SARAN BOYE COMPLETE

_★★★
A kano ta dabo kam baƙi sun isa gida lafiya da shatara ta arziƙin da suka samu. yanzun kam gidan ya koma shiru duk baƙi sun kama gabansu, hakan yasa suma duk basu wani yi zaman awa bibbiyu ba a gidan duk suka tafi. Sai Ananah kawai da ba yaune ranar tafiyar tataba ita. Amma jikokinta da sauran ƴaƴanta duk sun koma katsina tun jiya...........✍
Kuyi manage da wannan bajin daɗin jikina nakeba, mura tamin ram????????.
Hafsat miss xoxo????
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).????????
Mamu gee????
MIN ƘALB!!????????
Hafsat rano????
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!????????
Safiyya huguma???? SIRAƊIN RAYUWA????????
Bilyn Abdull????
SARAN ƁOYE????????
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka????????????????
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????
09033181070
????????????????????????????????????????
TEAM—-ZAFAFA BIYAR????????????????
LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana????????.
No. 47
I’m on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p.
INA MA’ABOTA KARATUN LITTATTAFAN HAUSA? WANDA ZAI NISHADANTAR DAKU, YA FADAKAR, YA KUMA TSUNDUMA KU A KOGIN LOBAYYAR KAUNA? TO KU MATSO KUSA... DOMIN MUNZO MUKU DA ALBISHIR DIN WANI GANGARIYAR LITTAFI.. DAYA NE TAMKAR DA DUBU.. YAZO DA WANI SALO NA DABAN WANDA ZAI SANYAYA ZUKATAH.._
LITTAFIN UNCLE NE… LITTAFI NE FIRST OF ITS KIND, DA YAZO A WANNAN SHEKARA TA 2021. AN BAJE KOLIN BASIRA A BOOK DIN UNCLE NE..
”Wait… Dakata hafsat Rano, Kina nufin NIMCYLUV, dai shararriyar murubuciyar nan itace tazo da wani salon rubutun..?..”
”Kede bari Billyn Abdul.. Tsaya kiji kanun labarin a tak’aice..NIMCYLUV Tace book din a ta’kaice labarin UNCLE NE ne yana tafe:
Da farko yana mata kallon uwa wacce ta haife shi kuma jigon rayuwarsa, ashe itace silar rushewar rayuwarsa????yarinyar da yakewa kallon ƙanwa uwa ɗaya Uba ɗaya ita aka wayi gari ta zama MATAR SA????????♀️ ƙaddara ta haɗashi da (Ahlil kitab) kiristan ya bata farin ciki, kulawa, soyayya, harya samu ta musulunta, Dalilinta sbd al’ƙawarin aure da yyi mata,ashe ba sonta yake ba????yaje birnin NUFAR domin kai masu tayin Muslunci, sun amince da hakan amma sharaɗin dole ya kwanta da ƴarsu,????????♀️gashi bashi da cikakkiyar lfy mazantakarsa bata aiki???? ashe mahaukaciya ce ta haife shi..
“Kai lalle akwai runguntsumi acikin wannan littafi.. Ba za’ayi babu ni ba, Domin Za’a sha lagwadar romon dadi. shin tayaya ake biya Hansatu?”
”Ai ta Abdul..LITTAFIN UNCLE NE Naira 300 ne, Idan kuma kana son vip inda za’a ake posting sau biyu a rana kuma za’a baku littafan data rubuta na kuɗi sai ka bada 600 mai ma kon 1k.. number asusu wato bank account details: 0116886423 : account name sulaiman Na’ima S. Bank name: unioun bank: Sai a tura shedar biya ta 08119237616… A nuna mata ƙauna ta hanyar turowa ta account????????kamar yadda Za’a faranta maku a littafin UNCLE NE
(Best romantic love story of the year//Had’adden labarin kauna na shekarar 2021)
No. 47
………..Sosai Nu’aymah tasha barcinta. Dan sai gab da la’asar ta sake farkawa. Yanzun kam Alhmdllh garas take jinta, sai dai jinta take wata fiyau tamkar iska zata ɗauketa ta yada saboda rashin nauyi. Wanka ta fara yowa da alwala. Tazo tai salloli sannan ta kimtsa ɗakin duk da bayyi wani datti ba. Tunda ta buɗe kwanikan dake saman tray ɗin da ke bisa centre table sau ɗaya bata sake ba. Sai ƙunƙuni da ta dingayi akan ita bazataci wannan jagwalgwalon abincin ba yasin. Dan duk da uban naman dake cikin miyar baiko birgeta ba.
Tsaf tai shiri cikin riga da sket na atanfa. Kayan sun mata ƙyau sosai. Tana cikin saka turare aka turo ƙofar. Saurin juyawa tayi danjin babu wani knocking balle a kai ga sallama. Haushi ya tuƙeta ganin Yoohan ne. Ta ɗauke kanta tana ɓata fuska.
Yoohan da waya ke manne a kunnensa alamar magana ya keyi da wani shima ɗin dai kallo ɗaya yay mata ya ɗauke idonsa, zama yay a kan sofa ya cigaba da sauraren abokin wayar tasa dake masa bayani daga can. Ita Aymah ma harta fara tunanin ko wani sabon wulaƙancine ba wayar yake ba. Dan ya kusan mintuna sha biyar wayar na kunnensa amma baice komaiba.. Dai-dai ta ɗago ta kallesa taji ya ɗan sauke numfashi, sai kuma ya fara magana a hankali cike da nutsuwa. Harga ALLAH bazata ɓoye ba muryarsa na mata daɗi. Ita bata buɗe yanda zaka tsorata mai sauraro ba, ba kuma ta sirance kamar ta mata ba. Tana fita da kauri da amo musamman daya kasance shi ma’abocin magana ne a nutse.
Haka ta dinga satar kallonsa harya kammala wayar. Ya cire daga kunne yana ɗago idanumsa kanta. “Am sorry, Assalamu alaiki”. Ya faɗa yana janye idanun kanta lokaci guda. Amsa masa tayi fuska a tsuke, kamar zata ɗauke kanta sai kuma ta sake dubansa. “Nifa yunwa nakeji”.
Da mamaki ya kalleta, sai kuma ya duba tray ɗin dake a jiye a wajen. Tabbas bana safe bane. Kulolin ya buɗe batare da yace mata komaiba. “Shi wannan abincin kuma fa?”. Ya faɗa yana kallonta. Baki ta kunbura tana wani sake tsuke fuska, “Yoni bazanci wannan abincin ba, dan ban iya cinsa ba”.
Shiru ya ɗanyi yana kallon abincin shima. Eba ne da wata miya da suke kira Abak Atama soup (miya ce da mutanen Akwa ibom state suke yinta) taji uban nama sai ƙamshi takeyi. Tabbas yasan da wahala ta iya ci ɗin, tunda abincine irin nasu. “Mi zaki ci to?”. Yanda yay maganar a daƙile ne ya sakata sake jin haushinsa, tai masa harar gefen ido. Kamar bazata faɗa ba sai kuma tace, “Noodles”.
Batare da ya ƙara kallonta ba ya ɗauka waya yay kiran Joy. Ring biyu kuwa ta ɗaga. Ko gaisuwar datai masa bai amsa ba yace, “Dafa min Noodles”. Daga can tace, “Okay Brother, and egg?”. Bai amsata ba, sai duban Aymah da yayi, wadda ya tabbatar tana jinsu tunda a Hans free ya saka. Kanta kawai ta ɗaga masa ta ɗauke idonta daga garesa. Amsa ya bama Joy ɗin da faɗa mata inda zata kawo ya yanke wayarsa.
Daga haka ɗakin ya ɗauki shiru, shi dai wayarsa ya keta latsawa, ita ko tana zaune a stool ɗin mirror ne kawai tana kallonsa ta ciki fuska a kumbure. Ba komai ke cinta ba sai kewar gida da yunwa. Damuwace fal ranta, a kallo ɗaya kuma zaka tabbatar da hakan.
Knocking ɗin da akayi ne ya sakashi faɗin “Shigo” a taƙaice batare da yako ɗago daga abinda yakeyi ba. Gabansa Joy taje ta ajiye tiren batare data kalli inda Aymah take ba, “Broth gashi, nikam inata mamaki, wai kai ne da cin Noodles yau a gidannan?”.
Wani mugun taɓe baki Aymah tayi ta ɗauke kanta daga kallonsu, a ranta kuwa rayawa take saita saita kan joy ɗinnan a layi idan har tace zatai mata hauka. Dan duk da ta girmeta sosai ai ita yanzu matar yayanta ce dan ƙaniyarta. (Madam son girma????lol).
Yoohan kam da ya gama sauraren Joy a taƙaice yace, “Thanks”. kawai. Duk da Joy tasan halinsa, ba kuma yau ne farauba sai na yau ɗin yay mata zafi saboda agaban Nu’aymah ne. A hasale ta nufi ƙofa tana harar inda Nu’aymah take. yanda ta fisgi ƙofar ɗakin da zata rufe ne ya sakashi ɗagowa, sai dai kafin yace komai ta bar wajen da gudu.
Shiru yay baice komaiba, sai idanunsa daya maido kan Nu’aymah. “Kizo kici zamuje ki gaida Momy da Papa”. Batare data dubesa ba tace, “Badai mai wancan zaƙo-zaƙon farcen bace ta dafa min ko?”. Yanzun kam sosai Yoohan yake kallonta, a ransa yake faɗin, ‘Yarinyar nan muguwar ƴar matsala ce wlhy’. A fili kam fuska ya ƙara tsukewa yana tsatstsare ta da idanu. “Kina ɓatamin lokaci malama, inada abu mai muhimmanci a gabana”. Kanta ta maida gefe tana ƙyaɓe baki, cikin ƙunƙuni da hausa tace, ‘Da waye ya gayyatoka anan balle ka ɗagan hanci’. Ta ƙare maganar tana tasowa inda yake. dan harga ALLAH wata shegiyar yunwa kecin hanjin cikinta.
Shikam baima sake bi takanta ba, ya cigaba da sabgar gabansa a wayar. Ba ƙaramin danne zuciya Aymah tayi ba wajen zaman cin indomie ɗin nan. Dan babu abinda ke zuwa mata a cikin rai sai farcen dake a hannun Joy zaƙo-zaƙo da tarin gashin dokin da akai mata kitso da shi kamar jikar bammali. Ko rabi kuwa bataci ba ta ture gefe.
Kallonta yay fuska a tsuke, cike da ƙosawa yace, “Wazai ci miki wannan ɗin?”. “To oho, ni dai na ƙoshi, yama zaka saka wancan mai farcen da Attachment ɗin kamar ɗiyar bammali taimin girki. Wanda naci ma da wahala ya zauna dan amai nakeji dana tunota. Ga uban bleaching tayi sai ƙarni takeyi”.
Sosai yaji zafin abinda take faɗa akan ƴar uwarsa, amma sai yake mata uzirin ƙuruciya ce kawai ke ɗauwainiya da ita. Watsar da ita yay bai sake duban ko inda take ba har tsahon mintuna uku. Kafin ya miƙe yana zura wayarsa a aljihu. “Muje” ya faɗa a taƙaice yana yin gaba abinsa.
‘Tab! Wai kaji haushi ne dan na faɗa abinda ke raina? Aiko aiki ya sameka, dan bazan ga abin maganaba nai shiru bakina yay wari. Da wani kansa kamar mulmulen furar hajjo’. Tai maganar tana miƙewa. Dan itama zaman ɗakin ya fara isarta kuma. Tanason taga gidan yaya yake?. gyale ta ɗauka da yay dai-dai da atanfar ta biyosa. A falo ta samesa tsaye, batare da yayi magana ba yay gaba ta bisa a baya suka fice.