SARAN BOYE COMPLETE

Mmn Mannir ce ta shigemin gaba wajen Nemo motar garinmu aka cajemu na biya sai da su Zahira suka hau sanan na juyo na rik’e hannun mmn Mannir Ina “Nagode da alkhairinki a gareni bazan manta dake ba”
Hawaye ne ya hau zubo Mata ta damke hannuna tana “Naeema Dan kin dage ne Zaki tafi da kin hakura kin zauna wuya Bata kissa watarana sai Labari da Zaki bani hadin Kai wlh zamuyi maganinta ya Naseer zaiji idan ya dawo yaga bakya Nan kin Kuma tafi da duka yaran wlh Naeema bazaiji dadi ba”
“Bazaki gane ba Mmn Mannir bazaki gane Hatsarin Zama na da Naseer ba Mmn Mannir da iya Ni kadai ummaa zata tab’a kila na iya jurewa da iya Ni kadai zata ganawa azaba kila na iya daurewa ko Dan sabida yarana Amma me Umma yanzu ta bar kaina ta koma Kan yayana Wanda duk abinan sabida su naki tafiya tuntuni Akan me Zan cigaba da zama yau idan Allah ya karemin Nadeeya gobe nasan salon da zata zomin dashi wlh Nagaji mmn Mannir ko baccin kirki bana iya yi na rasa Mai na Mata laifine Dan na auri danta yau kina ganin da iyayena suna rayye zata min abinda takemin banida kowa sai Allah sai Naseer toh shima Naseer din tace sai mun rabu toh na rabu dashi rabuwar mu bazai saka na kasa cigaba da rayuwa ba na barwa Naseer wasika Akan ya sakeni bazan iya ba Zan koma garinmu ko wanke wanke na ringa Yi Ina ciyar da yarana Dan bazan tab’a barin yarana da Naseer mahaifiyarsa ta kasheminsu ba Wlh mmn Mannir banji Ina nadamar matakin Dana dauka ba wlh nesa ma danayi daga gidan bakiji iskar danake shak’a Mai kyau ba nidai kawai ki Tayani da Addu’a watarana insha Allahu zamu sake had’uwa”
Mmn Mannir kasa magana tayi sabida kukan da take dak’yar na kwace hannuna na Shiga motar Ina shiga muka samu Karin passenger daya Yana shiga motar mu ta d’au hanya
Haka kawai naji wani Abu ya tsayamin a mak’oshi tambayar da Zahira ta Kara jefomin Akan tafiya zamuyi mu bar abbansu yasa na kifa kaina akan hannuna na fara kukan danake ta dannewa tun lokacin Dana shirya rabuwa da Naseer.
Allah yasan ba Haka naso ba Dan mijina Yana Sona Yana Kuma iya kokarinsa Dan yaga ya kyautata Min nida yayana Amma mahaifiyarsa ta daka tsalle tace sai mun rabu bansan Umma tsanar da takemin har ya tashi daga kaina zata iya tab’a min Yaya ba
gaba gaba kila wuka zata d’auko ta caka musu ni har mamakin halinta nake Dan wlh ko dabba bazan iya cutar dashi ba ko ragon layya a da idan zaa yanka tausayi yake bani sai da akacemin babu kyau na daure na daina Dan bana ma tsayawa Inda ake yanka d’abba Amma Wai Umma ita ce take zuba wanann zalincin har Yara kanana Bata Bari ba idan dai har zata iya yiwa Nadeeya Haka na tabbata ma Naseer Bai tsira a wajenta ba.
Addua kawai nake Allah yasa na Gane hanyar garinmu Dan shekaru dayawa rabona da can toh waye ma nawa acan ne inama Ina zuwa Naga Yaya Aliyu yazo shima Yana nemana inama na samu wasu suzo suce sune dangina inama na tambaya Mahafina ko Mahaifiyata.wani nasu da yanzu na samu wajen zuwa Amma ba komai Haka zanje ko makotammu na da idan na samu na tambayesu game da gidan da mahaifina ya Bari dan nasan kila yana hannun Mai unguwa idan Allah yasa basu siyar Mana ba sun ajiye Mana kayanmu sai na zauna nida yarana na nemi sana’a.
Biscuit da ruwa na siyawa su Nadeeya da sai Dana tashe su daga bacci.
Zahira ce kawai batayi bacci ba ta Yi jigum da biscuit dinta a hannu ta kasa ci Dan sai data karamin tambaya na daka Mata tsawa akan ta kyalleni naji da iya damuwar da nake ciki.
Sai da mukayi nisa da Kano Naji wani irin tausayin Naseer ya rufeni ko ya zaiji waya sani ma ko har yaje gidan yaga wasikar abinda nakejin Kuma nadamarsa Bai wuce ce Masa danayi na tafi garin kaduna ba Dan nasan kila ya tafi can neman mu alhalin ba can mukayi ba.
Ahaka nayi lamo Ina kallon Motocin dake ta tsere a titi Ni nasan Umma sai ta kusa taka rawa sabida murnar tafiya ta.
Naseer kuwa tunda ya bar gida yake Jinsa kamar Mai zazzabi ahaka ya daure yayi ta zama a katon shagonsa daya bud’e dake sabon gari dake d’auke da kayan electronic Dan Naseer Kam fanin arzki sai daya ce alhamdulillah dan shagunansa zasuyi uku a sabon gari shidda kenan har Dana kofar gidansa.
Yanzu Haka ma Yana Gina wani katon gida a kasan layinsu ko Naeema Bai gayawa da ace mahaifiyarsa Bata Sako shi a gaba ba da ace mahaifiyarsa ta rungumi Naeema a matsayin matar danta da ya ce shi kam ya samu rabon duniya sai dai Kuma na lahira.
Sam yaji zaman shagon ya gundureshi ba Kuma yajin dadin jkinsa hakane yasa duk da yawan mutane dake zuwa siyayya ya Sallame su akan bayajin dadin ya rufe shago ya nufi gida.
Ganin lokacn tashinsu Zahira ya kusa yasa ya tsaya a makarantar su Dan saura Yan mintina su tashi
Kansa tsaye ya shiga cikin makarantar ya nufi office din headmistress din tana ganinsa ta hau gaishe shi tana Masa gaisuwar rasuwan da aka musu
Cikin mamaki Naseer yace Bai Gane ba
Itama headmistress din cikin mamaki ta Kora Masa zuwan Naeema makaranta da Sunan an musu Rasuwa ta tafi da su Zahira.
“Kin tabbata Mahaifiyarsu ce tazo ta d’auke su”?
“Itace Mana Alhaji Naseer yanzu ma wajen awa biyu kenan”
Naseer Bai tsaya jiran sauran bayananta ba ya fita da Sauri gabansa na fad’uwa Mai ke faruwa Naeema tazo ta dauki su Zahira lokacin tashi baiyi ba ko Ummansa ce ta Kara musu wani Abu
Da ikon Allah ya Kara sa gida ko parking Mai kyau baiyi ba ya hau sama g da balain sauri.
Naeema ya hau kwallawa Kira Yana kiran sunansu Zahira Haka kawai gabansa ya tsinke ya Fadi daya shiga d’akin naeema.ya duba koina Bai ganta ba fitowa yayi da Sauri.ya fada Kitchen nan ma Bata nan.
Da sauri ya fito ya Kara sauka kasa.
Yana sauka ya hau tambayarsu lukman ko sunga Naeema da Zahira.
Dukansu girgiza Masa Kai sukayi sai Mai Zama a dayan shagon ne yace yaga ta sauko ita da Minal da Humaira a goye a baya tayi hanyar titi.
Naseer Bai tsaya ya Gama Jinsa ba ya da dan gudu ya nufi gidan mmn Mannir daya San Nan kawai take zuwa Sosai yaji Yana tsoron darsa tunani a Ransa akan ko wani abun ne ya faru addua kawai yake.Allah yasa tana gidan mmn Mannir.
Tsabar tashin hankali Bai tsaya Sallama daga waje ba ya fada cikin gidan da Sallama a bakinsa
Mmn Mannir dake zaune ta buga tagumi tunda ta dawo ta mik’e da Sauri tana sallati ganin Naseer a rude yasa jikinta ya hau rawa cikin jarumta tace.masa.lafiya
Naseer da Sauri ya hau tambayarta inda take ita da Yara.
Ita kuwa tace masa Bata ganta ba sosai taji wani irinn tausayinsa daya zaro Ido Yana sallati.
Ya juya da Sauri ya bar gidan
Sosai hankalinsa ya tashi ya koma gidan a hargitse
Yana Kara kwallawa Naeema Kira Dan gani yake.kamar Tana gidan..
Sai a lokacin tunanin shiga d’akinsu Umma ya Fado Masa.
Da Sauri ya fada d’akin suka dago suna kallonsa
“Umma Mai Kika yiwa Naeema Dan Allah Banga Naeema ba Banga yarana ba Umma Mai Kika musu Dan Allah ki gayamin kimin komai Umma Banda rabani dasu”
Wani irin kallo umma.ta hau yi.masa Hindatu kuwa ta fara zuba Mai harara cikin kishi a ranta tana ayyana Allah yasa ma Naeema ta mutu
Umma kuwa taja Tsaki ta Kau da kanta.
Fitowa ya Kara Yi daga d’akin Yana sallati
Ya Kara Shiga d’akin Naeema tsabar rudewar da yayi ya hau daddaga Kaya ahaka ya d’ago pillow har zai mayar ya Ajiye yaga farar takarda