Labarai

Me Tinubu Ya Fada Wa Kwamitin Tantance ’Yan Takarar APC?

A ranar Talata ce mai neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC kuma tsohon Gwamnan Jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana wa kwamitin tantance ’yan takarar shugaban kasar jam’iyyar dalilansa na neman takara a zaben 2023.

Kwamitin wanda tsohon Shugaban Jam’iyyar APC, John Odige Oyegun ya jagoranta ya fara zamansa ne a otal din Transcorp Hilton da ke Abuja, gabanin zaben fid-da gwanin jam’iyyar da za a yi dagar ranar 6 zuwa 7 ga watan Yuni da muke ciki Aminiya ta rawaito.

Tinubu ya fara bayar da takaitaccen bayani a kan rayuwarsa da kuma irin cigaban da ya kawo lokacin da ya ke gwamnan jihar Legas.

Ya ci gaba da bayar da bayanai kan yadda ya samu nasarar bunkasa tattalin arzikin da jihar, har take samar wa kanta kudin shiga Naira Miliyan 600 wanda a yanzu kuma yake kai akalla Naira biliyan 51 a wata.

Tsohon gwamnan ya kara da cewa cigaban da aka samu ta bangaren layukan sadarwa shi ya fara assasa ta a Najeriya, inda ya ce shi ne ya fara shigo da kamfanin sadarwa na Econet, wato Airtel a yanzu.

Ya kara da cewa shi ne wanda ya gayyato kamfanin samar da wuta na Enron domin samar wa Jihar Legas wuta da za ta rika amfani da ita.

Har ila yau, ya bayyana cewa shi kwararren masanin inganta tattalin arziki ne kuma yana da cikakken ilmi a kan siyasa da kuma tattalin arzikin Najeriya.

Wadannan su ne wasu daga cikin muhimman abubuwan da Tinubu ya yi bayani ga kwamitin tanatance ’yan takara a APC.

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button