TAKUN SAKA 1-10

Kusan a tare suka haɗa baki wajen faɗin, “ALLAH ya tashemu lafiya boss. Sweet dream tare da ƙarin ƙyaƙyƙyawar idea akan ƴan ruda”.
Daƙƙuwa yay musu batare da ya juyoba. Sai dai ya saki murmushi dai-dai yana shigewa. Duk da basuga murmushin nasa ba kasancewar ya juya musu baya hakan bai hanasu yin kananun dariyar farin ciki ba gaba dayansu.
Yana shigewa suka farma gasassun kajin da ya kawo musu tun shigowarsa da ci. Dama sun ɗan ɗaga kafa ne ganin yazo a cikin yanayin babu wasa. Yanzu ko sunsan komai normal ne, sai abinda ba’a rasaba saboda rikita-rikitar Master ɗinsu bata taɓa karewa. Daya toshe waccan matsalar zai ɓallo wata da kansa kafinma ƙurar wadda ya tayar ta lafa.
Shima ko da ya shiga ɗakin zazzafan numfashi ya furzar. Ko’ina fes dan tun bayan barinsu da yayi suka gyara komai. Ya jefa file ɗin hannunsa saman madai-daicin gadon. Kayansa ya shiga zamewa alamar son watsa ruwa. Ya rage da ga shi sai singlet da boxer. A haka ya nufi toilet ɗin.
Tsahon mintuna ashirin ya ɗauka a ciki kafin ya kammala, tun kafin ya fito da ga bayin ya ziro hannu ya kashe wutar ɗakin baki ɗaya. Batare da damuwa da duhun da ya mamaye ko ina ba ya fito a haka. Ta cikin duhun ya iso bakin gadon, ya kai zaune cikin lalube ya ɗakko wayarsa ƙarama. Fitilarta ya kunna, tare da ɗaukar file ɗin da Habib ya bashi. Sam ba’a ganin fuskarsa. Sai dai shi yana ganin rubutun file ɗin kasancewar shi ya haska kai tsaye. Sai alamun bathrobe ɗin dake a jikinsa wadda iya inda hasken ya haska kawai ake gani.
“What?!”.
Ya faɗa cikin subucewar baki ganin bayanan na nuna cewar da taimakon mace aka kai musu harin ɗazun. Macen ma ƴar 18 years kacal. Cikin wani irin rawar jiki yay wurgi da file ɗin yana faɗin, “Impossible! Ni! Ni! Ni ne yarinya ƙarama kamar wannan zata hara. Hari irin wanda wani mahaluki bai taɓa samun galabar yimin shi ba. Kuturun ubacan kayyasa????…………✍
*_HHHH anayi muna ɓallar rake na funtuwa mai zaƙi. Alaji Master yaya take ne?????????????. In baka saniba ma yanzu ne wasan zai fara????????????_*
*TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*????????????????????????
*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*
*_NAJI DADI SHINE GARI……_*
*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*
_ILIMI_
_NISHADI_
_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_
*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*
*NA SABUWAR SHEKARAR 2022*
*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*
*SABBIN LABARAI*
*SABUWAR SHEKARA*
*SABON NISHADI*
*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA’AYI NA DABANNE_*
*MAZA ‘YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*
*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.
*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_
*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_
*_ƊABI’AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_
*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_
*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*
09134848107
Littafi daya
1____300
2____400
3____500
4____700
5____1,000 (1k).
*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*????????????????????????????????????????????????
#team ZAFAFA BIYAR????????????????????
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????_*
*_Typing????_*
*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR ISTAGRAM_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
_________________________
*_Ina miƙa sakon ta’aziyya ga ɗaukacin musulmi musamman hausawa na rashin uba kuma jigo, Haziƙi, gwarzo, abin alfaharinmu Sheikh Dr Ahmad bamba. Ya rabbi ka gafarta masa. Ka yafe masa kurakuransa da iyayenmu baki ɗaya. Munyi rashi irin wanda cike gurbinsa abune mai matuƙar wahala a duniyar musulinci. ALLAH ka yafema wannan jarumin dattijan ƙwarai????????????_*
__________________________
*_MG’s SKINCARE_*
*_Ina manyan Mata, da manyan yara masu buqatan gyaran jiki da fata akan tabbaci da ingancin kyawu da aikin me kyau?_*????????
*_To maza kuzo ga mg’s skincare inda sukeda nagartattun sabulai da creams masu kyau da aiki_*
*_mg’s skincare nada black soap dasu molato soap hakama akwai gangariyar sabulu na musamman Mixed na Molato/black soap Wanda hadinsa da aikinsa karshene sbd mun gwada mun tabbatar ????_*????????????????
*_Akwai Kuma herbal whitening black soap Wanda shima aikinsa na musamman ne a gareku????????_*
*_Sai kuma beauty kit gbdy na gyaran jiki, su cream da komai ne acikin shi????????_*
*_Then akwai bridal kit shima abu 6 be aciki Wanda sai angwada za’a San kayan MG skincare qarshe ne agurin aiki._*
_Duk zaku tabbatar da hakanne ta hanyar nemansu ku gwada kuma har sai kun bama wasu labari????????????????_.
Chat
08062991549
07046881166
07067210195
Call
08064532391
Instagram: glow_with_mgs
Facebook:mg’s skincare
Location:kaduna buh we deliver Nationwide
Delivery is not free buh gamasu sari ko wnd yasiya Kaya dayawa kmn 20k above there will be free delivery+ gift
_*Sunada different varieties of frames gamai siyan daya Koh sari*_
_*Sannan muna karban order gamasu hidimar biki kmn dg abinci, snacks, juices nd so on*_
_*Kindly chat with us via 08062991549.*_
________________________
*_Chapter Ten_*
………..Ummi na shigowa falon ta wankama Ammar mari. Lokaci guda falon ya ɗauki tsitt. Hibbah ta zazzaro manyan idanunta waje, jikinta na rawa, dan abinda bai taɓa faruwa ba a tsawon sanin da taima Umminsu. Duk iya ɓacin ran da zata nuna idan sukai mata laifi iyakarta da su faɗa da nasiha tun basu kai haka ba.
Ba Hibbah kawai ba, hatta Yaya Muhammad da Yaya Abubakar sai da wutar kansu ta ɗauke. Hakama Yaya Umar da Yaya Usman da ke ƙoƙarin shigowa falon saboda kiransu da mai-gadi yayi ya sanar musu abinda ke faruwa tun sanda Ammar ke jibgar Junaid. Sai dai suna shigowa gidan motar Ameera na fita zuwa asibiti kai Junaid. Tare kuma suka tafi gaba ɗaya gidan, har da Hajiya mama dake fama da ƙafarta.
Ƙananun duka Ummi ta cigaba da kaima Ammar, hawaye masu zafi suna gangaro mata a kumatu. Ammar dake tsaye ƙiƙam tun marinsa da tai kallonta kawai yakeyi shima hawayen na sakko masa na tausayinta. Yayinda wani murmushi mai ɗaci ke bayyana saman fuskarsa. Ummi ta jawosa ta rungume jikinta tana magana cikin rawar murya, “Miyasa zakai haka Aliyu? Miyasa? Ba nace duk abinda zaku gani ba kuyi kamar baku gani ba.”
Da gudu Hibbah ta zo ta rungume Ummin da Yaya Ammar itama. Gefe Yaya Muhammad ya kauda kansa yana ƙoƙarin ɗauke hawayen da suka ciko idanunsa. Yaya Abubakar ma idanunsa sun kaɗa sunyi jajur. Yaya Umar yafi kowa zuciya a cikinsu, yayinda Yaya Usman duk ya fisu sanyi shi da Yaya Muhammad. A wani irin fusace ya juya zai fita a falon Yaya Usman da yasan halin kayansa yay azamar riƙo hannunsa.