Uncategorized

TAKUN SAKA 1-10

Chat

08062991549

07046881166

07067210195

Call 

08064532391

Instagram: glow_with_mgs

Facebook:mg’s skincare

Location:kaduna buh we deliver Nationwide

Delivery is not free buh gamasu sari ko wnd yasiya Kaya dayawa kmn 20k above there will be free delivery+ gift

 _*Sunada different varieties of frames gamai siyan daya Koh sari*_

_*Sannan muna karban order gamasu hidimar biki kmn dg abinci, snacks, juices nd so on*_

_*Kindly chat with us via 08062991549.*_

________________________

*_Chapter Ten_*

………..Ummi na shigowa falon ta wankama Ammar mari. Lokaci guda falon ya ɗauki tsitt. Hibbah ta zazzaro manyan idanunta waje, jikinta na rawa, dan abinda bai taɓa faruwa ba a tsawon sanin da taima Umminsu. Duk iya ɓacin ran da zata nuna idan sukai mata laifi iyakarta da su faɗa da nasiha tun basu kai haka ba.

        Ba Hibbah kawai ba, hatta Yaya Muhammad da Yaya Abubakar sai da wutar kansu ta ɗauke. Hakama Yaya Umar da Yaya Usman da ke ƙoƙarin shigowa falon saboda kiransu da mai-gadi yayi ya sanar musu abinda ke faruwa tun sanda Ammar ke jibgar Junaid. Sai dai suna shigowa gidan motar Ameera na fita zuwa asibiti kai Junaid. Tare kuma suka tafi gaba ɗaya gidan, har da Hajiya mama dake fama da ƙafarta.

            Ƙananun duka Ummi ta cigaba da kaima Ammar, hawaye masu zafi suna gangaro mata a kumatu. Ammar dake tsaye ƙiƙam tun marinsa da tai kallonta kawai yakeyi shima hawayen na sakko masa na tausayinta. Yayinda wani murmushi mai ɗaci ke bayyana saman fuskarsa. Ummi ta jawosa ta rungume jikinta tana magana cikin rawar murya, “Miyasa zakai haka Aliyu? Miyasa? Ba nace duk abinda zaku gani ba kuyi kamar baku gani ba.”

     Da gudu Hibbah ta zo ta rungume Ummin da Yaya Ammar itama. Gefe Yaya Muhammad ya kauda kansa yana ƙoƙarin ɗauke hawayen da suka ciko idanunsa. Yaya Abubakar ma idanunsa sun kaɗa sunyi jajur. Yaya Umar yafi kowa zuciya a cikinsu, yayinda Yaya Usman duk ya fisu sanyi shi da Yaya Muhammad. A wani irin fusace ya juya zai fita a falon Yaya Usman da yasan halin kayansa yay azamar riƙo hannunsa.

       “Sake ni!”

Ya faɗa cikin kaushin muryar da ya maido hankalin kowa kansu. Girgiza masa kai Usman ya shiga yi alamar bazai barsa ba. Dan yasan dama badan Ummi da ke dakatar da su ba babu shakka da tuni Umar yayma Abba dukan mutuwa a gidan harma da Hajiya mamar kanta… Da ƙarfi Yaya Umar ya fisgi hannunsa da ga cikin na Usman. Hakan yasa Ummi azamar sakin Ammar tasha gabansa.

        Cikin idonsa ta kalla batare da tace masa komai ba. A take yay ƙasa da kansa yana lumshe idanu da cije leɓensa da ƙarfi tamkar zai huda shi. Murmushi tayi tana kamo hannunsa cikin nata. Gaba ɗaya ƴaƴanta tasan lagonsu da hanyar sauke fushinsu. Shiyyasa a kowane lokaci take samun nasarar ladabtar da kowa cikin salon da ya dace. Babu wanda ta sake yima magana a cikinsu, sai kamo hannun Hibbah dake sharar hawaye har yanzu tai tana bin jikinta da kallo tamkar mai neman wani abu. 

      Da sauri Hibbah ta ce, “Ummi basuyimin komaiba fa, babu abinda ya faru ki kwantar da hankalinki”.

       “Ai sun sakaki a tarkon da za’ayi miki ne!”.

   Yaya Abubakar ya faɗa a tsawace cikin faɗan da kowa baisan yana da shi ba. Dan shima bai cika hayaniya ba sosai, amma yafi Usman da Muhammad zafi a wasu lokutan.

       Ya riƙe ƙugunsa da hanunsa ɗaya, ɗayan yana murza goshinsa cike da damuwa. Yanda ya ke ɗan kaikawo yasa su fahintar akwai matsala kenan. Ummi da dama yin komai ta ke cike da ƙarfin hali ta kafesa da ido. 

        Zaune Yaya Abubakar ya kai saboda jin zai faɗi, dan shi kaɗai yasan a wane irin damuwa ya ke game da halin da Hibbah ta ke ciki. Gaba ɗaya ƙuruciya ta hanata fahimtar ramin da ta jefa kanta a ciki mai haɗari ne………

       “Abubakar mike faruwa?”

Ummi ta katsesa tana takowa gabansa. Idanunsa da ke jajir ya ɗago yana kallonta, ya ɗan furzar da zazzafar iska yana girgiza kansa. “Ummi tabbas akwai matsala, rawar kanta ta kaita ga jefamu cikin ramin da sam ita bazata fahimci haɗarinsa ba….”

         Duk da hibbah a tsorace take da yanayin Yaya Abubakar ɗin, tai saurin katsesa ta hanyar faɗin, “Yayanmu wlhy babu abinda ya faru fa. Kawai dai sun sakani na bibiyar musu masu power bike ɗin nan dana sanar maka ne. Amma da ga haka basuyi min koma………”

       Tsawar da ta sakata kasa ƙarasa zancen ya daka mata. Ta maƙale a jikin bango jikinta na rawa saboda bata taɓa gamo da fushinsa irin haka ba. Shima tsaye ya miƙe yana nunata jikinsa har rawa yake ga idanunsa sunyi jajur. “Idan bakimin shiru ba wlhy sai na ɓallaki a gidan nan yau. Bance miki ki jirani a inda kike nazo na sameki ba? Su masu power rider ɗin da kike tunanin ba komai ba to sune tawagar ɓarawon nan da ake nema ruwa a jallo mai suna *Master!*, shine ya wawashi maƙudan kuɗaɗe jiya a asusun matar gwamna. Kowace hukuma ta jami’an tsaron jiharnan an basu awa ashirin da huɗu ne domin kawosa a mace ko a raye. Ba jihar nan da ƙasarnan kawai ba, hatta duniya baki ɗaya idonsu akan wannan mutumin yake. Amma shine k kika jefa kanki cikin abinda bakisan mafarinsa ba. Su waɗan nan jami’an da suka ɗaukeki zasuyi amfani da ke ne kawai su sami cikar burinsu, sunansu ya sake fiwowa a idon duniya. Kece zakiyi aikin amma sune zasu fito matsayin masu aikin. A tunaninki shi ɗin mahaukaci ne, kosu suna son matsalar tasa ta ƙare ne da wuri? Kuɗaɗen shigar da suke samu su dakata. Kafin yau an sha yimasa tarkuna da sukafi wannan haɗari amma bai kamu ba. Da ga ƙarshe kuma duk wanda yay masa tarkon ana nemansa ne a rasa ma baki ɗaya, ya ɓatar da shi. Wannan yasa a duk lokacin da ya aikata laifin manyan ke makalewa su saka ƙananun ma’aikata yin aikin, da ga ƙarshe suke nuna sunyi aikin ma duniya, wanda yay aikin kuma rayuwarsa ta faɗa a haɗarin da babu wanda zai sakejin yanda akayi, kuma basa wani ɗaukar matakin bashi kariya ko cetosa. Shekarunki goma sha takwas kacal da wasu wattani a duniya Muhibbat! Bama ki gama karatun gina rayuwar taki ba amma kika jefa kanki a wannan haɗarin saboda kunnen ƙashinki. Wannn kunnen babu wanda ya isa ya faɗa masa yaji sa”.

    Ya ƙare maganar da takawa inda take maƙure a bango jikinta na rawa ya damƙi kunnenta da ƙarfi yana murzawa cikin yatsun hannunsa. Rawa jikinta ya farayi tana girgiza masa kanta saboda zafi.

             Sakin kunnen nata yay yana dungure mata kai, yayinda sauran yayun nata da Ummi keta faman ambaton (innalillahi wa-inna ilaihirraji’un) a zukatansu. Yaya Abubakar ya cigaba da faɗin, “Ba wanann kaɗai bace damuwar Ummi, tunda har basu sami nasarar kamashi ba zargi zasu ɗarsa akanta itama. Dan zasu raba hankalinsu ne yanzu akan tunanin ko shine ya shirya komai wajen yin amfani da ita. Dan duk harin da jami’an tsaro ke kai masa ba’a taɓa cin nasara kamar nata ba da ya gudana cikin kanƙanin lokaci. Yanzu da zarar sun fitar da bayanai wa media cewar sun haresa, harin da kuma aka samu ci gaba a cikinsa fiye da na baya, to kowacce hukumar jami’an tsaro sai sun bibiyi yanda hakan ta kasance ta karƙashin ƙasa, walau jami’anmu nan gida kona ƙetare da ke nanuke cikin case ɗin kamar yanda suka saba mana kutse a cikin ayyukan daya shafi ƙasashenmu. Mu kuma bamu isa muyi koda tari akan nasu ba. A ƙarshe kowa ya bincika ita zai gano. Duk kuma zasu kasance wajen bibiyarta da mu kammu ba tsira zamuyi ba. Shima da ta aikata komai dominsa ba barinta zaiyi ba na sani.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button