabida nasan Allah shikeda komi kuma in sha Allah zanwarke nan kusa kude kuyimin addu’a Allah yasa nacinye wannan jarabawar muje gida yanzu banason kowa yasan matsalata a cikin masarautar mu bayanku nida kaina zan fahimtar da Hamidat kuma na tabbatar zata fahimta ” 

Ajiyar zuciya Ammin tasauke shima Sarki jabir haka hajiya  Fulani kuwa wasu hawayenne sukasake gangarowa daga idanunta shiko Abba girgirza kai yayi cikin tausayawa itako momcy tuni tabar cikin hospital din dede lokacin doctor yashigo  duban fuskar Hamut yayi sosai yayi mamakin yadda yaganshi kamar babu damuwa atare dashi kafin doctor yayi magana Hamut yace 

” doctor kabani sallama muje gida banajin ciwon komi yanzu ” kallonshi yayi sosai yace ” kabari zuwa wani lokaci kasake samun sauqi sosai ” doctor yanarufe baki Hamut yasakko daga gadon din sosai yaji mararshi ta amsa yamutsa fuska yayi sannan yace ” bazan iya qara koda 5 minutes ba a cikin wannan hospital d’in koda nazauna babu abinda zaka’iya yimin tunda kace bazan warkeba idan kaga zaka’iya kazo gida kaga yadda jikin nawa yake daga haka yafita ranshi a’bace yana fita yabud’e motar Hammat yashiga wasu irin hawaye yaji mazu zafi sosai suna zubowa cikin idanunshi  cikin sauri Hammat yafito shiga motar yayi driver yaja cigaba da kwantar mai da hankali Hammat yayi magungunan shi doctor yabamasu Ammin suka taho 

Itako Momcy tana fitowa tanufi masarautar kai tsaye tanufi part d’in Hamut d’in tana shiga tashiga kallon ko’ina tabbas ankashe dukiya cikin wannan part d’in Hamidat dake zaune cikin qawayenta cikin alhinin rashin lafiyar Hamut d’in tataso rungume Momcy tayi tasaki kuka tace ” Momcy dan Allah kikaini wajan Hamut naganshi banaso yamutu in…….” Kafin taqarasa Momcy tarufemata baki tazata zuwa bedroom zaunar da’ita tayi bakin bed tadubeta sosai tace 

” ke Hamidat garama kibar wannan kukan dan kam yazama dole kurabu keda Hamut ahalin dayake ciki yanzu babu wata macan dazata iya zama dashi ni nasan yanayin ki banzama daga cikin iyayennan wa’inda  basusanin yaya rayuwar yaransu takeba nasan abinda zaki’iya jurewa dakuma Wanda bazaki’iya to tabbas bazaki iya jure zamada Hamut ba ” 

Sosai Hamidat taji kanta yad’aure sosai tadubi Momcy tace ” towai maiye matsalar dan Allah kisanar dani ” batare dajin wata shakkaba tasanar da’ita komi kuka Hamidat tasaki tace ” kungani ko gashi kun tabani magunguna harma  sunwuce qa’ida nashiga Uku ” 

Miqewa Momcy tayi tace ” ina sauraranki naji wace shawara kika yanke idan kince bazaki zaunaba to ina bayanki ???? idan kuma kikace zaki zauna tobana tare dake ” 

Daga haka Momcy tafita kasa miqewa Hamidat tayi sabida tsananin razana da lamarin tana nan a zaune tsayin lokaci har su Hamut suka qaraso cikin tamke fuska Hammat yadubi qawayen Hamidat yace 

” to ay yakamata kutafi ko bakuji anfara kiran sallar magrip bane kuje driver yakaiku gida bayan Hamut yashiga cikin bedroom Hammat yakira Ansar yace yaje part d’in shi yad’auki kud’i yabama qawayen Hamidat hakan kuwa yayi suna qoqarin shiga motar yabasu sosai sukayi mamakin yawan kud’in bin cikin bedroom d’in Hamut yayi da kallo sabida yadda akatsara komi duban saman bed din yayi wasu had’addun kayane aka’aje mishi da’alamu wa’inda zaije wajan d’aurin auran dasune saurin kauda kanshi yayi yashiga toilet yayi wanka yayi alwala yafito cikin sanyin jiki yashirya cikin bedroom yayi sallah har issha’i sannan yad’auki kayan yasaka woow gaskiya yayi masifar yin kyau wayyo Allah ahaka kamar babu wata damuwa ajikin shi  fita yayi yanufi bedroom d’in Hamidat zaune take tarasa abinda yakemata dad’i jin kamshin turaranshi yasata saurin d’ago idanunta tazubasu kanshi take taji jikinta yadauki shauqi buqata tafara taso mata 

Qarasowa yayi gareta yasaki murmushin qarfin hali yace ” my B sorry seyanzu kike ganina haka Allah yaso zomuje wajan iyayenmu susakamana albarka idan mukadawo zansanar dake komi nasan bazaki barniba koda girman qaddarar yafi haka ” ta’be baki Hamidat tayi tace ” basekace komiba nasan komi amma gaskiya banajin zan’iya jurewa zanbada d’an lokaci qalilan idan naga babu labari to kam zannemar ma kaina mafita ” sosai Hamut yaji wata irin faduwar gaba sabida baiyi tsammanin Hamidat zata’iya furtame hakan ba 

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button