MUTUM DA DUNIYARSA 27 – 28

*_????MUTUM DA DUNIYARSA….!!????_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce????????_*
*_[27➖28]_*
…………..Babu dad’ewa Aunty Ruk’ayya ta iso asibitin, bisa kwatancen da Aliyu
yay Mata ta iso d’akin.
Har yanzu yana zaune kusada Maimuna dake barci, hannunsu Na sark’e dana juna har yanzun, shigowar aunty Ruk’ayya da sallama ya sakashi zame hannunsa a hankaki dukdama tarigada ta gansu.
Hannu ya mik’a ya kamo hannun yaronta Najib fuskarsa d’auke da murmushi. “Najibullah kaine ka k’ara girma haka?”.
Najib dako magana bai gama iyawaba ya lafe a jikinsa, yayinda Aunty Ruk’ayya ta zauna saman kujera tana dariyar maganarsa.
Yaranta Sadiya da Naja’atu suka shigo da sallama hannunsu d’auke da ledoji.
“A’a Aunty kice harda y’ammatana kike tafe?”.
Sadiya da Naja’atu suka durkusa suna gaishesshi da tambayar ya Mai jiki?, fuskarsu washe da murmushi, shima cikin sakin fuska ya amsa yana tambayarsu makaranta.
Suka had’a baki wajen fad’in Alhmdllh Kawu.
“Naga gida gaba d’aya amma banga Ameer ba?”.
“Kawu ai yana tare da Abba sunje anguwa”. ‘Naja’atu tai maganar cikeda ladabi irin Na y’ay’an da suka samu tarbiyya’.
Aliyu yace, “ALLAH Sarki, to ALLAH ya dawo dasu lafiya”.
Da amin suka amsa, kafin ya maida hankalinsa ga aunty Ruk’ayya suka gaisa tana tambayarsa Mai jiki.
“Aliyu maimuna dukta rame fa, sai haske data k’ara, kodai munsamu k’aruwane?”.
Murmushi kawai yayi, kafin yabata amsa doctor yashigo da sallama, bayan yabama Aliyu hannu sunyi musabaha ya mik’a masa takardar result d’in yana masa murnar cikin dake jikin Maimuna Na watanni biyu da wasu kwanaki.
Tuni murna ta kacame tsakanin Aliyu da aunty Ruk’ayya dasu Sadiya, wasu kwallan farin ciki suka taruma Aliyu a gefen ido Na dad’i, Aunty Ruk’ayya kam ai saida suka zubo a kumatunta, koba komai samun lafiyar Aliyu ta tabbata, dama tana tunanin kar aita tsogumi akan wannan auren nasa dazai k’ara, Dama taji anfara k’ananun magana a gidansu akan Maimuna, amma yanzukam hankalinta kwance.
★★★★
Lokacin Salla na gabatowa Aliyu yatafi gida yabar auty Ruk’ayya da aunty Siyama datazo daga baya.
Bai koma asibitinba sai kusan tara Na dare, danma yau bai xauna karatuba, yanema uziri akan Mai d’akinsa batada lafiya.
Mutane sunta mata addu’a da fatan samun lafiya.
Lokacin daya dawo ya iske harda malam da matan gidansu suma sunzo duba Maimunatu data farka tuni, baiyi zaton ganin su malam ba, dukda dai shine yakira ya sanar masa batada lafiya, amma bai fad’i maganar cikinba saida sukazo sukeji a bakin su Aunty Siyama.
Maimuna nata duk’ar dakai tak’i yarda su had’a ido da kowa, koda Aliyu ya dawoma kasa kallonsa tayi, saicin abincin da aunty siyama takawo take a hankali. Duk yanda yaso su had’a ido tak’i bashi damar hakan, murmushi yayi yana k’arajin k’aunarta harcikin ransa. Yanason Maimunatu saboda k’yawawan halayenta Wanda Ada kafin aurensu baiyi zaton tana dasuba. Shiyyasa babu k’yau yakema mutum hukunci akan abinda baka tabbatarba, kakuma k’yautata zato ga kowa shine nagarta da cikar kimar d’an Adam.
Basu bar asibitinba sai kusan sha d’aya Na dare. Kowa gidansa ya nufa, shima ya d’auki matarsa sukai gida bayan yad’an Mata sayayya a hanya.
Yanata janta da hira amma takasa amsashi da k’yau saboda barcin dake cike da idonta.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Tunda Abba yabar kasuwa babu abinda ke caccakar zuciyarsa sai maganarsa da Alhaji Garba, sai k’ullawa yake da kwancewa, yana hangen k’urar da zata iya tasowa tsakaninsa da Umma da Uncle yahya, gefe kuma yana kallon d’unbin kud’in da Alhaji garba hace ya barmasa inhar Jiddah ta dawo garesa, yasan ko k’asa da sama zata had’e bashida kud’in biyan Alhaji garba, koda kuwa za’a saida gidansane da kayan kasuwarsa da komai daya malakka, dan kud’in daya ranta a banki a shekarun baya dasune ya ida ginin gidansa, ya kuma k’ara jari sosai a kasuwa, suka kuma hau kan sauran kud’in shida Hajia Hindu da y’ay’ansa sunaci hankalinsu kwance, da kud’in kasuwa yad’an fara bama banki miliyan goma, daga baya kuma saiya daina biya, lokacin da suka ajiye shida banki na cika suka nemi kud’insu, amma sai suka iske babu wani abun arzik’i a k’asa sai kayan kasuwarsa, kwanaki goma suka bashi ya maido kud’in kokuma komaima yafaru shi ya sani, wannan ne ya tashi hankalinsa sosai har hajia Hindu ta fahimta, tashin farko tabashi shawarar Neman bashi wajen Alhaji garba. Baiwani dogon tunaninaba ya amince saboda mafita yake nema a lokacin, da taimakon Hindu hajia deluwa ta lalla6a musu Alhaji garba yabada kud’in, sai dai a lokacin shi Alhaji garba saiya 6oyema Hajia deluwa adadin kud’in da Abba ya nema saboda wani dalilinsa, cemata yayi kawai miliyan gomane. Shikuma Abba maimakon dayazo kar6ar bashi ya kar6i miliyan arba’in tunda yabama banki miliyan goma tuni, saiya kar6i hamsin d’in, ya biya banki arba’i ya ajiye goma a hannunsa da zummar ya k’ara jari danya samu ya gama biyan Alhaji garba da wuri. Bayan faruwar haka babu jimawa Alhaji garba yaga Jiddah, d’uwawunsa Na rawa yace yabarma Abba rabin kud’in inhar yabashi auren Jiddah, yakuma lamunce masa ahankali ya biyasa sauran rabin. To dagabaya da auren Jiddah da Alhaji ya rabu sai Alhaji garba ya aikoma Abba cewa ya janye k’yautar dayaymasa ta Rabin kud’i, a yanzukam yanemi miliyan hamsin d’insa ya basa cif. To yanzu kuma Alhaji garba yadawo ruwa saboda ganin Jiddah daya k’arayi ya rud’e, a wannan karonma gaba d’aya ya barma Abba kud’in inhar an maido masa Jiddah, idan ank’i kuma abashi kud’insa da wuri. kunga kuwa dolene Abba yashiga cakwakiyar tunanin son wargaza auren Jiddah da malam Aliyu yakuma k’ullawa da Alhaji garba a Karo Na biyu.
Tofa masu karatu, Yaya wannan cakwakiya zata kasance? Minene makomar Abba zakari idan baisamu cikar burinsaba?.
Nidai bilyn Ku nace yasaka yan MASARAUTAR BILYN ABDULL DA MUTUM DA DUNIYARSA GROUPS a kasuwa yabiya bashinsa hankali kwance????????????????⛹♀⛹♀⛹♀⛹♀.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Baki hajia deluwa ta ta6e saboda sauraren zancen Alhaji garba da takeyi akan Jiddah. “Wai kana nufin da gaske itace kenan Alhaji?”.
“Minene ribata idan namiki k’arya Yahanasu, to yanzuma haka maganar da nake miki mun k’ark’are magana da mahaifinta zai dawomin da ita”.
A zabure hajia deluwa tace, “Ban gane zai dawo maka da itaba, dama ba Saki uku kai mataba?”.
“A’a k’arya haramun, wlhy Saki biyune, da bama tagama iddah ba datun yau zance na maidata a gabansa, to amma babu komai, nanma da sati d’aya za’a sake d’aura mana aure”.
Wata makirar dariya Mai had’e da shewa hajia deluwa tayi, kafin ta callara bud’a akan Alhaji garba tana fad’in ALLAH ya nuna mana ango”.
Da wani kallo tuhuma ya bita harta bar falon amma baice komaiba.
Hajia Deluwa na shiga d’aki wayarta ta d’auka ta dokama malam Na marwa Kira, yana d’agawa ko gaisuwa bata tsaya sunyiba tafara magana, “Malam Alhaji zai kuma maido shegiyar yarinyarnan, wannan Karon sonake ka haukata min ita kawai tabi duniya”.
Numfashi Malam Na marwa ya sauke, kafin yace, “Hajia hakan bazata yuwuba gaskiya, dan a yanzu haka zancen da nake miki wandama yake kanta zai iya zame miki babban Matsala, dan aljanin dana had’ata dashi yana shan wahala a hajenta, Sam yarinyar bata sakaci da ibadar ALLAH, danma aljanin yanada nacine, amma wlhy yafara nunamin gazawarsa, kibi tawata hanyar kawai kidai dakatar da auren inaga zaifi”.
Tsaki taja tana yanke wayar, “Dak’ik’i kawai, ashema bakomai zaka iyayiminba”. (Hummm)
Maida akalar kiranta tayi ga hajia Hindu bayan sun gaisa tace, “Hindu wani aikin zakimin akan Y’ar mijinki, amma kafin sannan idan kinada wani malami kimin rakiya gunsa koki bani lambarsa”.
“To Hajia kinsanfa ni indai harkar malamai ce ba’a yinta Dani, akullum bakina shike kwatata a hannun miji da kishiya, dan shine malamina shine bokana, amma bazan bama k’aton banza kud’ina yaci ya had’omin k’aryaba”.
“Kinga ya isa haka, idan bak’ya wannan ai saikimin aiki da bakin naki, sonake kiyi duk yanda zakiyi kar auren Y’ar mijinki yakuma k’ulluwa da mijina, idan har kikayi haka Zan baki miliyan d’aya”.
A rikice hajia Hindu tace, “Miliyan d’aya fa? Akan hana aure kawai? To kibani nanda kwana uku kacal zakisha mamaki”.
“Nabaki, amma karya wuce haka”.
Gaba d’aya Hajia Hindu ta rikice, batayi sanyaba wajen nufar d’akin Abba, tashin hankalin data iskeshi a ciki naneman mafitar k’ulla auren Jiddah da alhaji garba ne ya sakata samun damar bugar cikinsa, nanko yashiga Mata bayani dalla-dalla akan k’udirinsa Na sake aurama Jiddah Alhaji garba.
Tana gamajin komai tai saving d’in recording d’in datayi.
Abba dai baisan anayiba????.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Washe Gari Abba Na fita kasuwa hajia Hindu tai shiri tatafi gidan uncle yahya, abinda batayi a rayuwarta, dan inba Maman Sadiq ce ta haihuba bazaka ta6a ganinta a gidanba, shima barka take zuwa, minti talatin kuma yayi yawa zata baro gidan.
Maman Sadiq ma tayi mamakin zuwan Nata, tadai kawo Mata ruwa sannan suka gaisa. Suna cikin gaisawa Uncle yahya dayay shirin kasuwa ya fito, shikansa yayi mamakin ganin Hajia Hindu, amma saiya zauna suka gaisa danyaji dami tazo. Batawani ja musu ajiba tabashi recording d’in yaji. Sosai mamakin Abba da d’unbin wautarsa ta Kama Uncle yahya amma sai baice komaiba ya mik’ama hajia Hindu wayar yana fad’in “ALLAH ya k’yauta” kawai. Dan itama bata isa ya tattauna komai da itaba akan lamarin. Sallama ma yaymusu ya fita abinsa.