SARAN BOYE COMPLETE

Aymah kam suna shiga ta zare hannunta cikin na Yoohan ta kwasa da gudu zuwa bedroom ɗinta tana faɗin, “Fitsari nakeji”.
Da kallo kawai ya bita harta banko ƙofar, ya ɗan girgiza kansa da ƙarasawa cikin falon ya zube akan kujera yana furzar da iskar ɓacin ran kwashe-kwshen papa. Baisan daga ina kuma ya kwaso musu wannan mai suffar marasa imanin ba.
Koda Aymah ta shiga ɗaki bata iya tsayawa a bedroom ɗin ba, dan tunaninta Yoohan zai iya biyota nan. Toilet ta shiga ta maida ƙofar ta rufe da murza key har sau biyu. Sai da ta tabbatar tayi gam sannan ta ɗaga rigarta ta zaro hoton da duk ya lanƙwashe. Bata damuba, sai tsuramasa idanu da tayi ko ƙyaftawa babu. Ba kowa bane a hoton face papa yana ɗanyen matashi jagab, sai ƙyaƙyƙyawar balarabiya mai tsananin kama da Yoohan a gefensa da shekarunta bazasu wuce sha tara zuwa ashirin ba. Da cikinta tsoho wanda yay mata ɗas a jiki. Hannunta dana papa duk akan cikin suna murmushi.
A take wani gumi ya fara karyoma Nu'aymah, ta nuna balarabiyar da ɗan yatsa bakinta nason furta magana amma ta kasa. Sai a zuciyarta zantuttukan keta kaiwa da kawowa na mamaki, al'ajabi, ruɗani, harma da firgici. ‘To mi hakan ke nufi?’. Ta ambata a fili da ƙyar.
Harga ALLAH man kanta fa yana neman kwararewa a ƙasa, dan haka ta jingina da ƙofar tana furzar da huci mai zafi tare da sharce gumin daya taru mata a goshi. ‘Tabbas akwai magana kenan. Wacece wannan tare da babansa? Sannan kenan wannan matar dake a gidan itace ta haifesa da gaske? Kokuwa yaya abin yake?’.
Waɗan nan tambayoyi suke sake rikitar da ita da hautsina mata man kai da ruwan kwanya awaje guda.....
Maganganu take ɗanji sama-sama kamar a cikin ɗakinta, hakanne ya sakata leƙawa ta kafar mukulli bayan ta zaresa a hankali. Momy ce ke magana a faɗa-faɗa. “My Son wai yaya ma zaku yarda da zancen yarinyarnan cewar wai taga wani. Sai dai idan itace da kanta ta shiga take neman raina muku hankali. tayaya idan ba ita baceba za'a kulle Miracle ta baya bayan kuma Joy ta tabbatar mana bata kulleta ba, ita kuma gashi tace babu key a cikin ɗakin”.
Idanu Aymah ta zaro waje, tai saurin kallon yatsanta da key ke maƙale wanda bana ko ina bane sai na ƙofar ɗakin su Mira data kulle. Gaba ɗaya tama manta da shi a hannunta. Kanta ta dafe dan ganin key na neman jiƙa mata aiki bayan ta tsalake rijiya da baya........
Cikin ɗacin murya da Yoohan ya fara magana ya katsema Aymah tunaninta... “Momy Please, banajin daɗin irin waɗanan maganganun naki akan matata. Taya zakice itace? Idan kince ita ɗince ma mita sani akan gidan nan da har zataje sashen papa kuma harma cikin bedroom ɗinsa? Mima zatayi acan?”.
Dariya sosai ya bata ganin yanda ya haƙiƙance akan abinda bai saniba wai shi nan mai mata. Taima ƙofar gwalo tare da jefa key ɗin cikin toilet tai flushing ɗinsa, sannan ta cire rigarta ta naɗe hoton a ciki ta hau yin wankanta hankali kwance. A ranta tana addu'ar ALLAH ma yasa kar a samu key ɗin buɗe Mira. Tun tana cigaba da jiyosu sama-sama har taji tsit. Ɗauraye jikinta tayi taja rigar wanka ta saka. Dama ta ƙirƙiri wankan ne dan batason fita ta haɗu da madam Chioma.
Koda ta fito bata samesu a ɗakin ba, hakanne ya bata damar ɓoye hotan sannan ta sake sabon shiri ta fita dan yunwa takeji batayi breakfast ɗin ƙwarai ba ta tafi ɗaukar magana.
Duk da hangosa da tayi a saman dining ɗin bata fasa nufar can ba. Sarai shima ɗin yaji motsinta amma ya basar yana cigaba da danna waya. ayaba da gyaɗa a gabansa. Bowl ɗin data haɗa madarar ɗazun ta ɗauka takai kicin, zubashi tayi a ƙaramar tukunya ta ɗora kan gas, tana tsaye sai da ya tafasa sannan ta juyosa ta fito. Inda ta barsa nan ta sake taddashi. Yanzun kam duk yanda taso haɗiye maganar dake bakinta ta kasa sai da ta tanka. ƙasa-ƙasa tace, ‘Yau ina ganin ƙazanta, wai ayaba akeci da gyaɗa’.
Shi dai baima jitanba balle yasan da shi take tunda da hausa tai maganar. Itama daga haka bata sake tankawaba ta zauna ta fara shan madarar data dafo. Kansa ya ɗago ya kalleta a karo na farko, kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya maida kansa ga wayar.
Gyaran murya ta ɗanyi, hakanne ya sakashi ɗagowa ya sake kallonta. Ta wani ɓata fuska irin bata son wargin nan. Shi dai baice uffanba. Lura da tai ba magana zaiyiba yasata faɗin, “Uhhm ni dai gaskiya zan dinga girka abincina anan ni kaɗai, dan ban iya cin waɗan nan abincin naku ba”.
Idanunsa ya ɗan lumshe ya buɗe a kanta, batare da yace komaiba ya maida kansa a kan wayarsa. A ƙufule tace, “Dan ALLAH Yah Yoohan”.
Duk yanda yaso basarwa hakan ya gagara. Karon farko a rayuwarsa da yaji sunansa a bakinta. Sannan yasan a hausance kalmar Yaya dai girmamawace ga wanda aka kira da ita. A hankali ya lumshe idanunsa ya buɗesu a kanta, yana binta da wani narkakken kallo data gagara fahimtar ma'anarsa. Kamar mai ciwon baki yace,
“Naji”
Ya bata amsa a taƙaice, dan har yanzu ransa a ɓace yake da zantuttukan Momy. Ita kuma mutuniyar taku da yake babu man kai ta kasa fahimtar ransa a ɓacen yake.
Shine ya fara bar mata wajen bayan ya cinye ayaba da gyaɗansa.
_★★★★
Bayan sallar la'asar tana a ɗaki kwance tanata faman ƙullawa da kwancewa akan yanda zata ɓulloma Yoohan da tambaya game da sanin matsayin Momy a garesa ya shigo. Harya ƙaraso gaban gadon bata sani ba. Sai da ya zauna ne jikinsa ya taɓa mata hannu sannan tai firgigit. Da sauri ta miƙe zaune tana cika baki da iska. Bakinsa ya taɓe da kauda kansa yana lumshe idanu.
“Ki shirya muje”
Ya tari numfashinta ganin zatai magana. Shi kuma baya buƙatar surutun sam. Haka yake idan abu ya ɓata masa rai, sai ya wuni yana ɗacin rai. Hakan yasa mafi yawan lokaci ƴan gidan suke gaza gane kansa. Ita kanta Aymah ganin har yanzu fuskar tasa a tsuke kamar ɗazun duk sai taji shakkar masa tsiwar tata. Duk da ma dai har ranta taji daɗin jin fita zasuyi.
Fita yay alamar bata damar shiryawa. Aiko cike da ɗoki ta shiga neman kayan canjawa. Tana cikin zarowa Yoohan na sake shigowa ɗakin. Kallonsa tayi da sauri, zatai magana sai dai ta kasa saboda cin karo da fuskarsa dake a matuƙar tsuke. Cikin kaushin murya yace, “Idan kin shirya ki sameni a waje”.
Kanta ta ɗaga masa dan bataga fuskar yin wargi ba. Yana fita ta sauke ajiyar zuciya. A ranta duk sai taji babu daɗi, dan tasan abinda ya saka masa ɓacin ran dai da gaske ta aikata, amma yanata ƙoƙarin kareta a wajensu har yana saka kansa a ɓacin rai irin haka.
Da ɗan hanzarinta tai shiri cikin wata doguwar rigar jallabiyar, amma yanzu baƙa. Taji adon blue stones sai ƙyalli da ɗaukar idanu takeyi. Bata wani tsaya ɓata lokaci ba ta saka hula da naɗa madaidaicin blue gyalen daya shiga da adon stones da akaima rigar. Taɗan gyara fuskarta tasa takalma ta fito tana ƙamshinta mai sanyi.
A sashen ta fito gaba ɗaya tana karanta:
اَللَّهُمَّ إِنَّا نَجْعَلُكَ فِي نُحُورِهِمْ، وَنَعُوذُ بِكَ مِنْ شُرورِهِمْ .
Allahumma inna naj’aluka fee nuhoorihim wana’oothu bika min shuroorihim.
Baƙi sosai ta samu a falon ƴan ziyarar Sunday. A taƙaice tace musu “Good Afternoon” dan taga akwai manya. Batare data jira sanin waɗanda suka amsaba tai ficewarta. A harabar gidanma dai duk baƙin fuska taita cin karo da su. Wasu ta gaishesu wasu tai wucewarta.
Da sauri Gebrail dake jikin motar da Yoohan ke a ciki ya buɗe mata ƙofa yana wani rissinar da kai kamar gaske. A ranta tace, ‘Munafuki dan ka gansa a wajen kake wani acting like mutumin ƙwarai. Zanyi maganinka ne ai, bara na gama da na sama da kai’.
Tana shiga ya maida ƙofar ya rufe tare da leƙowa. a marairaice yace, “Please Brother na shigo muje tare?”.
Wata banzar harara Yoohan ya watsa masa. Saurin barin jikin motar yay yana ɓata fuska. A ransa kuwa wani irin wutar son Aymah ce ke ruruwa masa a zuciya tare dajin zafin Yayan nasa mai share kukansa a koda yaushe wajen magance masa bukatunsa. Da ƙyar ya iya nufar garden inda abokansa suke zaune da giyar da zasu sha ransa duk a ƙuntace. Dan tabbas yanaji a ransa bazai iya haƙuri ya barma Yayan nasa zuƙeƙiyar yarinyarnan datai dai-dai da burinsa ba. Shi musilincinta ko yarenta duk ba damuwarsa ba. Itaɗin yake so, so irin wanda ke shiga ɗin nan farat ɗaya a zuciya batare da yayi shawara da mai zuciyar ba. Dan a kallo ɗaya da yayma Aymah a wajen dinner tai masa shigar corona virus a zuciya. Bakuma tayi sanya ba wajen mamaye dukan zuciyarsa da ilahirin jikinsa. Dan haka koda bala’i sai ya mallaketa, sai ya ɗanɗani zumarta, sai ya ɗanɗana mata tashi kuma. Yanaji a ransa zata soshi fiye da Brother Yoohan inhar ya bayyana masa abinda ke cikin zuciyarsa game da ita…………..✍
????Wa yaga kwamatsala ɗan Nageriya da mulkin Amuruka????.
ZAFAFA BIYAR 2021
Hafsat miss xoxo????
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).????????
Mamu gee????
MIN ƘALB!!????????
Hafsat rano????
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!????????
Safiyya huguma???? SIRAƊIN RAYUWA????????
Bilyn Abdull????
SARAN ƁOYE????????
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka????????????????
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????
09033181070
????????????????????????????????????????
TEAM—-ZAFAFA BIYAR????????????????
ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????.LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana????????.
No. 52
HAJARA COLLECTION, HAJARA COLLECTION, HAJARA COLLECTION, HAJARA COLLECTION.
Ina mata masu son ingattun kayan kamshi: Na kece raini? Kayan mata masu sa kishiya k’wafa? Bikin dangin miji ba za’a baki yankan albasa ba da wankin tumatir? To matso kusa domin HAJARA COLLECTION ta kawo muku kayayyaki na gyara ciki da wajen mace, Wanda suka kunshi:
Khumrahs: Sudaniyya, Chadian, Dufr, Fara da brown, Kai harda masu flavours…
Akwai turaren wuta irin su sandal, Hawi, Alut, Gab gab da sauran su..
Akwai turaren tsugunno dana jiki original gangariya tafiyayye dan gaske
Hajara collection ta kawo muku air fresheners, Mopping sprays da turaren wanki…
Akwai herbal organic soap wato sabulun gyaran jiki na maida tsohuwa yarinya..
Sannan Hajia hajara collection tana gyaran jiki.. Tana kuma siyarwa da kayan gyaran jiki na dilke set, Fata tai luwai luwai kamar ta jarirai..
Akwai special bridal spa wato gyaran jikin Amarya… Duk Amarya mai son tadinga kamshi har bayan shudewar bikinta to ta nemi hajara collection..
Akwai duk wasu nau’in kayayyakin turare masu kamsasa unguwa baki d’aya, Ki mopping tiles suyi sati suna kamshi, Kayan Haj hajara collection akwai inganci sosai.
Akwai page dinta a favebook mai suna GIDAN KAMSHI ga mai son zuwa ya duba hajarta, Ko kuma ya tuntubeta a number wayarta kamar haka: 09032069304
Adireshi: KANO NIGERIA, MARIRI dake Kan titin MAIDUGURI RD. KANO STATE..
TANA BADA KAYANTA AKAN FARASHIN SARI KO SAYA DAYA DAYA, SANNAN TANA TURA KAYANTA A KOINA AFADIN NIGERIA
AVAILABLE IN WHOLESALE/RETAILS. Nationwide deliveries. 100% tested and trusted…!!!
Kyau, inganci, Rahusa… Sai kayan HAJARA COLLECTION….!
idan anje siya ace daga zafafa biyar.. Akwai special package da Za’a hada maka masu kamshi????????????????♂️
No. 52
…………Motar tayi shiru, bakajin komai saina fitar sassanyan ac da sautin karatun al-qur’ani daya saka can ƙasa. A hankali yake tuƙin kamar baya so. Fuskar nan babu ko alamun yasan minene ma murmushi. Duk da Aymah tasan shiɗin ba mutum bane mai fara’a aɗan zaman da sukayi, sai duk tajita a takure da yanda yay matuƙar tsuke fuskar.
Sake lafewa tai abinta cikin kujera ƙamshin motar da sanyin ac na kuma saka mata kasala. A zahiri zakace idanunta a rufe suke, sai dai sam ba haka bane. Ta ƙasan ido take ƙare masa kallo daki-daki kamanin balarabiyar nan ta hoto na sake bayyana tattare da shi. A ranta kuwa rayawa take, ‘Dolene kayi ƙyau, ashe kanada alaƙa da larabawa. Ga papan ma duk da kasancewarsa ɗan African, Africa ɗin ma Najeriya, Najeriyarma kudanci shiɗin ƙyaƙyƙyawa ne tabbas’.
Yoohan dake ji a jikinsa kallonsa akeyi ya ɗan juyo ya kalleta. Duk da idanunta a rufe suke ya fahimci ba barci take ba. Dan inba ita ɗinba babu wanda zai kallesa tunda a mota suke, motarma mai tinted glass. Baice komaiba ya cigaba da tuƙinsa kamar baya son suje inda zasu ɗin.
Sun isa haɗaɗen shagon sayayyar da Abujawan da kansu keji da shi, (bazan faɗi suna ba, danni na dainama masu shaguna talla yanzun????, duk maison a ringa saka sunan shagonsa a littafi yazo ya biya kuɗi koda baturene????????).
Sai da ya gama dai-daita fakin ya buɗe motar zai fita sannan Nu’aymah ta buɗe idanu. Batasan wannan cinkushe fuskar dan haka cikin neman tsokanar data iya tai saurin faɗin, “Ni dai gaskiya bazan shiga da kaiba wani yazata kidnapping ma’aikatan mukazoyi”.
Jin abinda ta faɗa ɗinne ya hanashi zura ɗayar ƙafar da yay niyya dan har ya sauke ɗaya a ƙasa. Juyowa yay yana kallonta. Ta cika kumatu da iska tana tura baki. “Yoni ka daina kallona da waɗan nan idanun iya gaskiyata na faɗa. tayaya dan ALLAH zan bika, kaga fuskarka kuwa? Yasin kamar ta shekau na dajin sambisa. Dan haka yi gaba zan biyoka a baya”.
Duk yanda yaso daurewa ya gaza, ya kauda kansa gefe murmushi na suɓuce masa. A ransa yana jinjina rashin jin yarinyar nan da rashin tsoro. A fili kam sai ya ƙarasa fita yana faɗin, “Silly girl sakko, kafin in jehoki ƙasa”.
Baki ta murguɗa tana buɗe ƙofar ta fito. Cikin ƙunƙuni tace, “Kaima dai nakusa fara kiranka Silly boy ɗin nan daka ishi mutan da shi”. Ta ƙare maganar tana ƙarasawa inda yake tsaye yana gyara p-cap ɗin da a yanzu itadai ta gansa da ita. Dan da suka fito kansa babu hula. Kallonsa tai ta ɗauke kanta, a ranta kuwa tana yaba yanda p-cap ke masa ƙyau idan ya sanya. Musamman a yanzu da komai na jikinsa ya kasance baƙi, hularce kawai fara.
“Malama kallon da kikemin ya isheni”. Taji maganarsa a bazata. Sai dai yayi gaba kamar bashine ya faɗa ba. Murya taɗan ɗaga kaɗan yanda zai jita tace, “Kai da wane idon kasan ina kallonka?”.
Tsayawa yay tare da juyowa gaba ɗayansa. Ita kuma ta riga da tazo gab da shi sai tai ƙoƙarin yin baya ganin zasuyi karo. Tako tafi gaba ɗayanta zatasha ƙasa. Da sauri ya bita ya tallafo ƙugunta ta dawo jikinsa. A yanda ƙirjinta ke bugawa ya tabbatar masa taji tsoron faɗuwar sosai. Samun kansa yay dajin dariya na taho masa. Ya ɗanyi kamar zai saketa, tai wani uban tsalle ta mamuƙesa zata saki ihu yay azamar danne bakin da ɗayan hannunsa yana kallon yanda tsirarun mutane dake shiga da fita cikin wajen suna kallonsu. Wasu na dariya wasu na gulma.
Idanunsa ya rumtse da sauri yana faɗin, “Shikenan kin tara mana mutane hankalinki ya kwant…” Ai baima kai ƙarsheba ta fincike jikinta tana turesa. Sai kuma tai saurin komawa bayansa ta ɓuya ganin da gaske kallon nasu akeyi. Gaba ɗaya kunya ta dabaibayeta kamar ta nutse ƙasa takeji.
“ALLAH ne ya rama min”. Ya juya da wani salo yana yin manar a cikin kunnenta kamar bashi ya faɗa ɗin ba. Da sauri tabi bayansa tana tura baki gaba. Sai dai da alama bakin tsuwar ya mutu kam.
Kamar yanda ƙa’idar shiga wajen take sai da akai bincikesu sannan suka shiga, sai dai yanzu kam a jere suke tafiya gwanin sha’awa. Batare da ya kalleta ba yace, “Mizaki saya?”.
“Duka shagon”. Ta bashi amsa itama batare data kallesa ba.
Shima da yake ya iya baƙar maganar sai cewa yay, “Okay sai muje a saidama Shekau ɗin da kikace Kano muzo musai shagon da kuɗin”.
Babu shiri taja birki harda riƙe ƙugu. Shima tsayawar yay ya tura duka hannayensa cikin aljihun yana kallonta fuska a ciskule. “Ai wlhy sai dai a saida garinku, dan kano tafi ƙarfin shekau”.
“Trouble maker”.
Ya faɗa yanayin gaba. Bayansa tabi tana ƙunƙuni, sai dai bajin abinda take faɗan akeba. A haka suka shiga wajen kayan ƙwalam da maƙulashe. Irin kalolin biscuits da kayan ƙwaɗayin dataga ya tara a gida yaketa ɗiba yanzun ma, hakan yasa ta dinga binsa da kallo kawai tana gulmarsa a cikin zuciya, (wai maƙwaɗaici ne????).
Sai da ya kusan cika keken sannan ya kalleta. “Kifa ɗeba naki, dan ba ƙara cimin nawa zakiyi ba yarinya”. Idan ba ita datasan shine yayi maganarba babu yanda za’ai ace shi yayita. Dan ya ɗauke kansa ya cigaba da harkar gabansa.
Leɓe Aymah ta ciza, a ranta take raya ‘zakaga mugunta kuwa yau ɗan balarabe’ komawa baya tayi itama ta jawo nata keken. Ta shiga lodar chocolates da kayan ciye-ciye iri-iri. Wanima ko saninsa batayiba balle tasan zaiyi daɗi ko bazaiyiba. Saida ta cika kwandon nan dam da kayan ƙwaɗayi kawai har tana turawa da ƙyar tsabar mugunta. Tana a layin ƙarshe zata ɗauki wani roban chewing gum taji ƙamshin turaren da ya sakata waige-waige da sauri. Cikin kwandon ta jefa chewing gum ɗin tai saurin fitowa a lungun tana leƙe. Babu ko mai alamarsa, sai dai tabbas wannan ƙamshin shi kaɗai ta sani da shi. Duk da zuciyarta na ayyana mata wanine bashi ba ta kasa aminta. Sai ƙara kutsa kai take kowanne layi dan dubashi. Wani irin mugun bugawa ƙirjinta yayi jin an riƙo mata hannu. Ta waigo da sauri sai taga Yoohan ne.
“Miye kike nema haka?”.
Yay maganar babu wasa a fuskarsa. Sannan muryarsa a kausashe kamar wanda yake cikin fushin da ɓacin rai. Kanta ta girgiza masa tana ƙoƙarin maida ƙwallar da suka cika mata ido. Bai sake cemata komaiba yaja hannun nata suka bar wajen. Duk da taga bai maidata wajen kayanta data bariba, ba tai magana ba. A mamakinta saita hangi kayan can wajen bada kuɗi ana loda musu a ledoji. Suna isowa matar fuskarta faɗaɗe da murmushi tace, “Doctor ATM”. Zarowa yay a wallet ya miƙa mata batare da yace komaiba. Ta amsa idanunta akan Nu’aymah dake sake waige-waigen ko zata gansa anan.
“Amaryar Doctor Good evening ”. Maganar matar ta maidota hankalinta. A taƙaice ta amsa mata duk da ta fahimci akwai sanayya tsakaninta da Yoohan ɗin. Ta ɗan dubesa lokacin da ma’aikatan wajen ke kwashe ledojin zasu kai masu mota. Har yanzun fuskarsa babu sauƙi. Gashi ya wani riƙe mata hannu gam kamar za’a saceta. ATM ɗin ya amsa yaja hannunta suka fita.
A can wajen motar da sukazo taga anata loda kaya harma da wanda bataga sanda aka sayaba ita dai. Batayi magana ba dan bataga fuskaba. Saima buɗe mata murfin yayi yay mata alamar ta shiga. Tana shiga ya maida ƙofar ya rufe mata. Ta mazauninsa ya zagaya, taga ya buɗe lokar motar ya ciri kuɗi ya maida ya rufe. Batasan waya bamawa ba, sai dai bai jimaba ya dawo suka fice a wajen.
A lokacin anata kiraye-kirayen sallar magriba. Gudu yake yanzu sosai, kai tsaye anguwar su Abban Abdallah ya nufa. Daɗi ya kama Aymah sai dai ta haɗiye abinta a ciki har suka isa. Anata hada-hadar shiga sallar magriba a massallacin ƙofar gidan. Horn ɗaya kuwa yayi maigadi dake ƙoƙarin fitowa zaije salla yay murmushi yana komawa ya buɗe musu. Shiga Yoohan yay da motar har ciki yay fakin Aymah nata mamakin ƙarfin halinsa.
“Kije ciki zanje nai salla”. Yay maganar yana buɗe motar ya fita. Ai tuni ma ta rigashi fitar. Sai hangota yay ta tsilla da gudu hanyar shiga cikin gidan. Da kallo kawai ya bita harta buɗe ƙofar falon ta shige.
Ya ɗan lumshe idanunsa ya buɗe yana nufar hanyar fita gate ɗin da hanzari jin za’a tada salla.