NOVELSUncategorized

SOORAJ 11

????????????????????????????????????????

              *SOORAJ !!!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*????Kainuwa Writers Association*                *Wattpad*
          @fatymasardauna

     *Chapter 11*

Tunda jirgin su ya ɗaga bai buɗe idanunsa ba har jirgin nasu ya sauƙa a NNAMDI AZIKWE Internation airport. Buɗe idanunsa yayi a hankali tare da  zare sit belt ɗin dake jikinsa, dubansa ya kai zuwa gareta, wani babban abun mamaki ganinta yayi tana bacci, fuskarta  ɗauke da wani bushashshen hawaye,  takaicinta ne ya sake kamashi, shi sam baisan ita wace irin bagidajiya bace ba, yanzu aɗan tafiyan da bai wuce 30 minute ba har ace tayi bacci ?

Hanunsa yasa ya zunguri kanta, da yake baccin nata baiyi nisa ba, hakan yasa ta buɗe idanunta, ta sauƙe ƙwayar idanunta a kansa.

Nuni yayi mata da ta cire sit belt ɗin dake jikinta, cire sit belt ɗin tayi tana mai mutsutstsuka idanunta da suke cike da bacci.
Gudun kada tayi masa halinnata na ƙauyanci ta ba da shi agaban mutane yasa ya tusa ƙeyarta gaba suka nufi hanyar fita daga cikin jirgin.

Cikin takunsa na isa yake sauƙowa daga kan matattakalan jirgin, sanye yake da riga da wando na jeans baƙaƙe sai kuma facing cap white colour daya sanya akansa, kalan takalman dake ƙafansa. 
Kallo ɗaya zakayi masa kafahimci cewa shiɗin cikakken ɗan gaye ne wanda yake murza naira.  babu wani makusa  atattare dashi, komai nasa yayi hundred percent, sam a halittarsa ta bayyane bazaka taɓa kawo cewa yana ɗauke da wata damuwa ba,  saboda shiɗin irin mazan nanne masu aji da wayewa, sannan yanada cikar halitta, komai nasa abun so ne ga ƴa macen da tasan kanta.  yanada kyawun jiki data fuska, ajikinsa dai kam baida wata makusa, amma kuma saidai shikaɗai yasan menene aibunsa, wanda idan da zai bayyana rauninsa a fili,  to tabbas da sai kowacce mace ta gujesa, saboda aibun dayake ɗauke dashi, yafi tsananin kyawu da dukiyarsa tasiri wajen rugujewar farincikinsa.   idan akayi dubi da lalurar dake damunsa shekara da shekaru to tabbas kyawunsa da haɗuwarsa ba zasu amfana masa komaiba,  dama kuma hakane yawanci kowani bawa da irin tasa tawayan.  

Yana gama sauƙowa daga kan matattakalan ya gyara zaman facing cap ɗin dake kansa.  Wani matashin saurayi ne ya ƙaraso wajen da suke da sauri. Cike da girmamawa ya ce.

“Barka da zuwa Oga”
yaƙare maganar yana mai karɓan jakan dake hanun Sooraj ɗin…      

“Yauwa!” Sooraj ya amsa ataƙaice. 

Juyowa yayi ya kalli Ziyada dake ta faman murje gajiyayyun idanunta, tana kuma ƙarewa haɗaɗɗen wajen kallo, domin kuwa wannan airport ɗin ya ɗarawa wanda suka baro. 

“Kuje mota ina zuwa” yafaɗi haka yana mai ƙoƙarin shiga wata babbar ƙofa ta glass dake cikin airport ɗin.

“Ranki yadaɗe muje ko” wannan saurayin yace da Ziyada, da haryanzu take ta kalle kalle.   Babu musu tabi bayansa, sai dai a ƙasan zuciyarta shumfuɗe take da tsoro, zuwa yanzu wata zuciyar na sanar da ita cewa “Sai da ita Sooraj zaiyi”  hakanan zuciyarta tasa mata cewa ba banza yake ɗawainiya da ita ba, saidai kuma ta wata fuskar sam baiyi kama da mugayen mutane ba, duk da bayi da sakewa, amma baiyi kamanni da mugaye ba.

Direct wajen wata dan ƙareriyar mota taga sun nufa,  buɗe mata gidan gaba ɓangaren mai zaman banza matashin saurayin da ake ƙira da Kamalu yayi,  yana mai satan kallon fuskarta, mamakine cike azuciyarsa, yana mamakin a ina ogansa ya samota, yasan Sooraj yakuma san baida wata ƙanwa mace balle yace itaɗin ko ƙanwarsa ce, ya kuma san halin ogan nasa baya neman mata, balle ko yace  wata ya ɗauko zasuyi zaman haramci,  da wannan tunanin yashiga ɓangaren driver ya zauna.

Fuskarta ta manna ajikin glass ɗin window’n motar tana mai kallon mutanen dake ta hada hada a wajen.
Kallonta ta mayar ga ƙofar da taga ya shiga, daidai lokacinne kuma ta hangoshi ya fito,  fuskarsa ɗauke da wata ƴar guntun murmushi da iyakanta kan leɓe,    tunda take arayuwarta bata taɓa ganin mutum irinsa ba,  haka kawai take ganinsa wani daban acikin mutane, komai nasa special ne.    Gani tayi wani ya biyosa abaya yana dariya, atare suka jero da Sooraj ɗin fuskar wannan ɗin ɗauke take da fari’a saɓanin Sooraj da fuskarsa ke ɗauke da yanayi irin na ba yabo ba fallasa.  Har wajen motar Ma’arouf ya rako Sooraj. (Ma’arouf abokin Sooraj ne sannan babban matuƙin jirgin sama ne)         

Buɗe gidan baya Sooraj yayi ya shiga,  ɗan ranƙwafowa Ma’arouf yayi haɗe dayin knocking  glass ɗin window’n motar ta inda Ziyada ke zaune,  a hankali Kamalu yayi ƙasa da glass ɗin window’n, atunaninsa gaisawa Ma’arouf ɗin keso suyi dashi, don yasan halin Ma’arouf akwai kirki, baruwansa komin ƙasƙancinka zai sake kuyi mu’amala dashi.

Waro idanunsa yayi haɗe da sanya hanu ya shafi fuskarsa,  “Masha Allah!” yafaɗa acikin zuciyarsa bayan yayi tozali da kyakkyawar fuskar Ziyada.

“Wow!! Raj ina kasamo mana wannan haɗaɗɗiyar baby’n haka?     i hope dai ba kayan ka bace?”    Ma’arouf yatambayi Sooraj yana mai sake ƙarewa fuskar Ziyada kallo, saboda yarinyar tayi matuƙar tafiya da imaninsa musamman ma Innocent face ɗinta.

“Kaya na?” Sooraj ya maimaita tambayar da  Ma’arouf yayi masa abakinsa cike da mamaki.

Dariya Ma’arouf yayi haɗe da dawo da kallonsa ga Sooraj.  Gira ɗaya ya ɗage masa haɗe da cewa 

“To ya kagani idan da ace zata zama MALLAKINA?” 

Murmushin gefen baki Sooraj yayi haɗe da cewa ” ko zaka jarraba hakan ?” yanayin yanda yayi maganar cikin halin ko inkula,  shiya sanya  Ma’arouf yin murmushi haɗe da kallon Ziyada wacce idan da za’a kasheta bata fahimci inda kalaman nasu suka dosa ba, ita hankalinta ma ba akansu yake ba. 

“Zan jarraba idan kabani dama, amma bayanzuba zaifi kyau nayi kiwonta” Ma’arouf yafaɗi haka cike da shauƙi.

“Banda enough time zaka iya jan motar mutafi?” Sooraj yafaɗi haka ga Kamalu cike da halin ko inkula da zancen da Ma’arouf ɗin keyi.

Jin kalaman Sooraj yasa Kamalu saurin tada motar.   

Ma’arouf dake tsaye yana kallon Sooraj yasaki murmushi haɗe da maida kallonsa ga kyakkyawar yarinyar dako sanin sunanta baiyi ba.   Maida Glass ɗin window’n Kamalu yayi ya rufe, haɗe da yin reverse.   Juyawa Ma’arouf yayi yakoma inda ya fito yana sakin wani murmushi.

Tunda suka hau titi ta sake baza idanunta wajen kalle kallen shukokin dake jere gefe da gefen titi, dogin gine gine masu kyau suketa  wucewa, komai gwanin burgewa.             
Shikuwa tunda ya ɗauki jarida yamai da hankalinsa akai, ko ɗago kansa baiyi ba, sai dai har aƙasan zuciyarsa yanata juya kalaman Ma’arouf da yake tambayarsa “wai itaɗin kayansa ce?”   Hmmm lallai yasake yarda babu wani wanda yasan sirrinsa, inbanda ma rashin aiki irin na Ma’arouf mai zaiyi da wannan ƴar mitsilan yarinyar? shi bayaji idan ma akwai wani abu acikin iskanci to zai samu atattare da ita, duka dukanta bata wuce 18 to 19 years ba to me zai ɗauka ajikinta? balle ma shikam mace kodaga wacce duniya tafito bazata amfanesa ta fannin mu’amala ba, saidai ko tawani ɓangare kamar aiki da sauransu.

Asokoro.

Gaban  wani tangamemen gate mai kyau da tsari Kamalu driver ya tsaya haɗe da soma danna horn ɗin motar,  da sauri wani daga cikin gidan ya wangale musu makeken gate ɗin, shikuwa Kamalu driver ya shigar da motan ciki. 

Yana gama daidaita parking ɗin motar ya juyo ga Sooraj cike da ladabi yace “Ranka ya daɗe mun ƙaraso” 

Batare daya ɗago kansa daga karatun jaridan dayake ba yace “Okay!” 
Fita daga cikin motar Kamalu driver yayi bayan ya ɗauki jakar Ogannasa ya yi cikin gida da ita. 

Ganin yana ƙoƙarin fita daga cikin motar yasa itama ta buɗe murfin motar ta fito,  compound ɗin gidan take ta kallo.

Kamar jela haka take biye dashi a baya, kafun yaƙaraso ma tuni Kamalu yasa key ya buɗe ƙofar da zata sadasu da cikin katafaren falon gidan.

Ganin ya buɗe ƙofar yashiga yasa itama ta bi bayansa Tana jefa ƙafafunta acikin falon suka soma nutsewa acikin wani lallausan carpet dake malale aƙofar shigowa falon, wani sanyin AC ne ya ratsata.   Kamalu driver na ajiye jakan hanunsa ya fita daga cikin falon haɗe da rufo musu ƙofar,  sam tamanta ma tare suke dashi, falon tashiga ƙarewa kallo, komai na cikin falon milk colour ne daga kan kujeru har zuwa kan labulaye, falo ne haɗɗaɗɗe mai ɗauke da tsari irin na mazan da suka san kansu.  

Sooraj kuwa kota kanta baibi ba direct ɗakinsa ya wuce,  yana shiga yarage kayan dake jikinsa haɗe da shigewa cikin bathroom.    Al’adansane idan yaje wanka kafun yayi wanka sai ya kunna shower ruwa ya dakesa sosai, yau ma hakance ta kasance, sosai ruwan shower yadaki jikinsa, sannan yayi wanka.

Fitowa yayi daga cikin bathroom ɗin sanye da rigan wanka ajikinsa.

Akan kujeran dressing mirror ya zauna haɗe da ɗaukan comb yashiga taje sumar dake kansa wacce take a jiƙe da ruwa.
Yana kammalawa yayi amfani da handryer wajen busar da gashin kansa,  hakanan yake shi mutum ne maison tara suma akansa, sannan kuma koda yaushe, askin kansa irin na turawa ne, shiyasa always yake yanayi dasu,  sosai kuma askin keyi masa kyau, saboda gashin nasa yana da laushi, ga kuma gyaran da yakesha na mayuka masu tsadan gaske. 

Sosai yake son combat trouser saboda hakanema yawancin wandunansa suka kasance Combat.    Yanzu madai Combat jeans yasanya a jikinsa.   kwanciya yayi akan makeken gadonsa,  lumshe idanunsa yayi haɗe da jawo wayarsa ya saƙala earpiece akunnensa,  waƙa yakeji mai sanyin sauti, hakan yasa  duk yaji jikinsa yayi weak.  

Jin ansoma ƙiraye ƙirayen sallan Isha ne yasashi miƙewa,  jallabia ya sanya ajikinsa, haɗe da zura flat shoe aƙafafunsa ya fice daga cikin ɗakin.   
*** *** ***

Biro ya ɗauka ya cike wata farar takarda dake aje kan babban table ɗin dake gabansa.  Ɗaukar takardan yayi yashiga jujjuyata acikin hanunsa, kamar wani maiyin nazari,  kallon katafaren office ɗinsa yayi haɗe da fitar da wani dogon numfashi ta bakinsa.   

Hanu yasa ya shafi tarin sumar dake kansa,  ware idanunsa da suka soma rikiɗa daga farare zuwa kalan ja yayi, wani zafi zafi ya keji aƙasan ƙirjinsa, ga wani zazzaɓi dake shirin dirar masa lokaci guda,  haka yake  aduk sanda yayi yunƙurin tuna wani abu da ya danganci sha’awa sai yayi wani zazzaɓi mai zafin gaske, abun yakan fin ƙarfin brain ɗinsa, duk yanda yaso yayi wani tunani mai ƙarfi abun ya faskara.       Tashi yayi yanufi wata ƴar ƙaraman drawer dake cikin office ɗinnasa,     buɗe drawer’n yayi haɗe da ciro wata allura, tun ɗazu ya haɗata amma hatsarin dake cikinta yasa yaɗan jinkirta yinta, shikansa baisan mai zai biyo baya ba idan yayi alluran, amma bashi da wani zaɓi wanda ya wuce yayi ta. 
 akan jijiyar dake hanunsa  na dama ya saita alluran, rumtse idanunsa yayi haɗe da soma matse ruwan alluran acikin jikinsa,  yana gama yiwa kansa alluran ya buɗe durstbin ya jefa alluran aciki,     suit ɗin sa dake rataye kan kujera ya ɗauka yariƙe ahanunsa, haɗe da ɗaukan wayoyinsa.    Fitowa yayi daga cikin office ɗin haɗe da sa key  ya rufe ƙofar office ɗin.      Ta ƙofar baya yabi   direct inda zai sadasa da parking space ya nufa,   yana zuwa ya faɗa cikin motarsa, haɗe da kunnata yafice acikin Bank ɗin baki ɗaya….


Yanayin yanda yake murza steering motar kaɗai ya isa tabbatar maka da cewa ba ƙalau yake ba, saboda a slow yake tuƙa motar kamar wani wanda baida ishashshen ƙarfi ajikinsa,        ahalin yanzu yakai wani stage da ko iya kallon gabansa bayayi sosai,  idanunsa sun yi jajur dasu yayinda suka ƙanƙance alokaci guda, yanayin yanda yake danna horn ɗin motar ne yasa mai gadi ya yi saurin wangale masa gate,  kashe motar yayi haɗe da kifa kansa akan steering motar.  Jiyake gaba ɗaya duniyar na juya masa, gawani zazzaɓi da ya rufesa, hatta numfashinsa saida ya sauya.  Da ƙyar ya iya buɗe murfin motar ya fito. Direct babban falon gidan ya nufa.    

Tana zaune akan sofa ta ƙurawa TV plasma’n daketa aiki idanu, sosai kallon ya ɗauki hankalinta. Ahankali ya tura ƙofar falon ya shiga, idanunsa a lumshe haka yasoma takawa zuwa cikin falon,   ɗago da manya manyan idanunta tayi ta kalleshi, kasa ɗauke idanunta tayi akansa  ganin yanda yake tsaye kamar ma baya cikin hayyacinsa.     Yana ɗaga ƙafansa yaji gaba ɗaya jikinsa yayi sanyi komai nasa ya tsaya cak, take numfashinsa ya ƙwace mai, yanke jiki yayi ya faɗi a wajen baya ko numfashi.  


       *Vote me on Wattpad*
          @fatymasardauna
Ku danna hoton kasa don bada gudun muwarku

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button