KWARATA 45

???? —— 45
Tsaye yayi yana kallona , ni kuma da gudu nayi cikin gida har na kusa faɗuwa , a mamakince Dikko yabi Sultana da kallo a ranshi yana cewa ko lafiya ?
Mota ya koma ya gyara parking , yayi zamanshi ciki bai fito ba ranshi ɗauke da tunani daban ² , ga zafin mutuwar matarshi ga ciwon auren da za’a ɗaura mishi wanda rasuwar Sadiya yasa aka ɗageshi , ga iyayenshi sam² sun rufe idanuwansu akan aurenshi da Sultana…
Ya ɗan rame har yayi duhu saboda damuwa da tunani , a gajiye ya fito daga cikin motar ya nufi gidanshi , kafin ya ida shiga Baban Sultana ya faka tashi motar daga can gefe dan kar yayiwa Dikko laifi…
Dikko yana ganinshi ya dawo suka gaisa , bayan gaisuwa yace am dama ina san ganin wannan yarinyar ne , cikin damuwa Baba yace ta sake janka ne ? Fuska dai a murtuke babu fara’a yace a , a zanyi magana da ita ne kawai !
Baba yace tou Allah dai yasa lafiya , a ɗan rashin jin daɗi Dikko yace ba komai fa , shi baya so yayi ta nanata magana kuma anajinsa amma a kasa fahimta ,
Cikin gida Baba ya nufo zuciyarshi cike da damuwa , tunda ya shigo gida yake kwalamin kira kamar ranshi zai fita daga jin yanayin maganarshi babu daɗi a zuciyarshi ,
Da gudu na fito ina tambayar Baba lafiya , cikin faɗa yace me ya sake haɗaki shiga sabgar yaron can mara mutunci kuma ? Ɗan iskan yaro da baya ganin kowa da mutunci , ya raina arziƙin duk wani mai farin gashi dake doron ƙasar nan , fitinanne yaro dako bakin duniya baya tsoro ga rashin mutunci da masifa kamar kishiyar ɓarauniya…
A ruɗe nace ni babu komai , dakamin tsawa Baba yayi yana cewa babu komai inji waye ? Gashi can ya kafe mota ƙofar gida yana ɓacin rai duk abinda nace bana so sai kinyi Mamana kina so dai ki samin ɓacin rai idan na mutu kin huta ,
Hannuwa na duka biyu na ɗaga alamar bada haƙuri nace a , a Babana kayi haƙuri don Allah , dan bana so naga Baba yana fushi akan komai bare kuma ni daya ɗauki soyayyar duniya ya ɗoramin ,
Sassauta murya yayi cikin tausayi yace tou kije ki bashi haƙuri nidai bana so kina jawoshi faɗa uwar masu gida , nace tou Baba , a tsorace na fita ƙofar gida gabana sai faɗuwa yakeyi ,
Dikko yana tsaye ya jingina da mota , da gudu na isa inda yake na riƙe hannayen shi , na irin gani karka kasheni , kallona yayi cikin sigar so da ƙauna yace tou kin kama min hannaye ai gara ki riƙeni gaba ɗayana tunda abin har yakai ga riƙe hannu ,
Sakin hannuwan nashi nayi na ɗaga kaina na kallo cikin kwayar idonshi , wani irin kallo yayi min kwayar idonshi tana motsawa a hankali wanda idan baka iya saka ido ba baka gane motsi takeyi ,
Hmmm me yasa kika gudu da kika ganni ? Ko na zama dodo ? Bansan abinda yasa bana iya ma Dikko ƙarya ba amma da nauhi wannan kalma mai muni ta fito daga bakina ,
Tou tunda baki da abun faɗa ni zan faɗa nawa , shiru nayi ina saurarenshi , yace zanyi tafiya kuma bana tunanin idan na tafi zan dawo yanzu , bana so na shiga haƙƙinki da yawa dan ina baƙin ciki kiyi damuwa a rayuwa , ina so miki farin ciki bana so kiyi kuka haka kuma bana so ki kasance cikin damuwa ko ƙunci ,
Na baki daga yau zuwa jibi kwana biyu kenan ko ? Ya tambayeni , ina kallonshi banyi magana ba , yace tou kije ki natsu kiyi sharawa da zuciyarki shin kina so na ko bakya so na ?
Cikin yarinta nace ni bama sai nayi shawara ba gaskiya bana sanka , kallona yayi sosai yace karkiyi ƙarya An mata zakiyi nadamar hakan wata rana , nace wai ni ? Na ƙarasa maganar ina masa kallon rainin wayau nace Allah ya sawaƙemin ai baka cikin tsarin mazan da nake so , cikin damuwa yace .
Kina da matsaloli fa daban ² An mata , saurara samar da farin ciki a domin ɓatawa wani ba dai² bane , haka zafin murmushi a yayin da wani yake baƙin ciki da takaici hmm baya da amfani , karki damu kawai cewa zakiyi ina sanka , shi kenan fa babu wani wahala , uhum kana ba kanka wahala kaji , ince ina sanka ? Allah ya sawaƙemin ,
Murmushi Dikko yayi maicin rai yace tou ni kuma na san a cikin kwanaki biyu da wannan taurarin idanuwan naki zaki zamo masoyiyata babu jayayya , zaki zo ki rumgumeni , numfashinki zai shiga kwalwata, zaki kalli idanuwana , ina sanka , idan har baki faɗa kina so na ba , shiru yayi yana kallon fuskata , zuwa wani lokaci yace sai kin faɗa , yana faɗin haka yayi tafiyarshi ya barni a wurin…
Cike da damuwa na koma gida yayin da zuciyata ke shawarta ta ince ina san Dikko wata zuciyar tace karki sake ki faɗa ko zaki mutu ki barshi kawai kuje a haka , kina mace kice kina san namiji haba ai kinci ƙasa ,
Lokacin da kwana biyu ya cika zuciyata ta gama tabbatarmin da bata san Dikko , dan haka kuma na yanke shawarar sanar dashi bana sansa yayi haƙuri ,
Da daddare bayan yazo ya aiko aka kirani dan har yanzu ban kunna wayar ba tunda na kashe ta ban sake buɗewa ba , bayan na fita muka gaisa dashi , bayan gaisuwa yace ina saurarenki , nace gaskiya ansar dana baka tun farko itace har yanzu ,
Shiru Dikko yayi , bayan wani lokaci yace , wannan rana ta kasance min ranar juyayi ne , bana fatan wannan ranar ta sake zomin , ranar ƙarshe kenan banda wani ƙwarin guiwa , An mata ce kaɗai abin alfaharina , umm abinda bana so ya kasance duk lokacin dana runtse idanuwana nakan iya ganin kyakkyawar fuskarki , bansan mace ba sai a kanki idan har na taɓa san wata mace a rayuwata to kece An mata ,
Zan tafi idan har naci gaba da ganinki to zan ɓata miki , kiyi haƙuri bazan sake kiranki ba , haka ma zuwa ba zaki sake ganina ba An mata , kin daɗe kina ƙonani inajin kamar na rasa wani abu , me zanyi ? Bazan iya koda dariyar ƙarya ba , jawoni yayi ya rumgumeni duƙowa yayi ya kwantar da kanshi saman kafaɗa ta , cikin wata irin murya mai tsayawa a zuciya yace sai wata rana , ki yafemin don Allah karki riƙeni zan fita daga rayuwarki dan ina so kiyi farin ciki , zan tafi ki huta koda kuwa ni zan shiga halin damuwa ,
Bayan wani lokaci ya ɗago ya kalleni , cikin kallonshi mai ɗaukar hankali yaɗan ɗauki lokaci yana kallona sannan yazo dai² bakina lumfashin shi yana fitowa saman fuskata , gashin gemunshi yana shafar dai² saitin bakina , lokaci guda jikina ya canja tsikar jikina ta tashi ban taɓa jin irin wannan yanayi ba , bafa haɗa bakinmu yayi ba , daga waje ya sunbace ni wani abu naji ya shiga jikina da gudu saida ya gama zagayawa ya dawo zuciyata ya shiga da ƙarfi , ajiyar zuciya na sauke yanajin nayi ajiyar zuciya ya sakeni da sauri daga jikinshi yaɗan turani baya yace ki tsaya da kyau karki faɗi , zan bada saƙo Umar ya kawo miki kafin in wuce ,
Kasa magana nayi nabi shi da kallo da sauri ya shiga mota ya bar ƙofar gidanmu da gudu , har ya fita daga anguwarmu ina tsaye a wurin daya barni , yana ɓacewa na kyalkyale da dariya , na zabgaga wani irin ihu , daga cikin gidanmu Zainab ta fito da gudu tana tambayata lafiya ?
Sai dire² nakeyi kamar anyi ma doki allura ƙarfi , Zainab tace wai miye yake faruwa haka ? Goge hawaye nayi nace har yanzu na kasa yadda da wannan , Zainab tace miye ne kika kasa yadda dashi ? Nace masoyina ya faɗamin dukkan na kasunsa , shi da yace zan rungumesa sannan na faɗa masa cewa ina sanka DK ,
Zainab tace waye DK murmushi nayi nace baki sansa ba , Zainab tace tou ki faɗa masa kina sansa mana , nace ke jinan ya nunamin yatsansa yayin da yake ƙalubalanta ta cewa a cikin wasu kwanaki zance ina sansa , murmushi nayi tare da rufe idona , nace kamar dai yadda yace naji ina sansa , ƙara ɗaga murya nayi ina sanka mutumi na , ina sanka , Zainab tace to me yasa baki faɗa a gabansa ba ? A , a , a , a , idan na faɗa masa tou zaiyi ta jamin ƙafane har abada , Zainab tace zakiyi duk abinda kike so amma kuma idan kika makara a soyayyarshi fa ? Nace sam ² ki rabu dashi kawai yayi kuka na wannan daren nasan bazaiyi zuciya ba da safe zai sake zuwa , ni kuma yana zuwa zance barka dai DK idan ba tare dakai ba ina ne zanje …..?
Cike da farin ciki na shiga gida , Zainab ta rufomin baya , alwallah nayi na shige cikin ɗakina ina farin ciki ,
Dikko kuwa yana isa gidanshi wanka yayi , bayan ya shirya ya ɗan faffaka abu mai mahimmanci ba kaya ya ɗauka ba , wasu takaddu ne kawai ya tattara , layinshi ya cire ya ajiye , dube² yayi na irin banyi mantuwa ba kuwa ? Sannan ya fita daga cikin ɗakin ,
Wajen da aka tanada dan ajiye motoci ya samu Umar kamar yadda yace su haɗu , Ashiru a gefe sai Al ‘ Ameen , duk gaisheshi sukayi cikin girmamawa , bai ansa ba , makullin mota ya miƙewa Umar tare da nuna mishi mota yace ka kaima yarinyar nan akwai kuɗi a but in tasha mai , Umar yace mai gida wace yarinya ? Yarinya nawa kasan ina tare da ita ? Haƙuri ya bashi tare da cewa tou ai naji bakace An mata ba , murmushin baƙin ciki Dikko yayi a zuciyarshi yace tace bata so na , kuma fa ba’a soyayya dole Allah ma yasa bansha wahalar shawo kan kowa ba dasai nasha wahala na shawo kan iyayena tace bata aurena , gara kawai na haƙura nayi nesa da rayuwarta na barta ta huta , Umar kallon motar yayi Al ‘ Ameen ma ƙwalalo idanuwa yayi cikin tashin hanki yace mai gida wannan motar zaka bata ?
Cikin ɓacin rai yace Ey ita zan bata , cike da hassada yace ko ka manta nawa ka siyota ne ? Dikko yace kila babanka ya nemomin kuɗin shi yasa na manta , dan wani irin haushin Dikko yakeji kuma Dady yace idan yayi masa wani abu bai yafe masa ba , Al ‘ Ameen ya kalli motar ya ƙiyasta kuɗinta tou ai wallahi kaf garin katsina wannan motar ita ɗaya ce tak , bazai manta ba lokacin da Dikko ya siyo motar wallahi ganinta ake zuwa yi ana mata hoto ko wata motar batayi ba kuma Dikko bai taɓa hawanta ba , shine zai ɗauka ya bawa karuwa ? Kai amma yarinyar nan ta shanye mai gida da yawa , motar miliyoyin kuɗi haka ?
Kaf ma’aikatan gidan nan suka haɗu suna ma Dikko addu’a Allah ya tsare , wallahi game da kyauta dai Dikko baisan darajar kuɗi ba , yana kyauta maisa mutum ya kasa gane bacci yake ko idonshi biyu ? Bayan ya gama sallamarsu ya shiga mota Ashiru yaja suka bar gidan ,
Al ‘ Ameen kuwa sai ƙara kallon motar yake hada kukan baƙin ciki ina ma ɗiyar “yar uwarshi ta samu wannan mota ? Mai gida baisan abunshi haka nan yake neman kuɗin baisan darajarsu ba wallahi , yo wannan mota ai daya sani siyar da ita yayi ya sayi gidaje masu kyau kawai ya ɗauki mota ya ba shegiyar yarinyar da Z bata tantancewa , lallai zaima Yayarshi waya idan har Mai gida ya dawo nigeria Haneefa taje Abuja wurinshi…
Daga gidanshi gidansu ya wuce kai tsaye , danyi musu sallama , momy tace idan an ɗaura aure matarka zata isko ka , cike da biyayya yace tou , bedroom ta koma ta ɗauko maganinshi tace gashi nan saura idan ka tafi ka yadda shi , ansa yayi ya saka a aljihun wandoshi , addu’a tayi mishi tare da mishi fatan alkairi harya fita , Dady kuma baya nan ,
Cike da soyayya tabi bayanshi da kallo , haka nan taji dai bari ta mishi rakiya , bayanshi tabi har inda ya ajiye motarshi , saida zai shiga mota yaga Momy ta biyoshi , kallonta yayi yace inzo ? Murmushi tayi tace a , a , kusa dashi ta matsa tace karka zo rakiya nayi maka , taci gaba da mishi addu’a Allah ya tsare tana ɗaga mishi harya shiga mota suka tafi ,
Tun a mota ya goge hotunan Sultana , bayan yayi musu kallon ƙarshe dayi mata addu’a Allah ya bata miji na gari , ya kuma sa ta yafe masa karta riƙeshi a zuciyarta , shi kuma Allah ya bashi haƙuri da dangana akan ta…
Bayan ya gama goge ²nshi da addu’a shi ya anshi tuƙin motar dan gani yakeyi Ashiru ma baya sauri , tuƙin ganganci da wauta Dikko na fama da iskanci cike da kwalwarshi , ga raini ga rashin ganin mutuncin mutane amma yana da tausayi da taimakon wanda baya dashi ,
10:09pm suka isa kano , anan aka canja abokan tafiya , saida jirginsu Dikko ya tashi Ashiru ya juyo katsina bai kwana ba , sauka lafiya mai gida Dikko Allah ya tsare….
Cikin farin ciki na wayi gari kuma nayi alƙawari yau zan faɗawa Dikko nima ina sansa , duk wanda ya ganni yasan inajin daɗin wannan rana , saida hantsi ya ɗaga na sheƙaƙa wanka na , naci gayuna dan nasan yau Dikko yayi kwanan haƙuri nasan ya ƙagara gari ya waye zai fara zarya ganin dokuna ,
Cike da farin ciki nayo ƙofar gida na zauna ina jiran isowar jarumina , har lokacin zuwanshi yazo ya wuce babu Dikko babu labarinshi , gida na koma na ɗauko wayata na kunna , bayan ta gama kunnuwa na fara neman layinshi , amma dai inajin maganar ɗaya ce kodai wayar tana kashe ko kuma babu kuɗi a wayata ,
Gida na koma nasa aka dubamin ko banda kati , kowa sai yacemin akwai idan nace nawa ne sai su kasa lissafomin , Babana na bashi ya dubamin yace akwai kuɗi , nace nawa ne Baba ? Yace dubu ɗari biyu ne , nace tou kiramin wannan lambar na ƙarasa maganar kamar zan faɗa masa ,
Duba sunan da akayi saving in number yayi yai murmushi tare da cewa iye Mamana ta fara soyayya ya ƙarasa maganar yana kallona kuma cikin zaulaya yayi maganar , cikin jin kunya na zauna kusa dashi ina dafa kafaɗarshi nace aini bana soyayya , yace ai ba wani ne ya bani labari ba nine na gani da idona , tou me yasa kace haka ? A dai² lokacin da yacemin wayar a kashe take ,
Cikin rashin jin daɗi na anshi wayar kaina ya fara min ciwo haka nan naji ɓacin rai ya lulluɓemin zuciya , cike da damuwa na fito tsakar gida , amma sai naga gidan kamar yana juyawa , Baba kuma yana min magana daga bayana wallahi kwata² banajin abinda yake faɗa ,
Wai ance ana kiran Sultana , da sauri na fara kakkaɓa idona daya cika da hawaye inayin dariya cikin farin ciki , nayi ƙofar gida da gudu Babana ya fito da sauri ya biyo bayana yana lafiya ? Turus na tsaya ganin Umar , nayi tunanin zanga Dikko babu shi , sake cika da hawaye idona yayi nace ina yake ? Miƙomin makullun mota yayi a dai² lokacin da Baba ya fito yace gashi yace a kawo miki kuma akwai kuɗi a but wai kisha mai , sai ki bani tukuwici in wuce , nace tou ina shi Dikko yake ya aiko ka ? Umar yace yayi tafiya ,
Kallona Baba yayi yace waye ya kawo wannan motar ? Hawayen da suka taru a idanuwa na suka samu damar gangarowa daga saman kumatu na , da sauri na juya na rumgume Babana ina kuka , ɗagoni yayi daga jikinshi yace wai miye ? Waye ya baki wannan motar ?
Cikin kuka nace Dikko ne , kallon motar Babana yayi sannan ya kalli Umar yace wai wane Dikko ne ? Da hannunshi yayi mishi nuni da doki , kallona Baba ya sakeyi yace meke tsakaninki dashi ? Goge hawaye nayi na anshi makullin na buɗe but in motar , bandir in “yan dubu² ne guda goma , guda biyar na ba Umar nayi godiya , shima godiya yayi ya wuce abunshi…
Umar yana tafiya Babana yace wai Mamana ke ya akayi ya baki wannan motar ne ? Nace shi yaga dama ya bani ita ba roƙarshi nayi ba , kallon motar Babana ya sakeyi yace aiko wannan motar bata hawuwa wurinki garin nan saidai a siyar da ita kuma duk ma garin nan bana tunanin akwai mai siyenta shima ƙuruciya tasa ya siyeta , { ba rashin kuɗi baba yake magana ba da yace baya tunanin akwai mai siyenta } babu dai wanda zai ware wannnan kuɗaɗen ya siyi wannan motar kawai dan dai ya hau , murmushi nayi kaɗan nace baza’a siyar da ita ba gaskiya ,
Baba yace ki hauta ace miki wa Mamana ? Nace idan na hauta kaji yadda za’a kirani , tou ina zaki ajiye wannan mota ? Nace gidan dokunanshi zata riƙa kwana … Allah ya tsare Babana ya faɗa , na ansa da Amin ,
Da kaina nakai ma masu gadin gidan ajiyar mota , suma kansu mamaki ya kamasu ya akayi motar mai gidansu tazo wurina ? Saboda kowa ya sani tashi ce shi ɗaya yake da ita duk kaf cikar faɗin garin katsina , dan anyi surutun motar sosai a lokacin daya siyota kuma har yanzu ba’a gama ba , wannan ansa basu da mai basu ita….
Na shiga cikin ɗimuwar rayuwa nayi kukan rashin Dikko nayi harna gode Allah , na rasa ina zan saka kaina naji daɗi , “yar jakar daya bani a lokacin da muka kama shago dasu Amisty na ɗauko na zazzage , cingom in daya bani nashi na ɗauka nayi ta ci ina haɗiyewa , saida naji zan mutu na haƙura na tattara sauran na mayar ,
Na faɗawa iska ina san Dikko bansan adadin kalamai nawa suka fita daga sautin bakina ba , baida wani amfani dan Dikko dai baya nan kuma bazaiji ba , nayi kukan rashin Dikko har tsawon sati ɗaya ina zubar da hawaye duk nabi na rame na susuce , na kira wayarshi kullum dai maganar ɗaya a kashe , duk lokacin dana kira wayarshi naji kashe sai nayi kuka kuma bazan daina kukan rashin ka ba Dikko har abadan duniya….
Bayan wata ɗaya ,
Abubuwa da dama sun faru , Babana ya warke tas kamar bai taɓa wani rashin lafiya ba , su Amisty kuma an ƙaro iskanci domin dai suma a anguwarmu suka sayi gida ,
Ta siyi motar hawa ta baro iyayenta tana zaman kanta , Nana ma ta tashi daga gidanmu ta koma nasu Amisty , Saude A ` i Zalifa Karima ma duk sun tare a can , Hafsa ma nan take yini amma bata kwana , itama Asma’u anyi mata register kuma suna faɗa cewa yanzu zanga yanda ake shugabar duk wani ɗan iska daya kwana a katsina suna da masaukinshi , idan inajin nima wata ƙwaro ce na kafa manya ²n karuwai kamar nasu…
Lokacin da naji saƙon su Amisty dariya nayi , bana san komawa ruwa dan naji kwata bana sha’awar karuwanci dan zuciyata bata da lokacin sauraren kowa saboda Dikko yabi ya mamayeta da soyayyarshi , kafin inyi wani nazari na yanke hukunci naji gam × ³ a cikin kaina , kamar wacce aljannu yake shiga jikinta haka jikina ya fara fizge² idanuwana sunamin zafi sosai , kaina ya juye , nace tabbas zasu san nawa ba kalar nasu bane mu zuba mu gani dani dasu.
A wannan halin Mamy ta sameni , bayan mun gaisa ta fara rattafomin bayani akan Baban budurwar Dikko , wacce mukayi faɗa da ita a mota…..