SARAN BOYE COMPLETE

*_“Ma’anar Shaidawa Lallai MUHAMMADU MANZON ALLAH ne:_*
_Ma’anar shaidawa lallai (Annabi) Muhammadu
MANZON ALLAH ne shi ne a yi masa biyayya cikin abin da ya umarta, da gaskatashi a kan abin da ya ba da
labari, da nisantar abin da ya hana kuma ya yi tsawa a kansa, kuma ba za a bautawa ALLAH ba sai da abin da ya
shar’anta._
Tabbatar Da Shaidawa Lallai MUHAMMADU MANZON ALLAH ne:
_ MANZON ALLAH ne: Shaidawa lallai (Annabi) Muhammdu Manzon
ALLAH ne tana tabbata ne da yin imani da cikakken yaƙinin cewa lallai (Annabi) Muhammdu tsira da amincin ALLAH su tabbata a gare shi bawan ALLAH ne, kuma Manzonsa ne ya aiko shi zuwa ga Aljanu da mutane gaba ɗayansu, kuma lallai shi ne cikamakin Annabawa da Manzonni, kuma shi Annabi tsira da amincin ALLAH su tabbata a gare shi bawa ne makusanci a gurin ALLAH ba shi da komai daga siffofin ALLAH, kuma (wannan shaidar tana tabbata ne) da yi masa biyayya da girmama umarninsa da haninsa, da lazimtar
sunnarsa a baki, a aikace, kuma a ƙudurce._
ALLAH ya ce: “Ka ce: ya ku mutane lallai ni MANZON ALLAH ne zuwa gare ku gaba ɗaya” (A’araf: 158).
Kuma ya ce: “Ba mu kuma aiko ka ba face zuwa ga mutane baki ɗaya, kana mai gargaɗi da bushara” (Saba’a: 28).
Kuma ya ce: “(Annabi) Muhammadu bai kasance uban ɗaya daga mazajenku ba, sai dai (shi) Manzon ALLAH ne kuma cikamakin Annabawa” (Ahzab: 40).
Kuma ya ce: “Ka ce tsarki ya tabbata ga Ua UBANGIJINA, ni ba kowa ba ne face mutum kuma Manzo” (Isra’i : 93).
Wannan (tabbatar da shaidawa Annabi Muhammadu Manzon ALLAH) ya ƙunshi al’amura kamar
haka:
Na farko: yarda da Manzoncinsa da ƙudurceshi a ɓoye cikin zuci.
Na biyu: yin furuci da haka da harshe a bayyane.
Na uku: koyi da shi da yin aiki da abin da ya zo da shi na gaskiya, da barin abin da ya hana na ƙarya.
ALLAH Maɗaukaki ya ce: “Sai ku yi imani da ALLAH da Manzonsa, Annabi Ummiyyi¹, wanda yake imani da ALLAH da kalmominsa, kuma ku bi shi don ku shiriya” (A’araf: 158).
Na huɗu: gaskatashi a kan dukkan abin da ya ba da labarinsa.
Na biyar: Mutum ya so shi sama da son kansa da dukiyarsa da ɗansa da mahaifinsa da mutane baki ɗaya; domin shi MANZON ALLAH ne, kuma haƙiƙa sonsa yana daga cikin son ALLAH, da so saboda ALLAH Haƙiƙanin son MANZON ALLAH shi ne yi masa biyayya wajen bin umarninsa da nisantar haninsa da
taimakonsa da jibintarsa.
ALLAH ya ce: “Ka ce: idan kun kasance kuna son ALLAH, to ku bi ni, sai ALLAH ya so ku, ya kuma gafarta muku” (Ali Imran: 31).
Kuma ANNABI tsira da amincin ALLAH su tabbata a gare shi ya ce: “Ɗayanku ba ya zama mumini har sai ya soni fiye da mahaifinsa da ɗansa da mutane gaba ɗaya” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi daga hadisin Anas ALLAH ya yarda da shi.
Kuma Allah Maɗaukaki ya ce: “Saboda haka waɗanda suka yi imani da shi, suka kuma girmama shi, suka kuma taimake shi, suka kuma bi hasken da aka saukar a tare da shi, to waɗannan su ne marabauta” (A’araf: 157).
Na shida: Ƙudurce cewa sunnarsa asali ce ga shari’ar musulunci, kuma ita sunnar kamar Alƙur’ni mai girma take (wajen dogoro da aiki da ita), saboda haka ba a saɓa mata domin hankali ya ci karo da ita.
Na bakwai: yin aiki da sunnarsa da gabatar da maganarsa a kan maganar kowa, da miƙa wuya zuwa
gare shi, da yin hukunci da shari’arsa da yarda da ita.
ALLAH Maɗaukaki ya ce: “Na rantse da girman UBANGIJINKA ba za su yi imani ba, har sai sun sanyaka mai hukunci game da abin da ya faru a tsakaninsu, sannan kuma ba su sami wata ƙunci ba a zukatansu game da abin da ka hukunta, su kuma miƙa wuya gaba ɗaya” (Nisa’: 65).……………✍
ZAFAFA BIYAR 2021
Hafsat miss xoxo????
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).????????
Mamu gee????
MIN ƘALB!!????????
Hafsat rano????
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!????????
Safiyya huguma???? SIRAƊIN RAYUWA????????
Bilyn Abdull????
SARAN ƁOYE????????
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka????????????????
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????
09033181070
????????????????????????????????????????
TEAM—-ZAFAFA BIYAR????????????????
ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????.
[5/18, 6:00 PM] +234 808 711 8630: LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana????????.
No. 29
………….“Na faɗaɗa maka muhimmanci kalmar shahada ne domin kasan addinin musilinci ba abin wasa bane, sannan bautama UBANGIJI shi kaɗai bashi da abokin tarayya shine cikakken imani. Gujema shirka babba da shirka ƙarama domin dawwama da tsira wajen bautama ALLAH shi kaɗai da tabbatar da soyayyar MANZONMU a zukatanmu wajibine. Zaka karɓi kalmar shaha yanzun nan Yahya, da ga haka ka tabbatar kabar kafircema ALLAH har abada, ka tsarkake ranka da zuciyarka cewa babu wani sarki sai ALLAH, ANNABI MUHAMMADU kuma MANZON ALLAH ne”.
Kai Yoohan ya jinjina a hankali, zuciyarsa na wani irin tsitstsinkewa, tsigar jikinsa na tashi batare da yasan dalili ba. Hakama jininsa gudu yake a cikin jijiyoyinsa da sauri-sauri. Wannan yanayin sai ya saukarma jikinsa da kasala da wani rauni da bai taɓa tsintar kansa a ciki ba.
Baba malam na faɗar kalmar shahada yana maimaitawa, suna kai ƙarshe sai kawai hawaye suka ɓalle masa tamkar an buɗe fanfo. Ya sakko a kujerar da yake zaune a hankali ya durƙushe ƙasa jikinsa na wani irin rawa. A matuƙar mamakin su baba malam sai gani kawai sukai ya kai goshinsa ƙasa yayi sujda.
Ɗan yatsa baba malam ya saka ya ɗauke hawayen da suka sakko masa gefen ido kaɗan. Hakama Abban Abdallah sai da hawaye suka cika masa idanu, sai jin wata irin ƙauna da soyayyar Yoohan ɗin suke tana nunkuwa a zukatansu. Kamar yanda shima ƙaunarsu ke sake masa ninƙaya a zuciya.
Koda ya ɗago da ga sujudar da yayi kamar yanda yaga baba malam yayi ɗazun sai kawai ya matsa ya rungume baba malam ɗin yana cigaba da hawaye. Sunja tsahon lokaci a haka kafin baba malam ya ɗagosa yana murmushi, yace,
“Yahya ina tayaka murna. akwai ayyuka sosai a gabanka. Amma kafin su yanzu zakayi wankan shiga musulinci”.
Cikin lunshe idanu dajin wata nutsuwa ta musamman Yoohan ya gyaɗa masa kai.
Bisa jagorancin baba malam Yoohan ya gabatar da wankan shiga musilinci, tare da tsaftace wasu najasosi dake jikinsa, kamar tarin gashin kansa, an ragesa, amma ba sosai ba, dan baba malam ya shaida masa barin gashi ado ne, sannan koyine da MANZON ALLAH (S.A.W), bama ason ayi aski tas-tas ɗin nan kai na ƙyalli. Yanke masa ƙunba. Duk da shi bama mutum bane mai tarata, tare da sauran abubuwan da suka dace su kasance a tsaftace ga ƙa'idar musilinci.
Bayan ya shirya tsaf cikin sabuwar suturarsa farar ɗanyar shadda tas, da taji ɗinkin da yay masa ɗas a jiki baba malam suka rungumesa suna sake masa marhaban da shigowa addinin gaskiya, sannan suka sake zama da shi a karo na biyu domin masa bayani akan SALLAH.
yanzu kam harda su Abba Musbahu suma sun shigo tawagar. Bayan an kawo musu breakfast sunci tare su biyar abin sha'awa. Bayyana muku irin farin cikin da nutsuwa da Yoohan ke ciki a wannan lokaci ɓata lokaci ne.
Shiru falon ya ɗauka duk suna sauraren baba malam dake zuba bayani cike da nutsuwa da ƙwarewar ilimi da sanin da ALLAH ya azurtashi da shi.
Yoohan! Sallah na nufin addu'a.
Amma a shari’ance ibada ce ma’abociyar karatu da ayyuka Keɓaɓɓu, da ake fara ta da kabbara a kuma rufe ta da sallama, sallah ita ce rukuni na biyu a cikin Addinin Musulunci bayan kalmar shahada, wato (ASH’HADU AN LA ILAHA ILALLAHU WA ASH’HADU ANNA MUHAMMADAN RASULULLAH) sai ita. kuma ita ce kashin bayan addini, saboda girmanta da matsayinta ALLAH bai aiko mala’ika da ita ba sai ALLAH Madaukakin Sarki Ya kirawo ANNABI (SAW) a daren Isra’i da Mi’iraji ya bashi ita. Yana daga girman sallah ambatonta da ALLAH Madaukakin Sarki Yayi sau hamsin da takwas (58) a cikin Alkur’ani, kamar inda yake cewa:
{وَأَقِيمُوا الصَّلَوةَ} [البقرة: 43]
Ma’ana: “Ku tsaida sallah”
{قُلْ لِعِبَادِيَ الَّذِينَ آمَنُوا يُقِيمُوا الصَّلَوةَ}[إبراهيم: 31]
Ma’ana: “Ka fada (Ya Muhammad S.A.W) ga bayina da suka yi imani su tsaida sallah”.
Da sauran wurare a cikin Alqur’ani da dama.
Annabi (SAW) yana cewa: “Bainar rajuli wabainal kufri tarkus salati” (Rawahu Muslim).
Ma’ana: “Tsakanin mutum da kafirci shine barin sallah”. Kuma ana umartar karamin yaro da yin Sallah tun yana dan shekara bakwai, kuma in ya kai shekara goma a doke shi in ya ki yi.
Sallah bata yiwuwa sai da alwala.