NOVELSWASA FARIN GIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

WASA FARIN GIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

WASA FARIN GOIRKI COMPLETE HAUSA NOVEL

Lambar asusu:3131951977
Lambar waya:09035784150

Dan allah karki karanta koh karka karanta baka biyah kuɗin ba,domin akwai hakkina na naira jaka ɗaya(200) a kaknka koh akanki idan baki biyaba kike koh kake karantawa.

????Sadi-Sakhna________✍????????

(¯’•.¸,¤°’✿.。.:քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ.:。.✿’°¤,¸.•‘¯)

????•°• WASA FARIN GIRKI •°•???? {cigaban gidan gandu}

????39~40????

Hannu ta dagamin alamar na zo,cikin sanda na kaman wanda kwai ya fashemin a ciki na isa wajenta na durkusa.
Hannuna ta kama dukka biyun kafin tace,
“Duk da bansan wane hali kike cikiba amma nasan abin akwai wahala,saidai ina so ki sani duk da halin dakike ciki kar ki bari wuya ko kuma wani yanayi ya hana ki kusanci zuwa ga ubangijinki,tabbas nasan akwai abinda yah faru a daren dana badake ga ummanki hajara,amma nakasa koda abinda nayi lokacin barekuma mai ya faru,abinda nasani kawai shine idan nayi kokarin tuna mai yah faru nakan ji duk kaina ya juye ina kokarin fita daga cikin hayyacina,bansna mai ya faruba kwata kwata,har shikansa Abdulwahab bansan mai ya faru dashiba.
Sameemah muna cikin jarabawa dagani harke amma karki yanke kanki daga neman sauki a wajen allah ko kuma neman agajinsa,a duk inda kika samu kanki ki kasance mai mika lamarinki ga allah,a cikin dad’i harma da cikin wahala”
Wani irin rauni nakeji zuciyata tanayi lokacin da nake sauraron abinda yake fitowa daga bakinta,hawayen danaga yana zuba a cikin idonta ne yasani rungumeta a jikina kaman kar mu rabu.
“Nagode ummee inshaallah zanyi kokarin yin amfani da abinda kika fada min”
“Kici gaba da addu’a komai zaizo da sauki watarana sai labari inshaallah”
Daga haka tacigaba da yin lazimi ina zaune a gefenta,zaman wajen kadai tayarmin da hankali yakeyi amma haka dole na daure saboda naga farincikin a kan fuskarta.
Ranar na biyar da zuwana gidanne da rana ina kwance a kan gado naji ana kiran sallah,abinda ummee ta fadaminne yadawo min cikin kaina,saidai duk da haka ban taba gwada yin sallahr ba koda wasa,kenan ban dauki maganarta da kima ba koh,kuma ban kasance Y’a tagariba,bar batun wannan ya tsakanina da mahaliccina to,wanda shiya halicceni amma kuma nakasa bautamasa tsawon shekara da shekaru saboda bin umarnin wasu shedanu can,yanzu idan na mutu mai zancewa ubangijina,shin hujjar danake da ita na sun hanani yin ibada nikuma ban yi wani kokariba ta isa kareni daga ranar karshe??.
Wani saurin tashi nayi daga kan gadon hawaye na zuba a cikin idona,yayinda jikina yake rawa kaman an jonamin spring,tabbas akwai kalubale a gabana ba kadanba.
Hangar vandakin na nufa,duk da baraxanar bugawa da zuciyata takeyi amma haka nayi biris da ita na fara alwalar,yau na dauki alwashin gwada yaki da duk abinda yake cikin jikina.
Fitowa nayi na dauki hijabi a kan gadon ummee wanda take sallah dashi na saka,kafin na shimfida sallaya.
Tun daga hawa sallayar nakejin kaman nadora kafa akan wani abu mai zafi,amma haka na jure ina runtse ido.
Kabbara na tayar wanda ina ga ban tabsyin guda uku ba tsawon rayuwata,abinda yasa ban mantaba saboda anayinta a masallatai ne kullum.
Suratul maryam bakina yakama nafara karantawa,daga iyah aya biyu na yanke nayi ruku’u,ina jin kaina yana barazanar fashewa amma ban fasa abinda nakeyi ba,lokacin danakai sujjadane naji wata murya tansmin magana cewa,
Hakika kin Kaimu bango a yau,kina tunanin zamu sallamar da ruhin da anriga an yi mana kyautarsa,to hakan bazai yiyuba,daga yau zamu kasance mune zamu tinga control din gangar jikinki har zuwa nan da wata uku lokacin da zamu mallakeki ki rike matsayin dayake jiranki,idan kuma ba haka ba dole mu hallakar dake,yanzu ma dolene ki karbi hukunci
An gama fadar hakan naji wani zafi da kuma kara ya ratsa cikin kaina,hakanne yasa nima na zunduma tawa karar danima bazan iya zure azabarba.

????Sameer a madubin gani????

Yau kwanan sameemah biyar a gidan mahaifiyar ta, ko waya bamu tabayi ba duk kewarata ta isheni,duk da ba komai ne yake shiga tsakanimu ba amma ganinta kawai a cikin gidan yakan sa naji nutsuwa a tareda ni.
Hakanne yasa na yanke shawarar dama zanje wajensu ita da farouq sannan na gaishe da hajiyah maryam.
Hanyar gidannasu na nufa har na isa gidan,a falon na samu hajiyah maryam tana aiki a system tasaka glass,Murmushi tayi da taga nine,
“Lahhh ango ya biyo sawun amarya kennan,da alama kana kewar iyalanka,ya d’aya y’ar tawa take ita da mai sunan yaya ta”
“Lafiyansu kalau hajiya”
“Mutuniyar taka tana ciki bari na kira maka ita ko”
Dan sosa keya nayi dan dama hakan nakeso naji tace.
Ta ta shi kenan da niyyar shiga ciki,mukaji karar sameemah daga cikin daki,da alama wani abune yake faruwa da ita,da sauri dukkan mu mukayi dakin da muryar take fitowa.
Akan sallaya muka sameta duk gaban hijabinta ya baci da jini gashi dama mai haskene,saurin tallafarta mukayi nida hajiyah maryam muka nufi hanyar kofar gida wajen mota.
Da sauri muka turata zuwa dakin taimakon gaggawa,inda ummee tayi saurin sanja kayanta a office dinta ta shiga wajenta.
Muna nan tsaye zuwa lokacin kowa yazo yan uwa domin labari yah isa garesu.
Ummee ce ta fito daga dakin amma babu alamar nasara a fuskarta,alhaji musa ne yayi saurin tambayar mai yake faruwa,amma cewa tace bata farfadoba cikin karamar magana.
A zaune muke dukkanmu a office dinnata,
Dagowa tayi ta kallemu fuskarta dauke da damuwar halin da y’ar ta take ciki,
“To yanzudai bamusan mai yake faruwa ba,dan duk wani gwaji munyi amma babu abinda muka gani,gashi har yanzu bata farfado ba tukunna,saidai mu tsaya mujira mai zai faru.
Wasu sun tafi gida amma ni da hajiyah Fatima da kuma ummee a anan muja zauna domin ganin mai zai kasance,baba umaru ma an aika masa suna zuwa shida inna ramatu wanda tace zata zo ta gani saboda munafurci.
Ni kadaine xaune a gefenta akan kujera na kifa kaina akan gadon,can wajen misalin karfe dayan dare naji kaman hannunta dana rike yana motsi kamar a mafarki.
Saurin bude idona nayi na ga dukkan jikinta yana jijjiga,tashi nayi na tsaya akanta,a lokacinne naga idonta ya bude wanda babu alamar farar kwayar ido bakine sidik.
Wani mungun murmushi tayimin kafin tayi saurin tashi ta kama wuyana da wani irin karfi ta mannani a jikin bangon dakin,dariya taci gaba dayi da bakinta wanda yake bakikkirin,wuyana ta saita tana niyyar cizona ,har na lumshe idona na saddakar,saboda duk karfin mutum bazai iya kwacewa da wannan rikon ba,can kuma sai naji ta tsaya cak kuma tana huramin numfashi a wuyana,kaman wanda take yaki da wani abu a cikin ranta.
Karar budewar kofa naji dama na danna alarm danaga tana jijjiga.
Ummee ce ta shigo dakin wata nurse tana biye da ita a baya,
Jefar dani tayi a kasa kamar shamfora tayi kan ummee da wani sauri wanda ba nata ba,tsaywa tayi a gaban ummee tanayi mata kallon kaman yaro yana son gane mahaifiyarsa,har ta kama ummee sai kuma ta saketa da sauri ta kama wuyan wacce suka shigo da ita ta gatsa da karfi,ihuu ta saka na azaba kafin ta durkushe akan gwiwoyinta,daga baya kuma ta fadi summamiya.
Hanyar waje tayi tana nufin fita nayi sauri na tashi da dan karfin dayayi saura ajikina naje bakin kofar na tsaya inda zata wuce,
Wani kallo takemin na ranta ya baci amma ban matsa daga kofar ba,saima wayata dana ciro a cikin aljihuna na kira alhaji musa na fada masa ya taho da malami.
Tanajin abinda nafada tayi kukan kura da sauri ta nufi inda nake da niyyar bigeni ta wuce,saurin rike kunkuminta nayi tareda yi mata magana a kunne.
“Ki tsaya sameemah ki saurareni,karki bari koma menene yayi iko dake,kiyi kokarin yin abinda ya dace,ke jarumace sameemah kiyi amfani da jarumtarki,nasan kina jina kiyi kokarin saita kanki,nasan zaki iyah,kidaina cutar da wanda basu da laifi karki zama wacce zata kasance abar tsoro a cikin mutane”
“Ni ba mutum bace ni nakasance wata halittace daban,sannan zanyi abinda irina sukeyi,kadaina kusanto inda nake,inaso idan ka ganni ka gudu saboda ni dododanniya ce abar gudu ga kowa”
“Keba dododanniya bace,ke matata ce kuma masoyiyata abar sona,bazan taba daina sonkiba,sannan idan kina son ki fita ki cutar da mutanen to ki fara taina sameemah,niya kamata ki fara hallakawa saboda nine na bar rayuwarki lokacin da kike bukatar wani a kusa dake,sannan na kasa bincikar halin da kike ciki har sai da abin yafi karfinki,dan haka ki fara ta kaina”
Duk da har yanzu yanayinta na wani abune daban amma hakan bai hana na gano alamar sararawa ba a jikinta,zuyawa tayi ta kalli ummee wanda tayi suman tsaye tana kallon nurse din ta take kwance kaman gawa jini yana fita daga wuyanta.
Dago da idonta tayi ta dorasu akan y’ar tata wanda idonta yayi baki,hakoranta sukayi tsayi har da gashinta.
Baya ta fara ja da kadan kadan tana kiran sunan allah,wanda hakan yasa sameemah yin gurnani irin na namun daji tana rike da kunnuwanta. Ganin ummee bata daina salati bane yasa sameemah tayi kanta da niyyar shaketa,saurin riketa nayi ta baya dakyar,
“Dan kinga y’ar ki tana nuna tirjiya akan karmu tabaki shine har kika samu ikon fadamana wannan kalmar?,kece sanadiyyar sakata yin abinda mukafi tsana wato sallah,shine kike cigaba yanzu ma dan kinga mun kyaleki?”
Tana cikin maganar ne mukaji alamar tahowar wani,daga bakin kofa,hankalin ta ne yayi wajen da sauri,saidai tana isa wajen ta dawo da sauri tana buya a bayana,wani malamine da hiraminsa sai kuma alhaji musa shida baba umaru.
Karatu malamin yah fara tun daga shigowarsa,wanda hakan yasa sameemah ta zube a kasa tana wani irin karaji,itama ummee zubewa tayi tareda fasa kara mai karfi.
Dukkan mu abinne ya kidima mu muka fara kallon kallo.
Cigaba yayi da karanta wasu ayoyi da kuma addu’a harna tsawon lokaci kafin sameemah tai shiru kaman ta sankame.
Cikin sauri yace a daukesu a biyoshi yanzunnan.
Nine na ciccibi sameemah yayinda wasu nurse suka fita da wacce sameemah tayiwa rauni,wasu kuma suka sauki ummee zuwa cikin mota.
A hanya alhaji musa yayiwa hajiyah fatima waya ta samemu a gidan malamin.
Muna zuwa gidan ya bude wani daki mai dogon lungu,saida mukayi tafiya kafin muka zo wani daki,shiga mukayi ina dauke da sameemah a hannuna.
Wata igiya ya dauko siririya doguwa daga cikin wata kwarya mai ruwa ya daura a hannun sameemah kafin ya daura a jikin wani karfe dayake wajen.
Ajiyeta nayi a kasan wajen ya karisa daureta a wsjen,tausayinta ne yakamani sosai,hakika taga jarabawa dayawa,yanzu kuma wannan halin zata kuma shiga. Kallon malamin nayi kafin nace.
“Malam wannan igiyar zata iya tiketa kuwa,tana da karfi fa sosai”
“Hmm nasan karfinta,amma kai baka san karfin wanna igiyar a gun shedanu ba,duk da bansan wane irin shedanu ne a jikinta na haka ma bansan iya karfinsu ba,amma nasan bazata iya tsinka igiyar nan ba,yanzu dai muje tukunna sai anyi binciken wane irine kafin a fara magani,saidai naga kaman kuruwarta bata jikinta na tsawon shekaru,da wata kuruwar daban take rayuwa,dan haka dawo da tata kuruwar zai bada matukar wuyah”.
Daga haka inaji ina gani babu yadda zanyi muka tafi muka bar sameemah a wajen,wanda tayi summ kaman sankararriyar gawa.
Komawa mukayi daki inda hajiya fatima take yiwa ummee fifita,itama a kwance take kaman gawa.
Wucewa malamin yayi zuwa wani daki ya dakko wani kokon ruwa yah fesa mata,ajiyar zuciya ta sake kaman wanda aka sakawa sabuwar rayuwa.
Tashi tayi zaune kaman mai cutar mantau said kallon mu take,kokon hannunsa yah mika mata ,hannu tasa ta karba kaman mai karbar umarni tackai bakin ta,kurba biyu tayi mika masa abinsa,saboda wata atishawa da ta turnuketa.
Kallon muyayi kafin yace,
“Da alama an goge mata wani bangarene na tunanin ta a shekarun baya,kuma yana da alaka da abinda yaje jikin yarinyar”
Aikuwa bai gama rufe bakiba ummee ta fashe da kuka kafin takama rigar hajiya fatima ta tike gam tana cewa,
“Yaya fatima na tuna abinda yafaru,wallahi na tuna,yaya fatima Abdulwahab ya cuceni yah yaudareni ya zalunceni nida Y’a ta yasakamu cikin tsaka mai wuyah,bazan taba yafemasa ba har numfashi na na karshe ya fita daga jikina. Bazan yafe masaba sai anyi masa hisabi nida shi,uwa uba kuma sameemah ya cuceta fiyeda abinda baki zai yah fada yayi mata abinda ko a tarihi said an tona kafin a samu.
“Meyafaru maryam ki sanar damu,ko yamzumma baza ki iya fadaba kaman sauran lokuta a baya”
“Yanzu zan iYa fada,natunna komai duk abinda yah faru babu wanda ban tuno ba yanzu zan fadawa kowa mai yah faru,koda kuwa abinda yah fada gaskiyane cewar idan nafada abakin raina,to saidai na mutun amma sai na fada kowa yah ji…….toh fah????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button