NOVELSUncategorized

SOORAJ 7

????????????????????????????????????????

               *SOORAJ !!!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*????Kainuwa Writers Association*


_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

            
              *WATTPAD*
        @fatymasardauna

      *CHAPTER 7*

A ƙalla yaɗauki kusan mintuna 4 ajikin ƙofar, yayinda hanunsa ke  kan handle ɗin ƙofar. Cije laɓɓansa yayi kana yatura ƙofar ahankali yashiga.

Duka hannayensa ya zuba acikin aljihun wandonsa yana kallonta cike da takaici. Kallonsa yakuma maidawa ga ledan daya aje mata, yananan ayanda ya aje, don ko taɓa ledan batayi ba.

Ƴar ƙaraman tsuka yaja, haɗe da sanya hanu ya ɗan bugi kansa.   “Wannan yarinyar da’alama itace ƙaddarata ta biyu!” yafaɗi haka cikin wata silent voice, sam bayason damuwa, gashi yafahimci cewa ita kanta Yarinyar Damuwa ce mai zaman kanta agaresa.   “Yanzu da tayi bacci, shine takeso ya ɗauketa ko kuma me?” yatambayi kansa cike da takaicinta. 
Tsuka ya kuma ja kana yafice daga cikin ɗakin.

Mintuna kaɗan wasu nurses su biyu suka shigo cikin ɗakin, kasancewar alluran da Dr.Salees ya mata nada matuƙar ƙarfi bazata iya farkawa nan kusa ba, yasa Nurses ɗin suka ɗaurata akan wani gado wanda keda ƙafafun taya,   haka suka turota akan gadon har bakin motarsa, buɗe musu gidan baya yayi suka sanyata aciki.    Da wani irin gudu ya figi motartasa yafice daga cikin asibitin,    shikaɗai yaketa zuba tsuka, har ya iso makeken gidansa dake cikin unguwar Malali, yana gama daidaita parking ɗin motar tasa, yaɗauki goran ruwan dake gefensa,  ɓalle murfin yayi haɗe da kai goran bakinsa,   gaba ɗaya ruwan dake cikin goran yashanye tas, ko kaɗan bai rageba,   yanaganin wayarsa na ƙara amma yaƙi ɗagawa,  duk da bai duba sunan dake yawo akan screen ɗin wayarba, amma yasan wake ƙiransa, tunda yatafi yabarsa kuwa to shima bazai ɗaga ƙiransa ba, idan wulaƙancine shima ya’iya salo salo. 

Direct ɓangaren da zai sada sa da part ɗinsa ya nufa.   Yana shiga cikin bedroom ɗinsa yasoma rage kayan dake jikinsa.  Wani farin towel ya ciro acikin drawer’nsa ya ɗaura,  bathroom yashiga tare da kwanciya  acikin haɗaɗɗen jakuzzie’n da ruwan cikinsa ke ta tashin ƙamshi. lumshe gajiyayyun idanunsa yayi,  Sosai yakejin sanyin ruwan na ratsa sa.   Aƙalla yakusan 30 minute yana kwance acikin jakuzzie’n.    Da ƙyar ya samu ya iyayin wanka, jinsa yake amugun gajiye.      Koda yafito a wanka sama sama yashafa mai, da body spray ɗinsa mai matuƙar ƙamshi, ya feshe duka jikinsa, take ɗakin yasake gaurayewa da wani ni’imtaccen ƙamshi.   3 guater combat jeans yasanya, sai kuma wata riga da bata da nauyi.   Ƙara gudun AC’n ɗakin yayi, haɗe da faɗawa kan gado,  pillow  ya jawo ya ɗaura kansa, tare da lumshe idanunsa.  

Ƙarar wayarsane takaraɗe kunnuwansa, tsuka yayi cikin baƙin ciki yajawo wayar ya kara akan kunnensa,    shiru yayi batare da yace  komaiba, baiduba wake ƙiransaba alokacin daya ɗaga wayar, amma tabbas yasan cewa bawani wanda zai ƙirasa adaidai wannan lokacin in banda Mas’oud. 

Jin yayi shiru baice komaiba yasa Mas’oud buga tsuka cike da haushin SOORAJ ɗin yace…    “Karkayi tunanin nawani damu da kaine, tausayin yarinyar mutane kawai nake, yanzu yajikinnata? inafata dai ta farfaɗo ba wata matsala?”

Ƙirjinsa ne ya buga, da sauri ya buɗe idanunsa da suke a lumshe, haɗe da tashi zaune, hanu yasa ya ɗan doki kansa, harga Allah shi ya ma manta da batun wata yarinya, sam yamanta da tana cikin motarsa, da sauri ya kashe wayar, tare da sauƙowa daga kan gadon. Bedroom slipper ɗinsa yazura aƙafafunsa kana yafice daga cikin ɗakin.   

Key yasa ya buɗe murfin motar, tananan kwance tana sheƙa baccinta cikin kwanciyar hankali.

Hararanta yayi  kafun ya tura kansa cikin motar, ɗaukota yayi kamar wata ƴar baby yayi cikin gidan da ita.     Ɗakin dake gefen nasa yashiga da ita, komai na ɗakin neat kamar akwai wani wanda ke rayuwa acikinsa.  Yana zuwa daidai gadon ya saketa, ji kake tim tafaɗi akan lallausan katifan dake kan gadon.   Tabbas da badon alluran da aika mata mai ƙarfi bace, da ayanda ya wurgatan nan dole saita farka.   Juyawa yayi yafice daga cikin ɗakin.   Ɗakinsa ya koma, rigar jikinsa ya cire, komawa kan gado yayi ya kwanta. Shi kaɗai yake ƙunƙuni acikin zuciyarsa har bacci yaɗaukesa…..  

1:30 am

Tsananin yunwan dake damunta, shiyayi sanadiyar farkawanta daga bacci..    Buɗe gajiyayyun idanunta tayi tana jujjuyasu ahankali.  Azabure tatashi tana ƙarewa ɗakin data ganta aciki kallo,  tabbas idan zata tuna, wannan bashine ɗakin da ta ganta ɗazu aciki ba, da sauri tashiga waige waige, dirowa tayi ƙasa tana ƙarewa royal bed ɗin data ganta kwance akansa kallo,  jingina tayi da bangon ɗakin zuciyarta cike da tarin tsoro da kuma tambayoyi, hanu tasa ta dafe cikinta, da takejinsa kamar babu ƴaƴan hanji acikinsa, tsabar yunwan dake nuƙurƙusanta, wani irin juwa ne ke ibanta, durƙusawa tayi aƙasa haɗe da fashewa da kuka,   da duka hannayenta ta kama cikinta, tunda take adunia bata taɓa jin yunwa irin wanda takeji ayanzu ba, jitake kamar wani abu na tsakalan cikinta.  Miƙewa tayi ta buɗe wata ƙofa dake cikin ɗakin, atunaninta ko wani ɗakine da zata iya samun abinci taci,   gani tayi ɗakin ba komai sai fanfo da kuma wasu fararen abubuwa, saikuma wani abu da tagani asama kamar famfo, duk da cewa bata taɓa zuwa birni ba, amma jikinta yabata cewa nan ɗin banɗaki ne,  jan ƙofar tayi ta rufe haɗe da  nufar wata ƙofar, tana jan ƙofan kuwa ya buɗe, ahankali ta buɗe ƙofar ta fita,  ganinta tayi acikin wani katafaren falo wanda yagaji da haɗuwa, duk da cewa babu yalwataccen haske acikin falon, amma hakan baihanata ganin kyawun falon ba,  wurga idanunta dake ɗigar da ruwan hawaye tasomayi tako ta ina, tsorone yasake kamata, kawai saita sulale awajen tashiga rera kuka. 

Bayida nauyin bacci ko kaɗan, sama sama yakejiyo gunjin kuka acikin kunnuwansa, ɗan ya mutsa fuskarsa yayi, haɗe da buɗe idanunsa.  Shiru yayi yana maijin sautin kukan naƙara ratsa kunnuwansa,     Ahankali yace “Najidowa kaina masifa!”

Gyara kwanciyarsa yayi cike da takaicin tashinsa daga daddaɗan baccinsa da tayi, hanu yasanya ya toshe kunnuwansa,  sosai yatsani jin kukan mace arayuwarsa, so yayi ya shareta amma kukan da takeyi masa yakasa barinsa yayi hakan. Sauƙowa yayi daga kan gadon, batare daya sanya riga ajikinsa ba ya fice zuwa falo.   

Hanunsa ya ɗaura akan makunnin wutan dake falon haɗe da ɗan matsawa, take haske ya gauraye cikin falon, saurin ɗago kanta da ta cusa acikin cinyoyinta tayi, idanunsu ya sauƙa acikin na juna, wani irin bugawa kirjinta yayi kamar zai faɗo waje, take jikinta yaɗauki rawa,  da sauri ta rumtse idanunta, ganinsa a haka babu riga da tayi, ya mafi yunwar da takeji ɗaga mata hankali. 

“Wai Uban me kikewa kuka?” ya tambayeta a tsawace.

Bakinta ne ya ɗauki rawa, ƙanƙame jikinta tayi guri guda, ahankali ta shiga jijjiga masa kanta alaman  “Babu”

“Mcheeww” yaja tsuka cike da takaicinta. 

Kallonta yayi a ƙufule sakamakon yanda yaga gaba ɗaya jikinta na rawa. Harara ya wurgamata haɗe da nufar inda zai sadashi da kitchine ɗin dake cikin falon.

Tana ganin tafiyarsa, ta saki wani irin marayan kuka, aranta tana cewa, inane takawo kanta, wataƙila ma saida ita zaiyi, shikenan itakam ga abun da guduwa yajawo mata.

Mintuna kaɗan yadawo cikin falon, hanunsa ɗauke da wani cup, ƙarasowa gabanta yayi haɗe da miƙa mata cup ɗin.   Jikinta na rawa haka tasanya hanu ta karɓi kofin,  ruwan tea ne aciki, hanunta har ɓari yake alokacin da takai kofin  bakinta, abun da batasani ba shine Tea ɗin da zafi sosai,  da sauri ta furzar da wanda ta kurɓa, sakamakon ƙona mata harshe da yayi,    ta gefen ido yakalleta, haɗe da yin wata muguwar murmushi, yana sane ya haɗa mata tea ɗin da tafasheshshen ruwa.  

Hawayene suka gangaro daga cikin idanunta, harshenta ya ƙone sosai, amma Allah yasani bazata iya haƙura da shan tea ɗin ba, saboda yunwa takeji sosai.  Haka ta daure ta cigaba da shan tea ɗin tun tanajin zafinsa har ta daina ji, tas ta shanye tea ɗin ta aje kofin,  lokaci guda jikinta ya soma tsatstsafo da gumi,  sake jin gina bayanta tayi da jikin bango tana sauƙe ajiyar zuciya akai akai.

Fitowa yayi daga kitchine ɗin haɗe da sanya key ya rufe ƙofar,  plate ne ahanunsa, wanda ke ɗauke da yankakkun kayan fruit,   miƙa mata plate ɗin yayi cike  da haushinta yace  
“Gargaɗi na ƙarshe kada ki sake tashina idan ina bacci!”     

Itadai kanta na ƙasa bata sake ɗagowa ta kallesaba tun ganin farko da tayi masa,  jin ƙaran rufe ƙofarsa ne, yasa ta sauƙe ajiyar zuciya, da bibbiyu take tura yankakkun kayan fruit ɗin abakinta,  fruit ɗin nada yawa, amma saida taci fiye da rabinsa sannan taji ta dawo cikin hayyacinta, hamma tayi haɗe da tashi tsaye tanufi wajen da fridge ke aje, bata iya buɗe fridge ɗin ba, hakan yasa tasoma kiciniyar ɓalle murfin, da ƙyar dai tasamu ta buɗe dayake murfin na glass ne, kana iya hango komai dake cikin fridge ɗin, goran ruwa ta ɗauka tasha, mayarda sauran ruwan tayi cikin fridge ɗin,  saɗaf saɗaf haka ta koma ɗakin da ta ganta aciki tun farko, jingina tayi da jikin ƙofar tana mai ƙarewa ɗakin kallo,   tsananin tausayin kantane ya kamata, yau gata a wata duniya wacce batasan ina bane,  gata acikin gida tare da wani, wanda batasan ko shiɗin waye bane, ahalin yanzu batasan menene makomarta ba, zamewa tayi akan yalwataccen carpet ɗin dake malale a tsakar ɗakin, kuka tashiga rerawa marar sauti, sosai tayi kuka harsaida taji kanta yayi mata nauyi, sannan ta tsagaita ajiyar zuciya tashiga sauƙewa akai akai, tana jingine ajikin bango, wani wahalallen bacci ya ɗauketa…..

Tunda kukanta ya tashesa yakasa komawa bacci, toilet yashiga ya ɗauro alwala,  dardumansa ya shumfiɗa yatada sallah…. Yajima yana salla kafun ya idar, laptop ɗinsa yajawo ya soma gudanar da wasu ayyuka, yananan har aka ƙira sallan asuba,   rufe laptop ɗin yayi yafita zuwa masallaci…

Sauri Sauri yake shirya kansa kasancewar angayyacesa meeting ɗin gaggawa anan branch ɗinsu dake cikin Kaduna. 

Sanye yake da riga da wando na suit masu mugun tsada da kyau, navy blue colour,  takalmin ƙafarsa kuwa toms ne mai kyau shima navy blue colour,  sosai yayi kyau acikin kayan, nikaina bansan haɗuwarsa takai hakaba, sai yau dana gansa acikin shigar suit. Lol.
Agogon Rolex yake ƙoƙarin ɗaurawa a tsintsiyar hanunsa, babu abun dake tashi ajikinsa sai daddaɗan ƙamshin turarensa mai sauƙar da nutsuwa, gashin kansa kuwa sai ƙyalli yake fitarwa, sosai yasha gyara da mayuka kala kala,    wayarsa mai tambarin Apple abaya ya ɗauka, tare da key ɗin motarsa, kana yafice daga cikin ɗakin..  

Haɗaɗɗiyar sabuwar motarsa BMW ya hau,  mai gadi na buɗe masa ƙofa ya cillata kan titi ahankali yake murza steering motar cike da nutsuwa..

Tun ƙarfe 7 tatashi zama tayi jigum acikin ɗakin,  kallon kayan jikinta tashigayi gaba ɗaya sunɓaci da jini, gashi sunyi bala’in yin dotti, banda ɓarkewan da saman rigarta yayi.

Tun tana zaune tana nazari harta kwanta, juyi kawai take tayi, amma gaba ɗaya bata da nutsuwa,  jin ana knocking ƙofar ɗakinnata  yasa taji ƴaƴan cikinta sun sake hautsinawa saboda tsoro,  cigaba akayi da knocking ƙofar, yayinda itakuma ta matse jikinta waje ɗaya,  mugun tsoronsa takeji.   

“Good Morning Madam” taji muryan mai knocking ƙofar na faɗan haka.

Tsorone yasake kamata,  raba idanu tashiga yi tana neman wajen ɓuya don batasan meyake cewa ba, tasan dai wani yare kawai yake yi.

Peter dake tsaye jikin ƙofa hanunsa riƙe da leda ɗin abinci, yaji yasoma gajiya saboda haka, yaciro wayarsa yaƙira ogansa,    bansan mai SOORAJ yafaɗa masa ba, sai gani nayi ya aje ledan  abakin ƙofa yajuya yayi tafiyarsa. 

Jin shiru andaina ƙwanƙwasa ƙofarne bakuma alamar motsin mutum, yasata sauƙo daga kan gadon ahankali.  Saɗaf saɗaf take tafiya harta buɗe ƙofar ɗakin, bugewa tayi da ledan da Peter ya ajiye.  ko kallon ledan batayi ba tashiga takawa harzuwa tsakiyan katafaren falon.   Gaba ɗaya bata cikin nutsuwarta sai waige waige take, ƙirjintane keta bugawa da sauri sauri fatanta ɗaya Allah yasa kada wani yakamata.   Wata ƙofa dake cikin falon tanufa, tana buɗe ƙofar kuwa ta buɗu,  wani irin ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya tasauƙe sakamakon ganinta a waje da tayi.   Da sauri sauri ta nufi  inda ta hango wani ƙaton gate, burinta ɗaya shine ta ganta awaje, sam batajin zata iya zama agidan ƙattin maza, wataƙilama da wata manufa suka ajiyeta.      Taci sa’a kuwa babu kowa abakin gate ɗin saboda haka gadan gadan tanufi ƴar ƙaramar ƙofan dake jikin gate ɗin ɗaura hanunta tayi ajikin ƙofan tare da buɗewa….

*(Niba cikakkiyar bahaushiya bace dole sai kunyi haƙuri da hausana, nasan wasunku bakomai suke ganewa acikin rubutuna ba????)*

            *21/March/2020*

*✅OTE ME ON WATTPAD*
         @fatymasardauna

#hearttouching
#truelove

  

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button