NOVELSUncategorized

SOORAJ 8

????????????????????????????????????????

              *SOORAJ !!!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*????Kainuwa Writers Association*

_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_


*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

           
             *WATTPAD*
       @fatymasardauna


*????HBD Yaya Hayat wishing you long life and more money in to your bank account*

             *Chapter 8*

Tana buɗe ƙofan idanunsu ya sarƙe acikin na juna, wani irin tsorone taji ya kamata, take jikinta ya ɗauki rawa.   

Kallo ɗaya yayi mata ya watsar agadarance yace.

“Wuce mukoma ciki” 

Samun kanta tayi da kasa musa masa, tana gaba yana biye da ita abaya, suna shiga cikin falon ya murzawa ƙofar key, direct ya wuce ɗakinsa ko kallonta baiyiba,  tana ganin wucewarsa cikin ɗaki ta saki wani irin marayan kuka.    Yana shiga cikin ɗakin yasoma rage kayan jikinsa.  Toilet yashiga yayi wanka, fitowa yayi dagashi sai towel dake ɗaure a ƙugunsa.     Sama sama yashafa mai, farin riga da blue ɗin wando yasanya,   ba abun dake tashi ajikinsa sai daddaɗan ƙamshi, buɗe ƙofar ɗakinnasa yayi yafita zuwa falo, ko kallon inda take durƙushe tana kuka baiyi ba, kitchine ya nufa, mintuna ƙalilan yadawo hanunsa ɗauke da wani faranti wanda samansa ke ɗauke da kayan fruit. 

Zama yayi akan ɗaya daga cikin luntsuma luntsuman kujerun falon, haɗe da ɗaura ƙafansa akan rug,  apple ya ɗauka yana gutsura ahankali, jingina bayansa yayi da jikin kujera haɗe da lumshe idanunsa, ahankali yake  tauna apple ɗin dake cikin bakinsa, a rayuwarsa idan yaji kukan mace sosai hankalinsa ke tashi, amma a yau ko ajikinsa, daɗima kukannata keyi masa,  gani yake ita damuwarta ma  mai sauƙice tunda hartana iyayin kuka, shi kuwa shi kaɗai yasan abun da ya keji,  idan da zai samu daman yin kuka to tabbas da yayi, idan da za’ace dashi idan yayi kuka matsalarsa zata yaye to tabbas da shikam yayi kuka irin kukan da ya amsa sunanshi kuka, ba irin nata kukan na shagwaɓa da sakalci ba.  Ahankali sautin kukanta ke tashi acikin falon, ware idanunsa da suka somayin ja yayi haɗe da watsa mata su.     “Keee!!”   yafaɗa murya akausashe.

Ɗago fuskarta da yayi caɓa caɓa da hawaye tayi ta kallesa.  Yanayin yanda taga idanunsa sunyi jajur ne yasa taji gabanta ya faɗi, miƙewa tsaye yayi, haɗe da takowa harzuwa inda take, hanunsa yasanya ya finciko nata hanun, yana janta haka suka fita daga cikin falon, yana zuwa bakin motarsa ya buɗe murfin motar haɗe da cillata ciki da ƙarfi, har saida ta buge goshinta, shiga cikin motar yayi haɗe da kunnata, baijira mai gadi yagama wangale masa gate ɗin bama, ya figi motar da wani irin gudu haɗe da cillata kan titi.  Gudu yaketa shararawa akan titi, bai tsayaba harsai da ya kusan fita daga cikin Kaduna, parking yayi agefen titi.

“Fita!”
yace da ita cikin wata irin murya.

Tsaida kukanta tayi cak, haɗe da ƙura masa ido. 

“Kifitarmin amota nace!!” yanzu kam atsawace yayi maganar.

Jikinta na rawa tasoma kiciniyar buɗe murfin motar.  Yanajin fitanta yayi reverse haɗe da cilla motarsa kan titi, bayan ya buleta da ƙura yabar wajen. 

Tana ganin ɓacewar motarsa ta saki wani irin kuka haɗe da durƙushewa a wajen,  kuka take mai cike da tsananin tausayin kanta,  kuka take nakasancewarta marar gata, kuka take nakasancewarta ƴa mace marar galihu… Sama da mintuna 14 ta kwashe tana durƙushe a wajen,  jifa jifa motoci ke wuceta.

Wata haɗaɗɗiyar motace ta tsaya adai dai gabanta,   da sauri taɗago atunaninta shine yakuma dawowa,    wani saurayi tagani ya sauƙe glass ɗin motar sa, haɗe da sakar mata murmushi.   

“Ƴan mata mai yasameki haka kike kuka?” yatambayeta yana mai ƙarewa ƙirjinta kallo.

Sunkuyar dakanta ƙasa tayi batare da ta tanka masa ba.

Ganin bata kulasa bane yasashi fitowa daga cikin motar, batasan cewa yafito daga motarba sai ganinshi kawai tayi agabanta, har numfashinsu na dukan na juna. Da sauri ta matsa baya tana mai rau rau da idanunta.  Murmushi saurayin yayi mata haɗe da sake matsota, kallonta yake kamar tsohon maye.
  
“Wai tsorona kikeji ne? haba karki bani kunya mana, zo muje nakaiki masauƙina kiyi wanka kinji!” yanayin yanda yayi maganar saida yasa tsikar jikinta ya zuba.   Da sauri tashiga girgiza masa kai tana mai sake ja da baya, shikuwa sai ƙara matsota yake,  hanunta ya cafke haɗe da yunƙurin  jawota jikinsa,   tureshi tasomayi yayinda ruwan hawaye keta ambaliya akan fuskarta. 

“Ka…ƙyale..ni” tafaɗi haka cikin rarrabewar murya cike kuma da tsoro.    Idanunsa ɗaya ya kashe mata haɗe da sanya harshensa ya lashi laɓɓansa, cike da iskanci yace.
“Haba Babe karkimin haka mana, nafa kamu, please ko 30 minute ne kiban, muje mota please!”  yanzukam kuka mai sauti tasanya haɗe da soma turjewa,  hanunsa yakai zai taɓa kafaɗanta,  yaji anyiwa hanunnasa wani irin riƙo, da sauri yajuya don ganin wanda yayi masa katsalandan.    Ido huɗu sukayi, take saurayinnan yaji gabansa yayi wani irin faɗuwa, bakomai ya tsoratashi ba kamar  ganin ƙwayar idanun SOORAJ.    da gudu Ziyada tayi bayan SOORAJ ta ɓuya haɗe da sakin wani marayan kuka.    Irin kallon da SOORAJ keyiwa matashin saurayinne  yasashi sulalewa yashige motarsa da gudun gaske yabar wajen.

Aƙalla sun kusan mintuna 9 ahaka yana tsaye ya rumtse jajayen idanuwansa, yayinda ita kuma ke tsaye abayansa ta saƙala hannayenta akan cikinsa, fuskarta ta ɗaura akan bayansa tana kuka. 

Hanunsa yasa ya zare hanunta daga kan cikinsa,  baice ƙalaba, yakama hanunta suka nufi wajen da motarsa ke fake.  gidan baya ya buɗe ya sanyata aciki, kana yaja motar suka ɗauki hanyar komawa cikin gari.

Tunda suka shiga cikin motar ta kifa kanta acikin cinyoyinta taketa faman rera kukan maraici.  Shikuwa ko ƙala baice mata ba har ya iso gaban wani tafkeken mall.  Fita yayi daga cikin motar yashiga cikin mall ɗin.  Aƙalla ya ɗauki kusan sama da 20 minute acikin mall ɗin, fitowa yayi, yayinda wani yaro ke binsa abaya hannayensa riƙe da ledodi, inda Ziyada ke zaune SOORAJ ya buɗe masa yaron ya zuba ledodin aciki.     Shiga motar yayi suka sake ɗaukan hanya.

Horn biyu kacal yayi maigadi ya wangale masa gate, a parking space yayi parking motar.

   “Biyoni” 
yace da ita ataƙaice batare da ko kallonta yayi ba,  babu musu tafito daga cikin motar, dai dai lokacin Tanimu maigadi ya iso wajen.  
 “A kwai kaya acikin mota kashigomin dasu ciki!”  SOORAJ yafaɗi haka ga maigadi, kana yasa kai ya wuce ɓangarensa Ziyada na biye dashi.

Harsuka ɓace Tanimu maigadi baidaina kallonsuba, tsantsar gulmane ke cinsa,  a iya tsawon rayuwar da sukayi da SOORAJ baitaɓa ganin SOORAJ yashigo da wata mace cikin gidanba, ko auren da yakeyi ma kawo masa matan ake, amma yau abun mamaki gashi da wata ƴar ƙaramar yarinya,  ganin cewar gulma bazata kai mishi bane yasashi kwashe kayan ya bi bayansu SOORAJ ɗin.

Suna shiga cikin falon SOORAJ ya buɗe fridge ya ɗauko ruwa, ɓalle murfin goran yayi, haɗe da kai bakin goran kan nasa bakin,  baicire bakin goran daga kan nasa bakinba  har sai da yashanye ruwan cikin goran tas,  a durstbin  ya jefa roban ruwan haɗe da dawowa tsakiyar falon ya zauna akan kujera.  Dai dai lokacin Tanimu maigadi yashigo, aje ledodin dake hanunsa yayi kana yafice daga cikin falon sumu sumu. 

“Zo!” yace da Ziyada dake tsaye tana ta aikin murza ƴan yatsun hanunta. 

Kanta aƙasa tatako harzuwa inda yake, durƙusawa tayi agabansa haɗe da cewa “Gani” 

“Kinci abinci?” yatambayeta ataƙaice.

Kanta ta girgiza masa alaman “A’a” 

“Tashi ki ɗaukomin ledan da aka kawo miki ɗazu” yafaɗi haka batare daya ɗago kansa ya kalleta ba.

Babu musu taje ta ɗauko masa ledan, dama ledan tananan abakin ƙofa kamar yanda peter ya ajiye tun farko. 

Har ƙasa ta durƙusa haɗe da miƙa masa ledan.   

“Zauna kici  !” yafaɗa ataƙaice tare da tashi yanufi hanyar ɗakinsa. 

Zama tayi akan carpet tare da buɗe ledan take away ɗaya ta ciro haɗe da buɗewa.  Soyayyen chips ne da ketchup sai kifi,  ahankali take tsakuran abincin tanaci.   

Koda yashiga cikin ɗakin zama yayi abakin gado haɗe da sanya duka hannayensa ya dafa kansa.  Maganganun mahaifinsa da yayi masa ɗazune ke dawowa cikin kansa filla filla,  Damuwa da rashin gamsashshiyar nutsuwa sune abun dake damunsa ako da yaushe, haƙiƙa Allah bai tauye masa komaiba nadaga arziki da abubuwan jin daɗi, saidai kuma atawani ɓangaren yana da babban rauni,  akullum da tunanin ciwon dake damunsa yake kwana  yake kuma tashi,    tunanin zuwa gida wajen Ummu ne yaji ya ɗarsu acikin ransa, tashi yayi yashige bathroom, yana tsaye agaban shower ruwa na dukansa amma tunanin yanda zaiyi da rayuwar Ziyada ne yacika zuciyarsa, a yanda ya fahimta shine bata da wani gata, kuma tabbas akwai tawaya acikin rayuwarta, ya fahimci cewa kamar yanda yake cikin ƙunci haka itama take cikin ƙunci, saidai kuma damuwarsu sun banbanta, duk da baisan menene damuwarta ba, amma tabbas yasani matsalarta mai sauƙine akan nasa.

SOORAJ sarkin ado yanzuma sanye yake da  riga da wando farare ƙal ƙal sosai yayi kyau sai tashin ƙamshi yake.

Aƙalla yaɗauki sama da 10 minute yana tsaye abakin ƙofar ɗakin,  duka idanuwansa ya kafa mata, komai nata acikin sanyi take yinshi tundaga kan yanda take tsakalan chips ɗin harzuwa yanda take taunasa acikin bakinta.   Murmushin gefen baki yayi haɗe da girgiza kansa.  Ahankali yashiga takawa harzuwa tsakiyan falon.   

“Kije kiyi wanka, kiɗauki kaya acikin ledanan kisa” yace da ita yana mai ƙoƙarin gyara zaman touch watch ɗin dake saƙale a tsintsiyar hanunsa.
Baisake bi takanta ba yasanya kai yafice  daga cikin falon.   

Tana kammala cin abincin ta koma ɗaki.    Banɗaki tashiga haɗe da cire kayan jikinta, soso da sabulu ta ɗauka haɗe da tsugunnawa aƙasan wani fanfo,  sosai ta durje duk wani datti dake jikinta.   

Tana fitowa a wanka ta ɗauki ledan haɗe da buɗewa.  Wata doguwar riga mai kalan ruwan ƙasa taciro  daga cikin ledan,  ƙurawa rigan ido tayi, irin shape gown ɗinnanne mai kyau, anyiwa gabanta ado da kyawawan duwatsu masu ɗaukar hankali,  zura rigan tayi ajikinta, take rigan tayi mata ɗas ajiki,  zama tayi abakin gado tana mai wasa da yatsun hanunta, har acikin ranta taji daɗin wankan da tayi, harwani bacci bacci takeji.

“Meye kuma kazo kamin? hala duk ɓacin ran da muka gwada maka bai isheka bane dole sai kazo ka gani a aikace ko? katashi ka fitarmin daga falo tunkan nayi maka ba dai dai ba!” Abun da Ummu ke faɗa ga SOORAJ kenan cikin ɓacin rai.

Langwaɓar da kansa gefe yayi cikin yanayi mai ɗauke da rauni yace.  “Dan Allah Ummu kiyi haƙuri, bawai inayin haka ne don ɓacin ranku ba, bayin kaina bane, Ummu banjin zan iya zama da wata mace aduniya, dan Allah Ummu ku ajiye maganan aurena agefe,  ƙaddarata ce haka bazan iya zama da mace ba” 

“Saboda Sarauniyar Aljana ce  ta duniya ta aureka ko? wallahi SOORAJ kayi kaɗan da muzu ba maka idanu katafiyar da rayuwarka yanda kakeso, kaɗaukemu mutanen banza, mata ɗai ɗai har huɗu muna aura ma amma kana sakarsu,  wai shin kodai kana shan giya ne?” Ummu ta tambayesa.

Da sauri SOORAJ ya ɗago kansa ya kalli mahaifiyarsa,  sam baiyi zaton jin haka daga gareta ba.

“Wallahi Ummu…..”

“Katashi kafitarmin daga ɗaki nace, kar kuma kasake zuwarmin gida, zan sanarwa mai gadi kada yasake barinka kashigomin gida!!”  Ummu takatseshi tahanyar faɗan haka a tsawace.

Jikinsa a sanyaye ya miƙe tsaye, har acikin ransa baiso hukuncin da Ummu tayanke masa ba, amma babu yanda ya iya,, sumu sumu haka yafice daga cikin ɗakinnata. 

Jingina bayansa yayi da jikin ƙofar fita daga falon, haɗe da   lumshe idanunsa, yana maijin raɗaɗi acikin ransa…  Cikin zuciyarsa yace. “Kodai na sanar da Ummu ciwon dake damu nane?”

*(Kuyi haƙuri zan ɗauƙi hutu kwana biyu banajin daɗi wallahi, idan nasamu ƙarfi ajikina zan cigaba insha Allah.. Kuyi haƙuri namuku late update)*

    
*VOTE ME ON WATTPAD*
        @fatymasardauna

#hearttouching
#romance
#truelove

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *


The reCAPTCHA verification period has expired. Please reload the page.

Back to top button