BAKAR INUWA 25

Episode 25
……….8:15pm
Gagarumar dinner ɗin da su Alhaji yaro glass da Shugaban ƙasa mai sauka suka shiryama su Ramadhan ɗin ta fara gudana. Ƴaƴan manya ne da manyan ƙasar kansu kawai kake gani a wajen. Amarya da ango sunsha ƙyau har sun gaji. Dan zaman bayyana ƙawatuwar shigarsu da docration na wajen ma ɓata lokacine. Anci ansha daga kayan daɗi kamar babu gobe. Yayinda ango ya hana amarya tashi daga inda suke zaune ko sau ɗaya. Dan haka wanda sukai musu liƙi ma anan suka iskesu wajen zamansu sukayi. Cake ma nan aka kawo musu suka yanka a zaunen basu tashi ba. Humm sabon salo kenan wai rawa agaɓar gacci. Dan kuwa ƴan jarida da masu jiran ayi suce tuni sun sami abin faɗa.
Sai faman cece kuce suke na cewar wai mi Ramadhan ɗin ke ɓoyewane da ya hana a ga matar tasa yanda ya kamata. Dan kuwa duk da kwalliyar da taci yau fuskarta sanye take da facemask, kuma shine da kansa ya sanya mata sanda suke tahowa a mota. Ita kanta ta kasa fahimtar minene dalilinsa na son ɓoye mata fuska a duk sanda suka haɗu? Shin BABU SO! MIYA KAWO KISHI?! (Wannan littafi na nan tafe a gareku ba babu so miya kawo kishi? Insha ALLAH????????????). Bata da mai bata amsa dan haka ta haɗiye a ranta.
Ƙarfe sha biyu dai-dai aka tashi, bayan mawaƙa kala-kala sun baje basirarsu tunda daga kan na hausa har zuwa na turanci. Hakama masu wasan barkwanci. Kamar sanda suka taho yanzu ma sun koma gidane bisa tsaron na musamman daga jami’ai. Kamar kuma ko yaushe har suka iso ɗin ko kallo bai haɗasu ba ita da shi balle magana. Yay mata rakkiya har ɗakin Anne da basu riga sun iso ba su yay wucewarsa nasa part ɗin ya barta da sakin numfarfashin data tara a ƙirji. Duk da ko sau ɗaya bai wani taɓata ba, dan ko hannunta bai riƙeba a wajen dinner ɗin ƙamshin turarensu ya cakuɗe dana juna har baka iya banbance wanda take yi saboda ƙarfin nasa, ta kwanta lamo a gefen gadon Anne batare data iya cire ko zobe a yatsanta ba. Batasan mi zatai tunani ba a yanzu, girman mijin nata a mulki, ko auren nasu da baida alƙibilar kwatantawa?. Rabuwa da iyayenta ko shiga BAƘAR INUWAR da su suke hasashen Ni’imtacciyar inuwa ce a gareta?. Manufar su aunty Hannah a kan kashe su, ko tsananin ƙiyayya da ƙyamar da take hange a idon uwar mijinta da sai a yau wajen dinner tasan matsayinta na mahaifiya ga Ramadhan ɗin?. “Ya ALLAH kaji tausayina. Nayi tawassali da sunayenka ƙyawawa masu tsarki. Da kai na dogara dan bani da kowa sai kai ɗin tun farkon fari. ALLAH ka ƙyautata ni’imarka garemu a ƙarƙashin wannan BAƘAR INUWA da kowa kema kallon Ni’imtacciyar inuwa a garemu.”
Hawaye masu zafi suka gangaro daga cikin idanunta zuwa kumatunta har saman facemask ɗin fuskarta da ta gagara cire koda shi ne. A wannan yanayin gidan ya fara ɗaukar hayaniyar mutane alamar an dawo dasu gida suma. Dole ta miƙe ta fara zare sarƙa da tarkacen jikinta gudun kar Anne ta zargi wani abu. Duk da kuwa a ranta yanzu hankalinta yafi karkata da kwanciya akan ta tunkari Anne da batun da taji a bakin su Aunty Hannah. Sai dai kuma bata son tozarta yayar mahaifiyar tata dan koba komai bata da kamarsu a duniya, tunda gashi har ana aibantata da halayensu da suka aikata tunkan haihuwarta.
★★★
WASHE GARI aka gudanar da rantauwa ga shugaban ƙasa da gwamnoni. Kum harda Raudha shugaban ƙasa Ramadhan yaje wajen. Sai dai tana cikin dogon farin hijjab da facemask yau ma. Abin ya sake burge jama’a musamman talakawa. Da kuwa idan akai dubi da yanda mafi yawan matan gwamnonin suka cakire cikin shiga ta rashin mutunci da kece raini a yau ɗin. Ga gwalagwalai dake ƙyalli da walwali a jikinsu tako ina. Hatta da Hajiya Fanta da aunty Hannah matan vice president shigar tasu ba’a magana. Sai dai a kallo guda zaka gane ran Hajiya Fanta a ɓace yake saboda kasancewar aunty Hannah a wajen bayan mijin nasu yace mata da ita kaɗai zaije banda Hannah. Dan tunda aka maida aurensa da aunty Hannah suke tafka rigima har yanzu kuma babu daɗi a tsakaninsu, tace sai ya saki aunty Hannah ɗin. Shiko ya tabbatar mata hakan bamai yuwuwa bane dan Hannah nada muhimmanci a tafiyarsa ta yanzun.
Ga ƴan siyasa kuwa sai suka fara takale-takale da zungure-zunguren batun saka facemask da amaryar ta shugaban ƙasa ke yawan yi, dan tunda ya far bayyanata wa duniya ranar zaɓe ba’a taɓa ganin real face nata ba sai da facemask. To yau ma al’amarin yaci uban na da, dan farin siririn gilashi da Raudha ta saka a idonta saboda kumburin da ya ɗanyi na kuka da rashin isashen barci ya ƙara mata wani ƙyau da burge mai kallo. Ga facemask da ya saka ba’a ganin ainahin face nata kuma. Sai haka ya zam ba’a ganin komai nata a waje sai tafukan hanunta kasancewar hijjab ɗin data saka mai hannu ne.
Uban gayyar shima fararen kayane a jikinsa na wani haɗaɗɗen boyal ɗinkin babbar riga. Ya kawo hularsa tangaran data fita a fice ya murza. Bayan kammala Rantsuwa suka wuce wajen bikin da aka shirya gudun mawa da ga Mai-martaba. Ƙarfe biyu aka tashi aka dawo da Raudha kawai gida, shugaban ƙasa Ramadhan kuwa gidan gwamnati aka tafi masa rakkiya. Bayan idar da sallar la’asar aka gabatar da walima da addu’oi daga manyan malamai har zuwa ƙarfe shida na yamma. Daga haka taro ya tashi lafiya kuma zuwa anjima za’aima amarya rakkiya gidan gwamnati insha ALLAH tunda angonta ya tsufa acan.
★★★_______★★★
An yima amrya shiri na musamman domin miƙata gidan gwamnati da zasu zauna insha ALLAH. Ba wasu mutane masu yawa bane zasuyi rakiyar, dan haka da wuri aka kaita ga gimbiya Su’adah da su Adda Asmah da sauran matan Pa su Hajiya Mufida.
Duk da a lulluɓe fuskar Raudha take da golden color na veil hakan bai hana gimbiya Su’adah jefa mata kallon tsana ba. Da ƙyar ta iya dauriyar cewar “ALLAH ya bada zaman lafiya”. Daga haka ta tsuke bakinta. Sai su Addah Asmah ɗinne keta karaɗin kwarara addu’oi ga amaryar da ango. Abinda gimbiya Su’adah tayi yasa mutane da yawa fara tsarguwa, dan kuwa basuji daɗin yanda ta sallami surukar tata matar ɗanta na farko ba kuma namiji tallin tal.
Raudha da dai ba sanin mi ake ciki tai ba. Dan kanta a duƙe kuma a lulluɓe. Tunda ba wani farin sani tai musu ba bata iya tantance muryoyin da sukai magana ba. Daga part ɗin Gimbiya Su’adah part ɗin Hajiya Shuwa aka nufa da ita. Itako ta mata ƙyaƙyƙyawar addu’a harda ƙyauta da babu wanda yasan minene a cikin dan an riga anyi packaging nashi da leda mai ƙyalli alamar gift. Hakama Hajiya Mufida tarba ta mutuntawa taima amaryar da doguwar addu’ar zama lafiya harda fatan nan da baɗi a sake taron suna. Itama dai tayima amarya ƙyautar cheque na kuɗi da babu wanda yasan adadi tunda a ninke takardar take. Sai wani ɗan box a cikin ƙaramar bag.
Bisa jagorancin Hajiya Mufida aka kai Raudha ga Pa. Inda shima yay masu doguwar addu’a da nasiha ga Raudha tare da ƙyautar key na mota galleliya. Sai sashen su Yafendo inda can ɗin ma tasha addu’oi da kyauta ga dangin su Ramadhan ɗin. Daga haka aka sake maidota wajen Bappi da Anne suka sake musu addu’oi, Bappi ma yay mata ƙyauta a dunƙule wadda babu wanda yasan minene. Hakama Anne, koda yake gara na Anne da alama harda kayan turare dan ƙamshinsu tuni ya addabi hancin kowa. Sisters turarurrukan AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE 08067558902 daban suke dana saura. Zaka tabbatar da haka ne kawai yayinda ka mallaki naka. Ba turare kawai take saidawa ba. Harda kayan gyara amarya galla-galla na musamman da sai an gwada akan san na ƙwarai. Sirrinsu daban ne, idan nace na daban, ina nufin na daban dana saura????????????????.