SARAN BOYE COMPLETE

WASHE GARI
Washe gari suka tashi da farkawar madam Chioma. Sai dai tanata faman raki akan hannunta. Dan kuka ta dingayi kashirɓan kamar ƴar yaye. Papa kuwa dake nane da ita yana tayata da tattali.
Yoohan kam Alhmdllh tun a daren ya farka. Ya kuma takurama Omar sai ya nema masa ticket ɗin wucewa U.S. duk lallashin da Omar ya dinga masa sam yaƙi saurarensa. Ya dage akan shifa sai ya bari ƙasar. Kuma bayason papa ya sani. dan duk da ya farka duk shigowar da papa yazoyi dubashi sai ya nuna bai farka ɗinba. Badan Umar yaso ba dole yaje ya nema masa ticket, sai dai bana zuwa U.S bane direct. Amma duk da hakan Yoohan yace ya yarda. Sannan yaje gidan ya haɗoma Yoohan ɗin kayansa na buƙatar yau da kullum kamar su waya da sauransu.
To kuwa a safiyar yau ƙarfe goma batai masa a asibitinba. Dole Omar ya fita da shi a ɓoye batare da ko Dr Shikurah ta sani ba. Shine ya kaisa airport ɗin ma. Yanaji yana gani Yoohan ya wuce ya barsa da damuwa.
Asibitin ya dawo, inda ya tarar anata neman Yoohan. Shima kawai sai yayi pretending ɗin shiga cikin ƴan nema. Dan baisan wace amsa zaiba papa akan tafiyar Yoohan ɗinba. Bayan kuma shi kansa Yoohan ɗin ya masa magiya da roƙon bayason su papa susan ya wuce da saninsa.
Jin Yoohan ya wucene yasake birkita madam Chioma, yanda ta tashi hankalin nata har mamaki ya bama Uncle Joshua shi dai, amma sai baiyi maganaba dan hakan ba huruminsa baneba. Daga ƙarshe ma allurar barci sukai mata saboda yanda take faman rubzar kukan ita dai a nemo mata yaronta. Shi kansa papan itace ta sake birkitasa. Dan yasan dai Yoohan bazai ɓataba. Abinda kawai ya tsaya masa a rai shine minene ya saka Yoohan ɗin tafiya bayan kuma baida lafiya?. Dama tun jiya yaketa tunanin akan faɗuwar da akace yayi babu gaira babu dalili tunda har waya shidai yayi da shi a ranar da safe, kuma baiji wata damuwa tattare da yaronsa ba a lokacin da shuke wayar. Dan shine ma yace karya faɗama Momyn nasu zai dawo a jiya yana son ya mata surprise ne. Har Yoohan ɗin na masa dariya akan hakanma. Sai kuma gashi ya dawo ya iske waɗanan rikitattun tashin hankali da gaba ɗaya ya rasa makamar riƙewa akan faruwarsu.
Nu'aymah na gidan Juliet Omar ya kira akan taje gida ga Yoohan nan a hanya. Abin ya bata mamaki dan sunyi da shi sai nan da sati biyu ma zai koma. Haka dai tai shiri ta koma gidan nata ttareda Juliet da tai mata rakkiya danta tayata gyara waje. Duk da ma tasan baza'a samu datti sosai ba tunda duka yau kwananta biyar da barinsa.
Babu dattin dai kam sosai. Amma sai da suka gyara komai tsaf. Juliet ta tayata sukai har girki saboda tausaya mata da takeyi na halin da take a ciki. Sai da suka gama komai tsaf sannan ta wuce tabar Aymah na wanka.
Bata wani jimaba ta fito tai shiri cikin doguwar rigar atanfa mai faɗi data ɓoye cikinta. Wayarta ta ɗauka ta nufo falo dan yunwa takeji ta bala'i. Turus ta tsaya tana kallon Yoohan dake kwance a kujerar falon idanu a lumshe. koda wasa bataji motsin shigowarsa gidanba sam. Cigaba tai da takawa a hankali inda yake. Batare da tayi magana ba ta zauna a gefensa da kai hannunta ta janye nasa hannun daya dafe kai da shi.
A hankali ya buɗe idanunsa dake jajur ya zuba mata su. Itama kallonsa take cikin ido sosai. Sai kawai yaji zuciyarsa ta ƙara raunana. A take hawaye suka cika idanunsa. Ɗayan hannunsa ya kai saman cikinta yana murmushin ƙarfin hali.
Ita dai Aymah kallonsa take tamkar wata sokuwa, dan yanzu kam sai dai ta bama wani labarin mijinta badai ita a bataba. Cikin sanyin murya tace, “Baka da lafiya?”.
Haɗiye abinda ya tsaya masa a maƙoshi yayi da ƙyar, sannan ya yunƙura ya tashi zaune yana cije baki daboda kansa dake masa ciwo har yanzun. Zama yay da ƙyau ya rungumota jikinsa, hannunsa nakan cikinta yana shafawa a hankali. Cike da raunin murya yace, “I miss you Sweet girl”.
Maimakon ta amsa masa sai ta ƙara jefa masa kalar tambayar ɗazun. Murmushi ya sakeyi da sumbatar kanta. “Lafiya ta ƙalau baby, sai dai kewarki ce”. Duk da Aymah bata yardaba saita ƙyalesa kawai a hakan. Itama ta rungumesa tare da haɗe bakinsu waje ɗaya. Duk da ciwo da ƙunar da yakeji zuciyarsa na masa bai hanashi bata haɗin kai ba. Tsahon mintuna uku suna a haka kafin ta janye bakinta a cikin nashi suna maida numfashi. Batare data bari wani cikinsu ya sake magana ba ta kama hanunsa suka wuce bedroom. Sai da ta rakasa har bayi, duk da tana fama da kanta ta taimaka masa yay wanka. Da suka fito ɗinma da taimakonta ya shirya sannan sukai salla.
Bata samu matsala da shi ba sai a wajen cin abinci, dan cayay mata shi ya ƙoshi. Hankalin Nu'aymah ya sake tashi matuƙa saboda ta kasa gane kansa gaba ɗaya. da ƙyar dai ta samu yaci kaɗan ya sata ta ɗakko masa magani ya duba wanda ya dace ya sha. Bedroom ya koma ya kwanta daga haka sai barci.
Gadon tazo ta sauna tai tagumi kawai ta zuba masa idanu tana kallonsa cike da tausayi da damuwa akan da tasa damuwar data fahimci yana son ɓoye mata ne kawai.
KANO NIGERIA
A lokacin da madam Chioma ke can neman sa'a akan Yoohan anan kano su Little bee ne suka samu damar ƙwamushe Rabi mai aikin su Aymah da ta zo yima Umm aika a kasuwa.
Tunda ta fito gida suke biye da ita batare data sani ba. Sai da tazo bakin titi domin tsallakawa taga mota a gabanta kawai. Kafin ta wani yunƙuri aka fisgota ciki tare da daɗe mata baki yanda ta kasa ihu. Daga ƙarshe ma suka danna mata allurar data bugar da ita. Harko suka iso garin abuja bata sake sanin ina hankalinta yake ba, sai wayar gari tayi taga kanta a wani ɗakin da bata saniba. Da matuƙar tashin hankali ta tashi tana ƴan waige-waige, sai kuma ta fashe da kuka ganin da gaske dai fa baƙon waje aka kawota......
Tsawar da aka daka matane ta sakata sake gigicewa harda sakin guntun fitsari. Murɗeɗen ƙatone da iya gani kasan ya damƙi namiji ma sai ya shinshino ƙamshin lahira bare ita mace da girma ya kama. Abincin hannunsa ya dangwarar a tebirin ɗakin dake tare da kujera ɗaya. Sai yololuwar guntuwar katifar da Rabi ta kwana agefe. Da tsananin kaushin murya yace, “An gaya miki nan gidan kuka ne. Karna dawo na samu wannan abincin da hawayen fuskanki”. Ya ƙare maganar da juyawa ya fita abinsa.
Tashin hankali iya tashin hankali Rabi ta shiga. Hakan yasa ta share hawayen nata ta zauna ta fara cin abincin data san bazata ƙoshiba. Ga uban yaji a ciki na tashin hankali. Amma tasan inhar batacinba yunwa halakata zatayi. Mutumin nan kuma kashetama zai iyayi ƙila. Sai da ta kammala da kusan minti talatin, zuwa lokacin yajin ya gama wajiga rayuwarta sannan aka kawo mata ruwa rabin gora. Jikinta har rawa yake wajen ɗauka ta sha, dan ita kaɗai tasan a tashin hakalin da take ciki game da cin yajin nan...
Haka aka ringa wajiga rayuwar Rabi har tsahon kwana goma. Tayi kuka harta rasa hawayen zubarwa. Sai da suka tabbaar tayi laushi iya laushi sannan suka nema su sanarma su Yoohan. Sai dai an samu akasi Yoohan ya wuce U.S sai Omar kawai ne ya amsa zaizo, dan jikin madam Chioma yayi sauƙi sosai anma sallameta tun kusan kwanaki uku kenan, satinta ɗaya a asibitin. Ranta dai na nan danƙare da damuwar rashin sanin inda Yoohan ya nufa da kuma rashin samun cikar burinta. Duk da tun a asibiti sun yake magana da Rebecca zasu koma gidan Bangaruta, sannan Marcy ma tace zata rakata wajen wani bokan a Lagos.
__★
Bayan isowar Umar kai tsaye office ɗin Dawood sukaje. Sai da sukai zaman jiran Bilkisu Adam Makaho, mata ga Oga Jay sannan, dan itace oga kwata-kwata akan case ɗin. Tana isowa kuwa suka amsa kira ta hanyar telephone.
Sun sameta a office ɗinta. Bayan sun gaisheta ta basu iznin zama. Sam babu wasa tattare da ita, dan yanzu bayan miskilancinta girma ya ƙaru ga daraja. Babbar Officer ce da aikinta ke girgiza sansanin duk wani mai kunnen ƙashi.
Batare data kallesu ba tace, “Dawood azomin da matar nan”.
“Okay maa”. Dawood ya faɗa da sauri yana miƙewa. Kusan mintuna goma sai gashi ya dawo tare da Rabi dake wujiga-wujiga, dukta fita hayyacinta a kwanaki goma kacal. Kuma babu zagi babu duka. Zai gurfanar da ita a ƙasa Bily ta hanashi. Wata kujera dake can gefe ta bashi umarnin ya bama Rabi ta zauna. Shi dai Omar nata kallonsu ne da mamakin ganin yanda Rabi ta koma. Gashi kuma ko ƙwarzanen duka shi dai bai gani a jikinta ba. Itako bama ta gane Umar ba saboda a jigacen da take.
Little bee ce ta shigo bayan tayi knocking an bata izini. Tai salute ɗin mahaifiyar tata kuma ogarta a wajen aiki kafin ta ajiye takardun hannunta a tebir ɗin. Takardun Bily taja gabanta ta duba kafin ta ajiyesu gefe ta kalli Rabi.
“Nasan dai zuwa yanzu kinsan a inda yake ba wajen wasan nanaye bane. Dan haka ya rage ruwanki nutsuwa ki bamu duk amsar tambayar da zamu miki, ko kimana ƙarya”.
Muryar Rabi na rawa tace, “In ALLAH ya yarda bazanyi ba ranki ya daɗe”.
“Wannan ya rage naki”.
Bily ta faɗa cikin halin ko in kula tana sake ɗaukar takardun da Little bee ta shigo da su. A gaban Rabi ta diresu dai -dai lokacin da fuskar Yoohan dake zaune a office alamar yana a asibiti ta bayyana a cikin lap-top ɗin da Omar ya ajiye inda Yoohan zaiga kowa dake office ɗin.
“Wannan takardun bayanai na duk abinda ke cikin wayarki. Randa kika sayi layi, randa kika fara ɗorashi a waya. Sau nawa kina canja shi a wasu wayoyi. Mutanen da kika taɓa kira ko suka kiraki duk akwai bayanansu anan. Dan haka ki nutsu sosai”.
“In ALLAH ya yarda ranki ya daɗe”.
Kallon sashen da Dawood da Little bee suke Bily tayi, kafin ta kalli lap-top ɗin. Kai Yoohan ya risinar cike da girmamawa ya gaisheta. Itama ta amsa masa da kulawa kafin ta nuna masa Rabi.
“Ina fatan kana ganinta da ƙyau?”.
“Yes maaa!”.
Duk da Rabi ta kalli fuskar lap-top ɗin itama bata kawo komaiba, tadai ga kamar hoton mijin Nu’aymah, kafin tunaninta ya faɗaɗa Little bee ta katseta da faɗin, “Minene sunanki?”.
Murya na rawa tace, “Rabi?”.
“Shekararki nawa kina aiki a gidan Sheikh Soorajidden Hashim Jibiya?”.
“Goma sha takwas. Dan an kainine lokacin matarsa nada tsohon cikin dake wahal da ita dan na taimaketa”.
“Kin taɓa aure?”.
“Eh na taɓayi harda yarana biyu”.
“Keda ke aure miya kaiki gidan aiki har tsahon wannan shekarun?”.
“Ranki ya daɗe ai auren ya mutu ne a wancan lokacin. To domin neman na kaina saina samu aikatau ɗin dan nayi saboda iyayena duk sun rasu ni marainiyace”.
“Ƙwaɗayin zama gidan masu kuɗi yasa baki sake tunanin sake ƙara aure ba kenan?”.
Shiru tayi kanta a ƙasa ta kasa bada amsa. Shima Dawood da yay maganar sai ya shareta da ga haka ya sake jeho mata wata tambayar.
“Waye ya kaiki gidan?”.
A take ta ruɗe jikin na rawa, sai in ina take ta kasa bada amsa. Hakan yasa Dawood daka matsa gigitacciyar tsawa. Fashewa Rabi tayi da kuka. “Dan ALLAH ku gafarce ni zan faɗa”.
Babu wanda ya tanka mata. Sai bindiga da little bee ta ciro a gefen ƙugunta ta dire a gaban Rabi. Hakan yasa ta kuma diriricewa. Cikin hadiye kukanta tace,
“Ranku ya daɗe ni bansan ainahin wadda tasa aka kaini gidan ba. amma naje ta hannun wata matace amma yanzu ALLAH yay mata rasuwa”.
“Oho, idan na fahimci amsar nan taki kenan dama an kaiki gidan ne da wata manufa? Ba wadda kike a wajenta bace tasa aka kawoki gidan!!”.
Yoohan yay magana a matuƙar zafafe. Maimaita mata Dawood yayi da hausa. Dan duk da Yoohan ya haɗa da kalmomin hausa a maganar Rabi bata fahimta da ƙyau ba. Amma shi Alhmdllh yana fahimtarta sosai tunda jin nasa yafi faɗi da baki.
A take Rabi ta ƙara rikicewa, dan har ga ALLAH tazatafa hoton Yoohan ɗinne kawai a wajen. Suma dai su Bily yanda yay maganar duk sai da ya sakasu kallonsa. Tebir ɗin Little bee ta daka da hannu, da tsawa tace, “Ki basa amsar tambayarsa malama kin ɓata mana lokaci”.
Jikin rabi na cigaba da rawa tace, “Ranka ya daɗe ba haka nake nufi ba. Ni dai kawai an kawonine na kula da mai ciki, daga haka babu wani dalili dana sani na rantse muku da girman wanda ya halicceni”.
A karan farko taji saukar mari mai gigitarwa a fuskarta. Kafin ta dawo hayyacinta Dawood ya ƙara mata wani. Sannan kuma Bily dake zaune duk tana kallonsu ta hanata kuka. Dole Rabi ta haɗiye hawayenta sai ajiyar zuciya.
Dawood yace, “Inhar zakiyi mana ƙarya to zakiyita amsar irin waɗanan marukan babu ƙaƙƙautawa. Wa kikema aiki a gidan?”.
“Wlhy yallaɓai iya gaskiyata nake faɗa muku. Bani yima kowa aiki sai Hajiya Firdausi matar Sheikh Sooraj ɗin”.
Sai a yanzu Umar yay magana. “Eh ansan dama ita kikema aiki a zahiri. a baɗini kuma akwai ogarki mai sakaki shiryamata sharri ita da tilon ƴarta. Bayan ƙyautatawar data dinga miki a rayuwarki na tsahon shekaru goma sha takwas”.
Dawood ne ya sake fassara mata. Dan haka cikin rawar harshe da kuka mai cin rai tace, “Na rantse da ALLAH. wlhy tallahi ban taɓa cutar da Hajiya Firdausi da zuriyar ta ba. Ko Nu’aymah da muke yawan faɗa wani lokacin ina takalartane kawai wlhy saboda nasan bata barin saita kwana. Amma bada wata manufaba. Ko a mafarki bana fatan na cutar da waɗan nan bayin ALLAH ai balle a zahiri”.
Cike da ɗaurewar kai suka shiga kallon juna. Amma duk da haka bayan Dawood ya gama sanarma Omar abinda ta faɗa sai Umar ɗin ya bada vr ɗin nan na kwanaki da sukaji tare da Nu’aymah. Aka kuma tabbatar mata a wayar wanda aka samu.
“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un ni Rabi. Wlhy wlhy kinji na rantse ni ban taɓa waya da mai aikin Nu’aymah ba. Hasalima sam ban santaba tunda randa akazo za’a wuce da ita abuja a sashen hajjo Umm taje ta sameta itama. Yanzu haka ko zaku kasheni bazan iya nuna fuskartaba balle harna samu Number ta nayi waya da ita akan Nu’aymah. To niko idan ta faɗamin halin da Aymah ke ciki gidan aurenta ribar mi zanci bayin ALLAH?”.
Tsawa little bee ta daka mata. “K bama son rainin hankali. Idan kince bake bace waɗan nan lambobin dake akan wayarki harda ta Uwaliya ɗin na uwar waye? Wa kuma ya sakasu da har zaiyi zaman magana da su a wayarki batare da kin saniba?”.
“Wlhy iya gaskiyata nake faɗa muku. Ni yanzu haka ko waya zanyi ma sai naba Muhammad ya dubamin lamba. Dan shine kemin sebi idan ko zansa lambar wani ɗan uwana. Idan kuma zanyi kira shima ke dubamin abinda ya samun dan banyi boko ba. Da Nu’aymah ko Adawiya kemin, to sai suyita jamin rai, shine na koma bama Muhammad ganin ya iya. Amma ni lambar ma ƴan gidan bata kowa gareniba wlhy”.
Hannu Dawood ya ɗaga zai ƙwaɗa mata mari Bily ta dakatar da shi. Dan ita duk shirun datai musu nazarin komi takeyi. sannan kuma Jay ma duk yana saurarensu daga office ɗinsa ta hanyar na’ura. Shinema yay saurin cema Bily ɗin kar Dawood ya mareta yanzun ta hanyar abibda ke a kunnenta da su basu fahimta ba.
Dakatawa kuwa Dawood yayi yana huci. Bily dake kallon Rabi cike da nazari tace, “To amma ranar da Nu’aymah tai bleeding ko zamu iya sanin miya faru? Dan bincikenmu ya nuna mana kece kika bata abu na ƙarshe tasha a gidan. Daga haka ta fara ciwon ciki sai jini kuma ya ɓalle”.
Shiru Rabi tayi tana tunani dan tama manta. Sai zuwa can kuma tace, “Lallai kuwa ranki ya daɗe kamar anyi hakan. Ta sakani na dafa mata ruwan shayi baƙi”.
“Kenan a ciki kika saka mata maganin zubda jini da aka ɗauka cikine ta zubar??”…………..✍
Tofa masu karatu man kai na fa zai fara malalewa a dalilin amsoshin Rabi, nama rasa mizan tunano kuma. amma bari mu bita muji wace amsa zata bada a gaba??????????.
ZAFAFA BIYAR 2021
Hafsat miss xoxo????
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).????????
Mamu gee????
MIN ƘALB!!????????
Hafsat rano????
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!????????
Safiyya huguma???? SIRAƊIN RAYUWA????????
Bilyn Abdull????
SARAN ƁOYE????????
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka????????????????
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????
09033181070
????????????????????????????????????????
TEAM—-ZAFAFA BIYAR????????????????
ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????.
[7/3, 3:48 PM] Queen Meenali????: LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana????????.