SARAN BOYE COMPLETE

*_VIENNA AUSTRIA_*
Su Yoohan da basusan wainar da ake toyawa ba sunacan hankalinsu kwance. Dan wani shagon cin ƙwalam da maƙulashe na kalolon chocolate da ice-creem ya kaita. Ko sha zumamu baya faɗama Aymah shan zaƙi ba. Tako dinga lodama cikinta cike da farin ciki. Duk gargaɗin da yake mata akan tabi a sannu saboda duk zaƙin da take danƙara zai tambayetane a wajen period bata sauraresaba.
Sun daɗe sosai a wajen, kafin su fito da ƙafa kamar yanda ta buƙata wai tanason taga gari da ƙyau. Aiko ta gani ɗin. Dan birnin Vienna ya matuƙar haɗuwa da gine-gine masu ƙayatarwa. Sai da ta fara hakkin gajiya sannan ya tsaida musu keken doki suka shiga ya maidasu masaukinsu.
Suna isowa wanka Aymah ta shiga. Sai faman complain take wai ƙafafunta na ciwo. Baice mata komaiba shi dai tunda itace ta ja musu shan wahalar ai. Amma da yake ta fisa baki shine take cewa shine.
Wanka tayo ta fito tana ɗingisa ƙafa wai ciwo take mata. Da kallo kawai ya bita shi dai, ya ɗan girgiza kansa yana miƙewa da faɗin, Silly girl maganinki kenan ai”.
Juyowa tai tana hararsa. Sai dai shi baimasan tanayi ba dan tuni ya shige toilet ɗin abinsa. Koda ya fito ya iske har tayi shirin barci. Sai dai bata kwanta ba. Tana kwance a sofa tana kallo. Shirin barcin shima yayi. Yana kammalawa wayarsa tai Ring. Miƙewa tai zata kawo masa sai taga ya nufota. Hakan yasa ta koma ta zauna harya ƙaraso. Yana amsa yaga Rich ne, sai ya maida kallonsa gareta. “Please sa hijjab muje mu ƙarasa maganarnan yana jiranmu”.
“Okay” ta faɗa tana miƙewa. Ta ɗauki hijjabin sallarta ta saka tare da zura Slippers suka fito harabar hotel ɗin wajen swimming pool ɗin nan da mutane keta shanawarsu tamkar rana. Daga can gefen garden ɗin hotel ɗin suka koma. dan shima dai mutane ne keta hidimarsu. Aymah ta fahimci mutanen nan sam basa banbance dare da rana halan. Dan koda yaushe su dai hidimarsu suke hankali a kwance.
Zama sukai inda suka iske Richard. Ta gaishesa da ƴar sakewa fiye da ko yaushe. Shima fuskarsa da murmushi ya amsa mata harda tsokanar wai ta ƙwace masa aboki.
Murmushi tayi kawai batare datace komaiba. Shi dama Yoohan bai saka bakinsa ba, sai dai ya bama Rich ɗin hannu sun gaisa.
Bayan an kawo musu Coffee ɗin da yay musu order itama Aymah aka kawo mata lipton data buƙata sai suka fara tattaunawa akan yanda zasu ɓulloma lamarin. Suna gamawa da maganar gidansu Aymah Rich ya turama Joseph saƙo akan ya janye masa hankalin Yoohan.
Haka kuwa akayi, ko mintuna biyu da tura saƙon ba'ayiba kira ya shigo wayar Yoohan. Ɗagawa yay suka gaisa da Joseph batare da ya tashi ba. Sai daga baya kuma ya miƙe saboda magana da Joseph ɗin yace yanason suyi.
Yana barin wajen Rich ya kalli Aymah data ɗauke kanta daga garesu tana kallon wata mata da yaranta twins da babansu dake gefensu. Sai soyayyarsu suke zubawa da tattalin ƴan yaran nasu. jitai sun bata sha'awa sosai har tana kwatanta kanta da Yoohan ace yaran nasune wai (ƴar baba malam an fara hankali kenan????).
Gyaran murya da Rich yayine ya sakata juyiwa taɗan kallesa. murmushi yayi shima dan haka kawai yay zargin abinda take tunani akan mata da mijin da yaransu.
“Inason muyi magana Please, sai dai tsakanina da ke ne banason Yoohan ya sani”.
Cike da mamaki ta tsura masa idanun tana tsuke fuska. Saurin girgiza mata kai yayi yana murmushi. “Am sorry sister akan gidansu ne karki zargi komai”.
Ajiyar zuciya ta sauke a ɓoye da ɗan shafa gefen wuyanta alamun taji kunya. Shima sai ya ƙara murmusawa dan ta birgesa. Hakan na nufin a duk inda take zata karema ɗan uwansa mutuncinsa. Wayarsa ya miƙa mata tare da miƙewa yabar wajen. Can ya koma inda Yoohan ke zaune yana waya dan ya fahimci shima hankalinsa na kansu.
Binsa da kallo Nu'aymah tayi. sai kuma ta buɗe video ɗin data gani akan wayar, da alama shi Rich ɗin ke buƙatar ta gani. Ba ƙaramin bugawa ƙirjinta yayi ba, saboda cinkaro da kanta a ranar data shiga ɗakin papa ta ɗakko hoto. Sai dai iya falone. har shigowar Papa da Andrew falon. Shigarsa bedroom ɗin da fitowarsa da sake komawarsa. Harma fitarta da kayan harƙallar papa da suke magana akai shi da Andrew. Cocaine ce da wasu ƙwayoyi, sai abinda ke cikin ɗayar jikkar dai bai buɗeba, hakan yasa batasan minene ba. Hannu tasa ta sharce zufar data tarar mata a goshi. Ta ƙara playing ɗayan video ɗin dake a ƙasan wancan shima. Shi kuma papa ne da wasu mutane yana bada kwangilar a kasheta duk sanda suka dawo Nigeria. Randa aka kashetan kuma a kashe baba malam shima. ‘Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un’ ta shiga maimaitawa tana kallon inda Yoohan da Rich suke zaune. Ganin Rich nata jan ra'ayinsa ga barin kallontane ya sakata kauda kanta tana taunar lip ɗinta. A ranta kuwa sake jinjina lamarin papa take da jin tsanarsa a ranta. Lallai saita tona dukkan sauran sirrin mutumin nan duk da kasancewarsa mahaifin mijinta. To amma shi wannan Richard ɗin mi yake nufi da bata video ɗin ta gani?.
Kafin ta nemo amsar tambayarta taga sun miƙe sun nufota. Fita tai daga cikin folder ɗin da sauri ta ajiye masa wayarsa da ƙoƙarin control ɗin kanta dan kar Yoohan ya gane.
Rungumeta Yoohan yayi cike da tsantsar farin ciki yana faɗin, “Oh my Sweetheart ke haske ce a rayuwarmu. Rich yace yanason zama musulmi”.
Cike da razana Aymah tace, “What?!!”. Sakinta Yoohan ɗin yayi yana dariyar farin ciki da jinjina mata kansa. kafin yace wani abu Rich yace, “Tabbas abinda X-man ya faɗa ashine gaskiya Sister. Zama da mahaifinki ya ƙwaɗaitamin son kasancewa musulmi. Hakan ya ƙara tasiri ne a raina a ɗazun dana ganku kuna salla abin ya birgeni”.
Kallonsa kawai Nu'aymah take cike da tuhuma. Dan gani take wani ƙullinne kuma yake shirin musu ta hanyar shiga musilinci.
Fahimtar hakan da yayine ya sakashi girgiza mata kai idanunsa na kawo ruwan ƙwalla. “Na rantse da ALLAH ni Richard inason shiga musilinci ne da zuciya ɗaya bada wani daliliba. Ki yarda ke haske ce a garemu kamar yanda mijinki ya faɗa”.
Numfashi Aymah ta sauke tare da furzar da iska ta lumshe idanunta hawaye suka gangaro mata a hankali. Sai kawai ta faɗa jikin Yoohan ta rungumesa tare da rushewa da kuka. “I love you so much Yah Yoohan”. Ta faɗa a bazata tana ƙanƙamesa da ƙyau.
Da sauri Yoohan ya ɗagota yana kallon fuskarta. “Cikin rawar muryar zuwan bazatan maganar yace, “Really? Please sake faɗa naji dan ALLAH”.
“Babu ƙarya ko yaudara a maganata. Da gaske ina SONKA Yah Yoohan. Na rantse da ALLAH ina sonka da gaba ɗaya zuciyata”. Ta kuma rungumesa.
Ai gaba ɗaya yama manta da wani Rich dake wajen. cikin sauri yaja hijjab ɗin jikinta ya shige ciki tare da zame mata fuskarta itama ta koma ciki. lalubar bakinta yayi ya manne da nashi. Duk da kunya da tsoron abinda ya faru dake cikin ranta hakan bai hanata tayasa abinda yakeyiba batare da tasan ta zurma ba.
Dariya Rich ya sanya musu tare da miƙewa yabar wajen, can inda suka baro da Yoohan ya koma ya zauna yana kallon wani wajen daban, zuciyarsa fal da wani irin farin ciki da shi kansa baisan na minene ba.
Da ƙyar Nu'aymah ta ƙwaci kanta daga hannun Yoohan da ke neman sakin layi. Ta sauka daga jikinsa tare tabar wajen da gudu. Kasa motsawa yay saboda kasala data saukar masa. Ya kife kansa a table ɗin kawai yana sauke numfarfashi a jajjere.
Ganin wucewarta da gudu ya saka Rich tasowa inda Yoohan yake. Damtsen hannunsa yaɗan buga da faɗin, “Mara mutunci, a gabana ma babu ɗaga ƙafa”.
Gani kawai yayi Yoohan ɗin ya miƙe ya rungumesa yana faɗin, “Thanks you Rich, thanks you so very much. Gashi a dalilin gane gaskiyarka ta faɗamin kalma mai tsada dana fidda ran samu daga gareta. Wlhy ina sonta fiye da zaton mai hasashe Rich. ashe itama zata soni. ALLAH na gode maka. Rich ka zama sanadin farin cikina”.
Dariya sosai Rich keyi ta jin daɗin ganin farin cikin Yoohan ɗinsa da yake tsananin so da ƙauna. Suka zauna kowanne fuska ɗauke da murmushi. Cikin ɗage gira Rich yace, “Dama makauniyar soyayya kakeyi kai ashe?”.
“Makauniyar da ko idanu ba'a yanka mataba kuwa Rich, amma yanzu ta sanadinka gashi har numfashi ta samu”.
“To Alhmdllh, dama ni na fahimci tana sonka wlhy. Kawai dai akwai yarinta tattare da itane. But ko dai yayane ma kun dace. Dan na jima banga masoyan da suka dace da junaba irin ku. Dan haka Mr Lover Congratulations joooh”.
“Thanks you dear. Congratulations too. Nayi farin ciki da kai saurin gane gaskiya. Ya rabbi ka karɓi tubanmu ka gafarta mana”.
“Emen dear. Yanzu nawane zan biya? A wajenwa kuma zan biya”.
Fuska Yoohan faɗaɗe da murmushi yace, “Shi muslinci ba'a biyan komai a wajen shigarsa. Kalmar shahada kawai zaka faɗa. Amma bara na kira Uncle first”.
Kai Rich ya jinjinama Yoohan. Ya ɗauka wayarsa yay kiran baba malam cikin sa'a kuwa ya ɗaga. Bayan sun gaisa yay masa bayanin komai cike da jin kunyar da Aymah ta sakashi a ciki tun ɗazun. Dan duk yau ma ya kasa kiran baba malam ɗin. Yanzun ma shaf ya mantane saboda ɗokin musulintar Richard.
A take baba malam yace, “Ina mamana? Duk bayanin dazan muku itama zata iya yinsa insha ALLAHU Yahya”.
Cike da jin kunya Yoohan yace, “Tayi barcine Uncle. Gashi kuma Rich ɗin zai dawo gida nan 9ja gobe. Idan kuma ya bari sai yazo wajenka to”.
“A'a Yahya. Gara dai ya cikasa niyyarsa dan ranmu ai ba'a hannunmu yakeba. Nasan kaima zaka iya masa bayani akai. indai zaka iya tuna duk yanda kayi lokacin daka musulinta”.
“Insha ALLAH Uncle. Amma zanso kana saurarenmu”.
Dama baba malam ya bashi. Dan haka Yoohan ya maida kiran video call. A take Yoohan ya bama Rich kalmar shahada. Bayan ya maimaita baba malam ya faɗaɗa masa bayanai masu muhimmanci tamkar yanda yayma Yoohan a wancan karon. Sai ga Yoohan da Rich suna hawaye. Sunja lokaci mai tsaho kafin baba bashi zaɓin suna. A take Rich yace ya bashi dama ya zaɓa masa kowanne.
Cikin jin daɗi Baba malam yace, “Akwai sahabban manzon ALLAH da sunayensu sukai fice a garemu, bara na lissafa makasu, tare da na Annabawan ALLAH da Yahya ya samu ɗaya daga cikin sunayensu shima”.
A tare suka jinjina masa kai.
“Abubakar, Umar, Usman, Aliy…….”
Kafinma baba malam ya ƙarasa Rich yay saurin faɗin, “Uncle inason Omar”.
“Masha ALLAHU Son. Daga yau kazama Umar. ALLAH yasa ka zama mai koyi da ƙyawawan halayen Umar da gaskiyarsa da jarumtarsa harma da yawan ibada”.
A tare suka amsa da amin.
Daga haka suka sake ɗan tattaunawa sannan sukai sallama da shi. Masaukin Rich suka nufa. Inda Yoohan ya koya masa wanka da alwala harma da salla. Daga haka ya barsa. Saboda gobe idan ALLAH ya kaimu Omar (Rich) ɗin zai koma Nigeria.
Sun sake rungume juna suna hawaye da sake godema UBANGIJI. Sannan sukai nafila raka’a biyu a tare ta godiya ga ALLAH. Omar (Rich) yay sallar Magrib da isha’i dan lokacinsu bai gushe ba har sai alfijir ya keto. Musamman ma isha’i.
Daga haka sukai sallama Yoohan ya nufi nasu masaukin cike da ɗoki da farin ciki.
Nu'aymah dake kallo tanajin motsin buɗe ƙofar tai azamar kifewa rubda ciki dajan filo ta tura kanta ciki. Murmushi yayi yana ƙarasa shigowa dan ya rigada ya ganta. Television ɗin ya kashe tare da wutar ɗakin lokacin da yake ƙoƙarin hawa gadon. Cikin nutsuwarsa ya kwanto bayanta yana sauke ajiyar zuciya tare da saka hannu ya ɗauke filon data tura kanta a ciki.
“Wayyo Hajjo ƙaton nan zai ɓalla miki jika”. Tai maganar cike da rikicin kunya da nauyinsa daya sakar mata.
Murmushi yayi da rage mata nauyinsa sannan ya birkitota. Da sauri ta kanannaɗe masa jiki dan batason su haɗa ido.
Hannunsa ya tura cikin rigarta yana ɗora bakinsa akan kunnenta. Cikin raɗa yace, “I love kunyankin nan my sweet angel, my sweetheart my Heartbeat. My everything”. Ya ƙare maganar da ɗan cizar kunnenta kaɗan.
Kukan shagwaɓa ta saka mata tana murza ƙafafunta a jikinsa wai saita rama. yanda taketa masa mutsu-mutsu a jikine ya nema susutashi. ƙwaɗayin da yaketa dannewa tun da rana ya kasa dannuwa. Cike da kasala da tsumar jiki ya lalubi bakinta ya manne da nashi. Tun yana tunanin tsayawa iya kiss ya rage zafi har hakan ya nema fin ƙarfin ƙoƙarin nasa. Gaba ɗaya ya birkice mata. Tun tana biye masa da wauta harta koma masa kuka dan bata manta wahalar datasha daren jiyaba.
Duk yanda Yoohan yaso haƙuri ya bar Nu'aymah hakan ya gagara. cike da fita hayyaci ya fara sarrafata. Yau ma dai an maimaita na daren jiya, sai dai kukanta ya sakashi taƙaita tafiyar batai nisan zango kamar ta daren jiya ba ya tausaya mata dan yasan bata gama dawowa hayyacinta ba.
A take kuwa jikinta ya ɗime da zazzaɓin wahala. Hardasu rawar sanyi. Yasan ya ƙara laifi mai girma. Dan haka yayta lallashi da ban haƙuri harya samu ya kimtsa mata jiki yau ma yay gashi dan yasan zataji ciwo a wajen balle gashi yayi fami ne.
Da taimakonsa tayi wankan tsarki, shima yayo sannan ya taimaka mata suka fito. Lallaɓata yay tasha yogurt da maganinta, kafin ya ƙara mata shirin barci. Sai da ya sake kimtsawa shima sannan ya hawo gadon ya rungumeta dan harma ta fara barci. Irin allurar ɗazun da rana ta rage raɗaɗi yay mata. Kuka ta fasa masa jikinta na matuƙar rawa. Yay saurin haɗe bakinsu waje guda. Sai da ya janye allurar sannan ya janye bakin yana furzar da iska tare da rungumeta da ƙyau a jikinsa yana shafa bayanta da faɗin, “Am so sorry sweetheart. Please forgive me”.
Luf tayi a jikinsa tana zirar da hawayen. A haka barci yay gaba da ita yana faɗa mata kalamai masu sanyi cikin kunne da hura mata iska mai daɗi. Jin ta fara sauke numfashi na alamar barci shima saiya shiga sauke ajiyar zuciya a jajjere. Yana ƙara jin ƙaunarta mai tsanani tana ratsa masa zuciya da dukan jikin sama gaba ɗaya. Ta zama ta farko a zuciyarsa. Ta farko a sirrinsa. Ta farkon haskama rayuwarsa hanya. Ta farko.... Ta farko.... Da yawa harma baisan iyakaba. Insha ALLAH kuma itace zata zama ta farko har ƙarshen rayuwa????????.
Muma ALLAH yasa mu zama na farko ta ƙyawawan hanyoyi ga mazajenmu har ƙarshen rayuwa my dear fans. Ba dole sai kin kasance matar farko ba zaki zama ta farko????????. Kota huɗu kikaje ƙyawawan halayenki zaisa ki zama ta farko????. Uwar gida kema dage ki riƙe gam kar a ƙwace miki ta farko????????????.
Washe gari haka Nu'aymah taita zubama Yoohan shagwaɓa da raki yana faman lallaɓata da lallashinta. Tasa dole ya kira mata baba malam da Umm da hajjo. Inda anan itama hajjon ta fahimci takwararta ta kai mutuncinta gidan aurenta. Hakan ya mata matuƙar daɗi harta kaita da yin sujidar godiya ga ALLAH. Cike da tsantsar alfahari da jin daɗi ta kira Ananah ta sanar mata. Sosai Ananah taji daɗi tana godema ALLAH daya wanke Aymah cikin sauƙi a garesu bisa hikimarsa da rahamarsa. Daga haka sukai gum da bakinsu suna jiran bayyanar gaskiyar ga kowama cikin hikimar UBANGIJIN al'arshi.
Da ƙyar Yoohan ya samu yaje sukai sallama da Omar (Richard) da zai wuce Nigeria a yau. Daga haka ya dawo wajen ƴar amaryarsa sarkin shagwaɓa da shiririta. Haka suka kasance a gaba ɗaya wannan yinin cike da so da ƙauna. Dan itama tun tana nokewa da ƙunshe-kunshe harta saki jikinta duk da dai akwai kunyar tattare da ita, saboda ta kasance tarbiyyarta tun fil'azal...........✍
Hafsat miss xoxo????
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).????????
Mamu gee????
MIN ƘALB!!????????
Hafsat rano????
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!????????
Safiyya huguma???? SIRAƊIN RAYUWA????????
Bilyn Abdull????
SARAN ƁOYE????????
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka????????????????
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????
09033181070
????????????????????????????????????????
TEAM—-ZAFAFA BIYAR????????????????LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana????????.
No. 65
…………..A hankali soyayya da shaƙuwa mai ƙarfi ta cigaba da shiga tsakanin ma’auratan masu banbancin yare da yanki cike da birgewa. Yayinda Aymah ke matsayin malama ga Yoohan a ɓangaren ilimin addini shima sai ya zame mata malami a ɓangaren sanin soyayya da rayuwa. Dan sosai yake yawo da ita a lungu da saƙo na ƙasar Austria har wasu jihohinma suna zuwa yawon buɗe ido.
Tun tana tsoro da masa raki a shimfiɗa harta fara sakin jikinta da sabawa. Dan jarumin nata namijin gaskene babu wasa. Baya takura mata yanda zata wahala. ba kuma ya barinta ta shagala.
Sai ga Nu’aymah tai wani irin murjewa da ƙibarta na dawowa, (kunsanfa wannan harkar na gyara wasu matan harma da mazan????, shiyyasa da yawa amare farkon aurensu zakaga sunyi ɓulɓul da su????). To ga Nu’aymah ma dai an dace. Balle abin ya haɗa da kwanciyar hankali data samu, babu mai hantararta babu mai damun rayuwarta. Abinci saita zaɓa. Kullum zatai waya ko video call dasu Umm. Ga lafiyar jikinta Alhmdllh sai ƙaruwa take ƙarayi dan tana shan maganinta da ƙa’ida kasancewar Yoohan tsaye yake akanta da tsantsar kulawa.
Takanji yana waya da papansa da momynsa (Madam Chioma) sai dai yanda bai taɓa cewa gashi su gaisaba itama bata taɓa nuna sha’awar hakanba. Garama Momy ranar ta kira yana wanka har sau uku. Ganin wayar na wajenta ya sakata ɗagawa suka gaisa. Sai dai yanda Momyn ta amsa mata a daƙile ya sosa ranta. Dan ta fahimci har yanzu da sukai nesa da juna ba ƙaunarta takeyiba. Su Momy Destiny ne dai ta gaisa dasu kusan sau uku-uku harda su Victoria. Amma su tom and jarry mama debora ko yaya jiki basu taɓa aiko mata da shiba balle suce zasu gaisa da ita a waya. kuma taji ranar duk sai da suka gaisa da Yoohan. Gebrail nema ta lura idan ya kirashi baya ɗagawa, daga bayama sai taga ya sakashi a black list.
Gaba ɗaya ta hana Solomon musu gadi. Dan yanzu duk inda zasuje tuburewa take akan itadai bazataba inhar sai Solomon ɗin ya bisu. Hakan yasa Yoohan ya yanke shawarar kawai ya sallamesa ya koma Nigeria, dan baiga amfanin kisan kuɗin da yake ba a dalilin zaman Solomon ɗin tare da su.
Randa ya samu Solomon da maganar komawa Nigeria hankalinsa yayi matuƙar tashi. Ya kira iyayen gidansa ya sanar musu da hukuncin Yoohan ɗin. Hakan yasa papa kiran Yoohan ya nuna masa bai amince da dawowar Solomon gidaba. Dan bazai yarda ya barshi shi kaɗai yana yawo ƙasashen duniya a cutar masa da shi ba.
Yanda Aymah ta tubure kuma akan indai Solomon zai cigaba da kasancewa da su sai dai ita ta koma Nigeria wlhy yasa kan Yoohan ɗaukar zafi. Yayima Aymah lallashin duniya akan tabar zancen Solomon tunda papa ya dage amma sam taƙi saurarensa. har takaisu dayin ɓacin rai ranar akai barci kowa na ƙarshen gado. Washe garima taƙi kulasa shima ya shareta. Sai daga baya yaso su shirya taƙi. (A raina nace hummm Yoohan bakasan kafiyar Aymah bane ba).
Wannan tuburewar tata ya ƙara bashi haushi. Harya yanke shawaran ta shirya ta koma Nigeria tunda bazataji lallashinsa ba.
A mamakinsa kuwa sai yaga ta hau haɗa kayanta. Dan itafa tabbas tayi alƙawarin bazata sake zama inuwa ɗaya da Solomon ba. Dan tsaf ta gama fahintar wannan nanema Yoohan ɗin da yakeyi akwai wata a ƙasa. tabbas da gaske akwai abinda su papa suke ɓoyewa game da Yoohan ɗin. Inba hakaba minene na nana masa guard a duk inda yake. Sannan sau biyu tana kama Solomon na waya da papa. Na farko yare taji yanayi sai turancin daya saka kaɗan ya sakata fahimtar papa ne. na biyu kuwa da turanci sukai magana. Hakan ya sata jin komai akan duk wani motsinsu Solomon yana sanarma papa. Dan a ranar shi papan har maganar ya kamata ta koma Nigeria yayma Yoohan. Amma shi Yoohan ɗin ya nuna baya bukatar yana wani ƙasa matarsa na wata ƙasa. A ransa kuwa ya ɗau alwashin Aymah bazata ƙara zama a gidanba baya kusa saboda Gebrail. Dan ba ƙyalesa yayiba. ya ɗau alwashin duk randa ya dira Nigeria sai Gebrail ya yabama aya zaƙinta.
Ganin da gaske shirin tafiyar take ya sakashi sakkowa daga fushinsa shi. Ya fara lallashinta amma taƙi saurarensa. Saima kuka da take masa mai cin rai. Daga ƙarshe dai dole ya kira baba malam akan dan ALLAH ya lallasar masa ita. Dan shikam a yaune ya kuma tabbatar da borin Aymah bana wasa bane. Dan ko abinci taƙi ci, taƙi shan maganinta. ta birkice masa ita kawai ya kaita airport ta wuce gida kokuma ta tafi da kanta.
Murmushi baba malam yayi kawai yana girgiza kansa. kafin ya sauke ajiyar zuciya ya farama Yoohan nasiha. Daga ƙarshe ya koma masa faɗa akan sakacinsane ai ya saka Nu'aymahn iya bijirema umarninsa. Dan haka ya nutsu sosai wajen riƙe gidansa da ƙyau. dan su mata wani lokacin zuma ne sai da wuta. Sannan wutar kara ne sai da iji. Ba'a sakaci da su sannan ba'a musu tsauri da yawa. ana riƙesune tsaka tsaki sai a samu jin daɗin duniya.
Sosai Yoohan yaji shawarar sirikin nasa. tare da ƙarajin ƙaunarsa a cikin zuciya da ɓargo. Daga haka ya haɗashi da Nu'aymah kamar yanda ya buƙata.
Zata fara masa kuka baba malam yay mata jan ido. faɗa sosai yay mata akan tashiga hankalinta mijinta ba abin rainawarta bane. Idan batai wasabama sai yazo har Austria ɗin ya hukuntata. Sai da ya tabbatar tayi laushi sosai da faɗansa sannan ya koma yimata nasiha. Daga baya kuma ya buƙaci jin dalilinta na takurawa akan Solomon ya barsu.
Kasancewar Yoohan yana koyon hausa a wajenta ya sakata yin amfani da manya-manyan hausa wajen yima baba malam bayani akan abinda ta fahimta da zaman Solomon tare da su. Ta kuma bashi labarin abinda ya faru akan maganar hoto, harma da videos ɗin da Omar (Richard) ya nuna mata kwanakin baya da suka shuɗe. shi kansa baba malam ɗin hankalinsa yayi matuƙar tashi. sannan zarginsa ya fara zama gaskiya kenan. Albarka ya saka mata sosai da faɗan rashin sanar masa zance hoton da tayi tun a wancan lokacin. Duk da ya fahimci mijinta take son bama kariya akan matsalar da gajeren tunaninta ya kasa faɗaɗa mata. Yace,
“Mamana yanzu ina hoton yake?”.
Hawayenta ta share da jan majina. Tace, “Abba yana nan Nigeria a cikin kayana”.
“Masha ALLAH. ALLAH yay miki albarka. Saka wani ya ɗakkosa bazai yuwuba. Dan haka zamuyi haƙuri har ku dawo ƙasar sannan musan ta inda zamu ɓuloma al’amarin. Batun Solomon kuma bata hanyar rikici zaki yakicesa a jikin mijinki ba. Cikin hikima da wayon da ALLAH ya baku na mata da tarbiyyar Umm ɗinki zakiyi amfani wajen sakashi ya sallamosa. Ko kin taɓa ganin muna rikici da Umm ɗinki ne a gidannan?”.
Kanta ta girgiza masa tamkar tana a gabansa. Sannan tace, “A’a Abba”.
“To amma shine ke zakije kina rikici da mijinki. har yana taroki kina ƙwacewa? Wannan shashanci ne ai. Sannan kina zubar mana da kimar tarbiyyar da muka baki. Mu mazafa da kike gani munada wuyar sha’ani dason nuna mulki a gidajenmu, shiyyasa duk macen data fahimci haka ta iya zama damu mutane suke ganin kamar ta mallake mijintane nanko ba haka baneba. juriyace kawai da iya zama da mijin tayi. Ki kula da ƙyau. Mahaifiyarki abin koyice a gareki akan zaman takewar aure. Babu wanda zaice ga Jannat da wata matsala a gidan aurenta. da daɗi babu daɗi ta jure ta shanye komai. Yaya muka kwana yaya muka tashi ta jurema ranta. har takai wasu na ganin tsorona takeji da yawa. Nanko ba hakan bane. Mune muka san sirrin kammmu fiye da duk wanda ke zagaye damu. Karna ƙarajin haka kinji ko?”.
Nu’aymah na sharar ƙwalla tace, “Insha ALLAHU Abba bazaka sake jiba”.
“To Alhmdllh naji daɗin hakan kuwa. ALLAH yay miki albarka keda mijinki damu baki ɗaya”.
Cike dajin kunya ta amsa da amin. Daga haka suka ajiye wayar. Ta ɗan saci kallon Yoohan dake kwance ciki sofa idanunsa a lumshe tamkar mai barci. Tashi tai a hankali taje ta ajiye masa wayarsa a saman ciki batare datace komaiba.
Shima buɗe idanu kawai yayi ya bita da kallo harta shige toilet.
_★★
Batare da tasan yaya zancen Solomon ya kasanceba washe garin da suke cika sati biyu. ta kama randa zasu bar ƙasar kenan. Bayan sun kammala shirinsu tsaf sukaje asibiti aka ƙara tabbatar da ingancin lafiyarta, sukai sallama da su Dr Sophia kuma. Yoohan ya ƙara siya mata sauran magungunanta suka nufi airport cike da kewar ƙasar Austria da garin Vienna. Harma da mutanen cikinsa.
Yanzunma suna nane da jelar tasu Solomon. Sai dai kuma suna zuwa Airport ta fahimci Solo Nigeria ya nufa. ita da shi kuwa U.S zasu wuce dan Yoohan ya koma hutu. Zai kuma gudar da wani aiki a ƙasar United states ɗin, da wani taron manyan likitoci da zasuyi kuma insha ALLAH.
Duk da basu shiryaba har yanzun ita da shi sai da ya ga farin cikin komawar Solomon 9ja a fuskarta. Shidai hakan na bashi mamaki. dan ya gaza fahimtar ƙiyayyar dake tsakanita da Solomon. Shi kansa Solo ɗin ya kula baison Aymah. Sai dai baya iya nunawa a gabansa saboda shakkarsa da yakeyi. shi kuma bai taɓa nuna masa ya fahimta ɗinba dan yanason aje inda zai taka masa birki akan matarsa.
Shi kansa Solomon sai da sukaje airport ya fahimci Nigeria zai komai. Gashi babu damar kiran papa ko madam Chioma dan suna a tare. Sai dai zuciyarsa na ƙara jin zafin Nu'aymah. Dan ransa ya basa itace sanadin komawar tasa tabbas. Musamman da yaga yanda taketa faman moso. Dan ya fahimci kwana biyun nan daga ita har ogan suna cikin rikicine ko damuwa oho bai gama tabbatarwaba dai.
Jirgin su Solomon ne ya fara tashi zuwa Dubai. daga can zai hau Jirgin Nigeria. Ya tafi cike da alkairin da Yoohan yay masa da takaicin Nu'aymah da tsana mai tsanani. Dan shi baimasan ina zasujeba a yanzu haka. Solomon na wucewa da kamar mintuna ashirin da biyar suma nasu jirgin ya ɗaga zuwa U.S. yana ta wajen Window tana gefensa a cikin jirgin. Sai dai ya ɗauke fuska a binsa gashi ya ɗaureta tamau. Daga ƙarshema saiya kunna lap-top da liƙa earpiece a kunne ya hau kallon film. Duk da ran Nu'aymah ya sosu saita fuske tai kamar bama tasan da zamansa a wajenba. Koda akazo tambayarsu mi zasuci catai bata buƙatar komai. Shi kuma yasa aka kawo masa coffee da biscuits.
Lokacin da jirginsu ya sauka a U.S Nu'aymah barci takeyi. Hakan yasaka Yoohan shafa mata fuska. Sai dai tana buɗe ido ya ɗauke kansa tamkar bashine ya aikataba. Itama duk da ta fahimci shine ya tadata sai ta watsar da shi ta basar. Handbag ɗinta ƴar ƙarama kawai ta ɗauka tai gaba. Shi kuma ya jawo trolly ɗinsu sai lap-top bag ɗinsa a hannu. Yana biye da ita a baya. Sai dai da suka sakko dole ita ta koma bayan nasa dan ba sanin hanya tayiba. Da wannan damar ta ware ido tana kallon airport ɗin daya amsa sunansa airport. Sai dai ta haɗiye mamakinta a rai wai kar Yoohan ya rainata da ƙauyanci????.
Taxi ya ɗauka musu drop. Koda suka shiga nanma dai kanta naga Window tana kallon birnin da mutanen cikinsa. Daga haka suka isa wani haɗaɗɗen gida daya amsa sunansa gida. A tunaninta gidan nasa ne. sai dai batasan haya ya kama musu ba dan a yanzun baya buƙatar zaman hotel ɗin da ita. sannan yanason barinta anan U.S ɗinne dan yasan bazai yuwu yayta gantali da ita duk inda yakeba. Inba wajen daya san zai iya yin sati biyu kwana goma ko sama da haka ba. Amma kamar tafiyar kwana uku ko biyu zuwa sati ɗaya zai iya barinta yaje ya dawo. Inba dai buƙatar tafiya da ita taga duniya tasa suje tareba.
Komai da zasu buƙata na gida akwaisa a cikin gidan. Shopping ɗin abinci kawai zasuje suyi da kansu saiko suturar sakawa da sukazo da kayansu. Harga ALLAH gidan ya matuƙar burge Aymah harta kasa ɓoye shauƙin hakan a zahiri.
Duk da yaji daɗin yanda tai farin ciki sai ya basar bai nuna mataba. Ya fara shiga ko'ina ya duba gidan da ƙyau. Sai da ya tabbatar komai ya masa yanda yake buƙata tamkar yanda ya gani a yanar gizo daya kama gidan sannan ya shiga wanka.
Yana fitowa Nu'aymah dake kwance a gado ta miƙe itama ta shiga dan wankan take buƙata itama saboda gajiya. Koda ta fito zaune ta samesa a bakin gadon yana musu order ɗin abincin ta wayar landline. Da alama dai gidan abincin yana kusa da sune, kokuma yanada alaƙa da masu gidan abincin dama can.
Sai gashi kafin ta gama kimtsawa tai sallar magriba da lokacinta ya shiga an kawo abincin. Shine ya fita ya amso. Sai dai bai dawo bedroom ɗinba yay zamansa a falo. Sallama acan yay abinsa.
Wani mahaukacin yunwa Aymah takeji. Hakan yasa bayan ta idar da salla ko hijjab bata cireba ta biyosa falon. Dan bazata iya basar da cikintaba ta halaka a banza a wofi. Turus tayi tana binsa da kallon mamakin ganin yanda ya baje yana ɗora abinci a cikinsa. Ta kumbura baki ƙwalla na cika mata idanu. Cike da fushin data koya kwana biyun nan ta juya zata koma bedroom ɗin. Sai dai kuma caraf taji an riƙi mata hannu. Ƙoƙarin fisgewa ta farayi hawayen da take riƙewa na zubo mata a guje saman kumatu.
Ɗaukarta yay gaba ɗayanta ya dawo da ita a falon. duk yanda take watsal-watsal da faɗin ya sauketa bataso bai kulataba. Ya zauna cikin lallausar zagayayyar kujerar da aka ƙawata falon da ita kalar royal blue tana a jikinsa. Cikin hawayen da takeyi ta shiga kaimasa ƙananun duka a ƙirji da faɗin ita ya saketa bataso. Tunda yabar sonta yaje ta haƙura ta barma duniya dasu Miracle dake addabarsa da text massege kullum shi.
Zancen nata yaso bashi dariya. Dan haka ya lumshe idanunsa ya sake buɗewa akanta yana ƙoƙarin riƙe hannayenta da take kaimasa duka a ƙirji. A ransa kuwa yana sake jinjina rikicinta. Duk da ransa na raya masa wani abu game da saurin fushinta na kwana biyun nan. Sai dai bai tabbatarba dan ya san inma shine to ƙaramine kuwa sosai.
Bakinsu ya haɗe waje guda. Tun tana turesa harya samu nasarar maida mata jiki laƙwas ta fara bashi haɗin kai. Da ga ƙarshe ya ɗauki abarsa cak suka shige bedroom inda zaiyi lallashi ɗan gaske na zallar ƙauna da babu gaurayen algus a cikinta????. Saiga mutuniyarkun muna funfun dake faɗin zata barma duniya dasu Miracle tai luf kamar bata gidan????????.
(Su Aymah babu aji????????)
Sai da suka gama wadata juna da farin ciki yanda ya kamata. Yoohan ya kalli Aymah dake lafe a jikinsa idanu a lumshe alamar barcin nata na ƙa’ida zai ɗauketa. Dan duk sanda hakan ta kasance a tsakaninsu sai tayi wannan barcin. Shiyyasa yake kiranta raguwa.
Guntun murmushi yayi da lumshe idanunsa ya sake buɗewa a kanta tare da ja mata hanci. “Silly girl! Babu abinda ta iya sai jan mutane faɗa”.
Lumsassun idanunta da basu gama washewaba ta buɗe a kansa. Sai kuma ta tura masa baki tana maidawa ta rufe tare da tirza ƙafarta dake jikinsa tace, “Tab, kai wama ya kaika iya neman mutane faɗa”.
Sake jawo bargon data zazzame da ƙafa yayi ya lulluɓesu da ƙyau yana ƙara sakata jikinsa. “Nine ma mai neman faɗan kenan?”.
“Sosai ma. Tunda ai kaine dai kasa akayi wannan faɗan”.
Dariyar data bashi ce ta sakashin yin guntun murmushi. Ya sumbaci goshinta da laɓɓanta yana sauke ajiyar zuciya da lumshe idanu. “ALLAH na gode maka daka mallakamin ƴar rigimarnan tawa. Tare da mai ramamin gashinan yazo”.
“A ina?”.
Tai tambayar cikin yanayin barcin daya figeta.
“Mi kikeci na baka nazuba, zaki gani ai”. Ya faɗa yana miƙewa zaune da ita a jikinsa. Cike da shagwaɓa tace, “Ni wlhy barci nakeji”.
“To muje ayi wanka, sai kizo kiyi Sweet girl ɗin Yahya”.
Da taimakonsa sukaje akayo wankan. Dan barcin da bataiba na bayan lobewa ne cike da idanunta. Suna fitowa kuwa ta zube a gadon ta fara. Kayan barci ya ciro mata yazo bakin gadon ya zauna yana kallonta na tsayin mintuna uku. Hannunta ya kamo ya na kallon tafin, kafin ya juya ya tsurama yatsun idanu suma na kusan minti ɗaya. Ya miƙe inda ƙafafunta suke ya durƙusa a gaban gadon yana kallon yantsun suma na tsayin mintuna. Sassanyan murmushi ya sauke da ajiyar zuciya, ya sumbaci ƙafafun duka biyu sannan ya dawo kusa da ita ya zauna. Sake tsirama fuskarta ido yayi na tsahon wasu mintunan cike da so da ƙauna, kafin ya ranƙwafa kanta yana sumbatar bakinta da kumatunta, idanun har wuya. (Ni mai ɗauka muku rahotonma sai yaban dariya. Dan na kasa fahimtar inda ya dosa????????).
Kayan barcin ya sanya mata, ya gyara mata kwanciya, shikuma ya koma bayin ya ɗauro alwala ya dawo yay zaman karatun al-qur’ani. Dan tunda suka fara rigimarnan ta Solomon kota ɗora masa karatun ba fahimta yakeba da ƙyau. Haka yake kwata-kwata bayason damuwa. Koyaya irin haka ta faru da shi duk sai ya fita hayyacinsa. Ya jima yana duba al-qur’anin da sauran buks ɗin kafin ya miƙe zuwa fallo ya tattaro abincin da yaci ya rage dan yasan saita tashi cin abinci tunda yunwar takeji. Kwana biyun nan haka take, batama abinci sauƙi. Kodan jinyar da tasha ne oho. Sallaya ya hau ya kabbara sallar isha’i, bayan ya idan bai kwantaba ya ɗauki wayarsa da tun ɗazun yake ganin tana haske, ya tabbatar kuma kiransa akeyi dan a silent take.
Ilai kuwa missed calls ne na papa har guda takwas, sai na Momynsa biyar. Sai na Omar (Richard) biyu. Sauran kuma duk ba important bane a garesa dan haka baibi takansuba dan harda mayyarsa Miracle.
Kiran papa da Momy yasan bai wuce saukar Solomon Nigeria ba. Dan haka yay kiran Omar (Rich) kawai da shima yana Nigeria.
Sallama kawai Omar (Richard) ya amsa masa, ya shiga masa shaƙiyanci wai yanzu soyayya tasa sai ya gadama yake amsawa mutane kira a waya. Su G-boy ma jiya suka gama masa tsogumi a wajen birthday ɗin Osin da akayi a garin Lagos. Kai abokan suma da yawa sunyi wannan complain ɗin duk da dama sunsan shi Yoohan fa bai cika ɗaukar kiran da zuciyarsa ta raya masa mara amfani bane, saboda yanayin aikinsa da duk ya maidasa busy a gaba ɗayan rayuwarsa. Sai dai idan yana a cikin hutu da kansa yake bin abokan mu’amulat nashi masu muhimmanci ya kirasu su gaisa koda bazai zauna hira da kai ba. Musamman ma daya musulinta ɗin nan ya ƙara sanin darajar zuminci.
Murmushi kawai yayima Omar (Rich) ɗin da cewa “Humm ka samin ido da yawa”. Dariya kawai Omar yayi da ga can. Dan ya fahimci ƴan miskilancinne a kusa yau. Ajiye maganar wasan yayi suka fara tattaunawa kamar haka.
“X-man duk yanda muke tunanin aikinan bazai kasance mai sauƙiba. Amma dai na turo maka dukkan bayanan dake a hannuna yanzu ta Email ɗinka. Ni dai yanzu shawarar dana yanke, mizai hana mu sami wani amintaccen jami’in tsaro da zai taimaka mana akan case ɗin nan. Dan tabbas sai munyi kutse a cikin wayoyin mutanen gidan saboda fahimtar da nayi case ɗin babba ne dan yanada tushe”.
Ajiyar zuciya Yoohan ya sauke yana bin Nu’aymah da ta tashi zaune da kallo. Ya juya harshensa zuwa yare. “Tunaninka mai ƙyaune Omar. Inaga kuma babu wanda zai iya taimakonmu akan aikin nan sai Dawood, sai yay mana hanyar ganin bawan ALLAH nan dana taɓa baka labarin ya taɓa buƙatar na duba matarsa akan matsalar cancer ɗin mahaifa da sukai zargin tana da ita, sai dai hakan bata samuba a wacan karon sai haɗasu nai da wani likitan.. So dole zan shigo Nigeria kwanan nan, tunda kaga akwai aikin da zanzo nayima anan Lagos. Kuma shi mutumin babban jami’i ne zaifi dawood tsaya mana sosai”.
“To shikenan, sai mu bari sai kazo ɗin saimu tattauna, insha ALLAH madam ma zata dawo nextweek tunda kuna nan”.
“Idan kayi hakan kuwa zaka taimaka min, dan zaman Zeeynab a ƙasar nan yana buƙatar samun wanda zasu shaƙu. Inason samar mata admission ma ta fara karatunta insha ALLAH. Dan tanason karatu sosai na fahimta. Sannan tanada brain, sai dai shiriritanta yayi yawa wlhy”. Ya ƙare maganar yana satar kallonta, dan tana zaune ne tana cin abincin da yunwa ta hanata barcin nata yay tsaho.
Dariya Omar yayi daga can yana faɗin, “Ai da sauranta ne. 18years fa. bandama hausawan nan babu ruwansu ina ƴar 18years ina aure. Sai dai kuma yanzu ni tsarinsu birgeni yake. Indai madam ta haihu min baby girl nima tana gama secondary zan mata aure”.
Dariya zancen ya bama Yoohan. Dan haka ya murmushi yana bin Aymah da wani narkakken kallo. Itako ta zuba masa harara ta ɗauke kanta. Dan tana takaicin idan suna tare taji ya canja harshe yana magana. Sai taga kamar gulmarta akeyi????. Shiko tunda ya fahimta ma har yi yake danya takaleta suyi faɗan nasu.
Cikin ɗauke kai yace, “Saina faɗa mata duk abinda ka faɗa”.
“Kai! Kaifa baka da kirki wani sa’in dude. Ni karka ɓatamin suna wajen ƙanwata dan kaga dai tace yanzu nine yayanta, idan ka mata laifi zata kawomin ƙara na hukuntaka”.
“Kai kuma kaji daɗi ko? Shege mai shiga hancin masoya sai anjima. Wuce ka tafi wajen Juliet ɗinka dare ne anan inan buƙatar ɗumin baby na”. Kafin Omar yace wani abu Yoohan ya yanke wayar ƙitt.
Matsowa yay kusa da ita ya amshi spoon yana faɗin, “Wannan fake yayan naki yana takuramin da yawa Sweet girl”. Sai da ta buɗe baki ya saka mata abincin daya ɗebo sannan ta bashi amsa cike da kasalar barcin da takeji.
“Ai shine zai dinga saitomin kai idan ka birkice. Dan kaima rigimammene silly boy”.
Goshinsa ya shafa zuwa saman ido yana murmushi. Ya cigaba da bata abinci batare da yace komaiba. Ta fahimci yau dai halinne ya motsa, shiyyasa itama tayi shiru ta cigaba da karɓar abinci da yake bata. Sai da ta tabbatar ta ƙoshi sannan shina ta amsa zata fara bashi. Cikin marairaicewa yace, “Na ƙoshi Sweet girl. Karkisa naita ƙaton ciki kizo kina kasa ɗaukata dama gaki da rakin tsiya”.
Murmushin da batayi niyyaba ta saki. Ta kwanto a gefen hannunsa tana lumshe ido da faɗin, “Duk ƙaton cikinka zan iya da kai malam”.
“Oh wow!!. Da gaske?”.
Miƙewa tai zata gudu yay saurin riƙota ta faɗo jikinsa. A cikin kunnenta yace, “Yarinyar nan kinfa ƙware wajen guduwa ba’a gama magana ba”.
Da sauri ta taune lip ɗinta na ƙasa tana dariya ƙasa-ƙasa. “Ni kaga barci nakeji ALLAH. Ka barni na kwanta kona maka barci a jiki”.
“Ai jikinki ne baby”. Ya bata amsa yana miƙewa ɗauke da ita suka haura kan gadon. Fitilar ya rage musu yana gyara mata kwanciya a jikinsa da ƙyau. Kanta ya sumbata suka sauke ajiyar zuciya. Ɗagowa itama tayi ta sumbaci laɓansa da shafa kwantaccen sajensa. Cikin sauke murya sosai tace, “I’m sorry. Nayi alƙawarin bazan sake ba insha ALLAHU”.
“Thanks you sweet angel. ALLAH yay miki albarka. Nima kiyi haƙurin ɓata miki rai da nayi. Insha ALLAH bazan ƙaraba humyim?”. Ya ƙare maganar da cusa kansa a wuyanta yana shinshina. Ƙanƙamesa tayi dan salonsa a kullum mai wahalane a gareta…..



