SARAN BOYE COMPLETE

_★★
Tun wucewar su Yoohan Jay ya kasa zaune ya kasa tsaye a office ɗinsa. Gaba ɗaya man kan sa ya gama tsiyayewa tas akan wannan kamanni. Goshinsa ya murza da cewa, ‘Kai anya kuwa. Dolene nasan wanene wannan yaron’. Ya ƙare maganar da ɗaukar telephone yay kiran Dawood.
Dandanan Dawood ya amsa kiran boss. Nuna masa kujera yayi alamar ya zauna. Bayan kusan mintuna uku ya ture files ɗin gabansa yana kallon Dawood ɗin.
“Dawood nikam a ina kasan yaron nan ne?”.
Cike da girmamawa ya bashi amsa da faɗin, “Sir, tare mukai secondary school da su”.
“Masha ALLAH, lallai kayi masa sani na sosai. Anan cikin abuja suke?”.
“Yes sir. Ai yaron sanannen Pastor ɗin nanne Goshpower mai ƙaton catholic church ɗin nan dake a wuse2”.
Ɗan jimm Jay yay yana kallon
Dawood. Sai kuma ya sauke numfashi kaɗan yana wani guntun murmushi mai kama da an masa dole. “Okay thanks you, zaka iya tafiya”.
Miƙewa Dawood yayi tare da salute ɗinsa ya fice yana mamakin tambayoyin ogan nasu.
Dawood na fita Jay ya shiga Google. Bayanai ya nema akan dukkan handles ɗin papa dake a social network. Cikin mintuna ƙalilan kuwa suka watso masa komai. Facebook, Twitter, Istagram, Telegram, dama wasu daban-daban. Harda youtobe chennal da suke ɗaura dakan abubuwansu na church ɗinsu. Numfashi yaja ya furzar tare da shiga kowanne shafi ya duba followers nashi da duk wani posts da yayi a kai. Yawanci duk akan church ne dai.
Komawa yay bincike akan pictures nashi. A take kuwa suka bashi su da yawa. ‘Oh my GOD!!’. Jay ya faɗa da matuƙar razana. Gaba ɗaya kansa ya sake kullewa. yama rasa kalar tunanin da zaiyi dan da gaske shi dai ya shiga ruɗani. Ta yaya hakan zata kasance bayan shi shaidane akan abinda ya tabbatar a zahirin gani da ido. To amma inhar ta tabbata a tunanin da zuciayarsa ke bijiro masa lallai sai dai idan akwai yaudara a lamarin kenan, ko kuma...... Yay saurin girgiza kansa alamar ba haka baneba sam. dan da sun sani ai.
A wannan yanayin Bilkisu ta sake shigowa ta samesa. Rungumesa tayi ta baya tana sauke ajiyar zuciya. Shima ajiyar zuciyar ya sauke sannan ya zagayo da ita gabansa. Kaɗan ya ranƙwafo ya sumbaci laɓɓanta da goshinta.
“My Boss ina baƙin naka suke?”.
“Sun wuce Miemaa. sai dai ina cikin ruɗani wlhy”. Yay maganar yana jan hannunta wajen kujerarsa.
Zama tai a kujerar tana bashi amsa itama. “Bakai kaɗai bane a ruɗani. Ni kaina rikicewar ta hanani zama na gudo nabar su Ummie acan”.
Ta bayanta ya ranƙwafo yana nuna mata abinda ya samo game da papa. Ƙwarai da gaske ta cika da mamaki itama saboda ganin hoton papan. Dan haka sukayi zaman tattaunawa yay mata bayanin dukkan hukuncin daya yanke. Tare da alƙawarin zuwa wajen baba malam kozai ƙara samun wasu bayanai ta wajensa game da papan tunda sun zama surukai.
Ta gamsu ɗari bisa ɗari da hakan. Harma da zuwan wani cikin gidan, dan Little bee bazai yuwu taje gidan baba malam ɗin ta zaunaba saboda mijinta da wahala ya amince duk da yasan dokar aikin. Amma zai tura ƙaramar ƴarsu autar su Little ɗin mai suna Afrah akan case ɗin da su Yoohan ɗin suka kawo report.
_★★★
Lokacin da Yoohan ya shigo gidan ya iske duk suna church. Sai guards ɗinsa kawai da maigadi aka bari alamar papa yaji shawararsa ta kwanaki kenan. A cikin gidanma daya shiga ya samu Blessing. Cike dajin daɗin ganinsa da tunanin tare yake da Aymah ta shiga masa welcome. Ya amsa mata kadaran kadahan. Ya kama ƙafar benen zai haura Blessing da haƙurinta ya ƙare tace, “Sir Aunty fa?”.
Juyowa yay ya ɗan kalleta yana lumshe idanu da buɗewa. Sai kuma ya ɗan mata murmushi a bazata dan bata taɓa ganiba. Shi kuma jin daɗin nuna kulawarta ga matarsane ya sakashi yin murmushin. Sai da ya juya ya cigaba da hawa steps ɗin sannan ya bata amsa da, “Tana can na barota. Kina missing nata ne?”.
Cike da haɗiye ɗokinta tace, “Sosai ma Sir. I miss her so much”.
“Thanks you”. Ya faɗa a taƙaice yana idasa hayewa.
Da sanyin jiki Blessing ta koma kitchen dan ta haɗa masa wani ɗan abun duk da baice yana buƙata ba.
Shikam Yoohan ƙofar sashensa ya buɗe ya shiga. Mayen ƙamshin turaren da Nu'aymah ta fara amfani da su yana nan nane da sashen. Cike dajin sabuwar kewarta ya shiga yana kalle-kallen falon. Tsahon mintuna biyu sannan ya sauke ajiyar zuciya ya nufi bedroom ɗinsa. Harya tura ƙofar ya shiga sai kuma ya fasa ya dawo da baya. Bedroom ɗin Aymah ya nufa, yana ƙoƙarin saka key ya buɗe ya ga ƙofar a buɗe. cike da mamaki ya tura da sauri ya shiga. Turus yaja ya tsaya yana kallon yanda aka hargitsa ɗakin. Kayanta na sawa duk a watse a ƙasa. Littatafanta hardasu Al-qurani duk an yasar. Saurin ƙarasawa yay inda Al-qur'anin izu sittin ke a kife a ƙasa alamar jefarma da shi akayi. Ya ɗaukesa ƙwalla na cika masa idanu. Wani masifaffen fushi na yunƙuro masa da tarar masa a ƙirji.
Babu wanda yazo masa a rai da yin wannan aikin sai Gebrail. Kodan dama yana nan a maƙale a ransane oho. Ajiye Al-qur'anin yay saman mirror ya fito a matuƙar harzuƙe yana ƙwalama Blessing kira....
Hakan yayi dai-dai da shigowar su madam Chioma cikin falon suna dariyar shirmen Abraham. A kusan tare suka tsaya cak suna kallon yanda yake sakkowa daga upstairs ɗin da gudu-gudu. Ga wani razanannen kira da yake ƙwalama Blessing. Yana gama sakko idonsa ya sauka akan Gebrail da yake shigowa kusan a ƙarshe.
Ture Blessing dake isowa gabansa jiki na rawa tana amsa kiransa yayi gefe. Cikin rufewar idanu na rashin ganin su mama debora ya nufi kan Gebrail da duk ya daburce saboda tsorata na rashin gaskiya. A bazata Yoohan ya saukema Gebrail wasu gigitattun maruka a jajjere bisa kumatu. Kafin wani ya samu damar jin ba'asin wannan tashin hankali ya zare belt ɗin jikinsa ya shiga dukansa da shi kai kace ALLAH ne ya aikosa. Gaba ɗaya idon Yoohan ya rufe, Al-qur'anin nan kawai yake ganowa yashe a ƙasa da Nu'aymah a sume a randa Gebrail ya shigar mata.
Tunda su madam Chioma suke a rayuwarsu basu taɓa ganin irin wannan tashin hankalin da matsanancin fushin Yoohan ba. A take falon ya rikice da kuka da kururuwar ihu. Ina Yoohan sam bama yajinsu. Laftar Gebrail dake ihu yashe a ƙasa iya ƙarfinsa kawai yake ta ko ina.
Duk yanda madam Chioma da su mama debora ke kuka da masa magiya basa gabansa. hakama guards ɗin gidan kowa ya gagara matsawa inda Yoohan yake. Solomon da suka dawo tare da su Madam Chioma da yay ƙoƙarin matsawa wai ko Yoohan ɗin zai sauraresa sai da ya samu rabonsa. Dan zuba masa belt ɗaya Yoohan yayi jiki. Da wani irin mahaukacin tsalle da ihu yay gefe saboda azaba.
Dukan Gebrail Yoohan yayi sosai har sai da yaga ya daina motsi, dan har papa daya shigo gidan tare da su Uncle Godwin bai sauraresuba. Sai da yay tiɓis shi kansa sannan ya jefar da belt ɗin gefe. Daga Momy harsu Joy kan Gebrail sukai suna kuka. Yayinda Momy Destiny ta riƙo Yoohan da shima ƙwalla ke silalo masa tsabar zafin zuciyar da yake a ciki. Zaunar da shi tayi a cikin kujera.
A can gefe kuma Omar (Rich) daya shigo yanzun ne gidan, saboda ya fita tun safe. Tun a compound sauran guards ɗin gidan ke sanar masa abinda ke faruwa. Da sassarfa ya ƙaraso falon. A yanayin da yaga Gebrail da ihun Madam Chioma daya hargitsa falon da kururuwar cewar Gebrail ɗin ya mutu ya saka bama su Solomon daya gama shan tasa azabar umarnin cicciɓar Gebrail shi da sauran guards ɗin sufice da shi zuwa asibiti.
Sannan ya ƙarasa inda Yoohan ke zaune yanata huci har yanzu da sassarfa. Cike da tashin hankali ya kamashi ya miƙar batare daya saurari ihun da Maman madam Chioma kema Yoohan ɗin a kai ba. Dan ya tabbata shirun da yay mata zuciyarsa sake kumbura take. Idan kuma har ya miƙe wlhy zai iya bugeta itama dan Yoohan ALLAH yay masa zafin zuciya na bala'i.
Duk abin nan dake faruwa papa da su Uncle mike na tsaye suna kalonsu tamkar wasu gumakan farkon karni. Hakama baƙi da suka ɗan fara shigowa ziyara sunyi cirko-cirko da tsoro.
Harabar gidan Omar ya fita da Yoohan da binsa kawai yake cike da rufewar ido. Turasa yayi a mota ya maida ya rufe tare da zagayawa mazaunin driver yaja ya fice da shi daga gidan. Kai tsaye hotel ya nufa da shi. A motar ya barsa yaje ya kama ɗaki sannan ya dawo ya sake kamashi ya shiga da shi ciki.
Koda suka shiga cikin ɗakin zubewa Yoohan yayi a kujera kawai yana sauke wasu azababbun huci masu ban tsoro. Ruwa mai sanyi Omar ya ciro a fridge yazo ya miƙa masa. Fisgar robar ruwan kuwa yayi ya kafa kai. A mamakina sai gashi ya shanyeta tas yayi wurgi da robar yana juya idanunsa dake jajur abin tsoro.
__★★★
A ɓangaren Jay kuwa tun randa su Yoohan sukaje wa jensa a ranar kasa haƙuri yayi, da yamma liƙis ya shirya shi da Afrah suka nufi kano ta dabo gidan baba malam. Abinda bai taɓa yiba. Dan bai taɓa kai iyalansa gidanba tunda suke mu'amulat nasu.
Sosai baba malam yaji daɗin ganinsa. Dan yamasa ziyarane ta bazata. Ya kumaji daɗin zuwa da Afrah da akai. Wadda bai taɓa saniba a ido, sai dai a baki. Shima bawai ya taɓa tantance ƴaƴan Jay ɗin maza ne ko mata ba. Duk da kuwa Jay ɗalibinsa ne sosai. Dan ya sanshi ne a dalilin mijin Ummu. Dan shiɗin ɗalibin mijin Ummu ɗinne acan saudia. To acan suka taɓa haɗuwa da Jay shi baba malam yaje miƙa gaisuwa ga malaminsa, shi ko Jay yaje gaida Ummu ɗinsa ne da kuma yin Umrah shi da iyalansa.
Tun a can suka ƙulla alaƙa. Bayan sun dawo Nigeria kuma Jay ya ringa zuwa ɗaukar karatu wajen baba malam ɗin a duk ranakun weekend lokacin suna a gari ɗaya.
Har cikin gida baba malam ya kai Afrah. Inda ta samu ƙyaƙyƙyawar tarba a wajen Umm da Muhammad mai saurin sakin jiki da mutane. Cike da ƙwarewar aiki irin na Afrah data sha tun a cikin uwa da uba ta dinga jan Umm da hira akan hotunan Aymah data gani a falon. Umm kam tanada son yara. Gashi Afrah ta shigar mata rai lokaci ɗaya dan ta tuna mata da tata ɗiyar dake nesa da ita. Duk da kuwa Afrah zata girma Nu'aymah da kusan shekaru huɗu ma da wasu watanni, Afrah zatai shekaru ashin da biyu.
A take Muhammad ya shiga bama Afrah labarin sister ɗinsa. Umm na tayasu da dariya dan sosai drama ɗin Aymah yake bama Afrah ɗin. Har ranta kuma taji kaɗayi dason ganinta.
Lokacin da Baba malam ya shigo dan kiran Afrah da Jay ke jiran su wuce dan jirginsu ya kusa tashi sai Muhammad duk yay kalar tausayi. Umm ta haɗa mata kayan kwalliya da su kayan fulawa tanata saka mata albarka da godiya. Tare da roƙon ta dinga zuwa musu ziyara dan ita dai sosai yarinyar ta shigar mata zuciya................✍
Hafsat miss xoxo????
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).????????
Mamu gee????
MIN ƘALB!!????????
Hafsat rano????
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!????????
Safiyya huguma???? SIRAƊIN RAYUWA????????
Bilyn Abdull????
SARAN ƁOYE????????
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka????????????????
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????
09033181070
????????????????????????????????????????
TEAM—-ZAFAFA BIYAR????????????????
[7/2, 2:08 PM] +234 808 711 8630: LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana????????.
No 68
INA MASOYA MA’ABOTA SON ‘KAAWATA KITCHENS DINSU DAMA DECORATION NA GIDAJEN SU? TOH KU MATSO, DOMIN NESA TAZO KUSA…_
KAYA NE INGATTATU DA AKE KAWO MUKU SU TUN DAGA KASAR ???????? GERMANY..! KOWA YASAN GERMANY AKWAI KAYA MASU INGANCI, SEKA SHEKARA DA SHEKARU KANA AMFANI DA KAYAYYAKIN SU BASA LALACEWA. ANYI SU CIKIN TSANTSAR INGANCI DA KUMA RAHUSA… WADANNAN KAYA MAAB LUXURY HOME DAKE GERMANY TA KAWO MANA SU NIGERIA. RIGIJI GABJI FA KENAN.. BABU RUWAN KU DA WANI PRE-ORDER KO SHIPPING FEE, KAYAN MAAB LUXURY HOME SUNA NAN A KASAR MU NIGERIA, SAI DAI KAWAI KU HANZARTA KU GARZAYA KU BIYA KUDI KU KARBA…
MAAB LUXURY HOME, MAAB LUXURY HOME, MAAB LUXURY HOME…
SUNE A KAN SAHUN GABA INDE WAJEN SIYAN KAYAN KITCHEN NE DA NA KAWATA GIDA, WATO A TURANCE KITCHEN UTENSIL’s& HOME DECOR…
INA UWARGIDA? AMARYA? YAMMATA DAKE SHIRIN SHIGA DAGA CIKI? ZAWARA MASU SHIGA DAGA CIKI? IYAYE MASU NEMAN INDA ZASU SAYAWA ‘YAYAN SU KAYAN GIDA? YAYYE MAZA, MIJIN MATAR SA????? SAURAYI DAKE SON BURGE BUDURWAR SA WAJEN GWANGWAJE KYAUTA? TOH MAAB LUXURY HOME TA TANADAR MUKU DUKKANIN ABUBUWAN AMFANI NA KITCHEN, DANA KAWATA GIDA, YAITA WALWALI YANA HASKAKAWA..
AKWAI KAYAN KITCHEN MAI KAWATA KITCHEN, WANDA ZAI SA KISHIYA KWAFA, YASA DANGIN MIJI SU FARA HABA HABA DAKE, DUK INDA AKA SHIGO CIKIN GIDAN KI ASAN EH TABBAS KEMA KINA AMFANI DA KAYAN MAAB LUXURY HOME, KAYAN KAWAATA GIDAJE MASU HASKA KO’INA NA GIDAN KI, KAGA GIDA A NIGERIA AMMA TAMKAR A NAHIYAR ‘KETARE..
MAAB LUXURY HOME, TANA SAIDA KAYAYYAKI MASU INGANCI DA KYAWUN GASKE, AKWAI RAHUSA WANDA KOMAI KANKANTAR KUDI KANA IYA SIYAN WANI ABUN AWAJENTA, KAYANTA BA SAI MASU KUDI BA, KOWA YANA IYA GARZAYAWA YA SIYO NASA, ABUBUWAN DA YAWA, KAYAN DAGA CIKI AKWAI IRIN SU:
DINNER SETS, SERVING TRAYS, CUTLERY SETS, JUGS, FOOD FLAKS, THERMO FLASKS. DA SAURAN SU ABUBUWAN HOME DECOR.
DOMIN NEMAN/TUNTUBAR KAYAYYAKIN MAAB LUXURY HOME, GA DETAILS DIN KAMAR HAKA:
INSTAGRAM: MaabLuxury home.
WhatsApp number: +491521 4642007
Facebook: Maab Luxury Home
Adireshin su na yanar gizo: maabluxury.com
suna garin KANO. Amman suna tura kayayyakin su ko ina a fad’in nigeria.
KYAU, INGANCI, RAHUSA… SAI MAAB LUXURY HOME
No. 68
…………Sun fito har ƙofar gida Muhammad biye da su zai mata rakkiya. Shima Jay ya jashi a jiki da kulawa. Anan ne yake tambayarsa miyyasa yaga yana fushi. Hawaye cike da idonsa yace, “Uncle Please ka bar mana Aunty anan ta zauna. Kaga Aunty N Uncle Yoohan ya gudu min da ita. sai ni kaɗaine a sashenmu. Ni kuma inason na dinga ganina da abokiya kamar Aunty N”.
Cike da ƙaunar yaron Jay ya sumbaci kumatunsa yana ƴar dariya. Yace, “Oh woow sarkin wayo. inko hakane na maka alƙawarin Aunty Afrah zatazo maka hutu dan tana hutu dama yanzu haka”.
Cike da ɗoki Muhammad yace, “Uncle yaushe?”.
Yanda yayi ɗin har saida yasa baba malam da Afrah da Jay dariya. Jay yace, “Karka damu zaka iya ganinta a koda yaushe”.
Duk da Muhammad yaso jin ranar da zatazo dai sai yayta ɗoki. ya koma cikin gida da gudu ya sanarma Umm.
Bayan wucewar su Jay da kwana biyu Muhammad ya addabi su baba malam da zancen yaushe Aunty Afrah zata zo? Shifa idan bazatazoba to shi a kaisa gidansu yay hutu. Ganin ba hutu suka samuba shi sai baba malam ɗin ya kira jay da bukatar yaushe Afrah zata zo ɗin. dan sufa an saka musu zuma a baki kuma duk sun ƙagu. Hakan yama Jay daɗi, dan shirinsu na tafiya yanda ya kamata cikin rahamar ALLAH.
Bai wani ja zancenba yace zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu zai kawota da kansa insha ALLAHU. Wannan shine dalilin samun ƙofar shiga gidan su Nu'aymah da Afrah ta samu domin cika aikin ysyarta. Dan haka a safiyar yau kuma lahadi ta tashi da shirin tafiya can zatai zaman wata ɗaya rak insha ALLAHU.
Sai karfe biyar na yamma Anuwar ya gama shirin kai Afrah kano gidansu Aymah. Dan haka bayan ya kammala shirinsa tsaf ya saka Al-hassan Ya kira masa ita a can sashen Uncle Anuwar. Dan ita acan take zaune kamar yanda little bee ma acan tai rayuwarta har tayi aure. Tsakaninta da sashen iyayenta sai dai tazo gaisuwa kawai ko hira. Amma ita Uncle Anuwar da aunty Nabeelah ne iyayenta. Sauran yaran kuma Miemaa da Abie.
Tana zaune a falo hankalinta akan lap-top tana hidimarta Al-hassan ya shigo da sallama. Kasancewar yayima Aunty Nabeelah laifi yau da safe. ta kuma tabbatar masa idan ta kamashi sai ta zanesa sai ya dogare a bakin ƙofar yana kalle-kalle. Daga can yace, “Aunty Afrah kizo Abie na kiranki”. Bai jira ko amsarta ba ya shilla waje da gudu saboda leƙowar aunty Nabeelah dake kitchen dan jin muryarsa da tayi.
Aiko mi Afrah zatai inba dariya ba. Tace, “Mamma wlhy kin hana auta Sukunin shigowa sashen nan yau gaba ɗaya. Ɗazun ina kallonsa daya hangoki kin fita har faɗuwa yake wajen tiƙar gudu zai shige sashensu”.
Dariya Nabeelah tayi itama da faɗin, “Ai ya gama gudunsa babu fashi saina ruɗa masa jiki da bulala tunda shi bayajin magana. Iskancin yaron nan baya tashi sai ya ga su Miemaa na gida. To in ALLAH ya yarda shi abin nema da tsokana ya samu a wajensa tunda yasan basa bari a taɓasa”.
Miƙewa Afrah tai tana dariya da zura Slippers a ƙafarta. “A daiyi haƙuri Mamma na. Bara naje Abie na kirana inaga ya gama kimtsawa”.
A take mood ɗin Nabeelah ya canja. Cike da damuwa tace, “Kai ni dai wannan aiki nasu Abie yana moremin, da ƙarfi da yaji ya maida kowa jami'insu a gidan nan, ALLAH banason kina nesa dani ko kaɗan. Amma yaya zanyi, nanda lokaci kaɗanma zaki gudu gidan aurenki ki barni da kewa ta haƙiƙa kamar yanda little taimin.
Ƙasa Afrah tayi da kanta kawai cike dajin kunaya. Sai dai bata iya cewa komaiba dai.
Sallamarta Nabeelah tayi ta tafi dan tasan Jay jiranta yake. Ilai kuwa ta iskesu a falonsa shi da Miemaa suna jiranta. sai da tayi sallama suka bata izinin shiga sannan ta shiga. Bayan ta durƙusa ta gaishesu ne Jay ya nuna mata gabansa alamar ta zauna. Babu musu tazo jikin ƙafafunsa ta zauna cike da ladabi da ƙaunar iyayen nasu.
Gyaran murya Jay yayi yana kallonta fuska babu wasa. Yace, “Afrah!”.
“Na'am Abie”.
Ta amsa masa kanta a ƙasa.
Zamansa ya sake gyarawa sannan ya cigaba da faɗin, “Inason ki nutsu ki saurareni. Duk da bani da fargaba a kanki game da aikin nan tunda nasha sakaki inason sake jaddada miki muhimmancin na wannan lokaci. Kisa hankalinki da ƙyau dan banason kuskure a ciki. Baba malam yanada muhimmanci mai girma a gareni dake kanki. Inason kiyi komai da ƙwazo da hikima ok?”.
“Insha ALLAHU Abie zanyi duk yanda kace. Kuma zan kula nayi komai yanda ake buƙata. Kudai tayani da addu’a”.
“To Alhmdllh, addu’a kuwa dama akoda yaushe cikin yi muku ita muke. ALLAH ya baki nasara yay riƙo da hannunki kiyi komai cikin sauƙi. Wannan camaras ne”. Yay maganar yana miƙa mata wasu ƴan ƙananan dutsuna tamkar diamonds kusan goma. “Dasu zaki tafi, inason kibi duk sashen gidan ki maƙalasu a kowanne parlors. Idan sun wadata har Backyard na gidan dan suma wajene da masu baƙin hali zasu maƙale suyi magana. Ki ajiyesu da tsantsar kulawa yanda babu wanda zai gane minene. Duk da nasan koda a zahiri suke bawai ganewar zasuyiba inba dai ganinsu da yawa yasa suyi tunanin wani abun kuma daban ba. Inhar kika samu nasarar saka cctvs ɗin nan a ko ina na gidan to aikin zaizo da sauƙi insha ALLAHU. Dan zasu bamu damar kula da motsin kowa hankali kwance. Banason Little da Dawood susan komai kan camaras ɗin nan, wannan aikinane ni kaɗai zakimin. Abu na biyu shine saka ido akan duk wani baƙo da zai shigo gidan. Ma’aikatan gidan da yaran gidan suma. Banda wauta da surutu mara amfani, duk da namasan waɗanan ba halayenki bane. Biyayya ga nagaba. Aiki basai ance tashi kiyiba tunda nasan iyayenki sun tsaya akanki babu abinda baki iyaba. Dan ALLAH ki kula da mutuncin kanki dan gidane family house akwai samari a ciki. Duk da har raina bana zargin rashin tarbiyya daga wannan zuri’ar koda a mafarkina. Amma dai dolene na jadada miki kame kanki da kuma kula da ibada dan na fahimci aikin zai kaiki har cikin azumi dake gabatomu”.
“Inasha ALLAHU Abie zaka sameni mai kiyayewa”.
“To ALLAH yay miki albarka da sauran ƴan uwanki baki ɗaya”.
Amin ta amsa ita da Miemaa dake saurarensu. itama daga baya ta ɗora da nata nasihan da wasu dabarun aikin. Duk da kuwa tunda aka tsura maganar cikin koya mata take salo-salo harma Jay din kansa. To Alhmdllhi kuwa tana haddace komai. Dan dama itama bata wasan yara bace wajen tsayawa tsayin daka akan aikin nan da ba yau iyayenta suka fara tsundumata a ciki ba.