SARAN BOYE COMPLETE

“Duk wannan Abun fa laifinki ne Hajara ke Kika bar yarinya nan ta zauna dashi har yanzu har ta juyar Masa da kwakwalwa ace yau sati biyu da auren mu ya kasa kallon Inda nake tsabar wanan kanjalalliyar ta asirice shi ki barwa Umma komai ta Miki maganin shegiya”
Ta ce tana jefomin harara
Umma kuwa tayi wani irin murmushi ta mik’e tana k’ok’arin shiga daki.
Da Sauri na rik’e kafarta na saki ihu Ina ta taimaka ta fitomin da yata wlh idan Naseer ne Zan rabu dashi a yau
Tureni tayi ta shige daki.
Zahira dake lab’e a bayan kofar dakina ta fito ganin Ina ta rusa kuka Ina Kiran sunan Allah Dana Nadeeya ba irin tunanin da ba darsu a Raina ba Kar dai su Umma kashemin Nadeeya sukayi.
Zahira Humaira ta mik’o min dake ta tsalla kuka daga ita har Minal ba Mai Kaya a jikinsu sai Zahira karbar Humaira nayi na sa Mata no-no a baki take ta karba na umarci Zahira ta d’auko wa Minal Kaya ita da Humaira.
Tana tashi Mmn Mannir ta shigo ita da wasu makotana wasu ma ban San su ba duk sun zo min jaje sai Kara tambayata suke Taya Nadeeya ta b’ata ban ma iya musu magana ba sai bani baki suke suna kwantar min da hankali akan za’a ganta an Kai cigiya gidajen radio har da tv dayake Naseer nada Abun hannu duk an raba musu passport din Nadeeya.
Ni dai har lokacin sai Naga kamar zanga Nadeeya ta fito daga d’aki.
Mmn Mannir kuwa Humaira ta karba daga hannuna ta goyata Ni kuwa na mike na Shiga bandaki na daura alwala na fito na hau Kan Sallaya na tadda Sallah karatun Sallah ma da k’arfi na ringayi Ina kuka a Sujadda kuwa Haka na ringa rokon Allah ya Kare min yata a duk Inda take ta dawo gareni cikin koshin lafiya Ni nasan su Umma ne suka daukemin ‘ya har tsawon wane lokacin Zan ringa irin wanan rayuwa a yau na gaji wlh na gaji ya zama Dole na dau mataki.
Ina iddarwa na fito nayi k’ofar gida Inda duk makotana suke tsaye duk Yan layin ban gansu ba sun tafi neman Nadeeya daidai da masu shaguna duk basu bud’e ba sabida mutuncinsu Amma ace uwar mijina ita Tana daka ko a jikinta.
Waje daya na samu na zauna Ina ta tunanin ganin ta Inda zanga Nadeeya ta b’ullo addua kuwa na fili Dana zuci Haka na ringa Yi.
Lukman da danladi Mai Kai su makaranta sun dawo gidan yafi a kirga Akan suji ko an ga Nadeeya Amma shiru ba a ganta ba ahaka har Yamma tayi babu Naseer babu dalilinsa.
Kuka nake sosai Ina rokon Allah ya karemin Nadeeya har yanzu na kasa yarda Wai daga fitowa Nadeeya wanka an nemeta an rasa.
Naseer kuwa kudi ya saki sosai ya bada cigiyar Nadeeya gidajen radio da unguwa unguwa har Inda baa yi tunanin zuwa ba Haka aka ringa neman Nadeeya da passport din hotonta Sallah ma Naseer ba a nutse yake Yi ba har kunyar ya cewa mutane daga wanka Nadeeya ta fito aka nemeta aka rasa sai kace wata Kaya.
Ahaka suka danganta neman Nadeeya kusufa kusufa lungu da sako kwaryar Kano baa ganta ba wajen Magriba Naseer da wasu Yan unguwarsu suka tsayar da motarsu Dan suyi sallah a wani unguwa kawo dayake unguwar Bata fiye cika ba a wanan lokacin Kamar daji ne sai a lokacin ake yankar fili ake ginawa.
Daya daga cikinsu ne ya nausa wajen daji dajin da yayi fitsari ya fito yayi alwala daga nesa dashi ya hango wani katon Rafi ruwa nata Dan gudu gashi wawakeke wata Yar karamar yarinya ta bada baya tana Dan jefa abu a ciki ba Kaya a jikinta.
Murza idonsa yayi ya sake murzawa idonsa duk da Bai ga fuskar yarinya ba sai yake ganin kamar Nadeeya Amma Dan ya gasgata zargin da yake ahaka ya ringa matsawa kusa da yarinya kafin a hankali yace “Nadeeya”
A hankali Nadeeya ta juyo idonta yayi jawur hancinta duk Majina kana gani kasan taci kuka ta gode Allah wajen a ruwan yake ma da alama baa fiye wucewa ta wajen ba
Ihu ya saka ganin Nadeeya na ganinsa ta fara k’ok’arin mik’ewa tana mik’a Masa hannu Dan Dama Mai kawo Mata d’auki take nema shi kuwa cikin zafin nama ya Isa wajenta ya tarota da Sauri Dan kiris ya rage ta fada ciki.
Wani irin ajiyar zuciya Nadeeya ta ringa saukewa tayi lamo a jikinsa jikinta yayi zafi zau.
Shima Salisun kamkameta yayi yayi wajen da suka Parker motarsu da har Naseer ya iddar da sallah ya gaji da jiransa.
Kamar a mafarki ya hango ya fito da Nadeeya rungume a kirjinsa Bai San lokacin da ya nufesu da Sauri Yana “Mai ya sameta? A Ina ka ganta”?
Yace Yana karbe Nadeeya daga hannunsa ya hau tattab’a jikinta Inda Nadeeya tana ganin Abbanta ta fashe da kuka tana Kara kamkame shi.
Naseer kamar ya maida ta cikinsa ya rungumeta Yana shafa jikinta
Salisu kuwa ya hau bashi labarin yanda ya ganta ya Kuma ringa Al ajabin yanda Nadeeya ta iya zuwa tunda Goron dutse zuwa Kawo idan ba mutum ne ya kawo ta Nan ba Taya zaayi tazo Nan
Naseer Bai iya Jan motar ba sai salisu ne yaja motar shi kuwa ya zauna daga bayan motar da dayan makocinsa suna ta mamakin Inda suka tsinto Nadeeya Naseer kuwa rufe idonsa kawai yayi Yana Jin kukan Nadeeya a kirjinsa Yana Jin wani irin suya a kirjinsa shi ba yaro bane yasan d’auke Nadeeya akayi Kuma ba wasu ne.suka d’auke.ta ba sai Mahaifiyarsa tunda yasan wacece ita.
Baiyi magana ba har suka iso gidan da mutane ke cike Suna jajanta b’atan Nadeeya.
Naeema kuwa taci kuka ta gode Allah tayi zaman dirshan a kasa Ana ta Bata baki
Tsayuwar motarsu yasa ta mik’e da sauri Inda Naseer shi.kuma ya bud’e motar ya fito rungume da Nadeeya
Mutane na ganin ta suka hau hamdala suna “Alhamdulillah Anga Nadeeya a Ina aka ganta”?
Sosai mutane Suka nuna farincikinsu da ganinta suka hau tambaya inda aka ganta.
Naeema kuwa da Sauri ta ture mutane ta karbi Nadeeya daga hannun Naseer tana sauke wani irin ajiyar zuciya.
Ta rungume Nadeeya Gam tana hamdala
Hajara da Hindatu ihun Murnar anga Nadeeya ne yasa Suka fito daga d’akin da Sauri suka lek’o ta saman bene cikin tsananin mamaki Dan bakin ruwa Suka kaita Kuma suna da tabbacin fad’awa zatayi ta mutu Amma ga mamakinsu Wai an ganta Kuma su sun San Inda suka kaita sai anyi dagaske xaa San wajen.
Wani irin ihu Hajara ta saka ta sauko daga Kan benen ta zub’e a kasa ta hau buburwa ta cire zaninta ta Yar ya rage daga ita sai Dan skirt sai kuka take Tana zubawa kanta kasa.
Mamaki ne ya rufe mutane suna kallonta tare da mamakin Mai ya kawo ihun nata ita da zatayi farinciki anga Nadeeya (wlh page dinan babu fiction ko daya a gaske Haka matar Nan tayi Dan bakin ciki an ga Nadeeya)
Ni kuwa ko kallonta banyi ba na rungume yata na haye sama
Naseer kuwa kamar kasa ta bud’e ya shige Dan kunyar yanda take ihu tana watsawa kanta kasa Wai Nan da Sunan Mahaifiyarsa ce wato gawan Nadeeya taso gani
Mutane kuwa da basu San Mai ke faruwa ba hakuri Suka hau bata suna ba kuka zatayi ba ta Godewa Allah da aka ga Nadeeya ba Kuma abinda ya sameta.
Naseer shima da Sauri ya hau saman bene Yana Jin kamar kirjinsa ya fad’o
Sai Hindatu ce ta sauko ta dauko mata zaninta ta mikar da ita suka koma ciki.
Da yawa ta basu mamakin abinda tayi sabida tunda aka fara neman Nadeeya Bata lek’o ba Amma abin mamaki ana ganinta ta fito tana ihun kuka Mai hakan ke nufi.
Wasu Kuma basu kawo komai ba sun dauka kukan farinciki take da ganin Nadeeya.
Ni kuwa Ina shiga ciki d’akina na wuce da Nadeeya na kullo k’ofar na kwantar da ita na fara duba jikinta Naga babu abinda ya sameta sai kafafunta dai da suka balain suntume sukayi budu bud’ da kasa