NOVELSSARAN BOYE

SARAN BOYE COMPLETE

Umma kuwa hannu ta hau tafawa ta kalli Naseer tana “Ashe gulmana Naeema keyi Ashe Haka Naeema take bin mutane tana musu gulma ta abin har ya Kai har da ta tamin sharri
Dama Haka kike Naeema toh wlh daga yau makarantar ma kin daina zuwa tunda acan kike haduwa da mutane kiyi gulmana har ki zageni Naeema Ina uwar mijinki toh wlh duk zagin datamin ba Ni ta zaga ba uwarki ta zaga Kai Naseeru wlh Tallahi na soke zuwa makarantar ta ko k’ofar gida bana so Naga kafarta a da sati daya zanyi Amma na ma fasa tafiya sai na kwana biyu shegiya Mayya”

Daga Haka ta juya ta barni a durk’ushe Ina ta kuka ko kad’an ban kawo sirrin Dana gayawa mmn Mannir zata zo ta tona a gaban Umma ba Dama gudun Haka yasa tun farko naki Gaya Mata ko Naseer ma ai bazai ji dadi na fadawa wani maganar ba duk ba wanan yafi bak’anta min Rai ba sai makaranta data ce bazan koma ba Allah yasan idan akwai abinda ke faranta min a rayuwa yanzu Bai wuce makarantar da nake zuwa nake samun ilimi ba sosai nake Kara sanin rayuwa sai gashi lokaci guda Umma ta katsemin Mai yasa mmn Mannir zata min haka”

Dafani da akayi yasa na Dago Naga Naseer ne da idonsa ya kad’a yyi ja idan ba karya idona yamin ba har hawaye ne ya Dan kwanta a idonsa

“Kiyi hakuri Naeema ki cigaba da hakuri watarana sai Labari nafiki Jin ciwon abinda ke Miki Amma ba komai Zan sadaukar da farincikina na faranta Miki idan Naga Umma ta cigaba da matsa Miki Zan sawwaake miki sabida ki samu yancin Mahaifiyata ce bansan ya zanyi da ita ba Dan Allah kiyi hakuri mu cigaba da gayawa Allah Yana sane damu ko auren Nan data k’ak’a bamin ba so nake ba tilasta min tayi idan kin Gama kizo akwai sakon da Mallam Musbahu ya bani na baki”

Daga Haka Naga ya mik’e da Sauri ya nufi dakina da Minal a hannunsa.

Ahaka na daka Sakwaran Ina kuka Sosai naji komai ya ficemin a Rai na ringa Jin inama inada damar da Zan gudu da yayana ko bara ne ma na ringa Yi a titi Ina ciyar dasu Amma aka cigaba da Haka zaa Kai ga na gudun Dan na gaji Kuma Ina gudun ba’a garin Nan Zan tsaya ba Tasha zanje na hau motar da zata kaini garinmu.

Har daki na Kai musu abincin Dan sun bar palon Hindatu da Kawar Umma ne kawai a zaune Umma da alamar ta shiga bandaki.

Nazo fitowa Hindatu ta tsayar Dani tana na kawo Mata wani lemon Bata San wanan tace tana hararata

Haka na fita na dauko Mata wani na fito daga d’akin na shiga d’akina Dan nayi Sallah Magriba Dan Ina shiga d’akina Naga Zahira a kwance tayi rub da ciki bayanta yayi jawur dayake farina ta d’auko sai sauke ajiyar zuciya take.

Naseer Kuma na d’aga gefenta Yana Dan mulka Mata jikinta da Robb bandaki na shiga da Sauri sabida kukan dake neman k’wacemin.

Ahaka naci kukana na Godewa Allah nazo na tadda sallah Ina iddarwa na maida kaina nayi Sujjada na fara kuka Ina rokon Allah ya kawomin d’auki.

Naseer shima Yana daga daya barin nawa bansan.mai ya hanashi zuwa Massallaci ba ahaka mukayi sallar Isha muna iddarwa.naje kitchen na dauko Mana abinci dayake indai Naseer na Nan a faranti daya muke ci da yaran Minal ce kawai nake Dan Bata a baki Sabida Naseer da su Zahira na zubo abincin Dan bazan iya cin abincin ba sabida b’acin Rai.

Zahira har lokacin sauke ajiyar zuciya take Ni Kuma bana San ma na jawota jikina Dan yanda nakejin Raina kuka zanyi sosai bazan iya rarrashinta ba.

Naseer shima gani nayi ya kasa cin abincin ya hau bawa Nadeeya abinci a baki ganin Zahira Taki cin abincin yasa yace Mata taci Mana bud’ar bakinta sai cewa tayi “wlh Tallahi Abba ban yiwa Umma komai ba Nadeeya ce ta fara gaisheta shine na tsugunna Dan na gaisheta Dan Haka Umma ta koya.mana mu ringa tsugunna wa idan zamu gaida babba shine Ina tsugunnawa ta hau dukuna wlh ban Mata komai ba ta karashe tana fashewa da kuka.

Kau da kaina nayi Sabida hawayen dake tsere a fuskata Naseer kuwa sai daya hadiyi yawu Mai daci kafin ya jawo Zahira jikinsa ya hau Bata hakuri Yana Bata abincin a baki wanda dak’yar ta fara karbar abincin tana ta sauke ajiyar zuciya.

Yana cikin Bata muka ji a banko k’ofar Umma ta fado d’akin tana “badai kana nufin a d’akin ta zaka kwana ba ka dai San sai kayiwa Hindatu kwana bakwai ko”?

Dan Haka maza kazo ka wuce matarka na jiranka kafin Nan da wani wata Taran wanan Mai gindin haihuwar ta Kara haifo Mana Yarinya Mara tarbiyya”

Daga haka ta zabgamin harara ta Kara banko Mana k’ofar.

Daga Ni har Naseer babu Wanda yayi magana a cikinmu Ni zuwa yanzu ma na kasa kukan filin sai na zuci

Naseer shima sai daya Dade Bai motsa ba Bai Kuma min magana ba kafin Naga ya mik’e ya janyo jakar kayansa yan Ciro wani bak’in Leda ya bud’e.

Yana “Ga sakon da Mallam Musbahu ya bani na kawo Miki”

Da Sauri na saka hannuna na karba na duba Yar wasikar da yamin Inda yake cemin na rataya wani rubutu daya nanade da takarda a bakin k’ofata.

Sai wani shima da akayi rubutun a ciki aka nannade shi da laya yace na makala a kaina Amma na ringa kiyayewa idan Zan shiga bandaki na ringa cirewa ya Kuma ce Kar manta na ringa kwanciya da alwala a jikina.

Sosai naji dadin Aiken da Mallam Musbahu yamin Naseer ne ya ratayamin a saman bangon kofata na samu pin na makala abin akaina.

Zage zagen da muka jiyo Umma nayi na Naseer ya rainata yasa ya mik’e da Quraninsa a hannu da Sallaya da carbi ya kalleni yacemin sai da safe.

Bance masa komai ba ya fita a Daren ranar xan iya cewa sai bacci barawone ya sace Ni akan sallaya.

Naseer kuwa Yana shiga d’akin yaga Hindatu taci kwalliya ta Dane gado tana ta Masa fari Umma kuwa Dama a Palo ya barota da jar doguwar Riga ita da kawarta.

Bai kalli Inda Hindatun take ba ya hau Kan darduma ya bud’e Quraninsa yayi gyaran murya Hindatu kuwa ta duro da.sauri ta tsaya gabansa tana “Wai an Gaya maka Ni hoto ce ko wancan kanjalalliyar matar taka Haka kake Mata idan ka shiga d’akinta.

Karatun da Naseer ya fara Yi da k’arfi cikin zazzakar murya yasa ta fice da sauri.

Yanaji Umma tana kiransa daga nesa Dan Bata iya isowa bakin kofar ba ya shareta ya cigaba da karatunsa Dan ko umman ma da Karatun zai koreta daga gidan

Sosai ran Hindatu ya b’aci ta hau surfawa Umma masifa Umma na Bata hakuri.

Washegari sai Dana shirya su Zahira Dan su tafi makaranta wani irin bakin ciki ya Kara turnike Ni da yanzu nima na shirya na tafi.

Tamkar baiwa haka na zama.a gidan Dan sosai nake bautawa Umma da Hindatu dake balain.jin haushina Dan gani take duk sabida Ni Naseer yak’i kwanciyar Aure da ita Dan karatun Qurani dayaga basa so kawai yake yi daddare da safe Kuma sai ya fito ya shiga d’akina ya Sha baccinsa zuwa Sha biyu ya fice daga gidan.

Yana fita kuwa Haka zasuyi ta zagina har Hindatu ta ringa gwada kawo hannu jikina

Abinda na lura dashi basa iya biyoni dakina su mun Dan Umma ta Sha gwada shigowa d’akina sai Naga ta koma da gudu ta ringa cemin Mayya.

Banma San a rahama nake a baya ba sai da Hindatu tazo gidan ko hanyar waje Umma Bata barina nayi.

Naseer kuwa ya Sha fadan ya Sha zagi a wajenta Akan yak’i kula Hindatu shi kuwa sai dai ya Bata hakuri yace akwai adduar da yake yi yana gamawa zai kulata.

Ranar da su Umma suka cika sati da zuwa da sassafe na farka kamar yanda na Saba na Dora abincin Safe na fito na tashi su Zahira Dan na shirya su su tafi makaranta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button