NOVELSSARAN BOYE

SARAN BOYE COMPLETE

Sai jikinta da yayi zafi sosai.

Bana rabo da ruwan zafi hakane yasa na hada ruwa Mai balain zafi na wanke Nadeeya tas na Kara zuba wani na hau dadanna Mata kafa sai danaga ya fara Sab’ewa sanan na dauko robbb na shafe Mata jikinta dadin wankar yasa take bacci ya d’auke ta tana ta sauke ajiyar zuciya Ni kuwa na zuba Mata Ido hawaye na sauko min ko a Ina su Naseer suka ganta.

Naseer kuwa a Palo ya zauna ya rik’e kansa sabida azabar ciwo da tunanin halin mahaifiyarsa ahaka su Hajara suka hawo sama tana ta kuka

Suna dab da wuce Naseer

Naseer ya dago Yana “Umma ba Haka Kika so ba ko?kin so ace gawar Nadeeya na shigo dashi gidanan Umma Mai na Miki Haka Dan Allah Dan annabi Umma Mai na Miki Dan Allah Dan annabi ki gayamin na nemi yafiyarki Umma”

Naseer yace Yana durk’usawa Akan gwiwar sa kukan dayake d’annewa ya kwace Masa.

Hajaran Bata ce komai ba ta Shige d’akinta tana Jin kanta na ciwo sabida a rayuwarta Bata da burin daya wuce taga Naeema ckin bakin ciki a Rayuwa tunda ta kasa rabata da Naseer gwara ta Taba abinda tasan sune ranta Dan taso Zahira ta d’auke Dan ta lura itace Mafi soyuwa a wajen Naeema sai Zahira bata futo ba Nadeeya ta fito sai gashi cikin sauki wai har anga Nadeeya bama ta mutu ba da ranta lailai Naeema tabbas akwai abinda ta taka da Bata iya cin Galaba Akan ta.

Har wani zazzabin bakin ciki tayi

Naseer shima halin mahaifiyarsa da matsanacin tunani sai daya saka Masa zazzabi

Ni kuwa Ina daga d’akina Ina Jin duk abinda Naseer ke cewa Umma kukan da Naseer keyi ya tab’ani sosai hakane yasa na Sha alwashin kawo karshen wanan matsalar da muke ciki.

A Daren ranar duk mu ukun babu wand yayi baccin kirki Dan Naseer zazzabi halin mahaifiyarsa ya hau Yi ko shigowa d’akin baiyi ba a palon yayi kwanciyarsa ko sallah daya Saba yi daddare ma a ranar baiyi ba Ni Kuma hanyar da zata bille Dani ya hanani bacci ita Kuma Umma bakin ciki. Duk Abubuwan da takemin Ina tsallakewa gashi shugabarsu tayi fushi tace zata kwace komai daga hannunta tunda Naeema tana neman fin karfinta.

Washegari Nadeeya ta tashi fes ba wanan kumburin ahaka na had’asu na musu wanka na rufo kofata na nufi kitchen Dan na Dora Mana abinci banyi tunanin shiryasu su tafi makaranta ba Naseer ma ban ganshi a palon ba Dan tunda ya fice da asuba bana Jin ya sake dawowa sosai naji Ina tausayinsa.

Daga Umma har Hindatu banji motsinsu ba har na Gama Abunda nake na ajiye musu nasu a Palo na Kai Mana namu daki Dana Naseer.

Dan nayi alkawarin har na cimma burina bazan Kara Shiga dakinsu ba.

A faranti daya muka ci Abinci da yayana Sansu na ratsani Ina kwarara musu addua a Zuciyata.

A hankali Kuma Ina tambayar Nadeeya yanda ta ba ce bamu ganta ba Bata iya min magana ba Dan tana da Dan nauyin baki.

Har Minal ta Dan fita baki.

Wajen karfe goma na safe na fito daga d’akina bayan na kulle k’ofar dakina har lokacin Naseer Bai dawo ba Kuma banji motsinsu Umma ba Naseer nafi damuwa nasan halin da yake ciki ba Umma ba hakane yasa nayi waje.

Ina su lukman suka hau gaisheni suna tambayar Nadeeya Ni kuwa nace Tana Nan lafiya Lau daga Haka na wuce gidan mmn Mannir Dan zuwa yanzu banida dai Sama da ita bayan Naseer dan naji Dadin yanda ta nunamin damuwarta jiya tamkar yar uwa ta Haka nake ganinta.

Banyi tunanin Zan sameta a gida ba Dan na d’auka taje makaranta amma Ina zuwa na sameta taji dadin ganina anan muka gaisa taso ta tada maganar abinda ya faru tsakaninta da Umma har ta Dan sakomin zancen tana zargin ita ta d’au Nadeeya Ni kuwa na Kau da zancen na hau Gaya Mata abinda ke tafe dani da taimakon danake so tamin Dan Nagaji da irin wanan rayuwar da muke nida yayana Kuma idan na biyewa Naseer Haka zamuyi ta zama muna cutuwa.

Sai data Yi Dan Jim kafin tace zata taimaka min ta hau tsaramin yanda zamuyi take naji dadin shawararta Inda ta tsaramin duk yanda zamuyi Amma fa tana tausayin Naseer.

Murmushi kawai na nata Dan Mai daki shi yasan Inda yake Masa yoyo.

Sallama na Mata akan Zan dawo anjima

Ina koma wa gida Naga Naseer ya dawo idonsa ya fada sosai yayi wani sanyi kalau kamar mara lafiya Bai cemin daga Ina nake ba na Shiga d’aki na dauko masa abincinsa Ina k’ok’arin ajiyew yace min azumi yake bance komai ba na dauke abincin na mayar kitchen na fara k’ok’arin Dora Mana abinci Rana Ina cikin girkin Hindatu ta shigo ta ajiye kwanuka tare da dalla min harara sai anan nasan Ashe ma suna Nan

Ina gamawa na Kara shigewa daki a Inda Naga Naseer har yayi wanka zai fita.

Yacemin bazai dawo da wuri ba fatan dawowa lafiya kawai na masa Yana fita na dauko katon akwatina na hada Mana kayanmu nida Yara sai danaga ba kowa a palon Naja akwatin na Kai gidan mmn Mannir Kuma cikin ikon Allah babu Wanda ya ganmu.

Kamar Naseer yasan Mai nake shiryawa tunda ga ranar Bai Kara fita ba.

Nima sai neman hanya nake kwana biyar da faruwar.haka Umma ta fito palon Wanda tunda aka ga Nadeeya ta shige daki ban Kara ganinta ba sai ranar Dan Hindatu kawai nake ganin tana Shigar musu da abinci.

Wani irin kallo take min Ni kuwa na dauke kaina Zan iya cewa wnan shine Karo na farko a rayuwata da naki gaisheta.

Girgiza Kai tayi ta had’e Rai ta zauna a Palo Naseer kuwa Yana ganin ta fito ya mik’e ya fita.

A ranar wani kallo Umma take jefamin na tsana Kamar zata kamoni ta yankani Ni kuwa Ina Gama ayyukana na shige daki.

Washegari jikina duk ba kwari na shirya su Zahira suka tafi makaranta

Wajen Sha daya Naseer na fita na goya Humaira na karewa d’akina kallo hawaye na zubomin

Na ajiye wa Naseer wasika a karkashin gado na fito da ga d’akin

Banga kowa a palon ba Ina fita na amshi kudi wajen lukman a cikin kudin Naseer wajen Dubu goma wanan lokacin.

Na dau hanyar makarantarsu Zahira Ina zuwa nacewa mallamarsu inasan zamuyi tafiya ne an Mana rasuwa take ta Kira su Zahira suna zuwa na rik’e hannunsu muka hau tafiya sai da muka je karshen layin na had’u da mmn Mannir dake ta jirana da akwatin kayanmu…..
[6/13, 10:50 AM] Queen Meenali????: NAGA TA KAINA

 *NA SADNAF*????????

®️ PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
{We Don’t just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}????????

Free Novel

Page 18

      Bansan hawaye nake ba sai da mmn Mannir da itama Naga jikinta duk yabi yayi sanyi tace "Anya Naeema kina ganin wanan matakin shi ya dace ki d'auka?Anya kina ganin kinyiw Naseer adalci kuwa?

Ban iya ce Mata komai ba Dan matsawar nayi magana kukan danake dannewa zai iya k’wacemin Agaban yayana Zahira tana da wayo tunda muka fito daga makaranta take min tambayoyi Ina zamuje yanzu ma sai kallona take.

Mmn Mannir itama sosai Naga idonta ya kad’a yayi ja Ina biye Mata Haka zamuyi ta tsayuwar hakane yasa na Ciri hannu na fara k’ok’arin tsayar Mana da taxi Dan lokacin ba adaidaita sahu.

Dak’yar muka samu Wanda ba kowa a ciki na sunkuyar da kaina nace ya kaimu tasha.

Sai daya fito ya saka Mana kayanmu na bud’e bayan na saka su Minal Ina k’ok’arin kamo hannun Zahira ta Kara cemin “Umma Ina zamuje Dan Allah idan tafiya zamuyi mu tafi da Abba Kar shima Mama ta ringa dukansa dayake mama suke ce Mata”?

Hada Ido mukayi da mmn Mannir da har hawaye ya fara zubo Mata tana daukewa sabida Kar a gani.

Ni kuwa na saka Zahira a cikin motar da k’arfi Dan banasan magana kukan danake dannewa ya fito.

Ina zaunar da ita na shige na rufo k’ofar Ina k’ok’arin yiwa Mmn Mannir godiya Naga ta bud’e gaban motar ta hau.

Ba Wanda yayi magana a cikin mu har muka Isa Tasha muka sauka na biya Mai taxi bayan ya sauke Mana kayanmu

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button