SARAN BOYE COMPLETE

Zahira na fara yiwa wanka ta zauna a d’akin Dan indai Umma na Palo Bata fita Haka take zama adaki a yarana Zahira tana da balain San kallo duk Santa da kallo idan Umma na palon hakura take Haka ma take tsoron Hindatu sabida rankwashin da take Kai Mata a Kai.
Nadeeya ita Kuma rawar Kai ne da ita da Wasa hakane yasa Ina Mata wanka ta fito waje na hau yiwa Minal duk na dauka suna d’akin sai dana Gama yiwa Humaira na fito daga band’akin na ajiye Humaira Akan gado na fita zuwa kitchen Dan na juye ruwan tea d’in.
Ina gama juyewa na fito
Naga Umma ta Sha bakakken Kaya har kasa gefenta Kuma Hindatu ce tayi irin shigarta Haka kawai naji gabana ya Fadi da muka hada Ido ta min wanan murmushi nata Mai tsinka min zuciya da Sauri na shige d’akina Ina jan Allahuma ajirni fi musibati wa aklifnin khairin minha.
Ina shiga d’akin naji duk ba a nutse nake ba ahaka na dauko Vaseline na hau shafawa su Zahira Sam ban lura Nadeeya Bata d’akin ba sai Dana Gama shafawa Humaira na lura Nadeeya Bata dakin.
Da Sauri na kalli Zahira cikin fad’uwar gaba Ina tambayarta ina Nadeeya take”?
Sai tacemin ai Ina mata wanka ta fita waje aguje ko wandon ma Dana d’auko musu Bata saka ba.
Hankalina a balain tashe nayi waje na tsaya a Palo Ina dube dube banganta ba na shiga kitchen da Sauri Ina kwalla Mata Kira Nan ma shiru.
Kara dawowa nayi na shiga band’akin palon shima Bata Nan bana shiga d’akin Umma Dana Hindatu Amma sabida tashin hankali Haka na shiga Ina kwallawa Nadeeya Kira amma banganta a d’akin ba.
Haka kawai naji jikina ya fara balain rawa cikin tashin hankali Nazo tsakiyarsu Umma Ina “Dan Allah Umma kungane min Nadeeya”?
Umma ko.kallona batayi ba sai Hindatu ce tacemin ajiyarta Kika bamu”
Da Sauri nayi waje na sauka ringa hada stair uku biyu Kamar Zan hantsulo sabida tashin hankali.
Lukman babban yaron Naseer da fitowarsa kenan Yana bud’e shagunan Naseer na nufa da Sauri.ina tambayarsa ko ya ganemin Nadeeya ko amsa gaisuwar da yakemin banyi ba.
Girgiza min Kai yayi Yana Bai ganta ba.
Ban tsaya ma Jin Mai yake cewa ba na Kara Hawa Sama Dan sai yanzu na tuna Nadeeya Bata iya saukowa sai dai a sauko da ita Dan balain tsoro ne da ita Dan Zahira ce ma take iya Hawa bene amma Nadeeya ko lekowa tayi ta kasa aguje take ja da baya Dan gani take zata iya fadowa Dan mmn Mannir har tsokaneta take ta ringa daukarta kamar zata jefota idan tazo.
Ina hawa sama na ware murya Ina cigaba da Kiran Nadeeya ya Ina duba kowane lungu da Sako nice har da duba karkashin kujera da gado.
Umma da Hindatu suna zaune a Inda na barsu ko gezau basuyi ba kamar ma basu San da hallita ta a wajen ba.
Zubewa na yi a gabansu Ina “Dan Allah Umma Baku ga Nadeeya ba wlh Ina Mata wanka Nan ta fito Palo Kuma Bata iya sauka kasa sai dai a d’auketa Dan Allah Baku ga Inda tayi ba”?
Ba Wanda ya kulani a cikinsu kamar ma bad’asu nake magana ba hannu na Dora a kaina na fara zabga Sallati na Kara d’aukar hanyar waje a guje ko Humaira danake juyo kukanta daga d’aki ban bi ta kanta ba
A bakin kofa na ci Karo da Naseer da tunda ya fita massallaci Bai dawo gidan ba Dan yaje kasan layinmu adduar mutuwar wani bawan Allah daya rasu.
Ina ganinsa nasan shima lukman ya Gaya masa Banga Nadeeya ba
Kara tambayata yayi “Wai baa ga Nadeeya ba”?
Ban iya bashi amsa ba na cigaba da kuka Ina na shiga uku da Sauri Naga ya hau saman Benen batare da yabi ta kaina ba nabi bayansa da Sauri……….
[6/13, 10:48 AM] Queen Meenali????: NAGA TA KAINA
*NA SADNAF*????????
®️ PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
{We Don’t just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}????????
Free Novel
Page 17
D'akina ya shiga kansa tsaye Yana kwallawa Nadeeya Kira ya fito ya duba koina yana "Wai kamarya Ba'a ga Nadeeya ba sai kace almara Taya ya daga yiwa yarinya wanka ta fito kice baki ganta ba"?
Wajensu Umma da har lokacin basu nuna sun San Mai ke faruwa ba ya nufa Yana “Umma Dan Allah bakiga Nadeeya ta fito daga d’akin Naeema ba?
“Toh ko Ni na saceta da zaka zo kana min tambaya”?
B’acin Rai ne yasa Naseer yace a Dan tsawace “Umma daga tambaya sai kice ko saceta kikayi wanan wane irin magana ne”
Tsaki da Bai shiryawa fitowarsa ba yayi ya wuce waje fuu Hajara kuwa ta girgiza Kai tana har dasu Tsaki yayi kyau”
Zuwa lokacin Ni nasan jinina ya hau sabida tashin hankali.
Daga farkon layinmu zuwa karshen layin mu Haka muka zaga muna kwallawa Nadeeya Kira Amma shiru.
Mmn Mannir da itama ta fito ita da yaranta tuni ta fasa fita suka hau tayamu Neman Nadeeya makotana suna da balain kirki Dan ba iya matansu ba har da mazajensu Haka suka hau tayamu neman Nadeeya Inda sukayi ta mamaki idan nace musu daga wanka ta fito na nemeta na rasa Kuma duk Wanda yasan Nadeeya yasan Bata iya saukowa daga Sama.
Kukan ma kasa wa nayi sai sallati nake har komawa nake gidan na shiga d’akina Naga ko zan ganta har zazzaga kayan wardrobe Dina nayi ko shigewa tayi Amma ba Nadeeya babu labarinta Humaira kuwa har ta gaji da kuka tayi shiru a bayan Zahira da itama ta hau kuka.
Sosai nake mamakin Umma da ta kasance kakar Nadeeya da Bata nuna ta damu da neman da muke wa Nadeeya ba hasali ma tea Dana dafa Suka zubo ita da Hindatu da kwai suka dauko gwangwnin Madara Dana Milo suna Shirin hada shayi su sha
Waje nake so na sake yi Amma na tsinci kaina da nufar wajensu Sabida daga murmushi danaga.umma na min yasa nasan tana da masaniyar Inda yata take.
Agaban Umma naje na zub’e Ina “Umma Dan Allah na hadaki da Wanda ya halliceki ki gayamin Inda Nadeeya take Umma daga d’akina ta fito Kuma Kuna zaune anan ta fito daga d’akina Dan Allah Umma kimin komai idan ta Kama yau na hada kayana na bar gidanan wlh Zan hada Dan Allah ki dawomin da Nadeeya na tuba Umma Nadeeya bata Miki komai ba Ni na Miki Aunty Dan Allah Kuyimin Rai karku yiwa Yata komai”
Nace Ina k’ok’arin kamo hannun Hindatu
Adaidai lokacin da Naseer ya shigo da Sauri kana ganinsa kasan hankalinsa a tashe yake
Turus yayi Agaban mu Yana yiwa Umma da Hindatu wani irin kallo da yaga kayan shayi a gabansu
Cikin wani irin murya ya fara magana Yana “Umma Anya ke Kika haifeni kuwa Umma Anya Gaskiya Abba da Baba Suka gayamin da sukace ke Kika haifeni Umma ‘yata ce fa ta b’ata ake nemanta Umma jinina fa yata da ta kasance jika a gareki ita ake nema Umma Kika zauna ke da Wanan tsinaniyar zaku hada shayi ku Sha alamar ba Abunda ya shafeku Umma wlh ba Naeema Kika tsana ba Ni Kika tsana Umma Dan da kina kaunata bazaki ringa min abinda kike min ba Zaki so farinciki na Umma mak’ota da masu wucewa ma suna tsyawa sabida su Tayani neman Yata amma ke kin zauna Zaki sha shayi wane irin kallo kike so a Miki Umma ga wayanda suka san ke Mahaifiyata ce Umma Koda baki hada jini Dani ba Bai Kamata ace mutum Mai Rai sukutum guda ya b’ata batare da kin nuna damuwarki ba Umma,Umma lamarinki ya daina bani mamaki ya koma bani tsoro Umma insha Allahu Zan ga yata Kuma zan kawo karshen komai Dan Nagaji Umma”
Daga haka yayi ball da flask din gabansu ya shige daki ya canzo kayan jikinsa ya fito da Sauri hannunsa d’auke da mukullin motarsa da k’aramin passport din hoton Nadeeya da aka Mata lokacin da zaa Saka su a makaranta ya fice da sauri.
Ni kuwa na durk’ushe a wajen na cigaba da kuka na kasa yarda Wai Nadeeya ta b’ata yarinya da nayiwa wanka da hannuna ko wando babu.
Maganar da Umma keyi cikin huci yasa na tsayar da kukana Ina kallonta
“Yau ni Naseer ya ke d’agawa murya yake min ihu sabida yarsa ta Bata lailai Naseer yayi Nisa ba karamin asiriceshi wanan tsinananiyar tayi ba ba dai Dan Nadeeya kike wanan kukan ba ba Dan Nadeeya Naseer yamin ihu Ina mahaifiyarsa ba toh sai ku ganta nagani”