NOVELSWASA FARIN GIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

WASA FARIN GIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

WASA FARIN GOIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

????°•° WASA FARIN GIRKI °•°???? {cigaban gidan gandu}

????1~2????

????sameemah point of view????

Inajin duk abinda baba umaru yake fada akan wai na maida komai ba komai ba, kuma nayi tawakkali,saidai da yasan abinda nakeji a cikin raina a lokaci da bayyi gangancin yin wannan furucinba,dan ji nake kaman na sha’keshi yah daina motsi dan haushi.
Duk da gargadin danayi masa amma bai jiba sai ma cigaba da yayi da cewar,
“Nasan Har yanzu kina jin haushi da kuma shiga yanayin damuwa saidai ina so nasanar dake cewa,hakan yah kasance a zanen kaddararki yahke,sannan ni nacika alkawarine na matata hajara dana dauka,wanda tah bani kafin tah koma ga gidan gaskiya”
Saurin juyowa nayi na kalleshi jin yace wai wasiyyar ummah tah ce da ta bashi kafin ta rasu,kenan dama abinda ta fadawa baba umaru kenan ranar da ta ce mu fita tana shirin mutuwa,wannan tambayar ni kadai nayiwa kaina amma kuma banida amsarta.
Tashi nayi domin fita a dakinnasa dan a halin yanzu bana bukatar abinda zai hadani da wani ma tukunna,dan na gano duk tsawon shekarun danayi a rayuwata a cikin duhu kai da jahilcin rashin sanin mai yake faruwa nayi ta dukka.
Dakinmu na nufah koba komai naji dadin rashin ganin mutane a gidan domim kowa yah watse bayan kwana uku da biki.
Wanka nafarayi badan nasoba dai dan yanda naji jikina yana hamami,rabona da wanka tun kwana uku da suka wuce.
Kayan inna rabi nagani a gefen nawa kayan da alamun anan take zaune kenan tunda aka daura auren,kallon dakin nakeyi wani kululun bakin ciki yana cina a zuciyah,nayi niyyar gyarashi na zauna ni kadai ashe nima so suke su fitar dani a cikin gidan.
Duk da cewa yanzu ba wannan ne a gabana ba,burina shine na san mai yake faruwa tsakanina da sameer dan yamzu nasan shidin ba jinina bane tunda aka daura min aure dashi.
Kuma na dau alwashin nima bazanyi musu yanda suke so ba matukar basu fadamin mai yake faruwa ba.
Dukkan gidaje guda ukun na amare babu wanda yayi wani doki da zuwan amaryar tasa,saboda duk abinda yake mararin zai samu daga wajen ta daren farko dama ya riga da ya karba a waje tun da dadewa,daya kuwa ma bazawara ce dan haka baya bukatar yin wani rawar kafah.
Zainab ce tah kalli yunusa wanda yah ke kokarin saka kayan aikinsa na yansanda zai fita.
“Yanzu dan tsabar rashin mutunci irinna maza,daga kawoni koh satin amarci banyiba kace min zaka fita wani aiki,kuma itama waccar uwartaka hadda cewa yau nice dayin tuwon gidannan?,,t
Duk maganar da takeyi ta rike wani dan karamin kunkuminta mai kama da muciyah tana jijjiga shi,amma yunusa bai kukataba kaman tana magana da dutsi,sai ma cigaba da gyaran takalminsa da yayi.
“Yanzu yunusa inaa magaan amma kaaman ka bawa banza ajiyata,toh wallahi tun wuri kaje ka fadamusu ba zaman yi musu tuwo nazo yiba,toh in ma tuwonne haka kawai daga zuwana koh sati banyiba har za’a dameni da nazo nayi aiki,saikace an kawomusu jaka koh?,toh wallahi bazan yiba nikam”
“Ashe kuwa kema bazaki ciba,kuma ninan da kika ganni aradun Allah yau bazan sayo miki gurasaba,dan tah jiyama saida nayi bashi na sayo,kuma tunda na rakaki kwanan uku ai yah isheki koh,dan haka koh ki dafa su baki naki,ko kuma kice bazaki dafaba ki zauan haka kalass,danni kam bazanje nace musu ke ba jaka bace,amma tunda kina ganin sudin jakunai ne basu da iyaye koh kuma suma basuyi amarcin ba sai kije ki fada musu”
Yana gama kawo nan a zancen sa yah dauki hukarsa yayi gaba kaman ba shine mai daukin auren ba kwana uku da suka wuce.
Ajiyar zuciyah zainab tasake mai cike da takaicin abinda angonnata ya fadamata,dafe hannunta tayi akan goshinta dayan kuma ta rike kunkumi,abin duniyah duk yah fara isarta tun ba aje ko ina ba.
Ganin ba sarki sai allah ne yasata fitowa daga dakinnata ta nufi sashen surukar tata domin gaisheta.
Sun daga nesa take jiyo masifarta da babbar surukarta wanda duk cikin su tafi yi mata rashin mutunci saboda halinta na sanyi da rashin magana,
“Dallah can ta shi Kuban waje,dan mijinnaki yakawo kudi sai akace kuma a baki kiyi yanda kika dama dasu,wato dan baku kuke nemowa ba kuma zaune saidai kici kusha sai kuma kashi a masai,toh bazan bada jaka biyun ba,wazobiyah (hamsin)ga tanan ki sayo masa ja da yalo(tetracycline),yasha,ba duk ku kuke jawo gudawar ba,ko ina mutum yah wice banda kukdaje da wari babu komai,duk kun cika gida da kazanta”
Daga kai tayi tana kallon zainab wanda ta iso wajen ta zuba mata idanu sai masifah rakeyi babu full stop bare kuma comma,
“Ke kuma miye kikayimin shekeke akai kaman wata wanda tasaka wandon karfe iyee”
Saurin tsugunnawa zainab tayi tana jinjina masifa irin ta,inna laraba.
“Inna Ina kwana”
Saida ta yahtsina fuska kaman bazata amsaba kafin tace,
“Lafiyah,nikuwa kawuna(yunusa),yah fadamiki zancen yau zaki dora tuwon dareko,dan in bai fadamikiba toh bari ba nanata miki,yau kece da ciga magirka,dan kowacce yarknyah idan aka aurotah toh kwana uku takeyi saikuma tashiga layin dafa abinci,dafatan kin fahimta”
Saurin daga kai zainab tayi kirjinta yana bada lugufen duka,bata tsammaci abin haka yakeba sai gashi duk masifarta da raininta ta kasa yiwa inna laraba musu,sai ma wata karkarwa da jijinta yah debi yi………hmm muje zuwa.

Kwass kwass kwass kakejin karar takalimi mai tsini yana sakkowa daga kan beni.
Hajiyah mairoce ta sha wasu arnan kaya ga kuma sarkar gold a wuyanta,tun daga bakin kofa salma ta kafeta da ido ganin irin shigar da matar tayi da kuma itah kanta tsadar suturar.
Wannan shine kallonta na farko da hajiyah mairon,dan tunda yan gidansu suka kawota suka tafi koh wata halittar bata sake gani tah shiga sashenta ba sai mai kai mata abinci kawai,bare kuka uwa iba mijinnata rabinta dashi tun hirar dasukayi lokacin ana gobe daurin aure,sai kuma aikan da akayi mata akan maigidan yana kiranta sashen uwar gidan.
Saida tah gama jijjuyawar ta kafin tah dawo kujerar da take facing salma tah zauna,wani kallo ta ke zifanta dashi na zaki sani yarinyah,tun kafin wani a cikinsu yah yi magana sallamar su sameerah da umaruje ya jiyarci dodon kunnesu.
Ba laifi kam sameerah tayi shar da itah na kyallin amare,sai murmushi takeyi,a kasan kujera suka zauna,sameerah har wani sunne kai takeyi itah ga mai suruka.
Dauke kanta daga kallon salma tayi ta miyar kan sanyi zuviyar tata da kuma matar da suka shigo tare,
“Ina kwana mom”
“Lafiyah son yakk”
“Normal mom,yah abokiyar zamanki?”
“Hmm gata gaka ai,saika tambayeni itah,ko duk aurenne yasaka ka haka”
“Ahah kawai na tambaya ne”
Itama sameerah ganin sun gama gaisawa ne yasakata cewa,
“Ina kwana mom(uhmm a dole anji wani yah fada,duk da halin bakin cikin da salma take ciki saida taji kaman tah tuntsire da dariya)”
“Lafiyah”
Daga haka hajiyah mairo bata sake kallon inda sameerah take ba bare kuma salma wanda dama tunda suka zo wajen bata kulata ba,sai cigaba da magana da sukayi da danta.
“Lah my son nikuwa yah tafiyah Dubai dinanan ne,yakamata kaje karisa karatunka sananan idan ka dawo maganata tana nan”
“Mommy amma da sameerah zamu tafi koh,tumda wata shida zanyi acan bandawo ba”
Wani sihirtaccen dadine ya jiyarci zuciyar sameerah jin inda zasuje ita da mijinnata,har ta fara hasasowa irin rayuwar dazasuyi acan din,bazama ta yarda su dawoba idan suka tafi can,maganar hajiyah mairoce tah katseta daga hasken tunanin da takeyi zuwa na duhun bakin ciki.
“Bada it ah zaku tafiba kai kadai zakaje,so kake ka takura kanka ka kasa more jin dadinka,da budurwace ma ko kuma irin matanann na nuna wa sa’a sai ku tafi,amma banda wanda bata san komai ba kam tayi ta baka kunyah.
Sannan maganar mu na auren ku da Suhaila yana nan sannan itama ta dawo Nigeria lokacin dazaka dawo,nariga na yanke hukunci nan da sati daya zaka tafi”
Emotions guda uku ne yake yawo a cikin falon,umaruje kunyah ce ta kamashi,dan baiso mamar tasa tayu maganar auren da zayyi a wajen ba,itah kuwa sameerah tunda uwarta ta haifeta,da kuma duk irin tujarar da suke yiwa kansu a gida,bata taba jin disgawar da akayimata mai ciwo kaman wannan.
Yayinda salma a bangarenta kuwa dadi yah kaman yah kasheta jin yanda kishiyar tata take cakawa sameerah magana mai zafi.
Kowa dawowa yayi cikin hankalin lokacin ma har ummaruje yayi musu sallama yah tafi wajen abokanansa.
Suma tashi sukayi zasu tafi hajiyah mairo tah tsaida su tareda cewa,
“Bangama dakuba ai,inaso na sanar daku cewa na sallami dukkan yan aikin gidannan,daga yau kune zaku dunga yin komai na gidannan,na abincin mu da kuma na wanda ake fita dashi sadaka,ke zaki iyah tafiyah saboda ina da iko dake,ke kuma ki jira wanda yah kawoki yah tabbatar miki kiji da kunnenki,duk kuma wacce taga bazata iyaba toh yau basai gobeba zata koma gidan tsofi”
Har salma tayi niyyar juyawa tayi mata musu sai taga tamkar zakine a gabanta yake bata umarni,hakan yasa jikinta yayi sanyi tah koma ta zauna,duk da bata ce komaiba.
Itakuwa sameerah rarrashin zuciyar ta tayi ta bar sashen,zuciyarta sai bugawa takeyi tsoronta dayah kar asirin da take dan takama da shi ya karye ta,shiga uku gashi yamzu da gaske ta fara son umaruje aranta tun daren farkonsu yah kama zuciyarta.
Basu fi minti uku a zaune ba bayan tafiyar sameerah alhaji bala ya fito daga dakinsa yana gyara hannun rigarsa,wajen hajiyah mairo yaje yah zauna yana wani yake hakorah.
“Afuwan uwar gida sarautar mata,na barki a zaune kina ta jirana koh”
Saida hajiyah mairo tayi wani rausaya da kuma kallon salma ta gefen ido wacce tah zama tamkar kungi ganin koh inda take alhaji bala yayi bare kuma yayi mata magana,”anya kuma shine koh kuma wani ne daban”tah fada aranta.
“Babu komai honey kawai dai kasaka ni zamane har nakusan awa guda,nayi zaton koh kaki wankanne irin jiyah,ina shirin tashi naje na tayaka kuma sai gashi ka fitoma”
Dad’i kasheni haka alhaji bala yaji kaman an saka shi a cikin lambun soyayya.
“Ahah ahah karki damu gimbiyah mai tafiyah da ragamar rayuwata ,ina na isah nasakaki aiki bayan jiyah na saka ki,menene yake faruwa?”
“Sakonna na umarnin daka kafa gidanna nake so kasanar da matarka dan taji da kyau,karma ta daukeshi da wasa”
Kallonta alhaji yayi rai a bace kaman yaga kashi mai wari,
“Toh ma saina sake fada mata,ai duk abinda kika zartar dadai ne kawai yin biyayyane aikinta idan tanason zaman gidan”
Baki salma tasake tana kallonsu,musamman ma yanda alhaji yake wani cuccusuwa a jikin hajiya mairon,kaman wani mai shirin shan nono koh kuma mai kokarin komawa cikinta,koh kunyah basaji sai ka ce wasu yara.
Cikin dashashshiyar muryah irin ta wanda yashaki bakin cikinnan salma tace,
“Toh idan kun gama bani aikin dazanyi zan iyah tafiyah”
“Eh kina iyah tafiyah,kaima alhaji yah kamata ka tafi aiki haka,nima fita zanyi yamzu”
“Angama Ranki yadade”

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button