NOVELSUncategorized

SOORAJ 9

????????????????????????????????????????

            *SOORAJ !!!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

              *WATTPAD*
         @fatymasardauna

*(Banso cigaba da rubutunnan ba amma yazanyi daku???? My Wattpadians sun sakoni gaba, waƴand sukace aci gaba sunfi waƴanda sukace a dakata yawa…  Nagode da nunawa littafina ƙauna. Inayinku hundred percent My Wattpadians Allah yabar Ƙauna!!)*


            *Chapter 9*

Sake lumshe gajiyayyun idanunsa yayi, aransa  yanaso yaje yasanar da mahaifiyarsa matsalan dake damunsa, saidai kuma sosai wata zuciyar ke gaya masa hakan badai dai bane.   Jikinsa asanyaye ya nufi wajen da yayi parking motarsa.
***
Bacci tasha sosai ba ita tafarka ba sai lokacin da aketa ƙiraye ƙirayen  sallan la’asar. Banɗaki tashiga ta ɗauro alwala, kan lallausan carpet ɗin dake malale a gefen gadon ta hau haɗe da tada Sallah, bayan ta idar da sallan ta zauna jigum haɗe da sanya hannayenta ta tallafi kyakkyawar fuskarta.  Jitayi ruwan hawaye sun cika idanunta, tausayin kanta take, musamman ma yanzu da take cikin rayuwa irin ta BULAYI. 
***
Kallon Mamaki Mas’oud ke yiwa SOORAJ, da ƙyar ya iya cewa.  “Me hakan yake nufi kenan SOORAJ? kakuwa san illan abun da kake shirin aikatawa?  ajiye mace’n da ba muharramanka ba acikin gidan ka fa abune da baidaceba sannan kuma hatsarine babba”

Murmushin gefen baki SOORAJ yayi, haɗe da ɗaukan cup ɗin fresh milk ɗin dake aje agabansa yaɗanyi sipping kaɗan, miƙewa tsaye yayi tare da kai dubansa ga agogon dake ɗaure a tsintsiyar hanunsa. 

 “Ni zan wuce” yace da Mas’oud ataƙaice.

Kallonsa kawai Mas’oud yayi haɗe da girgiza kansa.
 “Nasani dama SOORAJ ba zaka taɓa sanjawa ba” Mas’oud yafaɗi haka acikin zuciyarsa.  SOORAJ baisake bi takan Mas’oud ba yanufi wajen da motarsa take.

Yana shiga cikin motar ya murza mata key haɗe da cillata kan titi. Direct babban asibitin dake cikin Garin Kaduna ya nufa.

Ajiyar zuciya mai ƙarfi Dr.Waleey yayi haɗe da gyara zamansa, kallon SOORAJ yayi cike da tausayawa….    “Ka kwantar da hankalinka SOORAJ, akwai wani sabon magani idan na ɗauraka akai wata ƙila adace” 

Kallon Dr.Waleey Sooraj yayi da shanyayyun idanunsa.

“Banatunanin akwai wani maganin da zan ƙarasha Dr.Waleey, zan haƙura kawai, zamana ahaka wata ƙila shine abu mafi alkhairi!” yafaɗi  maganar cike da raunin zuciya. 

“Karkace Haka SOORAJ, kada ka karaya, sauƙi zai iya samuwa ako da yaushe, kasan Allah Babu yanda baya ikonsa, amma nikaina al’amarinka yana matuƙar girgizani, nasha samun case ire iren  wannan, amma naka yayi worse.”  Ɗan tsagaitawa daga maganan Dr.Waleey yayi, haɗe da sauƙe ajiyar zuciya, cigaba yayi da cewa. 
“Kada kadamu Sooraj Insha Allah watarana sai labari.” ya ƙare maganar cike da son ƙarfafawa Sooraj guiwa.

Murmushi Sooraj yayi haɗe da cije lips ɗinsa,   jin Dr.Waleey kawai yake, amma ji yake ajikinsa kamar shikam ahaka zai mutu, ahaka zai ƙare rayuwarsa babu wata ingantacciyar farinciki.  
Sunan wasu magunguna Dr.Waleey ya rubutawa Sooraj a ƴar wata farar takarda.  Hanu Sooraj yabasa sukayi musabaha, kafun ya fice daga cikin office ɗin.

Direct Pharmacy yaje yasaya maganin, sannan yabar cikin asibitin.
*** 
Idar da salla’n isha ɗinta kenan ta zauna akan gado, haɗe da kama cikinta daketa yi mata kukan yunwa, gawani tsoro daya lulluɓeta, ayanda tafahimta shine ita kaɗaice ke rayuwa acikin gidan, domin kuwa tunda ta zauna bataji motsin kowa ba.  Sam bata saba irin wannan zamanba, tasaba gaba ɗaya rayuwarta cikin aiki take, sam bata da hutu, yi wancan ɗauko wancan, da haka ta saba, shiyasa gaba ɗaya takejinta amatuƙar takure.

Ƙarfe takwas na dare daidai motarsa ta kunno kai cikin gidan.     Yana gama daidaita parking ɗin motar tasa ya tattaro ledodin dake cikin  motar yafito.

Sake matse jikinta tayi haɗe da soma ƙif ƙifta oily eyes ɗinta, jin motsi acikin falon yasa taɗanji gabanta ya faɗi.  

Direct bedroom ɗinsa ya wuce, kayan jikinsa ya cire kana ya wuce toilet.  

Fitowa yayi ɗaure da towel aƙugunsa, jikinsa duk danshin ruwa.   Agaban dressing mirror ya tsaya, tare da ɗaukan ɗan ƙaramin towel yashiga goge ruwan dake jikinsa. sama sama yashafa body lotion ɗinsa mai daɗin ƙamshi,   3 guater jeans yasanya haɗe da saka wata riga marar nauyi, da turarensa mai sanya nutsuwa ya feshe jikinsa. aje comb ɗin dake hanunsa yayi, haɗe da sanya hanu ya shafi lallausan sajen dake kwance akan fuskarsa, wayarsa ya ɗauka yafice daga cikin ɗakin. 

Tsayawa yayi ajikin ƙofar ɗakin, haɗe da ɗaura hanunsa akan handle ɗin ƙofar, kamar zai tura ƙofar ciki kuma sai ya fasa, hanunsa yakai jikin ƙofar yayi knocking.

Da sauri takalli ƙofar jin ana ƙwanƙwasawa,  shiru tayi haɗe da ƙurawa ƙofar ido.    Sooraj dake tsaye ajikin ƙofar yasake ƙwanƙwasawa. 

Saɗaf saɗaf ta sauƙo daga kan gado, zuwa tayi ta buɗe ƙofar, karab idanunsu ya sauƙa acikin na juna, wani irin bugawa taji ƙirjinta yayi, abubuwa biyune suka haɗe mata, ganin kyawawan eyeballs ɗinsa da kuma daddaɗan ƙamshinsa mai sanyaya zuciya.  

“Biyoni!” yace da ita ataƙaice haɗe da juyawa ya koma cikin falon,  sumu sumu haka ta bi bayansa tana matse jikinta domin kuwa mayafin rigar dake jikinta iya ƙirjinta kawai ya tsaya. 

Zama yayi akan lallausan carfet ɗin dake malale tsakiyan falon, tare da tanƙwashe ƙafafunsa.  Cikin sanyi ta ƙaraso cikin falon, durƙusawa tayi aƙasa haɗe da sunne kanta ƙasa.
  “Gani”
 tace dashi in a silent voice.    

“Kinci abinci?” yatambayeta batare daya kula sashin da take ba.

Mamakin tambayar da yayi matane ya kamata,  ta ina zata samu taci abinci bayan babu abincin. 

“Bakiji bane?” yasake tambayarta cike da ƙosawa.

“A’a banci ba” tafaɗa masa haka a sanyaye. 

Ledan dake aje agefensa ya jawo.  “Ɗauko min plate” yafaɗa still batare daya kalleta ba.

Inda take tunanin nanne kitchine ta nufa,  sum sum ta dawo riƙe da plate a hanunta.  

Durƙusawa tayi haɗe da miƙa masa plate ɗin. 

Ledar ya buɗe ya ciro take away guda ɗaya, haɗe da tura mata gabanta,  ɗaukan ɗaya yayi ya juye abun dake ciki acikin plate ɗin da ta kawo masa.  

Spoon yasa acikin plate ɗin yasoma tsakalan jalop rice ɗin da yaji busashshen kifi.

Shiru  tayi ta kasa cin abincin, tsoron tashi take, sannan kuma bazata iya sakewa taci abinci a gabansa ba.  

Tunda yafara tsakalan abincin bai ko da ɗago kansa ya kalleta ba, abincinsa kawai ya ke cusawa,   fiye da rabi yaci sannan ya ture plate ɗin gefe, goran peach ɗin dake gefensa ya ɗauka, haɗe da tsiyayawa acikin wani ɗan ƙaramin glass cup, ahankali yake sipping peach drink ɗin,   yana kammalawa ya miƙe ya wuce ɗakinsa. 

Tanajin rufe ƙofarsa ta saki wata ajiyar zuciya mai ƙarfi, take away ɗin ta jawo gabanta, buɗewa tayi, amma amaimakon taga shinkafa kamar yanda taga nasa, sai taga ferfesun naman kaza ne aciki, wani yawu ta haɗiya haɗe da soma ci ahankali, bata wani ci sosai ba taji gaba ɗaya cikinta ya cushe, rufewa tayi tare da ɗaukan goran ruwan dake gefenta tasha.  Ɗauke plate da take away ɗin tayi tamayar kitchine, zama tayi afalon tana daɗa ƙarewa falon kallo, idanunta ta sauƙe akan makeken tv plasma’n dake cikin falon,  kasancewar ba akunne yakeba yasa ta ɗauke idanunta daga kansa, kanta ta jingina ahanun kujeran da take zaune aƙasanta,  shiru tayi haɗe da lumshe idanunta da suka kawo ƙwalla, tunanin babanta ne ya faɗo mata arai, take taji zuciyarta ta ƙara karaya,, tana cikin wannan tunanin bacci ya ɗauketa ahaka.

Tsab ya gama shirin kwanciyarsa,  bayan ya gama latsa laptop ɗinsa.   Kwanciya yayi flat akan gadon haɗe da lumshe idanunsa,  sosai yakejin daɗin sanyin Ac’n dake hurasa,   wani abune yazo ya toshe masa maƙoshi,  akowacce dare baya samun wata gamsashshiyar nutsuwa, yanaji ajikinsa akwai wani gibi a tattare dashi,  haƙoransa yasa ya datse laɓɓansa,  sakamakon tunowa da korar da Ummu tayi masa ɗazu da yayi,  sam baya ganin laifin iyayennasa, saboda kowa tunani yake cewa  ason ransa yake sakan matan da ake aura masa, tunowa da magungunansa da yasayo yau yayi, miƙewa yayi jiki a sanyaye ya ɗauko magungunan,  ruwa ya ɗauka ya sha.

Luf yayi akan tattausan katifarsa,  duk yanda yaso bacci ya ɗaukesa ya kasa shikaɗai yaketa juyi akan gado,  saƙƙowa yayi daga kan gadon haɗe da zura slippers ɗinsa, falo ya nufa hanunsa riƙe da wayarsa.

Bai lura da itaba sam saida ya zauna akun kujeran dake facing ɗin wanda ta ɗaura kanta akai.

Shiru yayi haɗe da ƙura mata idanu,  kallon yanda tayi kwanciyar nata yasoma yi, duka jikinta na ƙasa yayinda kanta kuwa ke kan hanun kujera, dagani kasan baccinne ya ɗauketa batare da ta shiryawa hakan ba,  kallon ɗan ƙaramin bakinta dake ɗan buɗe yayi, tare da kawar da kansa gefe.   

Ɗan zamewa yayi ya jingina bayansa da jikin kujera, lumshe idanunsa yayi haɗe da soma sauƙe numfashi ahankali.

*** *** ***

4:50 am  dai dai ya shiga buɗe idanunsa ahankali, azabure ya tashi zaune yana bin inda ya gansa akwance da kallo,  yana jingine akan kujera bacci ya ɗaukesa batare daya sani ba, hanu yasa ya dafe goshinsa haɗe da furzar da wani iska mai zafi daga bakinsa.  Kallon gefensa yayi tananan kamar ɗazu saidai yanzu tadawo da kanta ƙasa, yayinda ta takure jikinta waje ɗaya da alama sanyin AC ne ke damunta.

Miƙewa yayi ya wuce ɗakinsa yana me mamakin kansa, tunda yake bai taɓa kwana afalo ba sai yau, sam baisan yaushe bacci ya ɗaukesa ba.

Toilet yashiga haɗe da sakarwa kansa ruwa.  Yana fitowa ya zura maroon jallabiya tare da ɗaukar sallayansa ya fice daga cikin ɗakin.

Haka ya wuceta afalon tana ta bacci ko kallon inda take baiyi ba ya fice.


Ahankali ta ware idanunta akan haɗaɗɗen zanen POP’n dake mamaye saman falon, fuskarta ta ɗan yatsuna haɗe da sanya hanunta akan wuyanta, jitayi wuyannata ya ƙage  waje ɗaya sosai yakeyi mata ciwo,  ahankali ta miƙe tsaye, kallon falon tayi sannan ta wuce ɗaki, banɗaki tashiga ta ɗauro alwala,  tana idar da sallan ta zauna akan sallayan haɗe da sake lumshe idanunta, ciwo wuyanta keyi mata sosai hakan yasa ko motsa kanta batason yi.


Tunda yafita daga gidan baidawo ba sai Ƙarfe 9 na safiya, yana shiga bedroom direct toilet ya nufa,  kwanciya yayi luf acikin jakuzzien daya ji ruwan wanka wanda aka cakuɗasa da daddaɗan turaren wanka mai ƙamshin gaske,   lumshe idanunsa yayi, kansa ne ke ɗanyi masa ciwo kaɗan kaɗan, ajiyar zuciya yayi, sakamakon tunawa da yayi cewa gobe zai wuce Abuja,  sai dai kuma baisan ina zai saka wannan kayan daya ɗaukowa kansa ba.

***

Acan Ƙauye kuwa, Inna Ma’u sun wayi gari anata shirye shiryen ɗaurin aure, basu farga da cewa Ziyada bata gidan ba saida jama’a suka hallara don ɗaurin auren, tashin hankali kam Inna Ma’u ta shigesa, babu inda ba su bazama ba wajen nemanta amma babu ko wani wanda yace ya ganta.  Sosai hankalin Mahaifinta ya tashi, har baisan sanda wasu ƙwalla suka gangaro daga cikin idanunsa ba,   Inna Ma’u kuwa bala’i tashigayi haɗe da tsinewa Ziyada tana cewa wai ta cucesu ta kunyatasu,  shikuwa Tsoho Ɗan Dashe ai masifa yadingayi kamar zai tashi sama, take rashin mutumcinsa ya tashi, nan yakafe kaida fata lallai sai Inna Ma’u ta biyasa kuɗaɗen daya dinga narka mata, idanu Inna Ma’u tashiga zarewa kamar munafuka…..
***

Riga da wandone ajikinsa wanda suka matuƙar yi masa kyau, cike da ƙosawa ya ture laptop ɗin dake gabansa, kusan awansa biyu yana aiki da ita, gaba ɗaya jinsa yake agajiye,  kitchine ya wuce ya haɗa tea ɗinsa, dawowa cikin falon yayi ya zauna, kallon ƙofar ɗakin da take ciki yayi, kana ya dawo da kallonsa ga agogon dake saƙale ajikin bangon ɗakin 2:00pm dai dai yagani,  sake kallon ƙofar ɗakin yayi, sai alokacin ya tuno da cewa ko break bai bata ba,   kallon tea ɗinsa yayi haɗe da sake kallon ƙofar nata, yakan manta da cikinsa ma balle na wani, shi dama sam abinci bai dameshi ba, sannan ba ɗawainiyar kowane akansa ba,  shiyasa baiwani damu da wani yaci ko karyaci ba, baisan ya ake kula da wani ba, saboda shikaɗai yake rayuwarsa bawani a ƙasansa,  Saida yagama shanye tea ɗinsa kafun ya tashi daga zaunen da yake.  Wayarsa ya ɗauka ya turawa wata number text message, yanaganin alamar saƙon yatafi ya ajiye wayartasa.  Kwanciya yayi akan kujera haɗe da lumshe idanunsa.

(Readers anya Sooraj bazai kashe Ziyada da yunwa ba kuwa? My Wattpadians karku taɓa mantawa saboda ku kawai wallahi nayi typing, saboda haka kuma ku ɗaga darajata tahanyar bani comment da Vote, sannan kuma ba kullum zakuna samun Update ba.)


*Vote me on Wattpad*
     @fatymasardauna


#romance
#heartouching

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button