NOVELSSARAN BOYE

SARAN BOYE COMPLETE

 ★★<>★★

Tun wannan zama da akayi Nu’aymah bata sakeji daga bakin kowa ba a gidansu. Dan zuwa yamma ma gidan sai ya sake cika maƙil da baƙi dake ta sake ɓullowa ta kowanne irin kusurwa saboda walimar da za’a gabatar daga ƙarfe huɗu. Hakama su Yah Ab bata sake ganin kowa ba a cikinsu, harma iyayen nasu. Garama Abba Musbahu taji muryarsa bayan la’asar ɗin ya shigo suna magana dasu hajjo a falo.
Ana idar da sallar la’asar mafi yawan mutanen dake cikin gidan suka fice wajen walimar. Anguwar tayi tsit bakajin komai sai karatun alkur’ani Muhammad ƙaninta ke rairawa cikin zazzaƙar muryarsa mai daɗi. Lamo tai a kan gadon hajjo dan bata da sha’awar fita wajen walimar. Fitar tata zai iya fama mata ciwuka masu yawa da suka zame mata gyambo a zuciyarta. Hakan yasa ta zaɓi cigaba da zamanta tunda daga nanma tana iya jiyo komai da ake faɗa tamkar tana a wajen.
A wajen walima kam bayan Muhammad ya gama karatu baba malam ya buɗe taro da addu’a ga amare da angwayensu dama al’umar musulmai gaba ɗaya. Daga nan aka fara abinda ya tara mutane.
Duk yanda akaita ragargaza wa’azi mai ratsa jiki a kunnen Nu’aymah ne, duk ba itace amaryarba sai da ta taya su Aunty Hajarah hawaye. Lokacin sallar magrib nayi akaje akai salla aka sake dawowa. Sake ɗorawa da wasu nasihohin sauram manyan malamai abokan su baba malam sukayi. Daga haka akaci aka sha kowa yay haniƙan, aka kuma raba abubuwa kamar yanda suka saba duk lokacin aurar da yaransu ko yaran gidan marayunsu.

   Lokacin da aka tashi tuni Nu'aymah data koma sashensu tai barci a falon baba malam. Umm bata sani ba, dan tana can wajen taimakawa baƙin da zasu kwana a sashenta samun wajen kwana. Sai da baba malam ya shigo wajen sha biyu sannan ya ganta kwance a doguwar kujerar falonsa ta naɗe waje guda alamar sanyi takeji. Zama yay a kujerar gefen da kanta yake yana kallon ƙyaƙyƙyawar fuskar ɗiyar tasa mai tsananin kama da mahaifiyarta abar sonsa da ƙaunarsa. Ɗan murmushi yayi tare da shafa kumatunta sannan ya miƙe. Batare daya tadata ba ya cire babbar rigarsa ya lulluɓa mata. Yana jinta ta sauke ajiyar zuciya, tare da gyara kwanciya. Shima ajiyar zuciyar ya sauke ya ɗauka remote ɗin ac ya rage mata shi sosai sannan ya wuce bedroom ɗinsa cike da tausayinta.

JUMA’A

      Da asuba baba malam bai wuce massallaci ba sai da ya tada Nu'aymah. Bayan an idar da salla bai jimaba ya dawo dan yau basuyi zaman karatu ba daman. A falo ya iske Nu'aymah inda tai salla tana karatun Al-qur'ani. Zama yay kallonta da sauraren zazzaƙar muryarta da a yau take fita da sanyi matuƙa. Yayi kusan mintuna arba'in sannan Umm ta shigo falon da sallama. Tray ɗin hannunta ta ajiye a gabansa tana kallon Nu'aymahn da mamaki. dan ita dai bataga wucewarta ba. Kallon baba malam tai, ya sakar mata lallausan murmushi tare da maida idanun nasa shima kan Nu'aymah da batasan sunayi ba.
  Zama Umm tai a kusa da shi. Cikin magana ƙasa-ƙasa tace, “Yaushe tazo nan?”. Murmushin ya sakeyi kamar bazaice komaiba, sai kuma ya ɗan sauke numfashi yana riƙo hanun Umm cikin nasa. Cikin wani irin yanayi yace, “Anan ta kwana. Nima na dawo wajen walima na sameta anan da alama bama taje wajen walimar ba”.
       Guntun numfashi Umm ta furzar, batare da tace komaiba ta zare hannunta cikin nasa. Shayin daya saba sha duk irin wannan lokacin ta shiga haɗa masa. Yayinda Nu'aymah keta karatunta batare da tasan mi sukeyi ba. Sai dai tana ɗan jin motsinsu kaɗan-kaɗan, dayake hankalinta baya a tare da sune yasa batajin mi suke faɗa.

    Duk hidimar da ake a gidan da sake cika da yake yi da baƙi Nu'aymah tana sashen baba malam taƙi fitowa. Yau tare da shi ma sukai breakfast. Sashen nasa ma itace ta gyara masa yau. Bayan yayi wanka ya fito ta shiga ta gyara masa bedroom ɗinsa tsaf, ta dawo falo inda yake zaune shida ƙannensa da huhunan goro dana alawa da aka shigo da su, magana suke ƙasa-ƙasa alamar tattauna wani abu mai muhimanci a garesu. Cike da girmamawa ta gaidasu, duk suka amsa mata da kulawa tare da tambayarta yaya ƙarfin jikinta.
 Har zata fice baba malam yace ta koma tai wankan a bathroom ɗinsa tunda mutane sunyi yawa a gidan. Daɗi taji sosai, dan haka ta juya cike da ɗoki ta koma bedroom ɗin baba malam ɗin.

  Tsaf Nu'aymah tai shiri da kayan da Umm ta kawo mata ɗakin baba malam ɗin. Lass ne ɗan ubansu sky blue da akaima ɗinkin riga da zani. Ya zauna mata ɗas a jiki tare da haskaka farar fatarta daketa ƙyalli. Ƴar ramar da tayi sai ta sake fiddo ainahin dogon hancinta da manyan idanunta masu matuƙar haske da cikar gashi. Turaren baba malam dana Umm dake a bedroom ɗin babu wanda bata fesa ba. Hakan yasa take zuba uban ƙamshi tamkar tayi wanka da turare. Gashi cakuɗasun da tayi sai ya bada wani irin shu'umin ƙamshi mai narkar da zuciyar mai shaƙa. Ɗan kwalin ta ɗaura bisa gyararren gashinta da hajjo ta matsa jiya Yah Omar ya kaita wajen wankewa tare da su Amal. Ta saka sarƙa da sauran kayan adon sannan ta ɗauki blue gyalen da aka haɗo mata da shi ta ɗora a kafaɗarta. ta zira flat shoes ɗinta suma blue. Tayi ƙyau sosai tamkar ka saceta ka gudu. Kamar yanda Umm ta gargaɗeta akan idan ta shirya ta fito ta gaisa da baƙi batayi musu ba ta nufi sashen Umm ɗin bayan ta kulle falon baba malam ta taho da key ɗin a hannunta.

   Tunda ta fito jama'ar dake zazzaune a falon Umm keta ambatar masha ALLAH. Ita dai cikin ɗan jin nauyin wasu daga cikinsu ta shiga risinawa tana gaishesu. Masu tsokanarta kuwa ta kasa maida murtani. Saɓanin da da kowa yasan Nu'aymah bata barin saita kwana ga abokin wasa. da kace kule take cewa cas. Amma yau sai ga bakin ya mutu murus sai ɗan sassanyan murmushi kawai take musu a taƙaice.
  Har bedroom ɗin Umm ta shiga inda ƙanen Umm da yayunta ke cike da shi. Nanma gaidasu ta shigayi. Sukam sunata amsawa cike da ƙaunar ɗiyar ƴar uwar tasu. Aunty Hibba dake cin abinci ta jawo hanunta ta zaunar kusa da ita tana faɗin, “Zauna kici abinci. Ni wannan ramar taki sam banason ganinta dota”. A ɗan shagwaɓe Nu'aymah tace, “ALLAH na ƙoshi Umma, munyi breakfast tare da Abba, kuma naci sosai ki tambayi Umm ma kiji”.
 “Eh breakfast ai tun ɗazunne, kusan awa uku kenan, wannan abincin rana ne. Ke dama nasani da masifar son masa”. Duk yanda Nu'aymah taso zamewa sai da Aunty Hibba ta dinga bata masar a baki tare da naman. Sai gashi kuwa taɗanci babu laifi ta kuma shanye ƙaramar roban zoɓo data ɗauka.

★★★★

    A ɓangaren su baba malam kuwa duk sun ɗunguma massallacin juma'a inda za'a gudanar da ɗaurin aure bayan sallar juma'a insha ALLAHU.
  Massallacin ya cika danƙam da manyan mutane daga kowacce kusurwa ta Najeriya harma da wasu ƙasashen ƙetare. Tun daga kan malamai, ƴan kasuwa, harma da masu mulki. Sai abokan arzuƙa da ƴan uwa na kusa dana nesa. gayyar anguna dana jama'ar gari da girma da kimar su baba malam ɗince ta tarasu a wajen.
   Bayan kammala sallar juma'a akai ɗaure-ɗauren aure ciki harda na ƴaƴan su baba mala su Aunty Kubrah. Ana kammalawa manyan baƙi suka ɗunguma babban hall ɗin da aka kama domin gudanar da ƙwarya-ƙwaryar walimar cin abinci.
  Walimar ce ta jasu har sai bayan la'asar sannan suka koma gida da wasu tawagar baƙin da ba'a ranar zasu wuce gida ba.

 Zuwa yanzun kam gidan su Nu'aymah ya sake cika danƙam da mata, dan yau ne Addah ke nata yinin bikin. Hayaniya akeyi sosai babu maijin wani. Dan tun bayan ɗaurin aure su Omar sukaje gidan da labarin yanda komai ya kama.
Nu'aymah na tsakkiyar dangin Umm har yanzu. Sun sakata a tsakkiya anata hirar zuminci cike da farin ciki. Wata Gwaggon su Umm ce, data kasance kaka ga Nu'aymah ta shigo ɗakin tana guɗa. Da mamaki duk suke kallonta har suna rige-rigen faɗin, “Gwaggo an ɗaura ne?”. 
   “Ƙwarai da gaske an ɗaura. Yanzun ma haka ƴan ɗaurin aure sun dawo, kuma harda sabon albishir na ƙarin amarya”. 
    Aunty Fareeda tace, “Ƙarin amarya kuma Gwaggo? A cikin yaran gidan dai?”.
   “Ƴarku ma kuwa” ta sake basu amsa tana cillara wata sabuwar guɗar. Kafin su gama fita daga ruɗani su Nanah suka shigo suna ƙwala kiran “Nu'aymah amarya”.
 Dakatar dasu Aunty Hibba tayi. “Kai mufa kuna sake ɓatar damu, Gwaggo wai mike faruwa?”.
Da sauri “Raudah tace, “Momy baku san Nu'aymah ma an ɗaura mata aure ba yanzu tare da su Aunty Hajarah. Yanzun ƴan ɗaurin aure da suka dawo suke faɗa ai”.
    A take ɗakin ha harmutse da murna da taraddadin wanene angon? Miyasa kuma aka ɓoye musu, dan su dai basusan da auren ɗiyar ƴar uwar tasu za'ayi ba. Duk sunzone yima Addah baici kasancewar zumincine mai ƙarfi da kowa ya sani a tsakanin Umm da ita. 
   Tunda aka fara wanan kace nace Nu'aymah ta ɗora hanunta saman kai ta riƙe. Cusashi tai a tsakanin cinyoyinta jikinta na wani irin tsuma. Ga kanta ya fara sara mata sama-sama. Duk yanda taso ta daure ta kasa. Dan haka cikin ƙarfin hali ta shiga laluben wanda ke a kusa da ita. Cikin sa'a ta damƙo hanun Aunty Magajiya yayar Umm. Hankali tashe Aunty Magajiya ta dubeta, sai kuma yanda taga jikin Nu'aymahr na karkarwane ya sakata ambaton ‘Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un’ da ƙarfi.
 Kusan mafi yawan ƴan ɗakin sai hankalinsu ya dawo wajen. A take kuma sai duk sukai tsitt tare da zabura kan Nu'aymah......

      Gwaggo Ramma ce ta hana ɗaga maganar mawuyacin halin da Nu'aymah ke a ciki a gidan har lokacin da su baba malam suka dawo. Dan Umm ma bata fasa kai da kawowar da takeyi tsakanin sashen Addah da sashentaba saboda son ganin baƙi kowa ya samu abinci. Yin komai takeyi cike da ƙarfin hali. Sai ta fakaici idon mutane take share hawayen dake cika mata idanu. Duk da kuwa ita tasan da maganar auren. Kuma tana cikin masu goyen bayan ɗaurashi a yau ɗin saboda wasu dalilainsu ita da baba malam da hajjo.
Key da baba malam bai gani bane a inda suke ajiyewa ya sakashi kiran wayarta. Cikin sa'a kuwa wayar tana a tare da ita. Dan haka ta ɗaga ya sanar mata gashi ya shigo amma baiga key ba. Ta kira masa Nu'aymah ko ta canja masa waje.
  “To” kawai tace masa ta yanke wayar.
   Ɗakinta ta fara shiga inda danginta ke zaune jigum-jigum da Nu'aymah shimfiɗe bisa gado tana fidda wahalallen numfashi tamkar mai Asthma. Aunty Juwairiyya sai shafa mata ruwa take a fuska wasu kuma na tofa mata addu'oi. Wani Key ɗin ta ɗauka a drawer ta fita batare da tace musu komaiba ta fice.
     A kallo ɗaya baba malam ya fahimci akwai matsala. Tunkanma ta buɗe ya shiga jero mata tambayoyi akan mike damunta?. Sai da ta buɗe ƙofar suka shiga sannan tai masa bayani. Shima hankalinsa ne ya tashi, dan haka yace taje su maido Aymah sashensa, karsu bari kowa kuma ya fahimci halin da ake ciki. Bara ya kira Doctor.

    Tunda aka dawo da Nu'aymah sashen baba malam ALLAH ya bata ikon ganinsa saita damƙe hannunsa tana cigaba da jujjuya kanta da fisgar numfashi a wahalce. A hankali take magana wadda idan ba'a kusa da ita kakeba ma bazakajita da ƙyau ba.
    “Abbah kaina, kaina zai fashe Abbah. Kamin addu'a kaina zai fashe, Abba kamar ana kartamin ƙarfuna a ciki. Innalillahi... Abbana zan mutu..”
    Cikin rawar harshe baba malam yake girgiza mata kansa da haɗiye abinda ke cinkushe masa maƙoshi da ƙyar. “Bazaki mutuba Mamana kinji, daina magana kiyita addu'a a ranki insha ALLAH ga Doctor nan zuwa kinji”. Ya ƙare maganar da saka ɗan yatsa ya ɗauke hawayen da suka tsatstsafo masa saman fatar ido. Hajjo da Ananah ma hawaye sukeyi. Haka su Abban Abdallah ma duk zukatansu suya suke da tausayinta.
   Sallamar da akayi a bakin ƙofarne ya sakasu duk kallon ƙofar tare da amsawa. Ahmad ne ya fara shigowa, yana sanye cikin tattausan farar shadda harda babbar riga. Har yazo tsakkiyar falon sai kuma ya ɗan juya ganin wanda suke tare bai biyosa ba. “A'a Doctor shigo mana”.
  Kusan seconds biyar kafin a ɗaga labulen ya shigo bakinsa ɗauke da tausasa kalaman sallama. Sanye yake cikin wata shegiyar bugaggiyar shadda getzner kalar royal blue. Wando da riga harda babbar riga. Sai hular zanna daya murza itama royal blue data samu nutsatstsiyar saƙa. Hatta da agogon dake a tsintsiyar hannunsa kalar blue ne. Wanda bai saniba sai ya ɗauka wannan ɗin itace shigarsa dama can tun fil azal. yayi ƙyau harya gaji a cikin kayan. sun sake fidda masa kwarjini da cikar haiba da kamala. Farar fatarsa ta sake haskawa tamkar wata ɗan daren sha biyar. Yanda sajen fuskarsa da kwantaccen gashin kansa dake baƙi siɗik kwance a ƙeyarsa suke ɗaukar ido babu tababa zaka iya sakashi a jinsin larabawa. Idanba faɗa maka akaiba bazaka taɓa yarda Dr Yoohan ɗan gidan Papa da Madam Chioma ne ba wanda ko hausar bai gama fahimtar inda ta dosa ba balle akai ga larabci.
  A hankali ya cigaba da tako ƙafarsa dake sanye cikin baƙar safa cikin falon, dan ya cire takalman a ƙofa. 
     Tunda yay sallama  Ananah da Hajjo suka zuba masa idanu cike da jin daɗin isowarsa a kan lokacin da ya dace. Umm kam kallo ɗaya tai masa ta maida idanunta ƙasa tana sauke ajiyar zuciya a hankali. Cikin girmamawa ya gaida su Hajjo. Suma sun amsa masa da kulawa harda ƴar tsokana. Kaɗan gefen bakinsa ya motsa alamar murmushi. Dan bayan gaisuwar baiji mi suka faɗa ba sam tunda da hausa sukai magana.
  Baba malam da ya tashi daga inda yake zaune ne ya nuna masa alamar ya zauna anan. Bai musaba ya zauna idanunsa akan Nu'aymah da har yanzu take riƙe da kanta. Sai da yay mata kusan kallon minti ɗaya da wasu sakanni sannan ya ɗago. Ɗan kallonsu yayi sai kuma ya sake maida idanun nasa kan Aymah.
  Da sauri Ananah tace, “Ɗan nan ko akwai matsala ne?”. Ya ɗanji wani abu daga zancen nata. Sai dai bai iya haɗasu a jimlace yanda zai fahimta ba. Hakanne ya sakashi kallon Ahmad dake ɗan murmushi. Faɗa masa abinda tace yayi, hakan yasa Yoohan cewa, “No babu damuwa Mama. Sai dai a ringa kula, indai zata ringa shiga irin wannan yanayin akwai matsala. Aikinmu zai dinga komawa baya”.
     “Yoni yaro bafa jin wannan yaren naku na masu jajayen kunne nake ba, kai Amadu fassara mana mi yake cewa”. Ananah ta faɗa da iya gaskiyarta.
  Gaba ɗaya su baba malam murmushi sukayi dajin zancen Ananah. Umm ma saita nufi ƙofar fita ita dai tana nata murmushin. Cike da ƴar tsokana Ahmad yace, “Gaskiya Abba kubani kwangilar maida Hajjo da Ananah makaranta, dolene su fara jin turanci kwanan nan”.
 Daƙuwa Abban Adawiya yay masa. Yayinda Hajjo ta talle masa ƙeya tana faɗin, “Kaci gidanku Ahmadu. Yo turancin banza turanci wofi. tunda munajin yaren da ALLAH yayimu a cikinsa muna kumajin yaren dayafi kowanne daraja, yaran MANZON ALLAH larabci ai mungama nasara. Kune kuka ɗauki amanar kanku kuka miƙama masu jan kunne shiyyasa gashinan kullum sai hanyoyin wajiga rayuwarmu suke ƙara ƙirƙirowa. Shima Yahaya ɗin kwanan nan dan gidansu sai ya fara iya hausar”.
  Duk da Yoohan bajin abinda ta faɗa yay ba, baisan sanda murmushi ya kufce masa ba ganin yanda take masifa akan Ahmad tana duddungure masa kai hularsa har tana matsawa baya. Su Baba malan kuwa sai zuba murmushi sukeyi. Sosai abin nasu sai ya birgesa, musamman daya tuna nasa kakannin da kullum babu abinda sukafi ƙwarewa sai masifa da faɗa kamar kajinaye.......
Hannunsa da Nu'aymah ta riƙo ne ya sakashi saurin juyawa gareta. Cikin yanayin ciwo ta sake matse lallausan tafin hanun nasa cikin nata tare da ɗorasa bisa kanta, “Abbah ka riƙemin zai fashe”.
   A hankali Yoohan ya lumshe idanunsa ya sake buɗewa a kanta. Baiyi magana ba, bai kuma janye hannunsa data ɗora akanta ba ta danne da hannunta kuma.
   “Inaga mu bara mu barka kayi aikinka”. Ya tsinkayi maganar Abban Abdallah a cikin kunnensa. Janye idanunsa yay daga kallon da yakema Aymah, sai dai kafin ma ya ɗago su duk sun fice. Hajjo da Ananah da Ahmad kawai aka bari.
Baice komaiba sai hannunsa da yay ƙoƙarin janyewa daga kanta. Amma sai ta sake riƙesa da ƙyau tana faɗin, “Abbah Please karka tafi ka barni, kaimin addu'a kaji Abbana”.
  Sosai tausayinta ya sake lulluɓe su Hajjo. Yoohan ya ɗan matsar da kansa kusa da nata kaɗan, a hankali yace, “Ki daina magana zan baki magani yanzu zai daina insha ALLAH”.
   Tabbas taji muryar ba Abbahn ta bane, amma halin da take ciki bai bata damar banbance wanene ɗinba sam.  
   Kallon Ahmad Yoohan yayi, yay masa nuni da box ɗin da suka shigo yana faɗin, “Brother Please ko zaka iya haɗamin allurar nan?”. “Yes! Doctor babu damuwa”. Ahmad ya bashi amsa yana jawo box ɗin.
  Wata irin zabura Nu'aymah da zancen ya shigarma kunne tayi, batare da sun fargaba suka ganta tsaye bisa ƙafafunta jikinta na rawa. “Bana son allura, Abbah! Abbah! banason allura...” ta faɗa a wahale tana riƙe kanta da hannu biyu duka tai baya luuuu zata zube.
    Cikin zafin nama Yoohan ya miƙe tsayen shima, hakan yasa Nu'aymah faɗawa jikinsa nata jikin na wani irin karkarwa. Saurin riƙota yayi shima yana faɗin, “Relax, Please calm dawn!” 
  Ina batama san yana faɗa ba, kanta kawai take jujjuyawa a ƙirjinsa da faɗin, “Banason allura, Abbah banaso”. 
   “Okay shike nan, kinga baza'ai mikiba, ya isa ki daina magana, tana sa miki ciwo kai”. Yay maganar da ɗaukarta gaba ɗayanta ya maida a kujerar zai kwantar. Sake ruƙunƙumesa tai, sautin muryarta na ƙara fita da ƙarfi wajen faɗin, “Abbah karka bari sumin allura dan ALLAH ” ta ƙare maganar da fashewa da kuka.
 Su dai su Hajjo duk wannan drama dake faruwa suna tsaye ne suna kallonsu, Ahmad dake murmushi yace, “Hajjo kumuje kawai mu barsa da ita, nasan zaiyi duk dabarar data dace yay mata insha ALLAH ”.
 Cike da gamsuwa suka amsa masa. Allurar ya matsa ya miƙama Yoohan da Aymah ta kanannaɗema jiki kamar mage ta samu katifar audiga. “Gashi, bara mu baka waje kai aikinka Doctor ”.
   Yoohan zaiyi magana Ahmad ya ajiye syringe ɗin da sauri yabi bayan su Hajjo da har sun fice abinsu............✍

Likita bokan turai????????.

ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo????
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).????????

      Mamu gee????

MIN ƘALB!!????????

    Hafsat rano????

ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!????????

    Safiyya huguma???? SIRAƊIN RAYUWA????????

     Bilyn Abdull????

SARAN ƁOYE????????

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka????????????????

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????

09033181070

????????????????????????????????????????
TEAM—-ZAFAFA BIYAR????????????????

ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????.

I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p.

LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana????????.

No. 43

…………Ajiyar zuciya ya sauke a hankali jin yanda Aymah take sake tura kanta cikin ƙirjinsa. Ya ɗan lumshe idanu ya buɗe akan dogon gashinta dake ta uban ƙamshi ga ƙyallin mai daya sha masha ALLAH. “Silly girl!” ya faɗa a hankali yana kai bakinsa dai-dai kunnenta. Batare da ya jira amsarta ba ya sake miƙewa da ita ɗauke a hannunsa. Zama ya farayi saman kujerar sannan ita kuma ta koma saman cinyarsa da ƙyau batare da tasan mi takeyi ba. Syringe ɗin da Ahmad ya ajiye ya ɗauka, ɗan guntun ruwan allurar dake ciki ya kalla, ya ɗan yamutsa fuska kaɗan da zare hular kansa ya ajiye gefe. Ya sake kallon Aymah ya girgiza kansa, cikin ƙwarewa da sanin makamar aiki ya kuma turata jikinsa da ƙyau tare da ranƙwafowa ya ɗaura bakinsa akan kunnenta. Wata irin sassanyar iska ya shiga hura mata cikin kunne a hankali, yayinda can kuma hannunsa ke saita inda zai mata allurar batare da ta saniba.
A hankali ta saki wani irin nannauyan ajiyar zuciya da sake shigewa jikinsa, saboda ƙamshinsa na sake jan hankalinta. Hakane ya bashi dama tsira mata allurar dai-dai inda ya dace. Da masifar ƙarfi ta zabura tare da fasa ƙara ta sake damƙesa da ƙyau jikinta na wani irin karkarwa.
Zare allurar yay yana sakin wani lallausan murmushi daya sake fidda annurin fuskarsa. “I am sorry”. ya faɗa a hankali cikin kunnen nata.

    Ihun Nu'aymah duk sai da ya shiga cikin kunnen su baba malam. Duk rumtse idanu sukayi tausayinta na tsargama zukatansu. Sai dai babu wanda yay yunƙurin shiga cikin falon.
   A ɓangaren Yoohan kuwa idanunsa ƙyam akan Aymah dake ta juyi a jikinsa tamkar wata macijiya, sai zufa dake ta faman tsatstsafo mata a goshi. Handkerchief ɗinsa fari ƙal ya fiddo cikin aljihun gaban rigarsa ya shiga share mata zufar, tsahon mintuna biyar suna a haka kafin ta shiga sauke ajiyar zuciya a jajjere, a hankali kuma sai jikinta ya fara saki alamar barci. Cikin ƙanƙanin lokaci ta fara sauke numfashi. Kwanciyar ya gyara mata a cinyarsa yanda zataji daɗi sosai, sai kuma ya kai hannu saman gashinta daya barbaje ya tattaresa cikin hannunsa. Ribbon ɗin ya ɗauka ya ɗaure mata shi a tsakkiya ya nannaɗesa da ƙyau yanda bazai takura mata ba. Baya yayi ya kwanta jikin kujerar shima, ya lumshe idanunsa da sakin sassanyar ajiyar zuciya.
    Shirun da su baba malam sukaji babu motsinsu har tsahon wasu mintuna ne ya saka Ahmad faɗin, “ALLAH yasa dai lafiya naji shiru”. Ɗan murmushi baba malam yayi, ya kalli Ahmad ɗin yana faɗin, “Ai tunda kaji mamana tabar kwakwazo na tabbatar anyi alluran”.
   Kusan a tare duk suka murmusa. Hajjo tace, “Raguwar amarya ba, sai tsiwa a baki amma cikinta fal tsoro, gashi kuma ta zama matar likita sai su ƙarata ai”. Yanzun kam duk dariya suka ɗanyi. Ananah tace, “Ai irinsu dama hakane, zakiga akwai tsiwa amma matsoratane a bugun farko. Ahmadu leƙa kagani”.
  Da to Ahmad ya amsa yana nufar falon. Sallama kusan uku yayi baiji an amsa masa ba. Hakane ya sakashi tura ƙofar a hankali ya shiga. Sai dai daga bakin ƙofa ya tsaya yana kallonsu. A take murmushinsa ya sake faɗaɗa.
   Buɗe idanu Yoohan yayi a hankali tare da ɗagowa zaune sosai yana kallon Ahmad ɗin. Sai kuma ya yunƙura ya ɗaga Aymah cak daga cinyarsa zai miƙe.
  Da sauri Ahmad yace, “No Doctor, kayi zamanka dama na leƙone kawai naga idan komai lafiya. To ashema har tayi barci”. Yoohan daya ƙarasa miƙewa baice komaiba, sai da ya shimfiɗe Nu'aymah a kujerar da ƙyau ya gyara mata kwanciya sannan ya ɗauki hularsa ya maida bisa kai yana bama Ahmad ɗin amsa. “Barrister wannan ƙanwar taka ta cika raki da ragwantaka, saboda allura kawai duk ta jigatani tamin Squeezing ɗin kaya”.
    Ƴar dariya Ahmad yayi yana ƙoƙarin tattare syringe ɗin da komai da sukai amfani dashi. Yace, “A'a Doctor karmuyi haka da kai. Ni na tabbatar maka sai kazo wataran ka sanarmin Aymah jarumace, ballema itama likita zata zama insha ALLAH ”.
  Idanu Yoohan yaɗan waro yana gyara zaman rigarsa, yace, “A hakanne zata zama likita tana tsoron allura tamkar bindiga ɗin? Tab za'aga likitoci kam”.

   Da haka suka fito Ahmad na dariyar zancen Yoohan, shiko Yoohan ya fiske abinsa tamkar ba shine yay maganar ba.
   Kusan duk a tare su Abbah ke tambayar jikin Nu'aymahn. Ahmad yace, “Ku kwantar da hankalinku ita harma ta tafi duniyar barci. Dama ihun na allura ne”.
 Duk kallon Yoohan sukai cike da farin ciki, suka shiga jera masa sannu da godiya. Shi dai kansa a ƙasa yake faɗin, “Uncle karku damu aikina ne ai. Insha ALLAH zata tashi kamarma komai bai faruba dan amfanin allurar kenan. Sai dai a dinga kula dan abu kaɗan ita yanzu zai iya birkita ta, ruɗanin kuma shine ba'a so dan zai maida cigaban da ake murnar samu bayane. komai a ringa mata shi da lallashi”.
  “Insha ALLAHU za'a kiyaye. ALLAH ya saka maka da alkairi, ita kuma ALLAH ya bata lafiya yasa kaffara ne”.
  A tare suka amsa da amin, harsu hajjo da Ahmad ya fassara musu abinda Yoohan ɗin ya faɗa.

     A cikin gida kuwa dai hidimar bikinsu suke tayi, babu wanda yasan abinda ke faruwa da Nu'aymah sai shaƙiƙan Umm da suke a bedroom ɗinta kawai. Suma kuma tunda Umm taje ta sanar musu likitan da zai duba Aymah yazo duk sai suka samu kwanciyar hankali.
   Bayan wucewar Yoohan duk suka shiga har falon baba malam suka ganta. Hakan ya ƙara musu nutsuwa sosai, dan haka suka dawo ɗakin Umm suka cigaba da hirarsu ta zuminci tare da tattaunawa akan auren na Aymah.
   Koda suka koma can baba malam da kansa ya ɗauki Nu'aymah dake barci hankali kwance ya maida bedroom ɗinsa. Sannan ya fito shi da ƴan uwansa suka fice massallaci gabatar da sallar magriba. 

     Biki yayi biki masha ALLAH, dan Addah ta samu alkairi sosai daga wajen abokan arziƙinta. Hakama sauran matan gidan bisa al'adar biki da kowa ya sani suma sun samu rabonsu ga abokan arziƙansu. Harma da Umm da kowa sai yanzu yasan harda gudan jininta. Ana idar da sallar isha'i kuma aka shiga shirya amare. Hajarah da Kubrah. Nu'aymah dai babu wanda yay magana maybe ba yau ba kenan. 
  Kamar yanda kowa ya sani baba malam shike raka duk ƴaƴansu gidan aure. Babu wani gayyar ƴan kai amarya. Duk wanda yake da buƙatar ganin ɗaki yakanje da rana bayan ɗaurin aure ko washe gari idan amarya ta kwana a gidanta. To gasu Hajarah ma tsarin bai canja ba. Dan ana idar da sallar isha'i su baba malam duk suka shigo gida. Sashen Hajjo aka kai amaren, Hajarah nata kuka kamar zata shiɗe. Kubrah kam idanunta ƙyar cikin lifayar da aka naɗa musu. Sai uban ƙamshi suke kamar gidan turare.
  Duka iyayensu da shaƙiƙan ƴan uwa suka taru a sashen Hajjo aka shiga musu nasiha. A yanzunma dai Hajarah kuka take, Kubrah kam kanta dai a ƙasa tana saurarensu. Bayan nasihar da akai musu da gargaɗi mai ratsa jiki akai musu doguwar addu'a da fatan alkairi sannan aka fito dasu. Da motoci uku kacal za'a kai amaren. Motar farko amaren ne a baya sai baba malam da Omar da zaiyi driving. Mota ta biyu iyayene mata na ɓangaren Addah su huɗu, sai yayun Umm biyu, su kuma Malam ƙarami ne zai jasu. Sai motar ƙarshe da Yah Ahmad zai ja ita kuma tsoffin iyaye ne dangin su baba malam a ciki su biyu, sai Umm da momy da amaryar Abba Musbahu. Motar ƙarshe, Abban Abdallah, Abba Musbahu, Abubakar da zai jasu, Uncle Kabeer mahaifin Nasir, sai Uncle Babangida shima dai shaƙiƙinsu ne. 
 Haka suka fita a jere ana bin amare da addu'ar tafiya a sa'a. Dama mafi yawan ƴan biki na kusa duk sunata guduwa suma. Zuwa goma na dare sai hayaniyar gidan ta ragu sosai, wasu sunyi barci, wasu sun tafi.

★★★

    Su baba malam sun fara miƙa Hajarah ne dan itace ƙarama. Gidanta mai ƙyau da tsari a anguwar GRA, kowa ya yaba da addu'ar zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba. Sun sami tarba ta mutuntawa daga dangin ango su bakwai da sukazo tarbar amarya daga can gidan surukan Hajarah. Kasancewar sunsan dokar su baba malam ɗin suma cikinsu harda maza uku. Bayan sun ɗan zauna a falo akai addu'a baba malam ya kama hannun Hajarah har cikin Bedroom ɗinta ya kaita, zaunar da ita yay a bakin gado yay mata addu'a da saka mata albarka. Ya juyo zai tafi ta riƙe hanunsa. Tsayawa yay tare da juyawa jikinsa duk a sanyaye yana dubanta. Haka yake shi, yanada son yara, shiyyasa har ƴayan ƴan uwan nasa ƙaunarsu yake har cikin ɓargonsa. Duk kuma sanda yay irin wannan rakkiyar sai yayi ƙwalla dajin ɗacin rabuwa da yaran nasu ta dalilin aure ƙanin mutuwa.
 Hajarah data buɗe fuskarta ta share hawayen dake silalo mata. Cikin dasashshiyar muryarta tace, “Abbah dan ALLAH inason in roƙeka wani abu”. Kansa ya jinjina mata, yace, “Komi kikeso zan miki inhar baifi ƙarfina ba Hajarah, dan haka faɗamin koma miye kinji”. Sake share hawayenta tayi tana jinjina masa kai. “Abbah dan ALLAH idan yah Abdallah yace bazai maida aurensa da su Adawiya ba karku takura masa”. Jimmm baba malam yay yana kallonta. Sai kuma yace, “Uhm Hajarah miyasa kika buƙaci hakan? Bayan kinsan shi ɗin mai laifine”. “Abbah zan faɗa maka dalilina amma ba yanzu ba, dan ALLAH kuyi mani wannan alfarmar, suma su Abba zan kirasu duk na roƙesu har Hajjo”.
   Numfashi baba malam ya ɗan sauke, sai kuma yace, “Karki damu zan duba na gani, kibar kukan nan haka karya saki zazzaɓi. ALLAH ya baku zaman lafiya”.
Daga haka ya fita ya barta tana cigaba da rabzar kukanta.
  Daga gidan Hajarah saina Kubrah. Itama dai gidan ya haɗu masha ALLAH. Sai dai ita tana da abokiyar zama harda yaranta uku. Amma kowa da sashensa dan gidan babbane. Itama dai an tarbesu da mutuntawa. Baba malam kuma ya rakata har nata ɗakin ya ƙara mata addu'a sannan ya fito suka wuce gida kowa aka barsa da halinsa kuma.

       A ɓangaren Yoohan kam tunda suka baro gidan su baba malam sai ya koma Hotel ɗin da su papa suka yada zango. Babu yanda baba malam baiyiba akan su sauka a ɗaya daga cikin gidajen baƙinsu amma papa ya ƙi fir. Wajen ɗaurin aurenma da yake jirgin 12 suka shigo suna isowa ana idar da sallar juma'a, hakan yasa saida ma aka ɗan jirasu kafin su iso wajen ɗaurin auren daga airport. Yoohan ne kawai yazo tun goma na safe. Bayan an ɗaura auren aka ɗunguma har dasu hall ɗin da su baba malam ɗin suka tanada domin gudanar da walimar cin abinci. Anan akaci aka sha cike da farin ciki. Babu wanda zai kalli baba malam da papa yace akwai wani abu na rashin jituwa a tsakaninsu. Suma su papan sun sake sosai a cikin mutane bazaka taɓa cewa ga daga addini ko ƙabilar da suka fito ba. Musamman ma daya kasance a cikin manyan mutanen ƴan ɗaurin aure akwai waɗanda suke da alaƙa dasu sosai musamman ma ƴan siyasa. Wasuma papan ya sake gayyatarsu bayan gayyatar da baba malam yay musu.
  Bayan an kammala walimar ne mafi yawan baƙin suka kama gabansu, su kuma su papa da tawagarsa suka nufi hotel bayan sunƙi amsa tayin baba malam. Hakan yasa yanzun acan Yoohan ya iskosu. Sai dai kasancewar jirgin ƙarfe bakwai da rabi zasu bi zuwa Abuja duk ya iskesu sun fito shi ma suke jira. Basu wani zauna zaman ɓata lokaci ba duk suka shiga motocinsu. zasu kaisu airport ɗinne su dawo su kwana da safe suma su ɗauki hanya. Dama da safe suka taho kafin su papan.
      Ko mintuna goma cikakku basuyi da zuwa airport ba jirginsu ya lula birnin tarayya abuja. Inda a canma dai ɗaukarsu akazo akayi. Abokan papa kowa ya nufi gidansa, papa da Gebrail, Richard, Joseph, Godwin, Osin, Uncle Marcel, Uncle Anthony, kuma suka nufi gidan papan. Sai Solomon jelar Yoohan????.
 Sun iske gidan a hargitse da rikicin da suka bari su Mama Debora nayi akan auren Yoohan ɗin. Faɗa mai lasisi sosai akasha tsakanin tsofin biyu. Kuma duk akan sufa basu yarda jikansu ya aure bahaushiya mai salla ba. Momy da papa ya gama sanar mata komai akan manufar auren tanata ƙoƙarin fahimtar da su duk da kuwa jitake kamar tafi kowa shiga tashin hankali, amma sun ƙi fahimta. Sai kiran dangi suke na nesa a waya suna sanar musu. Miracle kam yanke jiki tayi ta faɗi a sume dama tunkan su Yoohan su wuce. Akace kuma ya dubata ya tsallake yay ficewarsa batare daya ko tanka musu ba.
Hakan daya aikatane ya sake fusata kakanninsa sabon wutar bala'i ya ƙara ruruwa. Sai asibiti aka kai mira bayan wucewarsu ɗaurin auren.

    Tunda Yoohan ya shigo idonsa ya sauka akan kakannin nasa sai ya sake tsuke fuska fiye da yanda take. Ɗauke kansa yayi ya nufi upstairs duk da yaga yanda suka miƙe zumbur suna kallonsa cike da wutar masifa.
 Cikin yare, mama Debora ta shiga ƙwala masa uban kira kai kace gidan zata fasa. Ko waiwayensu baiyiba ya buɗe ƙofarsa ya shige bayan ya amshi babbar rigarsa a hannun Solomon dake biye da shi a tsorace. Ruf ya rufe ƙofar ya murza mata key yama barshi a ciki dan kar wani yay tunanin amfani da wani key ɗin.
   A falo ya zube yana sauke numfashi da jan dogon tsaki. Jin an fara buga ƙofar tasa da ƙarfi ana masifa ya kuma jan wani tsakin ya miƙe ya nufi bedroom ɗinsa. Bai zaunaba anan, kayansa dake ta zuba ƙamshinsa dana Nu'aymah ya cire yanata faman lumshe idanu. Dan a matuƙar gajiye yake. Babu abinda yake buƙata a yanzu sama da kwanciya. Ya gaji harma baisan tataya zai faɗa ba a tausaya masa. Ga ihun su Mama debora da yake jiyowa sama-sama yana neman saka masa ciwon kai. ‘Nasan maganinku ai. Kwanan nan zaku bar gidan nan ku koma inda kuka fito’. Ya faɗa a fili yana harar ƙofar kamar sune wajen tsaye.
   Daga haka ya shiga yay wankansa kamar yanda ya saba. Ya jima bai fitoba daga bayin kamar mai naƙuda????????. Sai kuma gashi ya fito a yanayin gajiyar da yake ciki. Sama-sama yay shirin barci cikin tausasan kayan barci, yana fesa turare wayarsa tai ring. Kallon wayar yay, ganin Richard ne sai ya basar ya cigaba da hidimarsa. Sai da Rich ya sake kira bayan ta katse sannan ya ɗaga. A dakile yace, “Kana damuna fa”. A fusace daga can shima Richard yace, “An damekan, shine dan tsabar wulaƙanci ka wani kullema mutane ɗaki? Da ace babu wasu ɗakunan ina kake tunanin zamuje mu kwanta?”.
  “Oho muku” Ya faɗa a taƙaice da yare.
  “Zakace oho kuwa tunda mun gama maka wahala, mtsoww! Ka wani saka mutane zuwa cikin.....” Katse wayar Yoohan yayi batare da ya bari Richard ya ƙarasa ba. Ya taɓe bakinsa yana cilla wayar saman gado. Yanaji Rich ya sake kira bai kulaba. Sai da ya kammala shirinsa tsaf yay sallar magriba da isha'i da shafa'i da wutiri da addu'oinsa sannan ya mike ya haye gadon. Wayarsa daya cillar gefe ya ɗauka. Number baba malam ya lalubo yay dailing. Ring uku kuwa ya ɗaga. 
 Tamkar Yoohan yana gabansa haka ya risina cikin girmamawa yana gaishesa. Daga can kuwa baba malam na amsa masa da kulawa.
  “Abba mun iso babu jumawa. Ina fatan jikin nata babu wani matsala zuwa yanzun?”.
 Murmushi baba malam yayi da duban Nu'aymah da Umm ta gama canjama kaya zuwa na barci. Ya ɗauke kansa yana sauke numfashi. “Alhmdllh Yahya. ALLAH ya huta gajiya, ya kuma saka albarka. Dama yanzun nan muka gama waya da baban naka shima ya kira ya sanarmin isar taku. Mamana kuwa har yanzu barci ma take batako farkaba tun bayan allurar”.
   Sassanyan murmushi Yoohan yayi babu shiri, yace, “Alhmdllh Uncle, insha ALLAH zuwa da safe zata farka normal, ALLAH ya ƙara lafiya. Bara na barka ka kwanta sai da safe”.
 “To Yahya ALLAH ya huta gajiya”.

Daga haka sukai sallama. Baya yay ya kwanta ƙafafunsa a ƙasa yay filo da hannayensa. Idanunsa ya lumshe a hankali ya faɗa duniyar tunanin da shi kaɗai yasan akan abinda yake yi.

_★★★★

        *_To masu karatu sace shin ina Abdallah da Nasir?????????._*

   Tam nima dai tsayawar wannan tambayar a raina ce taja ra'ayina shiga bulayin nemansu a cikin gidansu Nu'aymah. Sai dai na karaɗe ko ina da ina tsaf babusu babu mai kama da su ɗin. Sai acan bakin su Omar dana tsinkayi yana faɗama Momynsu yanda ɗaurin auren ya kasance naji.
     Ashe faɗan da Abdallah da Naser suka tafka ne a daren shekaran jiya daya bama kowa tsoro yajawo su baba malam canja shawara akan zaɓin Nu'aymah. Ananah da hajjo sukai dogon nazari da shawarar canja komai. Dan yanda abubuwan ke nan canja salo tabbas zumincinsu zai iya girgiza akan matsalar Naseer da Abdallah. Dan haka suka kira su baba malam a wannan daren tare da Abban Naseer daya iso suka tattauna. Abban Nasir shine ya bada shawarar hana Abdallah da Nasir gaba ɗaya. Ya kuma bada shawarar aurama Yoohan kamar yanda ya bukata dan a samu zaman lafiya. Hakan zai kawo masalahar Abdallah ya maida matansa. Nasir kuma yaje ya auri wata.
 Kowa yayi na'am da wannan tunani na Abban Naser. Babu ɓata lokaci ko jinkiri suka kira Yoohan suka sanar masa. Yoohan kuma bai ɓata lokaci ba wajen sanarma papa. Sai dai yayi matuƙar mamakin ganin yanda Papa ya bashi goyon baya babu wani ja inja ko ƙalubalantar lamarin, ya kuma gargaɗesa karya sanarma Momynsa (Madam Chioma????) shi zai sanar mata.
   A wannan daren papa ya bada akai masa invitation na layin waya aka turama duk wanda yake da buƙatar gani a wajen ɗaurin auren ɗan nasa. Washe gari kuma ya ƙarasa dukan kai kawo da yake buƙata tare da bincikar duk yanda al'adar auren hausawa yake. Duk abinda ake buƙata sai da papa ya saya aka shiryasu a mota.

 Anan kuwa kano su Abdallah basusan wace wainar ake toyawa ba. Kowannensu dai ya ɗauki alwashi akan ɗan uwansa tsakanin shi da Nasir. Hakan yasa sukaje ɗaurin auren kamar kowa cikin kwalliya ta musamman. Sai dai kuma ganin Yoohan da tawagar ƴan uwansa da abokai ya basu matuƙar mamaki. Gashi waje ya ƙure balle su tambayi iyayen nasu. Basu fita daga ruɗanin ganin Yoohan ba aka fara ɗaurin auren. An fara ɗaura na Kubrah da angonta Al-ameen yuseef durɓi, sai Hajarah da angonta Dawood Sulaiman Rano. Naseer na jiran yaji shi da Nu'aymah sai yaji Zainab Sooraj Hashim jibiya da Yahya Goshpower”.
 Turƙashi zance ya girma. Ba Nasir kawaiba ne a ruɗani, Abdallah kansa hajijiya yaji tana ɗibarsa. Hakan yasa Omar dake kusa da shi ya taimaka masa suka fito daga cikin hayaniyar ya kaisa mota. Shima acan Nasir sai Ahmad ne ya kamashi ya fito da shi. Sun koma sanarma su baba malam, Abdallah ya tada motar da Omar ya sakashi ciki ya bar wajen batare da kowa ya sani ba. Nasir kam da ƙafa ya bar wajen shima a birkice.
   Daga wannan tafiyar ne har yanzu babu wanda yasan ina suke. Su baba malam sunyi neman a waya harsun gaji. Dan duk wayoyinsu a kashe suke. Halin da suka ahigo suka iske Nu'aymah a gidane ya sakasu yin shiru da zancen rashin su Abdallah ga kowa. Duk da kuwa Hajjo nata tambayarsu bataga Abdallah da Nasir ba.

WASHE GARI……….✍

ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo????
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).????????

      Mamu gee????

MIN ƘALB!!????????

    Hafsat rano????

ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!????????

    Safiyya huguma???? SIRAƊIN RAYUWA????????

     Bilyn Abdull????

SARAN ƁOYE????????

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka????????????????

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????

09033181070

????????????????????????????????????????
TEAM—-ZAFAFA BIYAR????????????????

ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????.

LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana????????.

No. 44

IDAN kaji ƙi gudu sai in sa gudu bai shigo wajen ba. Ƴan uwa abokan tafiya, gafa magani A GONAR YARO. domin tabbas idan kaji gangami akwai labari.

Ina masu wahala kullum cikin neman maganin sanyi (imfection) amma babu biyan buƙata. Kinyi na asibiti har kin gaji babu canji, na gargajiyarma taɓawa kike babu wani ƙyaƙyƙyawan sakamakon. Tofa kakarku ta yanke saƙa. Domin kuwa ga dama a tafin hannunku. Munada maganin NI’IMA, maganin GYARAN HIPS (mai gida bye bye????). Muna da maganin BOOBS (mai gida welcome????). Maganin BASIR mai hana sakewar zama. Duk ku garzayo domin samunsu akan farashi mai sauƙi da rahusa, ga kuma inganci domin an samosu ne daga tsaftatacciyar hanya mai nagarta.????????

AISHA S BAYERO TRADITIONAL MEDICINE AND HERBAL RESEARCH CENTER…

KUNJI SUNAN KO? CENTER CE TA MAGUNGUNAN GARGAJIA, WANDA DUK WANI DAMUWA DAKE DAMUNKA IDAN HAR KAZO WAJEN S BAYERO TA KARE DA YARDAR ALLAH.. KADAN DAGA MAGUNGUNANTA SUN KUNSHI:

MAGANIN SANYI
MAGANIN NI’IMA SET
MAGANIN NANKARWA
MAGANIN KIBA BABBA DA KARAMI
MAGANIN HIPS
MAGANIN GYARAN NONO
MAGANIN RAGE KIBA
MAGANIN SAKA FEELING
MAGANIN CIDA KWAI
ZUMA YAR ASALI
MAGANIN BASIR KOWANNE IRI
HODAR NI’IMA
MAGANIN MALLAKA
GUMBAR NONON RAK’UMI
GUMBAR MADARA
TURAREN FARIN JINI
KAZA MARA KWAI
TURAREN MALLAKA 3 STEP
HAD’IN MATAR MINISTER 1
KAZA ME KWAI

STEP 2:

TURAREN MALLAKA ME KWALBA
ME KUNAMA DAN MATSI
TURAREN GOSHI
TURAREN QIRJI
TAUWADAR MATA
MEMORY
KAHON MALLAKA
YAJIN MAZA
TEA DIN MAZA
DAMBUN MATSI
MAN AYU
MAN DAMO PURE
KWALLIN IDONKA IDONA
GARIN SHA DAKA ME KYAU
KUBEWAR MATA

DUKA WADANNAN INGATTUN MAGUNGUNA NA GARGAJIYA HAJ AISHA NA DASU GANGARIYA.. HERBAL MAGUNGUNA NE MASU KYAU DA INGANCI.. TAFIYAYYU NA KASAR CHAD. CHADIAN HERBAL MEDICINE AND RESEARCH CENTER.. KYAU, INGANCI.. RAHUSA… SAI MAGUNGUNAN AISHA S BAYERO TRADITIONAL MED AND HERBAL RESEARCH CENTER….

NUMBER WAYAR WHATSAPP: 08121491609 KO KIRA TA NUMBER 08145873617.

ADIRESHI: KUNTAU KARSHEN KWALTA KAN A KARASA YAN TIFA, DAIyDAI GADON KAYA CEMENT..

Sai kunzo????????????????


No. 44

……….WASHE GARI normal Nu’aymah ta tashi kamar yanda kowa yay fata. Sai dai rashin ƙarfin jiki da damuwar maganar auren da ta sake tabbatar an ɗaura mata shi. Dan bayan baba malam ya dawo daga massallaci zaunar da ita yay ya ringa mata nasiha mai ratsa jiki da ɓargo. Tun tana hawayen zuci, harta koma na zahiri. Hawaye suka dinga kwarara mata daga ido suna sauka saman fuska.
Fuskar baba malam ɗauke da murmushi ya kai hannu ya share mata hayen. Ya kamo hannayenta duka cikin nashi yana sake kwantar mata da hankali. “Kukan ya isa haka kinji mamana. Duk abinda kikaga ya shigo cikin rayuwarki saɓanin tunaninki ki ɗauka hakan shine mafi alkairi a gareki. Idan kuma har kika rasa abinda ke shine burinki da fatanki, ki saka a ranki UBANGIJI bai baki shi bane saboda ba naki bane, hanakin kuma shine yafi alkairi. Akwai abubuwa da yawa dana san suna damunki a cikin rai. Amma inason ki ɗaukesu ki watsar da su acan nesa, ki kuma manta da su ki shafe babinsu a tunaninki. Dan jiyanki ta wuce, kina cikin yau ɗinki ne. Kinga yafi kamata ki maida hankali wajen hangen gobenki. ALLAH yay miki albarka. Ya yaye miki damuwarki. Ya share hawayenki. Yay riƙo da hannunki. Yay miki jagora a gobenki da jibinki”.
“Amin Abbah na gode, ALLAH ya ƙara maka lafiya da tsahon rai”.
“Amin mamana nima na gode. Kije ki kwanta ki sake hutawa kinji. Sai dai ki zama cikin shiri dan zuwa jibi idan ALLAH ya kaimu kema za a miƙaki gidan mijinki”.
Kanta kawai ta ɗaga masa. kamar zata tambayesa waye mijin nata sai kuma tayi shiru. Ɗago idanunta dake jajur tai ta kallesa. Muryarta na rawa tace, “Abba dan ALLAH ka yafemin dukan abinda kake ganin na maka a sanina ko saɓanin haka. Sannan wlhy kaji na rantse ban aikata abinda likitocin nan suka tabbatar ba. Abinda ke a cikin hotunan nan kuma ya farune bisa ƙaddara……..”
Duk abinda ya faru a waɗan nan ranakun biyu sai da Nu’aymah ta sanarma baba malam. hatta da farkon haɗuwarta da Yoohan. Sosai baba malam ya gamsu da dukan bayaninta. Dan duk abinda Yoohan ya faɗa shine ta maimaita. Inda sukai saɓani kawai shine ita tana ganin da gangan ya aikata mata. Shi kuma ya sanar dasu baba malam duk akan taimakonta zata faɗi komai ya faru. Ya san Nu’aymah tun tana yarinyarta da wahala kaji tamaka ƙarya akan abu. Koda kuwa za’a daketa idan tai laifi aka tambayeta saita faɗa.
“Na yarda da ke Mamana. Insha ALLAHU kuma zamu ƙara sanin gaskiyar daga ina zancen ya fito. Dan wasu kalaman mijinki akan maganarnan suna nan tsaye bisa ƙwalwata ina musu fashin baƙi a hankali. Kuma lallai da gaske na fara ganin haske a ciki”.
“Abba na gode daka fahimceni”. Ta faɗa tana kuka da dariya lokaci ɗaya. Shima Murmushin ya keyi cike da tausayinta. Daga haka suka fara cin abincin da Umm ta shirya masa na breakfast shi da ita. Tana bashi a baki shima yana bata abin sha’awa.
Janyewa inuwar dake jikin windown tayi, baba malam da sai yanzu ya farga yay tsai yana kallon jikin Window ɗin cike da mamaki da al’ajabi. Sai dai kuma a zahiri ya maida hankalinsa ga Aymah ne. Daga can wani gefe na zuciyarsa yace, ‘Taya zakai zargin an muku laɓe ne bayan gidan cike yake da baƙi. Maybe wanine ke wani abu a wajen dai’. Ɗari bisa ɗari ya gamsu da hakan har cikin ransa. dan haka ya sake maida hankalinsa ga ɗiyarsa da tausayinta ke cike taf da ransa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button