TAKUN SAKA 1-10

Murmushi ya sakar mata har haƙoransa na bayyana. “Kinsan miyasa aka kawoki nan?”.
“A’a Uncle”. Ta faɗa cike da marairaicewarta da taso bashi dariya amma sai ya danne. Cikin ƙwarewar aiki ya ce, “Taimakonki muke nema akan masu power bike ɗin jiya da suka kusan tureku, harma sister ɗinku taji ciwo a ƙafarta”.
Kallonsa Hibbah tayi cike da tsarguwa. Fahimtar hakan da yayi ya sashi saurin faɗin, “Muna son gano kosu ɗin ƴaƴan waye? a garin nan, mu kuma kamasu mu hukuntasu. Dan bai kamata ba ace dan kawai suna ƴaƴan masu arziƙi ba su dinga shatar tituna suna zabga gudu tamkar nasu su kaɗai. Zasu iya amfani da wannan damar suyita kashe al’umma saboda ƙarfin ikon iyayensu kuma talaka bazai iya kai ƙara a ƙwatar masa haƙƙinsa ba. Yanzu bayan ALLAH ya taƙaita muku wahala jiya da bamusan halin da kuke ciki ba zuwa yanzu ai ko. Kalla nan kiga”.
Ya ƙare maganar yana ɗaukar remote ɗin da ke gabansa tare da janye idanunsa a kanta ya maidawa ga ƙatuwar tv dake mamake da kusan rabin bangon office ɗin. “Kinsan wannan mutumin?”.
Fuskar dattijo mai cike da ƙasumba a cikin shigar manyan kaya ta bayyana. Kallon kusan minti ɗaya tai masa kafin ta girgiza kanta. “A’a yallaɓai ban sanshiba. Bamma taɓa ganinsa ba”.
Wani ya kuma nunowa da faɗin, “Wannan fa?”.
“Shima haka ban sanshi ba”. Hibbah ta faɗa idonta akan hoton matashin saurayi mai saida rake a Wheelbarrow.
Cigaba yay da latso mata hotuna kala-kala na mabanbanta mutane tana cewa bata sansu ba. Sai wani guda biyu na kusan ƙarshe data taɓa gani an nuna a labarai kwanaki.
“Yallaɓai wannan dai na taɓa ganinsa a tv, dan an taɓa nunasa kwanaki a labarai, kuma hoton yata yawo a social media akan cewar shi ɗin babban ɓarawo ne ɗan yahoo da ya yashe manyan kuɗaɗen wani attajiri. Yayana ma yace suma suna nemansa ruwa a jallo. Kuma nemansa kukeyi halan?”.
Sosai ma kuwa nemansa muke muma tare da waɗancan na farkon dana nuna miki. Amma rashin mai taimaka mana irinki yasa mun gagara hakan. Amma shiɗin wanene yayan naki?”
Kanta tsaye batare da tunanin komai ba ta ce, “Uncle shima ɗan sanda ne”.
“Woow masha ALLAH. Lallai naji daɗin hakan sosai. Kuma zanso ganinsa shima harma nai masa ƙarin girma saboda samun ƙanwa irinki mai ƙwazon da ya kamata ƙasa gaba ɗaya tai alfahari dake”.
Murmushi tayi cike da jin daɗin jin za’a ƙarama Yaya Abubakar ɗinta girma ta sanadinta. Shima ganin ta hau yanda yake buƙata saboda ƙuruciya sai ya ƙara faɗaɗa murmushinsa da faɗin, “Idan har kikai mana wanann taimakon da zan miki bayani akansa yanzun to lallai yayanki zai ƙara zama babban mutum, kema kuma zaki rama jin ciwon da aka saka ƙawarki tayi jiya. Da ga ƙarshe zaki samu ƙyauta mai tsokar gaske”.
Batare da tunanin komaiba ta ce, “Insha ALLAH zan taimakeku Uncle, indai Yaya Abubakar zai ƙara samun girma”.
Cike da jinjina wautarta fara’ar fuskarsa ta sake bayyana. “Yauwa ɗiya ta. Aikin da zaki mana shine gano mana inda masu power bike ɗin jiya suke.”
“Lah Uncle ai nama g…..”
Sai kuma tai shiru tare da dafe bakinta saboda tunowa da gargaɗin Yaya Abubakar na ɗazun akan karta sake ta sanarma kowa.
“Miya faru ki kai shiru ɗiyata?”.
Da sauri ta girgiza masa kanta. “Babu komai Uncle, inason kai musu magana su fara bani wayata nayi magana da Yaya Abubakar”.
Shiru yayi cike da nazarinta, a zuciyarsa. Yace (Yarinya mai wayo). A fili kam ganin ta kafesa da ido yay saurin sakin murmushi. “Okay okay babu damuwa zan musu magana su baki. Amma kafin hakan zaki cika mana alƙawarin mu. Idan ba hakaba kuma zamu cigaba da riƙeki anan, tare da sakawa a kamo mana Mamanki dasu yaya Abubakar ɗin naki mu faɗama duniya cewar sunada alaƙa da wancan hotunan mutanen da muke nema kin amince?”.
A take dukkan fara’ar dake kan fuskar Hibbah ta ɓace ɓat. Shima tuni saɓanin murmushi ya maye gurbin tasa fuskar. Ya kuma tsatstsare ta da idanunsa cike da tsoratarwa. “Yanzun nan zan bada umarnin zuwa a ɗakko min Umminki. Tare da Yayanku Muhammad har wajen aikinsa. Sai Umar da Usman. Aliyu (Ammar) kuwa yanzu haka akwai jami’anmu dake zagaye da shi a makarantarku. Kalla nan”.
Ya ƙare maganar da juya mata lap-top ɗinsa. Wani irin firgici da ruɗani ne suka bayyana a fuskar Muhibbat ganin hotunan Yayunta tare da hotunan ɗazun daya nuna mata na waɗanda ake nema. Kowanne da taƙaitaccen bayanin dangantashi da waɗan can masu laifin. A ƙarshe aka bayyana Ummi matsayin mahaifiyarsu tare da ita mai taimaka musu kasancewarta masaniya akan ilimin sarrafa Computer.
Saurin ɗora hannunta tayi akan baki saboda kukan dake neman kufce mata. Ta shiga girgiza masa kanta a kiɗime. “Please yallaɓai kar kai haka dan ALLAH. Ni ƴan uwana ba ƴan ta’adda bane. Basu taɓa aikata laifin komai ba sai alkairi. Karka zaluncesu ta dalilina….”
“Inhar baki so ganinsu a cikin wani hali sai kiyi mana abinda muka sakaki ki zama sanadin alkairinsu. Bawai ina lallaɓaki bane dan bazamu iya sarrafaki kimana dole ba. Inda naso tursasaki da tun a daren jiya zamu ɗakkoki har gida kiyi mana aikin akan dole.” yay maganar a matuƙar kausashe yana bugar desk ɗinsa.
Ɗan zabura baya Hibbah tai jikinta na rawa. Yayinda shi kuma ya shiga ƙwala kiran sunan jami’in su Nura.
Da sauri Nura ya shigo yana ƙamewa da faɗin, “Yes sir!”.
“Maza a shirya jami’an da zasu fita operation yanzun nan.”
“Okay sir”. Ya sake faɗa da girmamawa yana ficewa.
Miƙewa yay shima yana nuna Hibbah da faɗin, “Oya miƙe”.
“Yallaɓ…..”
Hannu yasa yay zipping bakinsa alamar karta sake cewa komai.
Ɗakin da ke ajiye da na’urori masu ƙwaƙwalwa aka kai Hibbah. Inda suka sami mutane kusan goma sha uku a ciki. Kai tsaye wajen zama aka nuna mata alamar dama ita ake jira. Zama tai tana haɗiyar zuciya. Batason yin aikin saboda gargaɗin Yaya Abubakar. A gefe kuma batason a cutar mata da ahali akan abinda basu ji ba basu gani ba. A wani gefe na zuciyarta kuma nason yi kodan abinda mutanen suka nema yi musu jiya har ga Hafsat da ciwo.
Waya irin ta jami’an tsaro aka ajiye a gabanta. Tare da kunna ƙaton tv irin na office ɗin data baro da shima ke a jikin bango. Hoton yayunta da rahotannin da aka shirya na karya dan tsoratar da ita suka bayyana.
Ta sauke idanunta dake cike da ƙwalla a hankali bisa computer ɗin gabanta.
“Ki nutsu wajen yin aikin da zai ƙuɓutar da ƴan uwanki zama criminals zuwa taurari ta sanadinki, ko kiyi sakacin yin aikin da zai dusashe haskensu da ga taurari zuwa criminals ta sanadinki.”
Mutumin ɗazu ya faɗa cikin tabbatarwa da murya mai kaushi.
Kai kawai ta jinjina masa tana maijin wani ɗaci a zuciyarta da taurin zuciya. Sai da tayi addu’a a cikin zuciyarta kafin ta fara aikin cike da ƙwarewa. Kasancewar ɗazun dama ta binciko a inda suke sai yanzu batasha wahala ba duk da wannan Computer ɗin nada matuƙar tsaro fiye da tasu ta makaranta.
Da wayar gabanta ta dinga amfani wajen yin magana da jami’an da suka fita operation ɗin tana sanar musu hanyoyin da zasu bi har zuwa location ɗin da agogon data jefama masu power bike jiya yake. Hakan shike nufin tabbacin samun su inhar agogon na tare da su basu farga sun yadda ba…….