Uncategorized

TAKUN SAKA 1-10

 _*Sunada different varieties of frames gamai siyan daya Koh sari*_

_*Sannan muna karban order gamasu hidimar biki kmn dg abinci, snacks, juices nd so on*_

_*Kindly chat with us via 08062991549.*_

*___________________________*

*_Chapter Eight_*

………..Wani wawan tsaki ya ja tare da kai hannu kan Wadrobe ɗin dake a jikin bangon ɗakin ya danna wani maɓalli. A take ta zuge kanta, ɓoyayyar ƙofar sirri da ke a jikin bangon ta bayyana. 

        Cikin sauri suka shiga shigewa mamaki fal ransu, dan ko su da ke tare da shi tsahon shekaru basu taɓa sanin da ƙofar ba. Bama batun ƙofa kawai ba, ko fuskarsa ta ainahi har yanzun basu sani ba. Yanda yake zuwama duniya da mabanbanta fuskoki suma haka yake zuwa musu, duk da kuwa akwai alaƙa tsakaninsa da wasu a cikinsu ta zuminci.

        Shi mutum ne mai aiki da matuƙar taka tsan-tsan a kowane ɓangare, shiyyasa yay dogon zangon da har yanzu an kasa cimmasa a duk tarkuna da ake ɗana masa, dan kota ina idanunsa a buɗe suke, hakama kunnuwansa. Sai da duk suka gama fita yana kallon jami’an tsaron da ke shigowa cikin gidan da sanɗa ta cikin tab ɗin dake a hannunsa. “Humm” ya faɗa yana rufe tab ɗin, shima yabi bayan yaran nasa tare da maida ƙofar a yanda take kamar babu.

           Koda ya fito bai tankasu ba, sai wasu ƙananun fitilu masu azabar haske daya fiddo a aljihun wandonsa  ya shiga kunnasu yana mika musu, A take ko ina ya gauraye da haske har suna iya ganin gabansu. Sam babu ruwa ko datti a ciki, hanyace ɗoɗar da basusan iyakarta ba, domin dama can ba’a yisa dan ruwa ya wuce ba. Sukam dai ɗunbin tsoro da mamakin Master ɗin nasu tuni ya gama kashesu a tsaye. Tun fitowarsu a ɗakin da suka tsinci kansu a cikin doguwar hanyar ruwa komai ya kuma kwance musu game da shi. Sagade sukai suna kallon ikon ALLAH da sake tsorata da al’amarinsa. Lallai sun sake yarda da gaskiyar zantukan mutane da ke kiransa *Hatsabibi shu’umi*.

          “Zakuje ne ko zaku tsaya kallo na?”. 

        Sautin furicinsa ya maido da hankalinsu jikinsu kusan a tare lokaci guda.

       Da sauri suka haɗa baki wajen faɗin, “Sorry Master!”. 

★★★

            Jami’an tsaron da suka iso anguwar bisa jagorancin Hibbah da ke basu haske ta hanyar waya kuwa tun kafin su iso gidan suka ajiye motocinsu can farkon layin suka ƙaraso da ƙafa. Mai-gadi da dama yake zaman jiran tsammani kamar yanda Master yay masa bayani ana yin knocking gate ɗin ya tashi ya buɗe bayan ya ƙara ƙarar redio ɗinsa da yake ji.

       Jami’in da ya fara isowa wajen cikin son nuna basaja ya bama mai-gadi hannu yana murmushi. Babu musu shima mai gadin ya bashi hannu sukai musabaha cikin nuna ƙaulanin rashin sani.

        “Sai dai gashi ban waye kaba bawan ALLAH. Kuma su alhaji basu sanarmin wani baƙo zaizo nan ba”. Mai-gadi ya faɗa lokacin da yake sakin hannun jami’i da yazo a suffar basaja.

            Jami’in da furucin mai-gadi ya ɗan tsaya masa a rai ya ce, “Kana nufin masu gidan basa nan kenan?”.

       “Tabbas basa nan mai-gida. Yau kwanansu tara kenan da komawa can ƙasar da suke zaune ai”.

         Wani kallon kama rainamin hankali jami’in yay masa, amma sai ya saki murmushi da maida hannayensa baya yanama ƴan uwansa alamar su taho ba tare da yasan mai-gadin na lure da shi ba.

      Baki mai-gadi ya buɗe zai sake magana sauran jami’an suka iso suma. Bindiga wanda ya fara zuwa ya nuna masa tare da turasa cikin gidan duk suma suka shishshigo. Duk rarrabuwa sukai a kowace kusurwa ta gidan suka fara shiga da sanɗa, wanda ya fara zuwan kuma na tare da mai-gadi da zuciyarsa ke cike da tsoron kar dai ƙaryarsu ta ƙare yau, dan shi duk tunaninsa su Master na’a cikin gidan suma tunda bai sanar masa shirinsa ba bayan aikin da zaiyi kawai. Duk da ya yarda da hatsabibancin uban gidan nasu amma dolene akwai ɓacin rana. Da alama kuma idan har ta ƙwaɓe yau da shi zata fara ruftawa. To amma insha ALLAH zaiyi ƙoƙarin ganin ya bi duk abinda Master ya faɗa masa yanda ya kamata.

            Sai da jami’in nan ya tabbatar abokan aikinsa sun gama zagaye gidan sannan ya tasa ƙeyar mai-gadi shima suka nufi ciki. Ƙofar shiga da suka fahimci a rufe take suka bashi umarnin buɗewa. Amma sai ya nuna musu sam bai san password ɗin ba shi.

         Jikinsa jami’in ya fara laluba, ya ciro waya nokia da tasha ɗaurin ƙyauraye da salataf. Wayar ya jujjuya a hannunsa yana ƙare mata kallo fuska a yatsine, kafin ya maida dubansa garesa yana sake gyara zaman bindigar da ya ɗora masa a saman kai. 

       “Nasan dai kanada number ɗin mai-gidan, maza ka kirashi yanzun nan ya faɗa maka password ɗin komu ɓalla ƙofar a yanda muka gadama.”

       Babu wani nuna damuwa ko ɗar mai-gadi ya amsa wayar ya shiga laluben Number. Dailing yayi kansa tsaye, sai dai harta tsinke ba’a ɗaga ba. Ya sake kira a karo  na biyu, sai da taje gab da tsinkewa aka ɗaga cikin muryar isa. Cikin girmamawa mai-gadi yay gaisuwa, sannan ya ɗara da bayanin cewar jami’an tsaro ne sukazo gidan suna buƙatar password na ƙofa wai zasuyi bincike, bai san mi suke nema ba. Carab jami’in ya amshe wayar yasa a kunnensa bayan ya kalla no. Ɗin da mai-gadin ya kira ya tabbatar da ta ƙetare ce.

           “Jami’an tsaro kuma? Rabi’u!. To mu miya haɗa gidanmu da jami’an tsaro?”.

      “Bincikenmu ne ya nuna mana wannan gidan na masu laifine Alhaji. Bazamu tabbatar da ba haka bane ba sai mun shiga mun duba kuma. Dan haka muna jiran mabuɗin sirrin ƙofar da ga gareka kawai, kafin muyi magana ta gaba da kai idan har ya kama”.

      “Okay to babu damuwa yallaɓai”. Daga can aka faɗa tare da zayyano masa password ɗin. 

        

      A sakawa ɗaya kuwa ƙofar ta buɗe. kusan rabi a cikinsu suka shiga ciki akabar wasu a waje. Akan idon mai-gadi suka shiga hargitsa gidan tako ina. Sai dai abin mamaki babu wani alamun abun rashin gaskiya da sukayi gamo da shi. Cikin glass ɗin nan da computers ke ciki ɗazun yanzu babu shi, sai wasu ƙayatattun flowers masu ɗaukar hankali da ƙamshinsu ya cika falon.

        “Tabbas yarinyar nan ƙarya take mana. Ko tana ɗaya da ga cikinsu ne yawo da hankalinmu kawai take son yi”. Ɗaya daga cikin jami’an ya faɗa a hasale.

               “Sam banajin hakan a raina, akwai dai wani ɓoyayyen abunda bamu sani ba. Karku manta shiɗin mutum ne mai matuƙar wayo da dabaru kala-kala. Tabbas ya fahimci ana bibiyarsa ne ya bada ƙafa. Kokuma yayi amfani da wanann location ɗin domin sakamu zargi.”

        “Nima zuciyata tafi rayamin hakan yallaɓai”. Wani ma ya sake faɗa cikin jin zafi.

        “Karku samu damuwa. ai rana 99 da tara na ɓarawo, ɗaya tak na mai kaya. Inhar kere na yawo, zabo na yawo watarana dole a gamu. Tunda yace shi hatsabibi ne ya samu dai-dai da shi kuwa. Zamu bar wasu a gidan nan har sai mun tabbatar da gaskiyar babu wani abun zargi a cikinsa”.

      Duk sun amsa da girmamawa. Shi dai mai-gadi kallonsu kawai yake yana kwasar dariya a zuciyarsa. Koda suka fito harabar gidan sun tsara wanɗanda za’a bari, wanda zasu koma kuma suka nufi hanyar barin gidan. Karaf idon ɗaya ya sauka akan bag dake rataye acan ƙarshen gate ɗin gidan ta waje. Saurin zuwa yay ya ɗakko yana nuna musu. Commander ɗin operation ɗin nasu ya amsa yana zazzage jakkar cikin kulawa gudun kar a saka musu bom a ciki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button