NOVELSSARAN BOYE

SARAN BOYE COMPLETE

   *_“Zan iya amsar gayyatarki akan dalili guda ɗaya, idan kin amince da shi ko yanzu zan iya dawowa gida na fuskanci iyayenmu”._*
    _Dalilin kawai ki amince a ɗaura mana aure ranar bikin su Kubrah._

   Wani irin mugun bugawa ƙirjin Nu'aymah yayi, tai mugun waro manyan idanunta waje hawaye masu zafi na rige-rigen fitowa. A fili cike da karyewar zuciya ta furta, ‘Anya kuwa Yah Ab bai fara shaye-shaye ba jama'a? Na shiga uku ni Zainab, wane irin tsaka mai wuya bawon ALLAHn nan yake ƙoƙarin jefani a gidan nan?’. 
    Kuka sosai ta kuma sha fiyema dana ɗazun, dan sai da taji kanta ya fara sara mata sannan ta haƙura. Har bayan anyi sallar isha'i bata fitaba ta cigaba da zama a ɗaki. Wayar Umm ma da Muhammad ya shigo aran littafinta na *Ahdhari* ta bashi ya kai mata. Yunwa ce ta fara takura mata, dole ta miƙe ta shiga bayi, wanka tayo ta fito, tai shirin cikin wando da riga na barci masu taushi. Tanajin yunwa amma bata jin cin abincin kuma, sha'awar shan lipton ne yazo mata a rai. Dan haka ta miƙe ta ɗauka hula ta saka a kanta sannan ta fito.
  A falo sukaci karo da Rabi ɗauke da ƙaramin jug da alama ma ɗakinta zata. Baki Rabin ta washe ta na faɗin, “A'a uwar ɗakina kin tashi ashe? Kamar kinsan kuwa zoɓon nan zan kai miki dama ko zaki ɗansha dan na sanki da son zoɓo”.
  Ɗan lumshe idanu Nu'aymah tayi ta buɗe akan rabin tana ɓata fuska kaɗan. “No bar zoɓon nan ma dai baba Rabi. Idan ban takura miki ba dan ALLAH haɗamin lipton kaina ciwo yake min”.
   Da sauri Rabi tace, “Ah wlhy babu wani takura uwar masu gida. Kinga zauna bani mintuna biyar kacal, barama nai miki amfani da ganyen shayin baba malam, ina dai kina so ko?”.
    Kai kawai Nu'aymah ta gyaɗa mata dan surutunta ya isheta. A ƙasan ranta kuma tana mamakin yanda Rabin ta amsa dafa mata shayin ɗin babu ko musu balle sukai ga faɗan da suka sabayi kullum.

    Ɗakin Umm Nu'aymah ta nufa kafin Rabi ta kammala, sai dai ta iske tana wanka dan haka ta fito akan idan ta gama zata koma. Fitowarta dai-dai da fitowar Rabi da ga kitchen ɗauke da kofin shayi dake ta turiri. Sai da tai mata godiya sannan take tambayarta ko baba malam ya shigo?.
   “A'a bai shigoba, dan naji Muhammad na faɗin kamar yayi baƙi ne ma”.
 “Okay”.

Kawai Nu’aymah ta faɗa tare da ɗaukar kofin ruwan zafin ta kai bakinta tana ƙoƙarin kunna television da hannunta na haggu.
Sosai shayi yayma Nu’aymah daɗi, harta shanye wanda Rabi ta zuba mata itama ta sake zuba sauran wanda ya rage a butar shayin. Tana cikin shan wanda ta zuba ɗinne Umm ta fito…
“Oh dama kin tashi?”.
“Eh, nama shiga ɗakin na tarar kina wanka. Umm kaina ke min ciwo ALLAH”.
Cike da kulawa Umm dake dubanta tace, “Ba dole kanki yay ciwoba Nu’aymah, kukan da kikayine ai. Halan ma da kika tafi ɗakin ba barcin kikayi ba?”.
“Umm barcin nefa bai zoba. Amma yanzu naɗan fara ji, sai dai zan jira Abba ya shigo sannan naje na kwanta”.
“Wayasan sanda zai shigo, ki tashi kije ki kwanta banason sakarci. Miyasa ke wai sam baƙya tattalin lafiyarkine? Kin fison kullum ki ganmu hankali a tashe”.
“Kiyi haƙuri Umm ba haka baneba wlhy, dama dan yau duk bamu haɗu da Abba bane shiyyasa. Amma bara nasan insha ALLAHU da safe zamu haɗu. Sai da safe”.
“Ki tabbatar kinyi addu’a kafin ki kwanta”.
“To Umm”.
Nu’aymah ta faɗa tana nufar ɗakinta badan taso hakanba. Kamar jira tana kwanciya sai barci mai nauyi ya kwasheta batare da ko addu’ar da Umm ta gargaɗeta yi ba tayi ɗin.

★★

   Sai wajen sha ɗaya baba malam ya shigo gidan. Koda ya tambayi Nu'aymah Umm ta sanar masa ta kwanta sai ya nufi ɗakinta. Yayi sallama kusan sau uku babu amsa, dan haka ya juyo falo yana faɗin, “Nayi magana shiru, inaga tayi barci ma”.
    “Dama tace barci takeji, amma tsabar fitina wai zata zauna jiranka dan yau duk bata gankaba”.
 Murmushi kawai baba malam yayi, amma baice komaiba.

      Kusan ƙarfe sha biyu saura Nu'aymah ta farka da wani Masifaffen ciwon ciki. Juye-juye ta shigayi a kan gadon tana kiran sunan Umm. Tun abin na mata sama-sama harya fara fin ƙarfin tunaninta. Yunƙurawa tai da ƙyar ta tashi zaune tana ambaton ‘Innalillahi.....’ da ƙyar ta iya sakkowa da ga saman gadon. Sai dai yanda ƙafafunta da mararta suka riƙe sam bazata iya takawa ba. 
   Ƙasa ta durƙushe hannunta ɗaya riƙe da cikinta, ɗayan kuma ta dafe gado da shi tana matse idanu da cije baki. Cikin azabar data isheta ta fara ƙwalla kiran sunan Umm da baba malam tana roƙon suzo su taimaketa zata mutu. Yanda zufa ta jiƙeta sai ka ɗauka ruwa aka watsa mata. Wata gigitacciyar ƙara ta saki lokacin da idanunta ke sauka akan Windown ɗakinta. Gilmawar mutum ta gani, wanda alama ta nuna ya jima a wajen tsaye koma waye. Ai sai kawai ta daddage ta fasa ƙarar da tafi ta farko badan taji tsoro ba sai dan wani irin kartawa da mararta tayi tamkar numfashinta zai bar ganar jikinta a lokacin.......

    A rikice baba malam da Umm da barci ya fara ɗauka yanzun suka farka. Har rige-rigen fitowa sukeyi dan ƙarar Nu'aymah sun jitane tamkar a tsakkiyar ƙwalwar kansu.
Kwance suka isketa a ƙasa wanwar tana numfashi da ƙyar. Baba malam yay saurin kunna fitilar ɗakin mai haske, Umm kuma ta nufeta tana kiran sunanta. Sai dai ina Nu'aymahn ta suma. Sake rikicewa Umm tayi, ta fashe da kuka itama tana girgiza Nu'aymahn.
   Baba malam daya nufosu shima a rikice yay sauri ja da baya jin ƙafarsa cikin wani abu mai ɗumi. Kallon inda ya taka ɗin yayi. gabansa yay bala'in faɗuwa ganin jini. Cikin rawar jiki ya durƙusa da kai ɗan yatsansa ɗaya yaɗan dangwalo. Tabbas jinine kuwa. Dan haka yace, “Jini kuma?”.
 Saurin kallonsa Umm tayi itama. Tace, “Jini kuma malam? A ina?”.
  Da hannu ya nuna mata, sosai zuciyarta tai masifar harbawa. Tabi jinin da kallo har jikin Nu'aymah da alamu suka nuna daga nan yake fita. Kafin ta iya cewa wani abu sai ga Hajjo da Addah da Momy sun shigo a rikice. dan duk wanda yake a gidan yaji ihun Nu'aymah saboda dare yayi. Sai kuma ga matan Abba Musbahu su maman Yusrah, suma Samarin gidan duk sun shigo sai dai sun dakata a a falo.
   Hankalin kowa ya tashi da ganin wannan jini. Ga dare ya fara.
Hajjo tace, “Mafita ya kamata mu nema ba wai koke-koke ba. Ya kamata a tado su Ahmadu dan a tafi asibiti”.
   Addah data maida Nu'aymah jikinta ta share hawayen da ke ziraro mata itama da faɗin, “Hajjo inaga a kira Doctor Sale tunda nan kusa yake shi. amma yanzu ko asibiti akaje zaiyi wuya a samu likitan kirki. Gashi yarinyar nan tana ciki wani hali”.
   Dukansu sunyi na'am da zancenta. hakan ya saka Abban Abdallah fita dan ya kiran Doctor Sale a waya. A falo ya wuce samarin gidan tsaitsaye jigum-jigum. Kusan a tare suka shiga tambayarsa mike faruwa?.
   A taƙaice ya basu amsa yana ƙoƙarin kai waya kunnensa.

     Cikin mintunan da basu gaza talatin ba Doctor Sale ya iso. Malam ƙarami ne yaje ya shigo da shi, yay masa iso har ɗakin Nu'aymah. Zuwa lokacin su Momy nata ƙoƙarin saka abu ana kwashe jinin da har yanzu bai dai na zuba da ga jikin Nu'aymah ba. Su baba malam kuma sun koma da ga ƙofar ɗaki. 
  Ko gaisuwa bai tsaya sunyi ba ya shiga. Su Umm duk suka fito aka barsa da Addah da Umman su Yusrah a ciki. Ƙoƙarin tsaida jinin ya farayi, kafin ya fara bama Nu'aymah taimakon gaggawa.
 Kamar wasa sai da ya kwashe awa guda domin ƙoƙarin ceto ta, Umman Yusrah nata gyara wajen, Addah kuma na riƙe da Nu'aymahn har yanzun. Jinin an samu ya tsaya, harma an saka mata ƙarin ruwa bayan an samu ta farfaɗo. Fita yay ya basu waje dan su ƙarasa gyara mata jikinta.

     Yana fitowa duk suka yo kansa suna tambayar yaya jikinta. Doctor Sale ya sauke ajiyar zuciya yana faɗin, “Alhmdllh malam ku kwantar da hankalinku. Komai ya dai-daita, sai dai kuma anyi asarar cikin da ke jikinta. Nayi iya ƙoƙarina na ganin cikin bai dalwantaba amma hakan ya gagara, sai dai haƙuri”.
 Ga ba ɗayansu wani irin kallon rashin fahimta suke masa. Cikin ƙarfin hali Hajjo tace, “Kai ɗan nan bamu fahimci zancenka ba. Miya haɗa Zainabu da ciki kuma? Ko kuwa kana nufin wani ciki dai bana haihuwa ba?”.
    Shima ɗin dai kallon mamakin yake mata, kafin cike da son fahimtar da ita yace, “Mama ina nufin ciki na haihuwa mana, ko bakusan tana da shi ba ne?”.
    Kallon juna suka shiga yi ƙirjin kowa na bugawa da sauri-sauri musamman ma Baba malam da Umm da Hajjo. Da rawar harshe Umm tace, “Ya zakace ciki a jikin Nu'aymah?”.
      “Ikon ALLAH! Hajiya wlhy ciki ne da ita ɗan sati shida ma kuwa”.
   Umm zata sake magana baba malam da zufa ke karyo masa ta ko ina a sannan jikinsa yay saurin katseta da faɗin, “Doctor yanzu wane hali take ciki ita?”.
    “Ah Alhmdllh malam, yanzu haka tama farfaɗo, na kuma saka mata ruwa da zai sakata barci, zuwa da safe idan ALLAH ya kaimu zan dawo na sake dubata sai na taho da magungunan da ya kamata tai amfani dasu. Zuwa da yamma idan taji ƙarfin jikinta za'a kaita asibiti dan na sake dubata da ƙyau, a kuma yi mata wankin ciki, dan gaskiya ɓarin yazo mata da matsala kamar”.
  “To shikenan, mungode sosai Doctor, ALLAH ya saka da alkairi”.
  “Amen” Doctor Sale ya amsa saboda jin daɗin addu'a daga babban malami irin baba malam. Daga haka yay musu sallama ya tafi ya barsu da ruɗani.

  Tun fitar Doctor Sale kowa ya kasa yin ko motsi. Sai ma Umm da hajijiya ke ɗauka kaɗan-kaɗan ce ta ɗan zauna jin zata faɗi. Cikin ƙarfin hali Hajjo ta shiga ɗakin Nu'aymahr, ta iske su Addah sun kammala kimtsata harma sun lulluɓa mata bargo, ga ƙarin ruwan da aka saka mata yana tafiya dai-dai.
   “Kunga kuje ku kwanta dare na ƙara nisa. Tunda ALLAH yasa ta samu barci. Suma sauran ku sanar musu suje su kwanta”.
  Babu musu sukai mata sallama suka fita. Su da basusan mike faruwa ba sai suka shiga sake kwantar musu da hankali akan jikin Nu'aymahn da sauki. Hajjo ma tace kowa yaje ya kwanta.
    Su Abban Adawiya ne kawai sukace Alhmdllh, amma babu wanda yay yunƙurin tafiyar sai da Baba malam yay magana. Har kowa ya gama ficewa da ga sashen baba malam da Umm basu iya motsawa ba. Sai bayan kusan mintuna goma sannan ya kama Umm ta miƙe da ƙyar. Ɗakin Nu'aymah suka shiga. Hajjo dake zaune ta zubama Nu'aymah ido ta ɗago tana kallonsu.
 Saurin yin ƙasa da kai Umm tayi, dan sai yanzu me wasu zafafan hawaye suka sami damar ziraro mata. Har ga ALLAH zuciyarta ta shiga cikin matsanancin ruɗanin bayanin Doctor Sale. Wani sashe yana gaskatawa wani sashe na ƙaryatawa. Hakama baba malam a matuƙar ruɗanin yake. Amma da yake shi namijin duniya ne sai ya shanyeshi tsaf dan a ganinsa yana buƙatar lokacin yin tunani akan hakan..........
  Hajjo ce ta katsesu da faɗin, “Ban yarda da wannan maganar ta likitan nanba, duk da kuwa koni jinin ya matuƙar tsoratani tunkan bayaninsa. Sai dai hakan bashine ke nufin mu amince da cewa ciki a jikin Zainabu ba. To ta yayama hakan ta faru? A ina kuma? Yaushe kuma?”.
  Kan baba malam a ƙasa, muryarsa a matuƙar cinkushe da tashin hankali yace, “Inna bazamuyi saurin ƙin gaskatawaba, tunda kinga ai aikinsane hakan”.
  “Duk da aikin nasa ne ban yardaba. Sai an nemo wani likitan ya sake dubata tukunna. Kokuma muje asibiti da safe idan ALLAH ya kaimu”.
   Basu iya mata musu akan hakanba da ga shi har Umm da bata iya furta komai ba har yanzun. 

WASHE GARI

     Da safe Doctor Sale ya dawo gidan zuwa 8:30 kamar yanda yay alƙawari. A lokacin Hajjo ta gyara Nu'aymah da kanta. Yayinda Rabi ta sake tsaftace ɗakin ita kuma.
   Ya dubata yanda ya kamata, ya kuma tabbatar musu komai Alhmdllh dan UBANGIJI ya sauƙaƙa al'amarin. Ita dai Nu'aymah ba wani fahimtarsu take ba, dan batasan ainahin abinda ya sameta ba bayan ciwon cikin da zata iya tuna tayi kafin gushewar hankalinta.
 Ya bada magungunan da zatay amfani da su, da waɗanda bashi da su za'aje a sayo. Daga haka yay musu sallama akan da yamma zai dawo ya sake dubata idan ya taso aiki. Godiya baba malam yay masa. Hajjo da Nu'aymah dai basuce komai ba. Hakama Umm da tun daren jiya da hankalinta yabar jikinta har zuwa yanzun bai gama dawowa ba.

    Baba malam baiso maida hankali akan maganar hajjo na nemo wani likitanba. Amma ganin ta matsa sai ya bi umarninta suka kira wani Doctor Faisal abokin Ahmad. Wajen ƙarfe goma na safen shima ya iso, a lokacin an maida Nu'aymah sashen hajjo.
  Shima dai sun bashi dama yayi aikinsa yanda ya kamata. Kafin daga bisani yay zaman basu bayanin daya matuƙar tada musu hankali akan result ɗin shima. Ya tabbatar musu da gaske Nu'aymah ɓarin ciki tayi ɗan sati shidda da wasu kwanaki, amma babu wata matsala tattare da ita, magunguna kawai zataita sha jikinta zai koma normal.
  Har ya kai karshen bayaninsa babu wanda ya iya motsawa a falon, sai hajjo ce tai ƙarfin halin masa godiya.
 Bayan wucewar Doctor hajjo ta sake tabbatar musu shima bata yarda da nashi aikinba. Duk yanda baba malam yaso fahimtar da ita tace bata yarda ba. A yanzu sai su ɗauki Nu'aymah suje asibiti kawai, kuma na gwamnati take so.
Ɗari bisa ɗari su Abba Musbahu sun yarda da maganar hajjo, dan suma zukatansu sam basu aminta da maganar ɓarin cikin Nu'aymah ba sam. Sunfi baba malam yawa, dan haka dole yay shiru ya barsu. Amma a ƙasan zuciyarsa bai son sake fitar maganar kuma dan hakan tamkar tonama kansu asirine sukeyi, tunda yasan ba duka likitocinne zasu iya barin maganar a cikinsu ba duk da yasan basusan Nu'aymah bata da aure ba.

     Bisa matsawar hajjo suka ɗauki Nu'aymah da sam jikinta babu ƙarfi zuwa asibiti. Kasancewar su manyan mutane da ake girmamawa basu wani sha wahalar ganin likita ba, a yanzu kam mace ce ma Doctor Halima. Itama ɗin dai ta gunar da aikinta cike da ƙwarewa. Bayan kamar awa biyu ta basu samako dai-dai dana su Doctor Sale. Dan ta sake tabbatar musu da Nu'aymah tayi ɓarin ciki ɗan sati shida da wasu kwanaki dai, harma ta ɗora da faɗin Nu'aymahr na buƙatar hutu sosai da yawaita cin abinci mai inganci saboda jinin data zubar.
    Ba ƙaramin tashin hankali suka sake tsintar kansu ba a wannan karon kam. Dan ko masu tatsuniya sunce Ƙurun ƙus, anzo ƙarshe. Hajjo mai gardamar bata yardanba a yanzu sai bata iya cewa komai ba. Haka suka tattaro suka taho, dama ita da Ahmad da Naser da Abban su Abdallah da Addah ne suka je. 
    Ganin Hajjo na sharar hawaye Nu'aymah da ke magana da ƙyar saboda rashin ƙarfin jiki ta matsa da son jin mike damun kakar tasu?. Banza tai mata, hakan yasa tunanin Nu'aymah ko hajjo bataji ba ne sai ta sake maimaitawa.
    Tsawar data sakata ɗinke bakinta Hajjo tai mata, ta kuma ja mata dogon gargaɗi akan ta barta taji da abinda ya dameta. Shiru kawai Nu'aymah tai tana kallon hajjon, a ƙasan ranta ko fal tambayoyin mike faruwa ne?.
Koda suka iso gida Addah ce ta taimakama Nu'aymah zuwa sashen hajjo, inda suka iske Abdallah da ya dawo gidan tare da sauran samarin gidan suna zaman jiran tsammanin dawowarsu.
     Kowa ransa babu daɗi ya shiga yima Nu'aymah sannu, yayinda Yah Ab ya kafeta da idanu kawai yana kallo. Itama dai kallon nasa takeyi. a ƙasan ranta kuma tanajin daɗin dawowarsa gidan. 

  Basuyi zaman mintuna biyar ba baba malam da sauran ƴan uwansa suka shishshigo harda Umm ma da sauran matan gidan dan Hajjo ce ta aika kiran kowa. Sai dai babu yaran gidan da ƴammata. Yaseer ma dake falon zaune tun ɗazun korashi waje akayi, Abba Musbahu yace yaje ya tattara yaran su wuce islamiyya.
     Shiru falon yayi kowa na jiran mi hajjo zata faɗa, Nu'aymah da ganin ita ba'ace ta tashi ta fitaba taita binsu da kallo a ƙasan ido tana mamakin yanda fuskar kowa ke ɗauke da ruɗani da tashin hankali........
   Maganar Hajjo ce ta katsema Nu'aymah tunani.
    “Alhamdulillahi, kamar yanda na buƙaci zuwa asibiti dan tabbatar da abinda zuciyata ta kasa gaskatawa ga shi munje mun kuma dawo. Sai dai abin razanin da tashin hankalin shine babu banbancin magana tsakanin likitocin farko da wadda ta duba Zainabu a yanzu. Itama ta sake tabbatar mana cewar Zainabu ɓarin ciki tayi ɗan sati shidda........”
   “What?!!!”.

Nu’aymah ta katse hajjo a zabure tana miƙewa zaune zumbur tamkar ba itace kejin kamar iska zata ɗauketa ta faɗi ba yanzun. Jikinta na matuƙar rawa tace, “Hajjo ban ganeba dan ALLAH! Wace Zainabu kike magana badai ni Zainab ɗinba?”.
Matsananciyar tsawa baba malam ya daka mata, ai bama tasan ta koma ƙasa rib ba ta zube a carpet saɓanin kujera da take kwance a kai ɗazun. Baba malam ya nunata da yatsa yana faɗin, “Zainab!! Wlhy tallahi kinji na rantse, inhar na sakejin bakinki batare da an baki izinin magana ba sai kinyi nadama”.
Babu wanda ya iya ko motsi, dan jin ainahin sunan Nu’aymah a bakin baba malam ya tabbatar musu da lallai magana tazo iyaka. Ita kanta jin sunan daya kiratan ya saka zuciyarta ƙara gudu da tsitstsinkewa lokaci guda, wani bahagon tsoro da ruɗani suka da ɗa mamaye dukanin gaɓɓanta.
Hajjo data juyo tana kallonta tace, “Zainabu bama buƙatar wani ja’inja ko rantse-rantse, nan gurin duk zuri’armune babu wani bare a ciki. ki daure ki faɗa mana wanda ya aikata miki wannan ɓarna. Shin da ganganci ne kokuwa fin ƙarfinki aka y? Wanene uban cikin nan da ya salwanta jiya?”.
Sake rikicewa Nu’aymah tayi, jikinta na rawa tace, “Wlhy hajjo, na rantse da UBANGIJIN al’arshi ban taɓa aikata abinda kuke tuhumata da shi ba. ALLAH shine shaidata ni banda ciki………”
Wuƙa sharɓeɓiya Abba Musbahu ya fiddo ya nunama Nu’aymah, sai ƙyalli take da ɗaukar ido, mai kallo daya ganta yasan ta cancanci a kirata da suna GAYAWA JINI NA WUCE.
“Nu’aymah kinga wannan wuƙar ko?”.
Kai ta ɗaga masa da sauri jikinta na cigaba da rawa.
Ya jinjina kansa da cigaba da faɗin, “Inhar kikace zaki mana wasa da hankali to nan tsakkiyar falon nan zansa su Abdallah su kwantar min dake na yankaki kamar yanda ake yanka ragon layya. Ke dawa kuke aikata wannan shaiɗancin anan gidan…..?”
Kai Nu’aymah ta shiga girgizawa tana kuka tamkar ranta zai fita. Bakinta kuwa sai wani irin karkarwa yakeyi kamar laɓɓanta zasu zubo ƙasa. Ta buɗe baki zatai magana sai kuma ta sake rushewa da wani sabon kuka.

 Kamar daga sama sukaji a bayansu ance, “Malam nine kawai zan iya baku wannan amsar idan ita ta gaza baku..........”✍

????????To wane majanunun ne kuma wannan?.


ZAFAFA BIYAR 2021


Hafsat miss xoxo????
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).????????

      Mamu gee????

MIN ƘALB!!????????

    Hafsat rano????

ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!????????

    Safiyya huguma???? SIRAƊIN RAYUWA????????

     Bilyn Abdull????

SARAN ƁOYE????????

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka????????????????

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????

09033181070

????????????????????????????????????????
TEAM—-ZAFAFA BIYAR????????????????

ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????.
[5/25, 3:17 PM] +234 703 121 9749: No. 36

LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana????????.

KAWATA INA KIKA KOYO HADADDUN CAKES DA GIRKUNA NE HAKA? KINGA ABINCIN NAN NAKI DA NAYI TAKE AWAY BABAN AMEER BAKIGA YADDA YAKE SANTIN SABA, KWANA BIYU INA GIRKI AMMAN NAKI DAI YAKE TA SANTI, YACE LALLAI KAFATA KAFARKI KI RAKANI INDA KIKA KOYO

TAB! LALLE MAMAN SUDEIS AN BARKI A BAYA, AI WAJEN UMMU AYMAAN’S KITCHEN!NA KOYO HADADDUN BIRTHDAY CAKES, SNACKS, DA ABINCIN YAN GAYU KE HARDA NA NAHIYAR KETARE.. BIKIN ADAMA KANWATA MA ITA NA BAWA ORDER TAYI MANA NA MUTANE DARI BIYAR..

LALLE AN BARNI A BAYA, WAI.. YANZU YA ZANYI NA KOYA DAN ALLAH?

SHA KURUMIN KI MATAR MIJIN TA.. UMMU AYMAANS KITCHEN TA SAKE DAWOWA DA KOYAR DA BIRTHDAYS CAKES AND DECORATIONS WANDA ZATAYI A KWANAKI 2, PRACTICAL CLASS , AMMA IDAN KINASON KOYA TA ONLINE NANMA ZATA KOYA MIKI.

WAYYO ALLAH NA DADI..! YANZU YAUSHE ZAAI WANNAN BONANZA? KUMA NAWANE KUDIN?

NAIRA DUBU 6 KACAL WALLAHI, DUK ABUNDA YA SHAFI HARKAR BIRTHDAY CAKES AND DECORATIONS ZATA KOYAR

BA’ANAN TA TSAYA BA, AKWAI CAKE PARFAIT,
CUPCAKES
SAMOSAS
SPRING ROLLS
MEAT PIE DA DOUGHNUTS.

DUKA TANAYIN NA SHAGULAN BUKUKUWA, TARON SUNA, DANA CI A GIDA DAN MOTSA BAKI, KE HARDA GIRKUNAN DA KIKESON KI KOYA NA NAHIYAR KETARE DANA NAMU GIDA NIGERIA.

KAI NAGODE KAWATA, AWANE GARI TAKE NE?

FARKO DAI GA NUMBER WAYAR TA :08032964266

SANNAN TANA NAN KANO, UNGUWA UKU, LAYIN MAI FATA, ZARIA ROAD KANO.

CLASSES DIN ASABAR DA LAHADI NE KAWATA WATO 5 DA 6 GA WATAN JUNE DINNAN. MAZA FADAWA SU UMMI DAKE KADUNA KICE ZATA KOYAR A ONLINE MA..

KAI AIKO NAGODE DA SANARWARKI KAWATA. SHIN TANA INSTAGRAM?

Eh SUNANTA:
@Ummu_aymaan_kitchen.

TANA TURA KAYANTA A KOINA A FADIN KASAR NAN, INGANCI, KYAU, RAHUSA, LAGWADA GA CIKA CIKI DON DADI SAI UMMU AYMAANS KITCHEN AND CATERING SERVICES

No. 36

………….“Malam nine kawai zan iya baku wannan amsar idan ita ta gaza baku. Amma kuyimin afuwa idan ya kasance na shiga hurumin da ba nawa ba”.
Gaba ɗaya suka juya suna kallon bakin ƙofar har Nu’aymah data fara ganin dishi-dishi cikin idanunta.
Ba kowa bane mai maganar face ɗaya daga cikin amintattun almajiran baba malam mai suna Hamisu. Hamisu ɗan anguwar su Nu’aymah ne, hasalima maƙwaftan junane. Mahaifin su baba malam yayi zaman mutunci da girmama juna da kakansu Hamisu, dan takai harda ɗaukar nauyin karatun mahaifin Hamisun a wancan lokwcin. Sai dai ALLAH bai masa tsahon rai ba, dan ya rasu tun su Hamisu suna ƙanana sosai. Wannan dalilin ne ya saka zuri’ar gidan su Hamisu ta dawo ƙarƙashin kulawar zuri’ar ɗan Jibiya bisa wasulcin da ya barma ƴaƴansu su baba malam.
Tabbas baba malam ya cika wannan wasiyya, dan babu irin ɗawainiyar da bayayi da gidan su Hamisun, har takai Hamisu yana ɗaya daga cikin amintattun almajiransa da sukasan abubuwa masu yawan gaske da ya shafesa, kuma Hamisu har cikin gidan yakan shigo bisa yarjewarsa musamman akan aiko da wani abu cikin gidan idan babu ɗaya daga yaran gidan a tare da shi…

    A fusace Yah Ab ya miƙe yana nunasa da yatsa. Har tdallaken kalma yake wajen faɗin, “Amma kasan wannan matsalace ta family da bata shafekaba ko malam. To ta yayama akai kai kasan cewar ana wannan zancen a gidan nan? da har zaka wani shigoma mutane tsulum batare da neman izini ba sai kace wasu sa'anninka. Wannan ma ai raini ne da keta haddin mutane”.
    Nasir da shima baƙin ciki ya lulluɓe ya miƙe a fusacen yana cewa, “Tabbas maganarka gaskiyace Abdallah, mi zaisa ya.........”
  “Kunga ya isa haka” baba malam yay saurin dakatar dasu ganin yanda Hamisu duk ya muzanta abin tausayi. Ya cigaba da cewa, “Tabbas yayi kuskuren shigowa kai tsaye, amma ina ganin mu bashi dama ƙila mu sami bakin zaren matsalar tamu. Hamisu ya akai kasan da wannan issue ɗin?”.
    “ALLAH ya gafaeta malam ka gafarceni, tabbas nima a yanzu na fahimci nayi kuskuren shigowa babu izininku. Ba komai ya jawo hakanba kuma sai ɗunbin ruɗanin dana tsinci kaina a ciki. Abinda yasa kukaji zancen nan a gareni jiya da daddare na dawo daga inda ka turani kai saƙo. Duk da dare yayi sai naga ya dace nazo na kawo maka saƙon koda ban samu damar maka bayani ba. Da ƙyar ma na samu maigadi ya barni na shigo, to a lokacin dana shigone na samu duk jama'ar gidan a sashenka, na iskeku cikin tashin hankali shine na juya da saƙon gidanmu, sai da safe na dawo kawowa nakejin abinda ke faruwa bisa fahimtar da nai daga maganganun ku. Har fitarsu asibiti akan idonane, wlhy da farko naso ɓoyewa nima, sai dai tashin hankalin danaganka a ciki ne naga ya cancanci na bayyana abinda na sani kodan ka samu nutsuwar warware al'amarin yanda ya dace, ku fita daga ruɗani kuma”.
     Duk da sun gamsu da jawabinsa Naser da Abdallah sai zabga masa harara sukeyi. Baba malam ya bashi izinin ƙarasowa ciki. Da ga ɗan gefe ya durƙusa, ya miƙama Abban Adawiya dake kusa da inda yake Envelope ɗin dake a hannunsa.
Amsa Abban su Adawiya yayi, batare da ya buɗe ba ya miƙama baba malam. Nuni baba malam ɗin yay masa daya buɗe kawai. Abban su Adawiya ya buɗe Envelope ɗin ya ciro hotuna dake a ciki guda uku. Ba ƙaramin razana yayi ba matuƙa, har ta kai yana dubawa hannunsa na rawa.
  Hoton Nu'aymah ne da Yoohan, a ranar farko da tsautsayi ya saka shi taimaka mata lokacin da zata faɗi a ranar salla, har ta kaisa ga kissing ɗinta saboda baki data wage zata masa ihu. Sai rana ta biyu itama ranar daya musulunta. Saina ukun shima dai a ranar farko ne, ya ranƙwafa a kanta suna kallon juna.
   Yanda baba malam yaga ɗan uwan nasa ya shiga wani haline ya sakashi zare hotunan daga hannunsa. A take jinsa ya ƙauracema kunnensa. Hakama ganinsa neman kuɓucema idanunsa yake neman yi. Saurin fara ambaton UBANGIJI yayi yana ƙoƙarin ajiye hotunan Abban Abdallah ya amsa. Shi kam ma na farko kawai ya iya kallo ya miƙama hajjo. Itakam ta jima tana kallon hotunan ko ƙyaftawa batayi, ta haka ne Nu'aymah da ke gani dishi-dishi ta samu damar ganin hotunan gaba ɗayansu a hannun hajjo. 
   Babu wanda ya lura da ita. Sai ganinta kawai sukai kwance ƙasa wanwar. A take falon ya sake rikicewa gaba ɗaya. Duk suka rufu a kanta banda Baba malam da Umm da ko motsi basuyi ba da ga inda suke. Hajjo ma da bata tashiba sai ta maida hotunan a Envelope ɗin batare da ta sake bama kowa ba. Sai ma miƙewa tai ta shiga bedroom ɗinta da su. Babu jimawa ta fito lokacin anata ƙoƙarin zubama Nu'aymah ruwa dan son aga ta farfaɗo. Sai dai kuma ko motsi batai ba balle suyi tunanin dacewa.

  Gidan ya sake cakuɗewa fiye da farko, sai da baba malam ya musu magana sannan suka ɗan nutsu. Tamkar bai damu da halin da Nu'aymah ke a ciki ba ya kalli Hamisu dake zaune tsuru-tsuru yana zare idanu. “Hamisu su waɗanan hotunan ina ka samesu ne haka?”.
  Kansa a ƙasa yace, “Baba malam nine na ɗaukesu da waya gaba ɗaya”.
  “Hakan na nufin komai ka gani kenan Hamisu? Ina nufin duk abinda ke a cikin hotunan nan a gaban idonka aka yisa?”.
    “Eh wlhy duk na gani”.

“To miyasa baka taɓa sanar minba kuma?”.
Jimmm Hamisu yayi kafin yace, “Wlhy ina tsoron ɗaga maka hankaline, tare da gudun abinda zai iya zuwa ya dawo malam. Amma ka gafarceni nayi kuskure ”.
Nannauyan numfashin baba malam ya sauke. kafin a sanyaye yace, “Shike nan jeka abinka. na gode sosai”.
Godiya shima Hamisu yayi ya tashi ya fita.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button