Uncategorized

WAYAFI SONTA 8


 p8

 …. Akid’ime zainab ta dafe kuncinta sbd jin wani dummm had’e da ganin stars sun gitta acikin idonta… da gudu zainab tabar gun ….yaja tsaki ya yashigo ciki…Elham!ta kallesa tace uncle shine kadakamun anty zainab?”metayi maka? Be kula elham ba yyi wucewarsa cikin parlourn..

Adedenan Kuma Alh mahamoud (mahaifinsu) yyi sallama da sauri elham ta matsa gunsa had’e da rik’e Masa hannu , tace Abba kaga uncle yadaki anty zainab…tsab acikin kunnan hjy dake nufo parlourn.. da mamaki Abba yace to amaryar dg dawowata za’a matsamun da surutu ,wacece Kuma zainab?”hjy ta iso tanama alh sannu da isowa had’e da Kama hannun elham tace Ina haidar d’in yake?” bangan shiba granny! cewar elham tana janye hannunta sbd hango dadinta (faruq) datayi! Tanufi gunsa.. hjy tabi alh part d’in sa..

 

    Elham ta ahagwabe fuska had’e da fadawa jikin faruq tace daddy kaga uncle yadaki anty zainab,Kuma tanada kirki,Dan ALLAH Daddy muje karakani inrarrasheta har kuka tayi!surutunki yyi yawa ke Ina kika santane?” gdn anty mariya take ko…ok yanzun ga sweets da chacoolate naki dana Miki tsaraba…to daddy Ina na anty zainab?”oh ita ai babbace ko?” Kaga daddy tanada kirki har goyani tayi nayi bacci mukayi Sallah,shine wannan uncle d’in zaidaketa…in uncle yajiki zaimiki bulala bbu ruwana…to daddy yanzun muje anemo anty zainab muga ta Dena kukan , tafad’a tana cin chacoolate nata” Kinga kibari sai anjima yanzun abinci zamuci yunwa nikeji…kafin elham ta yi mgn…k’amshin turaren haidar yacika parlourn… murmushi faruq yyi had’e da tashi yyi hugging na d’an uwansa ,Yana murmushi yace Yaya barka da dawowa! Murmushi shima yyi yace yauwa! ALLAH Yaya kayi duhu taf! Uhum aiyau nadawo ko?”uncle Ina tsarabata? cewar elham tana rik’e ma haidar hannu”yyi murmushi had’e da sab’arta akafadarsa yace sai munje mota… uncle anty zainab tana can tana ku… I’m toking to you kika koma mun maganarta Zan zaneki! Stupid yafad’a fuska atamke had’e da ajiye elham din yanufi dinning area… faruq yadubi elham yace kidaina Kinga har zakuyi fad’a da uncle ko?” Turo baki tayi had’e da ficewa dg parlourn…faruq yqwuce dinning area shima ,yyi serving dinsu suka Fara cin abinci….saiga Alh da hjy sun iso…nan  haidar yagaishe da hjy ta amsa fuska a d’aure,sbd tanason sanin me zainab tayi Masa yadaketa ,tasan elham inbata ganiba ,bazatayi mgn ba!

     amma bara yagama cin abincin zata tambayesa”

 hjy da kanta ta zuzzubawa mijinta komai suna fira yanaci,kasancewar suntashi cikin wayewar Kai dakuma ilimin boko, Kuma dama atare suke cin abinci tun tuni…bayan sun idar  ne! Haidar na goge hannunsa ,yace hjy akwai sauran alkubus d’in nan a ajiyemun anjima naci dukda banacin abinci da dare,amma naji yyi dad’i sosai?” Wani kallo hjy ta Masa had’e da cewa wacce kadaka itace tayi maku alkubus d’in ,saikaje ka tambayeta..sbd kasan innayi ni gaddama yakemun…shiru haidar yyi had’e da daure fuska ,yace amma hjy yarinyar nan batada d’aa tazo ta bangajeni bazata bani hakriba saita wuce! yafad’a cike da bacin rai”inda nasan ita ta girka bazanci ba! Ko yanzun kana iya amayarwa ai! Ya isa Wai wacece ake mgn akantane?” Cewar alh, Faruq yace y’ar aiki ce ko ,amma ai hjy dabaki jajibotaba wlh saikace kin manta abubuwan dasuka faru abaya…hjy ta kallesu one by one..kafin tace to inkungama fadan iyayena Kun bani dama nayi mgn?” Murmushi alh yyi…kafin haidar yasassauta murya yace kiyi hkri hjy dan ALLAH!

To wannan yarinyar ba y’ar aiki bace,tanada gata da galihu da ilimi na zamani dana mahammadiyya,da Kuma  iyaye kamar kowane d’a…saidai ALLAH ya jarabeta…. tasanar dasu labarin zainab had’e da cewa Iyayenta sunbarta gun sule ta zauna na wani lokaci kodan k’uncin dake ranta ya ,yaye… yarinya ce me d’aa da tarbiyya zuwanta gdn nan dg jiya zuwa yau nagane hakan….. sannan haidar karage zafin zuciya Ina gayamaka,Inka Saba mu’a mala acan station da mutane Kuna dukansu itafa macece ,matsayinka na hukuma zata d’aukeka marar adalci…. sannan meta maka harka daketa?” Fuskarsa adaure yasanarmusu…kafin alh d hjy suce inyaganta yabata hakri…. HAKURI fa kukace??” Faruq da haidar suka had’a baki gurin cewa…banza dasu hjy tayi tabi bayan alh daya tashi ,tana cewa inkafi k’arfin bata hakurin Toni zanje nabata….sbd be kamata mamana taji wannan abinba duk da nasan da k’yar  ne zainab ta sanar Mata….

 

 

Zainab kuwa tana dafe da kunci hawaye na zuba tanufi part d’in su

    Kafin ta Ida isa ta tsaya gun wasu flours tazauna ,tayi tagumi ,tana kuka azuciyarta tana jin haushi da tsanar wannan mutum dabashida sanin darajan dan Adam..dan kawai ta bigesa bisa rashin sani zai Mata haka! Insha ALLAH bata koma zuwa part d’in inba hjy ta kirataba,Kuma bazata gayawa kowa dan tasan su anty mariya bazasu ji dad’i ba.

Inkuma makamancin hakan yafaru to saidai tabar musu gdnsu…bazata d’auki wulakanci ,besan ko wacece itaba kawai zai mareta dan tashigo gdnsu ,dg dawowarsa…. lallai mutuwa Mai tonan asiri…. ALLAH ya jik’an yy Umar ,mutuwa ce taja Mata…tashi tsaye tayi ta gyara hijab nata sosai ta rufe Mata fuska…zata juya ta tafi tajiyo muryar elham…

Da sauri elham ta fad’a jikinta tace anty zainab kiyi hkri Dan ALLAH aidama uncle mugune , to nagayawa Abba d granny zasuyi Masa duka.. zaro Ido zainab tayi jin elham tace tasanarwa hjy, hannunta ta Kama tana Mata alamar taje gatanan zuwa….itadai elham bata ganeba sai d’imi taketa yi….dg karshe zainab ta nuna Mata hanya,ita Kuma ta wuce part d’in su…bbu kowa a parlourn da sauri ta shige dakinta ta wanke fuskarta,ta zauna kan katifar….tana tunani…shigowar anty mariya yadawo da ita haiyacinta….anty mariya tayi murmushi tace oh zee kina gun hjy abinki ko?” Kije kici abinci to! Zainab ta girgiza Kai… alamar bazata ciga!

Anty mariya tace nan gabanmu akwai islamiyya asabar da lahadi,danike zuwa  baffanki yace zai sakaki ciki… zainab tayi Mata alamar to…kafin anty mariya tace gobe insha ALLAH zamuje asibitin mugani sudubaki….. zainab tayi Mata alamar to…..

 

Haidar kuwa tabbas maganganun hjy sunyi tasiri sosai azuciyarsa ! Sai yanzun yaga rashin adalcinsa na marinta!amatsayinsa na hukuma,zata iya kiransa azzalimi komarar adalci..saidai dayake miskilane be nuna hakan afuskaba. amma gsky shi bazai iya bata hakuri ba ,danbbu wacce yataba yiwa laifi balle yabata hakuri Kuma bazai Fara akantaba!yasandai astation in ankawo k’ara Yana shiga maganar yasansanta tsakanin masu rigimar yabasu hakuri…da wannan hujjar yawatsar da maganar zainab…hjy kuwa da dare da kanta taje part d’in su anty mariya tasami zainab ad’akinta tana karatun kur’ani,hjy ta zaunah…,byn ta idar hjy tabata hakuri akan abinda yafaru tsakanin ta da haidar, had’e da mik’a Mata ledar hannunta!

Zainab ta yiwa hjy alamar bbu komai yyi hakan acikin rashin sani, tana nuna Mata  tana murmushi had’e da yiwa hjy godiya….bayan fitar hjy zainab ta duba,taga kayane areviant gownt masu kyau kala 5 da mayafansu sai kayan kwalliya da turare guda2″ tashi tayi taje tanunawa anty mariya! Cike da jin dad’i anty mariya ke yaba kayan had’e da cewa da safe intashiga zata yiwa hjy godiya….

 

 

******************

Yau kimanin satin zainab biyu a Abuja kuma Masha ALLAH gsky bbu laifi tana ganin canji sosai arayuwarta ,sbd hjy d elham najanta ajiki ,Kuma tanasakewa dasu ,hakan na rage Mata damuwa sosai,gefe guda satin da yawuce tafara zuwa islamiyya dukda tayi sauka amma ance ilimi kogine… sannan sunje asibiti an azata kan magani dukda ancazesu kud’i da yawa…tunda haidar yamareta batakoma yadda sun haduba duk alokacin bata kalli fuskarsa ba. tasansadai a photo shida faruq! Duk lokacin datasan suna ciki to hjy ta Aiko akirata bata zuwa ,shikansa Mai gdn sau daya suka tab’a gaisawa dashi Kuma Bata kallesa ba! Hjy kuwa ta yadda da zainab sosai sbd ta lura yarinya ce da abin duniya baya gabanta batada zalama ko had’ama sau dayawa zatace Mata ta d’ibi kaza da kaza,amma bazata d’ibaba sai inbata akayi shima wani lokacin zatace bazata ciba…hakan yakarasa hjy jin zainab ta burgeta…

 

    Sanye take da jallabiya maroon colour,tayi rolly da mayafin”fuskarta bbu kwalliya rabon datayi make up harta manta, dukda haka tayi haske tayi kyau had’e da yin frash. ..ta nufi part d’in hjy sbd hjy t Kira anty mariya awaya cewa zainab ta je Tana kiranta…

Murda’k’ofar tayi ,taji gabanta yafad’i sakamakon jin motsin elham da daddynta…. yeeeeee daddy! gama anty zainab d’in nan. da gudu elham ta fad’a jikinta! Zainab ta rungume ta had’e da d’agata sama tana dariya har fararen hakoranta suka bayyana d wushiryarta…. faruq yakafesu da Ido ,Yana mamakin yadda elham tayi saurin sabawa da yarinyar,Kuma yasan elham batasan zuwa gun Wanda bata saniba… elham tace anty zainab Kinga daddy nah ! Shima yanada kirki yafi uncle kirki,kidinga gaidashi inbakinki ya warke zai ruk’a siyomiki kayan dad’i… zainab cike da kosawa da surutun elham narashin kan gado ta rabata zata wuce dan shiga parlourn hjy.elham tace bazaki gaida daddy naba,kobakinki be warkeba??” Zainab ta saki kallon faruq caraf suka had’a ido taji faduwar gaba”dauke Kai tayi fuska bbu walwala sbd taga Yana wani Shan k’amshi…tad’aga ma elham Kai tawuce kawai… elham ta kalli faruq tace daddy kaga anty zainab tayi tafiyar ta batagoyaniba! Tabe baki yyi had’e da cewa kuka sani…bin zainab elham tayi… faruq ya lumshe Ido Yana girgiza k’afa…. zainab kuwa byn sun gaisa da hjy ,tazauna tana yiwa hjy kitso…har elham ta shigo

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button