SARAN BOYE COMPLETE

Bayan wucewar Rich sumbatar kan Aymah Yoohan yayi. A hankali yace, “Is ok. Kukan ya isa haka. Na miki alƙawarin insha ALLAH sai inda ƙarfina ya ƙare wajen amso miki haƙƙinki ga duk ma wanda keda hannu akan wannan al'amarin. Dan haka banason ganin hawayenki masu daraja na zuba akan azzalumai ok?”.
Kanta ta jinjina masa. Ya miƙe riƙe da ita suka koma cikin ɗakin. A kujera ya zauna ya zaunar da ita saman cinyarsa. Zamewa tai a hankali ta kwanta dan jikin nata bawani ƙarfi yake mataba har yanzun. Ɗankwalin kanta ya zame ya sumbaci sumar kanta daketa ƙamshin gyaran jiya har yanzun. Cikin raɗa-raɗa yace, “Sweet girl!”.
“Uhyim” ta faɗa kamar wadda barci ke shirin ɗauka.
Ya tura hannunsa a rigarta yana shafa cikinta. Idanunsa a lumshe yace, “Bani labarinki, ina nufin yanda kika rayuwu a gidanku, da yanda kowama yake rayuwa a gidan”.
Hannunta ta ɗora akan nasa dake shafa cikinta, sotake ta janye amma yaƙi yarda, sai ma jitai yayi sama da hannun. Ɗan zabura tayi da ɗaga kanta ta dubesa. Idanunsa a lumshe suke, sai dai yana kallonta. Hakan ya sakashi yin ɗan murmushi da ɗaga mata gira ɗaya.
Tace, “ALLAH saima na fasa”.
Ƙasa yay da hannun nasa yana cigaba da murmushinsa bai dai ce mata komaiba. Itama sai ta saki numfashi a hankali, dan gaba ɗaya wuyar datasha jiyace ke dawo mata a rai. Kaudata tai a zuciyartata ta fara bashi labari tundaga asalin kakansu Malam Hashim ɗan jibiya har kawo yanzun. Yakan mata tambaya akan inda bai fahimtaba tai masa ƙarin bayani. A haka lokacin sallar la’asar tayi suka tashi suka gabatar. Bayan sun idan yace ta shirya suɗan fita tunda yaga jikin nata da sauƙi.
Cike da ɗoki kuwa ta shirya. Sai da ta kammala yana fesa turare ta dubesa tana kumbura fuska. “Amma dai bada wannan jelan naka zamuba ko?”.
Turaren ya ajiye yazo gareta, fuskar dai babu walwala. Hancinta yaja da faɗin, Silly girl waye jelana?”.
“Wannan basamuden Solomon ɗin mana. I don’t trust him bansan miyasaba”.
Da mamaki yake kallonta, furicinta na masa yawo a zuciya. Yaɗan ranƙwafo ya sumbacin laɓɓanta da sukasha lipsgloss sunata walƙiya. “Sweet girl! Kinada rigima da yawa. Miye laifin Solo kuma?”.
“Oho, nidai kawai I don’t like him gaskiya”. Tai maganar da juya masa baya.
“Alright. let go”.
“Indai da shine fa bazaniba”.
“Trouble maker badashi ba ne” yay maganar yana raɓata ya wuce.
Bin bayansa tai tana ƙunƙunin mita. Bai dai juyoba duk da yanajinta. Amma sai da yaɗan murmusa. Haka suka fice abin sha’awa. Yau dai taxi suka shiga bai amshi motar hotel ɗinba dan garau yake jinsa da sabuwar lafiya ma.
ABUJA NIGERIA
A rayuwa madam Chioma zata iya cewa bata taɓa gamo da dare mafi tsayo irin na yau ba. Duk uwar giyar data kwankwaɗar ma cikinta a wannan dare baisa ta samu nutsuwar da take buƙata ba. Dan barcin kansa ma gagarar idanunta yayi. Ƙarfe huɗu na asuba na bugawa ta tashi tai wanka ta shirya duk da tana a cikin halin maye. Burinta kawai takwas tayi subar gidan dan jirginsu sai tara dai-dai zai tashi zuwa River state. Tana zaune wajen kallon agogo ta ɓingire barci. Hakan yama Madam Rebecca daɗi. Dan dama ta addabeta akan ta shirya. Sake kwanciyarta tayi tai barci, sai takwas ɗinma ta tashi tai wanka tai shiri. Tara saura kwata ta tada madam Chioma dake barci a kujera.
Da wani uban ihu ta tashi saboda ganin abinda agogo ya nuna.
“Hhheeyyyyy!!!! Heyyyy Jesus!!! Rebecca!.....”
Da sauri Madam Rebecca ta dakatar da ita ta hanyar cemata “Please muje nidai karmu makara”.
Da yake tafiyar itace mafi girman damuwarta sai tai gaba jiki na rawa dan da gaske barci takeji yanzun. Amma da zaman wannan barcin gara ta ganta a gaban bokanta.
Aiko sun kusan isa a makare, dan har an fara shiga jirgi. Anan madam Rebecca tabar motarta cikin airport ɗin ta riƙe Madam Chioma dake malangarin suka shiga suma. A cikin jirgin ma barci ta kamayi, koda suka iso kuma cikin mintuna ƙalilan sai da taimakon madam Rebecca ta fita. Taxi suka ɗauka ya kaisu can tashar da zasu hau motar kusa da ƙauyen. Nanma suka samu drop da ƙyar saboda rashin wadatuwar motocin............✍
Ga tsoron mutuwa ga son soyayya su o, e zafafa’s fan????????????????????????????.
BARKA DA JUMA’A????????????
Hafsat miss xoxo????
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).????????
Mamu gee????
MIN ƘALB!!????????
Hafsat rano????
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!????????
Safiyya huguma???? SIRAƊIN RAYUWA????????
Bilyn Abdull????
SARAN ƁOYE????????
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka????????????????
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????
09033181070
????????????????????????????????????????
TEAM—-ZAFAFA BIYAR????????????????LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana????????.
No. 64
…………Motar ta ajiyesu a wani ƙauyene dan iya nan kawai zata iya shiga saboda uwar zaizayar ƙasar dake damun ƴan kudancin ƙasarmu duk ta cinye titunan. Ruwa mai uban sanyi na kwatami madam Rebecca ta samu ta sheƙama madam Chioma saboda sunyi-sunyi ta fita a motar ita da drivern madam Chioma da giya ke aiki a kanta taƙi fita.
Firgigit ta kawo numfashi tana wani bada faɗi tamkar zata make mutum. Duk baya sukaja kam suka bata fili. Sai kuma ta sauke ajiyar zuciya ta share fuskarta tana hararsu.
“Rebecca minene haka kuma?”.
Dariya Rebecca tayi tana miƙama yaron data ari roba a wajensa. “Inda ba hakan nai mikiba zaki tashi ne. Lokacin da ya bamu ya kusa cika kuma kinsan halinsa”.
Zabura kuwa madam Chioma tayi ta wawuro handbag ɗinta tana ambaton Jesus. Haka yasa itama Madam Rebecca ɗaukar tata handbag ɗin suka zagaye zaftarewar ƙasar suka koma kan titi sosai. Suna tafiya suna ƙoƙarin tare mashin dake wucewa. Amma kowanne sai kaga da mutum. Sai da sukai tafiya mai nisan zango sannan suka samu mashin ɗaya. Badan zai ishesuba suka hau, dan madam Rebecca balaifi tanada jiki. Tafi madam Chioma ƙiba. Haka suka shirma cikin jejin da korayen ciyayi suka ƙawata suna nishin matsuwa. Tafiya sukai sosai kafin su isa wani ƙauye again. Anan mai mashin shima ya saukesu dan zasu hau kwale-kwale ne. Ga madam Chioma da tsoron ruwan masifa. Duk sanda sukazo wajen bokan nan a tsorace take. Shiyyasa wani lokacin tafi buƙatar Rebecca tazo mata sai ta biyata kuɗin da duk ta buƙata. Haka suka shiga kwale-kwale tanata faman ƙunshe kanta a cikin cinyoyi. Tafiyar mintuna ashirin ta kaisu gaɓar ruwan. Daga haka kuma suka kwashi ƙafafunsu suka nausa cikin jajenin da bazaka taɓa ɗauka akwai mutum mai numfashi a wajen ba. Amma da yake zukatansu sun bushe ko tsoro basaji. Sun iso ƙauyen da bokan yake a galabaice. Kamar yanda ƙa’idar shiga wajensa take suna isowa ƙofar fadarsa suka cire duka suturar jikinsu. Haka masu tsaron ƙofar suka basu hanya suka shiga tsirara haihuwar uwarsu (????????????). Ba wannan ne ya firgitaniba. Dan su nasan komaima iya aikatawa zasuyi. Shigarsu wajen ne ya rikita tunanina da ɗarsa tsoron duniya a raina. Dan kuwa mutanene cike da wajen suna jiran layi kowanne tsirara yake. Abin kaico da takaici da ALLAH wadai harda musulmai a wajen, kai harma Hausawa saika samu ma’abota son duniya da ruguza lahirarsu. Manyan mutane ƴan siyasa da hasashenka bai taɓa baka ganin irinsu a wajenba sai gasu tumɓur suna zazzare idanu a fadar boka. Manyan mata masu neman duniya da gudun kishiya suma gasu nan ba’a magana. Wannan ya ƙara tabbatar min da sutura na rufawa bawa asiri a idanun mutane. Dan da yawan mutane munana ne idan ka gansu tsirara wlhy????.
Sai da suka tsaya gaban wasu ƙartai akai musu wankan ƙa’ida kafin su ƙarasa su hau layi inda sauran suke. Suna nan zaune masu shiga na shiga suna fitowa har layi yaxo kansu suka shiga suma.
‘Wa’iyazubillah’. Ɗakin bokan cike yake da gumaka na dodannin tsafinsa ta kowace kusurwa. Suna shiga suka zube sukai sujida a gaban waɗanan gumaka. Kafin su miƙe zuwa wajen bokan dake hakimce a kujera sai kace sarki. Shima sujidar sukai masa sannan suka miƙe tsaye haihuwar tsoffinsu. Shima dai a tsirarar yake dama????????. Gashi ƙaton gaske mummuna baƙiƙƙirin matsiyacin sheɗani. Kallon madam Chioma yayi ya kece da dariya, sai da yayi mai isarsa sannan ya haɗe fuska.
“Yaron da kike tattali da burin mallaka yana neman ƙuɓuce miki ko? Hhhhhhhh!!!!. Ai tun farko kece kikai sakaci. Miyasa kika barsa yay aure?”.
Kuka ta fashe da shi, “Bangaruta ba laifina baneba. Mijina nane ya cikani da daɗin baki akan ya yarda yaron ya aureta ne dan ya halakata da babanta. Shiyyasa na yarda ni kuma. Tunda nasan ka bani abinda bazai iya taɓa kallon mace da suffar mata ba”.
“Hhhhhhh!!!!!. Yardarki kuwa ta zamar miki matsala. dan wannan yarinyar daya aura tafi ƙarfinki. A duk inda take tana zagaye da wani haske da ko iya ganinta ni kaina banayi. A yanzu haka bana iya ganin yaron ma kansa a ƙwaryar tsafina saboda kasancewarsu tare. Ke koma basa tare shima bana ganinsa a watannin nan gaba ɗaya…..”
“Bangaruta ka taimakeni ta tsafemin shi. Na shiga uku shikenan tawa ta ƙare”.
“Hhhhhhh taki zata ƙarene idan wannan aikin dazan miki yazam bai kamasu ba”.
Da sauri ta nutsu tana sharar hawaye. Ya kuna ƙyalƙyalewa da muguwar dariyarsa mara daɗin ji. Kamar yanda na faɗa miki tun farko aikinmu dake kansa bazai taɓa barinsa mu’amula da mataba sai ke. dan haka ki kwantar da hankalinki wannan kam tabbatacciyar maganace hakan bazai faruba. Yanzu zakiyi ƙoƙarin rabasa da yarinyarne kawai. gaba ɗaya hankalinsa zai dawo gareki a wannan karon dan bazamuyi masa da wasa ba”.
“Nagode Bangaruta, sai dai kumafa igiyar nan ta tukunya ta kwance, wannan shine ya girmama tashin hankalina”.
“Karki damu da kwancewarta, mu ta wajenmu tana nan a ɗaure. Dan bazai taɓa kwanciya da wata maceba sai ke. Cike dajin daɗi ta duƙe gabansa ta sakeyi sujida????????????. A take ya haɗa mata duk abinda zatayi akan Yoohan da Nu’aymah. Ta dire masa maƙudan kuɗin daya buƙata sannan suka fito bayan itama Rebecca ta amshi nata aka abinda ya shafeta.
A ranar suka sake juyiwa cikin River state a matuƙar galabaice. hotel suka kama zasu kwana sai zuwa da safe su koma abuja.



