NOVELSSARAN BOYE

SARAN BOYE COMPLETE

_★★

     Alarm ɗin daya saka musu ne ya tadasu sallar asuba. Shine ya fara farkawa, sai da yayo alwala sannan yazo ya tada Nu'aymah da ƙyar. Ganin yanda take haɗa hanya alamar barcin bai saketa ba ya sakashi taimaka mata har ƙofar toilet ɗin. Bayan ta shiga ya canja kayan barcinsa zuwa jallabiya yasa abin salla ya kabbara raka'a-tainul fajir kafin ta fito.
    Itama koda ta fito doguwar riga ta cira a kayanta ta saka. sannan ta hau sallayan daya saka mata a bayansa tai tata nafilan raka'a biyu. suna zaune kowa na lazimi har lokacin sallan ya ƙarasa. itace ta bashi shawaran yay musu jam'i. Da farko ya nuna mata shi ina iliminsa ya kai da har zai musu jan salla. Ta masa taƙaitaccen bayanin da zai iya fahimtarta kafin ya jasu sallar asubahi.
    A mamakin Nu'aymah sai gani tai ya ɗakko Al-qur'ani ya dawo gabanta ya zauna. Kallonsa take kamar yanda shima nasa idanun ke a kanta.
 “Daga yanzu matata ce zata zama malamata kamar yanda Uncle ya bani shawara (baba malam)”. Sosai Aymah ta waro idanu waje, da faɗin, “Ni kuma Yaya Yoohan?”. 
  “Insha ALLAH kuwa. Dan duk abinda zanje nema a wajen wani malami na tabbata kinada kaso hamsin a cikinsa insha ALLAH. Karkiyi min wasa da damata Please Zeeynab, dan na yarda tun a farko UBANGIJI ya sakoki rayuwatane dan ki zamarmin fitila mai haska min hanya. So ni koda shekarunki basu kai hakaba zan zauna a gabanki na koyi abinda ban saniba. Cire duk wani kokwanto da shiriritanki nan wannan ba gaɓar wasa bane. Akwai manyan ƙalubale a gabana da dole sai da wannan ilimin zan tunkaresu”.
  Kan Aymah a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta ta jinjina masa kan. Cikin nutsatstsiyar murya tace, “Insha ALLAH zaka sameni yanda kake buƙata. Sai dai ka sani har yanzu ni ɗalibar ilimice, nima banje ko inaba a neman ilimin. Ko a gidanmu ƙaramin ajin yara nake koyarwa bawai manya ba”.
    “Bani da banbanci da waɗannan yaran nima ai Nu'aymah, domin abinda kike koya musu nima shi nake buƙata a yanzu ki koyar dani. Dukkan littatafan da zamu iya buƙata gasu Uncle yazo mani dasu. dan dama muna karatu da shi ta video call a kullum bayan sallar la'ar a duk inda nake. Da wannan ne na ɗan samu abin salla da addu'oin da kikeji a bakina”. 
  Sosai tausayinsa ya kama Aymah har idanunta suka cika da ƙwalla. Ya kuma birgeta matuƙa, dan ɗaukakarsa da girmarta da yayi, da matsayinsa na miji a gareta bata sakashi girman kai ba........
  “Please ki ceto rayuwata Zeeynab ”. Furicinsa ya katse mata tunani. Saurin ɗora hannunta tayi akan bakinsa saboda jin yanda yay maganar da rauni. Ta shiga girgiza masa kanta ƙwalla na sake taruwa mata a ido. “Ka daina roƙona, umarni kawai zaka bani a matsayinka na babba gareni kuma mij......”
  Sai kuma tai shiru ta kasa karasawa. Murmushi yayi da ɗaga mata gira. janye hannunta tai daga kan bakinsa ta hararesa. Yay karamar dariya da faɗin, “Hy karasa mana. Wai dama kinada kunya ashe?”.
  Harara ta kuma zuba masa tana kumbura baki, tace, “Silly boy”. 
 A tare suka fashe da dariya babu zato, dan ita kanta kalmar Silly boy ɗin datai saurin kiransa da shi kafin shi ya kirata ta bata dariya.. Sai da sukayi mai isarsu sannan suka nutsu. Ya gyara zamansa yana faɗin, “Silly girl kin rainani wlhy”. Batace komaiba sai murmushi.
   Shima dai murmushi ne ɗauke a fuskarsa. Ya kara gyara zamansa. “Gashi Al-qur'anin ɗaya ne yaya zamuyi kenan?”.
 Murmushi ta kumayi mai kayatarwa tana lumshe idanu. Batare data kallesa ba tace, “Karka damu, ko babu Al-Qur'ani a hannuna zan iya ai”.
     “Woow masha ALLAH” ya faɗa yanajin wata ƙaunarta da girmanta a cikin zuciyarsa da bargo. Daga haka suka nutsu ya fara karanto mata iya inda ya tsaya da harshensa da baya fita sosai. Hakan yasa karatun nasa yay mata daɗi. Sai da ya tsaya ta dubesa da kulawa. “Zamu cigaba da yin Al-qur'ani. Amma ina ganin ya kamata ka fara koyan larabci hakan na taimakama mai karatun Al-qur'ani sosai wajen furta abinda ake buƙata”.
 Idanu ya lumshe a hankali ya buɗe a kanta. cikin muryarnan tasa mai amo yace, “Okay maa. Duk yanda kikace haka za'ayi”. Duk da ya bata dariya batayi ba, sai dai ta murmusa kawai. Cikin baiwar da ALLAH ya azurtata da ita na wadatuwa da ilimin addini ta fara ɗorama Yoohan karatun. Ba ƙaramin nutsuwa da shagala yayi a kallonta ba. Dan yaune karan farko da yaji yanda take raira karatun Al-qur'ani mai girma a fili. Wata irin nutsuwace ta ringa saukar masa. har ƙananun ƙwalla suka taru masa a cikin ido bai saniba. Sai da suka sakko a fatar idonsa kaɗan idanunsa sukai masa gizo sannan ya lura. Ɗan yatsa yasa ya ɗaukesu yana cigaba da saurarenta.
    Tabbas Yoohan ya saka a ransa zai nema ilimin addini babu wasa a ciki. Hakanne yasa UBANGIJI riko da hannunsa. Gashi kuma ya bashi Aymah a kusa da shi da har cikin ransa ya yarda itace zata zame masa malama kuma sirrin rayuwarsa. Dan haka basu tashiba a wajen sai da ta tabbatat ya fahimci abinda ta koyar da shi. 
   Bayan sun kammala abinci mara nauyi yaymata, order dan taci tasha magani kar lokaci ya wuce. Tunda shan maganin nata akwai ƙa'ida. Hatta da barcinta yanzu yanada lokacin yi da tashi har sai komai ya ƙarasa dai-daita yanda ya kamata. Tea kawai ta iya sha da cake kaɗan, dan ita dai wannan abinci na Austrian baya mata daɗi. Wanima ƙyanƙyami yake bata. Musamman da harshenta har yanzu ba komai yake masa ɗanɗano ba. A hakama cake ɗin sai da Yoohan ya tayata ci sannan. Tana kammalawa ya bata magani tasha ta shiga wanka. Shi kuma fita yay dan motsa jiki a gym ɗin hotel ɗin. Da kuma son ƙarasa magana da Rich.
     Aymah na fitowa kaya kawai ta canja sai kwanciya. Ko mintuna biyar bata rufaba kuwa barci yay gaba da ita.............✍

ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo????
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).????????

      Mamu gee????

MIN ƘALB!!????????

    Hafsat rano????

ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!????????

    Safiyya huguma???? SIRAƊIN RAYUWA????????

     Bilyn Abdull????

SARAN ƁOYE????????

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka????????????????

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????

09033181070

????????????????????????????????????????
TEAM—-ZAFAFA BIYAR????????????????

ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????.LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana????????.

FEJI SATTIN????


*Sunana Nafisa k Abdullahi am a singer, actress.. wakokina are based on siyasa da kuma na sarakuna *

(YouTube link)????????

This is my YouTube channel IN SHAA ALLH! I will be bringing to you my latest films, And musical videos

NafisaKabdullahi Sabuwar ficacciyar jaruma ce data shahara wajen fina finai da kuma wakoki na siyasa, Masarautu da sauran su

Ina masoya makaranta littafan zafafa? Ku fito ga dama ta samu, Munason a nuna mana k’auna ta hanyar subscribing a sabuwar channel dinnan ta Nafisa mai suna a sama. ????????A kalla a kuma danna kararrawa domin sauraron shirye shiryen ta a duk sanda ta dora..

Danna kararrawa domin kasancewa da ita da zarar ta dora sabbin shirye shrye.

DAN ALLAH! Ayi subscribing, Akuma dinga viewing, Inda hali ma ayi comment da sharing zuwa ga wanda basu sani ba…

Akwai Facebook page dinta mai suna: https://www.facebook.com/preetyfeenat.abdullahi

*Domin karin bayani sai a tuntub’i Nafisa kai tsaye ta number ta: *

08071172003

kada ku mance ko minene daya danganci wakokin al’adun hausa, Da ire-iren fina-finan mu na hausa, Nafisa zata dinga kawo muku shi a wannan sabuwar channel din nata, Saboda haka MASOYA a temaka aje ayi mata subscribing a kuma dinga kallan abubuwan data dora..


No. 60

……….Koda Yoohan ya dawo ɗakin bayan awanni kusan biyu da fitarsa bai tada Aymah dake kudundune cikin bargo tana barci ba. Wanka yayi, yay shirinsa tsaf na fita asibiti. Turaren hannunsa ya ajiye dai da ring ɗin wayarsa. guntun tsaki yayi tare da ɗaukar brush ya nufo inda take yana kwantar da sajensa. Sai dai kuma ganin wanda yay kiranne ya sakashi ɗan waro idanu waje ya dafe goshinsa. Zama yay a bakin gadon dai-dai da katsewar kiran. Shine ya kirashi zuciyarsa fal takaicin tsakin da yayi. Koda baba malam yaga shigowar kiran da ga can murmushi yayi kawai ya ɗaga suna kallon juna da Umm dake a kusa da shi. Cike da girmamawa Yoohan ya shiga gaishesa. Shiko yana amsa masa da kulawa. Sunɗan taɓa hira da duk Yoohan ke ƙarajin ƙaunar Baba malam. Dan duk akan abinda zai amfani rayuwarsa ne suke tattaunawar. Daga bisani suka dawo da firar tasu akan Aymah. Hannu Yoohan ya kai ya janye bargon data rufe har fuskarta a hankali, dan ya gama fahimtar wannan ɗabi’artace na lulluɓa da bargo har kanta. Lumshe idanu ya ɗanyi ya sake buɗewa a kanta, dai-dai yana amsama baba malam da cewar, “Uncle babu wani damuwa yanzun kam. Gata nanma tasha magani tana barci. Sai nan da kamar awa uku zata tashi insha ALLAH”. Murmushi yayi mai ƙayatarwa saboda jin abinda baba malam ɗin yace daga can. Ya sake kai hannu akan girar idon Aymah ya shafa yana sakin murmushin da har haƙoransa suka bayyana. “Uncle ai zata daina watarana. Yanzunma ƙuruciya ce kawai, kowa dama da irin tasa. A dalilin aikin ma gashi yanzu tayi sanyi sosai. Duk ta zama shiru-shiru”. Faɗaɗa murmushinsa ya sakeyi sosai saboda amsar da baba malam ya sake bashi. Daga haka suka gaisa da Umm sannan yay musu sallama ya kashe.
Ranƙwafawa yay akan Aymah ya sumbaci kuncinta da saman ido. Bargon ya sake gyara mata yanda bazata rufe fuskarba sannan ya miƙe ya karasa kimtsawa yaɗan mata short note ya ajiye mata da wayar ya fice.

                X★x*x★X

Sosai Nu’aymah tasha barcinta. Bata farka ba sai bayan a wanni uku da fitar Yoohan kamar yanda ya ambata. Taji daɗin barcin sosai. ta miƙe tanata faman ɓata fuska irin ta wanda ya tashi a barci. Wanka tayo da ruwa mai ɗumi. Ta buɗe Wadrobe zata ciri kaya tajita gam. mamaki ya kamata da takaici ganin rufewa yayi. ƙunƙuni ta fara tana faɗin, ‘Gaskiya wannan mai jajayen kunnuwan yama rainani. Nasan maganinsa ai ALLAH kuwa. Sai yasan yayi da ƴar Umm da baba malam’. Ta ƙare maganar tana huci kai kace wani uban laifi akai mata. Har ta nufi gado da fushi sai kuma ta dawo da baya. Ɗayan murfin Wadrobe ɗin ta buɗe. A mamakinta sai taci karo da akwatin nasu anan. Shi ta buɗe tana ƙwafa da faɗin, ‘Na rantse akan kayanka zan huce takaicina. Dan sakasu zanyi naita birgima a ƙasan ɗakin nan har sai sunsan niɗin Zainabu ce jikar Zainabu Abu hajjaju Hajjo matar malam Hashim ɗan jibiy…….’ ta kasa ƙarasawa sabida cin karo da wata leda da tayi a gefen akwatin. Ɗauka tayi ta buɗe ledar tare da zazzago kayan ciki. ‘Ikon ALLAH sai kallo. shiko wannan bawa mi yake nufi dani dazai ajiyemin waɗannan kayan kamar ɗiyar tsuntsuwar sama jannati? Shin wai nufinsa ni jikar ɗan jibiya ce zansa wannan a tsokani shari’ar komi?, dama shiyyasa yaƙi ɗakkomin kaya sai wani jallabiya guda biyu dan tsabar ya maidani doll’. Tai maganar tana ɗaga wandon da bazai wuce rabin cinyarta ba. Ajiyesa tai ta cigaba da ɗaga sauran ma. Duk da bawani na fidda tsiraici bane sun bata haushi. Dan ba saba saka irin waɗanan ƙananun kayan tayiba a gida. Wani lokacin ko wando da riga ta saka sai Umm ta korata ta ɗora after dress a sama inhar zata fita daga sashensu. Mansa ta ɗauka ta shafa tanata cika baki da iska. Sosai takema man shafawar matsar mugunta. Wai shima sai yaji a jikinsa tunda ya saya mata waɗanan fingalallun kayan kamar wata ƴar tsana. To wlhy tunda ya raina mata jiki saita ta narkar abinci ta zama ƙatuwa kafin subar ƙasar nan. Sai tama aljihunsa ɗibar karan mahaukaciya (Danƙari. To kaji Yoohan talautaka za’ai a ƙasar Austria????).
Haka tasa kayan tana mita. ta ringa zazzagama jikinta turarensa wai shine target ɗin farko da zata fara. A gaban ƙaton mirror ɗakin taje ta tsaya tana kallon kanta. Ta wani riƙe ƙugu tana faɗin, ‘Woow na kumafa haɗu’ tai maganar tana jujjuyawa. ‘Yauwa nama tuna. Bara nayi yanda naga matar jiya tayi’ ta faɗa tana tattare ƙasan farar top ɗin tata ta ɗaure a gefe. Hakanne ya bama ɗingilis ɗin wandon nata kalar blue na jeans damar fitowa sosai. ‘Tab, wlhy su Umm an haifo baturiya ba’a saniba. Hummm inama zan haɗu da hajjo yanzun. Nunawafa zanyi bamma santa ba, dan saina gama folata irin nifa bamma san African ɗinnanba sannan’. Ita kanta abun sai ya bata da dariya. Ta ƙyalƙyale kuwa da ita kamar dai har yanzun kan da motsi????.
Haka taita shirmenta ita kaɗai harta gaji ta bari taje ta gyara gadon da kanta. A wajen gyaranne taci karo da note ɗinsa. Koda ta gama karantawa saita murmusa. Wayar daya ajiye ɗin ta ɗauka ta nufi ƙofar da taga sun fita jiya ta danna yanda taga yayi da zai rufe. a take kuwa labulen ya zuge. Ta sake dannawa ƙofar glass ɗin itana ta buɗe. Farar ƙafarta dake a cikin blue Slippers ta zira waje tana wani zuƙar daddaɗar iskan wajen. Barandan ta ɗakinne kawai, hakan yasa taji ta ta sake dan babu ruwan wani da wani. Sannan anyi iyakar da waɗanda ke maƙwaftaka da ɗakin bazasu gantaba, kamar yanda itama bata ganinsu sai ainahin birnin Vienna da kuma harabar hotel ɗin da ƙaton swimming pool yake. Shima sai idan ta miƙene a jikin ƙarfen barandar zata iya ganin masu hutawa na wanka, wasu kuma suna zaune a kujeru ana zuƙar drinks.
A ɗaya daga cikin kujerar wajen ta zauna, ta ciro buk ɗaya dage cikin ɗan kantan wajen ta ajiye sannan ta hau ƙoƙarin kiran su Baba malam cike da ɗoki. Kamar kuwa jira sukeyi, tana kira ring baifi uku ba Umm ta ɗaga. Dan baba malam yana wanka a lokacin. Cike da ihun murna ta farama Umm magana. Itako daga can sai dariya take da jinjina wauta irin ta ɗiyar tata. Dan ita ta tabbatar ba kuruciyace kawai ke ɗawainiya da Aymah ba. Akwai tsantsar wauta tattare da ita. A dai ƙasar hausa mai shekaru irin nata ai budrwace cikkakkiya kowa ya sani. Biye mata tai ko tanata faman bata labarin haduwar hotel ɗin da suke, da gine-ginen garin Vienna. Harda cewa Umm bara ta katse ta kira video call wai dan ta gani. da sauri Umn tace, “A’a shugabar rawan kai na gode. Nima ai nazo na gani da idona”.
“Yo Umm ai dai bakiyi yawoba” tai maganar cike da shagwaɓa. Dariya Umm tayi da faɗin, “ALLAH ya shiryeki Nu’aymah. Ga Abbanki nidai barni na hutama raina. Ga autana can kwance yana fama da zazzaɓi bara naje naji da shi”.
A take kuma sai mood ɗin Aymah ya canja jin abokin faɗa babu lafiya. Duk sai ta marairaice kuma har ma abin ya bama Umm da baba malam dariya. Haka dai ya amsa shima ta zuba masa shiriritarta. Sai da yace ta kashe wayar haka karsu ƙararma Yoohan da kuɗi sannan sukai sallama bayan anbama Muhammad shima sun gaisa, duk da a kwance yake bayajin dadi. Daga haka Hajjo ta kira. Itama suka gaisa. Badan tasoba ta haƙura ta ajiye wayan ta ɗauki buk ɗin data ɗauka ta fara dubawa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button