NOVELSSARAN BOYE

SARAN BOYE COMPLETE

   ★★★

“Sai yanzu kagama lallashin?”
Richard da ke danna lap-top ya faɗa cike da tsokana.
Hararsa Yoohan yayi, yaɗan sosa tsakkiyar kansa da cewa, “Ka samin ido da yawa fa”.
Dariya Richard yayi kawai. Sai kuma ya juyo masa da fuskar lap-top ɗin yana sauke numfashi. “Brother lamarin zancen cikin nan fa akwai rikitarwa. Kasan gaba ɗaya Doctors ɗinan gaskiyar abinda suka gani suka faɗa? A iya bincikena babu wanda ya haɗa kai da su wajen bada result ɗin ƙarya, aikinsu sukayi a gaske”.
Yoohan dake kallonsa yana ɗan taunar lip ɗinsa na ƙasa ya lumshe idanunsa da buɗewa a kansa. Da ɗan yanayin ruɗani yace, “Amma to miyasa sukaga haka? Yarinyar nan fa She’s virgin wlhy”.
“Really?”.
“Kasan bazan faɗa maka abinda ba haka yakeba Rich. Amma lallai akwai abinda ke ɓoye da bamu sani ba. Minene sauran bayanin?”.
Iska Rich ya furzar yana matso da kujerarsa kusa da Yoohan, ya gyara zaman lap-top ɗin. “Nabi diddigin duk abinda abin recording ɗin nan ya naɗa na mai aikinku. Ga su nan zaka iya samun lokaci ka saurara. Nata tunanin ta hanyar dazan samu wayarta, shine da mukai magana da kai kace nasa Blessing. A randa mukai maganar kuwa washe gari nasaka Blessing ta sato mana wayar har gidan Uncle ɗin madam ɗinka. Waɗanan sune gaba ɗaya Contacts ɗin wayarta. Na kuma bibiyesu dukansu da duk wayoyin da tayi da masu Numbers ɗin. Abinda na gano na farko shine kakar madam ɗinka kamar tana kan sani ta aiko yarinyar nan wajenku. Sai dai dalilinta nayin hakanne sam ban saniba gaskiya. Nabi duk hanyoyin dazan iya fahimtar wani abu ban samu dama ba”.
Kai kawai Yoohan da ke saurarensa da kallonsa yake kaɗawa.
Rich ya cigaba da faɗin, “Wannan itace Number datafi kira. Sannan da itanema mukafi samun bayanai. Sai dai matsalar da hausa language suke magana. Inaga dole sai madam ta taimaka mana. Wannan shine ainahin sunan da akai register ɗin layin da shi. Rabi’atu Halidu dauda kuma yanda alama ta nuna mana mai Number tana a cikin gidansu madam ɗinka. Sai dai bamu saniba ko anan take rayuwa, ko zuwa kawai takeyi”.
“Gaskiyarka, dolene sai da taimakon Zeeynab zamu san wasu abubuwan kam. Tunda ita dai duk wanda ke cikin gidan ko shiga da fita ta sani”. Yoohan yayi maganar hankalinsa akan lap-top ɗin.
“Tabbas wannan shine mafita, kuma itace hanya mai sauƙi. Dan inhar wannan Rabi ɗin tana a cikin gidan to itace first suspect ɗinmu, dan inhar aka samu nasarar kamata zamu iya samun bayanai masu yawa a wajenta”.
“Okay ina zuwa” Yoohan ya faɗa yana mikewa. Ɗakin ya koma. Sai dai daga bakin ƙofar ya tsaya yay kiran Nu’aymah da ke zaune yanzun ta kunna television tana kallo. Babu musu ta taso inda yake dan bataga fuskar wasa tattare da shi ba. Kafin ta ƙaraso ya juya ya fito, hakan yasa itama biyo bayansa har wajen. Ya gyara mata kujerar kusa da shi ta zauna.
Wayar da Richard ke dannawa ya ajiye ya ɗan kallesu, sai dai baice komaiba. Itama dai Aymah bata kallesa ba. Coffee ɗin da suke sha Yoohan ya nuna mata alamar ko tanaso?. Kanta ta girgiza masa.
Yace, “Okay, Please wani aiki zaki mana dama Sweet girl”. Kallonsa ta ɗanyi, sai kuma ta maida kanta ta duƙar. Shi dai Rich na jinsu amma bai saka baki ba. Sai ma latsa waya daya cigaba da yi yana turama Juliet ɗinsa text message.
Lap-top ɗin Yoohan ya tura mata gabanta yana nuna mata Number Rabi da sunanta. “Kinsan wannan Number da sunan?”. Ɗan tsirama lap-top ɗin idanu Aymah tayi tana gyara glass ɗinta. Tai wani ɗan murmushi a bazata tana ɗagowa ta kalli Yoohan da shima ita yake kallo. “Sunan dai kam irin na mai aikinmu ne, sai dai ban riƙe Number ɗinta ba. Amma bara mu kira Umm sai ta turo mana”.
Da ga Yoohan har Richard sunyi na’am da hakan. Yoohan ya mikama Aymah wayarsa alamar ta kira Umm ɗin. Number Umm ta saka tai dailing. Sai dai harta tsinke bata ɗagaba. Sake kira tayi, nanma har sun fidda ran zata ɗaga sai sukaji an daga. Zazzaƙar muryar Muhammad tai sallama. hakanne ya saka Aymah yin murmushi mai faɗi da cewa, “Uhm Auta kaine?”.
Daga can yace, “Lah Aunty N dama ke ce?”. Murmushinta ya sake faɗaɗa. Sai da ya gaisheta ta tambayesa ya makaranta sannan tace masa ina Umm?.
“Umm tana sashen Addah, amma bara na kai mata wayar”.
Da sauri Yoohan ya girgiza mata kai. Hakan yasa itama saurin cewa, “A’a barta, amma ko zaka iya dubamin Number Rabi ka turo min yanzun?”.
“Eh zan iya Aunty. Ranarma bani na tura miki Number Gwaggo ba da su aunty Zulfah”.
“Yes, hakane my sweet Darling. Yanzuma ka turomin Please, amma ka nutsu ka ɗauki Number dai-dai kaji ko”.
Amsa mata yay da to, sannan ta yanke wayar. Ko mintuna uku kuwa ba’ayi cikakku ba sai ga message ya shigo. Suna buɗewa sukaga Muhammad ɗinne ya turo. Number lap-top ɗin da wadda ya turo suka duba. Sai ko gata tazo iri ɗaya. A tare suka kalli juna. Cike dason jin dalilin zuwan Number wajensu Aymah tace, “Amma miya faru wai?”.
“Karki damu zan faɗa miki. Saka earpiece ɗin nan ki saurari vn ɗin nan yanzu dai. Munason musan abinda ke ciki”. Babu musu ta amsa earpiece ɗin daya miƙo mata ta saka a kunne. shi kuma ya makala jikin lap-top ɗin yay mata playing na farko.
Shiru tayi tana mamaki cike da tsoro da al’ajabi, duk da ta daɗe tana zargin rabi na musu SARAN ƁOYE bata kawo abin ya kai har hakaba. Yana karewa ta zare earpiece ɗin daga kunnenta ta riƙe a hannu tana kallon Yoohan da duk suka zuba mata ido.
Da damuwa tace, “Wai tana tambayarta ne yaya zamana yake a gidanku?. shine Uwaliya ta sanar mata ita dai bataga komaiba har yanzun, dan tunda muka shiga gidan na rakata ɗaki bata sake ganina ba har yanzu. Tanama ɗakin bata fitaba. hakan na nufin kenan ranar farko da mukaje da Uwaliya gidan”.
Sosai fuskar Yoohan ke a tsuke. Batare daya ce komaiba ya nuna mata ta maida earpiece ɗin. Sake mata playing na gaba tayi. Bayan ta gama saurare shima tai musu bayin, dan akan dai zaman gidanne. Na uku ma haka, har na randa Momy sukai hayaniya da Aymah. Sai randa kuma Gebrail ya shigarma Aymahn ɗaki wanda yay sanadin zuwansu Austria duk ta bama Rabi labari har suna kwasar dariya. Musamman ma Rabi har faɗi take ALLAH yasa Nu’aymah ta mutu acan wajen aikin, dan ta matuƙar tsanarta. Sannan ta godema Gebrail da yaba masa.
A matuƙar firgice Yoohan yace, “Hasashena yana dai-dai kenan. Gebrail!! Gebrail!”. Yay maganar da dukan tebir ɗin gabansu da ƙarfi yana miƙewa.
Aymah da dama Gebrail ɗin ta zarga itama ta sauke numfashi da faɗin, “Na Gebrail ba shine important ba Yah Yoohan, tunda ALLAH ya kuɓutar dani. Bakuma sake yarda zanyi ya kuma samun damaba insha ALLAH. Wannan matar da kullum take nane da Umm ɗina tsahon shekaru itace abin duba. Bansan mi take buƙatar ji tattare da niba data addabi Uwaliya da tambaya kullum a kai na harda min fatan na mutu ta tsaneni. Sannan ita kanta Uwaliya kenan dama an kawotane dan ta dinga tattara bayanai akaina tana faɗa musu ko mi?. Innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un”.
Richard ne ya sauke nannauyan numfashi tare da kamo hannun Yoohan da ransa ke a ƙololuwar ɓace ya zaunar. “Cool down X-man. Maganar Madam nakan hanya. Na Gebrail mai sauƙine tunda a kusa da mu ya ke…….”
A fusace Yoohan ya katsesa da faɗin. “Karku gayamin maganar banza mana Rich!!. Tayama zakuce nasa mai sauƙine shima? Ya shigarmin ɗakin mata sannan kuce mai sauƙi? Kenan raping ɗinta ya keson yi komi? Ni yaron nan zai shigarma ɗakin mata!!…..”
Ba ƙaramin firgita Aymah tai da yanayin Yoohan ba. Dan tsantsar wutar masifa dake gauraye da kishi ta hanga cikin idanunsa. Gashin jikinsa duk ya mimmiƙe tsabar bala’i. Rich ya fahimci kishin ƴan maza ne ya motsa. Dan haka ya daga kafaɗarsa cikin lallashi yace. “Please ka fahimcemu. Gebrail bai ƙyautaba kam. Amma abinda zaka duba shi namune. Zamu iya hukuntashi a yau ɗin nan idan munso. Itako wannan fatama fa take Madam ta mutu. Kaga lamarin nata ya gawurta kuma akwai ban tsoro a ciki. Dan zata iya bata wani abunda zai halakata ma ba’a saniba……..”
Maganar Richard kam tamkar ta tsikari Nu’aymah ne. ta dubesa zuciyarta nason kawo mata wani tunani da sai yanzunne yazo mata a cikin rai ma ita. amma badai tace komai ba.
Da ƙyar Richard ya samu Yoohan ya dawo hankalinsa akan zancen Gebrail suka cigaba da tattauna maganar Rabi.
Ransa a dagule yace, “Wannan matar lallai akwai wanda takema aiki a gidan wannan ba basirarta bace ita kaɗai. Sannan akwai wanda ke laɓema mutane a gidan ta Window, kodai itace ɗin dai, kokuma yazam wanine daban shima”.
Kallonsa Aymah tayi da sauri domin ƙara tuna abu na biyu. Tace, “Yah Yoohan kana nufin kaima ka taɓa ganin hakan a gidanmu?”.
Kallonta yay da jinjina mata kai. “Tabbas nagani a randa naje gidanku game da pictures ɗin nan. Naga mutum a jikin Window ɗin Granny. Shinema ya bani haske akan lallai an ƙulla miki ne akan zancen ciki, kokuma akwai wani abu daban dasu Uncle su basu saniba. Amma kema kin taɓa ganine?”.
“Na taɓa ganin inuwar mutum yafi a ƙirga jikin Windown ɗakina kona falonmu. sai dai ban taɓa kawo komai a raina ba dan bamayi zaton mutumu ɗin bane. Sai a daren da wannan abun zai farune lokacin cikina ya fara ciwo ina ɗagowa naga inuwar, sai kuma aka bar wajen shine dalilin zargin cewa mutumne a wajen”.
Kallon juna Yoohan da Rich sukayi. Sai kuma duk suka dubi Aymah ɗin. Yoohan ya kamo hannunta cikin nasa da kulawa yace. “To waini abindama ya kamata tun wancan lokacin duk mu sani shine. Tayaya ma kika fara bleeding a waccan ranar?”.
“Babu wanda ya taɓamin wannan tambayar, nima kuma ban taɓa tunanin bama wani amsarta ba,, duk da abin na’a cikin raina”. Tai maganar hawaye cike da idanunta.
“Kiyi haƙuri, maybe kowama bai tuna bane, dan ana cikin tashin hankalin ciwonki shiyyasa. Amma na tabbata koda kowa baiso mikiba Uncle da Umm zasuyi tunanin miki ita. Yanzu ki sanar mana yaya abin ya faru?. Maybe mu samu wani evidence ta dalilin jin”.
Hannu tasa ta ɗauke ƙwallar da suka cika mata idanu, Yoohan na shafa bayanta alamar lallashi. Cikin nutsuwa ta fara basu labarin tun daga fitowarta da gamo da Rabi datai ɗauke da zoɓo zata kai mata. Da shayi data sakata dafa mata har sauran abinda ya biyo baya ta suma. Sai da ta farfaɗo ne takejin sauran abinda ya farun a bakin Yusrah. Dan Umm bata taɓa mata maganarba har yanzu”.
Matso da ita yay jikinsa ya kwantar da ita a ƙirjinsa yana shafa damtsen hannunta alamar lallashi, dan hawaye takeyi. Shi kansa sai faman sauke ajiyar zuciya yake a jajjere da taune lip ɗinsa na ƙasa. Richard kansa mamakin tsantsar salon makirci yake yi. Da ƙyar ya iya katse shirun nasu shi.
“Wato idan na fahimta wannan matar itace ta bata abinda ya haifar da matsalarnan ta sha. To amma ni abinda ban ganeba anan, inhar da magani ta saka a cikin lipton ɗin ai dolene Doctors su gani? Su kuma san maganine ya haifar da bleeding ɗin. Amma kuma sai saɓanin hakan ma ya biyo baya kowa result ɗinsa na fita da zancen ciki. Kaina ya kulle gaba ɗaya”.
Ita kanta Nu’aymah kanta ya kulle ɗin. Yoohan kam baice komaiba dan zuciyarsa a wuya take natuƙa. Ganin yanda har yanzu Nu’aymah ke hawaye ya saka Rich cewa, “Brother kaje da ita ta samu nutsuwa. zuwa dare sai mu ƙarasa magana dan dole na juya Nigeria da wuri. Akwai maganar da nake son nayi da ku kuma zuwa anjima daman”.
Kai Yoohan ya jinjina masa kawai batare da yace komai ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button