NOVELSSARAN BOYE

SARAN BOYE COMPLETE

    Bayan baba malam ya shirya ya fita Nu'aymah ta koma sashen Umm. Ƙannen Umm ɗin da yayunta duk suna nan. Breakfast ma sukeyi. Sai wasu daga ƴan uwan Adda da suma anan suka kwana. Cike da jin daɗin ganinta ras duk suke kallonta. Ta risini ta gaidasu. Daga haka ta fito sashen hajjo. Nanma sunyi farin cikin ganin ta tashi lafiya kamar ba ita ba. Gaishe da baƙin dake a sashen tayi sannan ta shige bedroom ɗin hajjo. Acan tai wankanta tsaf, Yusrah data shigo taje ta amso mata kaya. Bayan ta shirya tare da Yusrahn suka fito. Hakan yayi dai-dai da shigowar Adawiya falon hannunta ɗauke da bokiti ruwan goro.
    Tunda sukazo ƙasar wannan shine gani na uku da Aymah tai mata. Adawiyan duk ta rame, tayi duhu kamar ba itace sukazo tayi ɗam da ita kamar zata fashe ba dan ƙyau. Ɗauke kanta tayi tamkar bataga Aymah da Yusrah ɗinba. Ta ƙarasa gaban Ananah ta ajiye bokitin tana faɗin, “Ananah gashi inji Addah na ƴan katsina ne da zasu wuce yau”.
  “To. To masha ALLAH, ALLAH ya sanya alkairi yasa albarka. Kice mata angode ALLAH yayi albarka”.
“Amin” ta faɗa tana ƙoƙarin gitta su Nu'aymah zata fice. Murmushi Aymah tayi, tare da cewa, “Adawiya an tashi lafiya?”. Da mamaki Adawiya ta juyo ta kalli Nu'aymah. Kamar bazata amsaba sai kuma tace, “Alhmdllh”. Daga haka ta fice abinta.
 Yusrah tace, “Humm ALLAH ya ƙyauta. Wlhy lamarin Adawiya har mamaki yake bani Aymah. Ita yanzu dai abinda take nunawa ta raba zuminci damu. Nifa tunda sukazo ƙasarnan batamin magana. Idan na mata kuma saita amsani kamar wata kashi. Koda yake kema da kuka shaƙu da ita fiye da kowa tana ɗaga miki hanci bare mu”.
  Murmushi kawai Aymah tayi, amma batace komaiba. Daga Ananah har hajjo duk suna jinsu suma. Amma sai sukai kamar basujinba. 

  An ƙarasa gudanar da shagalin biki yau. Zuwa bayan azhar sukaje gidan amare akai buɗan kai. duk baƙi masu tafiya daga can suka kama gabansu. Sai ɗai ɗai kune suka dawo nan gidan waɗanda su sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu. Nu'aymah dai tana gida bataje ko inaba. Cikin ranta kam fal damuwa dason sanin wanene ita aka ɗaura mata aure da shi?. Anya kuwa Naser ne datai fata? A ganinta idan shine yaci ace ta gansa ai. Amma tunda ta tashi daga Naseer har Abdallah bataga kowa ba a cikinsu. Kuma duk sauran samarin gidan ta gansu.

★★★★

*_FCT ABUJA_*

        A birnin tarayya kam taƙaddama ake bugawa sosai tsakanin Yoohan da kakanninsa. Harma da wasu a cikin ƴan uwansa da suke nuna borensu akan auro Nu'aymah da yayi. Hayaniyarsu da haukarsu duk bata damesa ba. Yamayi kunnen uwar shegu da su tamkar baiji akan mi sukeyi ba. Babban tashin hankalinsa da damuwarsa kawai halin da Momynsa ke a ciki.
 Dan tun daren jiya jininta ya hau sama sosai saida ya danna mata allurar barci, har kuma yanzun bata farka ba saboda mai ƙarfi sosai yay mata. Su Richard ne kawai da suma suka so tasashi gaba da magana akan auren yay azamar taka musu burki. Dukansu sunsan halinsa, idan rashin mutuncinne da buyagi duk ya fisu iyawa. Sannan suma ɗin kowanne allazi da nasa amanu ai. Kuma babu wanda sirrinsa ba'a tafin hanunsa yake ba. Haƙuri suka bashi akan masa katsalandan ɗin da sukayi. Suka kuma nuna masa zasu basa goyen baya tunda yana son matarsa.
Uffan baice da su ba daga haka. Su kuma duk suka tashi suka fice suka barsa. Fita sukai daga gidan duka, sai da sukasha gulmarsu iya iyawa a waje kafin su tattauna akan shagalin biki da suke son shirya masa tunda auren nasa yazo musu da salo na daban ba irin nasu ba.

    A cikin gida ma bayan su mama Debora sun turza sun turza akan Yoohan ɗin sunga babu mafita sai suka sakko dan kansu akan zasu amince da auren, sai dai da sharaɗin duk sun dawo da zama gidan papa. dolene kuma Nu'aymah ta zauna itama a gidan Yoohan bazai kaita ko ina ba.
    Sai dai a mamakinsu sai sukaga Yoohan yayi murmushi tare da lumshe idanunsa ya buɗe a kansu. Sai da yay musu kallon tsaf na wasu mintuna kafin ya miƙe cike da basarwa yace, “Na amince”. A ransa kuwa dariya ya tafi yana musu, dan yasan indai nu'aymah ce sun sami dai-dai dasu.
 Kusan duk a tare sukai wata irin zabura. Dan sam sun zata zaice bai yardaba su kuma su sake tada wani billin. Sai gashi sunga saɓanin tunaninsu. Kafin su gama dawowa hayyacinsu ya dawo falon ɗauke da takarda.  A tebirin dake tsakkiyar falon ya ajiyeta. Ya bisu da kallo fuska a murtuke yana faɗin, “Wannan takarda ce ta agreement tsakanina da ku. Zaku cigaba da zama a gidan nan, matata ma zata zauna. Sai dai da sharaɗin duk randa na kama wani da laifin mata koda maganar banza a cikinku ko cikin yaranku sai mutum yabar gidan nan koda ace kuwa cikin su Gebrail ne. Itama kuma na muku alƙawarin bazata shiga rayuwarku ba bayan mutuntawa da girmamaku”.
    Cike da wani mamakin suke kallonsa. Zasuyi magana papa yay saurin faɗin, “Wannan tsarin na John yayi dai-dai. Dan shine zai kawo mana masalaha da kwanciyar hankali a zuri'ar mu. Mukuma sake tabbatar da kowannenmu nada ƴancin aikata abinda bai saɓamana ba”.
  Babu wanda ya iya sake cewa komai. Sai singing ɗin da Yoohan ya fara yi ya basu suma duk sukayi. Ɗaya ya ɗauka ya basu ɗaya. Ɗayan copy ɗin kuma da aka saka cikin frame ya nufi bangon falon daga kusurwar d/table ya kafesa jikin ginshiƙin wajen daya zama kwalliya.
 Wannan abu da Yoohan ɗin yayi ya kuma girgiza su matuƙa. Gashi babu damar magana dan ya tsuke fuskar fiye da ɗazun.

 Wannan takardar Agreement itace ta zama makullun rufe bakin duk wanda keda ƙarfin faɗa a ji a family ɗin su Yoohan. Sai ma zaman shirya biki sukai dan nuna bajintarsu ga gudan jininsu tamkar yanda akema kowa.
   Shi dai Yoohan bai tanka kowa a cikinsu ba akan shirin bikin, ranarma yini yayi a asibiti shi da Richard. Basu dawo ba sai dare. Gajiyar da sukayi ce ta sakasu ko zaman hira basuyi ba Yoohan ya shige sashensa. yau ma tsabar wulaƙanci hana su Rich shiga yayi. da sukai magana yace shi yanzu yayi aure baya buƙatar su a sashensa. Suje can su ƙarata a sashen baƙi suyita loda kwalaben barasarsu.
  Aiko sun hayayyaƙo masa tamkar zasu cinyesa. Ya fice yana murmushi bayan ya musu gwalo.

★★★_

   *_KANO_*

A kano kam tunda garin ALLAH ya waye yau da shirye-shiryen tahowar su Nu’aymah aka tashi. Dan zasu taho abuja gidan su Abdallah. washe gari sai a miƙata ɗakin mijinta daga nan gidan. Saboda ma baba malam baya buƙatar ayi wata gayya jirgi zasu biyo.
Jin abuja zasu wuto yasa Nu’aymah fara tunanin ko dai yah Ab aka ɗaura mata aure da shi? Ko burinsu na mallakar juna ya tabbata ne? To amma idan har hakane mizaisa a ringa ɓoye mata?. Har yanzu babu wanda ya sanar mata wanene mijinta. sai dai kowa na zaunar da ita yay mata nasiha dai-dai gwargwadon saninsa. Haka ne yasa yau taci kuka harta godema UBANGIJI. Mai ƙunshi ma da Addah tasa aka kawo da ƙyar Aymah ta yarda akai mata. Hakama da za’a kaita gyaran jiki sai da baba malan ya saka baki wajen lallashinta sannan ta amince. Ai ko sai gata tayi ɗas tamkar ka saceta ga gudu. ƴar ramar da tayi saita sake ƙara fiddo mata da ƙyawunta da haskenta. Sai dai a kallo ɗaya kaɗai ya isa ka tausaya mata duk tayo laushi kamar ba Nu’aymah tsiwa ba. Duk ta zama shiru-shiru, ta kuma nanema Umm taƙi barinta sukuni.
Lokacin da aka idar da sallar la’asar Ananah tazo har sashensu tajata dan taje a kimtsata tunda jirgin 5:30pm zasu bi saita saka musu sabon rikici. Babu wanda bai lallasheta ba amma taƙi tai shiru. Sai da baba malam ya fito yay mata jan ido da nuna mata ɓacin ransa sannan. Aiko tana kuka tana sharɓar hawaye. Koda ta fito ma sai Aunty Kulu yayar Naser ce tai mata kwalliya ka ɗan dukda kuwa ba wai gidan su Yoohan ɗin zata sauka kai tsaye ba.
Tsaf ta sakata ta shirya cikin atamfa lass ƴar ubansu, ɗinkin zani da riga. Kasancewar atamfar baƙa ce da kwalliyar golden sai tai bala’in zama mata a jiki tamkar ka saceta ka gudu.
Iyayenta sun sake taruwa a kanta sun mata nasiha da gargaɗi mai faɗi akan rayuwar da zata fuskanta ta aure mai cike da ƙalubale. Dan aure ibadane. Ita kuma ibada a koda yaushe tana a cike ne da jarabawa kala-kala. Daga haka aka miƙata wajen Umm tai mata sallama. Ba Umm da Nu’aymah kawaiba, hatta duk wanda ke a wajen sai da ya matse hawayen tausayinsu. Da ƙyar aka ɓanbare Aymah jikin Umm. Hakama Muhammad dake taya yayar tasa kuka abin tausayi. Daga haka aka kaita kowane sashe tai musu sallama sannan aka shiga da ita ɗaya daga cikin motocin da zasu musu takkiya zuwa airport. Abban Abdallah da duka yaransa duk sun fito dansu daga haka zasu koma kenan sai kuma anyi hutun makaranta. Sai matan Abba Musbahu duka biyu da zasu mata rakkiya. Sai Ananah da Aunty Kulu. Aunty Aysha, Sai ƙanen Umm biyu da yayarta ɗaya. Sai Yusrah da Adawiya da taso tirjewa bazataje ba. Sai da Hajjo ta zageta tas sama da ƙasa sannan ta yarda da binsu badan taso ba. Sai Nanah, da Rufaidah autar su Naser.

  Tunda motocin suka ɗauki hanyar airport Aymah ta kwantar da kanta jikin Aunty Hibbah ta cigaba da raira kukanta a hankali. Aunty Hibbah dai nata shafa bayanta cike da lallashi amma batace uffanba.
 Basu wani ɓata lokaci ba a airport ɗin jirginsu ya ɗaga zuwa Abuja. Tafiyar mintuna ƙalilan kuwa ta kaisu. Anan ɗinma dai tarbarsu akazo akayi, daga gani dai daga company ɗinsu ne masu tarbar. Zuwa yanzun jikin Nu'aymah yayi zafi zau da zazzaɓi, hakan yasa suna isa Momy ta kama hanunta zuwa ɗakinta, sai da ta sakata tai sallar magriba da aketayi lokacin da suke shigowa gida, tana idarwa ta haye gado ta kwanta Momy ta lulluɓa mata bargo saboda rawar sanyin da taketa faman yi.
     Ganin yanda rawar sanyin nata ke ƙaruwa Momy taje ta sanarma Abban su Abdallah dake shirin fita massallaci sallar isha'i. Biyota yay suka dawo ɗakin tare. Shima sai hankalinsa ya tashi jin yanda jikin Aymah yay masifar zafi. Ga rawar sanyin na ƙaruwa harma tana roƙon a ƙara mata wani bargon.
   “Khadijah inaga bara na dawo masallaci sai a kira Yahya zaifi, dan yayi gargaɗin bata magani kai tsaye. Nasan yanzu kuma a duk inda yake yana ƙoƙarin yin sallar isha'i ne tunda kiji gashi can za'a tayar”.
   “Eh gaskiya, hakan zaifi Abbansu. Bara nayi sallar nima kafin ku shigo”. 

 Bayan an idar da sallar isha'i Abba ya shigo gida. Kai tsaye waya ya ɗauka yay kiran Yoohan. Sai dai harta katse bai ɗaga ba. Ya sake kira nanma bai ɗaga ba. Ajiye wayar yayi yana faɗin, “Maybe baya kusa. Amma idan ya gani nasan zai kira”. Kai Momy ta jinjina masa kawai.

   A lokacin da Abbah ke kiran wayar Yoohan yana massallaci, wayar kuma na mota, dan suna wani hotel tun kafin magriba shi da su Joseph akan dinner ɗin da za'a gudanar gobe idan ALLAH ya kaimu bayan kawo amarya. koda ya fito kuma wajen nasu ya koma dan dama yace musu ne kawai yana zuwa, sukuma tsare-tsaren da sukeyi ya ɗauke hankalinsu basubi ta kansa ba akan inda zaije ɗin.
  Kujerar daya tashi ya ja ya zauna yana harar Osin da aka ajiyema kwalbar giya da yayi oda. Bai dai ce komaiba, sai Osin ɗinne yay murmushi yana faɗin, “Duk iya hararka dai ba ƙinsha zan ba. Kaima koda ɗura gobe sai ka shata domin farin ciki, koba komai kaji daɗin cin soyayyarka da amryarka”. Dariya suka kwashe da ita gaba ɗaya. Richard yace, “No, bazai shaba a wajen dinner sai ya koma gida, so kake y......” bammm kakeji Yoohan ya dokema Rich baki da bayan hannu kafin ya karasa faɗa. Aiko mizasuyi inba dariya ba. Tsabar mugunta Godwin har faɗuwa yake ƙasan korayen ciyayin da akaima wajen shimfiɗa da su. Richard daya ɓata fuska yace, “Mr X da zafi fa”. “So..” Yoohan ya faɗa a wani salo yana ɗage kafaɗa. 
    “Aiko na rantse sai kaji a jikinka yau” Rich ya faɗa yana rarumo kwalbar giyar da Osin bai kai ga buɗewa ba. Da gudu Yoohan ya tashi yana dariya shima saboda yasan mi Richard ke shirin aikata masa. (a karan farko dana taɓa ganin dariyarsa mai faɗi irin haka). Suma gaba ɗaya dariyar sukeyi, dan Rich bin Yoohan ɗin yayi shima da gudu. Mota Yoohan ya buɗe ya shige ya saka lock yana yima Rich dake ƙoƙarin ganin ƙofar ta buɗe daƙƙuwa. Da ɗan ƙarfi yace, “Stupid boy”. “Same to you”. Shima Rich ya faɗa yana masa daƙƙuwar.
 Gwalo Yoohan ya sake masa yana ƙoƙarin ɗaukar wayarsa dake haske. Da mamaki yake kallon sunan wanda yay kiransa har 3missed call. Bai kula Rich dake masa knocking glass ba ya shiga ƙoƙarin dailing Number Abban Abdallah.
  Bugu biyu kuwa ya ɗaga. Kamar yanda yake gaida baba malam da girmamawa haka ya gaida Abbah. Shima Abba sai ya amsa da kulawa, sannan yayma Yoohan ɗin bayanin abinda ke faruwa. Ɗan lumshe idanunsa yayi ya buɗe a hankali tare da kwanciya jikin kujera. “Uncle bara nazo na dubata kawai”.
 Cikin jin daɗi Abba yace, “To shikenan ALLAH ya kawoka lafiya. Ai kana da address ɗin gidan ko?”.
  “Eh Uncle inada”.

Daga haka suka yanke wayar. Glass ɗin motar ya sauke yana kallon Rich da ke jiransa ya kammala wayar. Da ƴar damuwa yace, “Sorry Rich ina zuwa, bazan jimaba insha ALLAH ku cigaba kawai”.
Richard yace, “Lafiya dai ko?”.
“No, babu damuwa dear, wani ɗan uzirine idan na dawo zan maka bayani”.
“Ban yardaba gaskiya muje tare kawai”. Richard ya faɗa yana buɗe motar ya shigo shima.
Yoohan ɗin baice da shi komaiba, sai waya daya ɗauka yay kiran Godwin, yana ɗagawa yace, “G-boy muna zuwa Please, just 30minutes”. “Okay no prob..” ya amsa masa da salon iya shege na gayu.
Motar ya tada suka fice daga hotel ɗin. Yanda yake driving ɗin a hankaline ya sa Rich faɗin, “X-man are you ok?”. Ɗan murmushi Yoohan yayi kawai bai ce komaiba.

    Tafiyar mintuna ƙalilance ta kawosu gidan. Sun iske Omar tsaye a bakin gate da alama zuwan nasu yake jira. har ciki Yoohan ya shiga da motar. Da ga shi har Rich bin gidan suke da kallo dan kuwa ya haɗu. A ransa kuwa ayyanawa yake lallai su baba malam sunada ƙuɗi. Sai dai sun iya takunsu dan basu da fariyya akan ni'imar da ALLAH ya basu.
    Ƙofar da zata sadasu da cikin gidan suka nufa. Omar na gaba suna biye da shi, shi dai Rich ransa fal mamaki dan baisan ina suka zo ba. Su Aunty Hibbah na baje a falo zasuci abincin da Omar ɗin ya fita yayo musu takeaway suka shiga da sallama.  Cikin girmamawa Yoohan da yay musu kallo ɗaya yay ƙasa da kansa ya shiga gaishesu. Hakan yasa shima Richard da ke binsu da kallon tsaf ya gaida su. Daga haka suka wuce falon Abba dake zaman jiransu.

   Aunty Aysha ce tai ƴar dariya bayan shigewar su Yoohan. Duk kallonta sukai na alamar tambaya. Tace, “Wannan angon namu dai akwai kunya, abokinsa yay mana ƙuri da idanu, amma shi ya kasa kallon ko sashen da muke”. Aunty hibbah ta karɓe da cewa. “Sai kace jinin hausawa, inma ba faɗa maka akaiba bazaka taɓa cewa ba bahaushe bane wlhy. Musamman wanda yasan yanda ƙabilun nan suke da shegen tsaurin ido”.
  Haka suka cigaba da hirarsu ƙasa-ƙasa akan Yoohan. Har Umm tazo ta wuce ta fito da Aymah zuwa falon Abbah basu lura ba. Adawiya ce kawai da Amal babu a falon. Adawiya dai ƙin fitowa tai, tunda suka iso gidan ta shige ɗakin Amal bata sake leƙo waje ba. Amal kuwa kanta ke ciwo shiyyasa tasha magani ta kwanta tana idar da sallar isha'i.

     Tunda Momy dake riƙe da Aymah data langaɓe mata a jiki tai sallama duk suka ɗago kansu. A hankali Richard ya furta ‘Woow kaga wata ƙyaƙyƙyawar halitta’. Akan laɓɓansa ba tare da kowa ya jisa ba. Dan Yoohan ma dake kusa da shi zaune hankalinsa gaba ɗaya akan Aymah data takure cikin kujerar da Momy ta ajiyeta ya ke. Cikin rawar sanyi tace, “Momy Please ki bani bargo sanyi”.
 Kafin Momy tai magana Abba dake kallonta da tausayawa ya duba Omar da shima duk yay wani iri da tausayin ƙanwar tasa. “Omar kaga rage gudun ac nan”. Da sauri yace, “To Abba” yana ɗaukar remote ɗin.
 Murya ƙasa-ƙasa Rich ya cema Yoohan, “X-man who is she?”.
 Fuska Yoohan ya ɗan tsuke tare da ɗauke kansa batare da ya bama Rich amsa ba, saima maida hankalinsa yayi ga Abba da ke faɗin ga Nu'aymah ɗin nan. Yana gama faɗa ya bar falon Momy biye da shi. Har Omar ya juya zai fita shima Yoohan yace, “Excuse me Fharook”.  Dawowa Omar yayi fuska ɗauke da murmushi yace, “Yayah kana buƙatar wani abu ne?”.
   Ɗan murmushin kaɗan shima Yoohan yayi, yace, “Kaɗan samo mata tea tasha first”.
 Kai Omar ya gyaɗa ya fita.

Yana fita Rich ya bugi kafaɗar Yoohan da yare yace. “Kaifa banza ne! Ina tambayarka kana basar dani. Ina ka kawomu nan, gidan ƙyawawan mutane wai?!”.
Dariya yaba Yoohan, amma sai ya gimtse bai yiba. Da gatse yace, “Gidan kidnappers ne” tare da zuba masa harara. Hakan yayi dai-dai da dawowar Omar falon ɗauke da ƙaramin tire an ɗoro mug dake ta turiri………….✍

ZAFAFA BIYAR 2021


Hafsat miss xoxo????
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).????????

      Mamu gee????

MIN ƘALB!!????????

    Hafsat rano????

ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!????????

    Safiyya huguma???? SIRAƊIN RAYUWA????????

     Bilyn Abdull????

SARAN ƁOYE????????

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka????????????????

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????

09033181070

????????????????????????????????????????
TEAM—-ZAFAFA BIYAR????????????????

ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????.

I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p.

LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana????????.

No. 45

…………Hararsa shima Richard ɗin yayi, amma sai Yoohan ya watsar da shi ya miƙe yana nufar kujerar da Aymah ke kwance a kai. Omar dake murmushi ya ƙarasa inda suke ya ajiye tiren a copy table ɗin dake gefen kujerar. Hakanne ya saka Yoohan dake tsaye yana kallon yanda take rawar sanyi zama kan hannun kujerar kaɗan shi kuma.
“Thanks you” ya faɗa a hankali yana kallon Omar. Murmushi kawai Omar yayi shi dai.
Da hannu Rich ya yafito Omar, hakanne ya sakashi nufarsa. Tambayarsa yay wacece Aymah? Dan shi harga ALLAH ya gama rikicewa. Cikin ƴar dariya Omar ya faɗa masa amaryarsu ce mana.
Sosai kuwa Rich ya waro idanu waje yana faɗin, “Are you serious?”. kai Omar ya gyaɗa masa alamar sake tabbatarwa.

   Shi dai Yoohan na jinsu, amma sai bai ko waiwaye ya dubesu ba, sai ma hannu da ya kai a hankali ya janye bargon Abba da Momy ta ɗakko ta lulluɓawa Aymah. Zabura tai da sauri ta cafke hannunsa tana ƙwaɓe fuska zatai kuka. Dan a tunaninta Momy ce ma ita. Tace, “Momy Please karki cire sanyi nakeji”.  
      Hannunsa yay ƙoƙarin janyewa daga cikin nata amma ta riƙe gam, hakanne ya sakashi barin hannun kujerar ya dawo ta gabanta ya tsugunna. Sosai ƙamshin turarensa ya daki hancinta yanzu. Tai azamar buɗe idanunta da sukai mata nauyi, sai ko a cikin nashi. 
   Zabura tai da sauri tana saki masa hannu tare da wancakalar da bargon har yana rufe masa fuska. Hannunsa yasa ya janye bargon a hankali tare da saurin riƙota dan tana ƙoƙarin barin kujerar ne. Hannun taja zata fisge. Fuska a murtuke yace “ALLAH idan baki nutsu ba allura zan miki”.
   Ai babu shiri tai saurin komawa ta zauna hawaye na zubo mata saman fuska da uban gudu. Ta bashi dariya amma sai baiyiba ya gimtse abarsa. Sai dai hakan bai hana lips ɗinsa motsawa ba kaɗan. 
 Duk da halin da take a ciki sai da ta zuba masa harara ga hawaye na zirara kuma. Dariya Richard dake kallonsu tamkar ya samu television yayi. Juyawa Yoohan yayi yay masa daƙƙuwa yana danne tasa dariyar. Sai kuma ya mike daga tsugunnon da yay a gabanta ya koma kujerar da take zaunen daf da ita, dan tazarar dake tsakaninsu kaɗance. Harara Aymah ta kuma zuba masa tana maƙurewa gefe. Shi dai bai kulataba ya ɗakko kofin shayin ya miƙa mata.
     “Ban sha” ta faɗa tana kuma matse jikinta a cikin bargon. Sake tsuke fuskarsa yayi da ƙyau sannan ya kalleta, dan duk da da hausa tayi maganar sarai ya jita. Sake mika mata kofin yay tare da matso da fuskarsa gab da tata. Yace, “Silly girl! Koki karɓa ko ki sha allurai a bom-bom ɗinki yanzun nan”.
    Duk da tsoratar da tayi sai da tace masa ɗan iska a zuciya, saboda kalmarsa ta ƙarshe-ƙarshe. kofin ta amsa tana hawaye da tunzura baki gaba. Shi dai bai kulata ba, sai hararar Rich da kema su Osin gulmar haɗuwar matar Yoohan ta waya da yare yayi. Richard yi yay kamar bai gansa ba ya cigaba da rattafa bayani dalla-dalla.
      Nu'aymah bata son shan shayin amma tana tsoron allura, hakan yasa ta daure ta shanye duka tana hawaye. Amsar kofin yayi yana sakin wani shegen Murmushin gefen baki. Aymah kanta sai da Murmushin ya daki zuciyarta, dan tunda ta sanshi a rayuwarta bata taɓa ganin yayi murmushi ba sai yanzun. Saurin riƙe bargon da take neman rufama har kanta yayi. 
  “Ban gama da ke ba”. Yay maganar a hankali tamkar mai yin raɗa. Cikowa idanunta sukai da sabbin hawaye. Ta ture hannunsa dake riƙe da bargon tana faɗin, “Bana shanye ba, nifa ka takuramin da yawa, yanzu ba da bace inada aure ka daina taɓani banaso”.
   Da ɗan wani salo yace, “Oh really? Smalley! Waye mijin to?”.
         Sosai rawar sanyin nata ya fara raguwa, sai ma wata zufa dake taruwa mata a goshi, hakanne ya saka bakin tsiwar tata sake fitowa fiye da sanda suka shigo. Tai masa wata irin harar da ta saka tsigar jikinsa tashi tana murguɗa baki, “To ina ruwanka shugaban masu shishshigi. Idan ka gama abinda ya kawoka zaka iya tafiya”.
    Bakinsa ya taɓe ya ɗauke kai tamkar bai ji mita faɗa ba. Sai ma aljihun jeans ɗin jikinsa daya laluba ya zaro ledar daya ɗakko daga mota. Wani ɗan kwalin magani ne ƙarami ya zaro. Ya fiddo maganin ciki ƴan kanana, a gaban idonta ya ɓalli ɗaya, sai taga ya rabashi biyu ya maida rabin a ramin daya ciro ya liƙe tare da sakawa a kwalin. Miƙewa yay zuwa inda Rich ke zaune har yanzu yana waya, ya halbi ƙafarsa sannan ya ɗauki gorar ruwa ɗaya cikin waɗanda aka ajiye musu ya bar wajen batare da ya kula Rich daya riƙe ƙafarsa da yaji zafin halbin da yay masa ba.
   Duk abinda suke Aymah kallonsu, har addu'a tayi a ranta ALLAH yasa Richard yace sai ya rama koda sun fita ne. Cikin katse mata tunanin muguntarta ya miƙa mata maganin dake cikin hanun nasa. Baki ta buɗe zatai magana yay saurin ɗaura yatsansa kan baki yace, “Shiiii!! bana son musu malama, ki karɓa inada abinyi jirana akeyi”. Da mugunta tasa yatsu biyu zata ɗauki rabin maganin dake cikin lallausan tafin hannunsa da jini keta kai kawo tamkar zai tsillo waje. Saita haɗo da fatar hannun ta mintsina da ƙarfi. Duk da yaji zafi sai baiko motsa ba balle ya nuna yasan mi tayi. Tai masa harar gefen ido tare da jefa maganin a bakinta tana faɗin, ‘Sai shegen dauriya wai shi jarumi, ai ko baka nunaba nasan wlhy kaji zafi’ ta ƙare zancen zucin nata da jefa maganin cikin baki. 
   Shi dai yana kallonta ne ƙasa-ƙasa. Ya miƙa mata ruwan hannun nasa, babu musu ta amsa ta tuttula cikin baki tana yamutsa fuska tamkar zata fasa ihu. Dan shima maganin bawai tana ƙaunarsa bane ba. amma dai yafi mata sauƙi-sauƙi akan allura.
 Goran ta miƙa masa, ya amsa tare da ranƙwafowa ya kama bargon ya rufa mata a jikinta yana magana kamar baya so. “Kwanta”. Bata musaba ta zame ta kwanta tare da lumshe idanunta masu cikar gashin gira dana ido.
     Tasowa richard daya gama gulma a waya yayi yana gaisheta da jiki. Batare data buɗe idanunba ta amsa masa sama-sama alamar barcine mai nauyi ke fisgar idanunta.

  Jin motsi a bayansu yasa duk suka juya. Momy ce ta fito akan ko zasu buƙaci wani abu. Kai Yoohan ya risinar, cike da girmamawa yace, “Aunty mu bara muje, insha ALLAH barcin da zatayi yanzu zai taimaka mata zazzaɓin kuma zai sauka, shima sanyin zata bar ji”.
  Fuskar Momy da fara'a tace, “To Alhmdllh Son, mun gode sosai”.
   Kansa kawai ya jinjina mata sukai mata sallama suka fice tare da Omar dake zaune a ƙofar corridor ɗin Abban yana jiransu dama. Su aunty Hibbah duk sun shige kwanciya saboda gajiya. Hakan yasa suka fice abinsu babu wata gargada

  Tunda suka bar gidan bakin Richard ya kasa yin shiru wajen yaba ƙyawun Aymah, da tambayar Yoohan ya akai ya samota? Bayan yasan hausawan nan basa son bama kowa ƴaƴansu sai yarensu kawai. Tun Yoohan na sharesa harya gaji ya ɗauki Bluetooth ya maƙala a duka kunnensa alamar baya bukatar cigaba da jin surutun na Rich. Kai tsaye Hotel ɗin suka koma. Inda a canma Rich yay zaman bama su Joseph labarin matar ta Yoohan, sai dai a cewarsa ƴar karamar yarinya ce.
     Ko sau ɗaya Yoohan bai saka musu baki ba, gefe ma ya koma yasa aka kawo masa coffee dan su Godwin sun cika wajen da warin giyar da suka sha harda sigari. Dan dai ita sigarin ana mata shan gayune kara ɗaya ko biyu shikenan. Giyar ce dai aka maida ruwa????.

WASHE GARI

     Washe gari da safe company ɗin da aka bama kwangilar kayan Nu'aymah suka isa gidansu Yoohan bisa address ɗin da aka basu. Wannan al'amari ya bama dangin Yoohan mamaki, dan su dai basu saba ganin hakaba. A saninsu miji shike kayan gida. Amma sai gashi su an kawo musu. Da alama kuma babban company ne.
          Kiran baba malam. Yoohan yayi yana roƙonsa akan basai sun saka komai ba, shi zaiyi komai insha ALLAH. Amma sai baba malan ya nuna masa sam bazai yuwuba. Mu hausa fulani hakan al'adarmu ce, yayi haƙuri ya barmu muyi. Yanajin nauyin baba malam da kimarsa. Shiyyasa dole ya bari aka kwashe kujerun falonsa da kayan gadon dake a ɗayan ɗakin, harma dana karamin falonsa na hutawa da sai ya bushi iska yake shigarsa duk suka fidda. A wani sashe na cikin gidan aka maida kayan, su kuma suka shiga aikinsu cike da ƙwarewa. Kayane ƴan ubansu masu shegen tsada. Dan sai dama suka bama Yoohan ɗin zaɓin waɗanda yake so ta hanyar pictures sannan suka koma company suka ɗakko akazo aka shiga hadawa.
   Zuwa lokacin kuma gidan nasu ya fara ɗaukar baƙi na nesa. Dan sosai Papa da su Gebrail sukai gayya, hakama su Richard sun bala'i-bala'in gayyato abokansu kamar hauka. Harda na ƙasashen ƙetare. Shi angonma baisani ba, iya waɗanda kawai ya gayyata ne yasan da zuwansu.

    Anan gidansu Abdallah ma ragal Aymah ta tashi, sai dai rashin ƙwarin jiki da ƴar fargabar tunanin wanda ya kasance mijin nata. duk da ranta yafi bata Yah Ab, ganin an kawota gidansu ne na nan abuja.
 Gari na fara haske Aunty hibbah ta fara mata gyaran jiki na musamman, hakan yasa bataga idanun su Adawiya ba. Koma nace Adawiya kawai dan su Yusrah da Amal suna nane da ita.
       Ji tai duk kewar su Umm ta gallabeta, ta amshi wayar Yusrah tai kiran baba malam, ALLAH yasa lokacin yana gida bai fita ba. Shima yaji daɗin jin muryarta, dan Abba ya sanar masa jiya tayi zazzaɓi sai da Yoohan yazo ya dubata. Sai dai kuka data saka masa ne ya sashi fara mata faɗa, daga ƙarshe kuma yay mata nasiha mai haɗe da lallashi. Yace bazai bama Umm wayarba sai idan ya kirata anjima yaji bata kukan. daga haka ya yanke kiran itama ta ajiye tana sharar ƙwallan da har yanzu sun ƙi tsayawa. Sosai Yusrah da Amal ke tausayinta. Shiyyasa duk sai suka zama shiru-shiru suma. 

★★★★

     Kasancewar su dai basusan da zaman dinner ɗin da gidansu Yoohan ke shiryawaba ƙarfe huɗu suka shirin miƙa amarya ɗakinta. Dan jirgin 8pm zasubi ya maidasu kano. Anayin sallar la'asar kuwa aunty Aysha ta tsaya akan Aymah sai da taga ta shirya tsaf cikin lifaya fara da kwalliyar golden. Tai mata ƴar kwalliya duk da ta nuna bataso. Kowa ya ganta sai ya ambaci masha ALLAH, ga uban ƙamshi da take zubawa kamar gidan turaren (miss xoxo????lol). 
   Kamar yanda tsarin yake ga duk amaryar da za'a miƙa gidan miji a gidansu haka itama akai mata. Dan kuwa Abba ne yay mata rakkiya gidan aurenta sai su Momy dasu Aunty Hibbah. Su Adawiya ma Abba cayay bazasu je ba sai gobe idan ALLAH ya kaimu dan bandasu za'a koma kano dama. Zasu ɗanyi kwana biyu a nan.

     An tarbesu yanda basuyi zato da tsammani ba, ba kuma komai ya jawo hakanba sai dogon gargaɗin da papa da Yoohan ɗin sukayi, sai kuma sauran matan su Uncle Mike suma sunsha gargaɗi wajen mazajen nasu. Shiyyasa suka zama gaba-gaba wajen ƴan amsar amarya basu bari su mama debora sun kwafsa ba. Koba komai dangin Nu'aymah sunji ƴar nutsuwa, sai dai har cikin ransu sunji tausayinta na zama cikin waɗan nan gurguzin kahiran da idanunsu ke buɗe da wayewar karatu dana kuɗi. Amma sun rigada sunyi imani da cewar UBANGIJIN daya ƙaddara shigowarta cikinsu, yafisu sanin alkairi da hikimar yin hakan. Sun sake mata nasiha sosai, tanata kuka dai duk da bata fahimci ina aka kawota ba. 
     Duk da tarin abinci da kayan sha da aka kawo musu basu taɓa komaiba, sai ma miƙewa da sukayi da zummar tafiya bayan sun leƙa ko ina na sashen nata sukaga yanda company ya tsarashi gwanin birgewa. Ƴan gyare-gyaren da suka ƙara mata ba wasu masu yawa baneba, shiyyasa basu jasu lokaci ba.
  Ganin suna shirin tafiya kamar yanda Abba daya fita tuni suna tare da papa a harabar gidan papa yace ya zasu tafi bayan ana shirin yin taro suma anan.
 Murmushi Abba yayi, yace, “Ai su anjima kaɗanma zasu koma kano, muna musu fatan alkairi dai”. Yoohan da duk ke saurarensu yay saurin cewa, “Uncle Please ka barsu, na maka alƙawarin insha ALLAH zasu sami jirgin safe saisu wuce. Itama zata damu idan taga babu family nata a wajen”.
  Ɗan jimmm Abbah yayi yana nazari, yasan gaskiya Yoohan ɗin ya faɗa, duk da dai su ba ɗabi'arsu bace yin wannan bidi'oin, to amma a yanzu basu da iko akan Aymah tunda sun kawota gidan mijinta. Basu da ikon kuma cewa su Yoohan bazasuyi nasu shagalinba tunda shi aure rahama ne, yin shagali a cikinsa kuma ba aibu bane. Abinda kawai ba'a bukata wuce gona da iri da yin almabazaranci da dukiya. (Wadda a yanzu hakan ne yafi yawa a bukukuwanmu. shiyyasa tun a filin bidi'oin ake zazzage daraja da albarkar auren atafi da gayyar sheɗanu????????????).
   Kansa ya ɗan jinjina da faɗin, “Tom shikenan. Amma bara na fara kiran Yaya (baba malam) na sanar masa tukunna”. Wannan ɗabi'ar tasu na birge Yoohan matuƙa. 
   Bayan Abbah daya koma gefe ya gama waya da Baba malam ya dawo yana faɗin, “Shikenan zasu zauna ɗin, amma yanzu su fito muje idan lokacin yayi sai a kaisu can. Idan mun koma sai ƴan uwanta suzo su tayata zama su yanzun”.
   “Muna godiya Uncle, ALLAH ya ƙara girma”.
Murmushi kawai Abbah yayi, hakama Papa fuskarsa kamar gonar auduga.

★★★★★★

         Tun bayan magriba mai kwalliya tazo yima Aymah. Amma saita tubure akan sai tayi sallar isha'i. Dole aka haƙura akan hakan, duk da su ƴan bikima harsun fara wucewa inda za'a gudanar da shagalin. Duk yanda taso su Amal su sanar mata wanene mijin sunƙi. Dan Amal da Yusrah da wasu ƙawayen Amal ɗin biyu maƙwaftansu suna nan tare da ita. Adawiya kam batazo ba wai kanta ke ciwo tasha magani sai anjima zata biyo su Aunty hibbah. Hakan bai wani damu Aymah ba, dan ita mantawa take ma da babin wata Adawiya yanzun.
  Bayan an idar da sallar isha'i aka rangaɗama amarya Nu'aymah kwalliyar garari. Dan ko makaho ya taɓa saiya jinjina. Hakama su Amal an musu tasu. Momy daketa danne zuciyarta bisa shawarar ƙawartace da kanta ta kawoma Aymah rigar da zata saka wadda garariya garara har ƙasan amuruka akaje sayota daga aljihun papa da umarninsa.
  Nu'aymah taso yin gaddamar sakawa. Amma yanda Momyn ke mata da lallashi ita da ƙawarta ya sakata amsa ta saka ganin rigar akwai hannu a jiki. Ammafa ta bala'i-bala'in haɗuwa sai ɗaukar ido takeyi. Farace tas sai kwalliyar furanni pitch color data ƙawata rigar. Hakan yasa dogon takalminta da shi kansa abin kallone ya kasance pitch. Sarƙa ɗankwali duk pitch. Humm lamarinfa ba'a cewa komai. Ita da kanta Aymah tasan ta haɗu, sai dai zuciyarta a raunane take, dan ta tabbatar ba Yah Ab ɗinta bane angonta. Musamman data san danginta basa irin wannan shirmen bidi'ar, kuma tasan ba Yah Naser bane shima, dan da ace shine katsina za'a kaita. ‘Ni Zainab wanene iyayena suka bama ni’ ta faɗa cikin zuciyarta tana kukan zuci, a fili kuwa idanunta sun cika da ƙwalla. Tayi jarumta sosai wajen ganin basu zubo ba.

  Tare suka tafi dasu madam Chioma a mota ɗaya, dan shi ango yana acan hotel ɗin da za'ayi dinner ɗin, acan suke zaune da abokansa da baƙi da shi kansa wasu ma baisan da zuwan nasuba sai da sukazo ɗin. Dan ba ƙaramar gayya su Rich suka yo ba. Harda abokansu tunna secondary skull.
  Lallai biki yayi biki kam, dan tun a ganin zuƙa-zuƙan motocin dake cike da harabar hotel ɗin har waje zaka san eh lallai manya ne ke lokacinsu. Ga ƴan jarida da ƴan sanda a wajen harda soji. 
    Momy da ƙawarta ne kawai suka fita. Aymah kam zata jira angonta. Su Yusrah ma dake motar bayansu duk sun fito suna tsaye. Ba'a rufa mintuna biyarba sai ga Doctor Yoohan mai zamani ya fito tare da gayyar abokansa. Tab, lallai kam ita ranar aure ta musamman ce ga kowa. Duk da shigar suit ɗabi'arsa ce sai yau tafi ta kullum. A kallo ɗaya zaka gane cewa kuɗaɗe masu nauyi aka zuba wajen sayen kayan. Fararene tas shima sai shirt ɗin ciki ce kaɗai ta kasance pitch. Gashin kan nan nasa da saje sunsha gyara sai walƙiya da ɗaukar idanu sukeyi. Duk da fuskar babu murmushi a sake take bai ɗaure ta ba. Hakan ya saka ƙyawunsa sake fita da ƙyau, ga wani irin kwarjini na angwanci dana ruwan alwala daya fara bin ƙofofin gashinsa na ɗawainiya da shi. Duk da ƙyawun da abokansa sukayi suma duk sai ya damasu ya shanye saboda darajar hasken musilinci.
    Solomon yay saurin buɗe masa motar da Aymah ke a ciki zaune tanata haɗiyar zuciya. Baice komai ba sai matsawa da yayi jikin motar. Ya ɗan ranƙwafa kaɗan yanda zai iya ganinta da ƙyau. A tare hancinansu suka shaƙar musu ƙamshin turaren juna. Kowanne zuciyarsa ta harba kaɗan, musamman ma Yoohan da ƙyawun da Aymah tayi ya nema zarar da shi a tsaye. Amma a fili sai ya fuske abinsa ya miƙa mata tattausan tafin hannunsa, cikin harshensa da baya fita da ƙyau yace, “Bismillah”.
    Wani irin harbawa da ƙarfi ƙirjin Nu'aymah yayi a karo na biyu, duk da kuwa dama ta tsargu tun jin ƙamshin turarensa. Amma sai bata kawoma ranta shiɗinne ba..... Kafin ta fahimci ruɗanin da take neman afkawa taji ya saƙala hannun nasa cikin nata. 
  Da sauri taja zata fisge jikinta na wani irin tsuma. Riƙesa yayi da ƙyau tare da matso fuskarsa gab da tata. A cikin kunnenta yace, “Wlhy kina min tsiwankin nan sai wannan ya shiga jikinki, garama ki nutsu mubar wajen nan lafiya”. Yay maganar yana nuna mata syringe da batasan daga ina ya cirosa ba.
    ‘Innalillahi....’ Aymah kawai ke iya maimaitawa a cikin zuciyarta. Kanta ya sake shigewa a ruɗani har batasan lokacin daya fiddota waje ba, ta dai ganta akan ƙafafuntane kawai dake sanye da dogon takalmi. Sauƙinta ma ta iya tafiya dasu dama can, amma da ansha kunya yau.
    Gaba ɗaya ta zame masa mutum-mutumi, binsa kawai take duk yanda ya juyata. Ƴan jarida da abokansa da duk suka rikice sai zuba musu hotuna suke tako ina. Hasken camaras kawai kake gani babu ƙaƙƙautawa.
   Duk da a cikin abokansa wasu na ganin Nu'aymah tayi kanƙanta hakan bai hanasu taya abokin nasu murna ba da mamakin inda ya samo wannan ƴar shilar. Yoohan dai ya fuske abinsa, dan bayason yayi wani ɗan sakaci da Aymah zata birkice masa a wajen nan. A haka suka shiga cikin hall ɗin daya haɗu harya gaji, decoration ɗin wajen ma komai fari ne da kwalliyar pitch kaɗan-kaɗan. Gashi komai a tsare babu wani hayaniya ko shirme, ga uban haske tako ina tamkar rana. Ko allura ka yadda zaka ɗauka abarka. Kowa yana zaune a inda ya dace da shi. Ita dai kanta na a ƙasa ne bata yarda ta kalli kowa ba duk da uban tafi da ake musu, ga wata waƙar na tashi a hankali cikin hall ɗin. Bayan an musu rakkiya inda ya dace su zauna kowa ya nema wajen zama. Papa ya gudanar da addu'a a wajen da kansa, shidai Yoohan yayi tasa a cikin rai. Nu'aymah ma sunayi tanayin tata cike da takaici. Ita abinda yafi birkitata shine su baba malam basu san Yoohan arne bane suka aura mata kenan? (Kusanfa ita batasan Yoohan ya musulinta ba) wannan bahagon tunanin ne yake neman zauta mata ƙwalwar kai. Shiyyasa tai shiru bata sake koda wani ƙwaƙwƙwaran motsi ba har aka fara gudanar da abinda ya tara mutane. Ita dai komai a shirme ma take kallonsa, sai dai ta ɗanji sanyi a ranta lokacin data ɗaga kai idonta ya sauka akan ahalinta su aunty hibbah da sukazo wajen daga baya. Amma saboda girmamawa a garesu sai aka kawosu gaba inda aka tanadar musu tebiri biyu dama. A yanzunma bataga Adawiya ba tare da su.
   Lokacin da akace su yanka cake tasha uban takaici. Dan ƙin basa tayi. Idanunsa yaɗan lumshe ya buɗe a kanta ganin yanda hall ɗin yay tsit kowa ya zuba musu idanu. “Kinason muji kunya wajen waɗan nan ɗunbin mutanen da suka taru saboda mu ko? To idanfa kinƙi yin yanda akace ALLAH saina miki abinda sai kin kasa fita hall ɗinnan da kafafunkin nan”.
  Gabantane ya faɗi. dan tasan zai iya aikatawar. Tunda har baiji nauyi ko shakkar mata kiss a gidansu ba. Sai da taɗan hararesa ta gefen ido sannan ta ciri cake ɗin da suka yanka ɗin, batare da ta yarda ta kallesa ba takai hannunta bakinsa. Hannun ya kama da nasa hannun ya ƙarasa da cake ɗin cikin bakinsa. Ɗan kaɗan ma ya gutsira ya juya hannun nata dake riƙe a cikin nasa wajen nata bakin. Badan ta so ba ta buɗe kaɗan itama danta ɗan gutsirar sai ya tura mata shi gaba ɗaya tsabar neman rigima. Saurin ɗagowa tai a ɗan zabure, hakan yasata gullewa tai gefe zata faɗi yay azamar riƙo ƙugunta ta dawo kan ƙirjinsa. Tuni tsiwar mutuniyar taku ta motsa, ta ɗago birkitattun idanun nan nata da suka sake girma ruwan hawayen da suka taru a ciki suka sasu wani kala ta musamman. Cikin nasa manyan idanun suka shige caraf, ya sarƙeta da su yanda ya hanata koda motsi suka cigaba da tsaiwa a haka tana a jikinsa idanunsu sarƙe cikin na juna. Gaba ɗaya tama rasa wane kalar bore zatai masa yasan halin da take ciki akan ganinsa matsayin wai miji a gareta. A hankali ta motsa laɓɓanta zatai magana. Yatsansa ya ɗaura saman laɓɓansa. a hankali yace, “Shiiii!!!”. Kasa yin maganar kuwa tayi batare da tasan dalilin hakan ba. Sai ma wata iriyar kasala data saukar mata da bala'in kwarjininsa da bata taɓa ganiba cikin idanunsa.
     Kusan a tare hall ɗin ya ɗauki dariya, sai uban hasken camaras kake gani nata walwala su. Dan yanda suke a tsayen dolene su birge mai kallo, musamman ma'abota son soyayya.
  Saurin yin ƙasa da kai Madam Chioma tayi tare da saka handkerchief ta share hawayen da suka cika mata idanu, badan shirin da suka ƙulla akan yarinyar nan ba ita da ƙawarta da tun a wajen nan saita halakata ta huta akan yaronta da takejin tsananin kishi. Miracle ma tsaki tayi ta miƙe ta fice daga cikin hall ɗin tana kuka, daga nan sai gidan barasa, dan tana buƙatar sheƙe wasu kwalabe ko zata sami nutsuwa. Hakama sauran ƴammatansa da baisan da zamansu ba abun yamusu takaici, ko joy da take ƙanwarsa sai da ranta ya sosu duk da kuwa sun birgeta itama.
    Da sauri Nu'aymah data dawo hayyacinta saboda maganar mc tai saurin saka hannayenta ta ɗan turasa. Sakinta yay badan yaji turawar datai masa ba, sai dan kawai muguntar da tazo masa a cikin rai. Baya ta sakeyi zata faɗi ya riƙo hannunta da sauri ta kuma dawowa jikin nasa. Ya ɗan tsuke fuska kaɗan yana faɗin, “Silly girl”. Sannan ya saketa a hankali. Baki ta murguɗa masa kaɗan tana gyara tsaiwarta zuciyarta na wani irin harbawa da sauri-sauri. Kallo ɗaya taima sashen dasu Ananah suke ta maida idonta ƙasa ta duƙar saboda tsananin jin kunyarsu data lulluɓe ta.

   Haka dai taro ya tashi lafiya bayan anci an sha kamar ba'asan ciwon kuɗi ba. liƙi kam sai kace basu sa zafin nema ba. Dan ƴan dubu-dubu ne sabbi ƙal keta farfar a ƙasa. Musamman lokacin da ango da amarya suka fito filin rawa. Sai dai sunyi tsayene babu wanda ya motsa, dama can kowa yasan Yoohan baya rawa, to bare Aymah da basa samun wannan sakewar a nasu gidan dama.
 Su Osin abokan ango dai dasu Gebrail ƙannen ango an cashe gwargwadon iko. Mawaƙan da sukayi wasa a wajen sun kwashi kuɗi kam gwargwadon iko. Ƙarfe ɗaya dai-dai aka tashi.
  Wasu sun nufi gidajensu ne, wasu kuma anan hotel ɗin, sai masu komawa gidansu Yoohan da amarya. Su Amal dai binsu Aunty Ananah sukayi suka koma gidan Abbah kamar yanda Omar ya tasasu a gaba............✍

ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo????
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).????????

      Mamu gee????

MIN ƘALB!!????????

    Hafsat rano????

ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!????????

    Safiyya huguma???? SIRAƊIN RAYUWA????????

     Bilyn Abdull????

SARAN ƁOYE????????

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka????????????????

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????

09033181070

????????????????????????????????????????
TEAM—-ZAFAFA BIYAR????????????????

ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????.

LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana????????.

No. 46


INA MA’ABOTA KARATUN LITTATTAFAN HAUSA? WANDA ZAI NISHADANTAR DAKU, YA FADAKAR, YA KUMA TSUNDUMA KU A KOGIN LOBAYYAR KAUNA? TO KU MATSO KUSA… DOMIN MUNZO MUKU DA ALBISHIR DIN WANI GANGARIYAR LITTAFI.. DAYA NE TAMKAR DA DUBU.. YAZO DA WANI SALO NA DABAN WANDA ZAI SANYAYA ZUKATAH..

LITTAFIN UNCLE NE… LITTAFI NE FIRST OF ITS KIND, DA YAZO A WANNAN SHEKARA TA 2021. AN BAJE KOLIN BASIRA A BOOK DIN UNCLE NE..

”Wait… Dakata hafsat Rano, Kina nufin NIMCYLUV, dai shararriyar murubuciyar nan itace tazo da wani salon rubutun..?..”

”Kede bari Billyn Abdul.. Tsaya kiji kanun labarin a tak’aice..NIMCYLUV Tace book din a ta’kaice labarin UNCLE NE ne yana tafe:

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button