Labarai

Kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta Amnesty tace Ya zama wajibi ga hukumomin Najeriya su saki Matashin nan da ake Zargi da cin Mutuncin Aisha Buhari.

Kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta Amnesty tace Ya zama wajibi ga hukumomin Najeriya su saki Matashin nan da ake Zargi da cin Mutuncin Aisha Buhari.

Jaridar bbc hausa ta ruwaito cewa babban abin kunya ne a ce hukumomin Najeriya sun kama tare da azabtar da Aminu Adamu kawai saboda ya wallafa bayanai a shafin tuwita wanda ya shafi uwargidar shugaban ƙasar.

Haka nan hukumar ta ce abin da ya kamata hukumomin ƙasar su mayar da hankali a kai shi ne tsarewar da aka yi wa matashin ba bisa ƙa’ida ba da kuma azabtar da shi da aka yi.

Bayanai dai sun tabbatar da cewa kotu ta tura matashin mai suna Aminu gidan gyara hali, bayan da aka gurfanar da shi bisa zargin sa da cin mutuncin mai-ɗakin shugaban ƙasa, A’isha Buhari a shafinsa na tuwita.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button