NOVELSSARAN BOYE

SARAN BOYE COMPLETE

   “Ni da shi twins ne. Muna tsananin kamanni har takai jama'a basa iya banbantamu inba mahaifiyarmu ta faɗa ba. Duk da itama wani lokacin rikicewa takeyi. Suna ɗaya iyayenmu suka saka mana wato Goshpower. Takai inhar ka kira ɗaya a cikinmu sai mu amsa maka mu duka. Mamanmu ta taɓa faɗa mana kaifin basira da muke da shi da farar fata tasa har ana dangatamu da wasu sunaye. Wasuko na tsoronmu da faɗin mama debora ta haifi waɗanda ba mayu. Wannan ba sabon a bu bane daga hallayar mutanen ƙabilarmu da yankinmu wajen danganta mutum mai fari da ƙyawun jiki da suna na tsoro. Mutane basu fara samun basirar banbantamu ba sai da muka fara girma halayenmu suka fara banbanta tsakanina da ɗan uwana. Mu duka munada kaifin basira da wayo, sai dai kowa da yanda yake gudanar da tashi. Duk inda gaskiya take zaka samu ɗan uwana a wajen, niko saɓanin haka shine zaɓi na. Kullum cikin takalo rikici nake wa iyayenmu, ɗan uwana kuma bai gajiya da bayyana gaskiya idan an tambayesa. A duk lokacin kuma da nai niyyar cutar da shi akan wannan abu da yakemin sai bana samun nasa. Dan ko faɗa zamuyi yafi ƙarfina. A haka dai muka kammala primary, akwai shaƙuwa mai ƙarfi a tsakaninmu, amma bamu cika zaman lafiya ba da zama waje ɗaya na dogon lokaci. Bayan secondary skull muka wuce jami'a, inda anan mabanbantan halayenmu suka sake bayyana. Duk da mu duka muna karatu ni a koda yaushe hankalina nakan mata, sannan duk wani abokin banza zaka samu nawane. Hakan na ɓatama ɗan uwana rai, tun yanamin nasiha da faɗamin gaskiya har yayi zuciya ya daina, daga ƙarshema muka raba ɗakin kwana, dama ba department ɗinmu ɗaya ba. Haka dai muka cigaba da tafiya, kafin mu kammala jami'a na zama riƙaƙen mara jin magana dan har harkar ƙwaya na fara, sannan na shiga cikin ƴan Cult. Mun kammala degree ɗinmu na farko, ta hanyar ogan babanmu muka samu taimakon tafiya ƙasar Italy ƙaro karatu. Daga nan ne labarin canjawar komai ya fara. Dan watanninmu biyar kacal a makarantar na sake canjawa daga duk yanda aka sanni. Idanuna sun sake buɗewa sosai harna fara harkar cocaine. Ta hanyar wanda na fara harkar Cocaine ne idanuna suka sake bushewa. Ya kutsa dani cikin manyan mutane konace tantirai dake juya duk wani iya shege na duniya. Nasha wahala ba kaɗanba wajen karɓar horo daga garesu har takai makaranta ma na daina shiga duk da yawan damuwa da kirana da ɗan uwana keyi, tare da yawan ƙoƙarin son sanin abokan mu'amulata. Muna shekarar ƙarshe daya kamata mu kammala degree ɗinmu na biyu ɗan uwana ya haɗu da matashiyar Balarabiyar saudia mai suna Anum. Itama karatu tazoyi, wannan kuma shine zangonta na farko. Sun fara rayuwa kamar abokai a hankali suka rikiɗe zuwa masoya. Sam bansan da wannan soyayya tasu ba sai da tai nisa, muna ma gab da kammalawa. ko nace ɗan uwana na gab da kammalawa. Danni tuni na yaye kaina daga zuwa makaranta. Sai dai nakan shigo lokaci-lokaci saboda harƙallar dake tsakanina da ɗalibai ta kayan shaye-shaye. A wani shiga da nai cikin makarantar ne na haɗu da Anum, wadda ina cikin tafiyata tazo tasha gabana, a zatonta ɗan uwana ne. Da farko na harzuƙa matuƙa, sai dai ƙyawunta yayma idanuna barazana da danne fushina. Cike da tsokana take kallona tana dariyar wai yaushe nasai kayan jikina?, ita dai basu mata ba. Naji haushin kalamanta amma saina fuske na barta akan ɗan uwan nawa ne. Kiran wayata da ogana yayine yana min neman gaggawa yasa na sulale nabar Anum da nufin zan dawo gareta. Daga haka bansan yanda ta ƙareba bayan taga ɗan uwana. Shin ya warware mata mu ƴan biyu ne, kokuwa ya karɓa mata matsayin shine ni?. Kwana biyu da yin haka na dawo cikin skull neman Anum sai dai na samu labarin cewa sun wuce saudia ita da ɗan uwana. Samakon zuwa da yayunta biyu sukai suka ganta da ɗan uwana daba musulmi ba”.
    “Duk da bana shiri da shi hankalina ya tashi matuƙa, dan kodai babu komai shiɗin ɗan uwanane ai. Duk zatona ko zasu cutar da shi ne? Naso binsu duk da bansan ina suka nufaba sai kuma wani aiki ya sake taso mana zuwa ƙasar Germany. Haka na tafi al'amarin ɗan uwana na damuna a cikin rai. Kamar wasa sai ga wannan tafiya ta jani tsahon wata huɗu, lokacin da muka dawo ƙasar Italy saina samu munyi graduation, course mate ɗina duk sun kama gabansu har ɗan uwana. Na bincika Anum sai na samu wai itama tabar makarantar. Daga jin haka sai kawai na nufi Nigeria, a zatona ɗan uwana ya koma gida. Amma kash sai na iske saɓanin tunani. An dai tabbatar min yazo wata biyu da suka gabata wajen rasuwar mahaifinmu, nima anta nemana amma ba'a sameniba. Ko damuwa banyi da mutuwar babanmu ba, sai dai jin ogan babanmu ya bama ɗan uwana maƙudan kuɗin aikin da mahaifinmu yay aiki a ƙarƙashinsa dan yaje ya juya hankalina ya tashi na bukaci sanin ina ɗan uwana yake?. Mamanmu bata saniba, abinda kawai ta sanarmin shine ya sake barin ƙasar, bakuma susan ainahin ƙasar daya tafi ba. Yadai bar musu kuɗin da zasu ishesu, tare da musu alƙawarin nanda shekara guda zai dawo musu da daddaɗan labari. Nayi ƙwafa kawai bance komaiba. Daga haka na tattara kayana zan koma. Sai dai kafin na wuce na haɗa harƙalla da abokaina akan zanke turo musu kaya insha ALLAHU suna saidawa su tura min kuɗin. Sunko amince tare da min alƙawarin bazasu bani kunyaba. Daga haka na tattara na koma inda na fito, babu wani zancen nasarar da naci a karatuna dana zauna naima mahaifiyarmu. dan koma ban faɗaba nasan ɗan uwana ya gama tona mata dukkan zance a kaina”.
  “Ban sake sanin ina ɗan uwana yakeba, ba kuma mu sake haɗuwa ba sai bayan kusan shekara, ana gab da zai cika alƙawarin daya ɗaukama iyayenmu na komawa garesu da daddaɗan albishir. A lokacin naje kai kaya ƙasar Syria ne. Kwatsam zamu shiga wani shopping mail ni da abokin tafiyata sai ga twin Brother ɗina tare da balarabiyar yarinya dana taɓa haɗuwa da ita a Italy a bazata. Da gani har shi babu wanda baima ɗan uwansa kallon mamaki ba. Hakama mafi yawan jama'ar wajen kallon mamaki suke mana da al'ajabi. A zahiri dai gashi muna tsananin kamanni, amma a shigar sutura da yanayi bama muyi kama da ƴan yanki ɗaya ba. Ni na fara sakin murmushi ina kallon jaririn dake rungume a kafaɗarsa, sannan na kalli Anum na sake kallonsa. Goshpower kaine anan kuma?”.
  “Shima Murmushin ya saki a karo na farko yana girgiza min kai, yace my twin bro, wannan suna yanzu na bar maka. A yanzu sunana IBRAHEEM ne, wannan matatace Anum, ga yarona Abdul-Maleek. Woow!! Na faɗa ina dariya da tafa hannu, kafin na miƙa hannun ya ɗoramin jinjiri Abdul-maleek. Yaro ƙyaƙyƙyawa mai tsananin kama da mahaifiyarsa, sai dai ya kwaso kamannina nima ni da ɗan uwana kaɗan. Ganin dai da gaske munsan juna abokin tafiyata ya barni tare da su yana faɗin mu gaisa shi zaije ya kai kayan zuwa anjima saimu haɗu. Na amsa masa da jin daɗi, dan koba komai ina buƙatar keɓancewa dama da ɗan uwana dan naji yaya batun kuɗin daya amso a Nigeria suke. Dan ko kaɗan banji wani damuwa da fahimtar ya koma musulmi ba. Kamar ya shiga raina kuwa. Sai ya buƙaci mizai hana muje gidansa kawai, ashe nan yake da zama yanzun. Mun shiga danƙareriyar motarsa dani da ke wahalar nema da shiga haɗarin rayuwa ko wadda bata kamitaba bani da ita. Wannan abu ya sosamin rai, amma sai ban nunaba muka shiga, suna gaba shida matarsa niko ina baya tare da jaririnsu a hannu. Al'amari bai kuma tadamin hankaliba sai da muka isa ƙaton gida da yaji kayan more rayuwa a matsayin wai nashine. Lallai nasha kallo, cikin mintuna kalilan kuma matarsa ta gama cika gabanmu da kayan ciye-ciye. Sai bayan munci mun ƙoshi mukai gaisuwa da tambayar bayan rabuwa. Bai ɓoye min komaiba daya shafesa bayan rabuwarmu”.
  Yace, (Ɗan uwana kamar yanda na sanar maka wannan itace matata, mun haɗu a jami'ar Italy dakaƙi nutsuwa ka ƙarasa. Da farko tsakanina da ita abota ce, sai daga baya muka fahimci muna son juna. Sai dai ta tabbatarmin babu yanda aure zai kasance a tsakaninmu saboda addinimu ba ɗaya baneba. Hankalina ya tashi domin ina tsananin ƙaunarta. Nai alƙawarin inhar zata yarda mu zama ma'aurata zan koma addininta. Ta sake tabbatarmin indai saboda aurenta ko soyayyar da nake matane zan zama musulmi wannan bazaisa ta yarda ta aureniba. Na musulinta kawai domin ALLAH badan tarayyarmu ba. A hakanma na yarda na amince, a randa muke shirin zan karbi shahada aranar ƴan uwanta biyu sukazo dubata. Sun nuna mata tsantsar ɓacin rai nayin tarayya dani, harma yanda ake musalta musu a cikin makarantar mun zama tamkar wasu miji da mata. Dagani har ita hankalinmu ya tashi muma. Dan tunda nake da ita ko maganar banza bata taɓa shiga tsakanina da itaba. Bata taɓa yarda ko zama gab da juna munyiba balle akai ga aikata wani abu mara ƙyau. Ni bamma taɓa kawo wani mummunan al'amari tsakanina da itaba kamar yanda nasan itama hakanne daga gareta. Kawai dai ALLAH ya haɗa jininmune kawai, kuma ina koya mata karatu. Duk yanda mukaso su sauraremu sunki, daga karshe ma suka tattarata wai zasu wuce da ita. Banyi ƙasa a gwiwa ba wajen tattara duk abinda nake da shi na bisu batare da sun saniba. Sai da muka dira ƙasar saudi-arebia suka fahimci jirgi ɗaya ma muka shiga da su. Sun nuna jin zafin binsu da nayi, amma sai basu hanani na bisu har gidansu ba. Koda muka isa gidansu sunma iyayensu bayani akan dukkan alaƙar dake tsakanina da Anum. Maimakon nai zaton za'a koreni sai naga saɓanin hakan, dan kuwa sun yarda da bukatata ta zama mai salla. Amma babu zancen aurena da Anum, dan suncemin yarinyarsu karatu takeyi. Duk da na shiga tashin hankali saina amince a hakan zan musilinta ɗin. A take kuma na amshi shahada. Komawata musulmi ya sake canja komai, dan kuwa sunmin gagarumar ƙyauta maiban mamaki ta maƙudan kuɗaɗe wai na riƙe kaina, tare da haɗani da wani malami dazan dinga ɗaukar ilimi a hannunsa a ƙasar Italy. Satina biyu a saudia na dawo saboda karatuna. Amma daka ganni kasan bana cikin hayyacina saboda rabani da akai da masoyiyata. Duk na rame na fita hayyacina, amma hakan baisa nayi sakaci da karatuna ba. Na cigaba da neman ilimin addini da zana jarabawar ƙarshe data rage mana na tsahon watanni biyar. Har muka kammala jarabawa banji labarin kaba. Na bincika ance bakaje Nigeria ba. Hankalina ya tashi matuƙa. Amma yaya zanyi. Bayan yin graduation ɗinmu na tattara zan koma gida ƙasata. Amma maimakon nayi 9ja direct saina kasa haƙuri na nufi Saudia wajen Anum. Nayi mamakin tarbar dana samu daga iyayen Anum da ita Anum ɗin kanta daya kasance tazo hutu, dan lokacin karatunta ya dawo nan ƙasar Syria. Albishir na farko da suka faramin shine bani auren Anum, ashe dama sun gwadanine dan suga da gaske nakeson komawa addinin islama kokuwa dan son ƴarsu?. Shiyyasa suka haɗani da malamin dake koyar dani batare da nasan bayanai yake basu ba a kaina. Nayi farin ciki nayi kuka dan daɗi. Sai dai da aka nema na gabatar da iyayena na fito fili na tabbatar musu  akwai matsala. Dan nasan kaf danginmu babu wanda zai amshi canjawata matsayin musulmi balle kuma auren musulma kai tsaye. Naji tsoron Anum zata sake kuɓucemin sai gashi ba hakaba. Dan duk da abinda na sanar musu sai gashi sun amince sun bani aurenta. Bayan ɗaurin aurena da Anum an bamu wajen zama kafin ta koma makaranta. Watanmu ɗaya da tarewa ta koma makaranta, ni kuma naje gida Nigeria, sai dai kowa ya tambayeni ina kake sainace kanacan baka ƙarasa naka karatunba sai next year. Na tarar jikin babanmu yayi tsamari, amma sunki kaisa asibiti. Inada kuɗaɗe masu nauyi a accaunt dana samu saboda musilintar da nayi, dan haka nai amfani dasu wajen kaisa babban asibiti aka fara bashi kulawa. Sai dai kash, kwanakinsa huɗu a asibiti ya rasu. Bayan rasuwarsa da kusan sati biyu nace musu zan koma domin yin kasuwanci. Ananne ogan daddy ya bani kuɗaɗen daddy, wai yace a bamu idan munzo, tunda mune manyan ƴaƴansa maza. Na amsa kuɗi na basu wanda zasu wadacesu na koma saudia. Mahaifin Anum shine ya ɗaurani akan harkar kasuwanci acan ƙasar Syria, ya bani shawarar na koma can kusa da matata ina kasuwancina tana karatunta. Naji daɗin wannan shawara kuwa. Tafiyata Syria ta zama tushen nasarata, dan ina zuwa na iske matata na laulayin ciki. Nayi farin ciki matuƙa, harma bansan yaya zan musalta makaba. Haka na zauna kulawa da ita tare da fara kasuwancina. Cikin amincin ALLAH sai gashi dan danan na haɓaka. Saboda na farane da kuɗaɗe masu nauyi. sannan kuma ta hannun babban mutum irin mahaifin Anum. A haka cikin Anum ya shiga watan haihuwa, tana gab da haihuwa na sayi wannan gidan da nake ciki, tare da motar hawa. Sannan na zauna na banbance dukiyar da take matsayin mallakina, na kuma fidda wadda ta kasance ta mahaifinmu. Kwanaki uku da yin haka Anum ta haihu namiji, wanda yaci suna Abdul-malik. bansan yaya zan bayyana maka ɗunbin farin cikinaba ɗan uwana. Amma babu abinda zancema ALLAH sai godiya. A yanzu haka watan Abdul-maleek uku a duniya, muna shirin zuwa Saudia ne domin nunasa ga dangin Anum dan babu wanda ya taɓa ganinsa sai mahaifinta da yazo mana nan sanadin harkar kasuwarsa. Daga Saudia kuma zamu wuce Nigeria na nunata ga dangina, na kuma sanar musu na zama musulmi duk da a tsorace zuciyata take. Dan yanzu haka maganar da nake makama nayi cinikin wani gida a Lagos, idan munje can zamu ɗan zauna kafin hutun Anum na ƙarshen shekara ya ƙare. Waɗanan takardun sune takardun shaidar company na dana mallaka da dukiyata. Insha ALLAHU kuma zan mallakashi ga Abdul-maleek ne. Dan haka kaima inason ka zama shaida, kaimin signing anan wajen, a duk lokacin da yakai shekaru talatin na girma zan mallaka masa shi. Wannan kuma sune takardun dukiyar mahaifinmu, idan nazo Nigeria mu dukanmu zamu haɗu mu saka hannu alamar tabbatarwa da banawa bane ni kaɗai).
 “Rungumesa nai a lokacin, na nuna masa tsantsar jin daɗina da wannan ƙoƙari nashi, tare da bashi goyen baya akan zamansa mai sallah. Yaji daɗin yanda na bashi goyon, hakama matarsa. Sai dai ni a cikin zuciyata ƙulla ta yanda zan kwashe waɗanan takardun nakeyi, tare da damfare duk wata dukiya da yake fankamar ya tara. Banbar gidanba sai dare, na tafi da ƙudiri kala-kala a cikin raina da zuciyata”.
 “Washe gari ma naje na samesu, shine ya ɗaukeni ya zagaya da ni duk inda companys ɗin suke guda biyu. Na ƙara girgiza da wannan al'amari, dan dukiyace bata wasaba ɗan uwana ya tara. Tofa sai tunanina ya ƙara faɗi da girmama. Dan koda nabar wajensu a ranar kasa barci nayi, har takai na fito na bayyanama abokin tafiyata. Yace na bashi dama zaiyi tunanin ta yanda dukkan wannan dukiya zata zama tawa, amma sai nan da kwana biyu mun gama abinda ya kawomu zai faɗamin hukuncin daya yanke. Naji daɗi, na kumayi murna. Sai dai wayewar garin ranar al'amari ya canja salo, dan bamusan yaya akaiba aka kama wanda muka kawoma kayan cocaine. Har bincike yazo ta kanmu. Da farar safiya mukaji jiniyar motocin ƴan sandan ƙasar. Hankalina ya tashi matuƙa ni da abokin tafiyata, cikin zafin nama muka samu nasarar tserewa ta bayan gidan kafin ƴan sanda su gama shigowa gidan. Muna barin gidan muka rabu nida abokina, domin wannan gudune na ceton rai, kuma hakan abune da kowa ya sani daga tsagera. Idan bala'i ya tunkaro kowa takansa yakeyi. Ba'a sauraren dukiyar da aka tara balle abokantaka. Cikin kiɗima na nufi gidan ɗan uwana, dan duk da wannan bala'i da nake a ciki ban manta da batun takardu ba. Ina isa na samesu a tsakar gida suna hutawarsu cikin kwalliya. Dakewa nai daga ruɗanin da nake ciki na amshi jaririnsu, tare da faɗama matarsa nifa inajin yunwa. Dariyar tsokana suka dinga min, ɗan uwana na faɗin to nazo nayi aure, yafimin wannan gararin, danshi sofa yake na dawonan tare da shi mu haɗa ƙarfi wajen kula da kasuwancinmu. Murmushi kawai nayi, na shiga daga ciki ɗauke da yaron. Matar ta shigo ta bani abinci. Tana kammala haɗamin komai ɗan uwana ya shigo, kallonta yay cike da so da kauna, yace tunda ga bro yazo kizo muje muyi shopping ɗin nan da bamuyiba jiya, sai mubar Maleek tare da shi dan harmu dawo da wahala ya farka. A take ta amince da shawararsa. Yayinda ni kuma kaina ya kawomin wuta a take. Jacket ɗin jikina na cire jin yana faɗin bara ya karo riga a saman kayansa. Nace bro indai rigace ga wanann ka saka nasan zata maka ƙyau, dan yanzun nan dazan fito na ganta a wani shago na siya. Nama tambayi biyu akace babu. Cike dajin daɗi ya amsa, dan shi mutumne mai saukin kai. Sannan bashi da saurin zargi. A gabana matarsa ta taimaka masa ya saka suna dariya da yaba ƙyan da rigar tai masa. Murmushi nayi ina dubansa na ajiye yaronsu na tashi ina gyara masa rigar, cikin dabara na saka masa wayata da wallet ɗina a aljihu, na zare tasa wayar da wallet ni kuma. Sunmin sallama sun wuce bayan sun tambayeni abinda nake buƙata a siyomin nima, dan yace idan ya dawo zamuyi magana akan zamana a gidan. Suna fita na kulle ƙofar falon, na bar yaron anan na shiga cikin ɗakinsu binciken takardu dama duk wani abu mai amfani. Duk kuwa da a raina ina addu'a da fatan tarkon dana ɗana musu ya zama sanadin tafiyarsu har abadan. Komai na gansa, dan haka na tattare tsaf na hada a jikka, na fito falo inda yaron ke barci na ajiye tare da zaman jiran sakamako”.
  “Mintuna talatin kuwa ban rufa da zamaba saiga babban labarin da nake jiran gani daga television. Ɗan jaridan  dake bada rahoto ne ke magana cikin tsantsar sarƙewar harshe, akan samun nasarar kama mutane biyu da suka shigo daga ƙasar Italy da hodar ibilis. An samu nasarar cafke ɗaya a airport, ɗaya kuma daidai traffic light tare da matarsa. Sai dai bisa kuskuren guduwa da sukayi na gardamar su basusan komaiba ƴan sanda suka harbesu, wanda bisa tsautsayi suka matu har lahira. Sai ga gawar ɗan uwana an nuno tare da matarsa kwance cikin jini. Hannayensu riƙe dana juna. Ga ƴan sanda na lalube wallet din dana saka masa tare da wayata anata faman bincike. Ko ɗar banji a raina na nadamar yin hakanba, dan koba komai asirina ya rufu, zan fara sabuwar rayuwa. A take na ƙarasa haɗa duk wani abu mai muhimmanci dake gidan, tare da kayan yaron na shiga mota na fice a gidan. Na tabbatar yanzu bazan fuskanci kowacce irin matsalaba, musamman daya kasance hankalin jami'an tsaron ya koma gaba daya akan nasarar cafke masu laifi. Aiko banci karo da kowace matsalaba wajen barin ƙasar ta mota. Duk da naci uwar wahala ga yaro nata zubamin kuka ban damuba. Haka nai nasarar fita a ƙasar zuwa ƙasar dake maƙwaftaka da su, acan kuma nabi jirgin ruwa, inda anan ne na haɗu da Chioma, itama tsagerace ta kanta, dan kuwa kusan duk irin harkokina shi takeyi, sai dai ita oganta a Nigeria take. A dai takaice na samu nasarar komawa Italy tare da jariri da ɗunbin dukiya da takardun kaddarori da taimakon Chioma. Ogana yayi farin cikin ganina dajin labarin ta hanyar dana kuɓuta, dan haka yaymin alƙawarin taimakona ta hanyar tabbatar duk waɗannan kaddarori na ɗan uwana a tafin hannuna. Yanda Chioma ke taimakona da rainon jariri dana canjama suna da John ne yay sanadin ƙulluwar soyayya mai ƙarfi a tsakaninmu har mukaima juna alƙawarin aure. Ta matsa matuƙa muyi aure sannan mu koma 9ja dan haka na amince mata saboda nima ina sonta. Bayan aurenmu muka nufi ƙasar haihuwarmu cikin danginmu. Wanda zuwa yanzu labari ya gama zuwa kunnen danginmu na rasu ta hanyar kamani ina safarar hodar ibilis ni da wata, dan a haka labarin keta yawo. Kowa kuma yana ɗauka ni aka kashe, saboda kowa yasan halina. ni kuma nine ɗan uwana. Munzo Nigeria ne dama da shirin hutu mai dogon zango, dan ogana ya tabbatarmin dolene inyi nesa da shiga kowacce ƙasa. Inba hakaba kuwa babu makawa sai an bankaɗo ainahin gaskiyar nine mai laifi ba ɗan uwanaba. Nayi amfani da wannan shawara kuwa, dan haka na yada zango a Lagos gidan da ya sanarmin ya saya ta hanyar abokinsa. A labarin nanfa da nake baku kowa ya ɗauka dama nine aka kashe, dan ansan nine tsagera, ɗan uwana kuma shine ni. Dan haka na canja sosai wajen ɗaukar ƙyawawan halayyar ɗan uwana na yafama kaina akan dole. halena kuma na ɓoyesu, dagani sai matata muka sansu. Ban wani cika burin ɗan uwana ba na mallakama mamana da ƙannenmu dukiya ba, sai dai naja ƴan uwan nawa a jiki wajen sakasu cikin harƙallolina. Bansan yaya akai Godwin ya fahimci banine twin bro ɗina ba, sai kawai rana tsaka ya fuskanceni da wannan zance shi da Mike. Na matuƙar tsorata da firgita, amma sai Chioma ta bani dabarun maidasu a hankalinsu ta hanyar ƙara jansu jikina da rufe bakunansu da dukiya mai tsoka da kuɗaɗenta. Danni a lokacin bawani kudine da niba. Sunko bi sun tsuke bakunansu kuma, tun daga nan suka zama sunsan kowacce irin harƙallata, sun kuma san John ba ɗana baneba”.
    “Abinda ya faru baisa na daina harƙallataba, sai harkokine suka sake buɗewa sabbi dan yanzun dukiyar Chioma muke juyawa, nazama jan wuya anan Nigeria, ta hanyar turomin da kaya da ogana yakeyi. Cikin shekara huɗu kacal na shahara, na kuma sakeyin kutse cikin addini har saida na zama Pastor a wata ƙaramar church duk da babu wani ilimi da nake da shi. Zuwa lokacin John ya fara wayo, yanada shekara huɗu, dan ko ina zuwa yake, ga surutu a bakinsa ba'a magana. Yanda yaron ya shiga ranmu muke tarairayarsa bazaka taɓa kawowa a ranka ba dɗanmu bane, dan soyayya ta gaske Chioma ke nuna masa. hakan yasa na ƙara sonta a raina, dukda kaf dangina basa sonta dan ta rainasu, su kuma gani suke ta ƙwaceni ta hanani taimaka musu bayan kuma dukiyarsuce tunda dai kallona suke a matsayin twin bro ɗina. Dukiyar ɗan uwana tazo hannuna, sai dai ba dukantaba, dan wata an tabbatar da dolene sai John ya girma sannan  nasoba kuwa dole na haƙura, na cigaba da juya abinda ke hannuna ta hanyar harƙalla daban-daban. A wannan lokacin ne naje ƙasar France yin wani couse na watanni tara, dan rashin yawan ilimi nason min tangarɗa akan zamana pastor. inda acanne muka haɗu da Sooraj Hashim Jibiya. Bayan korarsa da akai a makaranta sanadin dukan da yaymin nai jiyya kusan ta watanni uku, da ƙyarma na kammala abinda ya kaini na dawo gida cike da alwashi kala-kala akan Sooraj dama yankin daya fito gaba ɗaya. Dan nayi alƙawarin sanadin abinda ya aikata mani saina tarwatsa duk danginsa da jama'ar yankinsa. Wannan shine dalilin farkon fara sato yara daga yankinsu ana kawomin ina cinikinsu. Sai dai na gaza lalubo a ina Sooraj yake? Dan ko'a wancan karon dama bansan taka-maimai shi ɗan ina bane, nadai san musilmine ɗan arewa. a zahiri kuma na lulluɓe True color dina da rigar addini, babu mai cewa ni shege ne. Cikin kanƙanin lokaci na shahara, dukiya da girma suka zauna saina tattaro na dawo Abuja. Wani halaye da John ya fara nuna mana na ƙyamar addini da wasu abubuwan namu duk da ƙanƙantar shekarunsa yasa hankalina tashi. Dan da alama yaron yanada wata baiwa dake nuna ya fahimci kamar muɗin ba iyayensa bane. Mike ne ya bani shawarar zuwa gidan boka a kulle tunanin Yoohan gaba ɗaya, koda ya girma bazai taɓa kawo a ransa muɗin ba iyayensa bane koda yaga rashin kamansa da Chioma. Naji daɗin wannan shawara, nakumayi amfani da ita. Bayan munje wajen boka ya amsa zai mana aiki, sai dai aikin zai zama sanadin saka ciwon rashin barci ga John lokaci-lokaci. A take kuwa muka amince, akai asiri John ya koma tafin hannunmu sosai. Duk abinda muka sakashi babu tantama yake mana, sai dai ban taɓa yarda yasan ɓoyayyar harƙallataba Mamana ma da sauran ƴan uwana nasa akai musu asirin da bazasu taɓa tunanin ko kawowa a ransu niɗin ba ɗan uwana bane. Ana haka Chioma ta haihu twins itama, Gebrail da Joy. Nayi farin ciki sosai da samuwar nawa ƴaƴan, amma samun nawa baisa naji tsanar Yoohan ba. Bayan su Joy Chioma bata sake yarda ta haihuba sai da John ya shiga jami'a ta sake haihuwar Victoria. Ta sake Abraham wanda cikinsa yazo mata babu shirin hakan, dan tace daga yaƴa uku ta gama. To ashe da rabon zuwan Abraham. Abinda yasa nasaka Solomon kullum yake tare da John tun bayan gama karatunsa, saboda tsoron kar wajen yawon ƙasashensa da aiki ya tilasta masa yin  gamo da wani dangin mahaifiyarsa ƙwaɓata tayi ruwa. Shiyyasa dukkan motsinsa sai na sani ta hanyar Solomon”.
    “Abu mafi ɗagamin hankali daya faru shine tarayyarsa da Sheikh Sooraj. Lokacin dana san wannan alaƙa hankalina yayi ƙololuwar tashi,  na kumayi murna dan sanadin John maƙiyina dana ɗauki shekaru ina bulayin nema ya bayyana. har ƙauye naje mukai zaman meeting da sauran mutanena, dan saboda gudun irin haka yasa na cusa masa ƙiyayyarsu tun yana yaro, amma daga ƙarshe sai gashi abinda nake gudun ya auku. John ya xama musulmi kamar mahaifinsa. Ranar nayi tamkar mahaukaciya a gidan nan, harma na yanke hukuncin kashesa kawai na huta bayan na sakashi ya sakamin hannu a takardun da naketa a jiya tsahon shekaru, dan company ɗin yanata haɓaka zuwa yanzun, sai dai ina mamakin ta hanyar wa hakan ke faruwa?. Su Mike ne suka haɗu wajen bani shawarar mizaisa na damu da musilincinsa. Sun san dai babu ta yanda za'ai ya iya gano shiɗin wanene saboda asirin da ke a kansa. Sooraj kuwa amfani zamuyi da kusancinsa da John ɗin mu yashe masa asusunsa tsaf mubarsa da ɗimautar ƙwaƙwalwa da bugawar zuciya. Amma wai koda na tuntuɓi John akan mike alaƙarsu sai ya nunamin wani aiki yakeyi akan Sooraj ɗin. Nafa yarda da shi har cikin raina. Saboda nasan irin horon danai masa tun yana yaro akan wannan yanki. Har raina daɗi nakeji zai ɗaukamin fansa akan abinda Sooraj yaymin tsahon shekaru, dan duk da korar da akai masa a makaranta wancan karon baisa na huceba, na kuma daɗe ina addu'ar haɗuwarmu amma hakan bai yuwuba sai yanzun. Ban fahimci John folani yake a kwalayeba sai akan aurensa da ɗiyar Sooraj, idan nace zan bayyana muku halin dana shiga ni da matata dasu Mike a wannan tsakanin ɓata lokacine, da ƙyar Godwin ya kwantar min da hankali akan na amince da auren, bayan anyi mu kashe yarinyar yanda Sooraj zaiji ciwo sosai a ransa kafin kuma mu yashe masa asusunsa. Wannan shawarace ta kwantarmin da hankali na amince akai aure batare dana yarda na nunama Yoohan nasan ya musulintaba, sanann matata ma ban taɓa faɗa mata ya zama mai salla ba dan nasan tana son John sosai fiyema da ƴaƴanta, kodan shita fara samu matsayin ɗa ne kafin ta haifi nata oho. Shigowar ɗiyar Sooraj cikinmu ta sake ruguza komai na shirinmu, dan yarinyace hatsabibiya. takai ko ganinta nai sai naji matsanancin tsoro na shigata. Bala'in kwarjini takemin kamar ubanta, gata bata da tsoro. Ban sake tabbatar da yarinyarnan abar tsoro bace sai randa ta shigar min ɗaki, ta kuma nuna ba ita bace. Da gaske nima ɗin na yarda ba ita ɗin bace a lokacin, sai daga baya na gane itace ta hanyar cctv dake a falona wadda ko matata batasan da zamanta ba duk da kuwa harƙalla ɗaya mukeyi, kai hasalima na sakatane domin ita dan haka harkarmu take a kullum bama yarda da juna. Bawai ina tunanin itama zata cutar dani bane, dan ina tsananin ƙaunarta, na kuma yarda da ita. Ina tsoron kar dai cikin abokan harƙalla wani yay amfani da ita ya cutar dani ne dai. Sosai hankalina ya tashi da lamarin yarinyar, da kuma tunanin mahaifintane ya turota leƙen asirina. Sai kawai na shirya yanda Doctor ɗin da zasu mata aiki zasu kashe min ita ta cikin sauƙi kafin na dawo kan John ɗin shima. Naji daɗin abinda Gebrail yay mata, dan nasan nesa tazo kusa akan aiwatar da aikina a kanta, sai dai kash Dr Mateo ya lalatamin burina. Naji takaici, naji ciwo, na kuma yanke shawarar halaka John da yarinyar gaba ɗaya da zarar sun dawo ƙasar nan. Zan fara halakata ita da duka danginsu da ubanta kafin shi ma na juyo kansa. Amma taurin kai irin na John da bani da tantama wajen ubansa ya gada sai ya sake ruguzamin shirina. Ya koro Solomon, ya kuma ɗauketa daga Austria ya canja mata ƙasar da bani da damar shiga, dan tuni aka hanani lasisin shiga ƙasar U.S. Wamnan shine dalilin yimin katanga a garesu, na zauna dakon jiran dawowarsu ko zuwansu ƙasar a tare. A randa John ya dakarmin yaro wai ya shigar masa ɗaki naji kamar shima na halakashi da hannuna. Amma na taushi zuciyata dan nasan a tafin hannuna yake. Shina ƙanƙanin lokacine ya rage masa ai. Na tattara komai na ajiyeshine ban masa magana a kaiba dan banason ya zargi komai a kaina har sai randa ya sakamin hannu a waɗannan takardun, ya kuma kawomin shegiyar matarsa ƙasarnan. Dan nagama shiryawa tsaf akan yanda zan yashe asusun ubanta kaf na maidashi sifili. Wai kawai kwatsam rana tsaka saiga yarannan da ciki sunzomin gida. Lallai naga baƙar rana kuwa, dan da gaske ranar susucewa nasoyi gaba ɗaya. Randa na gama shirya ƙudirin aikata lahira suka baro Abuja batare da ko John ya sanar minba da yake shima tantirin ƙwallon shege ne. Nasa a biyota kanon, a daren da zasuzo bisa jagorancin Solomon kuma ƴan sanda suka ritsamin yaro a hanyarsa ta kawomin kaya daga ƙasar Cameroon. Da ƙyar yasha zuwa abuja, duk sun fasa masa jiki da bullets, amma sai yayi ƙoƙarin zuwa ya isarmin da saƙon na gudu, dan da gaske wanann tarkone babba aka ƙulla a kaina tsahon lokaci. wannan shine sanadin tserema ƴan sanda da nayi, sai da na bada ƙafa ta watanni biyu na dawo da baya saboda jin matar John ta haihu ta hanyar wani ɗan leƙen asirina. Na fahimci lokaci yayi da zai sakamin hannu a takardu, daga haka na kama gabana bayan na kasheaa shi da ɗan da matar tasa. Sooraj kuwa zan dawo masa da nasa shirin bayan ƙura ta kuma kwanciya.......”
   Kallonsa kawai kowa keyi a falon kamar sun sami television. Dan shi kansa Jay makircin na Goshpower ya matuƙar rikitashi. Ashe shine sanadin halakar ƙanwarsa da mijinta. Iya bincike sunyi bayan faruwan wancan al'amarin amma suka gagara sanin gaskiya, dan sudai basusan mijin Anum da wani twin Brother ba. Ba komai yaja hakaba sai sakacin rashin bincike danginsa koda a ɓoyene, duk da dai shi yaso yayi binciken a lokacin mahaifin Anum ɗin yace a barsa darajar gaskiyar yaron, a bashi dama har ya bayyana mana danginsa suma ya bayyana musu mu. Tunda dai shi sun gwadashi ta hanyoyi da dama basu samesa da wani mummunan hali ba. A lokacin haushi shi Jay yaji yace ya cire hannunsa akan batun, dan ya rasa wane irin so sukema mijin Anum ɗin. Ganin yanda ya dage da harkar nema da neman ilimin addini yasa shima Jay din ɗaga masa ƙafa ya bashi lokaci zuwa sanda Anum zata haihu, dan yayi alƙawarin da zarar ta haihu kosu Ummu sun yarda ko basu yardaba dolene yasan dangin mijin Anum ta hanyar tasa ƙeyarsu har Nigeria aje tare da shi. Sai gashi a dai-dai gaɓar da take shirin kawo musu ribar auren nata su gani su kuma je ga dangin mijin nata wannan al'amari ya bayyana. Wanda ta sanadin haka suka rasa ƴar uwarsu da mijinta da ɗanta. Suka kuma rasa ainahin gaskiyar zance akan zargin da akema mijin nata. Haka suka haƙura badan zukatansu sunsoba, suka ɗauka wannan itace ƙaddararta kuma. Tare da mahaifinta sukaje suka amshi gawarsu wajen ƴan sanda bayan ansha gwagwamaya suka sallacesu aka kaisu makwancinsu. Sai dai basuga gawar yaronba, sai suka ɗauka wani ya ɗauke gawar a cikin wannan rubibi. Sai dai a binda ya ɗaure musu kai rasa muhimman takardun mijin Anum a gidansa. Bayan wasu watanni kuma akazo musu da batun an ƙwace duka kaddarorin nasa dake a ƙasar ta Syria. Basu da ikon nuna rashin yarda tunda sunsan hakan shine dokar ƙasar ga duk wanda aka kama da irin wannan laifin. Badan zukatansu sunso ba daga haka suka rufe babin Anum da duk abinda ya shafeta. Sai kuma gashi kwatsam bayan tsahon shekaru sunci karo da mai tsananin kamanni da ita a Nigeria, tare kuma da mai tsananin kamanni da mijinta matsayin ubansa. Wannan abu ya rikita Jay matuƙa, harma yaji a aransa inama Ummu da mahaifin Anum na raye su tayasa wannan al'ajabi.....
 Ta ɓasan da Jabeer yayine ya sakashi dawowa hayyacinsa daga tunanin daya tafi, Jabeer ya nuna masa agogo da faɗin, “Boss asuba fa na gab da shiga, muyi abinda ya dace kafin masu ƙarfin faɗa aji suce wani abu”..............✍

[7/9, 5:30 PM] Sweet Sis: No. 77

…………Kai Jay ya jinjina masa zuciyarsa a matuƙar raunane ya dubi Yoohan da kansa ke a duƙe yana hawaye. Nu’aymah kanta kuka take hakama Umar. Cikin ɗacin murya da soyewar zuciya Jay yace, “Goshpower nama rasa abin faɗa a gareka. Dan kaine mutum na biyu da bazan taɓa yafemawa ba da mantawa da shi, bayan gagarumin zalincin da akaima rayuwata da barmin tabo a shekarun baya. Ka cika azzalumi na gasken gaske. Ni nan da kake ganina nine yayan wannan mata ta ɗan uwanka Anum. Mune mukaje har Italy muka taho da ita, tabbas inaji a raina UBANGIJI ya lulluɓe idanunmu daga garekane saboda wannan shine rubutacciyar ƙaddarar Yoohan, wannan wata hikimace daga hikimomin UBANGIJI, ya kuma fimu sanin dalilin yin hakan, kamar yanda ban isa goge abinda aka zana daga zuciya ba, haka ma ban isa canja abinda ya zama rubutacciyar ƙaddara ba domin ALLAH shine kaɗai masanin gaibu, sai yaso mu sani, sai yaso mu gani, sai yaso muji”.
A kallo ɗaya zaka fahimci a tsananin firgice Papa yake, dan jikinsa har ɓari yake ya dubi Jay, bakinsa ma rawa yake amma ya kasa cewa komai. Hakama Yoohan da Nu’aymah wani irin kallo mai firgitarwa sukema Jay ɗin. Ya furzar da huci mai azabar zafi da ɗauke kansa. Dan ji yake kamar yay fata fata da goshpower kawai kozai samu sassauci a ransa. Lallai yanaji a ransa idan ya cigaba da zama a gidan nan babu abinda zai hanashi huhhuda jikin Goshpower da bullets, dan haka ya miƙe da sauri ya fice hawaye na ziraro masa a saman kumatu. Komai dawo masa yake sabo a rai da zuciya. Gawar Anum da mijinta ne ke dawo masa cikin ido tamkar yanzu komai ya faru. Zafi da raɗɗi da ruɗanin da suka shiga da mutincin mahaifin Anum da ya taɓu a idon danginsa da al’umarsa a wancan karon na dawo masa a zuciya. Aƙidar larabawa ce wannan gudun zubewar mutuncin dangi. Idan kuwa aka samu kuskure wani abu ya auku na zubewar mutunci ga ɗayanku sai ya shafi kusan duk zuri’arku. To hakance ta faru ga zuri’ar Anum, dan sanadin wannan al’amarin mahaifinta yabar duniya, ƴan uwanta kuwa sai da suka bar ƙasar saudia. Tsakanin rasuwar Abban Anum da Ummu kuwa baifi watanni bakwai ba. Kuma hakan nada alaƙa itama da kasa goguwar tabon da aka ringa jifan Anum da mijinta da shi na safarar ƙwayoyi. Duk da su sunsan ba haka baneba, amma tayaya zasu fahimtarma duniya ba haka ɗin bane?. wannan ciwon shine ya tarwatsasu zaman cikin saudiya ya gagaresu duk da kasancewarsu manyan mutane.
A hankali Yoohan ya miƙe yabi bayan Jay kansa na juya masa, da ƙyar yake iya ganin wajen taka ƙafarsa. Jay na tsaye jikin mota ya kifa kansa kawai yana hawaye yaji an rungumesa ta baya. Kamar dama wannan damar Yoohan ya ke jira sai kawai ya fashe da kuka. Duk mai imani ya gansu a wannan yanayin sai yaji rauni ya ƙara riskarsa. Juyowa Jawaad yayi ya rungume Yoohan ɗin, hakanne ya sakashi sake fashewa da sabon kuka dan yama manta shi namijine a yau.
Jay dake murmushi yana bubbuga bayansa yasa hannu ya ɗauke nasa sabbin hawayen da suke sake zubowa yana kallon su Aliyu dake fitowa da Goshpower da yaransa daga cikin gidan. Basu Jabeer ba, hatta da papa kansa sai da zuciyarsa tai masa nauyi. Sai da aka gama tasa ƙeyarsu cikin motocin sannan Aliyu yazo inda Jay da Yoohan suke. Cikin lallashi yayma abokin nasu kuma ɗan uwan nasu magana akan ya kamata su wuce lokaci na tafiya.
Kai kawai Jay ya jinjina masa. Sannan ya ɗago Yoohan daga jikinsa, hannu yasa yana share masa hawayen daketa zuba babu ƙaƙƙautawa. Ya ɗanyi murmushi da faɗin, “Yarona bazai kasance rago mai kuka a gaban matarsa da jikana ba ai na sani”. Murmushi ya suɓucema Yoohan da sabbin hawaye a lokaci ɗaya, sai yay saurin sake faɗawa jikin Jay ɗin kuma.
Suma su Naser dake sharar hawaye duk ƴar dariya sukayi saboda yanda Yoohan ɗin yayi. Jay ya yafito Nu’aymah dake goye da Deen tana ta faman kuka itama. “Zo nan my daughter ki lallashi mijin nan naki naga da gaske ɗan shagwaɓa ne”. Ƙarasowa Nu’aymah tayi tana murmushi da hawaye. Jay ya sake ɗago Yoohan yana faɗin, “Kai dama ashe likitoci ragwagene ban saniba ni Muhammadu?”.
Cikin dariyar ƙarfin hali Jabeer yace, “Boss da alama kam, dan gashi Son ya tabbatar mana”. Duk sukai ƴar dariyar ƙarfin hali data rage musu nauyin zukata. Daga haka suka shiga motoci, dan an bincike gidan babu komai a cikinsa. Sabone ma da alama suma su papan jiya suka shigesa. Su Yoohan mota ɗaya suka shiga da Jay. Umar yaja motar, Jay na gefensa, Nu’aymah da Yoohan a baya. Su Abdallah kuma suka koma a motar da sukazo suma. Waya Jay ya ɗauka ya turama Baba malam text message dan hankalinsu ya kwanta, kafin ya juyo ya kalli su Yoohan dake taimakama Nu’aymah ta sakko da Deen daya sake farkawa daga barci.
“Abuja zan wuce da ku, zanyi magana da malam insha ALLAH”.
Sun amsa masa da girmamawa, dan shi kansa Yoohan baya buƙatar yin nesa da Uncle ɗin nasa sam.
Su Abdallah sun wuce gida kamar yanda Jay ya basu umarni, su kuma suka wuce airport domin komawa abuja, fatansu suyi sallar asubahi acan insha ALLAHU.

_

    Idan nace muku wani babba mai hankali a gidan su Nu'aymah ya rintsa  a wannan dare nayi ƙarya. Kamar yanda su Ahmad suka kwana zaune tare dasu Papa haka suma su baba malam suka kwana zaune cike da tashin hankali. Duk da ma Abdallah yayi ƙoƙarin kiran wani a gidan ya sanar masa anga su Yoohan ɗin amma network yayta basa wahala. Dole ya haƙura kawai musamman da labarin da papa ke basu ya ɗauke masa hankali da tunani.
      Motar su na shiga cikin gidan duk su baba malam suka firfito da yakema asuba tayi. Ganin babu su Aymah tare da su ya saka jikinsu ƙarayin sanyi kuma. Sai dai kuma Murmushin kwantar da hankali da Naseer yayi ya saka zuciyarsu samun sassaucin bugawar da takeyi. Su Abdallah suka ƙarasa garesu jikkunansu duk a sanyaye, dan gaskiya ba ƙaramin tausayin Yoohan zukatansu suke a ciki ba.
   Kafinma wani a cikin su baba malam yay magana malam ƙarami yace, “Abba ku kwantar da hankulanku duk an gansu, sai dai sun wuce abuja yanzu haka tare da Uncle Jay, harma da masu laifin”.

Kusan a tare suka shiga sauke ajiyar zukata, dan baba malam baiga text message ɗin Jawaad ɗinba dama. Jin haka yasa baba malam cewa, “Alhamdulillahi ala’kullihalin, inaga sai muje kowa yay haramar salla dan lokaci yayi”.

  Ina idar da salla kuwa kowa dole ya nema gado ramuwar barcin daya gagaresu. Musamman ma Umm da jininta ya hau ita da Hajjo.

★★★

    Ƴan Abuja ma dai suna sauka wucewa akai da su Papa station, madam Chioma natama mutane kukan iskanci wai Yoohan ya taimaketa kar sonshi ya kasheta. Wannan kalma ta daki zuciyar papa. Ya bita da kallon tsoro da firgici sai dai babu bakin magana dan shi koma tafiya baya iyayi saboda duka ƙafafun sunsha harbi.

   Ganin yanda Deen ke numfashi da ƙyarne yasa Yoohan bayan sunje gida sun sauke Nu'aymah su kuma suka koma massallaci. Suna idar da salla yace zaije ya samowa Deen magani dan an ɗibar masa sanyi. Jikin yaronma zazzaɓine.

  Nu'aymah na shiga Miemaa ta fito ta shiga da ita ciki dan Jay ya kirata dama. Ganin yanda Deen keta kuka yasa ta amshesa ranta duk a jagule da ɗaukar alhakin yaron da akayi. Bata wani zauna jan zance ba tai ciki da shi, tare da cewa itama Nu'aymah ta biyota tazo tai wanka dan duk a galabaice take. Ruwa mai zafi ta haɗa mata, shima Deen tai masa wankan da ruwa mai ɗumi sosai. ta kuma gasa masa jikin da towel dan tasan mugayen can ba ɗaukar tausayi zasuma yaron ba. Aiko anayi yana uban kuka. ana kammalawa tunkan ta tsamesa a ruwan har yayi barci. Tausayin yaron ya kuma kamata. Goyashi tayi domin yin salla. bayan an idar ta nufi ɗakinta da Nu'aymah ke can. Har tayi wanka tama shirya cikin doguwar rigar data bata. kasancewar ba salla zatai ba tana zaune tana matsa ƙafarta da tun ciwon dataita mata da cikin Deen har yanzu data haihu bata gama saki da ƙyau ba. “Yauwa ɗiyata kin idar?”.
   Kan Aymah a ƙasa tace, “Eh Miemaa ina kwana?”.
“Lafiya lau, ya gajiyar gwagwarmaya?”.
 Murmushi Nu'aymah tayi dan kuwa da gaske jiya sunsha gwagwarmaya mai wahalar mancewa a tarihin rayuwa. Miemaa ta bata Deen daketa ajiyar zuciya yana barci. “Kinga bashi abinci, kema bara na haɗo miki ko tea ne kisha ku kwanta ku huta”.
Babu musu Aymah ta amshesa. Miemaa kuma ta fita haɗo mata tea. Yanda Deen ke amsar abincinsa har tausayi ya bata. Dan ita dai acan bawani samun nutsuwar ƙwarai tayi wajan basa ɗinba. Ta shafa kansa tare da kissing goshinsa, daga shi har mahaifin nasa ɗunbin tausayinsu da ƙaunarsu ya mamaye mata zuciya. Babu jimawa itama Miemaa ta kawo mata tea da bread da soyayyan ƙwai. Amsarsa tayi da cewa. “Zauna kema ki karya, bara naje da shi babansa zai dubasa, idan kin kammala ki kwanta kema ki huta”.
   Godiya Aymah tai mata. Miemaa kuma ta fita.

   A falo Yoohan ya amshi Deen ya dubashi da bashi maganin daya siyo sannan Miemaa ta sake amsarsa ta goya. Sashen Awwab da baya ƙasar yana Spain aka kaisu. Jay yace suyi wanka su sha tea ga shi nan da Miemaa ta haɗa musu suyi barcin gajiya. Sun masa godiya. Su dukansu barcine a idonsu, hakan yasa basu wani zauna zaman maida yanda akayi ba. Dan Yoohan ma sai da yasha magani saboda ciwon kai. da taimakon maganinne ya samu barci mai nauyi yay gaba da shi.

__

     Su Aymah sunsha barci sosai. Bayan tashinsu duk suka sakeyin wanka. Zuwa lokacin gida ya cika da su Little bee. Sunsha kuka labarin da Jay ya basu game da ainahin gaskiyar rasuwar Gwaggosu Anum da mijinta. Da kuma tabbatar Yoohan ɗan uwansu. Lamarin ya taɓa musu zukata sosai duk da bama sanin Anum ɗin sukai ba su. Sanda ta rasu Little kaɗai aka haifa, bakuma wanda ya taɓa faɗa musu gaskiyar magana akan rasuwar tata sai yau. Deen yana hannunsu kowa ji yake da shi, hakama da su Yoohan suka tashi sai murnar kowa ta ƙaru. Anuwar ya rungumesa yana kuka. Shima Yoohan ɗin sai da ya koka. Ransa kuwa cike yake da ɗumbin farin cikin tsintar kansa a cikin dangin mahaifiyarsa. Ya ɗauki komai matsayin ƙaddara kamar yanda Uncle Jay ya faɗa.
Sunci sunsha tare, kafin su zauna kuma aka gabatar da juna. Sannan aka tsaida ranar da zasuje Oman wajen sauran dangin Anum da ke can a yanzu suna rayuwa. Anan kuma Nigeria za'a zagaya dasu cikin danginsu suma insha ALLAH.
   Kiran Jay da aketayine ya sakashi fita dole. Dan yau daga shi har Miemaa da little basu fita aiki ba. Duk da kuwa gari ya ɗauki ɗumi akan kama Papa da yaransa da akayi. Musamman daya kasance an saki video ɗin labarin da papa ya bayar akan saka twin Brother ɗinsa a tarko domin shi ya kuɓutar da kansa. Wannan al'amari ya girgiza zukatan jama'a sosai. Masana nata sharhi akan hukunci daya dace ace ya fuskanta. Wasuma gani suke a kashesan kawai shine babbar mafita ga ƙasar gaba ɗaya. Dan barinsa koda a prison ne wataran wani zai iya fiddosa a ɓoye tunda ƙasar tamu sai a hankali. Hakama jama'ar gari ba'a barsu a bayaba wajen maida yanda akayi dayin sharhi akan wannan al'amari.
  Lokacin da labarin ya isa gidan su Aymah har cikin kunnen Mama debora sai ta yanke jiki da faɗi. Dan su su Abdallah ne sukai zaman faɗa musu yanda komai ya faru ma. Kwasarta akai zuwa asibiti a rikice, su Victoria nata faman kuka dan suna ƙaunar kakar tasu. Musamman daya kasance yau sun wayi gari da wannan tashin hankali na halayen iyayensu da ya ƙara fitowa duniya taji. Basu da kamarta a yanzu, dan sun tabbatar ko ƙauyensu kam yanzu sai ya gagaresu zuwa, dan maimakon tarba da zasu samu daga jama'ar garin kamar da, yanzu idan sunje duka zasuci. 
Ganin ta farfaɗo baba malam ya hana a faɗama Yoohan. Yace a barsa shima ya hutama ransa, idan ta warware zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu sai suma a maidasu Abuja ɗin.

  Su Nu'aymah basu san hidimar da akeba. suna nan cikin zuri'ar data kasance ta Yoohan hankalinsu kwance, kowa zallar ƙauna da kulawa yake ƙoƙarin nuna musu. Tare da bama Yoohan labarin dangi kala-kala dana mahaifiyarsa, tare da hotunanta. Ranar dai haka suka kasance cikin ɗumbin farin ciki, dan ma fitar Uncle Jay ta rage armashin hirar.

A ɓangaren Jay kuwa ashe kirane na sirri ya samu daga manyan ƙasa. Inda sukai zaman tattaunawa dangane da shari'ar papa. Sun yanke shawarar a miƙasa hannun ƙuliya manta sabo da wuri. Wasuko sunce ai masa allurar poison tun kafin shiga kotun, dan suna tsoron abinda zai iya zuwa ya dawo musamman da Goshpower ya kasace yaron manyan shegun duniya ne. Babu hanyar da bazasu iya biba domin ganin sun kuɓutar dashi. Barin irin su papa a duniya kam ai tashin hankaline. Dan babu makawa a yini guda suna iya tada jama'ar ƙasa da ƙasar baki ɗayanta. 
    Shi dai Jay bai yarda ya tofa wata maganaba, dan suma ɗin ai baisan yaya nasu zukatan sukeba, balle ayyukansu na ƙarƙashin ƙasa. Sannan baima saniba ko suma ɗin wani abu sukesan binnewa ta wannan hanyar tunda kowa yasan yanda papa ke mu'amula da manyan mutanen ƙasar ai. Sai da duk suka gama surutansu yace shidai a nashi shawaran kawai su bari a miƙasa kotun, yanke hukunci aikin alƙaline ba nashi shi jami'in tsaroba. Idan kaga mai laifi ya rasa ransa a hannun jami'in tsaro sai dai akan kuskure ko kare kansa ga mai laifi idan yanada makami. Amma haka ɓakatatan basu da damar yima goshpower allurar poison. Duk da wasu sun nuna jin haushinsa shidai bai damuba. Yay musu sallama ya wuce office. Gudun zuwan abinda zaije ya dawo ya sakashi tattara duk wasu bayanai dake a hannunsa a yammacin ranar ya tura ƙara kotu sannan ya koma gida.
  Miemaa kaɗai ya sanarma halin da ake ciki, amma su Yoohan baice musu komaiba, saima sakawa yay aka kawo masa Deen da bai gajiya da barci saboda kasancewarsa jariri har yanzu. Kwata-kwata yau kwanansa tara kenan ma a duniyar. Amma ya fara cin karo da gwagwarmayar cikinta.
 Kasancewar Aymah jego take yasa Miemaa tsayuwar daka a kanta ta ƙarasa jegon anan, dan summa gama magana dasu baba malam idan su mama debora zasu wuto Abuja gobe idan ALLAH ya kaimu zasu taho mata da kayanta dana Deen kawai. Koba komai hankalin Nu'aymah yaɗan nutsu waje ɗaya yanzu, hakan yasata ƙagara ma a kawo mata kayanta ta koma sauraren lectures kota online ɗinne kafin suga abinda ALLAH zaiyi akan maganar komawarsu. Danshi kansa Yoohan harma ya ɗauki hutun ƙarshen shekara mai nisan zango sosai.
 Washe gari su Jay suka tattare al'amarin papa suka miƙa kotu, yayinda dangi keta tururuwar zuwa gidan Jay ganin Yoohan. Dan su Afrah duk sun baza labari ta waya. Khairiyya kanta da ba'a garin take aure ba sai gata a wannan ranar ganin yayansu. Duk da dai bama wani girmanta yayi sosaiba, amma dai little ta girmesa. shiyyasa abu kaɗan ke sakasu fara faɗa. Shi son girma ita son girma. Daya motsa tace shiɗinfa ƙanintane. Shi kuma yace ALLAH ya kiyaye ya zama ƙaninta. Abun nasu na bama kowa dariya. Musamman ma Nu'aymah.

WASHE GARI

     Washe gari su Mama debora da taji sauƙi duk da bata koma garau ba suka iso abuja saboda suna son halartar zaman kotu da za'ayi. Ba kowa ya matsa hakanba kuwa sai mama debora. Dan tasha kuka, acewarta tanason taga idon papa ko zaiji kunyar yaudarar da yay mata na saka ɗanta mutumin kirki a tarkon da aka kashesa.
   Da yake tafiyar mota sukayo, kuma sun taho da wuri sai gasu kusan sha biyu sun shigo garin Abuja. Yoohan na tsakkiyar dangi da keta cigaba da zuwa kiran Gebrail ya shugo wayarsa. Ɗagawa yay ya koma gefe. Cikin girmamawa Gebrail ya gaidashi da faɗa masa gasu sun shigo Abuja. Zasu wuce can gidanne kokuwa suzo nan gidan Uncle Jay ɗin su samesa?. 
 Yoohan yay ɗan jimmm kafin ya furzar da numfashi, yace, “Okay, inaga ku wuce can, nima gani nan zuwa gidan”.
Da girmamawa Gebrail ya amsa masa da to. Yana yanke wayar ya sami Uncle Anuwar da maganar, dan Uncle Jay baya nan ya fita saboda sunata kai kawo akan lamarin papa da yaransa su Solomon.
 Uncle Anuwar yace, “Yahya ai daka barsu sun wuto nanɗin kawai, dan an riga da an zama ɗaya yanzu. A gidan nan kuwa munada isassun masauki insha ALLAH. Sanann kusancin zama da zamu samu dasu yanzu zaisa suma idan sunada rabo sai kaga sun karɓa musulinci”.
  Cikin ɗan sosa wuya da jin daɗin wannan fata Yoohan yay murmushi idonsa nakan Nu'aymah da suke hira dasu Afrah acan gefensu. Yasan komi rayuwarsa ta zama a yanzu itace sila, dan haɗuwa da ita shine ya zama hasken da ya haska masa hanyar da yake taka ƙafa, iska yaɗan furzan da faɗin, “Okay Uncle bara naje zuwa anjima ai sai nazo dasu ɗin, kagama sannan Uncle Jay ya dawo”.

  Kamar yanda Yoohan ya faɗa bayan sallar azhur ya nufi gidansu. Duk an janye ƴan sandan da suke zagaye da gidan, ko maigadi yanzuma babu balle waɗannan guards da ke cike da gidansu a da. Rayuwa kenan, ka shuka alkairi sai ka girbe abinka. Horn yayi kusan sau uku sannan Gebrail yazo da ɗan gudunsa ya buɗe masa gate ɗin. Sai da ya gama ƙarema harabar gidan kallo da duk motocin dake cikinsa kafin ya furzar da nannauyan numfashi ya fito, dan Gebrail ya buɗe masa tuni.
  Cikin gidan suka nufa yanama Gebrail tambayoyi, shi kuma yana amsa masa cike da damuwa, dan har cikin ransa kunya da ƙaunar Yoohan ce cike da ruhinsa. Bama shi kaɗaiba, duk sauran ƴan uwansama hakane. Suna shiga kuwa da gudu su Victoria sukazo suka rungumesa. hakama mama debora rungumesa tai tana kuka da rera addu'ar neman sakayya a garesa da yarensu. Ba itaba ko mai saurarenta yaji yanda take addu'an zaisan akwai tausayi a ciki.
Da ƙyar Yoohan ya lallashesu sannan suka zauna suka ɗan sake tattaunawa. Mama debora tace tunda har papa ya kashe ɗan uwansa da matarsa itama ta yarda a kashesa. Yoohan dai kunyar su Gebrail ya hanashi cewa komai akan iyayen nasu, daga ƙarshema yace su shirya zai wuce da su.

   Zan iya cemuku a ɗar-ɗar su mama debora suke da zuwa gidan Jay, kamar yanda sukaita ɗari-ɗarin zuwa kano gidansu Nu'aymah. Sai dai abinda ya basu mamaki anan ma sai akai musu tarba ta mutunci da kulawa. Hakan yasa suka sakeji a ransu lallai hausawa nada ƙyaƙyƙyawar zuciya a duk inda suke. Sannan musulmai ba mutanen banza bane kamar yanda a kullum papa ke musu huɗuba a gida da church. Sai gashi tundai suna ɗari-ɗari har suka saki jikinsu. Bayan Jay ya dawo suka zauna aka ƙara tattaunawa. Mama debora da su Momy Destiny sunsha kuka. Su kansu su Joy sunji ciwo da kunyar halayen iyayen nasu matuƙa. Sunata kuka da bama Yoohan haƙuri. Shi dai murmushi kawai yake musu. Nu'aymah ma haƙuri sukaita bata akan abinda sukai mata. Tace babu komai ita ta yafe musu. Gebrail kam ko yarda su haɗa ido Aymah baya yarda suyi sam saboda kunya. Ita har dariyama abin ke bata. 

    Ranar data kasance za'a shiga kotu da su papa ƴan jarida a abuja har bama magana. Kowa burinsa ayi komai akan idonsa. Kuma burin kowa ya nuna komai live. wannan kuwa duk a cikin shirin su Jay ne. Sun gayyato ƴan jaridune ta kowanne ɓangare dansu katange dukma wata kitumurmura da za'a iya ƙullawa game da shari'ar.
    Kotu ta cika maƙil itama da al'umma, musamman waɗanda aka samu ƴaƴansu a gidan papa. Duk da ma wasu iyayen nasu sun gagara ganesu, sukuma basusan daga inda aka ɗakkosu ba dan tun suna ƙanana ne. Shari'a ce da bata buƙatar lauya sam, saboda komai na papa a bayyane yake. Zamane kawai da za'ai maganar ƙarajin abinda ya shuka a yanke hukunci kuma.
  Yoohan dai da farko baiso su Gebrail su bisu ba. Amma sai Uncle Jay yace ya barsu suje ɗin dan wannan itace kaɗai damar da zasu samu ganawa da iyayen nasu. Badan yasoba kuwa suka shirya suka tafi kotun, cikin amincin ALLAH kuwa sun sami gaba-gaba saboda sun tafi da wuri.

 Sai da kotu ta gama cika tab da al'umma, alƙali ya shigo sannan aka shigo da papa da su Mike. Papa saboda harbin da yasha a kafafu sai a wheelchair, sauran kuwa babu ko ƙwarzanen duka a jikinsu amma a ido zaka gansu a wani irin bala'in galabaice. Su Jay kaɗai sukasan irin horon da sukema rayuwarsu cikin hikima. Bayan buga gudumar alƙali kotu tayi tsitt na wasu mintuna, dan da anata ƴan kananun magana saboda shigo da su papa da akayi. 
Alƙali ya sakeyin gyaran murya sannan ya fara magana, “Wannan shari'a ce da kowa zai iya fahimtar bata buƙatar wani kaiwa da komawa balle zaman lauyoyi a tsakani. Dan komai a bayyane yake wa duniya akan masu laifin. Amma duk da haka dolene mu karanto musu laifinsu su amsa kafin mu yanke hukunci”. Bai jira amsar kowaba dan ba ita yake jiraba daman. ya bama jami'an tsaro damarsu. Dawood ne ya miƙe ɗauke da file ɗin dukkan bayanan laifukan Papa ya kai ga alƙali. Batare da alƙali ya amsaba ya bashi damar karanto komai.
 Tsayuwa Dawood ya gyara yana fuskantar su papa. Ya fara bayani dalla-dalla. a duk gaɓar da yazo ƙarshe alƙali zai ma su papa tambaya akan shin hakane sun aikata?. sukan ɗan nuna tirjiya kafin papan ya tabbatar da sun aikata ɗin. A haka aka dinga bin duk laifukansu daki-daki tare da shedun da suka gani da ido wajen tabbatarwa. Hakanne yaja shari'ar tai tsaho sosai aka jima ba'a tashiba.
 Ƙara jin bayanan sai ya ƙara komawa mutane tamkar sabo a cikin kunne, wasu harda hawaye sukeyi, wasu ko kawai gani suke babu hukuncin da su papa suka dace dashi sai mutuwa. Da ƙyar Alƙali ya samu kotun nan ta lafa da ga hayaniyar data ɗauka akan cecekucen jama'a. Ya ɗauki ruwan dake a gabansa ya sha cike dajin gajiya da damewar tunani wajen yanke wannan hukunci.
Bayan kotu ta sake lafawa alƙali ya fara magana kamar haka, “Ya kamata kuyi hakuri ku bamu haɗin kai, nasan duk wani hukunci da zamu yanke anan bai zama lallai ya gamsar da waɗanda wannan mutane suka cutarba. Amma zamuyi iya bakin ƙoƙarin mu dan ganin mun yima kowa adalci. Sun tafka kura kurai da kowanne idan zamu ɗauka yanada nashi hukuncin ne, to amma kisan kai da suka shigo sun shanye duk wani laifuka nasu. ALLAH kaɗai yasan iya rayukan da suka salwantar, dan kosu a yanzu ba iya lissafawa zasuyi ba. Dan haka wannan kotu mai adalci, ta yankema waɗanan mutane hukuncin kisa ta hanyar rataya”. Yana gama faɗa ya doka gudumarsa.
A take kotun ta ɗauki ihun kace nace ɗin mutane. Har bakajin zancen wani. Sai dai duk wannan surutai babu mai goyen bayan su papa. Wasuma duk da an ambaci kashesun za'ayi su hukuncin sai bai musu ba. a ganinsu ayi gunduwa-gunduwa da su kamar shine yafi dacewama kowa ya huta. Kamar yanda kotu ke a harmutse haka jama'ar gari ke a harmutse dan ƴan jaridu nata kai rahoto live. A take duniya gaba ɗaya ta ɗauka. Inda wasu ƙungiyoyi kamar Masu kare haƙƙin ɗan adam suka fito suka nuna bore da wannan hukunci. Har suna iƙirarin ɗaukaka ƙara. Sai dai to bamusan zuwa wane kotu suke da burin ƙarar ta kaiba, tunda mudai anan Nigeria a babbar kotun ƙasa gaba ɗaya aka yanke hukuncin.
   Duk yanda Yoohan yaso su mama debora su gana da Papa al'amarin ya gagara dan da ƙyarma aka fiddasu daga cikin kotun. 

__★★

     Bayan kwanaki biyu da faruwar wannan al'amari da safe su Jay na tsaka da yin breakfast ya samu waya daga alƙali cewar sufa sun gama yanke hukuncin su papa. Dan sun fuskanci al'amarin neman canja salo yakeyi na ƙirƙirar rikici da hukumar kare haƙƙin ɗan adam ke neman haddasa musu. A yanzu haka maganar da ake ga gawarwakin su papa nan, a gaban ƴan jarida akai komi yanzu kuma zasu bada damar a saki labarin.
 Al-amarin ya girgiza zuciyar Jay matuƙa, to amma shima hakan yafi masa sauƙi tunda dai shine hukuncin da aka yanke musu a gaban kowa. Koda sukai sallama da shugaban alƙalai bai iya yima su Yoohan bayanin abinda ya faruba sai Miemaa kawai. Ita kanta duk da tasan su papa masu laifi ne sai da tausayin mama debora ya ƙara kamata da su Victoria. To amma wannan shine dai-dai kuma abinda ya dace..
  Kafin shabiyun rana labari ya gama zagaye ƙasar dama duniya akan zartar da hukuncin da aka yankema su papa. Wasu kam sun ɗauki ɗumi akan hakan, dan duk da mummunan halin su papa suna samun magoya baya musamman masu irin halayyarsu da ayyukansu. To andai yita ta ƙare. labarin su papa kuma ya zama tarihi, sai kuma na baya garesu, dan yanda mutane. kirki basa ƙarewa hakama mutanen banza kullum sake yawaita suke.
 Mama debora dai tasha kuka a ɓoye, dan ɗa da mahaifi sai ALLAH, musamman daya kasance mazan ƴaƴanta har uku. To amma tunda ta rasa mahaifin Yoohan da yafi sonta da ƙyautata mata tai haƙuri, dan ta rasa waɗanan azzaluman minene zaisa ta takura kanta kuma. Su Joy ma dai saida suka koka sosai. danma an hana Abraham da Victoria kallo sam. 
 Yoohan kansa sai da yay hawaye, koba komai yasan su ɗin jininsa ne. Nu'aymah ce kawai ta iya fahimtar shima kukan yayi, dan haka tana ganin ya fita itama ta bisa a sace ta ƙofar kitchen. Acan baya ta hangosa tsaye ya jingina da bango yay shiru idanu a lumshe. Ƙarasawa tai garesa ta kamo hannunsa cikin nata. Kusan a tare duk suka sauke ajiyar zuciya. Batare da yace da ita komaiba ya jawota jikinsa ya rungume. Luf kuwa tayi kusan mintuna uku sannan ya ɗagota yana murmushi. Kafin yay magana tace, “Silly boy! Kuka kakema waɗanda suka kashe mana su Abbabmu saboda son zuciya”.
 A karon farko ya saki murmushi da shafa fuskarta. Murya a raunane yace, “Silly girl! Kin samin ido da yawa fa”.
  Dariya tayi kaɗan ta kwantar da hankali, sannan ta ɗan marairaice fuska cike da kulawa tace, “Sai haƙuri Yah Maleek, haka rayuwa take, wani farkonsa yaji daɗi ƙarshen yasha wahala. Wani yasha wahala a ƙarshe yaji daɗi koba a duniyaba. Kaji labarin gwagwarmayar da Uncle Jay yasha shima shi da Miemaa. Amma bagasu komai ya wuce a garesuba tamkarma bai faru ba. Muma idan mukai haƙuri sai kaga komai ya zama tarihi insha ALLAH ”.
 Cike da jin daɗi ya sake rungumeta da sumbatar laɓɓanta. Ya lumshe idanunsa ya sake buɗewa a kanta. “Thanks you Zeeynab. Kin gama bama rayuwata dukkan abinda take buƙata, ALLAH yay miki albarka ya albarkaci Deen, ALLAH yasa ya zama mai gadon baba malam. ALLAH ya gafartama iyayenmu ya ƙara mana haƙuri da abinda ƙaddara ta danƙa mana a tafin hannunmu”.
 “Amin ya rabbi yah maleek”.

Sake rungumota yay jikinsa yana dariya ƙasa-ƙasa da fadin, “Sunan nan fa yayi daɗi Sweet girl”.
“Sosai ma, Mami da Abba sun iya zaɓen suna. Kaga yanzu ka zama mai suna biyu, danni kam daga yau Abdul-maleek zanke faɗa”.
“Silly girl! ki rage jan faɗa yanzu akwai Deen a gabanki”. Ya faɗa yana jan hancinta.
A tare suka sanya dariya, suna maijin farin ciki mai yawa a ransu.

    A daren ranar kuma sai ga saƙon rasuwar Addah ya samesu. Duk da abinda ta tafkama rayuwarsu Nu'aymah sai da taji duk ta rikice. Tasha kuka kuma a daren ranar. Washe gari kuwa tunda safe suka ɗauki hanyar kano a mota harda su Jay, cikin sa'a kuwa suka samu jana'izar Addah, dan sai goma aka kaita masaukinta na gaskiya. Sai kuma aje a girba abinda aka shuka.
 Duk da abinda Addah taima Umm rasuwarta tayi masifar girgizata, dan saida takai an saka mata ƙarin ruwan daya sakata dogon barci saboda ruɗanin data shiga. Jikin kowa ya ƙara sanyi kuma a agidan harma da sauran ƴan uwa. 
    Da yamma su Yoohan suka koma Abuja aka bar Nu'aymah anan kano, sai bayan anyi addu'a Yoohan yace zaizo ya ɗauketa dan zasuje Oman wajen dangin mahaifiyarsa da ƙaddara ta maida can.

    *_BAYAN SATI GUDA_*

Bayan sati ɗaya da rasuwar Addah da mutuwar su papa Yoohan yazo da kansa ya ɗauki Nu’aymah da Deen suka koma Abuja, zuwa yanzu kuma Alhmdllh Umm ta ɗan dake saboda kulawa da baba malam keta bata dan ganin ta samu kwanciyar hankali. Hakama Hajarah daketa fama da tsohon ciki sai Umm ta roƙu mijinta ya barta ta dawo nan gida harta haihu dan itama rasuwar mahaifiyar tata ta taɓata sosai. Bai musaba ya barta ta dawo, tana nan zaune wajen Umn yanzu haka. Zaman natanema ya ɗan ragema Umm raɗaɗi. Hajjo kuma koda yaushe takan yawaita shigowa ta sake kwantarma da Umm hankali itama, hakama Ananah da bata komaba.

OMAN

   SU Nu'aymah sun isa Oman lafiya, inda suka sami tarba ga dangin Mami (Anum) dan tunkan zuwansu labarin komai yazo musu. Abin mamaki sai su Yoohan suka sami Dr Shikurah acan Oman, ashe kanwarta datake faɗa ɗanta na kama da Yoohan itace ke auren yayan Anum da suke uba ɗaya. Sun haɗune acan Oman da taje karatu, a yanzu haka yaransu kusan shidda. Mahboob mai tsananin kamanni da Yoohan shine yaronsu na farko. Idan ka gansu shi da Yoohan saika ɗauka tagwayene saboda tsabar kamanni da sukeyi da juna, abin mamaki har tafi har maganarsu iri ɗayane. Sosai abin ya birge Yoohan. Har yaji a ransa inama ya amince tun sanda Dr Shikurah ke masa kamanni da Mahboob ɗin ya amince ta kawosa yagansa. To amma ya ɗauka hakan kawai matsayin abinda ALLAH bai hukunta ba.
      Da yake anzo dasu mama debora suma sai hakan yasaka dangin Anum ƙara jin daɗi, dan koba komai sun ƙara yarda IBRAHEEM mutumin kirkine shi. Ansha kuka da tunawa da rasuwarsu da yanda rasuwar tazo. tare da jifan su papa da kalmomin ALLAH wadarai danma ana ɗan tagawa darajar mahaifiyarsa dake a wajen. 
 Deen da Nu'aymah kam lallai sunga soyayya ƴar gaske, dan gatan da Yoohan bai samu ga dangin uwaba a yanzu kowa ƙoƙarin ganin ya nunama Deen yakeyi. Sunga gata kam sun kuma sha daɗi Alhmdllh. Satinsu uku cif suka dawo Nigeria badan ƴan Oman sunso hakaba.

  Suna dawowa kuma aka shiga hidimar bikin Naser & Yusrah, Abdallah aka maida masa Adawiya suje su cigaba da haƙuri da juna. Amal da malam ƙarami. Ahmad da Nanah yayar ƙanwar Umm. Ansha biki an raƙashe an ƙwalle Alhmdllh, yayinda Abban Abdallah ke kwance yana fama da kansa shima. Dan shikam bikinma bazaice yasan anyiba. To dama haka rayuwar take ai.

Bayan an gama biki an miƙa amare ɗakunansu komai ya zama Alhmdllh Yoohan ya tattara matarsa da ɗan ɗansu da yay ɓul-ɓul gwanin sha'awa syuka koma ƙasar U.S saboda karatun Aymah, shi kuma zai koma aikinsa na hidima wa al'umma.
Basubar ƙasarba sai da ya nemawa su mama debora gida anan kusa da su Uncle Jay aka saya musu, dan mama debora ta rantse bazata sake zama gidan can da papa ya gina ba. Hakan yasa aka saidashi suka dawo nan. Gebrail da Joy an nema musu makaranta a ghana. Mama debora zata cigaba da zama dasu Victoria dasu mama Destiny da suma suka dawo nan tare da mazajensu. Dan zaman can kauyen kam bazai yuwu yanzu a garesuba.

_

  Tunda su Nu'aymah suka dawo fa sai ta ɗaura ɗammarar dagewa akan karatunta, haka shima Yoohan ya sake dagewa akan neman iliminsa na addini. Ga renon ɗan ɗansu daketa ƙara girma masha ALLAH.
  Soyayyarsu da shaƙuwa kuwa sai abinda yay gaba. Yayinda Hajiya Nu'aymah aketa ƙara canjawa ana hankali da rage fitsara kamar ba itaba. Ga jikinta sai buɗewa yake tana ƙibarta masha ALLAH.
 Haka rayuwa ta ciga da gunguramawa waɗanan bayin ALLAH, yau asha zuma gobe asha maɗaci. Da sun sami hutu sukan shirya suje Nigeria, hakama ƴan Nigeria ɗin lokaci-lokaci Yoohan kan ɗakko wasu a cikinsu suzo su musu hutu.
Daga Deen dai Nu'aymah shiru, da alama kuma dai sune asuka tsarama kansu hakan, dan a yanzu haka ga Deen da shekara ta huɗu, Nu'aymah kuwa na shirin kammala karatunta. Yaro ya girma yay wayau, ga miskilanci ga zuciya ko kuturu haka ya gansa ya bari. 
  burin Yoohan dama nu'aymah ta kammala karatunta ya tarkatasu ya maida Nigeria, cikin amincin UBANGIJI kuwa sai gashi ta kammala lafiya cike da nasarorin rayuwa. Wannan karon kuwa Umm da baba malam ma sunzo U.S, taso azo da hajjo baba malam yaki dan tsufa sosai ya ƙara kamata, ga ciwon ƙafa dake damunta. Kowa ya taya Aymah murna da nasarar data samu daga ita har mijinta, bayan kammala komai suka tattaro zuwa ƙasarsu ta haihuwa, inda Yoohan ya saya musu gida suma duk da su Jay sunso Yoohan ɗin yay zamansa anan gidansu, amma ya ƙi, dan gaskiya yanajin kunyarsu ainun.
         Ƴan uwa da abokan arziki sun tayasu murnar gida. Dan ƴan kano ma duk saida sukazo, harda su Aunty Kubrah da zuwa yanzu tayi haƙuri a gidan aurenta duk da ba daɗin zaman takejiba dai.
 A wannan dawowane kuma kowa ya fahimci Nu'aymah laulayin ciki takeyi. Anko tayasu murna da addu'ar ALLAH ya raba lafiya.

Dawowarsu baifi da wata guda ba ALLAH yayma abban Abdallah rasuwa shima. Ansha alhini ansha kuka, daga baya kowa ya rakasa da addu'a. 

A KWANA A TASHI

  Lallai kam akwana atashi babu wahala wajen UBANGIJI, dan yanzu shekarun Auren Nu'aymah da Yoohan goma kenan. Zuwa yanzu ALLAH ya azurtasu da ƴaƴa uku, Deen, Ibrahim, sai auta Anum. Jay ne ya hana a ɓoye sunan yaran, yace a bari ake kiransu da sunansu hakan zaisashi farin ciki. Dan haka aka barsu kuwa da sunayensu ana kiransu da shi.
     Abubuwa da dama kam sun faru a waɗannan shekaru, masu daɗi da akasin hakan sai dai kawai muce Alhmdllhi ala kulli halin.

“Sweet girl! Sweet girl!!”

  Nu'aymah da ke a can backyard tana shanya kayan su Anum data wanke tana mita ta jiyo Yoohan na ƙwala mata kiran mafarauta. Kanta ta dafe dan ta tabbatar su Anum ne suka hanashi barci. Dawowarsa kenan babu jimawa daga asibiti a gajiye matuƙa. Sabodama kar yaran su gansa su hanashi hutawa a wajen gate yay fakin, ya shigo gidan a saɗaɗe saima yay sa'a su suna a can garden suna wasa Nu'aymah ta korasu itama ta huta. Shiyyasa itakam batama cika son weekend tai musu a gidanba. Tafi buƙatar su wuce gidan Uncle jay ko gidan Aunty Little ko wajen su maman Destiny.
  Jin ya cigaba da ƙwala mata kiran yasa ta ajiye abin matse kayan dake a hannunta ta nufi ciki da sauri. Ilai kuwa samun duk yaran tayi a bedroom ɗinsa ɗane-ɗane bisa gado kusa da shi kowa na ihun sai ya tashi an kaisa gidan Abie (Jay). Kai Nu'aymah ta dafe sannan ta ɗaure fuska ta daka musu tsawa. Tsitt kuwa sukayi kowa na kwaɓe fuska.
Sai a lokacin Yoohan ya janye filon daya cusa kansa a ciki ya tashi zaune, kallon yanda yaran duk suka zuba tagumi yay, ya kuma dubi yanda Nu'aymah tai bala'in tsare gida. Sai shima kawai yay tagumi kamar yanda yaran sukayi ya zuba mata ido. Hararsu tayi su duka ta ida shigowa cikin ɗakin. Da sauri Ibrahim dake da shekaru shida ya matsa jikin Yoohan ya lafe, sai itama Anum dake da uku ta matsa ta lafe. Duk yanda Yoohan yaso daurewa sai ya kasa ya saki ƙaramar dariya yana kama kunnuwansu yaja kaɗan.
  “Wato kuɗinnan fa nagama ni kuka raina a gidan nan, ita Mie-mie kuna tsoronta, amma ni kunma maidani Uncle Jay kakanku ko?”.

Yanda yay maganarne ya saka Nu’aymah yin dariya itama, ta yamutsa fuska da faɗin, “Dan ALLAH ka tattarasu ni kama kaisu gidan Miemaa, abar min Deen kawai anan”.
Cikin ɗage gira Yoohan yace, “Oh, saboda kinga yarona mai hakuri kina samin shi aiki ko. To naƙi wayon, waɗanan tom and jerry ɗin zan bar miki anan, Abbana kuwa kano ma zan kaisa yayma Umm Hutu da Uncle Muhammad. Inama yake?”.
“Haba Yah Maleek dan ALLAH kar muyi haka da kai, waɗanan mi suka iya banda takurama mutane”.
“Hhhh kunfi kusa ai. Kai mai jan kunne ina Abbana yake?”. Yoohan ya faɗa dajan kunnen Ibrahim.
Ƙwaɓe fuska yaron yayi yana tashi daga jikinsa ya koma wajen Nu’aymah. “Mie-mie ALLAH nama fasa sayama Dada birthday gift ɗin da nace miki tunda bazai daina cemin maijan kunne ba. Gashi nan har Wannan Anum ɗin ta kama bayan itama jajayen kunnen ne da ita”.
Sosai Yoohan da Nu’aymah suka kwashe da dariya. Cikin dariya Yoohan yace, “A to indai hakane bazan sakeba Abban Mie-mie. Zomu shirya kaji”.
Ɗan jimm yaron yayi, sai kuma ya kalli Aymah. “Mie-mie kin yarda na shirya da shi?”.
“Hhhh haba Abbana wake fushi da babansa dama inba shashasha ba”.
“Ai dama nima bana fushi da shi ko Dada?”.
Yay maganar da matsawa jikin Yoohan dake kallonsu da murmushi. Rungumesa yayi sannan ya dubi Aymah da wani narkakken kallo. “Wai ina Abbana?”.
Miƙewa tai tana bashi amsa. “Yana ɗakinsufa yana gyarawa, dukansa nai shiyyasa yaƙi fitowa, yana can yana faman haɗiyar zuciya uwa budiddigin ƙwaɗo”.
Sakkowa Yoohan yay daga gadon ɗauke da Anuma yana faɗin, Ayyah Mie-Mie mi mukayi haka ne harda taɓa mana lafiyarmu?”.
“Miskilancin da kuka saba mana. Yaron nan a gabansa na gama gohon gyara musu ɗaki wai dan wulaƙanci yana zaune a ɗakin su Anum suka sake hargitsashi bai hanasuba shi shugaban miskilawan Najeriya. Shiyyasa na dakesa dan gobe idan sunyi ai ya hanasu ko”.
“Aiko a kansu zansa ya rama. Abbana kana ina?”.
Kafin Aymah ta bashi amsa Deen ya fito daga ɗakinsu baki cike da iska. Yana ganin Yoohan sai gashi da gudu yazo ya rungume Dadan sa.
Cike da so da ƙauna Yoohan yace, “Oh my sweetheart so sorry yeah. Bar Mie-mie anayin hutu Kano zan kaika wajen Umm da Uncle. Aiko cike da jin daɗi yaron ya hau murna. Yayinda su Ibrahim suka koma jikin Aymah suka lafe wai sunan jealous ya motsa. Dariya Yoohan yayi suma ya miƙa musu ɗayan hannunsa. Da gudu kuwa suka ƙaraso ya haɗasu ya rungume yana maijin farin ciki a ransa da samuwarsu a garesa matsayin ƴaƴa. Waɗanda suka fito daga tsatson Nu’aymahrsa mai rigima da tsiwa. Shikam babu abinda zaicema ALLAH sai godiya kuma, dan ya gama masa dukkan rahama. Ko a musilinci n daya tsunta kansa a ciki bayan dulmiyar da shi da su papa sukayi ai ya gamacin ribar rayuwa. Balle kuma daɗin daɗawa ga ƙyautar mace ta gari da ƴaƴa nutsatstsu da ALLAH ya bashi. Wanda ya tabbatar tarbiyyar mahaifiyarsu ma tana taka rawar gani wajen samuwar tasu. Shiyyasa akace ka nemawa ƴaƴanka uwa ta gari, matama su nemawa ƴaƴansu uba na gari. Fatansa ALLAH ya raya masa su da baiwar ilimin addini tamkar mahaifiyarsu. Duk da shima zuwa yanzun Alhmdllh, ya sauke alkur’ani mai girma haryayi nisama a hadda. Yasan littatafai masu yawa na addini, bai kuma tsaya a hakaba yana cigaba da neman ilimi babu dare babu rana. Dolene ya kasance mai yawan ambaton Alhamdulillahi ala kulli halin a kowanne dakiƙa na rayuwarsa, suka kalli juna shida matarsa suna murmushi, hannu ya miƙa mata itama tazo ta haɗasu ta rungume cike da godiyar UBANGIJI mai rahama mai jinƙai.✍????????????????.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button