TAKUN SAKA 1-10

Sake maida hankalinsu sukai garesa domin sonjin ƙarshen zancen.
Ya gyara abin maganar gabansa yana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya. “Ma’anar mu jefa tsuntsu biyu da dutse ɗaya shine muyi amfani da wannan yarinyar ta hanyar riƙeta a jikinmu ta zame mana ma’aikaciyar sirri. Ta wannan hanyar zamu amfanu da alkairinta da kaifin basirarta. Mu kuma saka mata ido wajen gano shin akwai alaƙar da zuciyarmu take zargin tsakaninta da shi ko babu?”.
“Yes! Wannan shawarar taka tayi matuƙa *A.G*”. Ogansu ya faɗa yana tafa masa. Hakanne yasa suma sauran tafa masa duk da wasunsu batai musu ba sam. Dansu babu abinda zukatansu ke ayyana musu sai ganin babu abinda Hibbah zata iya matsayinta na ɗiya MACE mai kuma ƙarancin shekaru.
Sun cigaba da tattaunawa har zuwa wani lokaci, kafin ogan nasu ya bada damar shigo da Hibbah.
Hibbah da damuwar ahalinta kecin ranta ta shigo fuskarta a cinkushe babu ko ɗigon walwala. Babu abinda zuciyarta tafi bukata a yanzu kamar tozali da Ummi da yayunta dan tabbatar da babu abinda ya faru da su. Zama tai a kujerar da aka nuna mata bayan ta gaishesu ranta fal jin haushinsu, musamman mutumin ɗazun da tun shigowarta da shi ta fara haɗa ido yana mata murmushi.
Bayan sun gama nazartarta da ƙare mata kallo ogan nasu yay gyaran muryar da ta saka Hibbah ɗago manyan idanun ta kallesa. Ganin yanda ya kafeta da nasane ya sata sake maida kanta ta duƙar tana wasa da yatsun hannunta.
“Muhibbat Aliyu Hamza!”.
Ya kirayi sunanta murya babu alamar wasa. Hakanne ya saka gabanta faɗuwa, ta sake ɗagowa tana amsa masa da rawar murya. “Na’am yallaɓai”.
“Miye alaƙarki da Master!?”.
“Master kuma yallaɓai? Ni ban sanshi ba”.
“Kin tabbatar?”.
Kanta ta jinjina masa.
“Taya za’ai mu yarda baki da alaƙa da shi?. Bayan tsahon shekaru biyu kenan kowace hukuma ta jami’an tsaro farautarsa suke, amma sun gaza koda ganin farcen yatsansa. Sai gashi ke a cikin kwana ɗaya rak kin haresa akan dai-dai?”.
“Ni wlhy yallaɓai bansanshi ba, bakuma ni da wata alaƙa da shi ko sanin wanene shi. Na aikata duk abinda kukaga nayi ne saboda wasa da rayukan mutane da sukeyi ta hanyar power rider amma badan wani dalili ba”.
“Okay, mu ɗauka hakanne kamar yanda kika faɗa ɗin. Yanzu wane tunani kikeyi game da makomar ahalinki?”.
Saurin ɗagowa tai tana kallonsa idanunta cike da ƙwalla. Muryarta na rawa tace, “Amma yallaɓai naga na muku aikin da kuka buƙata dan na tabbata kun kamasa. Kuma kun tabbatar min hakan shine fansar ahalina ai”.
“Eh tabbas haka muka faɗa, sai dai kuma ba’a samu nasara ba kamar yanda mukai tunanin za’a samu. Rashin samun nasarar kuma na nufin shigar ahalinki a haɗari ta fuska biyu. Na farko mu jami’an tsaro ba zamu barsu ba har sai wancan hatsabibin yazo hannunmu. Hakan shine zai wankeki a garemu mu tabbatar baki da alaƙa da shi, ahalinki kuma su kuɓuta. Na biyu dole ne mu baki kariya yanzun dan tabbas zaki zama abin farautarsa kema dan bazai barki ba tunda kin karya masa tarihi. Dolene kowane motsinki dana ahalinki su kasance a tare damu. Idan kin amince ki cike wannan. Kokuma kiyi tafiyarki amma babu ruwanmu da abinda zai samu ahalinki. Zakuma mu fitar da bayanan sune ke aikata laifukan da muka nuna miki ɗazun da mabanbanta fuskoki. Kinga za’a kamasu a kaisu kotu, da ga ƙarshe a yanke musu hukuncin kisa bayan duniya ta sansu matsayin ƴan ta’adda”
Sosai tashin hankali ya bayyana a fuskar Hibbah. Idanunta suka ciko da hawaye ta shiga girgiza musu kai laɓɓanta na rawa. “Dan ALLAH yallaɓai karkuyimin haka. Wlhy bani da alaƙa da mutumin nan sam, iya gaskiyata na sanar muku.”
“Ta hanyar shigowa kiyi aikin sirri da mu ne kawai zai tabbatar mana da hakan, ahalinki kuma su kuɓuta da ga garesa da mu kammu. Gashi ki cike waɗan nan takardun idan har kin amince”.
Da ƙarfi Hibbah ta rumtse idanunta. Wani irin zafi da ɗaci na sauka mata cikin zuciya. Karan farko na rayuwarta da taji tsiwa batai mata rana ba. Tanajin tsana mai yawan gaske akan mutumin da batasan wanene shi ba. Yayinda gefe na zuciyar tata ke jin haushin waɗan nan jami’ai da ke son yin amfani da damar da ALLAH ya basu ta hanyar amfani da ita. Wani gefen kuma na haske mata ahalinta cikin bala’i mai muni da idan har ta zama sanadin shigarsu cikinsa har gaban abada bazata taɓa yafema kanta ba. A take wani irin kangarewa da bushewar zuciya suka saukar mata. Batare da yin wani dogon nazari ba wautar ƙuruciya ta fisgeta da zuciya wajen ɗaukar pen ta hau cike takardun da ɓarin jiki, batare data duba mi suka ƙunsa ba..
Fusatar tata ta basu matuƙar mamaki da al’ajabi. Sai dai zukatansu na ayyana musu tanayin komai ne domin ahalinta. Dan fahimtar sune rauninta ya sakasu yin amfani da su wajen tursasata. Aiko sunci nasara, dan ta cike takardun kamar yanda suka buƙata. Ta kuma saka hannu bisa takardar contract ɗin zatai musu aikin sirri har sai sun kama Master. Su kuma bazasu saki wancan bayanan ƙaryar da suka shirya ba domin mata ɗaurin talala saboda ƙarancin shekarunta.
Sun mata bayanai sosai da zata iya fahimta. Tare da bata date ɗin da zata fara amsar horo na musamman a ɓoye. Da ga ƙarshe sukai mata dogon gargaɗi akan riƙe dukkan abinda suka tattauna matsayin sirri. Dan inhar ta fitar tamkar ta bayyana ƴan uwanta ma duniya ne matsayin ƴan ta’adda. Daga haka suka sallameta.
Fitowar Hibbah da aka haɗa da jami’ai biyu zasu mata rakkiya zuwa gida yayi dai-dai da isowar Yaya Abubakar da Yaya Muhammad station ɗin. Tana ƙyalla ido a kansu ta kwasa da gudu garesu. Jikin Yaya Abubakar dake gaba ta faɗa tare da fashewa da kuka.
Shima rungumeta yay yana mai rintse idanunsa da suka kaɗa sukai jajur. Yaya Muhammad ya ƙaraso garesu da sassarfa shima. Dafa kanta da yayine ya sata barin jikin Yaya Abubakar ta rungumeshi shima. Cikin son danne nasa ɓacin ran ya saki murmushi yana ɗagota da shafa kanta. Hannu yasa ya shiga share mata hawaye. “Kukan ya isa haka nan, ba gamu tare da ke ba”. Ya ƙare maganar da sake sakar mata murmushi mai kwantar da hankali.
Yaya Abubakar da shima ke ƙoƙarin ganin ya shanye tasa da muwar ya ce, “Bara naje zanyi magana da su”.
Da sauri Hibbah ta riƙo hannunsa tana girgiza kanta. Cikin sanyin da basu santa da shi ba ta ce, “Yaya karka je. Ka barsu kawai babu abinda sukai min”.
“Karki damu, ba wani abu bane yanzu zan fito”. Yay maganar da zare hannunsa cikin nata yana shafa kanta. Kama hannunta Yaya Muhammad yay shima ya buɗe mota ya sakata, tare da ɗaukar goran ruwa ya miƙa mata. “Sha ruwa ki wanke fuskarki ina zuwa”.
Hibbah na ƙoƙarin dakatar da shi bai jira cewarta ba ya nufi cikin station ɗin shima. Jitai kamar ta fasa ihu, dan gani take kamar shigar tasu na nufi jami’an zasu riƙesu su sanarma duniyar ƴan ta’adda ɗinne su.
Ganin an shafe kusan mintuna a shirin tai yunƙurin bin bayansu, sai dai tana buɗe motar suna fitowa kowannensu ransa a ɓace. Ta sauke ajiyar zuciya da yin sagade tai tana kallonsu har suka ƙaraso. Yaya Muhammad ya sake kama hannunta ya sata a motar sannan ya zagaya ya shiga shima. Yayinda Yaya Abubakar ya zauna mazaunin driver.