SARAN BOYE COMPLETE

Yoohan na ganin motocinsu sun gama wucewa ya sauke ajiyar zuciya mai kauri, A ɗaya daga kujerun dake a waje ya zauna hannayensa duka dafe da kansa. Sai yanzu komai ke dawo masa a ƙwaƙwalwa tamkar almara. Dan ɗazun su Addah na bayani ne little na fassara musu shi da Umar, duk da shi yana ɗan jin hausarma kaɗan-kaɗan yanzun.
Kusa da shi Umar yazo ya zauna shima yana sauke nasa ajiyar zuciyar. Yoohan bai motsaba balle ya kallesa. Shima sai bai damuba ya fara magana a hankali. “Haka mafi yawancin mutanen da suka samu ɗaukaka suke. Sai kaga na nesa da su na matuƙar sonsu da begen kasancewa da su. Amma waɗanda ke tare da su mafi yawancinsu ba son gaskiya suke musu ba. Ƙaso ɗaya bisa uku a ciki zaka samu suna musu ƙauna ta tsakani da ALLAH. Kaso biyun kuwa sai kaga suna raɓe da sune bisa wannan ɗaukakar da ALLAH yay musu. A zahiri kuwa su zugasu da nunama duniya babu kamarsu, a baɗini sune masu musu SARAN ƁOYE. lallai waɗanan mutanen masu zagon ƙasa suna ɗaya daga cikin jarabawar masu mafi yawan ɗaukaka”.
Ajiyar zuciya Yoohan ya sake saukewa. Ya ɗago ya dubi Umar a karon farko, idanunsa sunyi jajur. Ga barci ga yunwa ga gajiya. Shi kansa Umar ɗin a galabaice ya ke. “Zancenka haka yake Umar, bazan ɓoye makaba al'amarin mutanen nan ya sake saka tsoro a zuciyata gaba ɗaya, nasake jin tsoron halin mutum da ayyukansa. Wannan wane irin bushewar zuciya ne haka? Su da ya kamata su zauna suyita godema ALLAH bisa ni'imar da yay musu ta rayuwa, su dinga ibada sai suka zama masu butulcewa ta hanyar cutar da wanda shi ya kusan ƙare tasa rayuwarne a ƙyautata tasu da ta ƴaƴansu. Umar wai miyasa ɗan adam keda manta alkairi da yawan butulci ne?. Miyasa ɗan adam yafi yarda da biyayya wa huɗubar shaiɗan akan dokar ALLAH ne?. Miyasa ɗan adam yafi yarda ya zama mai samu bamai sadaukarwa ba? Miyasa mafi yawan mutane sunfi sha'awar cutar da wanda suka ƙyautata musu amma sunajin tsoron mai munanasu?. Ko addu'a mutum zaiyi, sai kaji yace ALLAH ka tsareni daga sharrin masu sharri. To miyasa bama addu'ar ALLAH ya karemu da aikata sharri ga masu ƙyautata mana ne?”.
“Wannan shine halin ɗan adam ɗin da ake faɗa Dude, munada son kanmu, duk kuma mutum mai son kasa zakaga shine kullum a cikin wahalar nema da faɗuwa. Dan bazai taɓa doguwar nasara ba. Daya samu take kufece masa. Amma saboda bushewar zuciya gobe ma sai ya koma sake neman sa'a. Kowane addini akwai na banza akwai na gari. Irin waɗan nan mutanen suke ja ana zagin addinin islama bayan shi kuma addinine mai koyar da ƙyawawan ɗabi'u. Ko shekara banyi da shiga musilinci ba, amma wlhy Yoohan na fahimci babu wani addini dake gogayya da shi akan koyar da ƙyaƙyƙyawar rayuwa. Komai musilinci ya haɗa. Amma ka duba su da keda ilimin sani a tsahon shekaru sunfi zaɓar su saɓama ALLAH bisa son zukatansu”.
Sosai zukatansu Yoohan suka ƙara rauni da wannan al'amari. Imani da tsoron ALLAH ya sake shigarsu a zuciya da ɓargo. Suma kansu dai a wannan dare sunyi barci ne kawai badan jin daɗi ba.
WASHE GARI
Washe gari aka bama su baba malam damar shiga su duba Abban Abdallah. A lallai duniya abin tsoro. Bawa daina cikama rayuwa baki kai ba komai bane. Duk damar da kaga ka samu a rayuwa da ga rahamar ALLAH ne. Amma wlhy idan yaso ko ƙyaftawar ido baka isa gittawa ba. A jiya iyanzu shine zaune tare da ƴan uwa da iyalansa. Amma yau gashi babu ko ƙyan gani a fuska saboda tsabar jigata da rayuwarsa tayi. Ita kanta Addah jikin nata babu daɗi.
Duk wanda ya shiga duba Abban Abdallah sai kaga ya fito da kuka. Hakan yasa dama Yoohan bai bar Nu'aymah a wajenba. Suna zuwa ma ya jata wai tazo suje wajen awo. Bata fahimci wayo yake mataba ta bishi. Sai ya kaita office yasa aka kawo mata abinci. Duk da tace masa ta ƙoshi, dan basu fitoba sai da Umm ta bata abinci ya dage sai taci. Dole taci kaɗan dan ya barta. Sauran kuma ta bashi dan ta fahimci shima yana buƙatar a tsaresa yaci abincin.
Zuwa ranar dai dukan ahalin gidan sunsan halin da ake ciki, ƴaƴan Addah dake aure da ƙannen Abdallah ma duk sunzo. Ansha sabon kuka dai kam yau ma. Daga ƙarshe baba malam dake ta ƙoƙarin danne tasa damuwar yay musu nasiha da nuna musu muhimmancin ƙaddara. Ya tabbatar musu da cewar hakan jarabawane. Dan bazai yuwu dama a rayuwa a rayuwa babu jarabawa ba. Ya hana kowa kakkausan lafazi akan su Addah, dan kuwa shi a take ranar ya tabbatarma da kowa cewar ya yafe musu. Sai su cigaba da musu addu'ar ALLAH ya basu lafiya kawai.
Baba malam ya ƙara kima a idanun iyalan Addah da Abban Abdallah. Musamman ma Abdallah da har ran yakejin tsanar mahaifinsa da Addah. Sunso su gurɓata masa tunani ALLAH ya hana hakan. Dan bayan Addah ta ɓale a cikinsu Abbansa sake zaunar da shi yay ya ɗora masa sabon karatu akan maido da Nu'aymah rayuwarsa koda ta ƙarfin tuwo ne. Wannan shine dalilin da yasa dinga bibiyar rayuwarta. Ko a randa ya bisu shopping mail ɗin nan da nufin kidnapping Nu'aymah ya je. Sai akai rashin sa'a Yoohan ya gansa tun lokacin da suke faɗansu da Aymah harta faɗa a jikinsa. Dai-dai lokacin da yake cemata ta tara musu mutane idonsa ya sauka akan Abdallah ɗin. Har suka shiga mail ɗin kuma yana sane da shi. Sannan yana akan sani yabar Aymah a wajen ita kaɗai dan yaga mi Abdallah zaiyi?.
Lokacin da Nu'aymah taji ƙamshinsa da gittawar mutum Abdallah ne, yana gab da isa gareta Yoohan ya jasa baya da ƙarfi ya toshe masa baki suka koma ta bayansu. Cikin fushi Abdallah ya hakaɗe Yoohan ɗin yana faɗin. “Kai shasha minene haka?”.
Murmushi Yoohan yayi sannan ya haɗe fuska. Cikin ƙanƙance ido ya nuna Abdallah da faɗin, “Idan ka bari gangancinka ya ɗora zuciyarka bisa dokin shiga gona ta. Na rantse da ALLAH Abdallah sai na dawwamar da rayuwarka a dana sani. Na fika hatsabibanci fiye da yanda kake tsammani. Dan haka ka kama kanka kafin na ajiye mutuncin ahalinka da nake gani gefe na ɓata rayuwarka. Karka zata bansan wanene kai ba da ubanka. Ka kiyayeni kona fallasaku duniya ta sanku da aiyyukanku akan ahalinku”.
Yana gama faɗa yabar wajen, shine yaje yaja Aymah suka wuce wajan biyan kuɗi.
Tabbas kalaman Yoohan sun girgiza Abdallah. Hakan yasa ya janye daga bibiyar Nu'aymah. Dan dama can shi mutum ne da a rayuwa bai son yawan matsawa kansa, sannan baison fitina sam. Wannan halayyar tasa tasa lokacin yana yaro ake ganinsa matsoraci a cikin yara ƴan uwansa. Dan da gaske tabbas yanada tsoron faɗa a rayuwarsa. Dai-dai da film ɗin faɗa Abdallah baya zaman kallonsa sam saboda baya ra'ayin fitina, daya zama saurayune ma dai ya fara canjawa. har zuciyar tasa tai tauri saboda zuciyar gidansu ta gado.
Ƙin faɗama Abbansa zancen yayi. Amma yayi ƙudirin janye jikinsa daga bibiyar Nu'aymah. Daga bakin Abbansa yaji samuwar Uwaliya, dan a randa aka kawota a ranar Abbansa ya tattauna da ita tun a office kafinma a kaita gidansa. Uwaliya akwai son kuɗi. jin maƙudan ƙuɗin da Abban Abdallah ya tabbatar mata zata samu akan kaso masa auren Nu'aymah da kawo musu dukkan bayanai a kanta yasa ta amince zatayi. A ranar ya bata rabin kuɗin, sauran kuwa sai aiki ya kammala.
Tasha murna a ranar, ta kuma tabbatar da lallai ta shigo Abuja da ƙafar dama. Yo ko Yoohan ɗin sukace ta bibiya akan waɗanan kudin ai ta halakashi kuwa.
Wannan shine dalilin da yasa ta fara musu aiki. Sai dai abinda bata saniba suna amfani da wayar Rabi da muryartane idan suka kirata.
Lokacin da aka wuce da Nu'aymah Austria da gaske Abdallah yaje dubatane saboda son da yake mata. Sai dai baiso Yoohan da su baba malam su gansa. Shine yaso su fara haɗuwa da Abbansa. koda suka haɗun Abban ya dinga masa faɗan da har zancen Nu'aymah ya shigo ciki saboda Addah da tazo taga Abdallah ta zata cutar da Aymah zasuyi. Anna ne Yoohan yaji da Hajjo sukaji, abinda kuma basu saniba shine baba malam ma ya gansu, ya kuma jisu. amma sai bai taɓa nunawa ko da Umm ba balle su..........✍
[7/6, 9:39 AM] +234 913 412 2711: LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana????????.
No. 75
………….Su Jay dai sun wuce abuja, amma duk da su Addah na a asibiti suna a ƙarƙashin kulawar hukuma ne. Bayan wucewar su Jay shi ma Omar da Yoohan suka wuce da yamma. Ya bar Nu’aymah anan kano saboda Umm bata da lafiya. Har yanzu ta kasa fida daga ruɗanin data shiga. Ga jininta yaƙi sauka yanda ya kamata. Ita kanta hajjo jininta ya hau sosai. Sai dai ita Alhmdllh bai kai na Umm da komai yazo mata a yanda bata zata ba. Bama Umm kaɗai ba hatta da ƴan uwan Umm dana Addar wannan al’amari yay masifar rikita tunaninsu da basu tsoro. Anatama Addah ALLAH wadarai da wannan hali nata. Su Hajarah kam sunyi kuka har sun rasa hawayen zubarwa. Musamman Kubrah da dama ba daɗin zaman gidan mijin take jiba. Fitinar yau daban ta gobe daban.
Yanda gidan dai yay wani iri daga shigowa zaga fahimci akwai matsala. Baba malam salla kawai ke fiddashi. Da an idar yake dawowa gida. Komansa ya tsaya cak. Dan duk da daurewar da yakeyi a bala’in gigice ya ke da al’amarin. Bai taɓa ƙawowa a ransa cikin ƴan uwansa za’a samu mai wannan tunaninba akan dukiya dauɗar duniya. Yayi kuka bana wasaba a ɓoye, har ji yake gaba ɗaya ƙasar ta fita masa a arai.
_★★
Su Yoohan na isa Abuja suka iske sabon tashin hankali. Dan sun iske gidansu zagaye da jami'an tsaro. Da ƙyar ma aka barsu suka shiga saboda sanin Yoohan ɗansa ne. Cikin tashin hankali Yoohan ya ƙarasa falon inda ya tarar da ƙannensa duka da mama debora a hagitse. Suna ganinsa kuwa duk suka taso kansa a guje suna rusar kuka. Su duka rungumeshi sukayi har mama debora da Gebrail dake gudunsa a da.
Kallonsu kawai Yoohan keyi cike da tsoro, maganama ya kasa yi. Sai da Umar yay dauriyar cewa, “Granny wai mike faruwa hakane? Ku sanar mana Please. Gida zagaye da ƴan sanda. Gaku kuma cikin tashin hankali. Ina su papa suke ne?”.
Cikin matsanancin kuka joy tace, “Sun gudu Brother Richard”.
“Sun gudu kamarya? Ban ganeba nikam Joy?”.
Sakin Yoohan duk sukayi, mama debora ta kama hannunsa ta zaunar a kusa da ita. Shima Umar ɗin ya zauna. Sauran yaranma duk zama sukayi bisa umarnin mama debora. Tana sharar hawaye ta fara musu bayani.
“John munata kiran wayarka tun jiya ai amma mun kasa samunka. daren shekaran jiya kusan ƙarfe goma na dare wani mutum ya shigo gidan nan a kiɗime jikinsa jina-jina saboda harbi da akai masa. Lokacin duk munyi barci, kururuwarsa ta sakamu tashi batare da mun shirya ba duk muka fita compound. Tun a yanda mahaifinku ya ambaci sunansa a kiɗime na fahimci ya sanshi. Dan gaba ɗaya ya ruɗe shi da Chioma da guards ɗinsu. Shine ya sakamu komawa ciki akan dole batare da munji mike tafe da wannan mutumi dake a cikin jini ba. Muna falo tsaitsaye mun kasa komawa ciki mu kwanta sai ga shi sun shigo. Duk ɗakunansu suka shiga batare da sunce mana komaiba. Sai kuma suka sake fitowa a rikice. Mahaifinku ya rungumeni yana faɗin, karna damu na masu addu'a kawai, ga ATM card ɗinsa nan duk abinda muke buƙata Gebrail zai dinga ciro mana kuɗi. Daga haka suka fice zuwa garden. Ban taɓa sanin akwai wata hanyar fita gidannan ta garden ba sai a ranar. Dan sai bayan wucewarsu da kusan mintuna talatin ƴan sanda suka shigo anguwarnan sunata harbe-harbe. wasu suka shigo nan gidan suna nemansu harda guards ɗinkun nan. Sai lokacin mukasan guduwa sukayi harsu Solomon. Amma an kama guards uku a cikinsu. Su kuma ba'asan inda sukeba har yanzun”.
Wata irin masifaffiyar zufa ce ke ketoma Yoohan ta ko ina, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un yaketa faman maimaitawa. Shi kansa Umar zancen yay masifar rikita tunaninsa. Batare da Yoohan yace komaiba ya kama hannun Umar suka haye sama. Duk binsu sukai da kallon mamakin mizaiyi?. Bai saki hannun Umar ba sai da suka shiga sashensa can cikin ɗakin motsa jikinsa. Inda tanan yana iya hango duka ƴan sandan dake a compound ɗin gidan da anguwar ma.
Cikin matsanancin fushi ya yarfar da hannun Umar sannan ya tsatstsare sa da jajayen idanunsa. Muryarsa da tsananin kaushi da fushi yace, “Umar mi kuke ɓoye min kai da Matata akan iyayena?. kar kaimin ƙarya, dan ba ita nake buƙataba a yanzu na roƙe ka”.
Yanda ya ƙare maganar muryarsa na rawa kamar zaiyi kuka da haɗe hannayensa waje guda kuma sai zuciyar Umar ta ƙara raunana. Hannayen ya riƙe duka a cikin nasa ya sauke. “Yoohan anzo gaɓar da basai ka roƙeniba zan sanar maka. Sai dai inason ka fahimceni Please. Nima bani da wani zaɓin daya wuce hakan”.
Komai Yoohan bai ceba, saima cire rigarsa da yayi ya hau wani machine ɗin motsa jiki ya fara da sauri-sauri. Huci Omar ya sauke tare da fara bama Yoohan labari. Tun daga abinda ya fara ji akan kashe Nu'aymah da papa ya bama Dr Mateo kwangila har zuwa ɓoyayyun harƙalloli daya fahimci papa nayi a ɓoye. Kamar safarar miyagun ƙwayoyi da cocaine. Safarar makamai, satar yara yana tarasu a wani gida acan ƙauyensu........
Ihunsu Mama debora daya cika gidanne ya saka Yoohan dan Umar fita da gudu zuwa ƙasa.
Cike da firgici da tsoro Yoohan da Umar ke kallon Little bee da tawagar jami'an hukumarsu. Ta haɗe fuska matuƙa, babuma alamar tasansu. A fusace Yoohan yace, “Lafiya kuwa?”.
Uffan Little bee batace masa ba. Sai ma i'd card ɗinta kawai ta nuna masa. Sannan ta ɗora da faɗin, “Muna buƙatar shiga ɗakin Mr Goshpower domin yin bincike”.
Magana Yoohan zai sakeyi Umar ya girgiza masa kai alamar karya ce komai. Hannayensa duka biyu ya tura cikin aljihun wandansa ya koma jikin bango ya jingina saboda jiwa dake neman yaddashi a ƙasa.
Da Gebrail sukai amfani ta hanyar ɗora masa bindiga akai. Tuni fitsari ya jiƙe gaban wandonsa kuwa. Babuko kwana-kwana wajen kaisu har sashen papa. Tun a falo suka fara bincikensu. Yoohan baiyi niyar binsu ba, amma sai Omar ya kama hannunsa suka shiga. Basu sami komai a falon ba sai cctv dake a ɓoye. dan haka suka wuce cikin bedroom. Akan idon su Yoohan akaima ɗakin dalla-dalla. Ta hanyar tsabar ƙwarewar aiki su little suka gano ɓoyayyar drawer ɗin nan ta sirri dake a jikin bango. Sai dai kuma garƙame take da security, gashi kuma basu sani ba. An gwada password kala-kala baiyiba. Daga ƙarshe suka yanke shawarar yin amfani da na'urar fasa ƙarfe ko wane irine. Ta wannan hanyar aka fasa wajen. Sosai Yoohan ya firgita da ganin kalolin bindigu, da harsasai kala-kala. Sai tarin hodar ibilis da ƙwayoyin shaye-shaye masu matuƙar haɗari.
Kasa daurewa Yoohan yayi, sai da ya furzar da wani zazzafan hucin da sai da kowa ya juyo ya kallesa. An ƙara bibbincika ɗakin sosai kafin su kwashe duka kayan da suka samu ɗin sannan suka sakko ƙasa inda su mama debora keta faman kuka. Ganin makaman kuma ya sake rikitasu fiye da farko.
Koda suka fito sai suka shiga bincike gaba ɗaya lungu da saƙo na gidan, su dai su Yoohan suna binsu ne kawai da idanu. Sai da suka tabbatar da basu sake samun komaiba sannan suka tattara waɗanda suka samu ɗin zuwa mota. Sun buƙaci tafiya da wasu a cikinsu zuwa asalin ƙauyen su Yoohan ɗin, zakuma su cigaba da riƙesu har sai papa da madam Chioma sun bayayana kansu.
A take falon ya sake ruɗewa da kukan su mama debora. Ganin yanda suke neman fita hayyacinsu Yoohan ya ce zai bisu kawai shi da Gebrail. Kuka harda kururuwa Gebrail ya fashe da shi. Abun zat-tausayi zad-dariya. Haka su Mama debora naji na gani aka wuce da Gebrail daketa kwasar kuka da Yoohan.
Yoohan bai sake fahimtar al'amarin mahaifin nasu babba bane sai da suka iso airport, anan ma wasu jami'an suka tarar da alama jiran isowarsu sukeyi. Babu wani tsayawa ya akai ya za'ai aka shiga da su jirgi. Gebrail na nane da Yoohan cikin tashin hankali. Koda suka isa canma sun iske wasu jami'an tare da helicopters biyu. Nanma babu ɓata lokaci suka shiga zuwa can ƙauyensu. A canma sun iske garin a ruɗe sosai, dan uban batakashi akeyi tsakanin jami'an tsaro da yaran su papa. Gaba ɗaya ƙauyen a harmutse yake, dole aka bar su Yoohan a helicopter ɗin su little kawai suka firfita suma da nasu bindugun. Sai a yanzu ne fuskar Yoohan ta nuna tsantsar ruɗani. Gaba ɗaya komansa ya sare akan wannan al'amari. Lallai da alama mahaifin nasu ya jima cikin wannan mummunar harkar batare da su sun sani ba. Haba no wander yake ganin mahaukatan kuɗi basa gajiya da shiga accaunt ɗin papa. Sannan sam bayajin fargaba ko ciwon fitar da kuɗi wajen musu hidima ta bajinta.
Kallo dai iya kallo su Yoohan sun yisa. Daga ƙarshe su Little bee suka sami nasarar cafke gaba ɗaya yaran papa da su Uncle Godwin da aka ritsa a garin tun jiya. wasu sun sami raunika, wasu ko ma an kashesu. A cikin su little ma wasu sun sami raunuka.
Daga haka aka fasa ƙaton gidan da su papa ke ajiye yaran da suka sato ciki. ‘Hazbunallah’. Yarane mata da kananu, sai wasu baƙaƙen ƙartan bayi da kallonsu kawai ya ishi mutum amai, wasu da tsohon ciki, wasu cikin ƙananu ne, wasu kuma suna a tsaka tsaki. Sai jariran da aka haifa da har an gama cinikinsu ga masu buƙatarsu.
Tsabar tashin hankali little sai da tayi kuka ita da sauran ƴan uwanta jami'ai mata. A take Dawood yay kiran Jay ya tabbatar masa al'amarinfa babbane gaskiya. Ga ƴan jarida sunyi caa suna neman bayanai. Kamar yanda I.G na ƴan sanda ya kasance a wajen dole Jay ma ya taho ƙauyen da tawagarsa su Hafeez. Hakama gwamnan jihar dole ya shigo ƙauyen, dan kuwa kowa yasan da taimakon su papa ya hau mulki. Dan papa nada matuƙar ƙarfi cikin jahar tasu musamman daya kasance yana riƙe da muƙamin shugaba (Pastor).
Dole aka kawo manya-manyan motocin guda uku aka kwashe kaf mutanen dake gidan zuwa can babban birnin jihar. Su Dawood kuma suka shiga yima gidan filla-filla da bincike ta ko ina. daga haka suka sake kwasar jiki zuwa ainahin family house ɗin su Yoohan ɗin da suke zama idan sunzo garin. Ananma an samu abubuwa da dama, harda ɗakin sirri dake danƙare da Computers da suke gudanar da ayyukansu na yima mutane kutse, da zuba uwar sata a asusun bankuna dana mutane. A takaice dai papa shugabane mai zaman kansa na ƴan Yahoo.
Tuni zuciyar Yoohan ta gama bushewa tayi tauri akan wannan al'amarin. Binsu kawai yake da kallo tamkar mai kallon film a television. Shi ba zuwa ƙauyen yakeba sosai saboda karatun daya tafi ƙasashen ƙetare yayi. Bayan ya kammala kuma aikinsa baya bari sa samun nutsuwar irin waɗan nan ziyarce-ziyarcen. Idan ka gansa a ƙauyen sai lokacin Christmas da hutun ƙarshen shekara. Wannan kam a ko ina yake a duniya dolene sai yazo bisa sharaɗin papa. koda baizo Christmas ba zaizo a kwanakin ƙarshen shekara yayi new year. To mafi yawancin lokaci ma sai dai ya samesu anan. Bai taɓa damuwa da sanin sarrin duka gidanba. Iyakacinsa ɗakinsa da garden. Sai ko compound. Yawo ma a ƙauyen sai idan su Osin na tare da shine yake fitarsa. Amma shi kaɗai baya zuwa ko ina. Yafi buƙatar yay zamansa a gida.
Tone-tone dai kam an yisu a ranar game da sirrikan papa masu ban mamaki da tsoro. Hakan yasa su Jay fahimtar riƙe su Yoohan bazai taɓa saka Papa kawo kansa hannun hukumaba. Dan haka suka sallamesu su koma gida kawai. Dan aikine babba wannan ya wuce wasan yara. Shi dai Gebrail yaji daɗin barinsu da akayi. Yoohan kam gaba ɗaya kansama ba aiki yakeba a wannan lokacin. Dan brain ɗinsa ta toshe.
Tun a wannan daren ƴan jarida da masu alhakin faɗin albarkacin baki suka fara kayayatu. Inda ƙungiyar catholic tai azamar fara fitowa ta banbanta tafiyarta data goshpower. Sun tabbatarma duniya bada yawunsu ko saninsu yake aikata duk wannan al'amarin ba. Hakama gwamnan jiharsu da manyan ƴan siyasa sun fito sun nisanta kansu da papan kai tsaye.
Tofa abin magana ya samu lallai da gaske. Dan ƙasar tuni ta ɗauka tare da kafafen yaɗa labarai na televisions da redios. Yanar gizo dama duk wata kafar maida yanda akayi. Videos ɗin da wasu a cikin ƴan ƙauyen sukai ƙarfin halin ɗauka tuni ya fara yawo a yanar gizo. Yayinda ƴan jaridu suka fara tabbatar da cewar mafi yawan yaran da aka samu a gidan nasu papa yarane da aka sata daga arewacin ƙasar. Ƙalilanne a cikinsu suka fito daga kudanci. Tofa magana ta girma.
__★★
Baba malam ne ya fara cin karo da wannan babban al'amari a labaran ƙarfe goma na dare da yake kallo. Sai ga Nu'aymah data shigo kawo masa shayin da rabi ta dafa masa dan baya iya cin abinci sosai itama ta ganema idanunta.
Da ga ita har baba malam ɗin kasa magana sukai, sai tv da suka zubama idanu da tsananin mamaki da al'ajabi. Ganin tayi tsaye ta kasa zama baba malam yace ta zauna saboda ba ita kaɗai bace. Zama tai a kujera jikinta har rawa yake saboda ganin yanda aketa bata kashin ruwan harsasai a ƙauyen su papa da aka nuna. Idonta bai ganar mata Yoohan ba sai lokacin da akaje family house ɗinsu. Anan kuma Umm ma ta fito ta samesu. Duk da batajin ƙarfin jikinta itama saita zauna zaman kallo.
Can sai ga Hajjo a rikice itama ta shigo tana ƙwalama baba malam kira. Sai da Rabi ta sanar mata yana falonsa sannan ta nufo nan. Tunkan ta shigo ta fara faɗin, “Ɗan malam kaga kuwa tsiyatakun da aka tono yau na surikinka?”. Tana ida shigowa taga suma abinda suke kallo kenan ta shiga tafa hannu da jera salati. A kusa da Nu'aymah ta zauna suka cigaba da kallon tare.
Kafin kace mi sai ga kiraye-kirayen waya sun fara shigoma Baba malam a wayoyi. Yasan kwanan zancen, dan haka yaƙi ɗaga wayar kowa. Kansama gaba ɗaya sai ya ƙara ɗaukar zafi. duk da yasan papa riƙaƙen ɗan harƙalla ne baiyi xaton al'amarin ya kai haka girma ba. Dan yasan papa ne shekaru ashirin da takwas da suka shuɗe a jami'ar ƙasar France, lokacin yana haɗa degree ɗinsa na biyu a can. Shima papan yazo ne wani course na wata tara. Tunda yazo makarantar a tantirinsa yazo dama. Dan karatunma asha ruwan tsuntsaye yake masa. Duk wasu abokan banza zaka samu papa da su, dan adalilin takurama wata yarinya mai suna Sadiya ƴar ƙasar Niger da papan yayi akan dole sai tayi soyayya da shine ya zama sanadiyyar sanin juna da sukai da baba malam ɗin. Kasancewar baba malam shine shugaban mss na makarantar a lokacin duk da ba wani ƙarfi ne dasu ba sai yay tsaye a kan lamarin papa da Sadiya. yayma papa gargaɗi sosai akan ya fita harkar yarinya ya barta tai karatunta. Idan ba hakaba kuma zai ɗauki mataki a kansa. A lokacin papa baice komaiba sai dariya da suka shiga sheƙawa shi da yaransa suna busama baba malam hayaƙin taba da suke sha. Baba malam dai ya ja musu gargaɗi ya kama gabansa. Ba'a rufa wata ɗaya da wannan al'amari ba tsakanin papa da baba malam sai baba malam yaga wai papa ya zama Pastor. Harma yana kula da church ɗin cikin jami'ar. Abin ya ɗaure kan baba malam sosai, dan ya fahimci lallai da biyu goshpower ya samo wannan muƙamin.
Baba malam dai baice komaiba, dan sunama haɗa kwanaki sama da takwas basu haɗuba kasancewar kowa da sabgar gabansa. Sai dai tunda Goshpower ya zama Pastor a cikin jami'ar ƴar tsama mai ƙarfi ta shiga tsakaninsa da baba malam. a kuma lokacin akaima Sadiya fyaɗe tare da kasheta. Wannan al'amari yayi masifar girgiza baba malam dama sauran musulmai da suke a jami'ar. Dan kowa yasan goshpower ne zai iya aikata hakan ga sadiya. Su baba malam sun kai ƙararsa ga hukumar makaranta, an kuma amshi ƙorafinsu a zahiri, amma babu alamar za'a ɗauki wani mataki. Hakanne ya harzuƙa zuciyar baba malam yaje ya samu Pastor goshpower da kausasan maganganu. Amma abin mamaki ko ɗar papa baiyiba. Hasalima da bakinsa ya sake jaddadama baba malam cewar shine yayma Sadiya fyaɗe ya kuma kasheta. Tunda taƙi yarda ta bashi kanta da arziƙi shiyyasa ya ƙwata da ƙarfi dan yana ƙwaɗayinta sosai. Kasheta kuma da yayi yayine dan yaga mi baba malam ɗin ya isa yayi?.
Baba malam akwai zuciya, hakan yasa a take ya fara dukan goshpower da iya ƙarfinsa. Kafin kace mi makaranta ta ruɗe da ihun ɗaliban dake ta wajen da abin ke faruwa. Kowa yayi mamakin yanda baba malam ke dukan goshpower. Dan babu wanda yay tsammanin zaiyi wannan ƙarfin. Musamman da ake ganinsa shiru-shiru baida kwaramniya sam a cikin ɗalibai. Hasalima ko ƙwaƙwaran aboki baida shi. Jina jina baba malam yayma papa a wannan lokacin, dan da ƙyar security ɗin makaranta suka amshi goshpower a hannun baba malam. Harma wasu na tsammani da zaton papa ya mutu.
Kwana biyu da yin wannan rikici abin mamaki sai ga takardar sallama baba malam ya samu daga hukumar makaranta. Babu wanda yay kiransu ya zauna dasu domin neman ba'asin yanda akayi? Musulman ɗalibai dake makarantar hankalinsu ya tashi akan wannan rashin adalci da akaima baba malam. Amma sai shi baba malam ɗin ko a jikinsa. Dan dama koda basu koresaba yayi alƙawarin bazai ƙarasa karatunsa a wnann makarantarba, tunda har za'a iya kashe rai suƙi nutsuwa suyi ƙwaƙwƙwara bincike akai su gano mai laifi su yanke masa hukunci. Tunda baba malam ya baro jami'ar France bai sake haɗuwa da goshpower ba sai a sanadin Yoohan. Wannan shine dalilin da yasa yay matuƙar mamaki akan papa bai isa haihuwar Yoohan ɗin ba sam. Sai dai kamar da Yoohan ke ɗanyi dashi ya sakashi yin shiru da tunanin ko acan wajen yima ƴaƴan jama'a fyaɗen ya samosa. Sai dai zuciyarsa sam bata yarda da wannan tunaninba. Musamman da yaga yanda Yoohan ke da ƙyawawan halayya abin koyi. Sai gashi a hankali ya fara fahintar akwai wani ɓoyayyen al'amari dake a tsakkiyar papa da Yoohan, daga hakane ya fara burin saka ido aka lamarin papa ta hanyar Nu'aymah da wasu ɓoyayyun hanyoyi nasa. To binciken nasa bai gama kaiwa inda yaso ɗinba Jay yazo masa da tambayoyi akan Yoohan ɗin shima. sai dai shirin nasu akan binciken papa ɗin bai ƙarasa kaiwa can ɗinba gashi ɓoyayyun halayen papan sun fito a idon duniya.
Tun a dare Nu'aymah ta shiga neman Yoohan amma ta gagara samunsa sam. Sai washe gari tana idar da sallar asuba ta kuma gwadawa anan ta samesa. Hankalinta ya tashi dajin muryarsa. Ta tabbatar masa ita dai zatazo abujan tunda taji kamar baida lafiya. Amma sai ya lallasheta akan tai haƙuri ta cigaba da zama a kano dan gidansu bazai zaunu a garetaba yanzu kodan halin da take ciki. Bazai yuwu taita ganin tashin hankaliba. Jin yanda yaketa lallashin natane yasa taɗanjin sassauci. Daga haka ta kira Umar dan ta ɗan ƙarajin bayanai. Shine ya tabbatar mata da karta damu Yoohan ɗin yana cikin ƙoshin lafiya damuwar abinda ya faruce kawai. Hakan kuma dolene a garesa tunda al'amarin yazo masa a bazata.
Baba malam ma ya kira Yoohan yay masa nasiha da kwantar masa da hankali, tare da faɗa masa yayta addu'a a ransa ALLAH zai sauƙaƙa musu waɗanan jarabawoyi da suka samesu a kusan lokaci guda.
★★★★
Jami'an tsaro sun cigaba da neman papa, tare da zaƙulo dukkanin abokan harƙallarsa ta ƙarƙashin ƙasa. Harma waɗanda suke a ƙasashen ƙetare. Yayinda zancen yara da ake zargin mafi yawansu ƴan arewacin ƙadar ne ya tabbata. Wasu tun suna yara aka satosu, wasu ko suna a manyansu. An saida wasu ga masu buƙata. Wasu kuwa ana kaisu wasu ƙasashen ƙetare batare da sauran sunsan mi suke yi acan ba.
Yarinyar da aka tattauna da ita tace, shekararta tara kenan a hannunsu. An satota ne a jihar Jigawa bisa hanyarta ta dawowa daga makarantar islamiyya a wani yammaci ranar litinin. Tana kuka tace, “Wani abu suka shaƙamin, wanda yasa ban sake sanin ina kaina ya keba sai a wannan gidan da kuka ganni a ciki. A randa na dawo hayyacina abinci kawai aka bani naci wani ƙato ya haikemin yaymini fyaɗe. Naga tashin hankalin rayuwa kala-kala a wannan tsakani, dan saida ta kasance kullum sai mutumin nan yayi amfani dani. Bai barniba sai da aka tabbatar da na samu ciki sannan. Sai a lokacin na fahimci ashe duk macen dake gidan hakane ke faruwa da ita. Waɗanan gardawa zasuyita amfani da ke ne har sai ka samu ciki. Ka gama wahalar rainon cikin a randa ka haihu a ranar za'a ɗauke yaron, watama ko ganin fuskar ɗan nata batayi. Kina haihuwa da sati biyu waɗan nan maza zasu koma yi miki fyaɗe har sai kin sake samun wani ciki”.
Kuka ya sarƙeta ta kasa ci gaba. Sai da tayi sosai wasuma a jami'an tsaron na tayata, harma da ƴan jaridar dake ɗaukar rahoton. Da ƙyar ta cigaba da faɗin, “A shekara tara dana samu ni yanzu haka haihuwata takwas, dan duk shekara ƙa'idane sai ka haihu, a yanzu hakama satina baifi shida dayin wata haihuwarba. Bana tantama kuma ƙila na ƙara samun wanu cikin ma”.
Ai Yoohan baima san sanda ya fashe da kuka ba, dan tunda yake a rayuwarsa bai taɓa cin karo da makamancin tashin hankali irin wannan ba. Sai gashi wai mahaifinsa shine tushen aikatawa. Abin takaicima harda sanin Momynsa. No wander ta mitsike idonta ta nema yin tarayya da shi duk da shiɗin ɗanta ne. A yanda yakejin zuciyarsa game da waɗannan yaran koshi ya ga Papa da Momy sai ya ɗaukesu ya damƙama hukuma ya rantse da ALLAH kuwa.
A kano ma dai su Abban Abdallah na cigaba da kasancewa a hannun kulawar likita. Duk da dai jikin nasa kam dai babu ƙyan gani dan gaskiya yanajin jiki, dan har yanzu baya iya gane kowa dake a kansa. Addah ma dai jikin nata wataran yayi sauƙi wataran yayi tsamari. Duk da tsiyatakun da suka tafkama baba malam kuma bai gaza wajen fidda kuɗaɗen da ake kula da lafiyarsuba. Sannan shiketa tausar ƴaƴansu da zantuka masu taushi, tare da ƙoƙarin ganin wannan al'amari ya zama sirri a tsakaninsu batare da sauran jama'ar gari sunsan tushensu ba.
Abban Mustapha dai ya riga ya saki Addah, sai baba malam ya hanashi faɗa mata ita da ƴaƴanta, sunbar maganar a tsakaninsu su manyan har sai ta samu lafiya kamar yanda baba malam ya roƙa mata alfarma. Dan yanzu bai kamata a haɗa mata zafi goma da ashirinba musamman daya kasance tayi nadamar kurakuranta. Halin datake ciki kaɗai ya isheta tashin hankali mai tsanani ai.
Aikoda gaske tashin hankalin da Abban Abdallah da Addah ke ciki ko shi kaɗai kam ya ishesu. Dan suna cikin tsananin azabar ciwo da magauta. Duk taurin zuciyarka ka gansu dole ka tausaya musu kuwa.
Haka kwanaki suka cigaba da shuɗawa. Su Adda ba faman jiyya a asibiti, jami'an tsaro na neman su papa ruwa a jallo. Masu maida yanda akayi na cigaba da tattaunawa da ƙara gishiri da magi akan al'amarin. Yayinda ƙungiyar kiristoci ma ta fito ta nuna cewar bata goyon bayan papa sam, sannan bata tare da shi. Hakama Pastors nata sharhi akan papan da tabbatarma duniya wamnan ba halin kirsata na ƙwarai bane aka samu papa da shi, dama suma ba ƙaramin matsi suke fuskanta daga garesaba ta ƙarƙashin ƙasa.
Duk wannan cece kuce da ake famanyi suna shiga kunne papa a maɓoyarsa shi da mike, Anthony, Joshua da Solomon, sai madam Chioma. Abinda yasa aka gaza samunsu shine ajiye duk wani layin wayarsu da sukayi, dama duk abinda zaisa a iya bibiyarsu. Godwin da sauran ne ke a hannun hukuma. Duk wahalar da sukesha kuma sunƙi faɗar ina za'a samu su papa saboda basu saniba suma.
Haka dai kwanaki suka cigaba da shuɗawa har Yoohan ya bar ƙasar saboda aikinsa, Nu'aymah ta cigaba da zama anan Nigeria bisa shawarar da baba malam ya bama Yoohan ɗin. Dan rashin kama su papa ba ƙaramin haɗari baneba. Musamman daya kasance Nu'aymah tana ɗaya daga cikin mutanen da a yanzu haka suke a cikin mummunan ƙudirinsa ita da baba malam ɗin. Yoohan kuwa yaji wannan shawarar duk da baiso yin nisa da iyalinsaba. Itama kuma Nu'aymah taji daɗin haka duk da kewar mujinta na tare da ita. A haka kwanaki suka cigaba da shuɗawa cikin rahamar UBANGIJI da jin ƙansa.
Cikin Nu'aymah ya shiga watan haihuwa, aiko su Umm nashan raki sosai da taɓara, Hajjo taita mata dariya da kiranta ragguwa. Yoohan kansa yanashan nasa shagwaɓan ta waya. Inko yazo ƙasar kuka rurus take tasasa a gaba tanayi wai itadai ta gaji wlhy a cire mata cikin nan. Takan bashi tausayi da dariya, sai dai bayayin dariyar sai yayta lallashinta da nuna nata tayi haƙuri saura ƙiris ai.
Ai ko zuwan ƙarshe da yayi yay kusan sati ɗaya sannan ya koma, kamar jira Aymah keyi ya wuce washe gari ta tashi da naƙuda. Wayyo zo kaga raki wajen masu haihuwa. Yoohan har ALLAH ya isa sai da yasha a wannan ranar????, takuma rantse bazata sake yarda da wani cikiba dan wannan haihuwa daga ita bazata sake ba. Tun hajjo dake tare da ita a asibiti itada Mama amaryar Abba Musbahu na danne dariyarsu har suka kasa saida sukayi. Baiwar ALLAH tako sha wahala sosai, har dai ALLAH ya sauketa lafiya ta sunkuto jaririnta dake ta faman canyara uban kuka.
Su Dr Aysha sun gyarata tsaf da bata dukkan kulawa kodan darajar mijin aurenta da iyayenta. Shima yaro aka gyara shi tsaf sannan aka fiddoma su Hajjo shi. Kowa sai ambaton masha ALLAHU yakeyi a baki da zuciya. Yayinda Hajjo ta saka Ahmad ya kira mata Yoohan wai itace zatai masa albishir. Aiko ita dince tai masa dan ya dai gane hausar tata saboda Alhmdllh zuwa yanzun harshensa na ƙara faɗawa. Rikicewa yay gaba ɗaya, dan yasan dai hajjo bazata faɗa masa Nu'aymah ta haihu ba danta zolayesa. Sai kawai ya durƙusa yay sujidar godiya ga ALLAH. Duk da a ransa yaji babu daɗi da sai da ya taho ta haihu. Sauƙinsa ma zai tafi hutun ƙarshen shekarane daman dan al'umar Christians nata shirin bikin Christmas.
Zuwa dare aka sallami su Nu'aymah da ɗan jinjirinta bayan an tabbatar da ingancin lafiyarsu, kai tsaye sashen hajjo aka nufa da Nu'aymah, duk da ita dai a ranta taso zama ne wajen Umm ɗinta. Kafin su kwanta Yoohan ya kirata a waya a karo na kusan huɗu kenan. Dama tuni hotunan ɗansa sun gama cika masa wayarsa. Ganin jaririn nan Abdallah har hawaye sai da yayi, dan da yanzu ɗansane fa Nu'aymahrsa ta haifa masa. Sai dai ƙaddara ta riga fata labarin ya canja daga yanda ya fara.
Video call sukayi mai tsaho ita da Yoohan, tana rungume da ɗansu da sai a yanzune ta samu damar zaman masa kallon sosai. Yayinda ran Yoohan ke cike taf da tarin farin cikin ganinta da yaron a jiki, tayi ƙyau sosai ta kuma dace da uwa. Musamman da ƙibar ciki ta sata komawa wata babbat mace. Bai barta ba har sai da ya ga tana hamma. Yasan babu abinda tafi buƙata a yanzu kamar barcin, dan lokacin da cikin ya shiga watan haihuwa bata iya barci sosai. Wani lokacinma kwana take a zaune, sai da rana takan ɗanyi ta rage nauyin ido.
Washe gari ƴan uwa da abokan arziƙi suka fara isowa gidan ganin ɗan jinjiri. Yayinda tun a farar safiya ta amsa kiran ƴan Abuja su Mama debora, dan har yanzu suna nan a gidan su Yoohan ɗin tare da jami'an tsaro. Tun jiya kuma Yoohan ya sanar musu da haihuwar Nu'aymah harma ya tura musu hoton jariri. Sunso kira tun da daren yace suyi haƙuri sai da safe. Aiko gari na wayewa saiga shigowar kiransu ta hanyar video call.
Nu'aymah tasha mamaki matuƙa ganin wai harda Joy da Gebrail cikin ƴan murnan haihuwarta. Sun mafi kowa zaƙewar cewar zasuzo kano. Taji daɗin hakan har cikin ranta, dan koba komai dai ba'a canjama tuwo suna. Dole su wannan ɗan nata zai kalla matsayin dangin mahaifinsa. Sune kuma adonsa a cikin al'umma.
Baba malam shine ya tauna dabino ya bama jin jiri bayan yayi kiran Yoohan ya tambayesa akan yayi masa huɗuba kokuwa zaizo da wuri yayma yaronsa da kansa. Maganar ta bashi kunya sosai sosai. shi ko bama ɗansaba koshi kansa ai Baba malan ya isa da shi. Cikin jin nauyi yace, “Uncle dan ALLAH ka daina neman izinina aka. dukkan abinda ya dace da shi. Kai masa dan kaima ubane a garesa ai. Suna kuma asa masa sunanka, dan ina fatan ya zama mai gadon ɗabi'u da ƙyawawan halayenka da tarin ilimi”.
Baba malam yaji daɗi sosai da wannan girmamawa. dan haka yayma yaro huɗuba da suna Muhammad Soorajidden. Sai dai ya bar hakan a ransa sai ranar suna idan ALLAH ya kaimu. Ya dai sanarma Umm da hajjo kawai.
A washe garin data haihu da kwana biyu aka maido su Abban Abdallah gida daga asibiti. Dan baba malam dai da kansa ya roƙa Jay akan a bar maganar zuwa kotun ɗin nan a barsu suji da ciwukan dake tare da su. Badan Jay yaso ba ya yarda da buƙatar ta baba malam aka rufe case ɗin ma gaba ɗaya daga can ofishinsu. jikin Abban Abdallah yayi sauƙi, sai dai kuma fa akwai matsaloli sosai, dan sakamakon karayar da yayi a kafaɗu wuyansa baya iya zama sam, gashi kansa ya bugu ƙwaƙwalwar sa ta samu matsala daga ciki, matsala irin waddama tafi ta Nu'aymah muni. Baya gane wasu abubuwan yanzu tamkar ƙaramin yaro, ko dubashi kaje yi sai dai ya dinga kallonka kamar wani soko.
Addah ma dai al'amari ya tsananta a gareta, duk ta rame ta lalace tayi baƙi. Har yanzu da tayi tari kuma sai kaga jini duk da dai ya ragu ba kamar da canba.
Alƙawarin ALLAH ya cika ta ɗauki gudan jinin Yoohan da Nu'aymah a hannunta. Tai dariya tai kuka abin tausayi. Abban Abdallah kuwa koda aka kai masa jaririn kallonsa kawai ya dingayi amma babu bakin magana, hasalima ba wani fahinta yayi da ƙyau ba sai da Monyn Abdallah tai masa bayani, dan suna nan kano sunma dawo gaba ɗaya. Cikin karkacewar baki ya nuna Nu'aymah ya nuna jaririn yana magana yawu na dilalowa. Yace, “Mamana. Ɗanta?”.
Kai Momy ta jinjina masa. Hakan ya sakashi yin murmushi mai ciwo sai ga hawaye na zirara masa da gudu. Sosai hakanma da yayi ya bama kowa mamaki, dan baya magana balle nuna fahimtar mutane.
Ranar dai ansha sabon kuka a gidan, dan komai sabo ya dawo a zukatansu. Sai da baba malam ya sake musu nasiha sannan suka samu nutsuwar zukata.
Ƴan Abuja basu sami isowa kano ba sai kwana huɗu da haihuwar Nu'aymah. Ba ƙaramin shan mamakin ganin da gidan da Aymah ta fito sukayi ba, sun sake tabbatar da lallai itaɗin jinin babban gidace. Dan duk da kasancewarsu ba ƙabila ɗayaba, ga abinda mahaifinsu ya aikata daya jawo musu baƙin jini a waje. mutanensu acan anan sai ake nuna musu mutuntawa da girmamawa. Hakan ba ƙaramin sakasu jin kunyar Nu'aymah yayi ba. Mama debora harda kukanta kuwa. Dan batai zaton dangin Aymah zasu amsheau da hannu biyu kamar haka ba kodan cin kashin da taima ƴarsu..
Washe gari ana gobe suna shima Yoohan ya iso tare da Juliet ɗin Umar da baby Ayisha. Kai tsaye nan kano suka nufo dama. Inda Yoohan yay masauki a hotel da Omar ke jiransu. Juliet dai zuwa dare aka kaita gidansu Nu'aymah. Sunyi farin cikin ganin juna sosai, Juliet nata mamakin Nu'aymah da ɗa. itako dariya ta dingayi tana rungume da Ayisha ɗinta.
Su kansu Omar da Yoohan kallonta kawai suke. Daga baya Umar da Juliet suka basu guri. Tasowa Yoohan yayi yazo ya rungumeta yana sake godema ALLAH ɗan jaririnsa na jikinsa.
Tai dariya da faɗin, “Silly boy duk ka wani rikice kai ka zama Baba ko?”.
Dariya sukayi a tare cike da jin daɗi da farin ciki. Yoohan ya sumbaci goshin yaron da faɗin. “ALLAH ya raya Sheikh to be insha ALLAH”.
Murmushi kawai Aymah tayi da faɗin amin.
RANAR SUNA
Washe gari aka raɗama yaro sunansa Muhammad Soorajidden a masalaci. Tare da doguwar addu'a a garesa. Kowa yaji daɗin wannan suna musamman Nu'aymah da taji kamar ta haɗiye Yoohan dan farin ciki. Dan babu yanda batai da shi ya faɗa mata sunan jiya ba yaƙi. Kusan ƙarfe goma na safe kuma sai ga tarin alkairi daga Yoohan. Duk wani al'ada na hausawa a bikin suna sai da yayisa bisa shawarar Ahmad da Hamza manager.
Kowa kam ya yaba ƙoƙarin sa, baba malam ma ya dinga faɗa hidimar tayi yawa.
Amaryar jego tasha ƙyau harta gaji. hakama ɗan jinjiri Deen. Da yamma akasha walima a ƙofar gidan. wadda tai sanadin karyar da zukatan su Gebrail da su mama debora da suka fahimci Yoohan ɗinsu ya zama musulmi, basu nuna ƙyamar hakanba ko a ransu, saima yanda tsarin yake gudana da ɗabi'un musulman yasa Momy Destiny kasa yin shiru har sai da ta yaba. Dan har ranta abubuwan sun birgeta gaskiya.
Bayan tashi da ga walima ƙarfe takwas na dare kuma wani tashin hankali ya biyo baya. Dan sama da ƙasa an nema ɗan jariri Deen an rasa. Kafin kace mi gidan ya hargitse. A take Nu'aymah ta sume musu sai da aka zuba mata ruwa. Yoohan na cikin ɗimuwa shima aka ƙwamushesa. Faruwar hakan a gaban mutane ya sa Omar da Ahmad da Omar ɗin su Nu'aymah, da Abdallah da Naseer binsu a mota. Yayinda Nu'aymah ta faɗa miotar batare da kowa ya fargaba sai da sukai nisa.
A yau tai niyyar nunama Yoohan hoton papa da wadda suke zargin itace mahaifiyarsa. Sai gashi kuma abinda basuyi zatoba ya auku...........✍
‘Hummm mikuke tunani masu karati?????????’.
ZAFAFA BIYAR 2021
Hafsat miss xoxo????
KIBIYAR AJALI……!
(Sulke baya tareta saita gitta).????????
Mamu gee????
MIN ƘALB!!????????
Hafsat rano????
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA…!!????????
Safiyya huguma???? SIRAƊIN RAYUWA????????
Bilyn Abdull????
SARAN ƁOYE????????
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka????????????????
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????
09033181070
????????????????????????????????????????
TEAM—-ZAFAFA BIYAR????????????????
ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????.
[7/8, 10:16 PM] Sweet Sis: LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana????????.
No. 76
………….Gaba ɗaya gidan ya hargitse. Su Naser dai sunbi motar data ɗauki Yoohan a mota, sai dai babu tabbacin zasu iya cimmasu, musamman daya kasance dare ne.
Afrah da yake tazo wajen sunan ce tai azamar kiran Jay ta sanar masa, shima kansa hankalin nasa ya tashi matuƙa, amma sai ya shiga kwantar mata da hankali akan karta damu, indai da waya a jikin Yoohan gano inda ya ke abune mai sauƙi, ya kuma tabbatar a duk inda za’a kai Yoohan Deen na wajen insha ALLAH.
Suna yanke wayar yay kiran su Aliyu ya sanar musu. Tare da tura musu Number Yoohan dan yana son a bibiyesu da sauri kafin suyi tunanin yadda wayar a wani waje ko wani abu daban. Haka kawai a ransa ya kejin wannan aikin papa ne.
Lallai hikimar Afrah na saurin kiran Jay ya taimaka ainun. Dan cikin amicin ALLAH kuwa ta hanyar bibiyar wayar Yoohan ɗin da ke a jikinsa suka samu nasarar sanin inda aka kaisa.
_★
A ɓangaren Yoohan kuwa an shammacesa ne. Dan yana tsaka da firgicin jin cewa ba'aga Deen ba, da cewar Nu'aymah ta suma juwa ta nema kwasarsa. Yana dafe kansa kawai yaji an jasa ta ƙarfi an tura a mota, al'amarin kamar wani wasan yara. Suna sakashi a motar suka ɗora masa bindigu. Binsu kawai yay da kallo ɗaya bayan ɗaya ya girgiza kansa. Kafin yace wani abu ɗaya a cikinsu yace, “Indai kana buƙatar ɗanka a raye ka bimu salin alin”.
Guntun murmushi kawai yayi ya ɗauke kansa. Papa yana Nigeria kenan, dan a take ya gama fahimtar su ɗin yaran papa ne. A ransa yake tunanin shin da papa na buƙatar ganinsa sai ya bi ta hanyar sace masa yaro kenan? Minene amfanin yin hakan to?. (tsoron a kamashi mana) zuciyarsa ta raya masa. ‘To ashe kuwa shi da kansa zai damƙa papa a hannun huku yau ba sai gobe ba’.
Ganin baice komaiba yasa yaran ɗauka yayi ladab ne. A haka suka iso wani hotel. Duk maida bindugunsu sukayi a jiki daga su har Yoohan suka fito a motar. Yaji a ransa zai bisu kamar yanda suke buƙata. Sun shiga cikin hotel ɗin babu wani alamun rashin gaskiya tattare da su. Hasalima sun shiga a rarrabe ne. Yoohan tare da ɗaya a cikinsu, suma sauran biyun suka shiga su kaɗai.
Shi Yoohan sun wuce cikin hotel ɗin direct, sauran kuma suka tsaya reception kamar dai wani suke jira. Yoohan dai yanata bin hotel ɗin da kallon nazari har suka ƙarasa ɗaki mai lamba 23 vip section. Knocking ƙofar yayi sau ɗaya, sai ko gashi anzo an buɗe. da ido yayma Yoohan alamar ya shiga. Yoohan yay masa wani gajeren murmushi ya shige ɗakin, sai y bisa a baya yanayin ƙwafa. Dan yaji haushin murmushin Yoohan ɗin har ransa.
Ko kaɗan Yoohan baiyi mamakin cin karo da Momy a ɗakinba. Dan dama ai su zuciyarsa take raya masa gani ɗin. Ya kauda kansa daga kallonta saboda shegun kayan dake jikinta bata da maraba da tsirara. Takowa tai gabansa tana kwasar dariya da tafa hannaye ta shiga zagayesa.
Hannayensa kawai ya tura cikin aljihun wandon shaddarsa ya rumtse idanunsa. Sai da ta zagayasa sau kusan uku kafin tazo gabansa ta tsaya daf tamkar zata rungumesa. Ko motsi kuwa baiyiba, bai kuma buɗe idanunsa ba.
Cikin raɗan maganar shaƙiyanci da jin alfahari madam Chioma tace, “Abin mamaki ko my boy, haka muke ni da papanka kullum cikin bama mutane mamaki”. Sai kuma ta ƙyalƙyale da dariya mai cin rai tana ja baya. Komawa tai bakin gado ta zauna tana wani lashe baki da banƙaro ƙirji. Tare da jan rigarta sama sosai cinyarta ɗaya ta fito waje idonta akan Yoohan da har yanzu nasa idanun ke a rufe. Cike da salon iskanci ta sake narke idanu tana lasar laɓɓanta.
“My boy karka takura kanka da tunani, dan baka buƙatar hakan musamman akan soyayyar jaririnka, oh sorry jikana nefa ashe”. Ta kwashe da dariya sanna ta cigaba da faɗin, “Yi haƙuri my boy na mantane. Ta hanya ɗayane kawai zaka iya cetar my grandson John. Dan nice kaɗai zan iya kaika inda zaka samesa. Hakan kuma bazata kasance ba sai ta hanyar biyamin buƙata ta. Hhhhhh My lovely john dolene fa na ɗanɗani zumar nan taka da kaketa min rowa, dan itace burina tun kana shekaru sha takwas a duniya. Hhhhhh kaga kuwa ai bai kamata nasha wahalar dakon lokaci ba, kaima nasan zaka tausaya min dear soooon”. Ta ƙare maganar da wani salon iskanci tamkar zatai kuka. Sai kuma ta taso zuwa gabansa ta tsaya tana matso hawayen da suka cika mata idanu.
Hannayenta ta ɗora akan ƙirjinsa ta fara ɓalle maɓallin shaddarsa tare da cigaba da faɗin, “Karka damu duk ma na yafe maka wahalhalun dana sha a waɗancan shekarun kaji baby. Dan wannan daren kawai ya wadatar da cike gurbin duka sauran dararen da suka shuɗe”.
Duk wannan iskanci da madam Chioma keyi Yoohan na tsaye tamkar gunki, har yanzu idanunsa a rufe. Sai da takai ƙarshen duka maɓallansa tana sambatun haukan zantukanta, ta tura hannunta cikin rigar ta fara shafa ƙirjinsa ta saman singlet ɗinsa. Wani irin cije baki yayi ya hankiɗata baya da iya ƙarfinsa.
A take ta saki wani irin wahalalliyar ƙara saboda da gaske ta bugu. Da sauri yaran da suka kawosa wajen suka zagayesa da bindugu. Buɗe idanunsa dake a matuƙar jazur yayi akansu, ya wani ɗauke kai irin ba kune a gabana ba ya maida kan madam Chioma dake kwance ƙasa wanwar tana numfashi da ƙyar saboda azaba.
A hankali ya fara takawa gareta fuskarnan kanta tayi jazur kai kace aman wuta zatayo. Suko yaran madam Chioma na biye da shi da bindiga abin nasuma abin dariya????.
Ƙafarsa ya taka a samna gadon ya ranƙwafo kanta. Wani murmushin tsantsar tsana ya jefeta da shi tare da nunata da ɗan yatsa. “Na tsaneki, har cikin raina na tsaneki, tsana irin wadda ban taɓama wani mahaluki ita a wannan duniyarba. Indai nine zaki mutu da takaicin rashin samuna har ƙarshen numfashinki. Nayi takaici mai yawa akan kasancewarki mahaifiya a gareni. Bakuma zan taɓa yafe miki ba har abadan tunda ke karya ce wadda sam bata da zuciya a ƙirjinta balle ƙwaƙwalwar tunani. Badan ke uwata bece da yau na tabbatarma duniya ke ɗin dabbace, a cikin dabbobinma kina jerin aladu dan sune basu banbance junansu wajen neman kansu. Wlhy kinji na rantse ko tabon ƙwarzane na samu a jikin yarona saina halakaki da wannan hannun nawa”. Ya kai ƙarshen maganar yana wara yatsun hannunsa da jujjuyasu akan fuskarta.
Da gaske tsoro ya shigi Madam Chioma, dan tunda take a rayuwarta bata taɓa ganin irin wannan fusata da fushin na Yoohan ba. Tsaye ya miƙe yana zuba mata wani mummunan kallon tsana da ƙyama.
Da sauri ta zabura ta miƙe duk da azabar da bayanta ke mata. Tace, “Ku ɗauremin shi, wlhy koda ƙarfi saina lashi zumarka John. Kaje kaita tsanar tawa kai ya dama wannan kuma, ni ban tsaneka ba. Ba kuma zan tsneka ba”.
Kafin Yoohan yay wani yunƙuri kuwa suka dabaibayesa da igiya, duk yanda yaso kuɓutar da kansa ya gagara hakan sam, dan tsam suka ɗauresa a tsaye sannan suka kamashi suka ajiye a kujera suka sake ɗaurewa suna dariyar yanda sukaga yana wani irin huci na zafin zuciya.
Itama kanta Madam Chioma dariyar take tayasu da iya ƙarfinta. Ta tashi tsaye da ƙar tana riƙe ƙugu. Gabansa tazo ta tsaya tana cije baki. “John kana wasa dani ko? Na fika hatsabibanci yaro. dan tunkan asan za'a haifeka nake da taurin kai. Ai tunda nayi alƙawarin saina cikama rayuwata”.
Lokacin da su Yoohan ke wancan dabi shi da madam Chioma su Nu'aymah suna shigowa cikin hotel ɗinne tare da jami'an tsaro. Dan tuburewa tai akan saita biyosu. Ganin yanda ta rikice ɗinne ya saka Omar bada shawarar aje da ita ɗin. Sai da jami'an tsaron sukai magana da manager ɗin hotel ɗin sannan suka nufi cikin hotel ɗin kamar yanda alama ke nuna musu dai-dai inda wayar Yoohan take. Wadda toshewar basirar madam Chioma baisa ta kawo a ranta sanadin wayar ballinsu zaiyi ruwa ba.
Dai-dai madam Chioma ta ɗora kanta saman wuyan Yoohan tana shinshina kamar wata mayya ko tunkiya, hannayenta duka biyu na akan jikinsa. wani irin masifar tafasa zuciyar Yoohan keyi tamkar zata faso ƙirjinsa ta fito waje. Sai ko faman taunar lips nashi yake da masifar ƙarfi, a ɗaure yake, bashi da wata damar ɗaukar mataki akan uwar tasa.....
Da sauri ta ɗago saboda jin an buɗe ƙofar. Hakama yaranta dake tsaye a gefe kawunansu a ƙasa duk zabura sukayi suna rarumar bindugunsu...
“Ƙasa gaba ɗayanku, duk wanda ya taɓa wata bindiga anan kuwa a bakin ransa”.
Ɗaya daga cikin jami'an ya faɗa a tsawace yana nuna yaran madam Chioma. Da sauri ta fiddo tata ƴar ƙaramar bindigar jikinta ta ɗora bisa kan Yoohan daya buɗe idonsa a hankali ya sauke su akan Nu'aymah da ke shigowa tare da Jami'an.
Cikin rawar jiki data murya Madam Chioma tace, “Ku fita a ɗakin nan kona tarwatsa masa kwanyar kai duk da kasancewarsa ɗana”.
Da sauri Nu'aymah tace, “Ƙarya kike munafuka azzaluma. K! Ba mahaifiyarsa bace ba. Yah Yoohan wlhy ba itace mahaifiyarka ba ƙarya takeyi”. Tai maganar da fashewa da kuka tana zaro hoton nan daga envelope ta nuna masa balarabiyar nan. “Kaga mahaifiyarka nan Yah Yoohan, wlhy ba wannan shaiɗaniyar bace. Bana tantama akan har mijinta ba shine ya haifeka ba, akwai abinda suke ɓoye maka. Iyayenka na gaskiya bazasu sace maka ɗanka ba. Mahaifiya ta ƙwarai bazata so tarayya da ɗanta ba koda kuwa bata da addini, sai dai idan dabbace ita mai juyayyen tunani..........”
“Hhhh da ƙyau tsagera”. Madam Chioma ta faɗa tana dariya har yanzu bindigarta na akan Yoohan da zantukan Nu'aymah sukema kai kawo a rai. Ta cigaba da dariya da faɗin, “Ashe tsaurin idon naki ya kai haka? Ko da yake ashefa kinsan zafin haihuwa ko? Hhhhhhh. Ashe kuwa za'a kwashi gawa da yawa a hotel ɗin nan yau”. Tai maganar da haɗe fuska ta nuno Nu'aymah da bindigar.
Cikin kaushin murya Umar yace, “Kibar wannan haukar da kikeyi ki ajiye bindigar hannunki kawai madam”.
Kallonta ta maida garesa. Cikin yatsina fuska tace, “Richard kake kowama? Kai kuma a suwa shiga family issue?. Maza kama kanka wannan ba shigarka baceba.....”
Kafin ta rufe baki taji an hankaɗata, sai ga ta ita da bindigar ƙasa wanwar. Da sauri ɗaya a cikin ƴan sandamln ya ɗauke bindigar, wani kuma yazo ya danna mata ankwa ta baya. Yaran nata ma duk an kamesu. Nu'ayma kuwa da gudu ta ƙarasa jikin Yoohan dake a ɗaure ta rungumesa tana fashewa da kuka. Biyota Umar yayi ya fara warware igiyar da suka ɗaure Yoohan ɗin da ita, itama Aymah sai ta miƙe tana taimaka masa. Suna gama kwancesa ya rungume abarsa yana shafa bayanta. Sai dai bakinsa ya kasa furta komai saboda irin tafasar da zuciyarsa ke masa. Hoton hannun nata ya zare ya kafe balarabiyar jiki da kallo tare da papa dake gefenta. Jiyay wani abu na tsarga masa tun daga zuciya har zuwa tafin ƙafa. Ya kafe fuskar papa yana nazari sosai akansa batare da su Nu'aymah sun fahimci abinda yake nazartarba. A hankali ya janye Aymah a jikinsa yana miƙa mata hoton, gaban madam Chioma ya karasa. Babu wani kace nace yasa ƙafa ya taɗe ƙafafunta sai gata a ƙasa ta zube. Kasancewar hannayenta ɗaure suke ta baya da ankwa sai ta faɗi a rubda ciki. A take goshinta da hancinta da baki suka fashe, haƙoran gaba guda biyu sai gasu a ƙasa.
Wata wahalalliyar ƙara ta saki. Yoohan yasa hannu ya birkitota ta dawo rigingine. Gaba ɗaya fuskarta ta gama damewa da jinin raunukan data samu, “Ina ɗana?”. Wannan itace kawai tambayar daya jefa mata batare da ya damu da yanda jini yayma fuskarta jage-jage ba.
Kanta ta shiga girgiza masa, cikin rawar murya da laɓɓa tace, “Nima ban saniba John, Please ka yarda da ni”.
Uffan Yoohan baice da itaba, sai bindigar hannun ɗan sanda ɗaya ya fisge ya ɗora mata a goshi. “Humm ke ƙaramar ƴar iskace ashe. Idan kika cigaba da min gardama ba shakka zan tarwatsa ƙaramar ƙwaƙwalwarki da harsashin cikin bindigar nan. Idan kinada taurin kai tun kan haihuwata, ni ki ɗauka bayan haihuwar tawa na damaki na shanye. Da kika ganina anan tsageran kainane nima wlhy. Faɗamin ina Yarona yake?”.
Wutar bala'in da madam Chioma ke hangowa cikin idanun Yoohan ya sata saurin faɗin, “Zan gaya maka, amma ka taimakeni ka cikamin burina nima, kayi tarayya dani koda sau ɗaya ne naji sanyi a raina John. Ka tausayama wahalar danasha a kanka ta tsahon shekaru”.
“Lallai k! a tumakin ma balama ce”. Yoohan ya faɗa yana cije baki da ɗana kunamar bindigar ya maida bisa tsakkiyar kanta.
Jikinta karkarwa ya farayi, tana kuka tace, “Kayi haƙuri karka kasheni zan faɗa maka Jonh. Na rantse zan faɗa maka. Yaronka na a hannun Papanku acan wani gida dake cikin G.r.a, nima ya sakanine na kai masa kai, shine nai amfani da wannan damar domin fara cikama kaina burina a kanka na tsahon shekaru. Na biyo da kai tanan kafin na miƙaka wajensa. Miracle ita aka saka ta sace maka yaro a wajen bikin da kukeyi, dan dama muna biye da duk wani motsinku.......”
Duka ya kai mata a fuska ɗan sanda yay saurin riƙesa. “Cool down Mr Yoohan. Karka damu dolene ta kaimu har inda suke ai. Kwantar da hankalinka kaji”.
Huci kawai Yoohan ya keyi, tsabar zuciyar dake cinsa sai ga hawaye sharrrr suna sakkowa. Matsowa Nu'aymah tayi ta riƙe masa hannu batare da tayi magana ba. Da sauri ya jawota jikinsa ya rungume ko zaiji sassaucin zuciyarsa.
An tattara yaran madam Chioma zuwa police station da su. Su kuma su Yoohan da sauran jami'an suka shiga motar da aka sato Yoohan tare da madam Chioma bayan an sakata kiran papa ta sanar masa cewar gata ta samo Yoohan harda Nu'aymah ma. Wani ihun gigitacciyar dariya papa ya saki har su Yoohan na jiyosa. Umar da Jami'an sun rufe fuskokinsu tamkar su ɗinne yaran madam Chioma. Itace ta dinga nuna musu hanya har suka isa anguwar. A daidai ƙofar gate ɗin gidan suka tsaya. Maigadi na leƙowa yaga motar sai ya buɗe da tunanin su madam Chioma sun ciyo nasara suma.
Yoohan da Nu'aymah aka sakama ankwa a hannu suka fara shiga, jami'an tsaron da fuskokinsu ke a rufe na biye da su a baya. Umar ne ƙarshe da madam Chioma a gabansa. Acan waje dama tuni ƴan sanda sun gama zagaye gidan dan dama babban burinsu shine kama papa da sauran mutanensa. Abinda suka share watanni biyu suna nema ga dama ta samu a lokacin ƙanƙani.
Da sauri Papa dake zaune cikin kujera su Joshua zagaye da shi duk suka miƙe sabida ganin Yoohan da Nu'aymah. Deen na kwance akan centre table ɗin falon cikin showal ɗinsa. Yayi kukan wahala har ya gaji yayi barci. Gefensa an ajiye sharɓeɓiyar wuƙa.
Cike da wata irin mahaukaciyar dariya papa ya shiga tafa hannayensa yana kallon su Yoohan.
Ya tako gabansu a hankali batare da tunaninsa ya haska masa cewar waɗanda ke bayansu ba yaransu bane ba. Da dariyarsa ya shiga faɗin, “Oh my Son & Darling daughter in-low ɗina. Welcome to my new land. Nice meeting you my guys”.
Da ga Ayma har Yoohan dai kallonsa kawai suke. Papa ya kalli jami’an da yake tunanin yaransa ne yana fa faɗin, “Ku cire musu ankwa amfaninta ya ƙare ai. Dan game zamu buga da su mai zafi”.
Babu musu ƴan sandan nan suka cirema su Yoohan ankwa. Komawa papa yay ya zauna a kujerar daya taso. Ya ɗan taɓe bakinsa da dora ƙafa ɗaya kan ɗaya ya ɗauki kofin giyarsa ya kurɓa yana kallon su Yoohan. “John badan inada ƙarancin lokaci ba dana baka wani labari mai ban mamaki da al’ajabi. Amma share kawai muje ga game ɗinmu. Idan lokaci ya rage mana a cikinsa sai na baka labarin. Daughter in-low karki tada hankalinki kinji, ɗanki yana lafiya, kingama barci yake abinsa”. Yay maganar da tasowa daga kwanciyar da yayi jikin kujera ya yaye showal ɗin da deen yake ciki yana lakatar hancin yaron da ɗan yatsa. “Daughter kin iya haihuwar ɗa fa”. Ya faɗa yana kecewa da dariya su Mike na tayasa. Giyarsa ya kwankwaɗa ya ajiye kofin yana haɗe hannayensa waje guda. “Oh Sorry my son karka fusata na sanka da zuciya”. Takardun dake a gefen Deen ya jawo ya tura ƙarshen tebirin ta sashen da su Yoohan suke. “Wannan takardun sune game ɗinmu tare da ɗan jinjirinku ƙyaƙyƙyawa. John kanada zaɓi biyu. Kuɓutar da yaronka ta hanyar yimin signing a duk takar dunnan, ko kummaaaaa nai masa yannnnnkan rago da wannan wuƙar tawa a wannan lallausar fatar tashi”. Ya ƙyalƙyale da dariya yana ɗora wuƙar bisa cikin Deen dake barci a binsa yanata sakin ajiyar zuciyar kukan da yasha.
Ko motsi Yoohan baiyiba, haka ma Nu’aymah duk da hankalinta a tashe yake kallon papa kawai take zuciyarta na tunanin anya kuwa wannan mutumin ma mahaifin Yoohan ne?
Hannunta taga Yoohan ya saki tare da takawa a hankali zuwa gaban papa yana wani ƙyaƙyƙyawan murmushi, dan cikin ƴan sandan nan ɗaya yay masa alamar yaje. Zuwa yanzu sunsan sauran ƴan uwansu sun gama tattare yaran papa gaba ɗaya dake cikin gidan. Sannan sun gama nazarin su papa kaf babu wani makami tare da su anan sai wuƙar dake akan Deen. Babu wani alamar damuwa a fuskar Yoohan balle tambayar papa ba’asin yin hakan. Yazo gaban tebirin ya zauna akan ƙaton tum-tum dake kusa da shi yana murmushi. Cikin kwanciyar hankali ya ɗauki pen ɗin dake saman takardun ya rike a hannu. Shafin farko na takardun ya karanta cike da nazari. Yaɗan ɗago ido ya kalli papa da shima ke kallonsa. Murmushi Yoohan ya sakar masa da taune lip ɗinsa na ƙasa ya ɗage gira ɗaya da lumshe idanunsa ya sake buɗewa akan takardun. Har cikin jini Murmushin Yoohan ya daki zuciyar papa da su Mike. Amma sai basuyi magana ba. Ɗaya bayan ɗaya Yoohan ya fara signing takardun. Yana gab da gamawa Mike da ya farga babu Madam Chioma. yace, “Brother wai nikam ina madam ma ne? Ta kawo mana su amma banga ta shigoba ita”.
Da sauri Papa ya kalli Mike, sai kuma ya kalli Yoohan dake signing yana murmushi da taunar lip dinsa na ƙasa. “John mikake kullawa? Ina matata?”.
Ko motsi Yoohan baiyiba balle ya kalli papa. Sai da ya gama signing ɗin duk takardun sannan ya kalli papa da tsoro ya fara bayyana masa a fuska. Wuƙar kan Deen ya dauka yana faɗin, “Ashe kuwa inhar wani abu ya samu matata saina halaka wannan yaron”.
Murmushi Yoohan ya sakeyi har haƙoransa na bayyana. Ya miƙe tsaye hannunsa ɗauke da takardun da yay Signing. Yaɗan sosa pen din a gefen wuyansa yana duban papan. “Oh my sweet papa ya da karaya haka da wuri?”. Yay maganar da wani shegen murmushin yaƙe. Sai sukaga ya girgiza kansa yana ɗan buɗa hannayensa. “Karfa ka damu papa. taya zan cutar da mahaifiyata. Guys Please ku kawo masa matarsa”. Ya juya yana kallon ƴan sandan nan. Umar dake can ƙofar falon bai shigoba ya turo madam Chioma ta fara shigowa bakinta a ɗaure. Bindiga a bisa kanta.
Wani irin zabura papa yayi jikinsa na rawa. Kafin yay magana Yoohan yay ƴar dariya yana faɗin, “Oh my sweet papa relaxxxxx!!. Idan ban mantaba kace zamuyi game ko? So karka damu bazan canja ba zamu buga ai. Nasan kana son matarka, ba kuma zakaso rasata ba, gata ƴar ƙyaƙyƙyawa kuwa”. Yay maganar da wata shegiyar dariya. Sai kuma ya gimtse fuska da haɗe hannayensa waje guda yace, “Oh sorry papa bazan sakeba. Ga takardu na maka signing kamar yanda ka buƙata. Sai dai kana da zaɓi. Matarka ko waɗanan takardun. Idan su kafi buƙata, zan baka, amma zan tarwatsa kwanyar matarka a gabanka. Idan kuma matarka kafi bukata, zaka bani ɗana, na kuma wuce da takardun nan a gabanka. Wannan shine game ɗin Yahyaaaaaa! Much????! much????!!, I love you my papa!!”. Suka kwashe da dariya a ƙarshen maganar shi da Nu’aymah tare da tafawa.
Wani irin huci papa ya fara fitarwa kamar zai shiɗe. Ya kai hannu zai fisgi wuƙar nan Yoohan yay saurin faɗin, “No! no! no no no no!!!! Pastor goshpower. Karka fusata da yawa fa, kasan ɗan naka mai faɗa da cikawa ne. Ai yanzun game ya tashi daga tsakanin takardu da yarona, ya koma tsakanin takardu da matarka ok?”.
Kafin papa yace wani abu Yoohan ya fisge handkerchief ɗin da suka ɗaure bakin Chioma da shi. Wani wahallalen ƙara ta saki da fashewa da kuka. Cikin roƙo tace, “Please Darling ka basu yaronsu, ka taimakeni, na rantse john zai iya kasheni, kagafa yanda ya ciremin haƙwara, karkai jayayya dasu nan duk jami’an tsarone ba yaranmu ba”.
“What!!!”.
Papa da su Mike suka ambata a firgice. A take duk jami’an tsaron da Omar suka janye abinda suka rufe fuska. Sai ga wasu na shigowa suma akai ma su papa zobe. takawa Yoohan yayi gaban papa yana dariya ya ɗauki Deen ya rungume a jikinsa tare da sumbatar goshin yaron. Da sauri Nu’aymah ma ta matso garesa ta haɗashi shi da yaron ta rungume. Umar kuwa ya damkama ƴan sanda Madam Chioma ya matso ya ɗauki takardun da Yoohan yayma Signing yana dubawa.
“Kai!! Dude!, anya kuwa mutumin nan ma shine mahaifinka kuwa?”..
Ɗagowa Yoohan yayi daga sumbatar kumatun Deeen, yasa hannu ya share hawayen da suka cika masa ido yana miƙama Nu’aymah yaron. Yace, “Goyashi akwai sanyi”. Babu musu Aymah ta juya ya ɗora mata Deen a baya ta goyashi, ya gyara mata hijjab ɗin jikinta sannan ya dubi Umar da yay tambayar da furzar da zazzafan huci.
“Bana zaton haka Umar, dan abubuwa da yawa sun banbanta tsakaninsa da wanda ke a hoton nan. Sannan waɗanan takardun mallakin kaddarorine a cikinsu wanda alamu suke nuna ba nasa bane sam. Dan signing ɗin cikinsu ba irin nashi baneba. Akwai sirrin da yake ɓoyema duniya a kaina……..”
“Sirri mai girma kuwa”.
Muryar da basuyi zato ba ta karaɗe kunnuwansu a bazata. kusan gaba ɗayansu suka dubi bakin ƙofar inda maganar ta fito. Jawaad Abdul-aziz Yusuf ne tsaye cikin ƙananun kayan da suka rage masa shekaru, sai dai duk wanda yasan shekarun girma ya kallesa yasan shiɗin bana wasan yara bane, (Duk ya girmi masu karatu yanzu, duk da a gabansu aka haihesa????????????????).
Bayansa jami’ai ne biye da shi. Cikin falon ya karasa shigowa ya zauna a kujerar da ke kallon papa dake a durƙushe bisa gwiwoyinsa yanzu shi da su Anthony saboda zagayesu da akai da bindugu.
Ƙafa ya ɗora ɗaya kan ɗaya yana wani shegen murmushi, yace, “Hii Goshpower, sai kuma gaka. Hhhh ALLAH sarki. Haka rayuwa take ai, duk iya gudun mai tsere bai isa zarta ƙaddararsa ba. Dama naji a jikina dole ka dawo, dan yanzu da dukiyar da wannan takardun kawai kake tunanin ka tsira. Kafa birgeni, dan da gaske ka iya wasa. Kana da basira ƙwarai da gaske. Sai dai kuma kanada daƙiƙanci a wajen kuskuren lissafi. Da ace bakabar Yoohan a raye ba da lissafinka bazai taɓa ɓata ba. Sai dai kash a dalilin ƙwaɗayin abinda baka taraba ka saka kanka a tarko tsahon shekara talatin da biyu. Tsem! Tsemm tsemmm!!! Gaskiya ka bani tausayi. A farkon labarin dai cike yake da birgewa da ƙayatarwa ga marubucinsa. Sai dai a ƙarshe an samu dagulewar ƙwaƙwalwa ga marubucin. Mai makon yanda aka fara da nasara a ƙare da nasarori sai aka ɓige da faɗuwa ƙasa wanwar. Kash matsalar tunani ko Mr goshpower”.
Jay yay maganar ƙarshe yana ɗage gira da sakin dariya. Ya cigaba da faɗin, “Oh sorry bara na taƙaita, dan ka sani tafiyar da ban shiryaba a daren nan daga Abuja zuwa kano ga uban sanyi. Maganar gaskiya ma ban yafe ba. Ƴan jarida ku shirya kayan aiki”. Ya faɗa yana shafar girarsa da nuna hanyar ƙofa.
A take kuwa suka shigo kusan su shida. Duban Yoohan da Nu’aymah da Umar yay ya nuna musu kujerun alamar su zauna suma.
Zama sukai a sanyaye kamar an doke gwiyawunsu da ƙarfuna.
Jay ya kalli agogon hannunsa sannan ya dubi papa. “Mr Goshpower bamu da isashen lokaci, dan awoyi uku da mintuna ashirin da ɗaya suka rage alfijir ya keto. Bana son wasana da kai yay tsamari a wannan gaɓar dan daga ni har kai mun jigatu, inason sanin wanene Yahya? Su wanene kuma waɗanan na jikin hoton?”.
Shiru papa yayi ya ƙi magana, hakan yasa Jay ɗinma bai sake magana ba, sai kawai ƙarar bibdiga su Aymah sukaji da ƙarar papa. Ruɗewa Aymah tayi ta ƙwaƙume Yoohan jikinta na rawa. Ga Deen dake bayanta ma ya farka da wani irin firgitaccen kuka. Taimaka mata Yoohan yayi ta sakko da shi, ya rungumesa a jikinsa yana jijjiga shi. Da kallon papa da Jay yayma harbi biyu a duka ƙafafunsa saboda tsabar ƙwarewa a iya harbi.
Jay ya girgiza kansa da dafesa. Yace, “Oh kana neman fusatanine Mr Goshpower. Gashi ni kuma hannayena ƙaiƙayi sukeyi. Na faɗa maka a jigace nake matuƙa, karka jani da nisa ana idar da sallar asuba nake son komawa Abuja”.
Cikin magautar raɗaɗi papa ya fara magana. Ga wata irin zufa ta jiƙesa a take duk da uban sanyin da ake zubawa a garin. Yace, “Shima sunansa Goshpower, shi ɗin twin brother ɗinane. Wannan kuma matarsa ce”.
“Yayi ɗan gari, haka nake buƙatar jinka. Omar a cire masa bullets ɗin nan”.
Da sauri Omar yace, “Okay Uncle ”.
Tsabar son azabartarwa Umar sai ya ɗauki giyar da papa yasha ya rage ya zuba masa akan harbin. A take kuwa ya saki wata wahalliyar ƙara ya suma. Ko a jikin Omar. Ya amshi First aid box a hannun wani jami’i da sukazo da shi ya cire bullets ɗin cike da rashin tausayi. Sai da ya kammala komai sannan aka zubama papa ruwa ya farfaɗo.
Sai da suka bashi damar hutun kusan mintuna biyar ya daidaita sannan ya fara bada labari.