SARAN BOYE COMPLETE

Da Sauri na Dago har a lokacin hawaye kawai ke zuba a fuskata “Ga Auntynki Nan Hindatu matar Naseer Kuma zabina duk abinda take so shi za’ayi a gidanan duk aikin data sakaki ki tabbata kinyi Mata idan ba Haka ba wlh ranki ne zai b’aci kindai San halina sai dai ki bawa wani labari Dan Haka Maza tashi kije ki zab’a a cikin Dakunan can Wanda yafi girma ki gyara ki zo ki kwashe Kayanta ki Kai Mata ki saka Mata kuma.ruwan wanka idan kin fito ki daka Mana Sakwara muci kinji ko bakiji ba”?
Da sauri na gyad’a mata Kai na mike na nufi d’akin karshe Dan yafi na tsakiyar girma da Umma ta zauna ita da Saffiya.
Ina gyara d’akin Ina kuka wai ni Haka rayuwata zata Kare daga wanan sai wanan Mai Nayiwa Umma Haka ta tsaneni.
Ina Gama gyara d’akin na wanke band’akin dayake da ruwa a band’akin na tari ruwa a bokiti Yana cika na fito.
Na koma palon na fara kwaso kayan Hindatun Ina kaiwa daki Umma sai zagina take Tana zagin iyayena ita kuwa kawarta kur tamin Ido kamar zata cinyeni Ni kuwa na hau addua a Zuciyata Dan kallon da takemin yayi yawa ita kuwa Hindatu sai wani girgije girgije take Tana yatsina fuska.
Ina fitowa daga d’akin na shiga kitchen na fito da doya manya guda biyu na fara feraye wa Ina cikin ferayan naji Sallamar su Zahira.
Babu Wanda ya amsa musu bansan ya akayi ba sai ji nayi Zahira ta kwalla wani uban ihu sai dum dum nakeji kamar irin an samu babba Ana duka.
Jikina ne ya hau rawa na runtse Ido hawaye na zubomin ko ban lek’a ba nasan Umma ce ke dukan Zahira na Dade da sanin Umma ta balain tsanar zahira Ni nasan tsanar data min ne ya shafi Zahira shiyasa ma a cikin Yarana Zahira ko muryar Umma taji sai ta nutsu kaga alamar tsoro ya bayyana fuskar ta sosai dukan da takewa zahira na ringa jinsa a jikina ta Sha dukan Zahira ba tare da ta Mata komai ba na Kuma rasa Mai Yar yarinya da Bata fi shekara bakwai ba ta Mata.
Zagin Zahira kawai take Tana durma Mata duka tana “shegiyar yarinya tun kina karamarki an koya Miki bakin Hali baki iya Gaisuwa ba wane irin tarbiya Naeema ta muku wato ita ta kitsa muku idan Kun gani karku gaisheni ayi yara basuda tarbiyya balle wanan Yar iskar yarinya Ni nasan yarinya Nan idan ta girma Yar iska zata Zama shegiya Mai halin uwarta”
Naseer dake Sallah a a guje ya fito daya Sallame Sallar sabida yanda Zahira ke ihu Dan ba karamin Jibga take mata ba.
Nadeeya kuwa Tana gefe tana kuka
Fusge Zahira yayi cikin wani irin B’acin Rai ya kalli Hajara Yana “Haba umma Mai karamar yarinya Nan ta miki kike dukanta Haka kamar kin samu babba haba Umma “
“Zaka iya Rama Mata tunda na daki Yar gwal Naseeru Kai baka ganin irin tarbiyya da shegiyar matarka ta musu kwanaki Dana zo suna kallona Suka k’i gaisheni yanzu Kuma sun shigo wanan Yar iskar yarinya ta zo zata wuce ta gabana har da taka min kafa duk idonka Bai bud’e kaga irin tarbiyyar da Naeema ta musu ba sanan Dan na daketa kazo ka tsaya kana min tambayoyi Na daketa Naseer zaka iya Rama Mata nidai sukayi ba daidai ba Dole na hukunta su daga Kai har Naeema San Yaya ya rufe muku Ido Kun kasa musu tarbiyya ko baki akayi ai Dole aji kunya ai tunda yarinya Nan ta kwaso uwarta nasan inta girma ba lailai tayi albarka ba”
“Allah ya Miki albarka Zahira zakiyi Albarka insha Allahu nace Ina kankame wuk’ar hannuna da har ya yankeni jini na zuba bansani ba sosai kalmomin da Umma ke jifan Zahira dashi ya ringa min ciwo har tsanar ba iya Ni ya tsaya ba har Kan zahira da bani kadai na haifeta ba Jinin Naseer daya kasance danta na yawo a jikinta har Umma tace Zahira Yar iska zata zama baza tayi albarka ba wanan wane irin kiyayya ne kuka nake kasa kasa Ina jiyo muryar Naseer na “Umma wane irin kalamai kike Yi Haka karki manta fa yarinya Nan jikar ki ce akan me Zaki na cewa baza tayi albarka ba insha Allahu yayana zasuyi albarka Umma Dan Allah Umma kiringa kiyaye kalmomin da zasu fito bakinki Zahira fa yarinya ce ballantana kice ta mallaki hankalinta Umma Kinga yanda Kika kumbura Mata jiki fisabillilahi idan Haushin Mahaifiyarta kike ji ai Bai Kamata laifinta ya shafeta ba nawa Zahira take tsakani da Allah Naeema na iya kokari Akan yaran nan ba Kuma Ina fada Dan na kareta ba”
“Ai duka nake jira kamin Naseer ya ka tsaya iya surutai”
Naseer da idonsa ya kad’a yayi ja Bai ce komai ba ya daga Zahira da numfashin kirki ma Bata iyayi ya Kai ta d’aki dawo ya rik’e hannun Nadeeya ya d’auki Humaira da ihun zahira ya tasheta take ta kuka itama”
Nima kukan Humaira ne yasa naso fitowa daga kitchen din na d’auketa na goya ta sai Naga Naseer ya d’auketa
Hakane yasa na koma kitchen na daure hannuna da jini ke ta zuba na cigaba da aikina Ina kuka Ina tunanin abin Yi Taya ya ma Zan iya barin yayana tayaya Zan iya tafiya na bar yarana a hannun Umma da Raina Agaban idona tana azabtar min da Yaya inaga bana Nan.
Ina cikin had’a Miya naji Sallamar Mmn Mannir nasan Minal ta kawomin tunda Magriba ta kawo Kai
Gaida su Umma take naji Umma na tambayarta daga Ina take
Mmn Mannir kuwa Tana Mata wanan tambayar tasan wacece ita kuwa ta had’e Rai tana Ina matar gidan take”?
Take Hindatu ta watsa Mata harara tana “Gani Nan nice matar gidan ya akayi”?
Wani kallon Tara saura kwata Mmn Mannir ta mata ta ja Tsaki tayo hanyar kitchen da take Jin motsina ciki.
Ni kuwa Ina kitchen Ina Jin maganr da suke jikina ya hau rawa.
Har kitchen mmn Mannir ta shigo ta ajiye abincin hannunta ta kunto Minal da Saura wata biyu tayi shekara biyu da bacci ya d’auketa tana “Gata Nan tayi bacci Naga alamar yau gidan naki a cike yake toh nidai shawarar da Zan baki shine wlh ki kwatarwa kanki ‘yanci ki rage tsoron Nan idan babba Bai ji kunyar hawa jaki ba toh jaki bazai ji kunyar kayar dashi ba.
Ihu kawai mukaji Umma nayi ta hau kururuwa
Sosai hankalina ya tashi na rude da ganinta a bakin kitchen abinda ya ban tsoro yanda take zunduma ihu
“Yanzu Ni kike cewa jaka Yar nan Mai na Miki”?
Naseer a guje ya fad’o kitchen din mmn Mannir kuwa ta saki baki cikin mamakin sharrin da Umma ke neman Yi Mata
Kuka umma ta saka ta kalli Naseer dake ta tambayar Mai ya faru
Ta hau cewa “wanan yarinya Nan ce tayi Sallama muka amsa tana ganinmu taja Tsaki ta wuce mu ta shiga kitchen dinan shine Ni Kuma nayi mamakin tsakin da ta Mana shine na biyota naji dalilin dayasa ta Mana Tsaki Ina zuwa naji tana cewa Naeema wacce jakar ce wancan Yanzu Naseer har maganata Naeema keyi da wasu har a shigo Inda nake ace min jaka toh wlh daga yau Kar na Kara ganin kafar matar Nan a gidanan wlh daga yau Kar na Kara ganinta da Naeema idan ba Haka ba daga Kai har Naeema sai na dau mummunan mataki akanku da ganin matar Nan ba matuniyar arzki bace”
“Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun yanzu mama da girmanki kike karya da girmanki Zaki min sharri Ni nace Miki jaka kiji tsoron Allah”
Naseer kana kallo tana cemin Ina karya bazaka dau mataki ba”
Mmn Mannir Bata Bari ma Naseer yayi magana ba ta mik’a min Minal tana “ba sai kin biyo ta Haka Zaki rabani da Naeema ba ki kwantar da hankalinki bazan Kara zuwa ba kamar yanda kikeso sabida na lura bakyaso kowa ya rab’i Naeema Sabida ki yi ta azabtar da ita Kar tayi hulda da kowa ballantana a kawo mata d’auki toh Bari kiji na fada miki kiji tsoron Allah domin shi sharri Dan aikene watarana zai dawo Miki tun a gidan Duniya Allah ke hisabi kuma Zaki ga karshenki Naeema Zan tafi xan Kuma baki shawara idan Kinga akwai cutarwa a zamanku ki hakura da Naseer tunda Zama da danta ba Dole bane daga Haka ta bangaje Hajara tayi wucewarta.