NOVELSSARAN BOYE

SARAN BOYE COMPLETE

      A nan Austria kam Yoohan da ƙyar ya iya taimakama Aymah ta sake shiga cikin ruwan zafi. Sai dai yau batai rakin jiyaba. Hawayene dai kam tanata abunta. Baiyi maganaba dan shima takansa yakeyi, da alama ma yafita jin jiki yanzun. Tana ganin ya shiga wajen wanka tai alwala ta fice daga bayin tana ɗingishi. Yau ko jiransa ya jasu salla batayiba. Tana idarwa yana fitowa. Komawa tai kan gado ta kwanta.
  Bazai iya salla a tsayeba saboda jiri yake gani ga ciwon kai. Hakan ya sakashi yinta a zaune, yana idarwa shima gadon ya koma ya sake kwanciya. Wayar landline ya ɗauka da nufin kiran yima Aymah order ɗin breakfast saboda shan maganinta sai yaga wayarsa na haske. Hotel ɗin ya fara kira, kafin ya ɗauka wayar tasa dan silent take dama. Richard ya gani, cike da mamaki ya amsa kiran dan alamu sun nuna Rich ɗin yana a cikin Austria tunda da Number ƙasan ya kirashi. 
     Ko gaisawa basuyi ba Richard ya fara jera masa tambaya a rikice saboda jin muryarsa, cikin son kwantar masa da hankali Yoohan yace, “Ciwon kai ne kawaifa. Dama kana Austria?”.
   “Jiya da dare na iso, yanzu dai idan ba damuwa bara nazo ɗakin naku na dubaka hankalina zaifi kwanciya”. Murmushi kawai Yoohan yayi da faɗin “Okay”. Daga haka ya ajiye wayar ya juya yana kallon Nu'aymah data juya masa baya. Ta naɗe a cikin bargo alamar sanyi takeji. Maida idanunsa yay ya lumshe tunda yasan akwai kaya jikinta.

    Kusan a tare Richard da ma'aikaciyar hotel ɗin suka iso. Rich ya amshi abinci kawai sannan ya danna door bell. Miƙewa Yoohan yayi da ƙyar hannunsa dafe da kansa. Ya gyarama Aymah ɗan kwalin kanta daya zame sannan ya nufi ƙofar ya buɗe. Saurin riƙesa Rich yayi ganin yanda yake layi, duk ya rikice masa da faɗan yaya zai zauna da ciwo irin haka baije asibitiba?. Amma yana faɗin wai ciwon kai ne kawai. Murmushin ƙarfin hali kawai Yoohan yay masa shi dai, ya zaunar da shi a kujera yana sake jera masa sannu.
   Kansa ya ɗaga masa yana magana cike da ƙarfin hali. “Shine zaka shigo baka sanar min ba?”. 
   Rich da damuwa duk ta baibayesa yace, “Manta da batun shigowata faɗamin mike damunka Please X-man”.
  “Kai dai ka cika ruɗiya. Ciwon kai ne kawai da zazzaɓi”.
 Hararsa Rich yayi da faɗin, “Shine bazakaje asibiti ba? Ina madam?”.
  Da idanu ya nuna masa gadon da cewa, “Gata can, itama bata da lafiyar”. 
   “Oh GOD. Miya faru haka?”.

Murmushi kawai Yoohan yayi baice komaiba. Hakan yasa shima Rich ɗin bai sake magana ba ya miƙe ya fita yana faɗin, “Ina zuwa Please”.
“Okay” Yoohan ya faɗa da jingina jikin kujerar ya lumshe idanunsa. Yanason tashi yaje ya tada Nu’aymah data fara barci taci abinci amma jiri da yake gani ya hanashi motsawa. Har tsahon mintuna sha biyar Richard ya dawo da kayan magani. Sannu ya sake yima Yoohan ɗin sannan ya zauna yay allurai a cikin drip. Yana gamawa ya dubi Yoohan.
“Ya kamata ka koma kan gado sai a saka drip ɗin”. Idanu Yoohan ya buɗe da ƙyar, batare da yayi magana ba yay ƙoƙarin tashi tsaye. Taimaka masa Rich yayi har kan gadon. Aymah nata barcinta batasan hidimar da sukeyi ba ita dai.
Ɗaura masa ruwan yayi, sai da ya tabbatar ya fara shiga jikinsa sannan yace, “Ita kuma yaya zamuyi da ita?”. Isaka Yoohan ya ɗan furzar idanunsa a lumshe yace, “Inaga ita barta kawai, dan allura ya kamata ai mata kuma bazata tsaya ayi da arziƙi ba. Dan bata ƙaunar allura sam”.
“Okay, idan ka tashi kayi mata. Sai dai akwai alluran a wajenka ko sai an siyo?”.
“Sai an siyo”.
Ya bashi amsa a yanayin barcin daya fara fisgarsa. Sai kuma ya faɗama Rich ɗin sunan allurar da yake buƙata.
Idanu Richard ya ɗan waro waje jin allurar da Yoohan ɗin ya faɗa. Cike da neman magana ya shuri ƙafar Yoohan ɗin yana faɗin, “Shegen sama, ashe kasan tsiyar daka aikata”.
Shi dai Yoohan baice masa komaiba dan barcin ya fara masa Nauyi, Richard ya fice cike dajin daɗin ɗan uwansa ya zama babban mutum yau.

    Yanayin rashin jin daɗin jikin ya sakata kasa barci yanda ya kamata, ta buɗe idanunta a hankali kansa. Barci yake sosai yanzun. Ganin kamar ana ƙara masa ruwa ya sakata tashi aɗan zabure. Cike da ruɗewa ta kai hannunta ta ɗora a bisa kansa. Har yanzu kan nasa bai gama hucewa ba da zafi. Sosai damuwa da tausayinsa suka bayyana ƙarara a fuskarta. A fili tace, ‘Bawon ALLAH, ashe shima bashi da lafiya, shiyyasa ɗazun yaketa magana da ƙyar. Ɗan balarabe ALLAH na zata duk muguntar da kaimin ce ta sakaka komawa kalar tausayi ai’. Ta ƙare maganar da ɗora kanta bisa ƙirjinsa hawayena cika mata idanu ganin an saka masa allura a jiki. Dan itafa ba'a taɓa mata ƙarin ruwa cikin hankalinta dan bazata yardaba. Inhar yazam za'a ƙara mata ruwa to lallai sai an bata maganin barci ko an mata allurar barci saboda tsabar ƙiyayyar dake a tsakaninta da allura.
    Ta daɗe jikinsa kwance kafin ta tashi ta zauna, tagumi tayi hannu bibbiyu ta zuba masa idanu kaikace television ta samu. Ta shafe kusan mintuna talatin a haka kafin ta miƙe saboda fitsari da takeji. bayan ta fito kuma idonta ya sauka kan abincin. Yunwa takeji bana wasaba, dan haka ta zauna ta faraci dan ta fahimci natane dama. Tanaci tana kallonsa harta kammala dan kaɗan ma taci saboda rashin daɗin bakinta, cike da son ƙarfafa kanta da rashin daɗin da jikinta ke mata ya sakata ɗaukar magungunanta tasha kamar yanda taga yana bata kullum. Kasancewar barcin da suke sakata idan tasha ya sa ta ƙara ɓingirewa barcin a wajen.

★★★★

    A hankali Yoohan ya buɗe idanunsa saboda kaɗawar alarm alamar lokacin sallar zuhur yayi. Hakan kuma yay dai-dai da farkawar Aymah dake can kan sofa itama. Sai dai har Yoohan ya miƙe zaune ita ɗin bata tashinba tana kwancenta. Inda take ya kalla yana sake lumshe idanu da buɗewa. Sosai ciwon kan nasa yay ƙasa. Zazzaɓin ma kuwa duka ya sauka. Ya zare drip ɗin da kaɗan ya rage ya ƙare. Fuskarsa a yamutse na alamun wanda ya tashi a barci ya sauke ƙafafunsa ƙasa yana ambaton Alhmdllhi a cikin ransa. Sai da yay kusan minti uku a zaune sannan ya miƙe zuwa inda Nu'aymah ke kwance.
    Da sauri ta maida idanunta ta rufe, shikam batare da yasan idanunta biyu ba ya ɗora hannunsa saman kanta. Alhmdllh ya faɗa jin babu zafi. Ya taɓa wuyanta ma nanma sanyi ƙalau. Maganganun data sha ya dudduba yaga tashasu dai-dai, hakan ya sakashi miƙewa ya nufi bayi zuciyarsa sakayau da farinciki da nishaɗi. Jinsa yake tamkar wani sabon mutum a duniyar mutane. Aymah na ganin ya shige ta tashi zaune fuskarta a curkuɗe kamar zatai kuka. Gaba ɗaya jitake tama rasa abinda ke mata daɗi a duniya. Babu abinda tafi buƙata kamar ta ganta a gaban Umm ɗinta. Ta haɗiye ƙwallar daya cika mata idanu tare da zabga uban tagumi.
   A haka Yoohan ya fito ya sameta. Kallo ɗaya tai masa tai azamar maida kanta ƙasa saboda ganinsa da ga shi sai boxer da ƙaramin towel a hannu. Direct yayo kanta yana faɗin, “Kin tashi?”. Kunya ta hanata masa magana, sai kai kawai ta kaɗa masa. Bai damuba dan ya fahimci kunyarsa takeji. Ya zauna a hannun kujerar yana cigaba da goge wuyansa idanunsa a kanta. “Mike miki ciwo yanzun?”. 
 Murya na rawa tace, “Komai ma”.

A ransa yace, ‘Abin nemafa ya samu ga iya madam hajjaju malamar tsiwa da shagwaba’. A fili kam sai yace, “Oh so sorry Mrs Yoohan. Jekiyi wanka sai na duba wajen na gani”.
Da sauri ta ɗago tana hararar sa kai kace idanun faɗowa zasuyi ƙasa. Gashi dama sun kumburo saboda kukan data sha sannan akwai ja a cikinsu. Da sauri ya kauda kansa gefe gudun kar dariya ta kufce masa ya ƙara laifi. Miƙewa tai tabar wajen tana ƙunƙunin da baisan mitake faɗaba a ciki saboda hausa takeyi. Ya ɗan lumshe idanu ya sake maidasu kanta. Sosai yanda take tafiya da ɗingishi ya ƙara masa tausayinta da ƙaunarta a cikin zuciya. Tana gama shigewa ya sauke ajiyar zuciya ya miƙe…………..✍

Hafsat miss xoxo????
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).????????

      Mamu gee????

MIN ƘALB!!????????

    Hafsat rano????

ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!????????

    Safiyya huguma???? SIRAƊIN RAYUWA????????

     Bilyn Abdull????

SARAN ƁOYE????????

Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka????????????????

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????

09033181070

????????????????????????????????????????
TEAM—-ZAFAFA BIYAR????????????????LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana????????.

No. 63

…………Ganin lokacin salla zai wuce ya sakashi mata knocking dan taƙi fitowa. “Sorry baby fito muyi salla kinga munata makara. Na yarda idan mun idar ki hukuntani koda bulalane ok”.
Fitowa tayi, dan itama batason lokacin sallar ya wuce, dama ta sake shiga ruwan zafi ne dan tanajin daɗinsa sosai. Ƙin yarda ta kalli inda yake tayi. Taje ta saka doguwar riga, shi kuma ya saka musu abin salla. Suna raka’a ta biyu Richard ya shigo ɗakin bayan yayi knocking yaji shiru. A zatonsa ko jikin nasu ne shiyyasa ya shigo abinsa. A hankali ya ajiye kayan hannunsa idanunsa a kansu. Tsigar jikinsa sai tashi take. Haka ya zauna yanata kallonsu tamkar ya samu television har suka idar. Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da Yoohan ya zubo masa harara. Da yare yace, “Shine bazaka jira a baka izinin shigowa ba zaka wani faɗoma mutane ɗaki?”. Jikin Richard duk a sanyaye yake, shiyyasa yace, “I’m sorry” kawai yana furzar da iska. Kauda kai Yoohan yayi ya maida ga Aymah dake jinsu sai dai ko ɗago kai batayiba dan itama shigowar Rich ɗin ta bata haushi. Dan tarbiyyarta ta koya mata shiga waje da sallama da kuma jiran bada dama. Yoohan ya fahimci shigowar Rich ta bata haushi. Dan aɗan zamansu ya fara fahimtar wasu daga halayenta. A hankali yace, “Kiyi haƙuri. Sai kin taimakeni wajen ceto rayuwar ɗan uwana da ga duhu zuwa haske”.
Karan farko ta ɗago kai ta ɗan kallesa. sai kuma tai ajiyar zuciya da maida dubanta inda Rich yake zaune. Sai dai ba kallonsu yakeba yanzun. “Good Afternoon”. Ta faɗa da dasashshiyar muryarta datasha kuka.
Miƙewa Yoohan yayi yana faɗin, “Ana gaisheka”.
Buɗe idanu Rich yayi yana kallonta, ya amsa cike da kulawa da tambayarta ƙarfin jiki. A taƙaice tace, Am better now”.
“Thanks God”. Ya faɗa shima yana miƙewa. Fita yay ƴar barandar nan ya zauna, yayinda Yoohan kuma ya zauna inda ya tashi yana kiranta. Batare data tankaba ta miƙe ta nufesa. Gefensa ya nuna mata yana binta da kallo. Ita dai taƙi kallonsa sam. Abincin da Rich ya kawo musu ya buɗe. Gasashshen naman kaza ne da yasa akayisa na musamman domin Nu’aymah, sai haɗin salad da sauran tarkacen abincin Austrian daba gama haddace sunayensu tai ba itakam. Kamo hannunta yay ya matso da ita sosai jikinsa yana magana cike da lallashi.
“Ki daure kici wannan bakinki zaiyi daɗi sosai. Kuma zaki samu sauƙi insha ALLAH. Dan abincine da ya dace da buƙatar irin yanayin da kike ciki ok”.
Idanunta cike da ƙwalla tace, “Toni bakina fa babu daɗi ALLAH”.
“Eh idan kikaci wannan zai miki daɗi, idan kuma kinason na miki allura tom, ina dasu buhu-buhu a ɗakin nan. Ohya buɗe bakin”. Hawayen da take maƙalewa ne suka silalo, jin zancen allura ya sakata buɗe baki ya saka mata. Share mata ya shigayi yana faɗin, “Kefa yanzun babban mace ne, kin girmi harkar yara. Kona tayaki ci ne?”.
Da sauri ta ɗaga masa kanta alamar eh.
Yace, “Okay to dinga bani da kanki muyi maza mu mucinye kinga Rich yana jirana”. Babu musu ta dinga bashi shima yana bata. sai ko gashi sun cinye kazar tas harma suka ƙara da wani abun. Yana son ɗaukar allurar da Richard ɗin ya kawo amma bayason ɗaga mata hankali. Hakan ya sakashi ɗaukar ledar yabar wajen. Bata fahimci mizaiyi ba shiyyasa bata maida hankali kansa ba. Sai tattare kayan da sukaci abincin take.
Batare data san mi yayoba yazo ya sake zama kusa da ita. Kallonsa tayi sau ɗaya ta janye idonta tana tura baki. “Ba kace jiranka akeba”.
Wuyansa ya shafo yana gyaɗa mata kai. “Magani zansha sannan. Ɗakko min gasu can”. Kamar zata fasa masa kuka ta miƙe inda ledan maganin yake. Batason yin tafiya saboda zafin da takeji. Da kallo ya bita harta ɗakko ta juyo sannan ya janye idonsa.
Ledar data miƙo masa ya haɗa d hannunta gaba ɗaya ya jawota saman cinyarsa. kafin ta sami damar yin magana ya manne bakinsa da nata tare da saita allurar dake ɓoye cikin ɗayan hannunsa a inda ya dace. Tanajin shigar allurar ta nema fisge jikinta daya fara rawa dan abin yazo mata a bazata. Ya rumtse idanunsa da sauri saboda wani shegen mintsini datake masa a hannunsa. Allurar ya zare tare da bakinsa yana faɗin, “Ouch!!. sweet girl Zaki fasamin fata”.
Lafewa tai a jikinsa tana sauke ajiyar zuciya a jajjere da shashshekar kuka mara sauti. Ga hawaye na zirara. Goshinta ya sumbata yana ɗan murmushi. Am sorry bazan ƙaraba huyim?”.
Ita dai bata tankaba. Tanata hawayenta ne. Cigaba yay da shafa bayanta har sai da ta daina kukan sannan ya sauketa a kujerar, a gabanta ya durƙusa hannunta cikin nasa. Ya share mata hawayen da ɗayan hannun, a ransa yana dariyar rakinta akan allura. Sai da ya tabbatar ta samu nutsuwa yanda ya kamata sannan ya duƙo ya sumbaci kumatunta da bakinta. “Bara inje inazuwa. Insha ALLAH wajen zai daina zafi kinji”.
Batace komaiba. Amma yasan tana jinsa. Ya sake sumbatar laɓɓanta sannan ya miƙe. da kallo tabi bayansa harya fice ƴar barandar nan. Sai ta maida idanun ta lumshe duk da ba barci takejiba kuwa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button