SARAN BOYE COMPLETE

Sai da Nu'aymah tai sallama Addah ta bata izinin shiga sannan ta shiga ɗakin. Tsaye ta isketa tana ninke abin salla alamar sallar ta idar. Ganin Nu'aymah na sharar hawaye yasa fara'ar fuskar Addah gushewa lokaci guda. “Lafiya Nu'aymah? mi akai miki?”.
“Babu komai Addah, Umm ce tace na kawo miki wannan”.
Sam Addah bata yarda da maganar Nu'aymah ba, dan haka tai shiru tana cigaba da kallonta kawai batare data amshi man-shanun ba. “Nu'aymah bana son shirme, faɗamin gaskiya mi akai miki?”.
“Addah wlhy aunty Kubrah ce ta dakar mata baki dan hawai tacemin ta tambayeta kina ina ta mata banza”. Hajarah dake shigowa ɗakin ta bama Addah amsa.
Cikin ɓacin rai Addah tace, “Kubrah?!”.
“Eh wlhy Addah, ni bama dukan ya ɓatan rai ba, bakiji yanda take faɗama Nu'aymahr maganar banza ba. A kwanakin nan dama na kula tana matsama yarinyar nan a gidan nan, haka ɗazun a islamiyyar asuba dan kawai Nu'aymah ta fiddo Fahad ɗin maman Sadiya daga aji saboda suna faɗa da wani yaro wlhy bakiga abinda tai mataba. Alhalin baikamata taima Nu'aymahn maganaba tunda yaran duk ƴan ajintane, ta fita sanin halin kowa a cikinsu”.
Kama hannun Nu'aymah Addah tayi suka fito ranta a ɓace. Hakan yasa Hajarah biyo bayansu da sauri itama.
“Kubrah!!”. Addah ta ƙwala mata kira ganin bata a falon.
Da sauri ta fito daga kitchen hannunta ɗauke da plate ɗin abinci.
“Ubanmi Nu'aymah tai miki kika daketa?!”.
Sake tsuke fuska Kubrah tayi, ta kalli Nu'aymah data duƙar da kai tana hawaye har yanzun. Wani ɗan murmushin mugunta tayi kafin ta kalli Addahn. “Addah catai na daketa?”.
“Ni na faɗa ba ita ta faɗaba, tunda a gabana akai komai”. Hajarah ta bata amsa kafin Addah tai magana.
“Mtsooow!! Munafuka kawai. Addah ni ban daketa haka kawaiba, rashin kunya zataimin shiyyasa........”
“To amma shine zaki ce mata ƴar iska, kuma sirrinta a tafin hannunki yake. Idan kinso zaki tona mata asiri agaban kowa”.
“Wlhy Hajarah zan sauya miki kamanni, wai ni sa'ar wasanki ce?”.
“Kai!! Ya isheni haka, banason rashin mutunci. Bazan ɗauki wannan wawancinba kunji na faɗa muku. Shin kuɗin yaran goye ne da kullum baku da wani buri sai na samin ciwon kai? Kusani daga yau na sakejin makamancin wannan banzan al'amarin wlhy sainayi ƙololuwar ɓatama mutum rai a gidannan. Banda k kullum girma kike kinacin ƙasa Nu'aymah ce kuma ta zama abar tozartawarki Kubrah? To daga yau na ji wani abu ya sake fitowa makamancin wannan zakiyi nadama a gidannan kinji na faɗa miki”. Ta ƙare maganar da matuƙar zafin rai tana sake yima Kubrah gargaɗi da hannu.
Sai kuma ta juya ga Nu’aymah dake sauke ajiyar zuciya a jajjere. “Nu’aymah jeki wanke fuskarki kinji kuma kar naji wannan maganar a wani waje, kiyi haƙuri”.
Kai Nu’aymah ta jinjinama Addah, babu musu ta shiga toilet ɗin dake a falon ta wanke fuskarta ta fito. sallma tai musu ta fice batare data sake yarda ta kalli sashin da Kubrah take ba. Harga ALLAH hankalinta a tashe yake matuƙa da kalaman Kubrah.
Koda ta koma sashensu ɗakinta ta shige ta shiga raira kuka, Nu’aymah yarinyace da bata da tsoro sam. Amma yanda tai matuƙar damuwa da faruwar abin nan na jiya daya kasa barin ransta saita baka tausayi. Tasan tabbas wannan laifin na jiya yasha banban da kowane irin laifi, kuma duk wanda zaiji abinda ya farun sai yayi ALLAH wadai da ita, ƙilama baba Malam da Umm su tsine mata albarka.
Sake rushewa tai da kuka kamar zata shiɗe wajen jan zuciya. A haka ta tsinkayo muryar Umm na ƙwala mata kira. Da sauri ta miƙe ta shiga share hawayen, harta nufi ƙofar fita sai kuma tai saurin dawowa. Toilet ta shiga ta sake wanke fuska tazo gaban mirror tasa hoda da kwalli sannan ta fita.
Zaune ta iske baba malam da Umm a falo. Cikin raunin murya taima baba malam sannu da dawowa. Duk kallonta sukai shi da Umm, baba malam yace, “Lafiya kuwa? Naga idonki kamar wadda tai kuka? Mamana!”.
Kafin tayi magana Umm dake hararta tace, “Saboda namata faɗa akan rashin kunyar data iya”. (dan ita tazata faɗan datai matane ya sakata fushi har yanzun).
Baba malam baice komaiba sai maida kansa da yay ga tv kawai. Fuska a ɗaure Umm ta nuna mata trayn dake a kan centre table. “Ki ɗauka ki kaima baƙo a falon baba”.
Kai kawai ta jinjina mata ta koma ɗakinta ta ɗakko hijjab. Batare datai maganaba ta ɗauka tiren ta fice. Sai da ta fice gaba ɗaya sannan baba malam ya ɗauke kansa daga kallonta. maidawa yayi ga Umm da itama take kallon nata.
“Addu’a ya kamata ki cigaba da mata bawai nuna fushinki da zafi fiye da kima ba. Har yanzu Nu’aymah yariyace ƙarama, sannan kinsan lalurar dake tare da ita sam bata buƙatar yawan takura. Ki fahimci ita wannan tsiwar itace tata ƙuruciyar”.
“Amma Malam ka tunafa ƴa mace ce ita. Gidan wani fa zataje. Bandama ƙaddara daba yanzu tana ɗakin miji ba. Wlhy sam bana son tsiwarnan tata, bansan a ina ta kwaso wannan banzan halinba nikam”.
Murmushi baba malam yayi yana miƙewa, “To ayi haƙuri zata daina insha ALLAH, nima zan zauna da ita anjima ALLAH ya huci zuciyarki”.
Yanda yay maganarne ya saka Umm yin murmushi, dan ta sake tabbatarwa yau mijin nata yana cike da nishaɗi sosai kam, musamman data san yafi kowa ƙin jinin tsiwar ɗiyar tasu.
★★★★★★
Murya a sanyaye tai sallama a ƙofar falon har kusan sau uku. jin shiru ba'a amsaba ya sakata tura kanta ciki da haushi. Takaicin rashin amsa mata sallamar da ba'ayiba ne ya sakata ƙin kallon baƙon ma balle tasan wanene.
A gabansa ta dangwarar da trayn, murya a cinkushe batare data kallesa ba tace, “Ina yini”.
Shiru yanzuma ba'a amsaba, wani sabon takaicin ya sake lulluɓe ta. Har tayi niyyar dubansa ta sauke masa takaicinta saita tuna yanzufa Umm ta gama mata faɗa harda duka akan tsiwa, sannan kuma bai kamatama tayi wani abun rashin hankali ba tunda batasan wanene baƙon nasu ba. Zata iya yuwuwa babban mutumne sa'an baba malam ko cikin yayunta. Haɗiye haushinta tai ta nufi hanyar fita zata bar falon.
Yoohan da tun shigowarta idonsa nakan wani littafi da baba malam ya bashi ya duba ya ɗan ɗago kansa dan sam baiji sallamarta ba balle shigowartaba ma shi, sai gilmawarta kawai ya gani yanzu da take ƙoƙarin fita. Cikin tsautsayi ta bigi ƙaramar jakkar dake gefensa da ƙafa. baya tai taga-taga zata faɗi cikin sa'a yay saurin saka mata ƙafa dan son kareta bisa tsautsayi sai gata a cinyarsa ɗare-ɗare.
Duk da ya canja kayan jikinsa mayataccen ƙamshin turarensa na nan manne da shi. Shaƙa ɗaya Nu'aymah tayi tai azamar ɗagowa cikin tashin hankali da tsantsar takaici.
Idanunsu ne ya shige cikin na juna, cike da firgici Nu'aymah ta sake waro masa idanunta da kware baki zatai ihu saboda harga ALLAH ta tsorata da ganinsa. Saurin saka tattausan hannunsa yay ya rufe mata bakin ruf yau ma, tare da sake manneta a jikinsa sosai shima a cikin ɗan firgice.
Wani irin mugun bugawa ƙirjinta ya sakeyi, jikinta ya hau ɓari tamkar wadda aka jefa cikin garwashin wuta ko akan wayar lantarki. Ta shiga mutsu-mutsun ƙwace kanta tana kai masa duka.
“Oh my God! Just relax. Please calm dawn”. Ya faɗa yana janye hannayensa duka daga jikinta.
Cikin rawar jiki hawaye na zirara ta miƙe, sake bigewa tai da kujera ƙafarta ta tuzguɗe ta sake yin gaba kuma zata kifa yay azamar riƙo mata hannu ta sake dawowa jikin nasa.
“Wayyo Abbana ɗan isk.........” ta wage baki da iya ƙarfinta zata faɗa yay azamar saka hannu ya sake toshe bakinta da manneta sosai a jikinsa yanda bazata iya ko motsawa ba.
“Wa'iyazubillah!! Iskancin naku da rashin tsoron ALLAH yau har a falon malam?” Kubrah data shigo falon tamkar an jehota ta faɗa hannu bisa kai tana mai waro idanu waje..
Tashin hankali, tsabar ruɗewa Nu'aymah harda guntun fitsar ta saki a wando, batama san ta saka gwiwar hannunta ba ta kai ma Yoohan duka. Sai ko ya sauka a gefen cikinsa.
Saurin sakinta yay yana faɗin “Ouch!!!” dan harga ALLAH yaji zafi. Yay saurin ɗoura hannun nasa bisa cikin ya riƙe yana watsa mata mayun idanunsa masu haske da cikar gashi.
Nu'aymah dake ja da baya tana hawaye da kallonsa da kallon inda Kubrah take tsaye tace, “Ɗan iska kawai, ALLAH ya isa ban yafeba. Wlhy daga yau ka sake ƙoƙarin taɓamin koda hannu sai na illata maka wannan fuskar taka mai kama da jan ƙosai, na tsane ka wl........”
“Hhhhhhh! K! Ƴar iska bar wani pretending kinji!”. Kubrah ta faɗa tana ƙarasa shigowa cikin falon sosai.
Nu'aymah dake kuka tamkar ranta zai fita tace, “Aunty Kubrah wlhy ba abinda kike tunani bane. Wlhy tallahi kinji na rantse by mistake ne hakan ya sake faruwa yau ma, shine fa y.....”
“K dalla saurara mani! Mahaukaciya kika maidani irinki komi? Na ganki da idona saman cinyarsa kuna tsotsar bakin juna sannan ki hau mini wani rsantse-rantsen banza. Kinsan ALLAH, inhar kika sake faɗin tak saina kwarara ihu yanzun nan kowa yasan halin da kuke ciki”.
Ƙasa Nu'aymah ta durƙushe tana ƙara sakin kuka maiban tausayi. Yayin da Yoohan da sam bai fahimci mi Kubrah ke faɗa ba ya zuba musu idanu kawai yana kallonsu.
Juyowa Kubrah tayi garesa, sai dai wani shegen kwarjini da cikar haibarsa tai bala'in cika mata idanu. Muƙut ta haɗiye maganar tata ƙirjinta na wani irin bugawa da sauri-sauri. Cikin suɓutar baki ta firta ‘Tsarki ya tabbata ga ALLAH’.
Sake ɗaure fuska Yoohan yayi fiye da da, dan a rayuwarsa ya mugu-mugun tsanar kallo, musamman ma irin wanda Kubrah ke masa na ƙurulla a yanzun. Duk da ma bawai yaji mi take faɗaba ne ɗazun, sai dai ya fahimci ba magana mai daɗi takema Nu'aymah ba. Dan haka ya watsa mata wani mugun kallon da manyan idanunsa yana miƙewa.
Ganin ya nufita ya sata saurin zabura tai baya, sai dai kuma a mamakinta yama ɗauke kai daga gareta gaba ɗaya, raɓata yay ya nufi Nu'aymah dake durƙushe har yanzu tana kukan tashin hankalin datasan a yau babu makawa sai Kubrah ta tona mata asiri.
Handkherchief ya ciro a aljihunsa tare da tsugunawa gabanta, murya ƙasa-ƙasa yace, “Hello!”.
A razane Nu'aymah da batasan da isowar tasaba ta ɗago danjin maganarsa gab da ita. Ta waro idanu waje sosai da saurin duban inda Kubrah ke tsaye tana kallonsu kamar ta samu television.
Kamo hannunta yay, da sauri ta dawo da dubanta garesa tare da fisgewa da ƙarfi. Sai dai ko gezau baiyiba balle tai tunanin ƙwacewar. “Kai wane irin......”
Yatsansa ɗaya ya ɗaura akan baki. “Shiiii!!!” ya faɗa cikin katseta da zazzaro mata idanunsa sosai.
Ruf. Tai saurin rufe bakin kuwa. Dan wani irin shakkarsa da tsoronsa da bata taɓa fuskantaba daga gareshine ya shigeta yau ɗin. Ga wani irin kwarjini mai bala'in cika idanu da yay mata. Batare da yayi magana ba ya saka mata handkherchief ɗin cikin tafin hannunta tare da matso da fuskarsa gab da tata cikin wata irin raunanniyar murya yace, “Silly girl”.
Baya taja jikinta, dai-dai da sakar mata hannu da yayi ya miƙe shima. Batare da ya kalli ko inda Kubrah take ba ya ɗauka jikkar da Nu'aymah tai tuntuɓe ya fice abinsa. Ya tabbata idan ya cigaba da zama a falon to lallai zai iya aikata abinda shi kansa bazai yafema kansaba. Dan duk da baiji mi Kubrah ta faɗaba ya fahimci ba abune mai daɗi ba musamman yanda Aymah take kuka.
Yana ficewa Kubrah ta bi bayansa da sauri.
“Aunty Kubrah!” Nu'aymah ta faɗa da hanzari tana miƙewar itama. Amma sam Kubrah batako jiyoba balle ta nuna zata saurareta ta ficewarta.
اَللَّهُمَّ لاَ سَهْلَ إِلاَّ مَا جَعَلْتَهُ سَهْلاً وَأَنْتَ تَجْعَلُ الْحَزْنَ إِذَا شِئْتَ سَهْلاً.
Allahumma la sahla illa ma ja’altahu sahlan, wa anta taj’alu-l-hzana idha shi’ta sahlan.
Ya Allah! Babu wani abu mai sauki sai abin da Ka sanya shi ya zama mai sauki, kuma Kai kana sanya tsanani idan Ka so ya zama sauki.
Nu’aymah dake jin wata hajijiya na neman zubar da ita ƙasa ta faɗa tana mai dafe kanta da sauri. Da ƙyar ta iya kai hannu domin lalubar bango. Sai dai kuma ina bai kai ga bangonba wani duhu ya mamaye idanunta. a take ta zube ƙasa jikinta na karkarwa saboda wani bala’in sara mata da kanta yayi lokaci ɗaya…………..✍
ZAFAFA BIYAR 2021
Hafsat miss xoxo????
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).????????
Mamu gee????
MIN ƘALB!!????????
Hafsat rano????
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!????????
Safiyya huguma???? SIRAƊIN RAYUWA????????
Bilyn Abdull????
SARAN ƁOYE????????
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka????????????????
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????
09033181070
????????????????????????????????????????
TEAM—-ZAFAFA BIYAR????????????????
ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????.
[5/21, 9:18 AM] +234 816 133 8078: LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana????????.
No. 32
…………Tun isowarsu asibitin aka fara bama Nu’aymah dake a sume taimakon gaggawa. Sai dai harsu baba malam suka isa asibitin bata farfaɗo ba. Hakan sai ya sake ɗaga hankalinsu. musamman ma Hajjo dake ta faman sharɓar hawaye. Cike da kulawa baba malam ya zauna kusa da ita duk da kunyar ɗan fari dake tsakaninsu. Murya a tausashe da nuna ɗunbin kulawa da ladabi ya fara lallashinta da faɗa mata kalamai masu taushi da nutsuwa irin na masu ilimi. Ya nuna mata koda rasa Nu’aymah sukayi su zama masu haƙuri da godema ALLAH. Dan lokacin da ya basu ita baiyi shawara da suba. A yansu kuwa idan ya karɓeta ya fisu bukatarta ne.
Haka ya cigaba da mata nasiha harta samu nutsuwa tai shiru. Abba Musbahu yazo gabanta ya durƙusa tare da saka handkherchief ya share mata hawayen.
Ana haka Doctor ya fito daga ɗakin da aka sanya Nu’aymahn. Ya buƙaci ganin ɗaya daga cikinsu cikin nuna girmamawa a garesu. Abban Abdallah da Abban su Adawiya ne suka bisa office. Dan baba malam ya nuna kawaicin nasa da ya saba kamar ko yaushe. Amma zuciyarsa cike take da tsoro da rauni. Yana ta dai ƙoƙarin danneta ne da ambaton ALLAH wajen ƙarfafa imaninsa.
A office ɗin likita kuwa ya nutsu ne wajen rubuce-rubuce a wata takarda kafin ya maida hankalinsa gasu Abbah.
“ALLAH ya gafarta malam zan fara da muku albishir ɗin farfaɗowarta. Sai dai kuma kamar yanda kuka sani raunin dake a cikin ƙwaƙwalwarta shine ya motsa mata. Kuma gaskiya a bincikenmu yarinyarnan tana matuƙar buƙatar son ganin babban likita. Idan ba hakaba a koda yaushe zata iya fuskantar gogewar komai na ƙwaƙwalwar ta. saboda tana ƙara girma ciwon na daɗa faɗi. Musamman ma daya kasance kamar tana sakama kanta abubuwa masu nauyi a cikin rai. A duk kuma lokacin data shiga ƙunci ciwon na mata kuɗa a cikin kanta, ba dan ma tana samun kulawa da kuma addu'oi ba da gaskiya bana zaton yarinyarnan zata kai wannan shekarun batare data tsinci kanta a ciwon hauka ba. Duk da komai na ALLAH ne, babu wani bawa daya isa canja ƙaddarar wani bawa daga yanda tazo a littafinsa. Amma a wannan karon ayi himmar sadata da likitan daya dace da matsalarta, munan taimako kawai muke bata na dakatar da raɗaɗin a gareta a lokacin daya taso. Amma matsalarta sake hauhawa takeyi gaskiya”.
Su Abba da duk jikinsu yay sanyi sukaima Doctor godiya sosai. Tare da tabbatar masa insha ALLAHU a wannan karon zasuyi abinda ya dace.
Yaji daɗin hakan sosai. Ya sake ɗan musu wasu bayanan da suka dace akan yanayin kula da Nu'aymahn kafin ALLAH yasa a dace da samun Doctor ɗin daya faɗa. Dan ya basu note dazai taimaka musu samun ganin makusancin likitan da lokaci-lokaci yake shigowa cikin kano. Baya kuma duba marasa lafiya a ko ina sai a General hospital. Dan haka ya basu abinda zai taimaka musu ganawa da wata likita dake aiki a General hospital ɗin, wadda yake da tabbatacin ta hanyarta zasu iya ganin Doctorn.
Godiya sukai masa sosai, sannan suka fito. Sai dai basu ma su baba malam bayanin komaiba, a ƙoƙarinsu nason yin wani hoɓɓasa akan jinin yayan nasu da a kullum hidimarsa ke ƙarewa a kan su da nasu iyalin. Suma wannan karon sunason nuna tasu bajintar akan ɗaya daga cikin jininsa guda biyu da ALLAH ya bashi.
__★★
Ganin lokacin sallar la'adar ya gabato Yoohan ya buƙaci kaɗaicewa dan ya huta. Hakanne ya saka papa fita ya barsa shima ya nufi ɗakin da aka kama masa.
Yoohan ya ɗan sauke ajiyar zuciya yana miƙewa. Zuwa yay ya sakama ƙofar ɗakin key. Kafin ya nufi bayi yayo alwala kamar yanda baba malam ya koya masa. Duk da zuciyarsa na kwaɗayin zuwa massallaci yay salla cikin jam'i kamar yanda suka gabatar ɗazun a massallacin juma'a haka ya haƙura ya daure yin tasa shi kaɗai a cikin ɗakin kamar yanda aka koyar da shi.
Bayan ya idar da sallar a tsanake yay addu'a gwargwadon abinda ALLAH ya hore masa. Waya ya jawo yay kiran baba malam. Cikin sa'a kuwa bugu biyu aka ɗaka. Sassanyar ajiyar zuciya ya sauke wadda har baba malam ya jiyota.
“Banyi zaton zaka ɗagaminba Uncle. Nazata zakayi fushi dani bisa kuskuren papa”.
Baba malam da fitowarsa kenan daga massallacin cikin asibiti sun idar da salla kiran ya shigo masa yay sassanyan murmushi, ƙaunar Yoohan ɗin da ƙyawawan ɗabi'unsa na sake dulmiyasa a ƙaunar yaron. Cikin kulawa yace, “Haba Yahya! Mizaisa nayi fushi da kai? Ai koshi bazanyi fushi da shiba dan ya fini gaskiya. Da farko ina fatan dai ka gabatar da sallar la'asar. Na biyu kuma ina fatan babu wata matsala tsakaninka da mahaifinka a dalilin ganinka da yay a wajena?”.
Lumshe idanu Yoohan yay a hankali yana jingina bayansa da kujera, cikin so da ƙaunar baba malam dake ratsashi shima yace, “Alhamdulillahi Uncle. Yanzun nan na idar da salla, sai dai banje massallaci ba, ina fatan hakan ba laifi baneba. Dan nayi hakanne saboda ahalina, banason su fahimci ni musulmi ne tun yanzu dan zasubi hanyoyi da dama wajen kaini ƙasa. Amma idan na sami wadataccen ilimin addini musulinci duk ta inda suka ɓullo zan kare kaina”.
Baba malam dake murmushi ya sauke ajiyar zuciya. “Tunaninka mai ƙyau ne Yahya. Sai dai salla cikin jam'i tanada matuƙar muhimmanci, dan haka kar kayi sakaci da samun ladan dake cikin jam'i kaji”.
“Zan kiyaye Uncle”.
“Alhamdulillahi haka ake so. Mahaifinka fa?”.
“Karka damu da shi Uncle. haka yake da zafi, amma da an fahimtar da shi yanada saurin fahimta. Munyi magana da shi ya kuma fahimceni, kafin ma ya wuce zai shigo wajenka yacemin”.
Hakan ya bama baba malam mamaki matuƙa. Amma sai bai nunama Yoohan ba ya amsa masa kawai. Sannan sukai sallama.
Lokacin da Yoohan ke waya da baba malam a can papa ma yana ɗakinsa suna waya da Uncles ɗin Yoohan ɗin su Uncle Godwin. Ba akan komai suke wayarba sai akan baba malam. Kamar yanda papa ya girgiza da ganin Yoohan da farko haka suma suka girgiza dajin Yoohan a wajen baba malam. amma daga baya sai bayanin da Yoohan yayma papa ɗin yaɗan sanyaya musu rai.
Uncle Mike yay wata dariyar mugunta yana faɗin, “Wannan ɗan nakafa shegen kansane, inaga akwai aikin da yakema turawan nan ta ƙarƙashin ƙasa shiyyasa kullum bai damuwa da lamarin kowa sai wannan aikin nasa. A da ba ƙaramin haushi yake baniba akan hakan, amma jin wannan maganar ta yau sai naji ƙaunarsa da son haɗa tafiya da shi. Sai dai matsalar ɗaya ce yaron yanada taurin kai, nasan bazai taɓa yarda musan cikinsa gaba ɗaya ba. Amma ni a ganina mizai hana muma muyi namu aikin akan wannan hausa man ɗin, dan fa multi millions ne. Kawai dai baya nunawa ne”.
Papa ya kwashe da wata dariya, kafin yace, “Mike! tunaninmu ɗaya, dan haka ku bari sai na shigo Abuja mu tattauna da ƙyau. Yanzu dai matakin farko zanbi shawarar Yoohan zanje har gida na bashi haƙuri. Daga haka na ƙulla alaƙa mai ƙarfi da shi. Sauran bayani kuma sai mun zauna a tebirin shawara”.
Duk sunyi na'am da hakan suma. Dan haka yay musu sallama ya kashe wayar cike da zumuɗi a ransa. Kaɗan-kaɗan sai ya ƙyalƙyale da dariya. Dan gaba ɗaya zuciyarsa ta gama tsara masa yanda komai zai kasance.
__★★
Bayan Baba malam sun shiga sun duba Nu'aymah dake barci suka bar Hajjo da Abba Musbahu a asibitin. Koda suka iso gidan sai su Umm suka shirya su kuma suka tafi duba Nu'aymah. Wanka yayi ya zauna a falonsa yaci abincin da Umm ta shirya masa kafin su wuce. Abincin kawai yake ci a zahiri, sai dai zuciyarsa sam bata tare da duniyar mutane. Yayi zurfi matuƙa gaya a tunanin Pastor Goshpower (Papa). Ba komai ya kaisa ga tunaninba kuwa sai mamakin dama Papa nada babban ɗa a duniya kamar Yoohan? Ga shi dai a zahiri akwai kamanni tsakaninsu, sai dai baisan miyasa zuciyarsa ke kawo masa wani al'amari mai kama da kokwanto a cikin zuciyaba. Musamman da zuciyar tasa ke tariyo masa wani shuɗaɗɗen al'amari daya faru a shekarun baya tsakaninsa da Papan.
Haka yayta saƙawa da kwancewa har lokaci yaja bai farga ba. Sai da Abban Abdallah ya shigo dubasa sannan ya fahimci yayi zurfi sosai a tunani ashe. Alwala yayi suka fice massallaci dan lokacin sallar magriba ya gabato
Suna fitowa su Umm na dawowa gidan. tambayar jikin Nu'aymah sukayi. Suka sanar musu har yanzu tana barci, batama san sunje ba balle tahowarsu.
Baba malam yabi Umm da kallo harta shige. tausayinta mai tsanani ne ke sake shigarsa. Tanada haƙuri da kawaici matuƙa, shiyyasa yake tsananin ƙaunarta fiye da zaton mai hasashe. Yanzu haka inba shi daya gama sanin kayarsa ciki da bai ba bazaka taɓa fahimtar tanada damuwa ba a fuskarta. Ta dake ta shanye komai, baka ganin komai akan fuskarta sai tsananin jarumta da tarin haƙuri da juriya.
Haka ya tafi massallaci da wannan tunanin na Umm.
Bayan idar da sallar isha'i suna shirin zaman karatu kamar yanda suka saba ɗaya daga cikin ƴan agajin massallacin ya shigo ya sanar masa cewar yayi baƙi.
Jimm yayi alamar tunanin baƙi daga ina a wannan lokacin? Bai gama kaiwa ƙarshe ba ya hango Yoohan dake ƙoƙarin shigowa massallacin. Bai tashi ba, sai ya jira harya ƙaraso inda suke. Yoohan da kallo ɗaya zakai masa ka fahimci damuwa da rashin walwalarsa kamar ko yaushe ya ɗan bama na kusa da shi hannu sukai musabaha kafin ya ƙarasa inda baba malam ɗin yake. Cike da girmamawa ya risina ya gaishesa. Amma sai baba malam ɗin ya kamo hannunsa cikin nasa sukai musabaha kamar kowa. Cike da jin nauyi Yoohan yay masa bayanin tare yake da baƙi, wannan ya saka baba malam miƙewa bayan ya bama ɗalibansa haƙuri ya barsu da Abbansu Abdallah shi kuma suka fito.
Duk da dai yayi mamakin ganin papa ne sai baice komaiba. Da kansa yay musu iso gidan saukar baƙinsu. Sannan ya kira Umm ta bada abinda ke akwai a gidan cikin su Omar wani ya kawo.
Papa dake ta waya tun ɗazun ya ajiye yana kallon baba malam da murmushi, shima bai gazaba wajen maida masa murtani. A ƙasan ransa kuwa yana neman tsarin ALLAH da ga kowanne irin sharri papan ke tare da shi ko yake shirin ƙullawa. Duk da shi mutum ne mai ƙyautatama mutane zato zuciyarsa ta kasa ƙyautata zaton akan papa, dan shi shaidane akan sanin papa bayahude ne na gaske, sai dai bai saniba ko yanzu ya canja daga yanda ya sanshi a da ɗin.
Hannu ya bashi suka gaisa, hakan yay dai-dai da shigowar Omar ɗauke da basket da Umm ta shiryo abincin motsa baki. Sai da ya gaida Papan, suka gaisa da Yoohan da alamar sanayya tsakaninsu sannan ya fice. Papa ya gyara zamansa yana wani ɗan basarwa, fuskarsa da murmushi har yanzu ya duba baba malam da faɗin, “Kayi haƙuri da kuskurena na ɗazun, ina fatan zaka dubesa akan rashin sani na aikata. Bansan alaƙarka da yarona mai daraja bace irin haka sai bayan mun barka ne yaymin bayanin da har na fahimta, ina fatan zakamin afuwa”.
Sosai mamaki ya kama baba malam, dan duk zatonsa Yoohan ya ma mahaifinsa bayanin ya musulunta ne. dan haka ya ɗan dubi Yoohan ɗin. Da sauri Yoohan ya girgiza masa kai yanda papa bazai fahimtaba, hakanne ya saka baba malam fahimtar akwai abinda Yoohan ya sanarma mahaifinsa daban kenan. Sai kawai ya murmusa abinsa ya fuskanci papan shima.
“Karka damu komai ya wuce. Dama kuma ni ban ɗaukesa wani abuba. A inda ya faru anan na zubar da shi, nima ina fatan kaimin afuwa ka kuma fahimci alkairine ya haɗani da Yahya ba sharriba. Sanin shi wanene kuma bazaisa na taɓa cutar da shi ba insha ALLAHU. Saɓanin dake tsakanina da kai kuma bana fatan ya zama sanadin ɓata alaƙata da shi, dan sanin kai ne mahaifinsa bazai canja komai ba daga yanda na ɗaukesa a raina”.
“Naji daɗin haka, na kuma gode sosai da wannan girmamawa”. Papa ya faɗa yana sake faɗaɗa fuskarsa da murmushin mugunta.
Daga haka dai suka ɗan taɓa hirar da bawani tsaho taiba, shi dai ma Yoohan ba saka musu baki ya keba, yama maida dukkan hankalinsa ne ga wayarsa kamar baya falon. Kusan awarsu ɗaya da rabi sukai masa sallama suka fito inda su Solomon suke. Sai da baba malam yaga barin motocinsu anguwar sannan ya shiga cikin gida ransa taf da wasiwasi akan wannan ziyara ta Pastor Goshpower, amma sai ya bar abinsa a zuciya bai faɗama kowa ba, ya ma maida hankalinsa wajen kwantarma matarsa hankali akan damuwar ciwan ɗiyarsu.
WASHE GARI.
Washe gari papa ya matsa akan sai Yoohan ya bisa sun koma Abuja. Badan yaso hakanba ya amince zai bisa, dan dama yau ɗinne zai kammala abinda ya kawosa kanon. Yaso komawa wajen baba malam dansu tattauna game da neman iliminsa amma papa ya tsare ko ina ya hanashi matsawa ko nan da can. Asibiti ma binsa yay sukaje tare, ya kuma zauna a office ɗinsa har sai da ya kammala komai suka fito.
Da ga asibitin airport suka tafi kai tsaye, sai da jirginsu ya ɗaga sannan guards ɗinsa suka ɗauki hanya suma a motocin.
Baba malam na asibiti wajen duba jikin Nu'aymah da jikinta Alhmdllh saƙo ya shigo masa. Buɗewa yay ya duba ganin Yoohan ne. Murmushi baba malam yayi saboda ganin abinda saƙon ya ƙunsa, a ransa kuwa yana tsananin tausayi da ƙaunar Yoohan, insha ALLAH yayi alƙawarin zai taimaki yaron nan har ya zama HASKEn da zai zama HASKE ga waɗansu.
Ajiye wayar yay ya maida hankali ga Nu'aymah da Hajjo take lallaɓawa taci abinci amma sai shagwaɓa take ita ta ƙoshi. Ya ɗan murmusa tare da kamo hannunta cikin nashi. “Mamana daure kici ko kaɗanne kinji, inba hakaba fa kinsan Doctor yace allura zai miki, idan kuma kin fison allurar to sai a kirashi kawai”.
Da sauri ta shiga girgiza kanta idanunta cike da ƙwalla. “Abba dan ALLAH a'a banaso”.
“To ki daure kici abincin sai kisha magani ki kwanta ki huta. Kinga kince dama kanki na ciwo har yanzu, Doctor kuma yace kina buƙatar hutune sosai”.
Kanta ta sake jinjina masa. Hajjo da batace musu komaiba ta miƙama baba malam abincin. Babu musu ya amsa ya fara bata da kansa. Batafi spoon huɗu ba su Ahmad suka shigo ɗakin bayan sunyi sallama an basu izini. Ba Nu'aymah kawai ba hatta Hajjo da baba malam da ɗunbin mamaki suke kallon wanda ya shigo tare da su Ahmad ɗin. Ba kowa bane face Nasir jikan yayar Hajjo.
Babu kunya idonsa fes akan Nu'aymah da mamakin ganin nasa ya sakata masa kallo mai nisan zango. Hajjo ce ta katse su da faɗin, “Naseru yaushe a gari? Inji maƙi baƙo?”.
Goshinsa yaɗan sosa najin kunyar kallon da baba malam ke masa. Kafin yace, “Hajjo yanzun nan muka iso”.
“Kuka iso? To kai da wa kuma?”.
Kansa tsaye yace, “Rufaidah”.
Baba malam da tun gaisuwar daya amsa musu baice komai ba sai yanzu yace, “Lafiya dai ko Naser? Yau ka tuna damu a duniya”.
“Ayi haƙuri Kawu, ni ɗin mai laifine kam, mun tahone saboda ga biki nata gabatowa, ganin mun sami hutun makaranta mu duka sai kawai nace bara mu taho maɗan huta ai”.
“Oh to masha ALLAHU, ALLAH yayi jagora to”.
A tare suka amsa da amin. Nu’aymah dai bata tanka ba, tama ɗauke kanta tamkar batasan mi akeyiba. Sai da Naser ya tambayeta yaya jikin sannan ta gaidashi batare data kallesanba yanzun ma. Shiko yanata so su sake haɗa ido ko zaiji ɗan sanyi a ransa da ruhinsa.
Miƙewa baba malam yayi yana faɗin, “To ni bara naje gida hajjo, dan ina saka ran zuwan wasu baƙi ɗan anjima kaɗan idan ALLAH ya kaimu. Idan sun wuce insha ALLAHU zan dawo muji ko zasu bamu sallama, banason zama asibitin nan sam”.
Amsa masa hajjo tayi tare da binsa da addu’a. Nu’aymah ma ma dasu Ahmad sukai masa sallama ya fice. Hajjo ce ta sake cigaba da bama Aymah abincin, badan yana mata daɗi ba take amsa, sai dai mayataccen kallon da Naser ke mata duk ya sake takureta matuƙa, sannan ya tuno mata da wasu shuɗaɗɗun abubuwa dake tdakaninsu a lokacin ƙuruciyarta, hakan yasa taketa cuno baki gaba da ɓata fuska duk da ƙasan ranta cike yake da mamakin ganin nasa ya dawo bayan barinsu na tsahon shekaru da yayi akanta.
Idan bata manta ba shekara kusan takwas kenan rabonsa da kano. Dan tunda tace masa ita Yah Abdallah ne zaɓinta yay zuciya saboda goyon baya da Hajjo ta bama Abdallah a wancan lokacin. Anyi bukukuwa kashi-kashi a gidansu shi kaɗai ne baya zuwa sam.
Ta ɗan sake satar kallonsa da jijjina ƙyawun daya ƙara da cikar kamala tamkar ba Yah Naser ɗin data sani ba a shekarun baya. Kallo ɗaya zaka masa ka fahimci yanzu kam kuɗi sun zauna a garesa da hutu, dan sai ɗaukar ido yake kamar gasashshiyar kazar gidan gona.