NOVELSUncategorized

SOORAJ 19

????????????????????????????????????????

             *SOORAJ !!!*

   *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*
_{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*
*

           *WATTPAD*
     @fatymasardauna

#romance

          *Chapter 19*

Tsaye take ajikin window tana mai jiran shigowanshi,  amma kuma sai dai ga mamakinta har anshare sama da mintuna 10 baishigo cikin faƙon ba, sake gyara tsayuwanta tayi,  tare da soma murza ƴan yatsun hanunta.    Buɗe ƙofar falon yayi ya shigo, yana mai ƙoƙarin cire suit ɗin dake jikinshi,  idanunsa ne suka sauƙa akanta, amma saiyayi saurin kawar da kanshi gefe, tare da ƙarasawa cikin falon,  aje suit ɗinnasa yayi akan kujera tare da cire agogon dake ɗaure atsintsiyar hanunshi,  gaban fridge yaje tare da buɗewa ya ɗauko goran ruwa, ɓalle murfin yayi tare da kaiwa bakinsa, saida ya tabbatar da cewa babu komai acikin goran,  sannan yayi wurgi da goran cikin dustbin, dawowa cikin falon yayi ya ɗauki suit ɗinshi kana ya nufi hanyar bedroom ɗinsa, gaba ɗaya ma yi yayi kamar baisan da zamanta acikin falon ba,  tana ganin shigewarsa cikin ɗaki.  Ta saki wani gauron  numfashi, sam bazata iya yi masa magana ba, kwarjininsa ya wuce gaba ɗaya tunaninta, sumu sumu haka ta wuce tayi ɗakinta.

Kwance yake acikin jakuzzie ɗinsa, wanda yasha haɗaɗɗen ruwan wanka,  daga kan ƙafafunsa zuwa ƙirjinsa, gaba ɗaya lume suke acikin ruwa, kansa da hannayensa ne kawai suke waje, yayinda kyawawan idanunsa suke alumshe, kana ya ɗan jingina bayan kanshi da jikin jakuzzie’n,  gaba ɗaya hankali da tunaninsa baya tare dashi,  sam kwana biyunnan baya cikin wata gamsashshiyar nutsuwa, tunani da damuwa sune abun da suka sakoshi gaba,  akullum kuma ako wacce rana jin kansa yake tamkar wani baƙon halitta, ya sani acikin rayuwarshi akwai tawaya sosai, amma kuma baison ya zamanto mai rauni saboda hakan,  baiso yazama ɗaya daga cikin irin mutanennan da basa iya riƙe damuwarsu,   shikansa ya sani da ace lafiyarshi ƙalau, to da bazai taɓa iya kai wannan lokaci mai tsawo haka, batare da mace akusa dashi ba, “Menene matsalarsa? mecece damuwarsa? meyasa baya iya zama da mace?” yasan duk waƴannan abubuwan iyayensa suna da buƙatar sani,  “Amma mai yasa basa tambayarsa?” wannan tambayar shi ne abun da yake tambayar kanshi akullum, baikamata don ya kasance Namiji su sakar masa ragamar rayuwarsa ba, duk da cewa ya girma amma tabbas yana da buƙatar kulawan Iyaye atare dashi.
Wani numfashi yaja tare da fesarwa alokaci guda,    wani irin tausayin kanshi yakeji, sosai yake tausayawa al’amuranshi,  baisan taya zai dubi wata mace yace yana sonta ba, haka kuma baisan wace macece zata iya zama ta jure lalurar shi ba,  bazai taɓa yaudaran kanshi ba, saboda yasan babu wata mace da zata iya jure zama dashi ayanda yake, musamman ma idan tasan ƙatuwar matsalan dake tare dashi, yasani  shi me raunine ako da yaushe, safe, dare, rana, babu wani lokaci da zaizo masa yana cikin farinciki da walwala,  sau da dama yakanji kamar yayita kuka, ko da zai samu salaman rage ƙuncin dake cikin zuciyarshi, saidai hakan baya samuwa ayanzu, sakamakon zuciyarsa da tayi tauri,   haƙoransa yasa ya ɗan ciji laɓɓansa da ƙarfi, shi kaɗai yasan me yake ji, haka kuma shi kaɗai yasan kalan  ƙunci da yake ciki,  sama da shekara 10 kenan da haske ya gujewa rayuwarsa, azahiri acikin haske yake rayuwa, amma kuma idan aka duba bayansa duhune dulum mai wuyar kalluwa.    Cikin rashin kuzari haka yayi wanka, tare da ɗauro towel akan waist ɗinsa ya fito daga cikin toilet ɗin.
Zama yayi akan gado tare da ɗauko mayinsa ya soma shafawa, yana kammalawa ya feshe jikinsa da body spray mai daɗin ƙamshi.  3 guater jeans and white t-shirt ya sanya,  laptop ɗinsa mai ɗauke da tambarin apple asaman murfin ya ɗauka,  tare da ficewa daga cikin ɗakin.  Aje laptop ɗin yayi akan rug tare da buɗe fridge ya ɗauko goran pepsi mai matuƙar sanyi.  Zama yayi akan rug ɗin, tare da tanƙwashe ƙafafunsa, buɗe laptop ɗinshi yayi ya soma gudanar da aikinsa kamar yanda ya sabayi akowacce rana. 
** 
Ziyada kuwa komawa ɗaki tayi, tayi kwanciarta, harta fara bacci ta tuno cewa wulaƙanta abinci ba kyau,  hakan yasa ta fito saɗaf saɗaf  kan dinning ɗin ta nufa, abincin yana nan kamar yanda ta ajiye sa, ɗaukan kulan tayi ta fice daga cikin falon, direct wajen maigadi ta nufa nan ta sameshi zaune shida Kamalu driver suna hira,  kulan abincin ta basu, duk da basusan menene aciki ba saida sukayi mata godiya,  ita kuwa ta juya ta koma ciki.     Zama Kamalu driver da maigadi sukayi,  suka ci shinkafa da miyan, sam basuji wani abu na’alamar rashin daɗi acikin abincin ba, haka suka ci abincin sukayi nak.

*** ***

Washe Gari.

Tun kafun 7 yau ta kammala shirinta bayan tayi wankan tsarki, saboda tun jia da yamma bata ga komaiba,  hakan yasa taji ajikinta cewa ta samu tsarki. 7 nayi suka bar gidan.
 Zuwanta yayi daidai da zuwan Nasmah, nan suka zauna suka soma taɓa hira kafun Shukra tazo….   

*** *** 
Bayan sati biyu.  

Alhamdulillah. Ayanzu sosai Ziyada take gane karatun da ake koyar musu,  duk da cewa turanci har yanzu yana bata wahala,  sannan kuma bata iya wani abu sosai daga cikinsa ba, amma duk da haka sosai take gane karatun, saboda kullum idan malami yazo yayi musu lecture  yana fita Nasmah zata ƙara fahimtar da ita,  yau suke shirye shiryen farayin test don haka daren jia,  kusan kwana tayi tana biye karatun Maths ɗin da akayi musu, tun daga zuwanta har kama daga wanda akayi  batanan, duk Nasmah tayi ƙoƙari wajen ganin ta koya mata.   

Sunyi test ɗinsu lafiya, inda ko wanne ɗalibi dake cikin ajin yake sa ran cinyewa, ita ma Ziyada tayi ƙoƙari ƙwarai,  domin kuwa acikin guestions huɗu  da akace su amsa,  ta samu ta amsa uku, kuma aranta tana sa ran cewa zataci duka ukun. Koda aka raba musu paper’n test ɗinnasu, ta samu six  ɗayan da batayi ba kuwa tasamu zero, domin dama shine keda yawan maki har 4 mark yake dashi, duk da haka ma taji daɗi sosai.

Kwana biyunnan gaba ɗaya basu da wani hutu ko acikin school, kullum cikin karatun test suke ga exams ɗinsu dake ta gaba towa,  kasancewar exam ɗin third term ne, shi zai kaisu  s.s 2,  hakanne yasa gaba ɗaya hankalin ɗaliban dake cikin school ɗin atashe yake, domin kuwa matuƙar bakaci exam ɗin ba, to fa repeat ɗinka za ayi babu ruwansu dakai ɗan waye.   Ɓangaren Ziyada kuwa abun ya haɗe mata sosai, domin kuwa ta dage tana koyan karatun da akayi baya kafun ta shigo, ga kuma wanda akeyi musu yanzu hakanne yasa gaba ɗaya brain ɗinta ta ɗauki charge,  saidai kuma cikin ikon Allah da kuma tsananin nacin da tasanya aranta karatun yana zama akanta. Ayanzu kwata kwata ta daina haɗuwa da Sooraj,  bata sanin fitarsa bata kuma sanin dawowarsa, duk da kuwa tsananin son ganinsa da take, amma hakan baya samuwa agareta.  Agajiye ta ɗaura kanta akan kafaɗan Shukra wacce take ta faman latsa babbar wayarta.    Ɗan kallonta Nasmah tayi tare da cewa.
 “Badai kin gaji da karatun ba?”

“Nagaji mana Nasmah, zan bari sainaje gida kawai naci gaba!” 

“Amma kinsan fa Monday zamu fara exam ko?” Shukrah tafaɗa tana me maida wayarta cikin jaka.

Murmushi Ziyada tayi tare da cewa “Har kingama shan soyayyan?”  

Hararanta Shukrah tayi tare da cewa “Nifa wallahi kunsamin ido, hmm kawai don bakusan daɗin soyayya bane ba shiyasa”

“Daɗi? hmmm ina daɗi acikin wannan abar da kullum sai anbata miki rai? wallahi Shukra inaganin kawai wahalar dakanki kikeyi, s.s one kaɗai fa muke, amma wai ace ke har soyayya kike hmmm Allah ya kyauta!” Nasmah tafaɗi haka tana ɗan taɓe bakinta, ita sam wannan tsarin na soyayya baiyi mata ba, saboda ita atsarinta idan zatayi soyayya tafiso sai taje irin 2 hundred level ɗinnan. 

“Hmm kwata kwata bazaki gane ba Nasmah, amma kema watarana nasan zakiji abun da nakeji!” Shukrah tafaɗi haka tana mai ƙoƙarin tashi tsaye daga zaunen da take.

“Ba abun da zan gane!” Nasmah tafaɗi haka cike da jin haushi.

Murmushi Ziyada tayi tare da sunkuyar da kanta ƙasa, haka nan tunaninsa ya faɗo mata arai, jitayi gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, kallonta Shukrah tayi tare da cewa.  “Muje ki rakani kinji share wannan abar”   Still murmushi kawai tayi sannan tabi Shukrah suka tafi, Nasmah ma binsu tayi tace bazata zauna ita kaɗai ba, direct ɓangaren da ake koyar da girke girke  dake cikin makarantar suka nufa, ƴan department ne dayawa awajen kowa yana baje basirarsa, gani tayi Nasmah tashiga itama ansoma bugawa da ita, tsayawa tayi daga gefe tana kallonsu, dukkan abun da sukeyi tana haddace shi akanta, sunjima awajen kafun suka koma class.  

Koda ta koma gida gaba ɗaya bata wani samu sukuniba karatu ta dinga yi, har wayewar gari ta shirya tatafi makaranta, acikin ƴan kwanakinnan wani abu da ta fara fuskanta shine sauyawar da jikinta yasomayi, hips ɗinta ne taga sun ƙara faɗi, yayinda ƴan saffa saffan breast ɗinta suka ɗan ƙara girma, skin ɗinta ta sauya tayi wani fresh,  ga kyawun da fuskarta take ƙarawa ako da yaushe, ita kanta sau da dama idan ta kalli kanta takanyi mamakin yanda kamanninta ke ƙara sauyawa.    Tun ɗazu su Nasmah suka fita break suka barta, kasancewar bata ƙarasa note ɗinta da wuri ba, miƙewa tsaye tayi bayan ta kammala note ɗin, maida littafinta tayi cikin jaka tare da ficewa daga cikin ajin.

Wata haɗaɗɗiyar mota ƙirar benz ce ta kunno kai cikin makarantar. Adai dai kusa da parking space ɗin makarantar yayi parking motar,  buɗe murfin motar yayi tare da zuro ƙafafunsa waje, cikin yanayinsa na nutsuwa yafito daga cikin motar,  haɗaɗɗen saurayine mai kyau da gayu, ba fari irin tas ɗinnan bane, amma yana da nasa irin salon hasken, direct idan ka ganshi zaka ƙirasa da mai kyau, kasancewar babu laifi shima yana da nashi kyau’n, irin Handsome guy ɗinnan ne mai son ado da gayu,  dogone amma basosai ba sannan yana da ɗan faffaɗan jiki, yana da wani kwantaccen sajen da yaƙarawa fuskarsa kyau,  sanye yake da riga da wando na jeans masu kyau, yayinda ya rufe gashin kansa da facing cap blue colour.  Cikin isa yake takunsa yana mai ɗan kaɗa key ɗin motarsa dake riƙe a hanunsa, direct office ɗin principal  ya nufa.   Ta baya baya take tafiya tana dariya yayinda Nasmah ke biyota da ɗan sauri sauri, ɗan juyawa tayi sam bata ankara ba, saiji tayi ta bugu da mutum yayinda kanta ya daki ƙirjin mutumin da ta buge, da sauri ta juyo tare da sanya hanu ta dafe goshinta cikin yanayi naɗan jin zafi tace.  “Auchhh!!”  Shima hanu yasanya ya dafe ƙirjinsa, daidai saitin inda kanta ya buga. 

Ɗan zame hanunta tayi daga kan fuskarta,  idanunsune ya sarƙe cikin na juna, ɗan matsawa baya tayi tare da sake kallonsa.   
“Kayi haƙuri dan Allah bankula bane!” tace dashi cikin murya mai sanyi.

Murmushin daya bayyana dimples ɗinsa yayi mata tare da cewa.   “Babu damuwa!” shima cikin sanyi yayi maganar, yana mai ɗan ƙara faɗaɗa murmushin dake kan fuskarsa.  Raɓawa tayi taɗan gefensa ta wuce, Shukrah da Nasmah suka bita abaya.   Kafeta da sexy eyes ɗinsa yayi  har saida yaga shigarta  class sannan ya ɗauke idanunsa, sannan ya juya ya nufi inda zashi. 


Har ta zauna akan sit ɗinta tana dafe da goshinta, don taji zafin buguwar da tayi baɗan kaɗan ba. 

Dariya Shukrah tayi tare da cewa “Wai miye hakan kike dafe da goshi sai kace wanda kika bugi dutse?” 

“Ai inajin da dutse da shiɗin basu da maraba!” Ziyada tafaɗi haka tana mai ɗan mulmula goshinta.
 Dariya su Nasmah suka sanya.  “Dole zakiji zafi mana, daganinsa ai zaki san ma’abocin yin gym” Shukrah ta faɗi haka tana mai ƙoƙarin murzawa Ziyada goshinta.  Malami ne ya shigo cikin ajin hakan yasa suka nutsu, tare da maida hankalinsu kansa. Kwana biyunnan duk ba atashinsu da wuri yau har 5:30 sannan aka tashesu.  
**
Tana shiga cikin ɗakinta ta soma rage kayan jikinta, banɗaki ta shiga tayo wanka.  Riga da sket ƴan kanti ta sanya sannan taɗan yafa wani ɗan ƙaramin ɗan kwali akanta.   Direct kitchine ta wuce, duk wasu ƴan ƙananan girki yanzu babu abun da bata iyaba.    Indomie ta dafa bawai don tanaso ba saidon yunwan dake damun cikinta.    Gaba ɗaya kwanukan da suka ɗan yi ƙura a kitchine ɗin ta kwashe ta kai gaban sink wankesu tayi tas, sannan tayi mopping kitchine ɗin.   Acikin kitchine ɗin ta zauna taci abincinta,  tana gamawa ta wanke plate ɗin data ɓata.    Zame ɗan kwalinta tayi ta ƙarasa gaban sink, hanu tasa ta tari ruwa ta wanke fuskarta,  tana maiƙoƙarin ɗaura ɗan kwalin tanufi hanyar fita daga kitchine ɗin, harta jefe ƙafarta na hagu acikin falon, da wani irin ƙarfi taji an jawota cikin kitchine ɗin tare da sanya hanu aka rufe mata baki gam.


(Kucigaba da haƙuri kuna manage lokacin dazan ƙara yawan typing yananan zuwa.
Vote da Comment ɗinku kawai nake buƙata please karkuna bani kunya seriously ina da buƙatar vote ɗinku sosai, because tananne kaɗai zangane kuna enjoying story’n.)


   *VOTE Me On Wattpad*
        @fatymasardauna

       

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button