NOVELSSARAN BOYE

SARAN BOYE COMPLETE

REAL FEEDO hazikar marubuciyar nan ta zo muku da wani gangariyar littafi mai suna: BA AMO…! BA AMO wani nazartaccen littafi ne daya zo da wani irin salo na daban…

Labarin BA AMO ya faru akan wata yarinya da d’an sarkin garin su, yarinyar gidan su gidan yawa ne…Baban su yana auri saki ya tara ‘ya’ya da mata da yawa. Tirqashi! To ita yarinya sunan ta KHAIRAT… Tun farko dangin mahaifin su sun tsani mahaifiyar tasu,Bayan ya auro ta, Ta haifi yara mata zallah suna kiran ta da uwar mata kuma kwata-kwata basa kaunar ita da ‘ya’yan nata. To ita yarinya ta gama karatun ta…. wato KHAIRAT.. shekarun ta 22 matan gidan nasu suna mata gorin tayi kwantai tak’i aure. Kwatsam wata rana yarinyar ta samu labarin d’an sarkin garin su ya bude sabon company ya fara daukan sabbin ma’aikata, ????????♂️????cikin ikon Allah ta zuwa ta samu aiki. Ta fara zuwa aikin ta, a karshe su kansu da suka fahimci kwazan ta da nutsuwar ta samu karin matsayi. To a lokacin ne kuma Yarima da PA dinsa suka sami matsala aka kore ta a ma’aikata sai aka daura ita Khairat d’in a matsayin P.A dinsa. Tafiyar tasu batama yi nisa ba! Aka yi makiya suka yi masu sharrin wai karuwar sa ce, har labarin yaje gun mai martaba. Itama Khairat d’in labarin yaje ga mahaifin ta har ya nemi korar ta daga gidan sa, da kyar aka lallashe shi ya hakura..

Tab rungutsumi din fa kenan????Ya zata kaya ne ga YAREEMAH GA KHAIRAT..a roof d’aya? Ya rabbi???? labarin kauna yayi.. Amma fa Za’a sha rikici.. Karku manta khairat daga gidan yawa tafito????Ga basuda wani hali.. Shin sarki zai yadda da Khairat amatsayin personal assistant din yareemah ko kuwa.? Duk wannan ruguntsumi n REAL FEEDO ce kadai zata iya warware mana..

BA AMO::::: (Ba Labari…)

DOMIN MALLAKAR NAKI/‘NAKA TUNTUBE MU TA: +227 81 73 10 21


No. 50

…………Ya jima tsaye a jikin ƙofar wutar kansa a ɗauke. Kafin ya ja ƙafa da ƙyar zuwa saman gadonsa. Duk yanda yaso barci ya ɗaukesa hakan ya gagara, har kusan 2, daga ƙarshe dai ya miƙe zuwa toilet, ruwa ya sakarma kansa kafin ya ɗauro alwala ya fito. Daga haka yay nafilfilin daya saba, ganin ya kai har asuba saiya bari sai da yay sallar asuba ɗin sannan ya haye gadon ya kwanta ko azkar yau bai iya kammalawa ba saboda barcin dake cike da idanunsa.

      A ɓangarrn Aymah kuwa kanta ta dafe tare dayin jifa da hijjabin tana ballama ƙofar harara, sai kuma ta zabura ga ƙofar ta murza mata key wai karya dawo. Addu'a ta komayi akan ALLAH yasa bai ganta da ƙyauba, idanko ya ganta to bata yafe ba (dan ƙari????). Da ƙunƙuni ta koma gaban mirror ɗin inda ya ajiye tea ɗin, babu kunya ta zauna ta sha dan dama ƴar yunwa na cinta ƙasa-ƙasa, alwashin data ɗauka na daina cin abincin gidanne kawai ya sata cewa ta ƙoshi. Sai da ta shanye tsaf taci rabin biscuit ɗin sannan taje ta sake yo brush tazo tai kwanciyarta.

★★★★

    A ɓangaren madam Chioma kam ta fitane da wani irin jin zafi da takaicin Aymah, dan ita duk a tunaninta da biyu tayi abinda tayi. Batasan ita Nu'aymah ko tarin farko da tayi, tayine kawai dan neman tsokana bawai danta kawo wani abu a ranta game da zaman nasu ba, tunda tasan sudai basu ɗauki taɓa jikin juna komaiba musamman ma ita dake a matsayin mahaifiyarsa. Ko kallon Victoria da Abraham dake rigima akan camara batai ba ta shigewarta ɗakinta ta banko ƙofa. Zama tai kan sofa zuciyarta tamkar zata tarwatse dan tsanar Aymah. Waya ta ɗauka kamar zata kira ƙawarta sai kuma ta fasa, a ganinta gara ta bari su haɗu a church jibi lahadi zasufi yin maganar yanda ya kamata ai.
  Hular gashin dake a kanta ta tuge ta ajiye, cirkuɗaɗɗen ainahin nata dake guntu ya bayyana. Fitowa ta sakeyi daga ɗakin zuwa sashen Papa. Baya falo, dan haka ta nufi bedroom ɗinsa kai tsaye. Saurin tura hoton hannunsa da lighter da zai ƙonashi yayi ƙarƙashin gado dan yazata cikin yaransa ne wani ya shigo masa. Amma ganin matarsa ne sai ya ɗan sauke ajiyar zuciya. Sai dai hakan baisashi sake ɗakko hotonba duk da itama tasan wani abu akan hoton.
 Ita sam bama ta lura da abinda yayi ba, ta zauna a bakin gadon kusa da shi tana hawaye. Duk rikicewa yayi, ya shiga jera mata tambayaoyi da rungumota jikinsa. Bata iya bashi amsaba sai da tai kukanta ta more sannan ta labarta masa abinda ya faru. Murmushi yayi dan shi baiga wani abin fushi ba anan, a fili kam sai yace, “Uhm-uhm Darling cool down, ke mima ya kaiki sashensu yanzu? Kin sanfa yanzu yana da mata, duk kulawar da kike tunanin baya samu yanzu akwai mai masa”. Ɗan turesa tai ta tashi zaune sosai. Ya ƙyalƙyale da dariya yana riƙo hannunta, “Ah son ƴaƴa yamiki yawa Madam, karfa kice zaki ringa irin halin su mama akan matar John Please, dan indai kina nuna mata ƙi bazamuci nasara akan burinmu ba zaki rusa mana aiki”.
       “Honey yarinyar nan bata da kunya, ciwon da kaga Mira taji fa itace ta saka mata ƙafa ta faɗi saboda ta mata tsaki”. Idanu papa ya zaro waje sosai da faɗin, “Da gaske?”. “Na rantse maka kuwa Honey, abinda yasa nai shiru banyi maganaba saboda itama Miracle ɗin shegiyan kanta ne, danni tama isheni a gidan nan, ya kamata ta koma gidansu hakanan tunda ta kammala karatun ai”.
   Da sauri Papa yace, “No baza'ayi hakaba Darling, kawai dai zan mata gargaɗi karta sake shiga rayuwar matar John, inba hakaba kuwa shine da kansa zai koreta a gidan nan tunda tasan halinsa”. Wani shegen kallo Madam Chioma kema Papa mai cike da tuhuma. Amma sai ya basar kamar bai ganta ba. “Humm” ta faɗa tana haɗiye abinda ke a ranta. a ganinta inma hakanne ai zata saka idanu ta tabbatar. “Naji, yanzu dai inason kaima John magana, dolene idan yana garin nan ya ringa fita church bawai dole sai Sunday ba. Idan bamuyi hakaba yarinyar nan zata iya sakashi ya fara salla. Gara mu saka masa ido sosai itama kanta duk Sunday ya sata tana binmu tunda akwai addu'oin da ake masa, tunda kuma yanada mata kaima kasan a ƙa'ida dole saita ringa kasancewa a wajen”.
    “Eh maganarki gaskiyane kam, zan zauna da shi sai muyi magana”.
  Kanta ta jinjina masa alamar gamsuwa. Daga haka suka cigaba da hirarsu har ya manta da batun ƙona hoto ma.

  A ranar gaba ɗaya Nu'aymah wasan ɓuya ta dingayi da Yoohan, gaba ɗaya taƙi yarda su haɗu har yamma duk da dai ya daɗe bai tashi a barci bane, sai gab da azhur ya tashi, yana yin wanka kuma yay shirin massallaci ya fita. A lokacinne ya isketa a falo tana kallo. Amma tanajin motsinsa ta tashi da gudu ta shige ɗakinta harda mirza key. Shi dariya ma ta bashi a lokacin, amma sai ya gimtse baiyiba yay ficewarsa dan ya kusa makara.

      Sai bayan sallar la'asar ya dawo massallaci ne ya ritsata ta fito zataje garden. Karo sukayi a bakin ƙofa, tai baya da sauri tana tura baki gaba da dafe goshinta. Uffan baice mata ba, sai idanu daya kafeta da shi. Dan doguwar rigar atamfar jikinta ta mata ɗas, daka ganta kaga cikkakkiyar bahaushiya ƴar arewaci.
    Jin yaƙi cemata sannu ta sake tura bakin tana tara hawayen ƙarya, ita a lallai dole taji zafin bigewar da tayi. Raɓashi tayi zata wuce yay azamar riƙo hannunta ya dawo da ita gabansa. “Kin gama gudun?”. Ya faɗa a hankali kamar bayaso. Yanda yay maganar muryarsa a sanyaye ne yasa kallonsa da sauri, kallon ido cikin ido sukaima juna, ya ɗan lumshe nasa dake da ja a ciki, gashi sun ɗan kumbure ya sake buɗewa a kanta.
  Samun kanta tai da faɗin, “Baka da lafiya?”. Kansa ya ɗan jinjina mata da yamutse fuska, kafin yace, “Kaina ke min ciwo”. Ya bata amsa yana sakin hannunta dake cikin nashi. 
 A bazata yaji tace, “Dama likitoci na rashin lafiya?”. Tai maganar da waro idanunta manya waje sosai. A karan farko ya saki murmushi yana ƙoƙarin raɓata zai wuce, sai da ya shige falon sosai sannan yace, “Shi likita ba mutum bane?”.
     Harta buɗe baki zatayi magana sai ta fasa saboda hango Papa na sakkowa daga sama waya a kunnensa. Sai dai kuma idanunsa na kansu da ga ita har Yoohan ɗin. Juyawa tai ta fice abinta.

★★★★_

KANO TA DABO

    Kamar yanda baba malam yayma Umm bayani akan ƴar aiki da Aymah ta buƙata daga nan, itama Hajjo ya sameta da zancen, Ɗari bisa ɗari hajjo ta bada goyon baya, sai dai tace ya kamata a tuntunɓi Yoohan idan ya amince, idan bai aminceba a haƙura kawai, a hankali zata saba da waɗanda ƙadadara ta kaita zama da su. Harma suna mata fatan cin riba akan hakan. 
   Duk da baba malam ya riga da yayi magana da Yoohan akan maganar tun kwana biyu daya wuce sai ya amsama hajjo da cewar insha ALLAH a yau zai tuntuɓi Yoohan ɗin, yanda sukayi kuma zataji. A ransa kuwa da biyu yaƙi faɗa mata gaskiyar yanda al'amarin zai kasance. Ba komai ya jawo hakaba sai laɓe daya fahimci anai musu shi da Umm kwana biyun nan, inuwarnan daya gani a ranar da za'a kai Aymah Abuja. Sai kuma ya sake ganinta randa yakema Umm bayani akan wayar da sukayi da Nu'aymah. Sai dai yayi shiru da bakinsa ko Umm ɗin bai sanarmawa ba. Sai Yoohan da shima yay masa zancen ganin mutum a randa akai maganar cikin nan na Aymah,  dan randa Nu'aymah tai masa maganar mai aiki daga nan kano ya kira baba malam sunyi doguwar waya.
  A yanzu haka fatansa ALLAH yasa maganar da sukayi da hajjo an laɓe musu ɗin. Dan duk mai aikata musu SARAN ƁOYEN zaiso ace koma wace ƴar aiki za'a turama Nu'aymah ya samu dangantakar da zai ringa samin bayanai akan Aymah.
  Baba malam ya jima a wajen Hajjo da tunanin ko zai sake ganin inuwar mai laɓen nan. sai dai harya ƙaraci zamansa da kallon windows babu ko ƙyallin mutum balle wata inuwa. Hakan ya bashi mamaki amma sai ya share dan baya buƙatar hajjo ta fahimci komai tun yanzun, sai sun kammala ɗana tarkunansu tsaf sannan.

     Washe gari baba Malam ya sake samun Hajjo da maganar cewar Yoohan ya amince da maganar mai aikin. Fuskar Hajjo faɗaɗe da murmushi tace, “To to Alhmdllhi, madalla da ɗan albarka Yahya. Kaga bara na shiga nan gidan Iyami da kaina sai na mata bayanin a samo mai hankali ba yarinya irin Zainabu ba. Dan bazai yuwu a irin wannan zaman a haɗa ƙuruciya da ƙuruciya ba. Sai dai wadda taɗan tasa idan taga ba dai-dai ba ta nusar da ita”.
   “Eh gaskiya ne inna, hakan yayi kam. Dan mamana halinta kam sai ita, inba mai ɗorata a hanyar aka samoba sai aita samun matsala dan har yanzun hankali bawai ya gama isarta bane”.
      “Ai karka damu ɗan malam, wlhy duk abinda kaga Zainabu nayi nima nayisa, babu abinda ta bari na ƙuruciyata. Malam yasha fama dani bana wasa ba. Amma kaga ina fara haihuwa duk saina rage nawa. Garama Zainabu ai a shekarun da akai mata aure ta tasa fiye dani. Tunda ni ina sha uku aka aurama babanku ni, itako sha bakwai fa harda wasu watanni”.
      Baba malam dai kansa a ƙasa yanata ƙoƙarin haɗiye dariyarsa. Dan shima kafin mahaifinsu ya rasu ya taɓa bashi labarin ƙiriniyar da Hajjon tayi a gidansa. Da yake shi haka yake, duk randa ƴan labarin nasa ya motsa sai ya zaunar dasu yayta basu tarihin gwagwarmayar da yayi ta rayuwa harma da ƙuruciyarsu. Wannan ɗabi'ar ta mahaifinsu tana ɗaya daga cikin abinda basa iya mantawa a rayuwarsu su duka.

    Kamar yanda Hajjo tai alƙawari da yamma kuwa sai ta shiga gidan su Hamisu wajen mahaifiyarsa Iyami. Sosai Iyami ta dinga haba-haba da hajjo duk da kuwa kasancewar su maƙwafta. Amma da yake ba ɗabi'ar shige-shigence da suba inba da ƙwaƙwaran dalili ba, sai yazam duk randa akaga juna kamar baƙi.
   Bayan sun gaisa hajjo tasha ruwan da Iyami ta kawo mata duk da ba ƙishin take jiba, sai dai a cewarta ruwan zuminci yafi zuma garɗi. “Yauwa Iyami nasan kinata mamakin ganina da maraicen nan. To dama ba wani abune ya sani fitarnan ba ta gabannin magriba sai takwarata ƴar jikalleta Zainabu da aka kai Abuja”.
    Iyami dake murmushi tace,  “Oh ALLAH sarki Nu'aymah amarya zaki cemin, inadai fatan suna nan lafiya ko?”.
      “Ah lafiya lau suke sai alkairi kam. Mijin ne dama ya kira wai a nema mata mai aiki daga nan, shine nace to bara nazo da kaina wajenki ƙila ta hanyarki a samo wata mai hankali. Danni ƴan aikin gidan nan namu yanzu tsoro al'amarinsu ke bani wlhy Iyami. Kuma kinsan duk deluwa ce dama take kawo manasu gashi ALLAH yay mata rasuwa”.
    “To hajjo babu damuwa. Tunda har kika zaɓeni nikuwa insha ALLAH zan samoma Nu'aymah mai aiki ƴar gaske wadda baza'ayi kuka da ita ba. Duk da dai yanzu kinsa al'amarin mutanen namune sai dai addu'a. Baka fiya ganin abinda ke cikin zuciyar mutum ba a fuskarsa. Sai dai muce ALLAH ya datar damu”.
    “To amin dai Iyami. Lamarin bani adama kam na wannan rikitaccen zamani sai godiyar ALLAH kawai. Yanzu dai sai a bincika mana ɗin daga nan zuwa kwana biyu. Amma sai a samo mana ƴar babba ko tunda kinga ba'a haɗa Zainabu da sha katafi irinta ba. Wadda dai idan tayi ba daidaiba za'a tsawatama yaro a kuma ɗorasa akan hanyar data dace”.
   “Eh gaskiya kam hajjo, aiko indaima hakane bari zuwa anjima idan cikin su Hamisu wani ya ya shigo sai na saka su kira min Uwaliya idan zatayi, ƴar wajen yafendona ce acan wudil, mijinne ya tafi da ita can kudu da yake ɗansanda ne ya gama wajigo rayuwarta shine fa ya turota da takardar saki har uku. Shekara biyu kenan wani auren ya gagara abu kamar na magani”.
   Hajjo daba cika son irin waɗannan ƙananun maganar tayiba ta miƙe tana faɗin, “Ai ɗan adam sai ki barsa kawai Iyami, ALLAH dai ya ƙyauta ya shiryrmu mu da halinmu”.
   “Amin dai to”.

Iyami ta faɗa badan taso firar ta tsaya iya haka ba. Daga haka hajjo tai mata sallama ta dawo gidan dan anata haramar fara kiraye-kirayen sallar magriba ma.

★★★★

SUNDAY MORNING

     Washe gari ta kama Sunday. Gaba ɗaya ahalin gidan sun tashi ne da shirin tafiya church kamar yanda suka saba. Papa ya riga kowa fita shida bodyguard ɗinsa. Aymah da batasan hidimar da sukeyi ba tana tsaka da mopping a falo akai knocking ƙofa. Batare da ta damu da sanin wanene ba ta nufi ƙofar zata buɗe. Dan akwai hijjab ƙarami a saman kayan barcin jikinta. 
   Momy ce cikin shiga ta alfarma, anci uban kwalliya kamar zataje gasar ƙyau. Abraham biye da ita shima cikin gayunsa. Kamar zata shareta karta gaisheta sai kuma tace, “Good Morning”. Bata saurari amsarta ba tai gaba abinta. Haka kawai itadai Madam Chioma batai mataba, badan mahaifiyar Yoohan bace ba da lallai zamansu a waje ɗaya zai iya haifar da matsaloli, dan a rayuwarta ta tsani wulaƙanci koda a wajen babba ne.
    Da harara Momy ta raka bayan Aymah data koma kan aikinta batare da ta sake bi takansu ba. Ɗakin Yoohan kai tsaye ta nufa Abraham biye da ita. Sai dai koda ta tura ƙofar suka shiga sai taga wayam. Jikin ƙofar toilet taje nanma babu wani motsi, ta tura ƙofar ta leƙa babu kowa a ciki, amma dai da alama anyi amfani da shi babu jimawa. Tunanin ko yana ɗakin motsa jikinsa ne ya sata fitowa ta nufi can. Lokacin Aymah tana dining tana aikinta ko kallonsu batayi ba. Canma babu Yoohan, babuma alamar yau ya shigo wajen dan komai tsaf yake.
    “K ina my son?”. 

Nu’aymah taji muryar Momy a bazata. Ɗago dara-daran idanunta dake saka tsigar jikin Momy tayi tana kallonta. A yanayin halin ko-inkula tace, “Nima ban gansa ba tunda na tashi”. Daga haka ta ɗauki botikin ruwan mopping ɗinta ta nufi ɗakin Yoohan ɗin danta gyara tunda taji baya a ciki.
Cike da takaici Madam Chioma ta bita da harara, kafin taja hannun Abraham su fice. Fita tai harabar gidan, dan sauranma duk sun fita harma sun shishshiga motoci.
Guards ɗin Yoohan ɗin ta shiga tambaya ko sunga fitarsa?. Solomon ya bata amsa da cewar ya fita tun ɗazun ma, sunce zasu bisa yace baya buƙata. Ranta a ɓace tace, “Baku da hankali, sau nawa nake jaddada muku kubar barinsa yana fita shi kaɗai?. Da wace motama ya fita tunda naga duk ga motocinsa?”.
Kan Solomon a ƙasa yace, “Sorry maa. Babu yanda banyiba koni kaɗaima na bisa amma yaki, a mashin ya fita kuma”.
Wani shegen ihu ta buga tana ambaton “Jesus!!. Da wannan uban iskan safiyan kuka barshi ya fita a mashin dan ku kidahumai ne? idan Asthma ɗinsa ya tashi fa?”. Duk yanda sukaso ta fahimci ba laifinsu bane sam taƙi. Ihunta sai da yasa harsu Gebrail da suka shiga cikin mota duk suka fito. Nu’aymah kanta dake can sama sai da ta jiyo, hakan yasata buɗe Window ɗin bedroom ɗin Yoohan tana leƙosu. Ba ƙaramin dariya madam Chioma ta bataba yanda taketa faman tsalle da bala’i harta yadda takalman gayun nata saboda jarabar da takema guards ɗin Yoohan. Dariya sosai Aymah tasha harda hawaye, a ranta tana sake jinjina hauka da rashin kangado irin na waɗannan mutanen. Danma batasan akan mi madam Chioma ke bala’in bane????.

     Jin gidan yayi tsitt bayan gama bala'in madam Chioma da wucewarsu  sai tunanin maganar hoto ta dawo mata a cikin rai. Tabbas wannan shine lokacin da take da shi akan hakan tunda taga duk sun fice kamar maigadi ne kawai aka bari. Sai dai bata sani ba ko hadda duk masu aikin gidan. Sannan kuma bataga Miracle ba ma a amasu tafiyar.
 Ɗakinta ta koma tai wanka a gurguje. Shiryawa tai cikin doguwar rigar jallabiya blue. A falo ta zauna danta karya saboda yunwa dake cinta. Jiya tayi barci da wuri bataci abinci ba, duk da ma har yanzun ta kasa sakin jiki da abincin gidan sam. Ta gwammace zaman cin kayan ƙwalam ɗin da Yoohan ya ajiye. Aiko dukta kusan ganin ƙarshensu batare da ya sani ba.
   Yanzun ma madara ta haɗa da kauri tai zaman shan Cornflakes hankalinta kwance. Tana sha tana tunanin hanyar shiga sashen papa ɗakko hoton nan, a gefen zuciyarta kam cike da fargabar ALLAH yasa bai ƙona ɗin ba. Wannan tunanin ne ya saka cornflakes ɗin fita mata a rai ma. Ta ture bowl ɗin gefe tana miƙewa. Bedroom ɗinta ta koma ta leƙa harabar gidan ta Window, sai da ta tabbatar babu motsin kowa sai maigadi kawai sannan ta rufe glass ɗin a hankali.
     A falon gidanma bataga motsin kowa ba, hakama sama ko ina shiru ƙofofin bedrooms ɗin duk a rufe. Duk da haka batayi gangancin yin komai kai tsaye ba. Ta sauka downstairs ɗin ta shiga kitchen kamar zata ɗakko wani abu. Babu kowa a kitchen ɗin tabbacin da Blessing aka tafi. Ƙofar da zata kaika bayan gidan ta buɗe ta kitchen ta fito, nanma shiru babu kowa. Ta sake dawowa cikin jin daɗi ta haye upstairs ɗin. Ɗakin da take da tabbacin nasu Miracle ne ta nufa, tunkan ta ƙarasa jikin ƙofar sosai tajiyo minsharin Miracle dake barci. A hankali ta tura ƙofar ɗakin ta leƙa kanta. Kan gado ta hangota a cikin bargo, ga kafarta data sha ɗaurin bandage taɗan leƙo, key ɗin ƙofar dake ta ciki ta zaro a hankali, sannan taja ƙofar ta kulle mira ta waje.
  Lumshe idanu tayi a hankali tana karanto addu'oin neman nasara. Daga haka ta nufi sashen papa da addu'ar ALLAH yasa a buɗe yake. Cikin sa'a kuwa tana tura ƙofar sai gashi ta buɗe. Nannauyan numfashi ta sauke da turawa gaba ɗaya ta shiga corridor ɗin. Ƙofar falon ma ta sameta buɗe, nanma ta shige cike da ɗoki. 
  Koda wasa batai tunanin tsayawa a falon ba, dan tasan yanda papa ya nuna muhimmancin hoton nan bazai yarda ya ajiyesa anan ba sai dai bedroom. Bedroom ɗinma dai a buɗen ta samesa. Da alama ma ko gyara bai samu ba dan gadon duk a curkuɗe yake. Bata damu da wannan ba. Ta fara buɗe-buɗen bedside drawer farko tana ɗaɗɗaga abubuwan ciki. A duka biyun bata sami hotonba. Dan haka tabar nan ta juya kan Wadrobe ɗin kaya. Sai dai koda ta buɗe ma sai ta rasa da ina ya kamata ta fara?.  Sunan ALLAH ta shiga ambata tana ɗaɗɗaga duk abinda taci karo da shi. Amma babu alamar wannan hoto. Harta sare da tunanin kodai ya ƙona. Sai idanunta suka sauka kan wani ɗan kanta dake can gefe da tarin littatafai da takardu. Nanma zuwa tai tanata ɗagawa ɗaya bayan ɗaya sai dai babu anan ma.
  Kanta ta dafe hawaye na ciko mata idanu dan takaici, tabbas yanzu kam tama yarda ya riga da ya ƙona kenan?.  Zuciyarta ce ta ayyana mata ƙasan gado. Saurin nufar gadon tayi. sai dai tana ɗora hannunta a kai tajiyo dariyar Papa a falo yana faɗin, “Kai! Kai kai gaskiya kamin bazata Andrew, da alama ka matsu da kayan nan kam gaskiya”. Dariya wanda ya kira Andrew taji yayi shima, cikin harshen turancin yake faɗin, “Mr Goshpower bazaka ganeba ne, kuɗi masu nauyi ne na hango mana shiyyasa zuciyata ta kasa zama waje guda duk da nasan kana church a irin wannan lokacin”.
    Wata shegiyar dariya Papa ya kece da ita yana nufar hanyar bedroom ɗinsa, “Ai kai indai akan kuɗine zakama iya saka kanka a kowane kalar haɗari, shiyyasa kaga bana wasa da al'amarinka”. Ya ƙare maganar yana ƙarasa tura ƙofar bedroom ɗin da Aymah ke a ciki ya shi????????............✍

Hannuna ya firgita ya gaza aikinsa????????????.


ZAFAFA BIYAR 2021


Hafsat miss xoxo????
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).????????

      Mamu gee????

MIN ƘALB!!????????

    Hafsat rano????

ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!????????

    Safiyya huguma???? SIRAƊIN RAYUWA????????

     Bilyn Abdull????

SARAN ƁOYE????????

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka????????????????

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????

09033181070

????????????????????????????????????????
TEAM—-ZAFAFA BIYAR????????????????

ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????.
LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana????????.

No. 51


HAJARA COLLECTION, HAJARA COLLECTION, HAJARA COLLECTION, HAJARA COLLECTION.

Ina mata masu son ingattun kayan kamshi: Na kece raini? Kayan mata masu sa kishiya k’wafa? Bikin dangin miji ba za’a baki yankan albasa ba da wankin tumatir? To matso kusa domin HAJARA COLLECTION ta kawo muku kayayyaki na gyara ciki da wajen mace, Wanda suka kunshi:

Khumrahs: Sudaniyya, Chadian, Dufr, Fara da brown, Kai harda masu flavours…

Akwai turaren wuta irin su sandal, Hawi, Alut, Gab gab da sauran su..

Akwai turaren tsugunno dana jiki original gangariya tafiyayye dan gaske

Hajara collection ta kawo muku air fresheners, Mopping sprays da turaren wanki…

Akwai herbal organic soap wato sabulun gyaran jiki na maida tsohuwa yarinya..

Sannan Hajia hajara collection tana gyaran jiki.. Tana kuma siyarwa da kayan gyaran jiki na dilke set, Fata tai luwai luwai kamar ta jarirai..

Akwai special bridal spa wato gyaran jikin Amarya… Duk Amarya mai son tadinga kamshi har bayan shudewar bikinta to ta nemi hajara collection..

Akwai duk wasu nau’in kayayyakin turare masu kamsasa unguwa baki d’aya, Ki mopping tiles suyi sati suna kamshi, Kayan Haj hajara collection akwai inganci sosai.

Akwai page dinta a favebook mai suna GIDAN KAMSHI ga mai son zuwa ya duba hajarta, Ko kuma ya tuntubeta a number wayarta kamar haka: 09032069304

Adireshi: KANO NIGERIA, MARIRI dake Kan titin MAIDUGURI RD. KANO STATE..

TANA BADA KAYANTA AKAN FARASHIN SARI KO SAYA DAYA DAYA, SANNAN TANA TURA KAYANTA A KOINA AFADIN NIGERIA

AVAILABLE IN WHOLESALE/RETAILS. Nationwide deliveries. 100% tested and trusted…!!!

Kyau, inganci, Rahusa… Sai kayan HAJARA COLLECTION….!

idan anje siya ace daga zafafa biyar.. Akwai special package da Za’a hada maka masu kamshi????????????????♂️


No. 51

…………Tun fara jin dariyar Papa Aymah ta rintse idanunta da ƙarfi, ko ɗar bataji a rantaba na tsoro. Sai dai bata fatan ya ganta a ɗakin. Harta yunƙura zata ɗaga katifar da zaton ba shigowa zaiyiba sai taji sautin takowarsa. Da sauri ta saki tana waige-waigen ina ya dace ta shiga ta ɓuya. ‘Toilet ’ zuciyarta ta bata amsa a taƙaice. Da gudu ta nufi toilet ɗin dai-dai da murɗa handle ɗin ƙofar bedroom ɗin da papa yayi. Yana shigowa tana turo ƙofar bathroom ɗin.
Da sauri ya kalli ƙofar toilet ɗin danjin ta ɗanyi ƙara alamar rufewa. Yay tsaiy yana kallonta zuciyarsa fal mamaki. Shi dai yasan baiyi tsammanin ganin kowa a ɗakinsa ba. Musamman daya san duk ahalin gidan ya barsu a church ne. Shima harya fara lecture sai ga baƙonsa mai muhimmanci Andrew yazo. Dole ya baroma Uncle Mike shikuma yazo yaji da baƙon nasa dan yafi lecture ɗin da zaiyi a church ɗin muhimmanci.
Duk da yasan babu kowa ɗin dai, sai ya sami kansa dason tabbatarwa. Dan haka ya nufi toilet ɗin yana zancen zuci.
‘Ya ALLAH!’. Nu’aymah ta faɗa a zuciyarta tana rumtse ido da ƙarfi jin kuma ya nufo toilet ɗin. Da sauri ta koma ta jikin bayan ƙofar, yanda idanma ya buɗe bazai gantaba sai dai idan shigowa yay ya rufe.
Ƙofar kuwa ya tura ya leƙa kansa yana bin ko ina da kallo. Baiga alamar akwai wani motsi ba saboda numfashi Aymah ta ɗauke gaba ɗaya. Yay guntun tsaki ya jawo ƙofar ya rufe ransa na raya masa abarda ya shace a daren jiya bata gama sakinsaba kawai.
Yana maida ƙofar ya rufe Aymah ta saki wani nannauyan numfashi, hannunta toshe da bakinta, idanunta kam har sun kaɗa sunyi jajur dan wahala. Da sauri ta matsa tana leƙensa ta kafar makulli. Ta zaro idanu waje da saurin sake toshe bakinta jin zatai suɓutar baki saboda ganin Papa daya danna wani ɗan abu a jikin Wadrobe ɗinsa. A hankali Wadrobe ɗin ta zuge kanta gefe, bangone sosai kamar yanda kowa ya sani ya bayyana. Amma a mamakinta sai taga yasa hannu yana shafa bangon a hankali, yanayi yana kallon ƙofar shigowa bedroom ɗin. Da alama tsoro yake ƙila kar baƙon nasa ya biyosa. Gani tai ya sake danna wani abu a jikin bangon, sai ga wani ɗan loko kamar drawer ya bayyana. Sai dai shi wannna murfinsa na ƙarfene. Key ya ɗakko a samansa ya buɗe, bata ganin abubuwan dake ciki saboda murfin ya tare ta. Wani madaidaicin jakka ya fiddo a ciki ya ajiye a kan gado, ya cigaba da ɗebo abubuwan da ba fahimta takeba yana lodasu a jakkar. Yana ƙoƙarin rufewane farar envelope ta faɗo. Gani tai ya duƙa ya ɗauka yana jan ƙaramin tsaki, ya ɗanyi magana da yare sai kuma ya ajiye envelope ɗin a saman gadon itama sannan ya maida Wadrobe ɗin yanda take ya ɗauki jakkar ya fita yana gyara wuyan rigarsa.
Da sauri Aymah ta fito tana haɗa gumi, ta ɗauki envelope ɗin jikinta na tsuma ta buɗe. hoto ta gani, duk da bata iya zaman kallon wanene a hoton ba haka kawai zuciyarta ta bata hoton da take nema ne tabbas. zaresa tayi a cikin envelope ɗin, ta buɗe bedside drawer data ga invitation a ciki ta zaro ɗaya ta saka a envelope ɗin. Shi kuma wanda ta ɗauka ta ɗaga rigarta ta saƙa ciki sannan ta gyara ta nufi ƙofa cikin sanɗa. Leƙasu ta farayi ta kafar makulli, hakan yay dai-dai da tasowar papa ya sake nufo ɗakin. Da sauri ta shige cikin labulen window tana rumtse ido, dan harga ALLAH yanzu kam zuciyarta bugawa take da dauri-sauri.
Jinin ɗan adam ya wuce wasa a waje, dan haka papa sam zuciyarsa ta kasa gaskata masa babu mutum a ɗakin. Ƴan kalle-kalle ya farayi a ɗakin, idonsa ya tsaya ƙyam a inda Aymah take cikin labule. Duk da bawani nuna alamun tana wajen labulen yay ba, saboda yanada kauri da cika, sai ya nufi wajen. Baƙaramin bugawa ƙirjin Nu’aymah ya keyi ba a wannan lokacin, zuciyarta ta buɗe sosai kamar zata faso ƙirjinta ta fito ta toshe bakinta da ƙyau tana rumtse idanu da ƙarfi, dan tama rigada ta sallama sai ya ganta.
Yana ɗora hannunsa saman labulen wayarsa nayin ring. Tsaki ya ja tare da ja baya, ya zaro wayar yana sake jan wani tsakin. Sai dai ganin mai kiran nashine ya sakashi ɗagawa da sauri yasa wayar a kunne.
A hankali Nu’aymah ta sauke numfashi da buɗe idanunta ta sake buɗewa a hankali hannunta dai-dai saitin zuciyarta. Kobi takan wayar da papa keyi bataiba, sai dai jin ƙauri yasata ɗan buɗa tsakkiyar labulen ta leƙa. Hoton nan taga yana ƙonawa yana cigaba da amsa wayar. Sai da hoton ya kammala ƙonewa tsaf a cikin envelope ɗin dabai ciresa ba sannan ya ɗauka abinda ya shigo ɗauka ya fice yana cigaba da wayar.
Saurin fitowa tai daga cikin labulen, dan ta fahimci dolene tabar sashen nan kafin baƙon papa ya tafi.. Komawa ta sakeyi jikin ƙofar yanzunma ta leƙa. Hangosu tai gaba ɗaya hankalinsu nakan centre table da alama wani abu suke lissafawa. Buɗe ƙofar tayi a hankali, ALLAH ya sota ma bata ƙara, ta ziro ƙafarta ta dama tana ambaton sunan ALLAH, ɗayar ta sake zirowa ta fito gaba ɗayanta batare data rufe ba. da sauri ta duƙe ganin baƙon papa zai ɗago, ta fara tafiya da rarrafe har zuwa bayan kujerar da papa yake.
Ganin yanda Andrew ke kallon ƙofar bedroom ɗin kamar baya fahimtarsane ya saka papa tambayarsa ko lafiya?.
Kai tsaye Andrew ya tabbatar masa tabbas mutum ya gani ya fito a ɗakin. Zabura Papa yayi ya miƙe, hakan ya bama Aymah damar rarrafawa da sauri tai gaba hanyar ƙofa, ta buɗe ƙofar da gudu ta fita. Gudunta ya sakasu juyowa da saurin suma, sai dai ta rigada ta fice. Biyota sukayi dan sunajin sautin gudin nata. Suna fitowa tana maida ƙofar sashensu data sami damar shigewa ta rufe. A falo sukaci karo da Yoohan da shigowarsa gidan kenan shima, jin babu motsinta a sashen ya sakashi leƙawa ɗakinta ko barci takeyi. Sai ya sami ɗakin wayam.
Sam baiga daga ina ta fitoba. Jinta kawai yay a jikinsa a bazata, hakan ya sakashi yin baya suka faɗa a kujera a tare, yana ƙasa tana a samansa. Riƙeta yay da ƙyau yana matse ido dan yaji zafi a kafaɗunsa, in kuma ya saketa zata faɗi, itama a firgicen da takene ya sakata mamuƙesa yanda ya kamata, har yana jiyo yanda zuciyarta ke gudu akan ƙirjinsa. Kusan mintuna uku suna a haka, sai da ya tabbatar bugun zuciyarta ya dai-daita yanda ya kamata sannan ya tura hannunsa cikin gashinta, gyalen jallabiyar ya zame. Saurin yunƙurawa tai tana ƙoƙarin ture masa hannun. “Nikam minene haka kuma?”. Ta faɗa tana kumbura fuska.
Bai kulata ba, ya cigaba da tura hannunsa har sai da ribbon ɗin data ɗaure gashin ta fita gaba ɗaya gashin ya baje. Ƙara yunƙurawa tai da zafin nama zata raba jikinta da nasa ya maidata suka sake mannewa. Zatai magana yay saurin faɗin, “Shiiii!!”. Bata fuskar ta sakeyi da cewa, “Toni ka sakeni na tashi”.
Batare da ya saketanba yace, “Daga ina kike haka?”.
“Babu ko ina, tsoratani akayi”.
Ta bashi amsa tana ƙoƙarin sake tashin, maidata yayi fuskarta gab da tashi har hancinsu na gab da gogar na juna. Duk yanda taso yin tsiwar tata sai ta gaza. Dan yanda ya sarƙeta da mayun idanunsa, ga numfashinsa da yake busa mata yana zuƙar nata shima sai taji kamar ya wani ɗaɗɗauretane da igiyoyi, ga wani shegen kwarjini da yay mata da cika idanu. A takema ta fara jin kasala na saukar mata.
Ƙofar falon da aka buɗe ne ya sakasu sauke ajiyar zuciya a tare, ido huɗu sukayi da papa daya shigo da gani kasan a rikice yake. Nu’aymah tai azamar yunƙurawa zata tashi daga jikin Yoohan. Shima sakinta yay saboda ganin a yanda papan ya shigo.
Papa ko da kallo ɗaya yay musu ya ɗan kauda kansa sai ya sami kansa da sauke numfashi. dan a yanda ya gansu kawai ya tabbatar masa ba ɗaya daga cikinsu bane ya shigar masa ɗaki kamar yanda yay zargi daga farko.
“Papa lafiya kuwa?”. Yoohan ya faɗa yana sauke Aymah dake ƙoƙarin barin jikinsa a hankali”. Da sauri papa yace, “No Son karka damu, kuyi haƙuri na shigo muku babu knocking ”.
“Babu damuwa papa. Amma inji dai ba wani abune ya faru ba ko?”. dafe kai papa yayi dan duk ya shiga ruɗani. Yace, “John ni nama kasa fahimta gaba ɗaya, mune a ruɗe kokuwa abinda mukai tunanine a gaske?. Kawaifa muna zaune da baƙona sai mukaga kamar mutum ya fito a bedroom ɗina. Mun duba ko ina na gidan nan kuma amma babu alamar kowa. Maigadi ma ya tabbatar mana shi baiga kowa ba sai kai daka shigo tun ɗazun”.
Kafin Yoohan yay magana Aymah tai saurin faɗin, “Yes papa nima naga mutum, ina kitchen zan dafa noodles naji gudu an sakko daga downstairs, shinefa na tsorata na shigo da gudu na zatama ɓarayine ko aljanu”.
“Daughter da gaske?”.
“Eh papa, da gaske naga mutum ya fita da gudu”. Tai maganar tana satar kallon Yoohan ta ƙasan ido.
Daga Yoohan har papa sun yarda da zancen Aymah, hakan yasa duk suka fito har ita da keta faman maƙalewa bayan Yoohan wai a dole tsoro takeji (????wagga ɗiya ko).
Tsaf Nu’aymah ta saka papa da Maigadi da Yoohan da Andrew zagaye gidan nan duk faɗinsa. Tana kuma biye dasu kamar jela. Sai dai babu ko alamun wani yama shigo gidan balle maganarta ta tabbata.
Dafe goshi Yoohan yayi yana faɗin, “Papa wannan shi nake faɗa maka a koda yaushe. Ka daina saka guards ɗin gidannan gaba ɗaya tafiya church, taya za’ace maigadi ne kawai za’a bari a gida bayan wasu su irin wannan damar suke nema. Dolene a sake tsari dan wannan tsarin baiyiba na shigo mana da kowa cikin gida”. Ya ƙare maganar da kama hannun Nu’aymah suka shige ciki.
Daga papa har Andrew dake lasar baki tun ganin Aymah da kallo suka bisa. Kasa haƙuri kuwa Andrew ɗin yayi, ya shiga tambayar papa ina suka samo wannan ƙyaƙyƙyawar young lady ɗin haka?. Duk da takaici daya kama papa sai da ya bama Andrew amsa da cewar daughter in-low ɗinsa ce. Da yake baisan Yoohan ɗin yayi aureba, dan papa bai tura masa invitation ba. Kai duk ma abokan harƙalarsa ta bayan fage bai gayyacesu wajen taron ba.
Ciki suka koma ya sallami Andrew dan maganganun Yoohan ne ke neman masa tasiri a cikin zuciya. Idan har ya fahimta dai-dai Yoohan yana zargin wani shirine da Andrew kenan? Maybe shine ya shigo da wani batare da shi ya sani ba saboda wani dalilinsa. Wannan tunanin da yay masa tasiri ne ya sakashi bincike tun daga bedroom ɗinsa har falon gaba ɗaya. sai dai baiga wata alama ta wani abunda zarginsa ke a kai ba. Amma duk da haka bazai sakankance ba kai tsaye. Dan haka ya canja password ɗin kwaba ɗinsa ta sirri yama ƙara mata wasu securitys ɗin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button