NOVELSUncategorized

SOORAJ 10

????????????????????????????????????????

          *SOORAJ !!!*

   *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*????Kainuwa Writers Association*

           
            *WATTPAD*
      @fatymasardauna


        *Chapter 10*

Baijima da kwanciya ba aka soma knocking ƙofar falon, yana daga kwance yabawa maiyin knocking ɗin izinin shigowa. 

Peter ne yashigo cikin falon hanunsa riƙe da wasu ledodi, cike da girmamawa ya rusuna ya gaida ogan nasa.

Amsan ledodin Sooraj yayi haɗe da ciro wallet ɗinsa ya zaro fararen ƴan dubu dubu har guda uku ya bawa peter,  karɓa peter yayi yana godiya ya fice daga falon.

Ɗaukan duka ledodin yayi haɗe da nufar ɗakin da take,  amemakon yayi knocking kamar yanda ya sabayi kullum, sai kawai ya tura ƙofar  ya shiga ciki, a zuciyarsa kuwa yana maijin haushin bautar da yakeyi mata.

Tana kwance akan gado tayi kwanciyar ruf da ciki, bacci takeyi hankalinta a kwance,  harara yaɗan wurga mata haɗe da aje ledodin, har ya juya zai fita daga ɗakin kuma sai ya tsaya, kallonta yashigayi tundaga ƙafanta har zuwa kanta,   ahankali yataka zuwa inda take kwance, ƙafansa yasa ya ɗan zunguri nata ƙafan, azabure tatashi ta zauna tana mai murje manya manyan idanunta da sukayi ja.      Sake kallonta yayi, sai alokacin ya lura tun rigar jiya itace har yanzu ajikinta. “Ƙazama” yafaɗi haka acikin zuciarsa.

“Ki tashi kije kiyi wanka, ke wace irin ƙazamace zaki wuni da kaya ki kuma kwana dashi?” yatambayeta yana mai kawar da kansa daga kallonta.

Ɗago idanunta tayi ta kallesa, gani tayi kamar bashine yayi maganan ba, saboda yanda ya fusge yawani kawar da kansa gefe guda. 

Kallon kanta tashigayi, sam rigar jikinta bata da wani alaman abu wai shi datti,  ita lokacin da take ƙauye ai sai kaya suyi sati ajikinta ma bata cireba, to inama taga yawan suturun balle ta dinga sanjawa akai akai.

“Idan kin gama ki sameni a falo”  yanagama faɗan haka yafice daga cikin ɗakin.

Kamar yanda yace haka tayi, kayan jikinta ta cire taje tayi wanka, tana fitowa awanka still wata doguwar riga ta ɗauka ta sanya, sai dai wannan ba kalan waccar da ta cire bane.   Ledan da ya aje mata ta ɗauka haɗe da buɗewa, yau madai robobin take away ne acikin ledan har guda uku,  ɗaukan ɗaya tayi haɗe da buɗewa ta soma ci, sosai taci sannan tasha ruwa.    Mayafin rigar tayafa asaman kanta sannan tafito zuwa falo.

Yana tsaye agaban fridge yabawa cikin falon baya,  jin motsinta afalon yasa batare da ya juyoba yace.   “Muje”  nufar hanyar fita daga cikin falon yayi. 

Yana gaba tana biye dashi abaya har suka ƙaraso inda motarsa ke fake.   Buɗe murfin motar yayi ya shiga, key yasanya zai ta da motar,  gefen da take tsaye ya kalla cike da takaici. 
“Sainace ki shigo sannan zaki shigo?”  yatambayeta cikin yanayi naɗan jin haushi. Buɗe murfin motar tayi ta shiga ta zauna, ƙirjinta kuwa bugawa yake kamar zai fito waje.

Tunda suka hau titi bata ɗago kanta ba,  wasa take da yatsun hanunta, yayinda ƙwalla suka cika idanunta, ita kanta batasan ƙwallan na menene ba.

Yana gama daidaita parking ɗin motar ya cire earpiece ɗin dake saƙale acikin kunnensa.

“Muje” ya faɗa yana maiƙoƙarin fita daga cikin motar.
Sai alokacin ta ɗago kanta ta kalli inda ya kawota,  batasan ina bane, saidai taga mutane nata shiga da fice a wajen,  haka ta fito daga cikin motar ta shiga bin bayansa, saida suka shiga cikin wajen sannan tafahimci cewa asibiti suka zo,  ji tayi gabanta ya faɗi, aranta tace  “Allah Yasa ba allura yakawoni ayi min ba.” 

Tafiya suka ɗanyi sosai itadai binsa kawai take kamar jela,  abakin wani ƙofa suka tsaya, knocking ƙofan yayi, daga ciki aka bashi izinin shigowa.

“Ki tsaya anan” yafaɗi haka yana mai ƙoƙarin buɗe ƙofar, tana ganin shigewarsa taja ta tsaya haɗe da sauƙe ajiyar zuciya.

Dr.Salees  Yana ganin Sooraj ya miƙe haɗe da soma haɗa kayan aikin dazai buƙata, atare suka fito daga cikin office ɗin.

Murmushi Dr. Salees Yayi haɗe da kallon Ziyada.

   “Ƴan mata yajikinnaki?” yatambayeta cike da kulawa.

“Da sauƙi!” tabasa amsa murya araunane, saboda tana ganinsa taji ƙirjinta ya tsananta bugawa. 

Kansa yajinjina haɗe da cewa “Biyoni muje ko” 

Da sauri takalli Sooraj saidai gani tayi idanunsa ba akansu yake ba, earpiece ne ma sanye akunnensa, ya wani haɗe fuska, hakan yasa cikin sanyin jiki tabi bayan Dr. Salees.

Akan wani ɗan gado ta zauna, yayinda Dr.Salees dakansa ya soma warware mata bandage ɗin dake nannaɗe akanta, yana gama cirewa ya ɗauki auduga haɗe da ɗan ɗiga wani farin ruwa mai ɗauke da sinadarai akai, hanunsa ya sanya ya kama goshinta  ahankali yasoma goge ciwon da audugan dake hanunsa, wani irin ƙara tasa haɗe da cije laɓɓanta,   sake riƙe kanta yayi cike da kulawa yace.   “Sorry da zafi ko? ki nutsu awanke miki hakan shine zai sa ciwon ya bushe” 

Sake sakin wani ƙara tayi haɗe da soma ƙoƙarin ƙwace kanta daga hanunsa, sosai takejin zafin ruwan dayake sawa yana goge ciwon,    sake kama kannata yayi da ƙarfi, haka yashiga wankewa, ita kuwa banda kuka babu abun da takeyi, duk yanda taso ta ƙwace kanta ta kasa,  saida ya wanke ciwon tsab sannan ya sake naɗa mata wani sabon bandage ɗin.   kallon innocent face ɗinta Dr. Salees Yayi haɗe da ɗan sakin murmushi.
“Sarkin raki, sai ki tsayar da kukan hakanan tunda angama”  

Harsuka fito daga cikin  ɗakin Ziyada bata daina zubar da hawaye ba,  gaba ɗaya idanunta sunyi ja, fuskarta kuwa duk yayi face face da ruwan hawaye.   Wasu magungunan Dr. Salees yabata sannan suka bar cikin asibitin.

Kamar yanda suka zo haka suka tafi babu wani wanda yace da ɗan uwansa ƙala,  gaba ɗaya hankalinsa nakan tuƙin dayake, ahankali yake ɗan kaɗa kansa, sosai yake enjoying cool music ɗin dake tashi acikin earpiece din dake saƙale acikin kunnensa.    Duk abun da takeyi yana lure da ita.  Sauƙa yayi daga kan titi haɗe da ɗan gangarawa gefen hanya, tsaida motar tasa yayi haɗe da ɗaukan goran ruwa ya kafa akan bakinsa,    sauƙe goran ƙasa yayi haɗe da fitar da wani dogon numfashi.

“Kukan me kikeyi?” yajefo mata tambayar da bata taɓa zato ba.

Ɗago kanta tayi ta kallesa, daidai lokacinne kuma wani guntun hawaye dake maƙale acikin idanunta, yasamu daman gangarowa.

A fakaice ya kalleta ta gefen idanunsa…  “Inaganin lokaci yayi daya kamata ki koma ga iyayenki, saboda haka zan ajiyeki anan peter zaizo saiki nuna masa garinku zai kaiki gida” yafaɗi haka cikin halin ko inkula yana mai latsa iphone 11 pro ɗin dake riƙe a hanunsa. 

Hawayene suka shiga gangarowa daga cikin idanunta kamar an buɗe famfo, murya araunane tace.

“Bansan kowa ba, bani da kowa sai mahaifina wanda kwata kwata bai ɗaukeni a matsayin ƴarsa ba, tun farko na fara rayuwata ne acikin ƙunci, bansan wani abu waishi ɗan ɗanon farinciki ba,  kataimakeni banaso rayuwata ta salwanta!” tuni hawaye sun gama wanke mata fuska.

Tunda tafara maganan bai ɗago ya kalleta ba baikuma daina abun dayakeyiba, sai ayanzune ya ɗago kansa daga latsa wayar da yake…   “Wani irin duhu ne acikin rayuwarki da har kika zaɓi salwantar da kanki? wacece ke?”  yatambayeta batare daya ɗaura idanunsa akan ta ba.

Hawayen da kebin kan kumatunta ta sanya hanu ta share.

“Nima bansan koni wacece ba, saidai kawai nasan tsananin duhu ne ke bibiyar rayuwata” tafaɗi haka tana mai sharce hawayen dake kan fuskarta.

Sai alokacin ya ɗago idanunsa ya kalleta, gaba ɗaya idanunta sunyi jajur dasu,  bai sake ce da ita wani abuba ya tada motar suka bar wajen.    Harsuka isa gida bata daina sheshsheƙan kuka ba. 

Yana shiga cikin ɗakinsa ya zauna akan gado haɗe da sanya hannayensa ya dafe kansa,  baisan meyasa yakejin son taimakon yarinyar acikin ransa ba, sai dai tawani ɓangare na zuciyarsa bata aminta da abun dayake ƙoƙarin aikatawa ba,  sam bayaso wata ko wani su shigo cikin rayuwarsa, amma kawai yana ganin zaiyi abun daya dace.

** ** ** 

Ajiyar zuciya yasauƙe akaro na barkatai haɗe da jawo trolly ɗin dake gefensa, tun adaren jiya ya gama shirya kayansa, ƙarfe 6 na yamma jirgin da zai hau zuwa Abuja zai tashi, kallon agogon dake ɗaure a tsintsiyar hanunsa yayi ƙarfe 5:20  na yammaci dai dai, ajiyar zuciya ya sauƙe haɗe da fitar da numfashi daga bakinsa.   Jan ɗan ƙaramin trollyn nasa ya yi haɗe da ficewa daga cikin ɗakin. 

Tsayawa yayi abakin ƙofar haɗe dayin knocking.  Kamar dama jira ake yayi knocking ɗin aka buɗe ƙofar.

Ganin ta buɗe ƙofar ne yasashi juyawa yasoma tafiya, batare da yace da ita wani abuba.  Ganin haka yasa ta fito jikinta asanyaye tashiga bin bayansa. 

Ganin yana ƙoƙarin shiga cikin motar yasanya itama tashiga ta zauna haɗe da takurewa waje ɗaya.  

Ga mamakinta sai gani tayi yashiga gidan baya ya zauna yayinda Peter ya zo yashiga mazaunin driver. 
 Tafiya sukayi mai ɗan nisa kafun suka isa inda zasu,  baki hanci da ido duk ta buɗe tana ƙarewa wajen data tsinci kanta aciki kallo.  A hankali tafara bin mutanen dake ta hada hada a wajen da idanu ɗaya bayan ɗaya,  yawancin jama’ar dake wajen ɗauke suke da ƴan akwatunansu, yayinda wasu kuwa ke tsai tsaye.

“fito muje” Sooraj yace da ita yana maiƙoƙarin cire sit belt ɗin dake jikinsa.  
Tana biye dashi abaya sai wurga idanunta takeyi takota ina,  daga bayanta kuwa peter ne ke riƙe da ƴar jakan Sooraj,  tunda suka shigo cikin wajen, idanun yawancin mutane musamman ƴan mata ya dawo kan Sooraj,  suna ƙarasowa wajen ana sanar da cewa matafiya Abuja su shirya jirginsu yakusa tashi.   Tsayawa daga tafiyar da yakeyi yayi haɗe da juyawa ya kalli peter.    “Kawuce gida kawai peter sai munyi waya”  yafaɗa yana duban lokaci a gogon dake hanunsa.

Kai Peter ya jinjina alaman gamsuwa haɗe dayi masa Allah Ya Kiyaye hanya.

Pass yaciro daga cikin aljihunsa guda biyu ya miƙa mata ɗaya, amsa tayi tana mai kafesa da ɗara ɗaran idanunta. 

Suna zuwa bakin ƙofar shiga yanuna pass ɗinsa, ganin abun da yayi yasa itama ta nuna ƴar takardan daya bata, dan batasanma takardan ko ta mecece ba, sannan aka barsu suka wuce.

Idanu ta ware tana bin jiragen dake wajen da ido, tunda take aduniarta bata taɓa ganin jirgi ido da ido ba sai ayau, hakanne yasa take ganin abun kamar almara,   direct inda jirginsu yake ya nufa,  har yaje kusa da  matattakalar jirgin ya juyo donyi mata magana, amma abun mamaki bai ganta abayansa ba,  ɗan kalle kalle ya somayi, can ya hangota tsaye tana ta kallon jirage.   (Like ƙawata hauwa lokacin da ta fara zuwa airport.Lol)   takaicine ya turnuƙeshi,  nufar inda take yayi, yana zuwa ya kamo hanunta, haɗe da turata gabansa, suka soma tafiya,   saida suka kawo ƙofar shiga jirgin, ta tsaya tana kallonsa lokaci guda idanunta sukayi raurau dasu, zuciyarta ta karye, wani tunanine yashiga yawo acikin ranta.   Da Kyawawan idanunsa ya kalleta, aƙufule yace.       “Wuce muje!”    

Kasa koda motsa ƙafafunta tayi, tsanin tsoro takeji, bazata iya taka matattakalan ba. 

Kamar yasan abun datake tunani kenan, ganin tana masa wasting time yasa ya kama hanunta suka soma haura matattakalan.

Direct  ɓangaren Business class suka nufa,  suna shiga ya nufi  inda kujeransa yake ya zauna wacce take kusa da window,  tsaye tayi takasa zama sai raba idanunta take, abun kamar amafarki wai yau itace acikin jirgi.   Ganin ta tsaya mai aka yasa shi ɗago da kansa ya harareta,  aibatasan lokacin da ta zauna akan kujeran dake kusa danasa ba.   Sit belt ya ɗaura ajikinsa, haɗe da kwantar da bayansa ajikin kujera, kana ya lumshe idanunsa.   Gaba ɗaya Ziyada amatuƙar tsorace take, jitake kamar tazama tsuntsuwa ta fire.  Lokacin da aka soma announcement  cewa kowa ya ɗaura sit belt ɗinsa,   ɗan ranƙwafowa kusa da ita yayi, har suna iya jiyo hucin numfashin juna, sit belt ɗinta ya ɗaura mata, kana yakoma ya kwanta ajikin kujeransa, sannu ahankali jirginsu ya ɗaga sararin samaniya. 

Tsananin sanyin AC’n dake ratsa cikin jirgin, shine dalilin da  ya sanya  tatakure jikinta waje ɗaya, sam bata saba da sanyiba ko kaɗan.


   *Vote Me On Wattpad*
       @fatymasardauna

  
#arrogant
#fantasy

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button